Kenza eBookz

Afra ko amrah complete - Chapter 10

Afra ko amrah complete - Chapter 10

Afra ko amrah complete Chapter 10: Afra ko amrah complete Chapter 10. Leesa na ta6a ta ta buga ihu tace"Afrah nice fa" Anti tsoro nake ji bazan iya bacci…

4,432 words

Leesa na ta6a ta ta buga ihu tace"Afrah nice fa" Anti tsoro nake ji bazan iya bacci ni kad'ai ba kuma bazan iya komawa d'akin uncle ba wani abu yake min. Uhm Afrah kema da ke ciki me ya kaiki d'akin Farhan bayan kinsan yanzu baya da cikakken hankali ko gwaggo bata sanar da ke bane? Ta gaya min....amma shine kika tafi d'akin shi har na samu yana saka miki wannan abun ....wlh Anti bai riga ya saka min ba....kinci arziqi domin da ace ya saka miki ba abinda zai hana ki d'auki ciki kuma da kin sami ciki rayuwar ki ta lalace ma'ana mutuwa zakiyi domin kinyi qanqanta da d'aukar ciki amma idan za ki iya gaki ga hanya.....wlh Allah bazan iya ba ni ko kusa da shi bazan sake zuwa ba bare d'akin shi domin ina tsoron na d'auki ciki na mutu....eh haka ne amma ban hana ki zuwa gun uncle d'in ki ba kawai dai nasan zaki d'auki ciki idan kinje kuma yaro qarami bawa daukar ciki ya rayu sae dai wani ba shi ba don haka shawara ta rage miki amma kar ki ce zaki daina zuwa gun uncle d'in ki then kinga tafiya ta......nidai zan biki mu riqa bacci tare.... Au shawarar da kika yanke kenan? Eh to idan uncle dinki yace meyasa ba kya zuwa bacci fa?nifa Anti bana jin zan iya sake zuwa kusa da uncle bare har ya min magana sae idan ya sami lafiya tukun. Uhm to shikenan kukan ya isa haka nan ta share mata hawaye suka tafi.

Bayan kwana biyu da faruwar haka , Afrah ta qauracewa Farhan kwata kwata bata yarda ta kalli ko qofar dakin sa.

Farhan kuwa duk dare baya iya bacci shiyasa yake son ya lalla6a Afrah kamar yadda leesa ta gaya mishi amma da yazo kusa da Afrah da sauri take barin gurin har ma tana tuntu6e sbd a kullum suka zauna qara tsora ta ta leesa keyi wanda yanzu har mafarki take Farhan yazo zai kusance ta ai kuwa tayi ta ihu cikin bacci tana neman agajin leesa.

leesa in banda dariya ba abinda take yayinda take fad'in kad'an kika gani indai sharrin leesa ne. Kamar yanda na kasa bacci kan baqin cikin rashin nasarar auren farhan haka kuma baza kuyi bacci ba. Ke ihu shi kuma jaraba na can ta hana shi bacci. Kuma nayi alqawari har abada ba wata 'ya mace da zata ta6a ra6ar farhan face ni. ****** 5:00pm Afrah ta dawo daga school a gajiye tana shiga d'aki ta cire uniform d'in jikin ta ta fad'a toilet tana fitowa ta saka vest da three quarter ta fito ta sami leesa zaune ta d'ora qafa kan qafa tana shan ice cream tace"Anti ya naga kan dining ba komai yau ba a kawo abinci bane ?eh....oh no yunwa fa nake ji sosai ,Uhm to ai sai ki tashi ki sami abinda kika d'ora muku keda farhan domin ko shi bai ci abinci ba...girgi fa Anti? Eh man ko baki iya bane?Ni ban ta6a yin girki ba ina so nayi amma gwaggo bata bari nayi wai sae idan na isa koyo tukun,,,,to ai ga irin ta nan ba a koya miki ba kuma aka zo aka miki auren wuri,,,ni Anti idan zaki koya min yanzu zan iya d'orawa ,olryt muje.

