Afra ko amrah complete - Chapter 7
Afra ko amrah complete Chapter 7: Afra ko amrah complete Chapter 7. Farida tace"ya haka keda nake ta sauraren kiran ki na aika miki mota....bari kawai mom…
4,498 words
Farida tace"ya haka keda nake ta sauraren kiran ki na aika miki mota....bari kawai mom farida gayen ya mugun hallakani ashe kwata kwata bai san aikin sa ba wlh! ban san me yasa yazo shi kadai ba ya kuma tsaya er qaramar yarinya tana ja'inja da shi har ta bude gambu mota ta fado,wanda hakan yayi dai dai da isowar farhan, dole ya gudu buqata bata biya ba. Kuma wani abin takaici nan farhan ya barni,duk da irin kukan da na mishi ina bashi haquri abinda ban ta6a yiwa wani d'a namiji ba, amma ya tafi ya barni wai shi ba zai iya biya wa wani guri ba sbd halin da Afrah take ciki,shine ya wani bani kudin taxi bayan ba alamar taxi a gurin. Amma lallai farhan din nan shi bai lura da ba abin hawa ba ko kuma ya manta cewa idan ana ruwan sama abin hawa wuya yake....mom farida Ta ya zai fahimci hakan bayan gold dissa na cikin matsala. Gashi shi kuma dan iskan gayen can nayi kiran shi a waya yafi a qirga akan kiran sa ne ma cajin wayata ya qare bai d'aga ba, daga qarshe ma sae yayi rejecting, wanda hakan ya nuna min ya gudu da mota da kuma kudi ba tare da ya biya min buqata ta ba. Hm ai mutanen basu da kirki domin tunda naji kince shi kadai yaje nasan bai sanar da sauran ba don kawai yaci kudin shi ka dai. Hake ne man,gashi yanzu zafi uku uku kenan bana ga mota da kudi bana ga biyan buqata, na kuma sha kashin ruwa a banza, ,kuma wai duk akan er qaramar yarinya hakan ta faru dani,amma na rantse... Mtsw mom bari kawai na watso ruwa na dawo na gaya miki wata mafitar!
Hm ko ce mata akayi idan Allah ya kare bawansa akwai wani mahaluqi da ya isa ya cutar da shi. Muje zuwa dai muga abinda leesa ke shirin yi wanda take tunanin Allah zai bata sa'a.
*```Futha Luv💅🏻& Billy giro😊```*
®NWA✍🏻 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:20PM, 11/30/2016] Billy Geeero: : [ 8/1/2016] ~*AFRAH KO AMRAH* ~
*Na* *Billy giro😊 & Bilqis Sidibe💅🏻*
🏅2⃣1⃣🏅 Bayan Leesa ta fito daga wanka ne, take ce ma, mom farida"ni shawarar da na yanke itace"dole zan koma gurin boka sbd na fahimci duk inda Afrah ta shiga farhan na biye da ita hakan kuwa zai min wahalar sace ta kuma asiri na zai iya tonuwa tunda ko yanzu ban san cewa yabi bayan mu Don haka abin da naga yafi sauqi zan je gurin wani boka na da ke min aiki domin bai ta6a min aiki bai ci ba,kuma ba magani yake ba mutum yayi aiki da kansa ba, Shi da kansa yake aikin domin aljani yake turama wanda za'a yi ma aikin,kuma da ya tura aljanin komai ya kammalu,,amma akan Afrah za'ayi aikin ba farhan ba, domin Afrah yarinya ce ba addu'a ta sani ba,don haka nake so ya tura mata baqin aljani lokacin da taje makaranta ta 6ace 6at aljanin ya kai ta wata uwa duniya ko kuma a mata kurciya tabi duniya! Shike nan matsala ta ta tafi!shi kuwa farhan ko zai iya ganin aljanin yabi bayan shi oho! Mom farida ta kwashe da dariya tace yaga me!ai daga ranar shida afrah sae dae a mafarki ko zai gan ta. Bare ma nafi son ayi aikin kafin a tashi daga school koda zai je daukar ta sae dae ya samu bata nan"leesa tayi maganar kafin suke tafawa ita da mom farida.
Sae da akayi kwana biyu sannan leesa ta tafi qauyen da bokan yake,cike da murna ta dawo domin ganin take har aikin yayi,sae sauraren gobe take sbd sae gobe yace mata za'ayi aikin.
