Afra ko amrah complete - Chapter 9
Afra ko amrah complete Chapter 9: Afra ko amrah complete Chapter 9. π 3β£0β£π Cikin kuka tace "me nama ka ne uncle da har zaka ce baka sanni ba kuma waiβ¦
4,413 words
π 3β£0β£π Cikin kuka tace "me nama ka ne uncle da har zaka ce baka sanni ba kuma wai baka son ganina don Allah uncle koma mene ne kayi haquri wlh Allah daga yau bazan sake ba please uncle, ta fadi haka ne yayinda take matsawa kusa da shi,shi kuma sae sauri yake zai rufe ganbun mota,yana fad'in idona zai fashe gwaggo don Allah muyi mu bar gurin nan. Leesa ce ta jawo ta jikin ta tana"haba Afrah ba kya jin me yake fad'a ne sae qoqarin matsawa kike kusa da shi, ki tausaya ma uncle d'in ki mana"Aunty uncle yana fishi dani ne ba wani idon shi da zai fashe don Allah Anty kice yayi haquri Allah bazan sake ba. Leesa ba tace da ita komai ba sae lallashin ta take yayinda take wata magana a cikin zuciyar ta, gwaggwo taje gurin farhan da ke roqon su kan suyi su bar gurin tace"kaga farhan wannan wasan ya isa haka jibi yanda kasa Afrah ta dauki abun da gaske sae kuka take ta faman yi,don haka fito daga cikin motar muna so zamu shiga daga ciki.
Nan gwaggo ta matsa mishi kan ya fito cikin motar, tayi 2 dashi amma yaqi nan ta fahimci fa da gaske yake bayan son ganin Afrah. Kan ta ya d'aure sosai haka ma kowa cike suke da mamaki tace"innanlillahi wa inna ilaihi raji"un! yau me nake shirin gani da rana ido biyu ba a cikin mafarki ba. Gwaggo ina ga kamata yayi ayi a sallami su Afrah domin a gaggauta zuwa asibiti a duba shi aga kodai wani abu ke damun idon shi domin ni kaina abin ya d'aure min kai sosai,,leesa ce tayi maganar yayinda Afrah ta qara fashewa da kuka tana fadin"allahumma ajirni fi musibati....haba kukan ya isa kiyi haquri kinji,leesa ce ta fad'i hakan wanda tayi haka ne domin kar Afrah ta qarasa addu'ar. Amrah ta lura da hakan domin a cikin sauri leesa ta rufe mata baki sae dai kuma bata fahimci me leesa ke nufi da hakan ba. Nan suka shiga gidan vc yayinda suka sanar da ita abin al'jabi domin sun dauke shi kamar al'ajabi. Basu jima ba leesa ta matsa kan suje fa an bar farhan a mota nan suka sallami su Afrah wacce sae kuka take suna lallashin ta inda har suka bar gidan Afrah kuka take. Bayan sun koma leesa taje gida da murna tana labartawa mom farida duk abinda ya faru tace"mom farida bari gaskiya aikin sabon bokan nan yana ci sosai sae dai matsalata dasu sun fiye addu'a amma kuma dad'i na da bokan yasan aikin shi ko yaushe yana kan qwaryar tsafin sa wanda da addu'ar su ta karye maganin zae d'ana wani. shiyasa hankali na ya d'an kwanta kinga ko da sun fahimci sammu ne yasa farhan ya tsani Afrah ko sun karye shi aikin banza ne domin boka na kan aikin shi. Ni yanzu fal farin ciki nike ciki zanyi aure da farhan cikin kwanakin nan sae ki fara shirye shirye... Au kin kar6o turaren kenan,na kar6o amma yana da sharadi bcs sae da yammacin la'asar zanje na masa shi kuma sae idan yana bacci kuma idan na masa turaren zan kasance daga ni sae shi a d'akin sbd ba a so ya fara had'a ido da kowace mace face ni, idan kuwa nayi kuskuren barin shi ya had'a ido da wata mace wai fa koda uwar sa ce to kuwa da ita za'a d'aura auren bani ba...he lallai turaren nan yanayi, ai bari kawai mom farida har da wani kaskon tsafi ya bani kuma ki kwanta kiyi bacci abinki domin da na auri farhan wlh tamkar dukiya ta dawo hannun ki,ta fadi haka ne yayinda suka tafa.
