Afra ko amrah complete - Chapter 8
Afra ko amrah complete Chapter 8: Afra ko amrah complete Chapter 8. Ba jimawa suka zo a rikice ita da uncle Basheer da JB wanda yayi dai dai da isowar…
4,457 words
Ba jimawa suka zo a rikice ita da uncle Basheer da JB wanda yayi dai dai da isowar ambulance.
Ana shiga asibiti su fu'ad suka kar6e shi zuwa theater room gabadaya hanklin fu'ad ya gama tashi ganin fuskar wanda yake shirin treating,hakan ya dake ya danne kukan sa ya shiga bawa Farhan taimakon gaggawa.
Su uncle Basheer suna waje sae faman sintiri suke suna jiran fitowar su fu'ad.
Wayar gwaggo ce tayi qara yayinda umman fu'ad ya bayyana a screen jiki sanyaye ta d'aga wayar sae dai muryar da take sa ran taji ba ita taji ba,muryar Afrah ce taji wacce da ji tasha kuka tace"gwaggo meyasa uncle ya kashe wayar sa, ko yayi fishi dani ne don naqi daina kuka? please gwaggo kice yayi haquri na, daina kuka,ina so nayi magana da shi,gwaggo meyasa kika yi shiru ko yaqi haqura ne?da qyar gwaggo ta tsaida kukan da take ji yayinda ta shiga tunanin abinda zata ce da Afrah can tace"farhan baya kusa ya d'an d'aga"ok bye gwaggo i wiil call u letter before i back to hostel.
*Futha luv💅🏻&Billy giro😊*
🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:20PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [7:15AM, 8/7/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 ~*AFRAH KO AMRAH* ~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*Na* *Bilkeesu giro😊& Bilqis Sidibe💅🏻*
🏅2⃣4⃣🏅 Nan gwaggo ta kashe wayar jiki sanyaye, tana tunanin ko me za'a fito a sanar da su game da farhan.
Sun jima sosai sannan aka fito dashi, Fu'ad ne ya nufo gurin su gwaggo,kafin ya qaraso gwaggo ta tafi cikin sauri tace"ya ake ciki,inace dai bai mutu ba ko" Gwaggo ki kwantar da hankalin ki farhan yana raye sae dae unconscious koma nace ya shiga coma,inda ya sami raunuka da kariya biyu a qafar sa ta hagu,amma kar ki damu gwaggwo sauqi zai zo inshaAllah. Gwaggo tayi shiru tana fadin"innalillahi wa inna ilaihi raji'un ya Allah ka tashi kafadar farhan. Fu'ad yace amin kafin yake zuwa dasu dakin da aka kai farhan.
Duk wanda ya shiga sae ya zubar da qwallah bcs gabadaya jikin farhan bandage ne se kussuwar hancin sa kadai sae idanun sa ake gani.
Jikin kowa a mace suka sami guri suka zauna. Leesa kam kasa zama tayi tana tunanin rashin karamci irin na mom farida domin ita ce tasa akaje har aiport aka banye ma farhan tayar mota, sbd taji hakan da kunnen ta a lokacin da take waya da wanda yayi aikin. Qarasawa tayi gab dashi tana ci gaba da kallon shi, fatar ta d'aya kar farhan ya sami wata naqasa a jikin sa,domin dama zubin kyaun sa ne yaja ta. Nan kuma ta shiga wani tunani idan mom farida taji farhan bai mutu ba zata iya sa azo a qarasashi.nan ta shiga maganar zuci. _ya zama dole naje na san yanda zanyi da mom farida kar ta sa a qarasa shi, idan kuwa har dukiya take buqata zan bata wasu qadarorin da mahaifina ya mallaka min_ Nan tace da gwaggo Allah ya sauwaqe ni zanje gida na dawo Gwaggo ta gyda mata kai.
