Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 4
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 4: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 4. ............Nunani ta farayi da hannunta tana jifana da…
3,280 words
............Nunani ta farayi da hannunta tana jifana da wani mugun kallo"mommy wannance me aikin. shafa kumatunta hajiyan tayi "eh,itace daughter."Ammafa mommy senaga kamar bazata iya aikinba,kalletafa sanyinta yayi yawa.jifa yanda take tafiya kamar bata da laka. " hmmm,daughter kenan rabu da 'yayan talakawannan idan sunason kudi zagewa sukeyi,suyi aiki.tabe baki tayi bata kara cewa komaiba,amma se kallona takeyi.nidai ina durkushe ina dubansu. Maido da dubanta hajiya tayi gareni ta faramun magana. "Maryam kikacemun sunanki ko? "eh hajiya. "ohk, Aikin dazakiyi agidannan iya part dinnanne,kawai.anjima za'azo a miki bayanin aikin daza kidingayi.ina fata bazan samu matsala dakeba,kinga wadannan,ta nunamun duka matasan dake dakin.ahankali na dago ina dubansu.taci gaba da magana.dukansu 'yayanane,idan sukaje aiki suka dawo anan suke zama,saboda haka kome suka saki kiyi,banason bacin ransu kokadan dan haka kibisu sau da kafa. "Insha Allah hajiya zankiyaye. nafada cikin sanyin murya ta."zaki iya komawa,dakinki.harna mike sekuma naga dacewar naje nagaida 'yayannata. Gabansu naje na durkusa nace. "ina wuninku."Daga Wanda yadago ya wurgamun kallon banza,seme bina da harara,da kallon tsana.guda dayane Wanda kamarsa ta bambamta danasu.ya ajiye wayar hannunsa,fuskarsa dauke da fara'a ya amsamun gaisuwata.harda 'yan tambayoyi yamun.tare damun fatan nasara arayuwata.naji dadi sosai yanda be kyamaceniba kamar sauran 'yan uwansa.mikewa nayi jikina a matukar sanyaye na fara tafiya.karaf idona ya hadu Dana wannan budurwar.wani kallon tsana naga tana jifana dashi se wani yamutsa fuska takeyi tamkar taga kashi. "Jibeta yanda take tafiya tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki.muryar budurwar na tsinkayo tana fadar haka.kwashewa da dariya naji sunyi,"to kekuwa suhailat bataci ta koshiba ai dole kiganta haka.da sauri na karasa dakin danasauka,dan bazance nawaba.idona ya cicciko da kwalla.saboda na fuskanci mutanennan basusan darajar dan Adam.yanzu haka zanyi rayuwa acikinsu.tsanata da kyamata kawai nake hangowa a atattare dasu,nabar kyarar gwaggo Ashe nanma zan tadda wata.hawayene yafara zubowa Daga idanuwana,na tausayin rayuwata.
Turo kofar dakin akayi,da sauri na dago ina kallo bakin kofar.wata 'yar tsohuwace domin ko tantama banayi tayi jika dani.sallama tayi na'amsa mata,ina goge hawayen fuskata.tsugunnawa nayi cikin girmamawa na gaisheta.murmushi tamun,tana amsamun gaisuwata.kamo hannuna tayi muka zauna a bakin gado."yarinya yaya sunanki. "Sunana maryam. "Allah sarki,maryama ta baban gida,.ni kuma sunana talatu nice babba a masu aikin gidannan,nice wadda hajiya ta turo in miki bayanin aikin dazakiyi amma kafin sannan,idan bazaki damuba inason jin labarinki,wato tarihin rayuwarki. Dasauri na dago ina mata kallon mamaki. "mamaki kikeyi ko 'yannan,na shigo na tarar dake kina kuka,Daga gani dole akayi miki a aikinnan,inason jin labarin kine domin insan ta inda zan iya taimakonki. shiru nayi ina juya maganganunta araina,banason tuno abubuwan da suka faru a baya arayuwata,amma kuma a kallo daya danayiwa matar ta shiga raina,kuma bazan iya mata musuba,kodan kasancewarta babbace. " Baaba,labarina yanada yawa amma zan takaita inbakishi. "Yawwa yarinya,dafatan bantakuramikiba,inason sanin wani abune Daga gareki,domin nima inason sanar dake wani Abu game da gidannan.numfashi naja tare da gyara zama na farabawa baaba talatu tabarina.