A 6angare su Afrah kuwa kan kukan da take yasa ta kamu da zazza6i mai tsanani.
Hakan tayi ta fama da shi kusan kwana 4 bata iya komai. Dole Vc ta yanke shawarar mayarda ita gida sbd magani da allura ba wanda bata sha ba amma ciwon sae qaruwa yake sbd yanda tasa damuwa a ranta sosai.
A 6angaren leesa kuwa zaune take a d'akin gwaggo tana taya ta jimami kan yanzu ko sunan Afrah farhan baya son yaji an ambata kuma sunje asibiti ba a gane komai akan matsalar idon sa ba.
Sae da suka d'anyi shiru leesa tace"farhan d'in yana nan kuwa naga tun lokacin da na shigo ban ganshi ba? inaga bacci yake domin tun da ya dawo masallaci ban sake jin d'uriyar sa ba. Tace to gwaggo zanje naga idan farke yake sae mu gaisa kafin na wuce. To a gaida gida, cewar gwaggo kafin leesa ke fita.
Leesa na zuwa 6angaren farhan bata zarce koina ba sae d'akin farhan ta same shi sae sharar bacci yake. Nan tayi hamdala tare da fitar da kaskon turaren ta na tsafi wanda gawayi ke laqe a jikin sa basa moving,sae da ta furta wata kalma kafin take hura iskan bakin ta sae kawai gawayin sukayi jajir har suna fitar da belar wuta. Nan ta zuba turare tana kewaye farhan da shi duk dakin ya surnuqe sannan ta nufi toilet wanda yayi dai da shigowar Afrah wacce kallo d'aya zakayi mata kasan tana jin jiki. Bata damu da yanda taga d'akin ya cika da hayaqi ba sae qoqarin zuwa gurin farhan take wanda ya fara motsi alamar zai farka, sannu a hankali ya bude idon shi ya sauke su kan Afrah.
Masu karatu kuyi haquri zamu dakatar da yin Afrah ko Amrah na d'an wani lokaci sbd wani dalili. Tagwayen marubuta kece muku Luv u allπ
Billy giroπ& Futha Luvπ π» π π π π π π π π π [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [9/18/2016] π π π π π π π π π *~AFRAH KO AMRAH ~* π π π π π π π π π
*Na Billy giroπ & Bilqis Sidibeπ π»*
*π 31π * Fad'awa tayi kan jikin shi tana kuka nan farhan ya fara jin wani abu na fizgar shi wanda ya sΓ mi kanshi da fara shafar jikin Afrah......qarar fashewar wani abu suka ji da sauri suka tashi suna kallon leesa wacce ta fito daga toilet tazo fuuuu ta fizge Afrah da ke kan jikin farhan ta ingiza ta da qarfi har sae da ta fad'i ,nan farhan ya tashi kamar wani zautacce yaje ya tada Afrah ya kalli leesa cikin 6acin rai yace" me matata ta miki da zaki kada ta!... Matar ka?eh mata ta ce.... Afrah ce fa ,kallon Afrah yayi yace"ko ita ce fa ai mata ta ce...kai wawa ne yaushe ta zamo matar ka?kaji ta yanzun nan mana......fuuu tayi cikin Afrah ta fara dukan ta tana fad'in er iska kin lalata min komai da yanzu nice matar shi amma kinzo kin 6ata min lissafi baqar makira kawai!haka tayi ta maganganu tana dukan Afrah wacce tuni farhan ya kare ta dukan na sauka kan jikin shi, leesa kuwa bata ma san wanda take duka ba idon ta ya riga ya rufe........Aa! Aa! Lafiya me yake faruwa haka da kike faman dukan su!? cikin kuka leesa tace"gwaggo ki taimaka a kar6e Afrah daga hannun shi so yake ya lalata mata rayuwa.....lalata rayuwa kamar ya farhan ne fa......to ai gwaggo yanzu na same su kan gado yana qoqarin raba ta da kayan jikinta dana hana shi yace na barshi wai Afrah matar sa ce don haka kar na qara shiga sabgar su kuma tambaye shi ma kiji, Wai haka farhan? Eh gwaggo mata ta ce .....ikon Allah ,Allah ya taimaka da kika zo da anyi 6arna, kai fa farhÑñ baka gane ta bane Afrah ce fa, ba marigayiya Amrah ba don haka sake ta muje ta sami abinda taci bata ko da lafiya yanzun ne dawowar ta,,,nan gwaggo taja hannun Afrah, Afrah ta marairai ce tace "Gwaggo ni ki bar ni gurin uncle ba abinda yake min "naji muje kici abinci sae ki dawo kinji,to gwaggo amma da uncle zanci abincin...."kinga Afrah uncle d'in ki bai yi sallah ba ki bar shi yayi sallah ke kije kici abinci"
Cewar leesa wacce ta danne zuciyar ta ne kawai tana magana.