Haka ko akayi domin washe gari farhan yaje daukar Afrah da wuri wanda yana ma tsaye aka buga tashi, amma koda yaje class d'in su bai ganta ba, har kowa ya watse farhan na ta faman neman Afrah shida uncle Basheer wanda sunyi kusan awa d'aya suna neman ta basu gan ta ba kuma duk inda ake tunanin yaro mai rashin ji na shiga bata can. Nan farhan yace da uncle Basheer ko dai JB ya dauke ta? Bana tunanin haka sbd junaid tun kafin a tashi ya fita. Ai kuwa nan hankalin farhan ya tashi sosai dmn Afrah bata ta6a mishi haka ba duk yazo daukar ta yana samun ta. Bai bar makarantar ba sae ma zama da yayi cikin mota tare da dora kansa a sitarin mota.........unce!firgitgit ya dago kanshi ya fito cikin motar da sauri,yayinda Afrah tazo da gudu ta fada jikin sa, ya qanqame ta sosai kamar wanda ya shekara bai ganta ba. Ya kalli JB da ke tare da su yana faman murmushi yace"Afwan ba haka naso ba wlh" Ba wani gsky kasa na tsora ta kasan fa abinda ya faru da Afrah bayan kwana biyun nan,shine ka fita da ita kafin a tashi da school don kawai hankali na ya tashi....yi haquri na manta da waya ta ne da na kira ka na sanar da kai,to me ya fitar da ku ba'a ko tashi ba?wlh Afrah ce yau rashin jinta ya motsa... Farhan yayi dariya yace"waya gaya ma motsawa yake ai kullum tana tare da rashin ji,,,a'a my little wife kam tana jin magana yau dai ne,,,farhan dai murmushi kawai yayi domin ya fahimci Jb baya son ana ce ma Afrah bata ji, yace"to naji tana jin magana amma kuma yau wa ta tsokana?ita da wata ce suka qullah ko er me.... Keep and go only me! cewar Afrah,JB yace to kaji, to da suka qulla ita Afrah kullum akace mata keep and go bata ajiye wa ko kallon kirki ma baza ta ma ta ba, amma ita Afrah da tace dole a ajiye taci, to shine yau qawar ta wacce suka qullah abun, ta gaji sae da ta bari Afrah taje break fast ta kwashe kaf sweets din da ke cikin jakar Afrah ta cinye gasu da yawa fa,nan fada ya hadu tsakanin su sae da nace tazo muje na siyo mata wani sweets,,,farhan ya bude ido yace kace sweet din da yawa?sosai kuwa ba kai ke bata ba?JB kasan Allah wlh bana ba Afrah sweets da yawa bcs bana son tana shan zaqi sosai...cab ai kuwa duk makarantar nan Afrah tafi kowa shan sweets, domin har suna aka sa musu ita da qawar ta Amrah,Afrah sweet,Amrah chewing gum haka ake kiran su, domin ko yaushe ka gansu even during class ma zaka sami Afrah da sweet a bakin ta Amrah kuwa chewing gum, not only break fast time.
Cike da damuwa farhan ya lumshe ido yace"oh Allah"sannan ya kalli Afrah wacce ta noke fuskar ta a cikin jikin sa,wanda ya fahimci ko yanzu sweet ne a bakin ta,ya fara magana cikin fada yace "poppy luv! Kinsan bana son ki dauki abu ba tambaya,amma shine kullum kike yi!meyasa! nace me yasa!?dago idon ta tayi wanda har hawaye sun fara fitowa dmn ko kadan bata son fada har dai idan farhan ke mata shi, kama kunnen ta tayi tace"please uncle am sorry"wace ce qawar ki Amrah?motar JB ta nuna mai, wanda yayi dai dai da fitowar Amrah ciki domin tun dazu bacci take sae yanzu ta farka, farhan yace"that's y ashe wannan Amrah ce qawar ki shiyasa rashin jin ya hadu guri daya, Amrah da bata san me ake ciki ba tazo da murnar ta gurin farhan tace"lah uncle dama Kaine uncle din Afrah"nine Amrah ina dad da bai zo daukar ki ba? Mun hadu dashi kan hanya uncle JB yace da shi idan ya siyo mana sweets zai maida ni gida, to meyasa ba a maida ke ba bayan an siyo? Afrah tace tana son taje gidan mu shine yace mu fara zuwa school tukun muga idan kazo, farhan ya kalli Afrah wacce tayi saurin nokewa kan jikin sa tana ci gaba da kuka. Yace da Amrah ok muje na maida ki gida. Nan sukayi sallama da JB suka wuce. Har aka kai Amrah gida suka zo gida Afrah bata sake cewa komai ba duk da cewa ta daina kuka,ta dai qi magana ne sbd farhan yaqi sake mata fuska.