Nan suka je kitchen leesa tace"me zaki dafa muku? White rice da stew,ok nemo tukuñya nan Afrah ta nemo tukuñyà leesa tace ta d'auraye tukuñyà ta zuba ruwa bayan tayi hakan tace"sae ki kunna gas cooker ki d'ora akai idan sun tafasa sae ki zuba shinkafa" Tana gama fad'ar haka tasa kai zata bar gurin Afrah tace"Anti nifa ban iya kunna gas cooker ba kuma ya ake gane idan ruwa sun tafasa.... even tafasar ruwa ma ba ki sani ba hm lallai gwaggo ta shagwa6a ki da yawa 12yrs baki san yànda zàki gane idan ruwà sun tafasa ba,,,ni Anti ina so na sani amma gwaggo ce bata barina naje ko kusa da gas cooker wai kar na qone,,, Allah?hm yayi kinga ki duba kiga yanda zan murd'a abubuwan nan da ke jikin gas cooker sae kinyi pressing then ki murd'a akwai high low and midi but barshi a high tunda sauri kike kina jin yunwa.

Yauwa ungo ashana amma kar ki qesta sae kinji duk kitchen d'in nan ya d'auki warin gas dai dai ya hau kanki da kyau sae ki kunna ashana hope get it?I got it Anti thank u.....no ba sai kin gode min ba ai yiwa kaine ta fad'i haka ne yayinda ta fita daga kitchen sae murna take yau zata raba Afrah da duniya.

*Futha luv💅🏻&Billy giro😊* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [, 9/22/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *~AFRAH KO AMRAH ~* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*🇳a*

*```🇧ilqis 🇸idibe💅🏻&🇧illy 🇬iro😊```*

*🏅34🏅* 🇱eesa na zaune ta fara jin ihun Afrah sae kiran sunan ta take. Le6ace baki tayi ta tashi tare da fadin"Allah yasa ma kifi gawayi quna ni bazan je na ceceki ba" Nan ta sa kai ta tafi d'akin ta . Afrah kuwa sae ihu take sosai wacce da ji buqace take da neman taimako . Tun tana kiran Anti har ta koma kiran uncle cikin muryar kuka . Farhan da shigowar sa kenan shida d'an gidan suka tafi da gudu zuwa kitchen jin ihun Afrah da kuma warin gas da ya cika gida. Koda suka shiga sun sami Afrah duk ta fitsare wandon ta tayi zufa zufa ta jefar da ashana gefe sae rawar tsoro take tana tsalle yayinda take kallon d'an qaramin kyankyason da ke matsowa kusa da ita.

Farhan ya riqo hannun ta yayi 2 tabi ta gefen kyankyason tazo amma ta kasa sae kuka take mai had'e da ihu, sae da aka kashe kyankyason ta iya zowa jikin farhan tana sauke ajiyar zuciya tare da share hawayen fuskar ta yayinda d'an gidan da naji farhan ya kira shi da "Amir" ya kashe gas cooker suka fito. Farhan ya haura sama tare da Afrah inda suka nufi d'akin Afrah wacce da isar su ta qi yarda ta shiga d'akin.

farhan yace "mata ta ki shiga mana ki canza kayan jikin ki"uncle ni wanka nake so nayi kuma bazan iya wanka ni kad'ai a cikin d'aki ba,, muje na tsaya miki, saurin kallon shi tayi had'e da girgiza kanta tace"um um bana so d'akin Anti zan shiga"ba ta jira me zai ce ba ta shigewar ta d'akin leesa . Leesa na ganin ta ta had'e girar sama da ta qasa tana qarewa Afrah kallo taga ba alamar qonuwa a jikin ta tace"ya akayi haka ba kece naji kina ta faman ihu a kitchen ba? Nice Anti amma shine kina jina kika share ni "to nasan abinda kike yiwa ihu ne tukuna ma mene ne kike ma ihu kamar bala'in duniya ne ya same ki?tace"Anti garin neman kayan abinci naje na had'u da kyankyaso a drawer" guntun tsaki leesa tayi taji duniya tayi mata baqiqirin yayinda take tambayar kanta shin me yake faruwa ne kan duk abinda nayi wa Afrah bana samun nasara a kanta,ko wata hanyar zan canza ne amma ba komai ai idan na kasa da ke zan iya da farhan shida yanzu a qarqashin mulki na yake na riga na maida shi tamkar yaron goye sae abinda naga dama. Nan dai ta qaraci zantuttukan ta yayinda tuni Afrah ta shiga wanka .