Fitar leesa keda wuya wayar gwaggo ta shiga ruri kallon wayar ta shiga yi tana tunanin me kuma zata ce da Afrah domin bata son tasan wani abu ya faru da farhan. D'aga wayar tayi tace har yanzu fa bai dawo ba"to gwaggo zan sake kira anjima.. a'a Ku koma hostel haka... Why gwaggo ko dai wai uncle fishi yake dani shine kike 6oye min?a'a ba wani fishi da yake da ke, to gsky ni bazan koma hostel ba sae nayi waya da uncle, shiru tayi tana kallon farhan wanda ba a ma san yaushe ne zai farfad'o ba....kinji gwaggo don Allah ki bar ni na zauna na en minti, da nayi waya da uncle zan koma hostel... haquri zakiyi Afrah. Kuka ta fashe ma gwaggo dashi cikin shagwa6a tana mai fadin Allah gwaggo dana koma hostel baza a barmu mu fito ba ko yanzu mama ce ta fito da mu, kuma ni bazan iya bacci ba idan banyi waya da uncle ba... Gwaggo kasa ce mata komai tayi tana tunanin dama tasan wataran sae hakan ta faru wannan sabo da farhan ya ma Afrah zata wahala ne wani lokaci....JB ne ya katse ta da cewa gwaggo bani wayar na lallashe ta, Nan ya qar6i wayar ya qara a kunnen sa tare da fadin Afrah, da sauri ta share hawayen ta cike da jin d'adi tace"yes uncle please kayi haquri ka daina fishi da ni kaji,,Afrah nine uncle JB ba farhan ba...to ina uncle? uncle ya daga kiyi haquri ki koma hostel kinji,nan dai JB yayi ta lalla6ar ta har ya samu ta yadda zata koma hostel. Nan fu'ad ya kar6i wayar ya sanar da mahaifiyar sa halin da farhan ke ciki don tasan yanda zata riqa yiwa Afrah wayo kar ta sake kira har a samu Allah ya farfado da farhan. Sosai umman sa ta cika da jimami kafin suke ajiye wayar.
Cike da tausayi umman fu'ad ta qara lalla6ar Afrah sannan suka fice hostel ita da Amrah.
Da dare bacci ya gagari Afrah sbd kwanciyar da ta saba yi kan cinyar farhan kafin ta samu bacci ya dauke ta. Haka tayi ta juyi tana kallon Amrah wacce tuni tayi baccin ta sharkaf.
Ganin da gaske ta kasa bacci gashi tana jin tsoron kasancewar ta ita kadai a farke, Nan ta dauko teddy ta wacce ke cike da qamshin turaren farhan wacce farhan ke mata wayo da ita idan ya fahimci baccin ta bai yi nauyi ba kuma yana buqatar ya tashi se ya dauko teddy ya shafe ta da turaren sa ya kwantar da ita kusa da Afrah shi kuma yaje zuwa aikin sa.
Rungume teddyn tayi tana mai shaqar qamhin turaren farhan har ta soma jin tamkar shine a kusa da ita,daga haka kuwa bacci mai nauyi ya kwashe ta.
*Billy giro😊&Futha Luv💅🏻*
🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [8/10/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *~AFRAH KO AMRAH ~* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*Bilqis Sidibe💅🏻 & Bilkeesu giro😊*
🏅2⃣6⃣🏅 Bala'i!cewar Nina wacce ta d'aga hannu zata kai wa Afrah mari,Afrah ta riqe hannun!tana qoqarin fara dame da Nina.... dakata Nina!kar ki yadda ki had'a jiki da ita zata rainaki banni da shegiya na ci ubanta yanzu na mata dukan tsiya dama ina da cikin ta" cewar senior wacce suka sami sa6ani da Afrah dazu da safe.
Tana gama fadin haka tayi d'amara tayo cikin Afrah da bulala zata fara dukan ta, Afrah ta duqa ta kwashi qafafunta sae ga senior qasa tumus, nan Afrah ta haye ruwan cikin ta ta shiga kai mata duka ta koina.