***************
"Sunana maryam,na tashi na ganni a hannun kakata,wadda ake kira inna.a unguwar darmanawa dake nan kano.innata itace ta haifi mahaifiyata.ita kuma mahaifiyata ta rasune a wajen haihuwata hakan yasa bansantaba.innata kawai nasani.mahaifina kuma tunda cikina,inna tacemun aka nemeshi aka rasa.dama badan kasarnan bane dan Niger ne.bashi da kowa yazo kasarnan neman kudi.anan cikin garin kano yake sana'arsa.innata tacemun,itadai batasan sanda suka fara soyayya da mahaifiyata ba,kawaidai da mahaifinta yace ta fito da miji tace shitakeso,duk da tarin masoyan datake dasu,domin mahaifiyata kyakkyawace.kyawun asalin Fulani.
Nanfa inna tace bata isa ta auri,Wanda ba'ason asalinsaba,ita kuma mahaifiyata ta dage dole seshi takeso.inna kuma ta kafe tace sedai ta zaba,ko shi ita.amma mahaifiyata taki hakura dashi,har ciwo ne ya kwantar da ita.ganin tana kokarin mutuwa mahaifinta yace yabata shi.ita kuma inna tace be isaba.sedai idan mahaifiyata ta mutu.shikuma mahaifinta yace shiya haifi maryam,dan haka Wanda takeso ze bata baze mata auran doleba,kokuma yanaji yana gani ita kadai din dayake da ita yarasata.dama ita kadaice 'yarsu.inna tanaji tana gani aka daura auran mahaifiyata da mahaifina.inna tacemun,kwata kwata batason auran tayi iya yinta kar ayi auran,amma Allah yayi dole se'anyi.haka inna ta hakura,amma tace babu ita babu mahaifiyata. Bayan bikin befi da wata dayaba,Allah yayiwa kakana rasuwa.halin dasu inna suka shiga baze misaltuba.a lokacin mahaifiyata tayi Dana sanin bijirewa inna,tazo tana kukanta ta nemi yafiyarta domin ta gane duniyar ba gidan zama bace.itama inna a lokacin jikinta yayi sanyi,hakan yasa ta sassauta mata,amma bata sakko dukaba.a lokacinma tanata fama da laulayin dan karamin ciki.
Haka sukaciga da rayuwa,tsawon shekara uku.inna tacemun mahaifiyata bata taba zuwa ta kawo mata karar mahaifinaba,akan ya mata wani Abu ba daidai ba koya muzguna mata.kana ganin yanda suke rayuwama,kasan cikin kwanciyar hankali da jin dadi sukeyinta.duk da mahaifiyata Daga ta samu ciki baya wuce wata uku ya bare.amma kokadan mahaifina be nuna damuwarsaba,ko kuma ya canzawa mahaifiyata.ita cema take damuwa akan haka, shikuma yana kwantar mata da hankali.