Bayan en wasu kwanaki gidan yayi tsit ba wani motsi da ake ji kasancewar dare ne yayinda kowane d'an Adam ya samu damar bacci face Farhan da keta faman juyi ya kasa bacci kamar yanda yake faman yi a ko wane dare .

Leesa ce ta shigo d'akin sanye da rigar bacci wacce ita da babu duk d'aya gashi ba komai a jikin ta face wannan rigar. Cikin hanzari farhan ya tashi domin ya d'auka ko Afrah ce wacce yau ba yanda bai yi da ita ba kan ta haqura tazo suyi bacci amma taqi sae yaga ba ita bace leesa ce. Bata ce da shi komai ba sae zare rigar jikin ta tayi ta zamo topless, hakan ta juya gaba da baya shape sae kace amoeba ,tayi tsaye cike da yanga kamar wata er fashion sannan ta kashe masa ido d'aya tace"ya ka ganni na isa a kewaya dani,ko da yake tambaya ta da amsa take don haka zo kawai na taya ka cire kayan jikin ka" Farhan dai bai ce mata komai ba sae qarewa surar jikinta kallo yake. Nan ta qarasa gurin shi ta shiga cire mishi kayan jikin shi ta fara sarrafashi tamkar ita ce namiji shine mace da haka har suka fad'a kan bed.

*Billy giro😊&Futha luv💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [9/24/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *~AFRAH KO AMRAH ~* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*Na Billy giro😊& Bilqis Sidibe💅🏻*

*🏅35🏅* Gab take da cimma burin ta taji an daka mata wata uwar tsawa tare da wani gigitaccen marin da aka d'ora mata kan fuska take taji dif a kunnen ta qarar komai bata ji sai sautin kukan mari da ke ta maimaituwa a cikin kunne ta wanda da qyar ta samu ta saisaita kanta domin tayi bala'in rikicewa dajin abubuwa guda biyu wato saukar mari da kuma tsawar da aka daka mata da bata san waye ya mata su ba.

kan tayi wani abu taji an tunkud'a ta da qarfin tsiya har sae da ta fad'a jikin wardrobe inda ta shiga rud'u ganin farhan ne ba kowa ba sae huci yake kamar wani kumurcin zaki.

Guduwa take qoqarin yi sbd farhan da taga ya zaro belt wanda kai tsaye ya fara dukan ta baji ba gani.

Ihu ta ke sosai yayinda farhan ke ci gaba da dukan ta duk ya farfasa mata jiki . Da qyar ta samu ta qwaci kanta zata fita da gudu se taci karo da Afrah wacce ta shigo d'akin da gudu ta fad'a jikin leesa tana kuka ba tare da ta lura da yanayin da suke ciki ba ,da sauri leesa ta ture Afrah ta bar d'akin cikin sauri har tana tuntu6e , Nan Afrah ita ma tayi sauri zata bar d'akin Farhan yace"Afrah zo kar ki bita , ina zaki je uncle ne fa zo kinji poppy Luv"fasa fita tayi domin jin sunan da ya kira ta da shi wanda hakan ya bata tabbacin uncle d'in ta ya fara samun lafiya amma kuma ta kasa isa gurin shi bcs ta ganshi nudely sannan idanun shi jajir suke sbd 6acin rai, da sauri ya nemo beedsheet ya rufe jikin sa domin shima ya manta yanda yake kuma ya fahimci shine dalilin qin zuwan ta . Duk da haka kasa zuwa tayi tana tuna maganar leesa wanda hakan yasa ya qaraso da kanshi,yaja hannun ta suka zauna kan bed sae kallon sa take tsoro tsoro yace"my Afrah lafiya me ya tsorata ki kika shigo da gudu cikin firgici ?shiru tayi tana kallon shi sbd shakku take ko ya sami lafiya. Yatsun shi yakai ya lotsa su kan kumatun ta wanda hakan ya qarawa Afrah tabbacin cewa Farhan ya sami lafiya yace" my Afrah say something kinji" A hankali ta kwantar da kanta kan kafad'ar shi tare da sauke ajiyar zuciya tace" dama na tashi ne banga Anti ba kuma sae wani ihu nake ji,amma yanzu zan koma tunda ta koma" Bai so ta koma ba amma hakan yaja hannun ta yakai ta har bakin qofar d'akin leesa sannan ya juyo.