Da shigar su farhan ya wuce 6angaren shi Afrah ta wuce 6angaren gwaggo.
Sae da yayi wanka ya tafi 6angaren gwaggo ya samu ita ma Afrah an mata wanka nan ya jawo musu abincin su suka ci.
Da suka gama cin abinci ne Afrah ta kalli farhan dake fira shida gwaggo cike da nishadi, nan taji qarfin cewa"unce a ina kasan Abban Amrah....a gidan ku na sanshi!nan Afrah ta le6a ce baki zuwa kuka ta tafi da gudu ta fad'a jikin gwaggo. gwaggo tace"yau kuma kai ke fada da Afrah abinda ban ta6a gani ba,,Afrah ba taji gwaggo wai ace ta debi sweet bata sanar da ni ko ke ba, tabi'ar da na tsana a rayuwa ta shi Afrah keyi,sweet din da ba kullum nake bari taje da shi ba,ashe aikin banza nake har qarawa take akan wanda na bata....ya isa farhan kaga sae kuka take,, haba gwaggo bafa tabi'a mai kyau bace,kamar halin 6era ne wanda zai iya bin ta har girma.
Haka ne kuma,ke kuma Afrah kar ki sake yin haka ba kyau,, shidai farhan bai ce komai ba ya tashi zai fita,cikin kuka Afrah taje ta tarbo gaban shi, tace"pls uncle kayi haquri bazan sake ba"farhan yayi tsaye yana kallon ta wanda kallo d'aya zakayi masa kasan yana jin zafin kukan da take yana jurewa ne kawai. Sauke ajiyar zuciya yayi yace shike nan,idan kika sake... kamin dukan tsiya har sae nayi kukan jini,gwaggo ce ta fara dariya kafin farhan yace"lallai akan ki zan sayi bulala na ajiye, ya fadi haka ne yayinda ya ja hanun ta suka zauna ya shiga share mata hawaye,yace idan kika sake rashin ji kuma zan kai boarding school ne,girgiza kanta tayi tace"Allah uncle bana son boarding school nayi qanqanta,ai ba yanzu zan kai ki ba sae kin shiga secondary,maqale kafada tayi tace"gsky uncle bana so,amma idan na sake tsokanar wani na yarda,haka kike ce?eh,, to shike nan gwaggo ki zama shaida. Gwaggo dai murmushi kawai tayi amma tasan da wuya Afrah ta daina tsokana, farhan kuwa bazai iya rabuwa da Afrah na en kwanaki ba bare zancen boarding school.
*Billy giro😊&Futha Luv💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:20PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [8/4/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 ~*AFRAH KO AMRAH* ~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*Na* *Bilkeesu giro😊&Bilqis Sidibe💅🏻*
🏅2⃣2⃣🏅 A 6angaren leesa kuwa tun lokacin da farhan ya fito da su Afrah school har suka je gida tana biye da su. Inda kanta ya daure sosai na ganin Afrah tare da farhan kuma tana da tabbacin boka ya turo baqin aljani sbd tun da farar safiya taje qauyen gudun kar ya manta wanda a gaban idon ta taji boka yayi magana da baqin aljani ya tura shi gun Afrah.
Cike da baqin ciki ta koma gida sae dai kuma tana isa gate ta kasa shiga sae juya akalar motar ta tayi zuwa qauyen da bokan yake.