Farhan yace "gaskiya gwaggo baza a je min da mata ta koina ba" komai gwaggo kasa cewa tayi yayinda al'amarin Farhan ya fara bata mamaki yanda yake abubuwa kamar wani wawa ,nan tayi ta lalla6a shi kan ya saki hannun Afrah da xarar taci abinci zata dawo amma yaqi sae ma qara riqe mata hannu yake, leesa tace"kinga Afrah yi masa magana ko zai sake miki hannu ba musu Afrah tace"uncle ka bari na tafi idan naci abinci zan dawo kaji"to matata amma kar ki jima kinji, bazan jima ba uncle . Nan aka samu ya saki hannun ta, gwaggo ta tafi da ita.
Ihu ne kawai leesa bata saki ba sbd tsananin abinda take ji na baqin ciki kallon agogon d'akin tayi ta fizgi jikin ta kamar wacce ta zauce ta kwashi kayanta ta bar gidan a guje.
Farhan kuma kasa haqura yayi domin ji yake kamar za'a fizge ransa idan Afrah bata kusa da shi hakan yasa ya tafi 6angaren gwaggo yayi zaune kusa da Afrah tare da riqe hannun ta kamar mai gudun kar ta tafi ta barshi ,gwaggo tace"wai kai ba sallah zakayi bane?gwaggo na fayi sallah kafin na kwanta. Daga haka gwaggo ta shiga kallon ikon Allah yanda farhan ya d'ora Afrah kan cinyar shi sae lalla6a ta yake yana ciyadda ita kamar ba shine kwanaki yace ya tsani ko jin sunan ta ba.
Ba abinda ya qara d'aure mata kai irin Afrah na son shiga toilet amma yace sae tare zasu shiga baza ta tafi ta barshi ba gawaggo tayi juyin duniyar nan amma yaqi haka suka kwashe kusan awa d'aya yaqi bari Afrah ta d'aga ko nan da can ga fitsarin da take ji sae qoqarin kufce mata yake,ga farhan sae wasu abubuwa yake mata kamar wanda ke shirin rΓ ba ta da tufafin jikin ta.
Ganin haka gawggo ta kira fu'ad a duba shi domin abinda yake ya wuce aikin hankali.
Da fuad yazo gwaggo ta mishi bayanin komai ya kuma gani da idon sa ya nisa kafin yake cewa "lallai al'amarin nan da mamaki sae dai kuma ni a gurina bazan yi mamaki ba sbd dama akwai wata matsala da ban gaya muku cewa farhan na d'auke da ita ba sbd gudun kar na tashi hankalin Ku inda a cikin magungunan da yake sha akwai maganin wannan matsalar wanda nake sa ran idan yana shan shi daily matsalar zata rage sae gashi naga matsalar tana qoqarin yi masa karaf d'aya wato matsalar ita ce qwalqwalwar farhan ta sami matsala wacce ako yaushe zata iya bugawa ya haukace kuma da kamar wuya ya iya dawowa normal....cikin tashin hankali gaggwo ta miqe zumbur ,fu'ad yayi saurin cewa "kar ki damu akwai wani abu da na fahimta yanzu a game da Farhan wanda inshaAllah idan akayi masa yanda yake so za'a ji sauqin shawo kan matsalar......koma mene ka fad'a inshAllah ni mai yi masa yanda yake so ne,, gwaggo ba wani abu bane face aure farhan ke so.... Aure kuma?eh gwaggo ki dube shi da kyau ki ga abubuwan da yake yiwa Afrah duk wanda ya kalle sa sau d'aya zai fahimci aure yake buqata har dai Kalmar nan d'aya da yake ta furtawa *"mata ta"*kuma ko ba haka ba farhan mutum ne da ya kamata ace ya buqaci aure sbd tun rasuwar Amrah bai sake yin