Da shigar shi ya shiga gyara gadon shi da ya yamutse yana cikin gyaran ne Afrah ta dawo tace "uncle Anti bata nan" yace"ina taje ?nima ban sani ba gashi kuma ina so na koma bacci"zo ki kwanta anan,,,um um uncle' yace"My Afrah ba abinda zan miki "ya fad'i haka ne yayinda yazo yaja hannun ta inda tsoro tsoro ta yarda ta bishi ya kwantar da ita kan bed ya rufa mata blanket sannan yaje ya watso ruwa yazo kan sofa ya kwanta cike da tunani kala kala a ranshi da har ya hana shi bacci shiyasa ya tashi ya fara nafilfili kasancewar yana d'auke da arwala.

Washe gari har dare ba leesa ba labarin ta Afrah duk ta dami Farhan da tambayoyin da shi kanshi ba ya da amsar su kan cewa ina Anti taje tun jiya har yanzu bata dawo ba tun yana bata amsa har ya gaji ya mata shiru hakan yasa ta ajiye mishi kuka bcs bata son ta sake kwanciya a d'akin farhan sbd ko jiya tayi mafarkin da ta saba yi duk dare.

Lallashin ta ya shiga yi tare da kira mata gwaggo a waya inda suka jima suna waya.

Bayan ta gama wayar ne tace"uncle gida zaka je ne naji gwaggo tace zata baka saqo ka kawo min "yace "eh gobe zanje Nigeria ke kuma zaki koma 6angaren su Amir da zama har na dawo "marairaice wa tayi tare da fad'in "pls uncle ina zuwa" "no Afrah ai kwana d'aya zanyi na dawo" " dan Allah uncle kaje dani",,,,"kin manta kina zuwa school ne" Tace"ai kwana d'aya ne uncle"ko mnt bana son kiyi missing ba kya school, kiyi haquri kinji"idanun ta ne suka ciko da qwallah tace"to uncle dan Allah kazo da Amrah ita ma ka sanya ta school d'in da nake"ai ba ni ke da iko da Amrah ba, but uncle ta gaya min cewa kai ne ke daukar nauyin school in ta ba Abban ta ba"shiru yayi bai ce mata komai ba sae hannun ta yaja yace muje lokacin bacci yayi kuma surutun ya isa haka . Cike da fargaba ta yarda ta kwanta inda da qyar ta iya bacci duk da cewa farhan akin gaban sa yake wato nafilfili.

Washe gari sae da ya kaita school yabi jirgin qarfen goma.

Koda Afrah ta dawo daga school 6angaren su kawai ta nufa domin ta manta cewa Farhan yayi tafiya kuma Amir da ya d'auko ta bai sanar da ita ba . Ganin 6angaren a rufe yasa ta tuna yayi tafiya inda da kuka taje 6angaren su Amir,mahaifiyar Amir ce ta lallashe ta har tayi shiru taje tayi wanka sannan taci abinci.

Farhan kuma koda ya isa Nigeria ya sami gwaggo ta had'a mishi lafiyayyen abinci sae da yaci abinci sannan yaje ya watsa ruwa yazo ya zauna suka qara gaisawa da gwaggo wacce sai murna take ganin farhan ya fara samun lafiya . Tace "Farhan yanzu ne zamuyi maganar ko sae da safe dai dai ka huta? gawggo na fiso muyi maganar yanzu bcs bana son na sa6awa Afrah kan cewa zan koma gobe nasan kuwa komai dare sae tayi jiran koma wa ta,,,lallai kam indai Afrah ce tana iya musu kuka idan taga baka koma ba,,uhm ai da na sauka a jirgi nayi waya da Amir yake sanar dani har kuka tayi da ta dawo daga school bata ganni ba" Sae ba Afrah ba kam ai nasan qaramin aikin ta ne. Inace da alamu Alhmadlh ka fara jin sauqi ko?"eh gaskiya gwaggo Alhmdlh but wasu abubuwa ne sukayi matuqar d'aure min kai wad'anda nake gani kamar a mafarki bayan gaske ne shiyasa nake son muyi magana akai.

