Abunda ka shuka complete hausa novel - Chapter 5
Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 5: Abunda ka shuka complete hausa novel Chapter 5. Bankara sanin meyafaruba,se farkawa nayi na ganni akan…
3,040 words
Bankara sanin meyafaruba,se farkawa nayi na ganni akan cinyar umma,tanamun firfita,idanta yayi luhu_luhu alamun taci kuka ta koshi.yunkurawa nayi dakyar,na tashi zaune.sannu mutanen dake dakin suka kama yimun,kaina kawai na iya daga musu.saboda wata muguwar sarawa da kaina yakemun.dole na hakura nadau dangana,akan tabbas inna ta rasu.amma tashin hankalin da rudanin da zuciyata ta shiga baze misaltuba.kowa yazo ya ganni seya zubarmun da hawaye.nasiha sosai umma tamun.akan yadda da kaddara.nayi kukan fili Dana zuciya.Mara adadi akan rashin inna.haka akayi sadakar uku aka watse,a lokacin mutuwar inna tadawomun sabuwa.bana ci bana sha,se aikin kuka.dakyar umma take sani nakecin kwayoyin abinci,suma jinsu nakeyi tamkar madaci.komai ya tsayamun cak.kunci da damuwa sun taru sun mun yawa.hakan ya haifarmun da matsanancin ciwon kai,Wanda ko idona dakyar nake motsawa.karshedai har kwanciya nayi a gadon asibiti saboda ciwo,mutuwar gwaggo ta dakeni sosai,kuma har yau bata bar dukanaba,idannatunota inajin tamkar yau abunyafaru.
Ahankali ahankali komai yake wucewa na duniya,haka innata ta shude ta zama sedai tarihinta,ahankali rashinta yafara bin jikina,nabawa zuciyata hakuri da dangana akan rashin innata.addu'a kawai nake mata nasan shine abunda tafi bukata.'yan uwan inna,sunso tafiya dani kauye amma gwaggo tace"zata rikeni anan,saboda makaranta ta,badan sunsoba,suka hakura suka barni,awajenta.
Gwaggo ta gaje,gidan innata,tagaje komai nata.ta koma dakinta ma da zama ni kuma ta koroni dayan dakin.gwaggo bata bani abinci,babu ruwanta da cina balle shana.shargoriyarta kawai takeyi.tatara kawayenta su cika gidan,su kunna kida suyita rawa wataranma har maza take kawowa.mutuwar inna ko'ajikinta.umma ce,take bani abinci da duk wani Abu danake bukata.kudin makaranta kuma babansu saleemat ne yake bamu tare.ahaka rayuwa taita tafiyarmun babu dadi kokadan.cikin ikon Allah muka zana jarrabawa,kuma duk munci nida saleemat.nayi farin ciki sosai,danaci, kuma naji dadi.shine Abu na farko daya sanyayamun rai bayan mutuwar inna.amma naso inna tananan tatayani murna. Babansu salermat ne yamana,komai tun daga uniform,littattafai da duk abubuwan da'ake bukata.duk da shima bawani karfine dashiba,sedai rufin asirin Allah.
Nafara makaranta,kuma inajin dadinta sosai,tana debemun kewa.amma term 2 kawai naje,gwaggo ta hana.tacemun tagaji da zama ba Sana'a dole inzauna,indinga mata Sana'a agida.nayi kuka,na roki gwaggo,amma gwaggo taki hakura.akan haka har fada sukayi da umma.baban saleemat yace"umma ta kyaleta saboda shi bayason fitina.tun daga lokacin gwaggo ta maidani tamkar jaka,ko wata baiwa.nice,wankinta,shara,wanke_wanke,girkin gida dana kayan sana'arta.baruwanta da kankantar shekaruna haka take tulamun uban aiki.bani da Hutu kwata_kwata se cikin dare.Tun inayi ina kuka saboda rashin sabo da gajiya,harna saba.mugunta kala_kala nashata a wajen gwaggo,ta rabani da kowa,har umma ta hanani zuwa wajen ta,sedai na saci hanya naje,bata saniba.naci wahala bakadanba,awajen gwaggo.duk abunda zan mata,bata gani sedai ta sakamun,da duka koda zagi,ko mugun alkaba'i.gwaggo bata da imani,kokadan muguwace ta karshe,kanta kawai tasani arayuwarta.indai zata samu kudi ko menene zatayi,makota kowa kuka yakeyi da ita.saboda munanan dabi'unta.