Tayi barin ciki,yakai biyar Allah yayi dai zanzo duniya. Mahaifiyata tasha wuya akan cikina tamkar zata mutu haka take shan wahala.hakan yasa inna ta dakkota ta dawo da ita gidanta.duk shima suna tunanin ze bare kamar sauran.amma abun mamaki ana wuce wata uku,hudu se ciwo ya dauke,ta komar sumul da ita.ta koma gidanta suka cigaba da rainon cikina ita da mahaifina.soyayya sosai mahaifina yake nunawa cikin,tun lokacin yaketa siyan kayan haihuwa. Saboda murnar wannan cikin ya tsaya tunda haryakai wata shida.mahaifina dama akusuwar kantin kwari yake a shagon wani uban gidansa.inna tace mun,yana samu sosai.yanada rufin asirinsa.wata rana yaje kasuwa mahaifiyata taga har dare bedawoba.shida yake dawowa kafin magriba.hankalinta ya tashi,ta kira duk Wanda take tunanin suna tare an tabbatar mata daya taho gida lafiya kalau.shiru_shiru tana jiransa,amma har wajen goman dare shiru,bedawoba.zarar hijabinta tayi ta nufi gidan inna tana kuka ta sanar mata.itama inna ta girgiza sosai,amma ta daure ta kwantar wada mahaifiyata hankali.shiru_shiru har cikin dare bedawoba.abun kamar wasa har washegari.duk inda ake tunanin za'a sameshi anje bayanan.hanakalin mahaifiyatafa ya tashi bataci batasha se aikin kuka.tun ana saran ganinsa har kwanaki suka shude babu shi,babu labarinsa.nan maganganu suka dinga yawo akan ya gudu yabar mahaifiyata,dama abunda yasa yake zaune da ita danbata haihu bane,yanzu kuma tunda yaga zata haihu shine ya gudu ya barta.bayason wahalar 'yaya.tundaga ranar mahaifiyata ta koma,bata da aiki se kuka,tun inna tana rarrshinta harta zuba mata ido.haka tacigaba da rainon cikina cikin bakin ciki.ranar wata juma'a da yamma ta haifeni.a gida ta haihu.bayan an gama gyarata aka miko mata ni.inna tacemun kamarmu daya,hakan yasa ta kuramun ido tana kallonna.idanuwanta cike da hawaye.lafiya kalau ta haihu,amma bayan befi awa biyuba, wani ciwon cikina me tsanani ya kamata.ana kokarin kaita asibiti,tace kada su wahalar da Kansu ita mutuwa zatayi,amma tabar wasiyya,idan Allah yarayani a bani wata takarda data rubuta tana cikin kayanta.kuma asamun sunanta wato maryama,saboda shine sunan da mahaifina yace mata zesaka idan ya haifi diya mace.su inna basu kulataba da ita da maganganunta,suka dauketa zasu kaita asibiti domin sunyi tunanin zafin ciwone yasata fadar haka.amma kafin sukaiga asibitin Allah ya mata rasuwa.
Inna tayi kuka,tamkar ranta ze fita.mutuwar tilon yartata bakaramin dukan ta tayiba.ta gane rabonane yasa mahaifiyata ta dage seta auri mahaifina. Hakan yasa tayafe mata duniya da lahira.ita kanta shedace akan mahaifiya mutumin kirkine,kawai dai matsalarsa rashin sanin asalinsa.inna ta rungume ni,tacigaba da rainona cikin so da tsantsar kauna,tana jina tamkar maryam dinta data rasa.inna bata boyemun sunaba maryam take kirana dashi.
Nataso cikin gata da kulawa a wajen innata.innata bata rageni da komaiba.abincin siyarwa,dasu sobo da kunun aya, shine sana'ar da inna takeyi take rufa mana asiri.duk da girma yafara kamata.komai nakeso innata tanamun,tasani a private school. Tare da islamiyya.Burina arayuwata,inyi karatu me zurfi Insamu aikinyi,in hutar da inna Daga wannan wahalar datakeyi,kullum tana bakin wuta.inna bata da 'yan uwa a garinnan,yan uwanta duk suna can kauye a garinsu.iyayenta kuma Allah ya musu rasuwa. 'Yar uwarta guda dayace,da suke uwa daya,uba daya wato gwaggo.
Amma nidai tunda naso so daya nataba ganin gwaggo a gidan innata.innata batamun irin rikonnan da'ake cewa rikon kakaba,ta shagwabaniba kota sangartani.ta bani tarbiyya ingantacciya.tun ina karama take nunamun rayuwa,takemun nasiha,akan narike mutuncina.nakasance me hakuri a duk halin Dana shiga.bansan kowaba,se innata.itace uwata itace ubana,itace dangina.itace gatana.shakuwa me karfi,tare da tsantsar kaunace a tsakanina da innata.dominni a lokacinma saboda yarintata,bansan ba itace ta haifeniba.innata macece,ta mutane saboda kirkinta da mutunta dan'adam.
Dogon Numfashi,naja ina duban baaba talatu,nace "zan takaita miki labarinane,saboda yanayin lokaci.domin idannace zan fayyace miki komai,semu kwana anan bangama mikiba. "Tom shikenan maryam,kici gaba domin inason jin karshen labarinnannaki.
"Wata rana,nadawo Daga school, da misalin karfe biyu na rana.a lokacin shekarata goma shabiyu. Ina J.S.S 1. Da sallamata na shigo gidan da murnarta ina kwalawa inna kira,kamar kodayaushe,idanna dawo.turus na tsaya ganin banga innata a kitchen ba,agurin saida abincin ta.babu alamun ma tayi girkin yau.dasauri na nufi dakin da muke kwana ina kwala mata kira.Kudundune na hangota akan gado ta lulluba da abun rufarmu.jakar makarantata na cillar na nufi kan gadon.ina cigaba da kiranta.yaye bargon data lullaba nayi,jikinta se rawar Dari yake.wuyanta na taba naji zafi zau. "Innata baki da lafiya meyasameki meke damunki.na tambayeta kwalla na taruwa a idona.Bakinta ta fara motsawa alamun tanason tace wani Abu,amma maganar taki fita.jikinta serawa yake hakoranta na hadewa kamar me jijjiga.bantaba ganinta cikin ciwo irin hakaba.kuka na farayi ina girgizata.tare da tambayarta abunda yake damunta,amma inna ta kasa magana.abunda yafi tsoratani yanda naga idanuwanta sun juye.gashi gida ba kowa dagani se ita.
Wani tunanine yazomun cikin zuciyata.dasauri na tashi nanufi gidan su umman saleemat,dake jikin gidanmu. Umma! Umma! Nashiga kwala mata kira. "Na'am maryam wannan kiran hakafa,lafiya? "Umma innace bata da lafiya,tana kwance jikinta se rawa yakeyi. "subhanallah, shiyasa yau banji hayaniyar masu siyayyar abinciba,muje inga jikinnata.bari in dakko hijabina........✍️
```sannu bata hana zuwa,sedai adade ba'ajeba.kada kudamu da sannu zamuzo inda kukeso.```🥰😘
Meson complete Whatsapp 08166674823
*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*Bismillahirrahmanirrahim*
0️⃣7️⃣
..............Muna shiga dakin nida umma,mukatarar inna har lokacin jikinta se rawa yakeyi.dasauri umma ta karasa kanta dagota tayi taji jikinnata yayi zafi sosai,"maryam debomun ruwa abaho,kitaho da towel. "To umma" har lokacin kuka kawai nakeyi.da sauri na debo ruwan nakawo mata.harta fara cirewa inna rigarta,kara umartata tayi naje nakirawo wani isa me chemist dake bakin layinmu.
Cikin yan mintuna muka iso gidan nida Dr isah,a lokacin har umma ta gama gasawa inna jikinta.dubata yayi ya mata allura tare da sanya mata Karin ruwa.se alokacin nasaki wata ajiyar zuciya.saboda ganin jikin innata ya dena rawa,numfashinta yana fita dai_dai alamun ta samu bacci.magunguna ya rubuta ya bani yace kafin tatashi naje na siyo,kuma atabbatar tasha koda ruwan tea ne idan ta tashi.ranar ninayi duka aikin gida.saboda inna babu abun data iyayi.abinci kuma ummace ta kawo mana.washegari, jikin inna tatashi dashi da sauki.amma bata warke duka ba. Inna tayi_tayi inje school,amma nace mata nibazanjeba.seta kara samun sauki.haka ta hakura ta kyaleni.bayan nagama share_share da wanke_wanke.muna zaune adaki da inna,ta dubeni tace.
"Maryam,ina horanki daki kasance me juriya,akan duk halin dakika tsinci kanki aciki.komai runtsi komai wahala kada ki zubar da mutuncinki,domin mutuncinki shine kadararki.koda na mutu,kada ki koma kauye wajen 'yan uwana,kici gaba da zama anan saboda kisamu ingantaccen ilimi,saboda iliminkine kadai ze taimakeki a rayuwarki.nasiha sosai inna tamun me ratsa zuciya me kama da wasiyya.rungumeta nayi ina kuka nace."inna kidena fadar haka bazaki mutuba,insha Allah harse kinga yayana,kinci gajiyar ilimin da kika dorani akai.lallashina kawai inna tafarayi.itama tana zubar da hawaye.