Nina tazo da gudu, Amrah ta tattare ta tana ta bata haquri, yayinda Afrah ke ci gaba da dukan senior wacce ta kasa yunqurawa ta tashi sbd yanda Afrah ta d'obo qasa ta watsa mata a ido ta kuma cika mata baki da ita tana ci gaba da kai mata naushi duk bakin ta yayi jini.
Wannan senior wacce ta ja Afrah da safe ko yanzu ita ce tazo ta ja Afrah, Wanda yayi dai dai da Nina ta bangaje Amrah tayo cikin Afrah..... Ke! ke!lafiya me yake faruwa"cewar VC wacce ta shigo ganin lafiyar hostel.
Nina bata bi takan Vc ba sae qoqarin take kaiwa Afrah duka, vc tace"ke Nina ba magana nakeyi da ke ba,me ya had'a ki da Aleesa har kika mata jina jina kuma kina qoqarin had'awa da er qaramar yarinya tahowar jiya jiya.
Nina tace"mama er qaramar yarinyar da kika kira tahowar jiya jiya ai ita ce tayi ma Aleesa jina jina ba ni ba...bana son shashanci Nina na fa san halin ki ta yaya Afrah zata yi wa Aleesa haka ko kunyar fada ba kya ji ace Afrah ce tayiwa Aleesa haka!wlh mama ita ce, Vc ta kalli Afrah wacce ta wani tunzuro baki kafin tace wani abu Afrah tace"mama ai sune suka fara tsokana ta"afrah kenan da gaske ke kika yiwa Aleesa haka?eh mama ita ce wai sae ta dake ni.
Ya salam ikon Allah Afrah ,yanzu er qarama dake kika iya fad'a da babba haka kuma wa ya gaya miki ana dukan senior.....ai barta mama wlh mama yau sae ta sha kashin tsiya... Nina a gabana kike fadin haka ban hana Ku dukan yaran mutane ba bare Afrah er j.s.s one da ba komai suka sani ba....mari na fa tayi mama, kai Nina wai meyasa ba kya iya zama sae kin ma mutum sharri,mama ki tambaya kiji fa ai shine silar fad'an su da Aleesa..... Mama ruwan arwala muka zo d'iba ina tara buta ta ta buge min sae da ta watse, ta fad'i haka ne a shagwa6e, Vc taja Afrah jikin ta tana lallashi tace kar kiyi kuka Afrah, ya isa inace Nina yau kun fahimci abinda nake sanar da ku ko yaushe duk makarantar nan ba wanda yafi Ku yiwa senior rashin mutunci,, sae gashi kun had'u da wacce ta fi ku har tana yin dambe da ku,kuma kar inji kar ingani kuce zakuyi wa Afrah wani abu,,kema Afrah ki kiyaye dukan siniyo ba a yin haka kinji, sannan ta kalli wacce Afrah ta bawa kashi,idanu sunyi jajir sae fitar da ruwan hawaye suke, ga baki duk ya sundule yana fitar da jini, tace ke kuma Aleesa ki jira ni yanzu muje clinic a duba ki. Nan mama taja su Afrah da Amrah zasu fice, Nina wacce ta kai qololuwar suquwa tace"haba mama wlh Allah wannan hukun cin baiyi ba, Nina ni kike gaya ma haka, in banda rashin hankali wa zai biye wa d'an j.s.s one,ai sai dai kuyi ta fahimtar da su har su fahimci yanda zaman makaranta yake ba wai da sunyi abu ku dake su ba,kuma bari kiji in gaya miki duk naji wani tashin ta shina sae na sanar da Abbanki ai kinsan abinda ke nan. Vc na gama fadin haka ta wuce Nina ta kalli Aleesa tace"hm cab!ke kin yarda j.s.s. one tayi miki dukan tsiya a banza,taci bulus kenan... Kan Bala'i !kina wasa dani Nina sanin kanki ne bana cewa komai a gaban mama domin kar ta hana ni abinda nayi niyya,na fison idan na aikata tukun ko zata ji, domin wlh ni idan baki na kadai ta fasa to ni zan manta ubanshi ne,yanzu mama kawai nake jira ta fita daga hostel d'in nan zan farfasa mata jikin ta ne na kuma sa juniors su mata wanka da ruwan gishiri,ta yanda zata fahimci ruwa ba sa'an kwando bane kuma ta gane da farkon sa'a ce kawai tayi bai wai qarfin ta ko dabarar ta yasa ta min haka ba.