wani aure ba. Haka ne fuad amma aure yanzu ba a shirya ba ta ina ma z'a fara wanda ko nema banji ya fara yi ba ,,, haka ne gwaggo amma matsΓ lΓ r da yakΓ© ciki za a dubΓ domin ina tsoron kar yawΓ n tunΓ nin son aure ya masΓ yawΓ har qwaqwalwar shi ta kasa dauka aje abinda ake yiwa gudu ya faru sae dai kuma samuΓ± wacce za'a aura masa ne matsala ba ma auren ba but yanzu gwaggo ba wata wacce kika yaba da hankalin ta kuma of course zata so farhan....ni kuwa ina zan sani fuad yanzu kai a gurin aikin ku nan asibiti ba wata wacce kake ganin jinin ta ya had'u da farhan?gwaggo kinsan fa farhan mutum ne da baya kula mace bare har shiri ya shiga tsakanin sa da ita but wannan yarinyar leesa fa wacce ke yawan zuwa gurin Ku me zai hana a tuntu6e ta muji ko zata iya auren farhan a halin da yake ciki.....shine fa amma kuma kana ganin zata yadda ta aure shi idan taji matsalar shi ?ba mamaki zata amince sbd naga kamar tana tausaya mishi kuma idan aka yi auren ina ga ba wata matsala tunda aka yi masa abinda yake so wanda inshaAllah qwaqwalwar shi zata sami natsuwa , in yaso bayan aure a fita waje da shi zuwa asibiti.... Eh lallai kayi magana inshaAllah kuwa zamu zauna nida mahaifinka da kuma kawun shi Basheer duk abinda suka ce sae na tuntu6i ita leesa kafin muje ga iyayen ta.
To gwaggo bari na masa allurar bacci domin ita kad'ai ce tafi sauqi a samu ya saki Afrah .
Bayan yayi masa allura ne ya fita daga gidan yayinda gwaggo ta zauna tana ta nazarin maganganun fu'ad.
Afrah kuma ta tafi toilet a gurguje tayi fitsari wacce bata fito ba sae da ta watsa ruwa.
A 6angaren leesa kuma tana fita gidan bata zarce koina ba sae qauyen da take zuwa gurin boka taje mai da bayanin abinda ya faru tana buqatar in da wata hanya yayi gaggawar karye wannan magani, nan boka ya nuna sam ba wata hanya inda da kukan ta da komai take roqon sa ya dai duba amma yace sae dai tayi haquri domin kuskuren d'agawar da tayi har Afrah ta riga ta had'a ido dashi yaja mata don haka ba fashi yau sea an d'aura auren Afrah da farhan muddin d'ayan su yana numfashi a doron qasa, cikin tsananin takai ci ta bar qauyen wanda tana cikin driven sae kawai kalmar boka ta fad'o mata a rai kalmar ita ce *"Ba fashi a yau sai an d'ura auren Afrah da Farhan muddin d'ayan su yana numfashi a doron qasa"* Ta furta a fili cewa "kenan hakan na nufin idan na kashe d'ayan su ba zancen aure,gud idea ba makawa zanyi abinda nake ganin shine dai dai domin kuwa zan sa ayi taron mutuwa a maimakon na d'aurin aure. Nan ta qara wa motar ta wuta bata zarce koina ba sae gidan su Farhan tana fitowa ta had'u da taro a bakin qofar gidan sae rarraba goro ake bata san lokacin da jakar hannun ta ta sa6ule qasa ba sbd jin sunan wacce aka d'aura aure da ita wanda hakan yasa tayi mamaki.
To masu karatu muje zuwa muga shin meyasa leesa tayi mamaki da jin sunan wacce aka d'aura aure da ita shin sunan ta ne taji ko kuwa na Afrah?
*Futha Luvπ π»&Billy giroπ* π π π π π π π π π π [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [9/19/2016]
π π π π π π π π π *~AFRAH KO AMRAH ~* π π π π π π π π π
*Na Bilqis Sidibeπ π»&Billy giroπ*
*π 32π * Qafafun ta ne taji sun kasa d'aukar ta ta samu da qyar ta shiga cikin gidan da shigar ta tace"gawggo me nake shirin ji a bakin qofar gida? D'aurin Aure ne leesa d'aurin auren da yazo mana kai tsaye na Afrah da farhan....ihu ta saki ta d'ora hannu a ka tace"na shiga tara! shike nan shike nan gwaggo kun auradda Afrah ga Farhan! ha! wayyo Allah na! .....gwaggo tace"ah ah leesa lafiyar ki kina qoqarin tara mana jama'a haka....wlh Gwaggo dole ne Afrah ce ta ban tausayi qaramar yarinya ayi mata auren wuri haka wacce ko qidan dangi yanzu ne ta fara.
Nan gwaggo ta nisa ta ja hannun leesa suka zauna tace"Ni kaina na tausaya ma Afrah matuqa kuwa don dai ba yanda zamuyi ne kawai abu ne da ya riga yazo domin farhan ya rikice mana kamar wani mai aljanu shi sae anyi masa aure da Afrah duk yabi ya hauka ce mana har sae da aka kira malamai duk wanda yazo sae dai yace a gaugauta yi masa auren shi yafi , ba yanda muka iya dole aka gaggauta d'aura auren.
Amma shine gwaggo ko a sanar da ni ko Allah zai sa na samo malamin da zai duba shi ko ayi dai dai..... ko da yake ni ba kowa bace a gurin ku ina faman cusa kaina ne kawai.
Ba haka bane leesa kina fita gidan nan abun ya fara rikicewa sae da Fuad yazo ya masa allurar bacci amma kamar ba a yi ba domin ko minti biyar ba a yi ba ya tashi,shine fa tun daga lokacin bamu sake samun natsuwar sa ba sae da aka d'aura auren nan,,,
Shiru leesa tayi yayinda take magana a ranta cewa _"lallai sae yanzu na qara tabbatar da aikin bokan nan yana ci tamkar yankan wuqa,sae dae kuma aikin nasa ya fad'a inda bai dace ba a bisa kuskuren da na aikata wanda ya zama dole na gyara kuskure na ta hanyar ganin cewa wannan auren bai d'ore ba_"
Bayan ta gama tace"amma dai gwaggo da mamaki aji cewa kun aura masa er qaramar yarinya kamar Afrah me zai gane da ita face kawai ya lalata mata rayuwa, ni a gani na gwaggo da raba auren nan a kayi domin za a cuci rayuwar Afrah ne kawai".....ta yaya kike ganin za a raba auren nan leesa? Cike da zumud'in samun nasara ta share hawayen ta tace"gwaggo indai aure farhan keso a gaskiya ba Afrah ya kamata a aura masa ba cikakkiyar budurwa ta dace da shi domin yaji dad'in d'ebe qishirwar da ya jima yana d'auke da ita kuma ko ba haka ba Afrah ba komai take iya yi na aikin gida ba kuma karatun ta fa tayi yaya da shi naga kamar zai yi mata wahala da aure a kanta,,,haka ne leesa amma...... Amma me gwaggo fisabilillah ko ni kuka tuntun6a bazan aure shi ba duk da cewa ina da tsayayye wanda zan aura kuma ina matuqar son shi amma akan farhan zan iya haqura da duk wani d'a namiji sbd kawai na taimaka masa yaji dad'in rayuwa yanda kowa keji sbd ni a matsayin en uwa na d'auke ku bana jin akwai wani abu da zaku nema a guna da baxan iya muku shi ba,wanda ko yanzu a shirye nake da na aure shi indai har za a rava auren sa da Afrah domin shine yafi dacewa da kowanen su , shi ya samu ya auri wacce zata iya da lalurorin shi ita kuma Afrah ta samu ta qarasa karatun ta cikin sauqi, ko ya kika ce gwaggo?
Sosai gwaggo ta nisa kafin take cewa "sosai kinyi tunani leesa sae dai mun riga ki yin wannan tunanin amma muka haqura da hakan sbd farhan ba aure kad'ai yake so ba Afrah dai ce yake so ya aura ba wata ba wanda idan muka ce mu raba auren to komai zai iya faruwa sbd yanzu qwaqwalwar Farhan ba kamar ta kowa bace abu qalilan zai iya sa qwaqwalwar shi ta kasa d'auka ya haukace, shiyasa muke ta kaffa kaffa da shi , kuma zancen karatun Afrah ba matsala bane sbd za a fita da farhan qasar indiya zuwa asibiti yayinda zasu samu masauki a gun wani abokin mahaifin sa inda za'a nemawa Afrah makaranta a can taci gaba da karatun ta....shin gwaggo kin manta cewa idan farhan yaji sauqi dole zai koma ga aikin shi ko kuwa zai zauna ba wani aikin yi ne?a'a zai dai nemi aiki a can har sae Afrah ta kammala karatun ta sae su dawo sbd dama a can yayi karatu har suka so su d'auke shi aiki ya nuna yafi so yayi aiki a qasar su,amma har yanzu suna son ya koma qasar su domin su d'auke shi aiki. kinji dalili.