Da zuwan ta bokan ya tarbe ta da maganar domin duk abinda ke faruwa baqin aljani ya sanar da shi. Dogon bincike ya shiga yi a cikin qwayar tsafin sa yayinda ya shiga kallon rayuwar Afrah tun lokacin da aka haifi Afrah har izuwa yanzu yana ganin komai tamkar video. Long time da qare binciken sa yayi shiru,sae zufa ke karyo masa ya kasa ce ma leesa komai domin tabbas a cikin rayuwar Afrah ya hango wani abu da ke sa duk mugun nufi baya fadawa akanta ,amma ba zai sanar da leesa ba har sae ya qara shan romonta ko zai iya sanar da ita daga baya,leesa ta katse shi da cewa"lafiya dai boka ko da wata matsala ne?akwai er matsala domin wannan yarinya da kike gani aiki daya baya yi da ita, kamar ya?ina nufin sae mun maimata abin da mukayi jiya,gaban ta ne ya bada ras domin ko kadan bata son maimata abin da sukayi jiya,ko fama da doyin jikin sa aiki ne bare kuma wani baqin garin magani da yake yi yana shafa mata a gaban ta. Cike da damuwa ta kalli bokan tace"ba wata hanya ne sae wannan? Inace tun jiya na sanar da ke,ba wata hanya sae ita, domin kusan ta ta dake tamkar muna kusan to rabuwar Afrah da Farhan ne,, haka ne kuma ka gaya min,, amma ki sani wannan karon bayan haka ta faru zamuyi wanka a tare da mazubin ruwa daya, ina fatar kin fahimta. Shiru leesa tayi ita wankan ba matsala bane a gurin ta irin hada jiki da shi amma tabbas idan zai kawo rabuwar Afrah da farhan zata yi koma me ne. Nan tace"da bokan na amince,nan boka ya washe wargazazzun jajayen haqoran sa har ana hango wani yauqi a bakin sa sbd daud'a. Daga nan suka shiga daki domin aikata mummunan aiki.
Wa iyazu billah.
******** Haka rayuwa taci gaba inda lokaci ya tafi sosai domin su Afrah har an kammala primary school. Yayinda leesa keta rabon ido na ganin 6acewar Afrah amma shiru har anyi shekaru. ga boka sae yaudarar ta yake yana sheqe ayar sa da ita a duk qarshen wata wanda yaso ace kullum yake samun hakan, sae dae karatun da ta fara yi ne a Abuja bazai basu wannan damar ba.
Leesa har ta fara gajiya ganin aiki yaqi ci yaqi cinye wa hakan yasa ta fara tunanin ko wata mafita zata nemo.
Zaune take sae tunanin mafita take, mom farida ce tazo ta same ta. Fuskar ta a daure tace"leesa nifa na gaji da shirmen da kuke keda bokan ki, wane irin abu ne kusan shekaru hudu magani bai ci ba,wai kuma sae faman abu d'aya ake ba canji. Nima mom farida abun yana damuna sosai kullum sae yace min aiki ya kusa ci tsirif ya rage amma shiru har na gaji, shine yanzu nake tunanin wata mafita.. ....mtsw ni yanzu na gaji da jin shawarar ki ace yanzu duk yanda kuka shaqu da farhan har ya dauke ki kamar er uwa ace kin kasa masa kissar mata ki kai masa takardu ya sa hannu kin tsaya sake da baki wai sae ya fara sonki! Haba mom farida koda ace farhan ya fara sona ta ya zan kai masa tarkadu ya sa hannu ko takardu wadan da idan ya gansu na gama yawo tunda akan hayyacin sa yake dole ya fahimci takardu waye......lallai yanzu ke dama duk a tunanin ki sae ya san takardun mene ne zai yiwa signing,ke mace ce fa kina iya kai masa takardu a matsayin wasu takardun asibiti ne,tunda kema karatun asibiti kike, se ki samu ki jashi da fira har ya sa hannu ki kar6i abinki bai san yayi ba. Hmm mom farida wlh farhan na daban ne komai akan tsari yake yinsa ba a yanda kike tunani ba....to lallai kuwa zanyi aikin da kai na idan ke baza ki iya ba, ga hanyoyi da dama sunzo har dai yanzu da Afrah ta fara girma ko mutuwa farhan yayi bani da baqin ciki sbd Afrah zata iya sa hannu akan tarkardun tunda dama mallakin ta ne.... A'a don Allah kar ki sa a kashe farhan ki qara bani lokaci zanyi duk abinda kike so.... gaskiya leesa sae dae kiyi haquri da son farhan domin son da kike mishi bashi zai sa na fasa aiwatar da abinda nayi niya ba!tana gama fada ta fice. Yayinda leesa ta shiga tension tasan ba makawa mom farida zata iya sa a kashe farhan ta kuma sa a kama Afrah tayi signing akan dole. Kut "dole na hana faruwar hakan domin don son farhan kadai nake wannan yaqin ba don ki mallaki dukiyar ba" ta fadi haka ne a fili kafin take barin falon.