Bayan kwana 2 inna ta warke rass,tamkar ba itaba.hakan yasa na koma makarantata.naci gaba da karatuna.sekuma wata sabuwa,bayan befi wata biyuba inna ta fara wani irin ciwo,cuta me tsanani.ko hannunta bata iya dagawa.sedai akwantar atayar.gashi babu me jinyarta ni kuma alokacin nayi kankanta.ummace take dawainiya damu da sauran makotan arziki.'yan uwan innata na kauye sunzo amma basu wani jimaba,suka koma.ciwofa yakici yaki cinyewa.babansu saleemat ne yakai inna asibiti.aiko ana zuwa suka bata gado.babu me jinyar inna,umma kuma ga 'yayanta ga aikin gida,baze yiyu tazo asibiti jinyaba.hakan yasa akace dole wani Dan uwan inna seyazo jinyarta. Dakyar wani kanin babansu inna,yasamu gwaggo a yawon gagarinta.da farkoma datazo cewa tayi baza ta iya jinyaba,amma kuma kome tatuna Daga baya kuma seta amince.nidai banda insaka inna agaba ina kuka babu abunda nakeyi.makarantama dakyar umma ta lallabani na koma.inna tayi watanni a asibiti,a canza mata wannan a maidata wannan.gaba daya dan kudin data mallaka duk ya kare a yawon asibiti.amma cuta dai tananan a jikinta.ahaka har na shiga J.S.S 2,nida saleemat.bayan dogon lokaci da inna ta dauka tana jinya.cikin ikon Allah se sauki yafara samuwa har aka sallamota muka dawo gida.murna a gurina kamar me innata ta warke. A lokacin gwaggo ta nuna tanason tafiya amma inna ta hanata.taitai mata fada akan rayuwar datakeyi da girmanta bane dorewa bace.gwaggo tayi aure_aure,amma bata taba haihuwaba.kuma duk auran datayi bata jimawa take fitowa,saboda masifarta da rashin mutuncinta ba kowa ze iya zama da itaba.gashi taita Tarawa mutum kawayenta 'yan duniya a gida.ta yarda ta zauna damu da kyar,duk da badadin zama mukeji da itaba. amma,kullum.seta fice yawonta.inna sedai kawai ta bita da addu'ar shiriya.
Watarana,danar dabazan taba mantawa da itaba arayuwata, na dawo daga school da murnata,saboda a makaranta anzabemu nida saleemat acikin wadanda zasuyi J.S.S.C.E EXAM. Saboda kokarinmu.base munyi j ss3,ba kawai zamu tafi senior class.kamar kodayaushe idannadawo daga makaranta gwaggo batanan,yauma haka,dakinmu na nufa,inna tana kan sallaya azaune tana lazimi. "Innata! Innata! na shiga kwada mata kira tare da fadawa jikinta. "Oh ni,fateemah maryam koyaushe zaki girma.dariya nayi nace "kai inna na girma mana,amma agurinkine bana girma,tunda ni kadaice bani da kani.murmushi inna tayi ta shafa kaina tace. " idan baki da kani maryam,ai wataran uwa zaki zama,dan ko yanzu akai miki aure zama zakiyi. Rufe fuskata nayi da hannuna,cikin jin kunya. "Kai inna aure kuma,nidai ban girmaba.sonake nayi karatu me zurfi,na zama likita idan baki da lafiya base munje asibitiba,nizan baki magani da kaina,in miki allura. Murmushi inna ta karayi tace."Allah yasa maryam dita,Allah ya cika miki burinki,nima burina naga kinyi karatunnan maryam. " Ameen innata,yawwa inna,nazo miki da wani daddadan albishir. A makaranta yau aka kawo mana form din makarantar science ta kano,shine aka zabemu hardani da saleemat,nanda watanni kadan zamu zana. "Wacce makarantar science din kuma maryam?. "makarantar da usainan bayan gida tayi me fararen uniform da ratsin Kore. " to aike,maryam naga yanzu aji biyu kike,shine kuma za'akaiki babbar sakandire,ai bakiyi aji uku ba. "Principal din makarantarmuce,ta kirawo mu harda 'yan aji 3,shine aka mana wata 'yar jarabawa kuma naci,makina haryafi na 'yan aji ukun. "Toh shikenan maryam,Allah yabada sa'a ya taimaka. "Ameen inna,nafadi hakan ina mikewa zuciyata cike da murna.na fara cire uniform dina.wani kallo naga inna tana bina dashi Wanda nakasa gane kona mene. " inna lafiya naga kinamun wannan kallon. "Babu komai maryam.mikewa tayi taci gaba da jero nafilfilolinta.lafiya kalau muka wuni da inna,munata hirarmu cikin nishadi. Amma anayin magriba,tacemun kanta yana mata ciwo.ta kwanta,dakyar ta samu tayi sallar isha'i. Ta kara kwanciya.
Cikin dare naji inna tana wani irin nishi,sama_sama nakeji cikin baccina,tun tanayi a hankali harnaji ya hanani bacci.tashi nayi na lalubi makunnin kwan dakin na kunna.
Inna nagani,hannunta dafe da kirjinta,numfashinta na fita dakyar."inna meyafaru,meyasameki.innalillahi.......kanta kawai take girgizamun tanamun nuni da hannunta,tana kokarin yimun magana amma ta kasa.dakyar nagane ruwa take bukata.da sauri na fita na dakko mata me sanyi na kawo mata. Seda tashanye Tass,natambayeta na karo mata tacemun A'a.
Gyara mata kwanciyarta nayi,saboda ganin numfashinta ya fara daidaita.ina jera mata sannu.hannunna ta kama cikin muryar marasa lafiya tafaramun magana."maryam! Kidauki duk kaddarar datazo miki arayuwa,kada ki butulcewa Allah.jikina yana bani bazan kara wasu kwanaki masu yawaba.ki riki gaskiya aduk inda kike,sannan kuma jigon zaman duniya,hakuri. Kiduba kasan gadona,akwai wata akwatin karfe.cikin wata jaka,zakiga wata takarda da wasu hotuna.hotunan mahaifinkine Dana mahaifiyarki,takardar kuma mahaifiyar kice ta rubuta tace abaki.kirjina yanamun ciwo sosai maryam,tamkar andoramun dutse haka nake jinsa inaji ajikina ajalin......da sauri na rufewa inna bakinta ina sakin kuka,"inna kidena cewa haka,bazaki mutu yanzu ba insha Allah,kinyi cutama datafi wannan kuma gashi kin warke,wannanma insha Allah nasan zaki warke. Inna ta bude baki zatamun magana wani tarine ya sarketa,ta fara yinsa ba kakkautawa.tamkar numfashinta ze fita.da gudu na fice daga dakin na nufi dakin da gwaggo take kwana,na fara bubbuga mata kofa da karfi. Dakyar gwaggo ta tashi,cikin masifa take tambayata menene.cikin kuka na mata bayani tataimakeni mukai inna asibiti.amma gwaggo seta rufeni da masifa tana zagina,rokonta nakamayi amma Sam gwaggo taki yarda tace bacci takeji da safe, akaita asibitin babu abunda zefitar da ita cikin darennan.jikina a sanyaye na koma dakinmu.shiru na tarar da inna idonta,a rufe.abunka da yarinta,sena sauke ajiyar zuciya ina cewa,tama samu bacci ya dauketa. Bargo na lulluba mata,nima na kwanta,amma Sam nakasa bacci juyi kawai nakeyi.har asuba. Amma abun mamaki senaga inna bata tashi sallahba,kyaleta nayi saboda naga bata da lafiya.har gari yafara haske inna bata tashiba.kuma abunda yaban mamaki yanda ta kwanta haka take ko juyi batayiba. Tashinta na farayi ina bubbuga jikinta,amma shiru inna ko motsi.hannunta na daga naji yakara nauyi,ina sakinshi naji ya koma sharaf.wata irin bugawa zuciyata tayi,wani gumi yafara tsatstsafomun.kiran sunanta na farayi da karfi ina jijjigata da dukkan karfina,amma shiru.ihu na kurma,na nufin dakin gwaggo ina bugawa inacemata tazo inna ta suma,mukaita asibiti.amma gwaggo tana fitowa ta tsinkamun mari, wai tun cikin dare na hanata bacci.idan ban tafi na bata guriba seta babballani.