Ajiyar zuciya,nasauke ina duban baaba talatu,data kuramun ido kawai tana saurarona,idanuwanta na zubar da hawaye.nima hawayen fuskata na share,nace"wannan shine takaitaccen labarina.naso fayyace miki komai,amma lokaci baze barmuba,kuma banason tuno wasu abubuwan da suka faru dani.
"Gaskiya,maryam kinga rayuwa tunkina yar karamarki,labarinki akwai abun tausayi,Allah yajikan innarki da mahaifiyarki.mahaifinki kuma idan har yana raye Allah ya bayyana miki shi,da gaggawa. "Ameen baaba,nagode. "to,amma maryam wayakawoki gidannan aikatau?. "Wata kawar gwaggoce lami,ta dakkoni daga gida,amma ba ita ta kawoniba wata hajiya lamice daban. Jinjina kai talatu tayi,tabbas nasan hajiya lamin,mutuniyar hajiyace sosai.Mikewa baaba,talatu tayi tana fadin,"muje muyi sallah kinga har anyi isha'i.sena fada miki aikinki a gidannan,da kuma takaitaccen tarihin gidan,kafin masu gidan su fito cin abincin dare.
Bayan mun idar da sallah,talatu ta gyara zamanta ta fara bani labarin gidan."kamar yadda kika sani,sunan me gidannan alh.sulaiman menasara.fitaccen dan kasuwane,Wanda yake da shaguna a kasuwannin garinnan da kuma kamfanoni da dama.alh.mutumin kirkine,gashi da kyauta kuma shi baya wulakanta talaka.sedai kuma gaskiya bashida iko da gidansa,domin matarsa tafi karfinsa juyasa takeyi, abunda tace shiza'ayi a gidannan.ita kuma hajiya,gaskiya batasan talaka,ya rabeta.idan kazo da Neman taimako zata taimaka maka,amma fa ita Sam bata Hulda da talaka.macece ita meson a girmamata,ana nuna mata kuma ita tafi kowa.gata da bala'in son 'ya'ya,kamar me.idan kinaso Ku shirya da ita to kiso 'ya'yanta.wadannan samarin dakika gani duka 'ya'yantane.kome zasuyi mara kyau bata kwabarsu,akwaima daya babbansu me suna mustapha,Wanda hajiya duka tafi sonsa agidannan,tamkarma tsoransa takeji.tana masifar sonsa,bata boye soyayyar datake masa. Duka 'yayan,gidannan basu da mutunci,nidinnan dakika ganni da girmana,dakamun tsawa sukeyi.guda dayane acikinsu me suna sadiq,shine na 2,shikadaine yayo halin babansa,yanda kamarsa take daban haka halinsa,yake daban.domin shi kowa nasane,kuma baya wulakanta mutane,kamar sauran 'yan uwansa. Se kuma uwar gayya,wato suhailat,taci uwar kowa a rashin kunya da wulakanta mutane a gidannan. Bata tsoron kowa,duk girmanka idan ka mata badaidaiba setace zata tsinka maka mari.mustapha ne kadai,take tsoro kuma take shayi agidanna.shine Wanda zata aura kuma.ita 'yar kanwar hajiyace,mahaifinta kuma kanin alhajine.ita kadai suka haifa,ankawota yaye gidannan,iyayenta sunyi tafiya sukayi hadari Allah ya musu rasuwa.hakan yasa zamanta yadawo gidannan gaba daya.hajiya da alh,da sauran yayyenta suka dauki son duniya suka Dora mata.kasancewarta ita kadaice mace. Ki lura,kisan irin zaman dazakiyi da kowa,domin yaran gidannan basu da mutunci ko kadan,wulakanta mutum ba komai bane agurinsu.dayannan Dana gaya miki shikadaine me hali na gari.sekuma babbansu,Wanda shi tsabar miskilancinsama ba'a gane halinsa.kinganninan nafi shekara 20 ina aiki agidannan, amma bazance miki ga abunda yafiso da Wanda bayasoba.wannan shine halayensu atakaice.
Ajiyar zuciya na sauke,nace." Toh baaba,nagode sosai kuma insha Allah zan zauna da kowa daidai da halinsa. "Yawwa yarinya,sekuma maganar aikin daza kidingayi.zaki dinga gyara dakin hajiya Dana suhailat.da kuma duka falukan dake part din nan.se wanke_wanke.amma banda girki kuku ne, yake girki,kekuma idan suka hallara zasu ci abinci zaki dinga saving dinsu.sekuma wani aikin idan wani yagadama yasakaki dankaran Kansa. "shikenan baba talatu nagode sosai.Allah yasaka da alkhairi. Mikewa talatu tayi,har ta kai bakin kofa bankuma San meta tunaba, naga ta juyo ta dawo ta zauna.
"maryam! Takirawoni,cikin wata irin murya bata jira na'amsaba taci gaba da magana,tunda naganki naji kin shiga raina,kuma naga bakiyi kama da irin 'yan kauyen da'ake kawosu aikatauba,dakika bani labarinki naji wani matsanancin tausayinki ya kamani,hakan yasa na kudiri niyyar taimakonki,kin rabu da masifar gwaggo,to nanma akwai wata babbar masifar.zanfada miki wani sirri na gidannan Wanda ba kowane yasanshiba,ko wasu masu aikin gidannan basu saniba,balle wani na waje.amma sekinmun alkawarin idanna fada miki bazakiyi yunkurin barin gidannanba.rasssss!!! Gabana yayanke ya fadi,duk da bansan meneneba,amma daga ji nasan ba'abun dadibane. "Insha Allah baaba,bazanyi yunkurin guduwaba, na miki alkawari."kinsandai nauyin alkawari,kada kikarya. "Insha Allah,baaba.nafadi haka cikin zakuwar jin mezata cemun. Dogon numfashi baaba talatu taja,tace. "Hajiya bata taba daukar babbar mace a matsayin me aikin part dinnanba,tafison yarinya karama kamarkinnan.kuma duk yarinyar da'aka kawota.aikatau gidanna,sedai a wayi gari aga anmata fyade,anyiwa 'yan mata masu aiki sama da 10,haka agidannan, kuma duk wadda aka mata fyaden bata jimawa take mutuwa.......✍️ Meson complete Whatsapp 08166674823
*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
* *Bismillahirrahmanirrahim*
0️⃣8️⃣
.............mikewa tsaye nayi cikin tsananin kaduwa da razana."innalillahi,wa'inna'ilaihirraji'un.naita maimaitawa saboda bugawar da zuciya takemun,tamkar zata Faso kirjina ta fito,haka nake jinta.mikewa talatu tayi ta kama,hannuna ta kara zaunar dani. "Maryam,ki kwantar da hankalinki,insha Allahu hakan baze faru akankiba.dasauri na dago ina dubanta.gyadamun kai tayi alamun tabbatarwa.taci gaba da bayaninta."ba'ayiwa kowacce yarinya fyade setayi watanni,kuma abunda ze baki mamaki,ba'asan Wanda yakeyin fyadenba.duk da yaran gidannan basaji,rayuwarsu gaba daya a turai sukayita.a can suke karatunsu gaba daya,sesun gama karatu uban yake dawo dasu nan,suyi aiki.duk da basasan zaman kasarnan kokadan,amma kasancewar alh. Me kishin kasarsane,yasa baya barinsu acan yake dawowa dasu,nan.suhailat ce kadai,basu kaita karatu wajeba,duk da burinta kenan,amma hajiya Sam taki,saboda kaunar datake mata, bazata iya bari tayi nesa da itaba,sedai idan tayi hutun makaranta se taje duk kasar datakeso tayi Hutu acan.