🏅2⃣3⃣🏅 Afrah ce kwance kan bed sai sharar bacci take,wacce yanxu zata kai 12yrs ta qara kyau fiye da yanda take yarinya domin kamar yanzu ne asalin kyanta ke fitowa. Ta dan qara jiki ba kamar da da take sililya ba yanzu dai dai take ba qiba ba rama.
Farhan ne ya shigo cikin sauri yana fad'in poppy luv! yana hango ta kan bed yayi saurin rufe bakin sa yace da gwaggo da ta sallame sallah"ashe bacci afrah keyi nake faman kiran ta,, gwaggo tace"ai da ka tashe ta da kar ka tashe ta kasan farkawa zatayi tunda ka shigo dakin"saurin fita zanyi kafin ta farka dama so nayi muje a siyo kayan makarantar ta,bcs ban sani ba ko akwai wani abinda zata buqata....wai Farhan da gaske kake zancen kai Afrah boarding school,eh mana gwaggo kinsan rashin jin Afrah sae abinda ya qaru gashi kuma har yanzu bata daina kukan zuwa school ba,shine abun ke damuna sosai...amma farhan bata yi qanqata ba kuwa, no akwai iren iren ta a can, kuma ko ban kai Afrah boarding ba dole na canza mata school bcs of *JB international school* din nan da take ciki kwata kwata JB ya shagwa6a ta duk abinda ta ga dama yi take,wanda ba don gifted ce ba da sae dae ta riqa cije bindi kan shiririta.
Haka ne kuma da har na so nace kabar ta school din tayi boarding a ciki tunda makarantar akwai borders amma bayanin da kamin na fahimta, sae dai kasan JB ba zai ji dad'i ba har dai a yanda suka shaqu shida Afrah, haquri zai yi domin bana son rashin jin Afrah ya kai ta ga ta6ar6arewar tarbiyarta. Ni zan fice ina sauri sbd zan koma asibiti anjima gashi da safe ne zamuyi tafiyar. Nan ya kama hanya zai fita....Afrah wacce tun dazu ta farka taji duk abinda suke fadi, tace"uncle wlh bana son boarding school, at all bana son a canza min school, jiki sa6ule yaje ya zauna kusa da ita cikin muryar lallashi yace"poppy luv haquri zakiyi, sbd gaskiya ba zan ajiye zancen boarding school ba bcs na gaji da rashin jin ki kuma keda kanki kika ce idan baki daina rashin ji ba akai ki boarding school kin tuna...uhm uhm no uncle i cant remember ,please kar ka kai ni boarding school,ta fadi haka ne yayinda ta kwanta kan cinyoyinsa tana ci gaba da kuka. Am sorry Afrah na riga na yanke hukunci ba kuma zan canza ba,, hawaye sha6e2 ta dago tana kallon shi tace"yanzu uncle so kake naje inda ban san kowa ba, ba kai ba gwaggo ba Amrah ba uncle JB ni kadai ban san kowa ba kamar wacce aka tsinta" tayi maganar ne cike da muryar kuka had'e da shagwa6a har ma ba a gane me take fada sosai. Komai farhan ya kasa ce mata sbd duk kukan da take bai ta6a jin zafin da yake ji a ransa kamar yanda yake ji yanzu ba. Nan ya tashi ya fita ya bar Afrah sae kuka take yana jin tana roqon gwaggo kan ta roqa mata shi. Gwaggo dai haquri kawai ta shiga bata.
Sosai ya jima kafin yake dawo wa dauke da kaya niqi niqi Afrah na ganin shi ta turo baki tare da kauda kai akasin kullum da take tarbo shi da gudu ta kar6i kaya.
Gwaggo ce ta taimaka masa ta kar6i wasu kayan sbd sunyi masa yawa a hannu ga kuma wasu kayan da mai gadi ya shigo da su.