*Billy giroπ&Bilqis Sidibeπ π»* π π π π π π π π π π [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [9/21/2016] π π π π π π π π π ~*AFRAH KO AMRAH ~* π π π π π π π π π
*Na Billy giro π& Bilqis Sidibeπ π»*
*Note* *```Mun san a page 32 zaku ga munce farhan yΓ yi karatu a qasar India to a gaskiyΓ kuskure mukΓ yi qasΓ r larabawa muke son sakawa domin haka muka tsaro novel d'in mu tun farko but muna fatar zΓ kuyi haquri da kuskuren da mukayi.```* Luv uπ
*π 33π * Shiru leesa ta yi yayinda abin cewa ya gagare ta . Nan ta shiga tunanin wata mafitar kuma. Gwaggo tace"yadai leesa ko da wata magana ne ?no gwaggo ba komai sae dae nace Allah ya sanya alhairi ya kuma basu zaman lafiya shi kuma Farhan Allah ya bashi lafiya. Amin amin leesa Nan leesa ta tashi wacce kallo d'aya zakayi mata kasan cewa tana cikin yanayi. Sae da tayi sallama da gwaggo kafin take fita gidan.
Washe gari su Afrah suka harba zuwa qasar Oman. Wanda koda suka isa suna cike da gajiyar zaman jirgi. Suna zuwa masaukin abokin mahaifin Farhan suka huta suka ci abinci sannan aka kaisu 6angaren da zasu zauna.
Da shigar su 6angaren ko zama ba suyi ba suka ji door bell Afrah ce ta bud'e qofa tayi tsaye tana kallon leesa da ke janye da akwati yayinda mamaki yake d'auke a fuskar ta. Leesa ta shafo gefen fuskar Afrah tare da fad'in "kinyi mamakin gani na ko, ga shi kuwa jirgi d'aya muka shigo da ku sae dai mune sahun farko na shiga jirgin inda ina ciki naga shigowar ku"
Afrah tace"Amma anti shine baki mana magana ba,domin ba mu san cewa tare zamu zo ba bcs gwaggo bata sanar da mu ba" kallon ta kawai leesa ta yi taqi ta bata amsa sbd ko mum farida bata san da zuwan ta ba bare gwaggo.
Nan ta maida duban ta gun Farhan wanda tun lokacin da ta shigo kallon ta yake tace"Farhan nazo ne domin na taya ku zama bcs nasan zaku buqaci haka kasancewar kun saba rayuwa ku uku shiyasa nazo domin na zame muku cikon ta uku ,ina fatar kunyi farin ciki da hakan kuma kuna maraba da ni? Da sauri farhan ya gyad'a mata Kai sbd yanda ta tsure shi da kallo.
Afrah tace"gaskiya anti naji dad'i domin har kuka na yiwa gwaggo kan tazo mu tafi tare tace baza ta zo bΓ ashe akwai surprise d'in da take son bani na zuwan ki. Uhm Afrah kenan,,, mene ne Anti? No ba komai. Yauwa Anti ko zaki kira mana gwaggo mu sanar da ita cewa mun iso lafiya? KinΓ nufin abokiΓ± mhfin farhan bai kira gwaggo ya sanΓ r da ita ba? ....oops am sorry Allah na manta cewa ya kira.... _to ai yanzu na tuna miki baqar makira kawai to ko gwaggo taji cewa ina qasar nan tare da ku ba yanda zata yi domin ban zo ba sai da na shirya_ Tayi maganar ne cikin zuciya.
Nan ta haura sama kamar ita ce jagoran tafiyar yayinda su Farhan ke biye a bayan ta .