Dafarko bangane fyade akewa yan aikin gidanba,sedai kawai na wayi gari naga basanan,seda akayiwa jikata sannan nagane,itace yarinya ta Biyar a wadanda akayiwa,na tambayeta wane tacemun bata saniba,bama ta hayyacinta aka mata kawai farkawa tayi ta ganta cikin mawuyacin hali. Kudi kawai hajiya tabamu metarin yawa tare da kaita asibiti,harta warke amma kuma bayan wasu kwanaki ta fara wani irin ciwo tamkar ana tsotse ta kafin kuma ta mutu.
Gaba daya bayanin da baaba,talatu takeyi bana fahimta,kokadan.saboda hankalina baya jikina.hannunta na kama cikin kuka nace."nashiga uku ni maryam,baaba wannan kuma wanne irin bala'ine Allah yakawoni,dama shiyasa hajiya lami ta tambaya, *bani da gata* Ashe da wani Abu a kasa, akwai wani kulli da suke kullaw.....kukane yaci karfina na kwantar da kaina,akafadar talatu ina cigaba da fashewa da kuka.bubbuga bayana ta farayi alamun rarrashi. "Kiyi shiru maryam,na miki alkawari zan taimakeki,yanzu dai lokaci ya kure mana,idan hajiya ta fito taga har yanzu,inanan zata gane na fada miki wani Abu,zantafi da safe zanzo nanuna miki yanda zakiyi amfani da komai na gidannan ,alokacin idan kin samu nutsuwarki zankarasa miki bayani. Sannan kuma ina gargadinki da kada kinuna wata alama,da hajiya zata gane,wani Abu ya faru,domin idan ta gane Daga ni harke munacikin matsala.janyeni tayi Daga jikinta ta mike ta fice Daga dakin.gaba daya kwakwalwata ta kulle,tunanina ya tsaya narasa tunaninma mezanyi,mutuwar innatace ta dawomun sabuwa,nasan datananan da duk banshiga wannan bala'inba.knocking kofar dakin aka farayi da sauri na tashi na nufi toilet na wanke fuskata,sannan na fito,na bude kofar.
Matarnan nagani,hannunta dauke da faranti,da sauri nakakaro murmushin yake,ina mika hannu na karbi farantin hannunta,sannu na mata.tacemun bakomai ta juya ta fice.wasu hadaddun food flaks ne,masu matukar kyau akan faratin.murdawa na hauyi dakyar na samu na iya budewa,wani kamshine ya daki hancina,na abincin dake ciki.babu tantama Daga ganin abincin ze hadu,amm Sam naji bana sha'awarci ko yunwama banaji saboda zullumin dake addabar zuciyata.maida murfin nayi na rufe.na zabga tagumi......
Fitowarta kenan Daga toilet,ta hango wayarta tana ringing.batabi ta kantaba,kararasawa gaban mudubi tayi ta fara mulke jikinta da tsadaddun lotions dinta,tafi 20 minutes agaban mudubin,kafin,ta koma ta bude ward rope din kayanta dake cike makil da kaya,ta dakko wata red gawn me adon black,pant kawai tasaka da bra,ta zirata ta matukar kamata,kasancewar rigar robace.gashin kanta wanda bashi da cika da tsayi sosai ta kamashi da wani red ribbon.gaban mudubi ta koma tana karewa kanta kallo,ita kanta tasan tayi kyau,duk da ba wata kwalliya tayiba.perfumes dinta ta fesa sannan ta koma ta dakko,wayarta.missed call din kamal, ta gani.murmushin tayi,tare da bin bayan kirannashi. "Hello kamal!" ta furta, bayan ya ɗaga wayar. cikin wata wahalalliyar murya yace."aini fushi nakeyi baby,yau kwata-kwata koki nemeni,kuma kinsan banajin dadi idan banjiki ajikina ina kuguigwitakiba".ya karashe zancen tare da busa mata wani numfashi cikin son yarikitata. Wani dogon numfashi taja saboda sakonsa ya isa inda yakeso."am sorry my kamal,nima nayi missing dinka,but don't worry,gobe bani da lecture throughout muna tare.wani ihun murna kamal yasaka wanda yasa da sauri suhailat ta kashe wayarta.karya kashe mata dodon kunne. Number,habibinta tayi dialing tayi ringing harta gama be daukaba.tana shirin tashi kuma yakirata,da sauri ta picking cikin,zumuɗinta.shagwaɓarta kawai taita zuba masa,tana faɗa masa yanda tayi missing ɗinsa.Da kuma,korafin,ya tafi basuyi sallama.samu yayi,ya lallabata.kusan 20 minutes suna wanda,wanda gaba daya suhailat ce take ta surutunta. Cike da murna ta fito,daga dakinta zuwa falo domin yin dinner......