A gajiya farhan ya zauna kusa da Afrah da taqi yarda ta kalli ko gefen da ya zauna, yace duba kiga na siyo miki duk abinda kike so,har da wani sabon chocolate na siyo miki kingan shi, Afrah kam kamar ba da ita farhan ke magana ba ko kallon chocolate din taqi, yace"to albishirin ki"nan ma ta masa shiru, yace"Afrah ni kike sharewa,, uhm uhm ta fadi inaji"sae kin duba sayayyar da na miki tukun, nan Afrah ta shiga duba komai da taga kamar na mutum biyu ne,tace"uncle siyayyar kamar ta mutum biyu ce"lumshe idon shi yayi yace"keda Amrah zaku je.... Yeee! uncle thank u!ta fadi hakane yayinda ta maqale shi,tana murna nan take kuma idon ta suka ciko da qwalla tace "but uncle I gonna miss u"no my Afrah zan riqa zuwa miki visit every month kinji... Maqale kafada tayi tace"ni kullum nake so kaje"...ba zai yiyu ba Afrah,yana fadar haka ta fashe masa da kuka yace"um um my Afrah stop crying idan ba so kike ko a month kar naje ba. Kuka take ji sosai amma haka ta haqura ta share hawayen ta domin tana son ya riqa zuwar mata. Wayar farhan tayi qara ya daga wayar yayi magana ta en mintina ya bawa Afrah tare da fadin ga Amrah kuyi magana ita ma taji labari a bakin abban ta sea murna take ke kinxo kina kuka. Nan ta kar6i wayar wanda sun jima suna wayar hakan yasa damuwar Afrah ta d'an ragu.
Farhan ya kalli agogo yace gwaggo bari naje na shirya na tafi asibiti..... Zanje uncle, ok to...kash sorry JB ya kira ni a waya yace zai zo ki kaima mamansa yawo bcs yaji zanjen zan kaiki school gobe shine ya buqaci haka,ok uncle yaushe zai zo?inaga yana kan hanya ki shirya kafin ya qaraso.
Kafin farhan ya fita har Jb yazo a tare suka fita inda farhan ya nufi hanyar asibiti Jb ya nufi hanyar gidan su.
Suna shiga Jb ya hadu da wata er uwar shi wacce bazata wuce 15 yrs ba tazo da gudu ta tarbe shi, ta kalli Afrah sau daya ta kauda kai.
Suna shiga falo umman JB na ganin shi da Afrah ta bala'in sha mai toka.ً Afrah ta gaishe ta, ta amsa mata ciki ciki. ta wuce fuuu zuwa upstairs, nan Jb yabi bayan ta suka je daki,inda ta shiga yi masa fada sosai kan cewa tun dazu Nina tazo tana faman jiran ka amma kayi zaman ka shine da zaka shigo kawani kwaso Afrah kuka zo tare don kawai ka nuna min baka da buqata da Nina ita da ma ar er uwarka..mom ba haka bane wlh tafiya Afrah zatayi gobe to boarding school, shine na kawo ta bcs bata ta6a zuwa nan gidan ba kullum nace zan kawo ta sae kice min a'a... But about Nina inace kina zancen ne kawai shiyasa ban dauki abun serious ba bcs kinsan da zancen Afrah,, junaid ni qaramar yarinya ce da kullum zan zauna ina maka zancen da bashi bane, haba mom gsky ni Afrah nake so kuma zan iya jiran ta... Ni kuma bazan iya jiran ta ba junaid domin na matsu na ga en jikoki na, inace qaramar yarinya kake so ka aura ai ko Nina yarinya ce...no mom nifa ba zancen qaramar yarinya nake ba kawai dai Afrah nake so... bari kaji in gaya ma dole sae ka auri Nina in yaso daga baya ka iya auro Afrah... gasky umma bana ra'ayin mata biyu...to ko mahaifin ka da ya fika cijewa ya amince da zance na, don haka tun wuri ka sani Nina na kammala makarantar ta za'a daura auren ku,,JB ya kalli umman sa cike da son yayi kuka ta qara da cewa kuma yanzu yanzu nan kaje kuyo shopping kai da Nina domin ban kwana tazo mana gobe zata koma Abuja sbd hutun makarantar su ya qare. Ba yanda Jb ya iya haka yaja Afrah da Nina domin zuwa shopping. Sae dai tun da suka shiga mota ran Junaid ya qara 6aci har dai yanda yaga Nina ta shige gaban mota ta bar Afrah baya,kuma sae faman hararar Afrah take ta jikin mirror se dai shi bai lura da hakan ba, sae Afrah da ta lura wacce jin take idan nina ta matsa da hararar ta zata iya dambe da ita ba ruwan ta da ganin nina ta girme ta domin ko kadan bata daukar raini nan tace"uncle JB ni ka maida ni gida"shopping zamu je yi Afrah ki bari idan muka dawo....no uncle ni ina son na koma gida, jB da baya son ganin 6acin ran Afrah nan ya garzaya ya maida ita gida. Amma da sukayo shopping sae da yakai mata tulin kayan da ya siyo mata wanda hakan ya qara sa Nina ta qara jin haushin Afrah.