D'akin tsakiya ta d'auka ta bawa farhan na farko Afrah na qarshe. Nan kowa ya shiga d'akin shi sbd shirin bacci kasancewar dare yayi.
Afrah ta riga kowa fitowa daga wanka sbd tsoro wacce har fitsari take ji amma bata yi ba ruwa kawai ta watsa a gaggauce ta fito.
D'akin Farhan ta nufa d'aure da towel a jikin ta . Bata jima da shiga ba ya fito daga wanka ya qaraso gurin ta yaja hannun ta suka zauna tare da fad'in "mata ta bacci kika zo muyi? um um Uncle tsoro nake ji bazan iya bacci ni kad'ai ba...yauwa ai dama ina so nace kizo ki taya ni bacci kinga ko jiya da ki ka kwana a gurin gwaggo kasa bacci nayi,amma kinga yanzu ba gwaggo sae mu riqa yin bacci kamar yadda muka saba. Shiru Afrah tayi tana kallon Farhan da har yanzu mamakin canzawar shi take duk da gawggo ta sanar da ita dalilin samun matsalar shi. Can tace"to uncle ka manta cewa da ma ba a tare muke yin bacci ba kawai na kanyi bacci kan cinyar ka ne idan kuna fira da gwaggo da kun gama firar tafiya kake 6angaren ka. Eh Afrah to kin manta yanzu mu mata da miji ne dole zamu riqa yin bacci a tare. Shiru tayi sbd ita d'aurin auren a wasan kwaikwayo ta d'auke shi bata d'auka cewa da gaske bane.
Haka shima farhan shiru yayi yana kallon ta cike da son ya samu gamsuwa da ita kamar yanda ango da da amarya keyi. Wanda duk sha'awar da yake jin tana azazzalar shi va yin kansa bane wannan turaren da leesa ta masa ne yake d'auke da hakan har ma yana wasu abubuwa kamar yaro/wawa.
Hakan yasa ba ruwan shi da tunanin Afrah yarinya ce shi dai ya samu yaji ya gamsu.
A nan zaune d'in da suke ya fara mata abubuwa sae lalla6ata yake yana mata wayo kan cewa bacci zasuyi da haka har suka qarasa hawa gadon nan ya kashe wuta tare da qoqarin zare mata towel . A rikice Afrah tace"uncle meye haka towel d'in jiki na ne fa not bedsheet" Tamkar bada shi take zancen ba tuni yasa qarfi ya zare towel d'in gashi ba komai a jikin ta inda nan yaji sauqin ci gaba da yin abubuwan shi. Afrah da bata ta6a sanin meye haka ba duk ta tsorace sae kuka take tana so ta qwace kanta daga farhan nan ta saki razanannen ihu da jin wani abu na qoqarin ratsa cinyoyin ta ai kuwa nan fitsarin da take ji ya kufce mata inda kai tsaye taga an ture farhan koda ta duba leesa ce. Da hanzarin ta ta fad'a kan jikin leesa tabi ta qanqame ta, jikin ta sae qyarma yake ta koina.
Nan leesa ta kunna wutar d'akin tare da kallon farhan da yaja bedsheet ya rufe jikin sa tace da Afrah"jeki d'aki" Ba musu har tana had'awa da gudu ta bar d'akin. Ta dakatar da Farhan da ke son bin bayan Afrah tace"wace irin jaraba ce haka farhan?yace"mata ta ce fa...ai nasan matar ka ce ban kuma ce zan hana ka yin wani abu da ita ba, sbd Allah ya riga ya hallata maka ita ba wanda ya isa ya haramta ma ita. Kunji ta kamar da gaske Allahn ta sani.
sae dai matar taka qwaila ce she is too young ba abin tsinta a jikin ta kuma bata san komai ba don haka dole ka bi ta a sannu kana nuna mata meye rayuwar aure sannan ko zakayi zancen kar6ar haqqin ka. Bazan iya haqura bane sbd ko jiya banyi bacci ba. _"Uhm ai na fika sanin baza ka iya haqura ba_"
Ta furta a fili cewa"haqura dai ya kamata kayi idan kuma ka kasa bacci ga TV nan ta zamo abokiyar firar ka" Nan ta kunna mishi TV ta jawo qofa ta fito cike da dariyar mugun ta a ranta.
D'akin Afrah ta nufa ta same ta ta qundundune cikin blanket sae kuka take a tsorace .