Dare ya tsala, amma babu digon bacci a idona.ina zaune na zabga uban tagumi,se kuncewa da sakawa nakeyi amma babu mafita,gashi nayiwa baaba,talatu alƙawarin,bazan gudu daga wannan *baƙin gidanba* shawarar zuciyata nabi nafada toilet na watsa ruwa,tare da dauro alwala,na fara jero nafilfili ina kaiwa Allah kukana.bansan adadin raka'ar danayiba nasan dai na dade ina sallar.Ina zaune akan daddumar ina lazimi hannuna naɗaga nafara rokon Allah. _ya Allah ina roƙonka da tsarkakan sunayenka,kakareni da karewarka,ka tallafi rayuwata,ya Allah kaine gatana bani da wani gata senaka.Allah kakawomun ɗauki arayuwata,ka nisantani da duk wani abunda ze cutar dani,ka bayyanamun mahaifina da gaggawa idan har yana Raye, alfarmar darajar annabinka._ shafa addu'ar nayi,inajin wata nutsuwa tana zagaye dukkan jikina,kunci da damuwar danake ciki gaba daya,ya fara yayewa.mikawa Allah komai nayi,tare da kudirin fuskantar kowacce irin kaddara ta rayuwa ta.nasan Allah baya bacci kuma yanaji yana gani. Da wannan tunanin na mike na ninke sallàyar da nayi sallah,abincin da'aka kawomun na tsakura naci kadan,bayan nagama na hau kan gado na kwanta,na lulluba da bargon Dana gani a ninke a gefen gadon.zuciyata cike da kewar umma,da saleemat harma da gwaggo,cikin mintuna kadan wani bacci me nauyi yadaukeni.......
Kiran assalatune ya tasheni daga baccina,dakyar na yunkura na tashi nayi sallah,saboda wani bacci danakeji,ina idarwa kuwa nakara Jan bargo na koma baccina.
Ina cikin daddadan baccina, Wanda na manta rabon danayishi naji ana tashina.ahankali na bude shanyayyun idanuwana, baaba talatu nagani tsaye akaina.yunkurawa nayi na tashi zaune,gaisheta nayi.amsamun tayi tare da zama agefena. "Da'alamudai maryam jiya baki samu kinyi bacciba,tunda gashi har rana tafito baki saniba.murje idona nayi nace. "Eh baaba,bansamu nayi bacci da wuriba. Amma duk da haka nayi mamakin dadewar da nayi ina bacci." "Kitashi ki watsa ruwa,kishirya nafara nuna miki abubuwan,saboda yau zaki fara aikinki". " tom baaba,na amsa mata ina sauka Daga kan gadon. "Akwai komai na amfani dazaki bukata adakinnan,harda kayan sawa idan kin shirya kisameni a falo. Dakai na amsa mata na nufi toilet. Sabon burush din danagani da MacLean nayi amfani dasu,wajen wanke bakina.kamar yadda baaba talatu,ta fada akwai komai na amfani adakin, kayan shafene kawai babu sosai,kayan sawama gasunan burjik a wardrobe din dakin,abunda ya matukar dauremun kai kenan.banyi gigin saka kowanne kayaba,kayana na saka.na nufi falo gurin baaba talatu.
Tundaga kan toilet ta fara koyamun yadda zanyi amfani da komai,se kuma kitchen shima ta nunamun komai yadda zanyi amfani dashi,Alhamdulillah kuma na gane sosai,sedai dan abunda baza'arasaba Wanda se ahankali,tana nunamun take fadamun sunan kowa nagidan,da kuma yadda zan tafiyar da aikina. Dakina muka koma bayan ta debo mana kayan breakfast,tare mukaci abinci da baaba,tanata bani labaran ban dariya, duk akokarinta nasan ganin ta kwantar mun da hankali. Bayan mungama na tambayeta nace."waini baaba,wannan kayan Dana gani nasawa na waye"?. Murmushi baaba talatu tayi tace"nakine maryama.cike da mamaki nadago na kalleta "nawa kuma baba"? "Eh maryam,kidauki dukkayan dakika gani adakinnan kisaka mallakinkine,kafin kizo nawatane amma yanzu ya zama naki,idan za'akawo me aiki gidannan kafin tazo komai dazatayi amfani dashi se'an tanadar mata.yanzu ni zanje nafara aikina,naga goma ta kusa idan nagama komai anjima zanzo nakarasa miki bayanin gidannan.kekuma Daga yanzu zaki fara aikinki.
Kayan da mukaci abinci,na tattara na kai kitchen seda na fara gyara dakina na wanke toilet sannan na gyara falon gidan, nayi mopping dinsa,amma abunda ya bani mamaki har lokacin babu Wanda yafito na gidan.araina nace wannan wanne irin baccine.kukune ya fito Daga kitchen yafara jera abinci akan dinning,gaisawa mukayi cikin rubabbiyar hausarsa,sejana yakeyi da surutu.ni kuwa dariya hausarsama take bani.hakan yasa nabiye masa,tamkar munsaba da juna munata hira.fitowar hajiya ya katse mana hirarmu,ta fito cikin takunta na ishashshiyar mace,taci kwalliya kuma tayi kyau sosai.fuskarta ba yabo ba fallasa.tsugunnawa nayi har kasa ina gaisheta amsawa tayi tana bina da wani irin kallo.nidai ina tsugunne kaina akasa,ina jiran umarni.kusan mintuna 10 muna haka,yayantane suka shigo gaba dayansu falon.
Daya bayan daya naga suna hugging dinta,ita kuma sefara'a take saki.babu Wanda ya kulani acikinsu da gaisuwar danake musu. Se guda dayannan.gaba dayansu suka nufi dinning har hajiya.gajiya nayi da tsugunno na koma gefe na rakube,ina kallonsu kawai. "Haidar yakaji yau,munsha baccinmu mun more, saboda big bro bayanan dayanan da tuni muntashi tun dazu" dariya haydar din yayi "kaidai bari ai big bro akwai takura" harararsu mommy,tayi batace komaiba.kamshinta yarigata karasowa falon,rasss gabana yayanke ya fadi,haka kawai Allah yadoramun wani matsanancin tsoronta a kallo daya Dana mata,arayuwata.tana sanye cikin wani Riga da wandon jeans,rigar iya gwaiwace,kanta sanye da wata hula me matukar kyau. Dagudu ta karasa ga yan uwanta tayi hugging kowanne,sakin baki nayi ina kallonsu araina nace sukuma haka al'adarsu take,sekace ba musulmaiba,domin ni aganina,wannan badaidai bane, mu'aro al'adar daba tamuba........maganar suhailat ce ta dawo dani hankalina cikin tsawa takemun magana. "Dalla malama me kike jira,ko zuwa kikayi kisamu agaba kina kallonmu da kwalakwalan idanuwanki,kamar mujiya" dasauri na mike jikina har rawa yakeyi na karasa dinning din,batare da nace komaiba.kamar yadda baaba talatu tacemun sena tambayi kowa abunda