Ina gunjin kuka,na zare sakatar gidanmu,na nufi gidansu saleemat.gidan abude yake,idan babansu yaje masallaci baya kara rufewa.ko sallama banyiba saboda rudewa kafata ko takalmi babu,umma tana kokarin hura gawayi saboda yan makaranta ta hangoni nashigo a hargitse. "Maryam lafiya dasassafennan? "Umma kitaimakamun mukai inna asibiti ta suma,kuma babu inda yake motsi ajikint...ai umma bata bari na karasaba tayi hanyar fita,dama da hijabinta ajikinta.bin bayanta nayi.muna zuwa naga ta kara kunnanta akan hancin inna, duddubata naga tanayi.batacemun komaiba,kawai gani nayi taja bargo ta lullube inna har fuskarta.
Janyoni tayi jikinta idanuwanta na zubar da hawaye,sonake nayi magana amma na kasa,saboda nidai nasan Wanda ya mutu kadai ake lullubewa.dakyar na iya tambayar umma cikin rawar murya."umma,bangane me hakan yake nufiba,umma dan Allah kada kicemun innata ta mutu,wlh nima mutuwa zanyi.cikin San kwantarmun da hankali,umma tace"innarki bata mutuba,bari na fadawa baban salermah,yasamo mota mukaita asibiti. Ajiyar zuciya na sauke.umma ta rabani da jikinta ta fice daga dakin.intakaice miki zance,baban saleemah yazo,da wani likita har dakin inna,karshe dai likitan ya tabbarmana,Allah ya karbi baiwarsa inna,ya mata rasuwa.
Cakumar likinta nayi,ina kuka nace."karyane innta bata mutuba,innata bazata taba mutuwa tabarniba.janyeni umma tayi daga jikinsa,itama tana kuka tace."haba maryam, kefa musulmace,kuma kinsan dukkan merai mamacine,ki yarda da kaddara,yanzu inna bata bukatar kukanki addu'arki kawai take bukata. "Yanzu umma kema kinyarda inna ta mutu,wlh bata mutuba suma tayi,damafa bata da lafiya mukaita asibiti,wancan karanma haka tayi,umma kitaimakeni mukaita asibiti,nasan zata tashi,inna bazata mutu ta barniba.kuka kawai nakeyi na fitar hankali,ina maganganu marasa kan gado.hannuna umma ta kama muka fice daga dakin. Duk wannan abun da akeyi gwaggo tana daki tana barci,har lokacin bata fitoba.
Kafin karfe 7 na safe,gidanmu ya cika da mutane anata koke koke,makuta da abokanan arziki domin inna ta kowace,kowa seyabonta yakeyi.se'alokacin gwaggo ta fito ta kama kukan munafurcinta,babu Wanda yabi ta kanta. Nidai ina zaune nayi jigum,kukanma babu ya dauke,zuciyata ta kekeshe.duk da ni yarinyace a lokacin amma nasan dacin mutuwa.bin kowa nake da kallo,domin ni banyarda inna ta rasuba,nasan suma tayi kuma zata farfado. Seda 'yan kauyenmu suka karaso sannan,aka mata sutura.nidai ina daki umma ta rikeni gam taki sakina.wata 'yar uwarsu innace,dasukazo daga kauye tazo ta kama hannuna,ta kaini dakin inna.wata irin harbawa zuciyata tayi saboda ganin inna,kwance a cikin makara,kwace hannuna nayi na fada kan makarar ina sakin kuka."wayyo innata,dan Allah kitashi,karki tafi ki barni,kitashi kice musu baki mutuba,inna bani da kowa seke,meyasa zaki tafi kibarni,kece uwata,kece ubana,kekadai nake gani inji dadi araina,innaaaa!!!..... Kuka yaci karfina. Janyeni akayi,su baban saleemah da wasu 'yan uwan inna,suka kinkimi makarar. Wani karfine yazomun na tashi da sauri, na kankame makarar,ina ihu ina fadin baza'a fitarmun da innataba,amma inaji ina gani aka janyeni aka ficemun,da sanyin idaniyata,me tallafar rayuwata.