Da dare gwaggo ce ta packer musu komai Abban Amrah ya kawo ta nan gidan ta kwana sbd jirgin safe zasu bi zuwa abuja bcs a cikin garin Abuja farhan ya nema musu makaranta.
Da safe Afrah na tashi tayi arba da kayan su da aka packer, ai kuwa tayi zaune tana ta rusar kuka da qyar gwaggo ta rarrashe ta taje tayi wanka ita ma Amrah tayi wanka suka shirya, farhan yazo sukayi break fast sae kallon Afrah yake wacce tayi suka suku.
Suna gama cin abinci suka kama hanyar airport.
Koda suka sauka garin Abuja wata mata wacce ake kira da"Hajiya saudah wato mahaifiya ga fu'ad" da yake dama fu'ad mazauna garin abuja ne aiki ne yakai sa garin bauci. Itace ta tarbi su farhan suka je har makarantar a tare sbd itace VC din makantar abu ga mai galihu har hostel farhan ya bisu bcs duk student na class, shida kanshi ya za6a musu room dinda zasu zauna wanda bai wuce daukar mutum biyu ba,wanda ba don galihu ba da sae dae su zauna dogon room. Farhan ne ya tsara musu komai yanda ya dace kamar wani mace wanda yayi haka ne don kawai ya samu Afrah ta sake,duk da haka bai hana Afrah taci kuka kafin ya bar makarantar ba.
Tafe yake cikin garin bauci ya fito daga airport sbd har jirgin su na dawowa ya sauka.
Leesa ce keta faman sheqa gudu tana biyar farhan a baya duk tabi ta rikice tana ta faman kiran farhan ta waya sai dai line busy bcs a lokacin waya yake da Afrah wacce har yanzu kuka ta ke.
Leesa da qyar ta samu wayar farhan ta shiga, sae dae Hankalin ta ne ya gama tashi hango tayoyin motar farhan da suka fara juyi kafin kace me har tayar gaba ta cire inda motar ta shiga juyi da farhan wanda sae faman salati yake yana qoqarin ganin motar ta tsaya amma ina! tuni ta fada daji tana kaurar itatuwa long time kafin take haduwa da wani qaton dutse ta tsaya se hayaqi ke fita a cikin ta.
Leesa kuwa tana qarasowa ta fito mota da gudu, sosai ta shiga rudu hango motar farhan yanda tayi daqa daqa kamar ba d'an Adam a ciki.
Taro ya hadu sosai sbd hanyar ta kasance ta mutane,tambayar leesa suka shiga yi ko dan uwan ta ne amma tamkar da statue(gunki) suke zancen, hakan yasa wasu daga ciki suka tafi domin bawa farhan taimakon gaggawa,kafin a samu a kira en sanda,
Anyi minti talatin kafin ake samun fitar da farhan a cikin motar, fararen kayan sa duk sun rine zuwa ja.
Nan en sanda suka nemi sanin en uwan sa inda mutane suka nuna leesa acewar suna sa ran er uwar sa ce,da qyar en sanda suka samu tayi magana inda ta basu numbar gwaggo. Ta tsure farhan da kallo wanda yake sheme ba ya motsi sae jini da ke ta fita a jikin sa,gaban ta sae dukan uku uku yake bata son aje asibiti taji labarin cewa farhan baya raye.
Police kuwa ana basu numbar gwaggo suka kira ta suka sanar da ita halin da ake ciki.