*Billy giro😊&Futha luv💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [9/25/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *~AFRAH KO AMRAH ~* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*Na Billy giro😊& Bilqis Sidibe💅🏻*

*duk mai niman afrah ko Amrah daga farko,zai iya dubawa a blog dinmu.*

Futhalurv.Wordpress.com

*🏅36🏅* Musamman auren da aka d'aura nida Afrah abubuwan nasan sun faru amma kamar mafarki nake ganin su shiyasa nake mamakin me ya kawo hakan bcs tun lokacin da nayi accident haka nake ganin komai. Farhan wato qwaqwalwar ka ce ta samu matsala shiyasa kake ganin abubuwa haka haka.... to gwaggo meyasa kika ce leesa ta bi mu har Oman sae kace er uwa? Leesa kuma sam ban san da zuwan ta ba amma meyasa baka sanar da ni ba domin abun da ban mamaki da d'aure kai,,,gwaggo nima jiya nayi ta mamakin abin musamman idan na tuna yanda na kasa tambayar ki dalilin zuwan ta kuma naga duk wayar da kuke da Afrah ban ta6a jin ta miki zancen leesa ba haka ko Abban Amir da suka ganta ba wanda ya tambaye mu wace ce ita,,,ikon Allah ita ko leesa ayi haka taje bata sanar da ni ba don nasan ba abinda yasa taje face tausayin Afrah da take ji tana ganin kamar baza ta iya wasu abubuwa ba amma kuma ai Afrah bata wani aiki face zuwa school...wai zama taje taya mu,haka ta gaya ma?eh kuma gaskiya yarinyar bata da mutunci kamar yanda kika dauke ta da mutun ci wanda kan rashin mutunci ta yasa na mata dukan tsiya har ma ta gudu ta bar gidan.....subhanallah anya kuwa farhan qwalqwalwar ka ta sami lafiya kuwa in ba shi me leesa za tayi da har taci duka a gun ka! Gwaggo da hankali na kuma abin da taso ta min mai munin gaske ne ko a gurin ubangiji shiyasa na mata dukan tsiya sbd koda ace na koma er gidan jiya da nake ganin abubuwa na faruwa na kasa cewa komai baza ta ta6a tunanin maimaita abinda tayi niya ba. Farhan wane irin abu ne ta maka haka? Gwaggo kiyi haquri ki bar zancen kawai domin bana so ki tsane ta da yawa kawai abin da zan ce Allah ya shirye ta. Gwaggo ta jinjina kai tare da fad'in "amin" But gwaggo aure na da Afrah fa?kamarya Farhan? wai gani nayi Afrah tayi qanqanta da yin Aure duk da cewa a dalilin ta ne naqi yin aure sbd ita na ajiye a matsayin matar da zan aura amma a tsari na sae ta kammala high school tukun kuma sae idan har tana ra'ayin aure na,,,,to Farhan tunda ubangiji ya riga da yayi tsarin sa sae kayi haquri da yanda ya tsaro abun amma kasan yanda zaka riqe Afrah a matsayin ta na yarinya ,inshaAllah gwaggo zan bi komai a cikin tsari,,, haka nake son ji Allah ya baku zaman lafiya,,Amin gwaggo . Daga haka suka d'an ta6a wata fira sannan farhan ya tashi ya koma 6angaren shi.

Washe gari ne ya koma Oman bai zarce ko ina ba sae 6angaren su Amir ya samu Afrah ta tasa su gaba tana musu kuka ga abinci gaban ta taqi taci sallamar da yayi ce yasa ta tashi tazo da gudu ta rungume shi . Sae da ya gaisa da iyayen Amir sannan ya dago Afrah da ke kan qirjin sa yace"lafiya kukan na me?Amir yace"wai ta d'auka baza ka dawo ba sbd baka kira kace ka taso ba kuma idan aka kira ka ba a samun ka,,, Uhm Afrah kenan to gani na dawo sae ki daina kuka ko,,,le6ace baki tayi tace "to uncle ina Amrah ?wai da gaske kike nazo da ita?eh mana Uhm Uhm baka zo da ita ba kenan....Pls Afrah kar kiyi kuka muje muyi magana ya fad'i haka ne yayinda ya kalli iyayen Amir yace"mu zamu je 6angaren mu bcs dargar ta tashi sae nayi da gaske ko zata daina"umman Amir tayi murmushi tace"Abinci fa koda yake kuje Amir yazo muku da shi, yace"yauwa mun gode fa" Nan suka wuce 6angaren su yayinda Amir ya biyo su da abinci ya ajiye kan dining ya wuce.