yakeso,takan Wanda naji ankira da haydar na fara. "Yaya haidar me kake bukata?" Na tambayesa kaina akasa. Wani banzan kallo ya watsomun yana karemun kallo tundaga sama har kasa. Dagowa nayi ina kallonsa jin yayi shiru,kamar yadda kowa na falon yayi,wata uwar harara ya wurgomun,yace "dawannan dattin hannunaki zaki zubamun abinci." da sauri na kalli hannuna fess yake babu dattin komai,kawai tsabar son ya bakantamun raine,kuma yayi nasara. Seda yagama mun shakiyancinsa,sannan ya fadamun abunda yakeso. Tsabar kasaitama da hannu yanunamun abunda yakeso din.zuba masa nayi nacigaba da tambayarsu ina zubawa kowa. Suhailat ce ta karshe,tambayarta nayi amma memakon ta bani amsa senaji ta tsinkamun mari. "Ke wacce irin dabbace,mahaukaciya jahila" dafe kuncina nayi idona ya fara kawo ruwa. "Kiyi hakuri aunty suhailat",duk da bansan mena mataba,amma na bata hakuri. Tsaki taja tare da tabe baki,ta fadamun abunda takeso na zuba mata.babu Wanda yayi magana akan abunda tamun,cin abincin su kawai suke hankali kwance.
Dakin hajiya na nufa,domin gyarawa,bayan nagama shan kukana adaki,na yadda mutanen gidan suke nunamun kyama a fili.duk yanda nake ganin kyan dakin Dana sauka,amma kokama kafar wannan beyiba,bansan yazan fasalta kyau da tsaruwar dakinba. "Aljannar duniya na furta afili,wannan daki haka sekace baza'a mutuba.babu wani datti adaakin sosai,gadon nafara gyarawa....seda nagama gyaran dakin duka sannan koma toilet.bayan nagama da dakin hajiya na koma dakin suhailat,alokacin duk sun fashe Daga falon se hajiya kadai tana kallo. Itama dakin suhailat din tamkar na hajiya,kalar kayan dakinne kawai kowa danasa,seda nagama kare masa kallo sannan na fara gyarawa,amma ita suhailat,dakinta da datti sosai,tamkar ba maceba, duk yayi kaca kaca kayan data cirema gasunan akasa,dakin gaba daya ba kintsi komai a hargitse.toilet dintama duk datti............
Kwance yake akan makeken royar bed dinsa,se juyi yakeyi yakasa tashi.hannunsa dafe da mararsa,saboda wani ciwo datake masa,ga muguwar sha'awar data addabesa,lumshe idonsa yayi cikin jin azabar ciwo,tare da taune lips dinsa na kasa..........✍️
Meson complete Whatsapp 08166674823
*ABUNDA KA SHUKA*......... _*(shizaka girba)*_
*MALLAKIN* 👇 *ZAINAB USMAN KUMURYA*
*Bismillahirrahmanirrahim*
0️⃣9️⃣
............sosai yakejin azabar ciwon marar,Addu'a yafara karantowa yana neman taimakon ubangiji,cikin ikon Allah yasamu ciwon yafara lafa masa.daurewa yayi ya yunƙura, ya tashi zaune,agogon bangon dake ɗakin ya kalla, "yasalam" ya furta tare da dafe kansa,saboda ganin lokaci yana Neman ƙure masa,ga wadanda zasu kawo kaya suna jiransa.miƙewa tsaye yayi ya nufi toilet ya sakarwa kansa ruwa,kozeji sanyi ajikinsa.yakai 20 minutes yana wankan,kafin yafito daure da towel a ƙugunsa,sedan karami dayake goge jikinsa dashi.cikin mintuna ƙalilan ya shirya,cikin wasu tsadaddun ƙananan kaya,Wanda suka ƙarbi jikinsa.fuskarsa tayi fayau alamun ba ƙlu yakeba.batare da yayi tunanin cin abinciba ya kwashi wayoyinsa ya zira a pocket dinsa,ya fice daga ɗakin.........
***********