Vc na shiga dasu Afrah d'akin su, Afrah ta marairaice tace"mama wai uncle bai kira ba har yanzu?Afrah waya ta ba caji kuma ki kwantar da hankalin ki ai farhan ba zai share ki haka kawai ba.
*Note* Idan baku manta ba nayi muku bayani a page 10 cewa mahaifin farhan yana da qannai guda biyu da suka fito ciki d'aya, wato gwaggo da Alhj usman,Alhj usman shine mahaifin fu'ad,wannan vc da kuke ji itace matar Allhj usman (Abban fu'ad) wato mahaifiya ga fu'ad. Wanan kenan ina fatar wad'an da suka manta sun tuna.
Afrah tace"to mama mu haka za mu riqa yin komai da ruwan sanyi....to Afrah haka school life take but kar ku damu zan had'a ku da wata innar da zata riqa taimaka muku da ruwan zafi, amma yanzu kuzo muje gidana kuci abinci kuyi sallah, ta fad'i haka ne sbd cike take da tausayin Afrah kan had'arin da farhan yayi wanda har yanzu bata ji ance ya farfad'o ba.
Nan taja su suka wuce tare da Aleesa wacce aka ajiye clinic amma bata d'auka cewa Vc dasu Afrah zata je gidan ta ba, ta d'auko rakiya sukayi ma vc zasu koma hostel ne,domin sae qisa yanda zata ci uban Afrah take da ta koma hostel.
A 6 angaren su leesa kuwa.
Sorry I can't continue let tomorrow please.
*Futha Luv💅🏻&Billy giro😊* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 8/9/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 ~*```AFRAH KO AMRAH```* ~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*```Bilqis Sidibe💅🏻&Bilkeesu giro😊```*
🏅2⃣5⃣🏅 washe gari Afrah na farkawa taga cikin dakin da take kuka kawai ta shiga rerawa sbd mafarkan da tayi tayi sae yayi mata kamar tana gida.
Amrah ce ta farka ta same ta ta dora kai kan guiwa tana ta rusar kuka kamar wacce aka yiwa mutuwa.
Cike da damuwa Amrah tace haba Afrah me kike ma kuka tun da asuba haka? Allah uncle bai kyauta min ba nace masa bana son boarding school amma shine ya kawo ni.
Ajiyar zuciya Amrah ta sauke tace"kinga sannu sannu zamu saba kinji yanzu muje muyi sallah. Nan ta samu da qyar taja ta suna fito wa gaban house. Afrah taja birki tace wai ke Amrah ina zamu je haka kina fama da bokitayya,har da wata buta? Ruwa zamu je diba mana mu sami na wanka da na arwala....dibar ruwa fa? Eh man idan bamu dobo ba wa kike tunanin zai ba mu?
Afrah bata ce komai ba nan Amrah taja ta sae fanfo. Afrah na ganin layin mutane tace"kai! yanzu duk layin nan a gaban mu suke kuma har sae mun jira sun d'iba?eh amma zamu bada butar mu ne su en muna na arwala koda zamu gama sallah layi ya kai kusa kai gare mu cos kinga ba mutane sosai. Turo baki kawai tayi tana kallon mutanen da suka tsura mata ido, cike da tsiwa tace"to kije ki tara butar mana kinga sae faman kallon mu suke da idanun su kamar mujiyoyi.
Da mamaki Amrah tace"Afrah...to qarya nayi kalle sufa,wlh Allah duk d'iya bata daina kallo na ba sae munyi ta tunda ba ubanta ne ya kawo ni makarantar ba....ke! mind ur tongue ko kuma wlh yanzu na hora ki" cewar wata senior wacce ke zaune gaban fanfo tana cika bokitayya tana bawa junior suna kai mata kwana. Afrah ta kalle ta sama da qasa ta watsar tace"horo sae kace wata masa, ki dai hora wad'an da kike horawa su da suka dauka,wawaye kawai kuna ganin kanta kamar gijen shirwa amma kun wani bi mata layi kamar bayi tana baku ruwa kuna kai mata bayan duk abu d'aya kuka zo yi a makarantar....cikin 6acin rai senior ta miqe ta nuna Afrah da yatsa tace ke!kin san abinda kike fad'a kuwa,a da nayi niyar raga miki ganin ke new comer ce baki san komai ba amma wlh yanzu sae kin gane kuren ki! Amrah tace"don Allah sister kiyi haquri wlh bata san makari ba ne.... Am not ur sister!ta nuna juniors din da take ba ruwa suna kai tace"sune sisters dinki domin sune tsaran ki!ni dole ki kirani da Anti.... Ai gwai Amrah! ji yanda wannan abar ta wani gwasale ki! Tana fama da rama kamar wata figaggiyar kaza har taga bakin cewa a kira ta da Aunty.... Fuuu senior tayo cikin Afrah,Amrah tayi saurin shiga tsakanin su tayi ta bata haquri gurin duk ya cika da student ana kallon ikon Allah yanda junior ke zagin senior har tana fadin Amrah da kin barta wlh na kakkarya lenge lengen jikin nan nata, senior kuwa sae zillo take tana son ta cafko Afrah.
Da qyar aka samu wata senior taja Afrah inda waccen senior ke fad'in yau duk wanda zai miki tsaye a cikin makarantar nan sae nayi discipline dinki!
Suna shiga daki senior tayi ta fahimtar da Afrah ba a yiwa senior haka respect ake basu tamkar aunty ki ta gida,Afrah jin ta kawai take ita ina taga Anti bare ta san da hakan. Nan senior ta fita ta dawo, sae gata tare da junior dauke da ruwa aka ajiye ma su Afrah.
Bayan sunyi wanka sun shirya cikin uniform, su kazo gun Kari, Amrah ce ta had'a musu tea ta ba Amrah nata.
Afrah na kur6awa ta furzar tace"Amrah lafiyar ki zaki mana tea da ruwan sanyi! To Afrah ina kike tunanin zamu sami ruwan zafi baki ga da ruwan sanyi mukayi arwala da wanka ba. Nan Afrah ta le6ace baki zuwa kuka kamar taga uncle d'inta kusa tace"wayyo Allah uncle ka kashe ni,nayi arwala da ruwan sanyi nayi wanka da ruwan sanyi sannan kuma nasha tea mai sanyi uhm uhm uncle ka kashe ni da ka kawo ni boarding school,nan ta hau bakin ta ta fara rera kuka iya qarfin ta duk house a na jin ta. Wata senior ce tazo ta leqa dakin tana fadin wace ce ta cika mana house da kuka sae kace gidan da akayi mutuwa!cike da masifa Afrah ta d'ago domin ganin wace ce, mamaki tayi ganin Nina wacce suka had'u da ita gidan su JB, ita ma Nina tayi mamakin ganin Afrah nan ta ya mutse fuska kamar wacce taga kashi tace" wai dama kece mtsw ta buga tsaki ta wuce. Afrah ta yunqura zata tashi Amrah tayi saurin rirriqe ta tace"please Afrah kar kija mana wani bala'in....bana so Amrah! bana so kina hana min abinda nayi niyya! kinsan bana son raini yaza tazo har dakin mu tana fama da guntun gashi kamar bindin akuya ta watsa min banzan kallo ta wuce! Yi haquri Afrah... Mtsw ni tashi mu wuce da Allah!
Nan suka wuce zuwa area class ba tare da kowannen su yasha tean ba.
Bayan sun dawo sunje fanfo dibar ruwan arwala, Afrah ta hango Nina tsaye a bakin fanfo ta tasa junior gaba suna d'ibar mata ruwa. Nan Afrah ta fizgi butar da ke hannun Amrah tace"bani ki ga".
Afrah na zuwa bakin fanfo bata damu da bokitin da ke tare ba, Kawai ta tara butar inda rabin ruwa na shiga ciki rabi na bin jikin butar suna sauka cikin bokitin da ke tare kuma tana sane tayi hakan.... Nina ta buge butar har saida ta kufce a hannun Afrah duk ruwan da suka fara shiga suka watse, ba wata wata Afrah ta kai mata wawan mari wanda yayi da isowar senior da suka sami sa6ani da safe.
*```Billy giro😊&Futha luv💅🏻```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 8/12/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 ~AFRAH KO AMRAH ~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
Na Bilkeesu giro😊&Bilqis Sidibe💅🏻
🏅2⃣7⃣🏅 Leesa na zuwa gida ta sami mom farida ta gama waya kenan rai 6ace,tana ganin leesa ta hau ta da masifa tace"wato shine sae da kika je domin hana faruwar hakan to qwalelen ki domin lokaci ya qure miki.... Haba mom farida kinsan yanda nake son farhan amma kika sa aka mishi haka bayan na roqe ki kan ki bari wannan karon wlh zanyi duk yanda kike so na ganin yasa hannu a takardun....kinga dakata yanzu dai kowa tasa ta fishsheshi ai naji labarin farhan ya na asibiti to wlh indai bai mutu ba,lallai kuwa zaki ji labarin mutuwar sa a daren yau... A'a mom farida don Allah kar ki min haka indai dukiya kike so nayi miki alqawarin zan baki kadarorin da mahaifi na ya mallaka min.... kin kuwa san irin dukiyar da Alhj Basheer ya barwa Afrah, duk dukiyar nan da kika ga muna damawa cikin ta kad'an kika gani domin cikin kashi dari na dukiyar sa,kashi ashirin muka sami damar ci domin tamanin d'in duk ya mallaka su da sunan Afrah!ta yaya kike tunanin er dukiyar da kike son mallaka min zata amfane ni, keda mahaifin ki dukiyar da yake taqama da ita iyakar shi sahun farko a masu kudin garin kaduna amma Alhj Basheer tsaf za'a jero shi a sahun farko na masu kud'in Nigeria ....mom farida ai bance baza ki mallaki dukiyar ba nidai abinda nake so dake kar kisa a qarasa farhan don girman Allah... ke Allah kika sani da zaki wani had'a ni da shi! ki sani tuni na fahimci soyayyar farhan tafi damunki ba wai ganin na mallaki dukiyar ba.
Don haka kowa tasa ta fishsheshi.
Tana gama fad'a ta wuce leesa ta bi ta har zuwa dakin ta tana ci gaba da roqon ta.
A 6angaren su gwaggo kuwa ita kad'ai aka bari a d'akin tana sallar isha'i su uncle Basheer sunje masallaci.
Leesa ce tazo ta same ta ta sallame sallah kenan, wanda sae da gwaggo ta kammala addu'oin ta sannan suka gaisa da leesa. Sukayi shiru na d'an wani lokaci leesa ta katse shirun da cewa"ni kuwa gwaggo me zai hana a fitar da farhan qasashen waje sbd ya sami kyakkywar kulawa, gwaggo ta nisa tace"ai leesa asibitin nan da kike gani suna da komai na kayan aiki kuma suna da qwararrin likitoci, zai sami kulawa fiye da yanda kike tunani,amma gwaggo ganin nike kamar can zai fi kuma ko don Afrah bana son taji labarin wani abu ya faru da farhan hankalin ta zai tashi sosai gashi tana school, amma idan aka fitar da shi waje za'a iya ce mata tafiya yayi, ai leesa kinsan zata iya damuwa kan sae tayi waya da shi da ya na garin da baya garin,haka ko dazun mukayi ta fama da ita da qyar aka samu Jb ya lalla6ata. Leesa tayi shiru tana tunani domin hankalin ta yafi kwanciya idan aka dauke farhan da qasar nan, duk da cewa ta samu ta shawo kan mom farida amma bata tunanin ta haqura da gaske,ko kuma taje ta canza ra'ayi bata sani ba,hakan kuwa zai iya sa taji mutuwar farhan kai tsaye.
A 6angaren su Afrah kuwa sae da marece suka koma hostel dauke da flaks din ruwan zafi da suka samo gidan Vc da kuma kular abinci.
Da dare sunyi shirin bacci,suka dauko kular da suka zo da ita, faten dankalin turawa ne mai zafin gaske suka zuba a plate zasu fara ci, sae ga Nina da Aleesa sun shigo d'akin,kowacce da zabgegiyar bulalar ta.
Futha Luv 💅🏻&Billy giro😊 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [8/16/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 ~AFRAH KO AMRAH ~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
Na
Bilkeesu giro😊&Futha luv💅🏻
🏅2⃣9⃣🏅 Tashi dai ka zauna my dear sbd nasan bayan ka yayi ciwo sosai kana buqatar tashi zaune. Nan farhan ya tashi zaune wanda yayi dai2 da shigowar gwaggo. Murna ta shiga yi sosai tana godewa Allah, sae ga su Alhj Basheer,Jb,fu'ad sun shigo nan suka shiga taya gwaggo murna yayinda suka tambayi leesa yaushe ya farfad'o. Nan ta sanar da su yanxu ne farfadowar sa.
Fu'ad ya duba shi yace a bashi ruwa yasha, leesa ce tayi saurin tsiyayo ruwa a cup inda ta fakaici idon kowa ta zuba garin wani magani fari qal da shi. Taje ta bawa farhan har ya kar6a, gwaggo ta kar6i ruwan a hannun farhan tace"ai leesa ba a bawa mara lafiyan da ya jima bai farfad'o ba abu haka kawai yana da kyau ayi addu'a tukun. Tana gama fad'ar ta tofe ruwan da addu'a ta bashi yasha. Ran leesa yayi mugun 6aci idanuwan ta sukayi jajir. Fu'ad ya nemi a kawo ma farhan abinci ,gwaggo ta debo ta shiga bashi abincin da kansa. Sae dae tun shigowar su farhan bai ce komai ba sae kallon su yake. Da ya gama cin abinci Fuad ya keka shi zuwa toilet sbd yayi wanka, amma farhan ya kasa yin komai sae da fu'ad yayi masa wanka da brush inda ya shiga tunanin akwai matsalar da farhan ya samu domin baya yin komai sae ance yayi.
Sae dae bazai sanar da su gwaggo ba har sae yayi bincike ya gano inda matsalar take.
A washe gari ne ya gama binciken sa inda ya gano matsala biyu farhan yake dauke da ita, d'ayar matsalar cikin qwaqwalwar sa take, komai ba zai iya yi ba har sae an bashi command an kuma nuna mai yanda zaiyi,tamkar wanda ya manta abubuwa. D'ayar kuma abu ne da ya d'aga mishi hankali sosai wacce baya jin zai iya sanar da kowa.
Cike da damuwa ya sanar da su gwaggo matsalar da farhan ya sami ta rashin yin komai har sae ance yayi. Sae dae ya nuna musu ba wata matsala ba ce idan ana nuna mishi sannu sannu zai dawo normal.
Duk da haka sae dae sukayi jimami sosai.
A 6angaren sau Afrah kuwa sati biyu da suka wuce. Suna samun kulawa sosai a gun inna Adama wacce Vc ta hada su da ita haka ko Aysha tana iya qoqarin har yanzu domin tana kan nuna musu yanda ake zaman school.
Sae dai Afrah duk tabi ta rame sbd rashin waya da farhan amma tana waya da su gwaggo inda suka ci gaba da lalla6a ta kan cewa farhan yayi tafiya ya manta wayar sa amma in ya dawo zai kira ta, *hakan ya faru ne tun kafin farhan ya farfad'o*
A 6angaren su gwaggo suna cikin jimami ne wayar gwaggo ta shiga ruri, tana ganin Vc tasan Afrah ce, nan ta d'aga wayar se kuwa taji Afrah cikin kuka tana tambayar uncle nan gwaggo ta miqa wa farhan waya,kallon gwaggo kawai yake riqe da waya har sae da ta nuna mishi yanda zai yi,,bayan an nuna mai ya kuma yi shiru Afrah na magana bai bata amsa.
Cike da tausayi JB ke sanar da shi abinda zai ce ma Afrah kamar qaramin yaro. Da haka aka gama wayar Afrah kam da farin ciki ta yini har ta kwana.
Sannu sannu kwanaki na tafiya yayinda farhan ke samun sauqi kuma dai2 gwargwado ana nuna mishi yanda zai yi abubuwa har ya fara yin wasu abubuwa da kanshi.
A 6angaren leesa kuwa ba abinda ta matsu irin lokacin zuwa visiting yayi sae damun gwaggo take kan cewa aje da farhan ko Afrah zata fi farin ciki,gwaggo tace"farhan da baya iya taka qafar sa zuwa wani guri,leesa tace amma gwaggo ya kamata aje da shi ko akan wheelchair ne, to Allah dai ya nuna mana lokaci muna masu rai da lafiya.
Yau ce ranar visiting Afrah sae murna take zata ga uncle,gashi har yanxu bata san yayi had'ari ba.
Gwaggo,JB,Fu'ad,Baban Amrah,leesa sune suka d'unguma zuwa visiting,fu'ad ne ke tuqa motar inda ya zarce cikin makarantar se staff quarters ya tsaya qofar gidan vc wato mahaifiyar sa. gidan shine na farko ba nisa da gate.
fu'ad ne ya taimakawa farhan ya fito,ya jingina shi a jikin mota zai d'auko Wheelchair wanda in kaga farhan a jikin mota tsaye tamkar lafiyar sa qalau.
Su Amrah ne tafe sun fito daga hostel zasu je gate sbd en class d'in su ne messengers. Amrah ce ta hango su duk sun fito daga mota tayi saurin ta6o Afrah cike da murna tana nuna mata su Farhan, wani ihun murna ta saki har sae da idon mutane yayo kanta taje da gudu ta fad'a jikin farhan, da qarfin tsiya farhan ya ture ta har sae da ta fadi,gwaggo tace subhanallah! farhan me yake faruwa Afrah ce fa....gwaggo ban santa ba kuma bana son ganin ta,don Allah mu bar nan gwaggo,ido na zai fashe idan na sake kallon ta.
Mamaki qarara a fuskar Afrah wacce ta tashi tsaye tana kallon farhan da yasa tafukan hannyensa ya rufe idon sa gam yana qoqarin ganin ya shiga mota.
Cike da murna leesa ke kallon alamarin yayinda kan kowa ya d'aure musamman Afrah da ta dasqare guri d'aya hawaye wani na bin wani.
Futha Luv💅🏻&Billy giro😊
🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [8/21/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 ~AFRAH KO AMRAH ~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
Na Billy giro😊&Bilqis Sidibe💅🏻