Farhan yaja hanun Afrah suka zauna duk ta cika fam wai ita fushi take farhan yace"Afrah da dawowa ta kike fushi da ni? to uncle ai kaine kaqi zowa da Amrah,, ban san cewa da gaske kike ba kuma nida naje sharp sharp ina naga time na zowa da Amrah wacce tana school ,,uncle baka ga yanda tayi kuka ba da aka bani permission yanzu idan taji gabad'aya na bar school in ya zata ji ?shike nan naji zanyi tunani akai....da gaske uncle?of course... Yeah Allah ya bar min kai uncle! Amin my Afrah nima Allah ya bar min ke, sae muci abinci ko?kai ta gyad'a mishi daga nan suka fara cin Abinci cike da nishad'i.

Bayan sun kammala suka je d'akin farhan da shigar su Afrah ta fad'a wanka yayinda farhan ya zauna jiran fitowar ta . Aljihun sa ya shiga lalaba da alama wayar sa yake nema bai gan ta ba yaje downstairs kan dining wanda da isar shi wayar ta shiga ruri koda ya duba gwaggo ce nan ya d'aga wayar inda sun jima suna wayar kafin suke ajiyewa .

Yana komawa d'aki bai zarce koina ba sae toilet ya sami Afrah ta gama wanka kenan tana qoqarin jawo towel tana ganin shi tayi saurin duqewa duk da cewa akwai pant a jikin ta,farhan da sam ya manta cewa tana cikin bayin yayi murmushi had'e da girgiza kanshi domin ya fahimci d'an qidan dangin da ta fara ne take jin kunyar ya gani, yace"Sorry my Afrah na manta cewa kina bayi"daga Haka ya fita yaje ya fara cire kayan jikin sa har ya gama ya saka bathrobe Afrah bata fito ba . Nan Farhan ya qyalla idon sa ya hango ta bakin qofar toilet tsaye ta wani turo baki cikin fishi taqi ta qarasa fitowa . Tashi yayi yaje ya jawo hannun ta suka zauna kan bed yace"nifa ban ganki ba in shine kike fushi dani" tace"da gaske uncle?Allah kuwa ,sannan ne fa tayi murmushi ta kar6i Vaseline d'in da yake miqa mata shi kuma ya wuce toilet.

Bayan sati Biyu da faruwar haka still ba leesa ba labarin ta Afrah kuwa duk ta dami Farhan kan zancen Amrah sae dai yace mata ai Abbanta ya kusa kawo ta.

Tafe suke cikin mota ya d'auko Afrah daga school duk ya gaji sosai sbd ya fara zuwa aiki sae sauri yake yaje ya sauke Afrah yana son zai koma asibiti yayinda Afrah ta cika shi da surutu se duk kan sa ya qara d'aukar zafi bai san lokacin da ya daka mata tsawa ba yace"u are verry stupid sau nawa zan ce ki min shiru! Le6ace baki tayi cike da son tayi kuka yayi saurin cewa "sorry Afrah kar kiyi kuka kinji"ya fad'i haka ne yayinda ya tsaida mota yana so zai saya mata ice cream, hakan ya bawa Afrah damar fita tana kuka ta nufi gurin da bata ma san inda zata je ba. Farhan kuma da murnar sa ya dawo cikin motar yana fad'in kinga na siyo miki ice cream d'in da kika fi so......sai kawai yaga ba Afrah face school bag da hanzarin sa ya fita yana qwala mata Kira yana neman ta . Afrah kuwa tana ganin Farhan na nemanta ta fara gudu tana keta mutane a cewar sae ta wahalda Farhan kafin ya ganta tunda ya mata fad'a. Cikin gudun ta ne ta ci karo da wata tayi saurin d'ago idon ta domin taga wace ce ta bata haquri. Baki ta saki cike da mamaki ta saki murmushi tace"lah Anti dama kina.....sae kawai ta hango Farhan tafe tace"Anti ki 6oye ni bana so uncle ya ganni muna wasan 6uya ne " Wani irin dad'i Leesa taji ta saki murmushin mugunta taja hannun Afrah tare da fad'in " yauwa muje kafin ya gan mu" nan suka tafi a gurguje suka tari taxi suka wuce yayinda Farhan yayi tsaye yana rarraba ido cike da damuwa.

Futhalurv.wordpress.com

*Futha Luv 💅🏻Billy giro😊* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [30/09, 10:35 p.m.] My Lady 2: [9/29/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```~AFRAH KO AMRAH ```~* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*```Na Billy giro 😊&Futha luv💅🏻```*

*🏅38🏅*

6angaren Farhan kuwa dare ya tsala sosai amma kwata kwata ya kasa samun natsuwar kwanciya yayi bacci hakan yasa ya d'oro arwala ya shiga yin nafilfili wanda har akayi sallar asuba bai kwanta ba sae aikin ibadah yake.

Yana dawowa daga sallar asuba sae ga kiran mahaifin Amir yake sanar da shi cewa yazo suje asibiti sae dai bai sanar da shi dalilin zuwan su asibiti ba sae duk hankalin farhan ya tashi kaddai ace wani mummunan abu ne ya samu Afrah.

*Asibiti*

Kafin su farhan su iso, Billy da Hakeem ne zaune a gaban Afrah wacce tun daren jiya da suka tsince ta bata motsa ba har yanzu . Iya qoqari likitawa sunyi na ganin ta farfad'o amma abu ya faskàra ga jikin ta da ya sandare tamkar gawa bayan a iya binciken da sukayi computer ta tuna akwai rai a tare da ita.

Billy ta kalli Hakeem kamar zata yi kuka tace"Bobby anya ba gawa muke tsare da ita ba kuwa,ni ina jin tsoro kar ace gawa ce"Billyta inshaAllah tana da rai tunda har kika ga basu furta cewa ta mutu ba" Tace"to ya jikin sukee ya rage zafi kuwa ? Hakeem ya shafi jikin er sa da ke maqale a kafad'ar sa yace"ya rage zafi ba kamar jiya ba" Ajiyar zuciya ta sauke tare da fad'in "thank God, ita kuma wannan Allah yasa ta farfad'o"Hakeem yace"Amin"

Farhan kuwa tafe suke cikin mota sae dai ya kasa haquri har saida ya tambayi Abban Amir me zasu je yi asibiti nan ya shiga sanar da shi cewa "tun jiya aka sami Afrah sae dai unconsciously shiyasa aka kaita asibiti wanda commissioner yayi ta faman kiran wayoyin mu amma baya samu sae yanzu ne ya sami tawa" Farhan bai iya cewa komai ba sbd sun iso asibiti wanda cikin hanzari ya fito mota suka nufi *A&E* ward.

Suna shiga d'akin farhan ya nufi gurin Afrah hankalin sa ne yayi mugun tashi ganin Afrah tamkar gawa ga jikin ta duk ya kumbura se duk yabi ya rikice yana ce ma Hakeem ya duba mai ita idan ba mutuwa tayi ba wanda da alama ya d'auka cewa Hakeem doctor ne haka kuma ya manta cewa shi doctor ne sbd rikicewar da yayi gashi asibitin da yake aiki ma ne aka kawo ta. Ganin da gaske ya manta waye shi kuma sae damun Hakeem yake kan ya duva mai ita, Commissioner en sanda ya katse shi da cewa"ka manta cewa kai doctor ne kuma wannan fa ba doctor bane shine wanda suka tsince ta a ruwa amma ka jira kad'an doctor zai shigo yanzu"yayi maganar ne a harshen larabci kasancewar sa balarabe . Nan farhan ya kai hannu cike da son ya ta6a jikin Afrah amma yana tsoro kar yaji alamomin da ake ji idan mutum ya mutu. Bai iya ta6a ta ba har doctor ya shigo ya duba Afrah sannan ya mata allura yace da farhan ya kwantar da hankalin sa nan da en awanni zata farka. Hankalin farhan bai kwanta ba sae da ya kai idon shi kan computer yaga alamar Afrah na raye sannan ya iya sauke ajiyar zuciya cike da tunanin ina Afrah ta shiga a ina aka tsince ta ya akayi haka ta kasance da ita? Tunanin da ya shiga yi kenan ba tare d ya tambayi kowa ba sbd da alama ko magana ba ya son yayi har sae yaga farfad'owar Afrah tukun. Nan ya sami guri ya zauna.

Sunyi awa biyu zaune suna jiran farfad'owar Afrah inda Farhan tun lokacin da ya zauna yake kallon Afrah ba ya ko son qiftawa .

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull