Kenza eBookz

Afra ko amrah complete - Chapter 6

Afra ko amrah complete - Chapter 6

Afra ko amrah complete Chapter 6: Afra ko amrah complete Chapter 6. Tun da safe leesa ta shirya tsaf inda ta shafe jikin ta da kalolin turarukkan magani.…

4,213 words

Tun da safe leesa ta shirya tsaf inda ta shafe jikin ta da kalolin turarukkan magani. Ta fito gidan ba tare da sanin farida ba. Bata zarce koina ba sae makarantar su Afrah,wanda yayi dai dai da isowar farhan,taji dad'in da ya tsaya a bakin gate bai shiga daga ciki ba domin ba kowa ake bari ya shiga da mota ba sae wane da wane, bata bari ya ganta ba domin bata so ya ganta. Kallon shi take ya zagaya ya bude ma Afrah gambu sae lallashin ta yake akan ta daina kuka, afrah kuwa sae qara shagwa6e masa take tana maqale kafad'a ita baza ta shiga school ba. Nan ya dauke ta ya dora a kafad'ar sa yana ci gaba da lallashin ta. Leesa kuwa takaici yazo mata iya wuya domin ta tsani ganin farhan da mace ko me qanqantar ta kuwa, bare a yanda taga yana ji da Afrah har wani fargaba take ji a ranta da ita kad'ai ta barwa kan ta sani. Wata er qaramar kwalba ta fitar tare da bud'e murfi yayinda wani baqin suracin hayaqi ya shiga fitowa a hankali bai zarce koina ba sae gun farhan ya shiga cikin idanuwan shi, wanda hakan yasa farhan yaji wani irin jiri mai qarfi ya d'ebe shi yayi saurin sauke Afrah kan jikin sa ya dafa jikin mota yayinda yake fitar da "bisimillah" a bakin sa had'e da karanto addu'o'i. Sannu sannu ya fara daina jin jiri har ya dawo normal,sannan ya kalli Afrah wacce tun lokacin da ya sauke ta sae kallon shi take tace"uncle baka da lafiya ne"girgiza kanshi yayi yayinda ya durqusa yana share mata hawaye yace "lafiya ta qalau poppy luv" JB ne ya qaraso gurin su bayan sun gama gaisawa da farhan yace "my little wife ya akayi kika makara yau tun d'azu nake dubin hanyar ki,, farhan "yace yau na kasa ciyo kanta ne har muka makara, kuka take tun gida sae yanzu na samu ta daina, kan makarar ma yasa ban shiga daga cikin makarantar ba na tsaya a gate. To ai gani nazo sae mu tafi ko, nan yaja hannun ta sae bye bye take yiwa farhan shima haka har sae da suka shige sannan ya shiga mota. Leesa na kallon shi yana qoqarin cusa hancin motar sa a cinkoson motocin mutanen da ke kawo 'ya'yan su makaran ta. Sai mamaki take yanda turaren ya shiga idon sa amma bai sa wani abu ya canza a tsakanin sa da Afrah ba, sae dae ta lura da lokacin da yake addu'a wanda yasa ta fahimci cewa kenan ko biscuit d'in jiya akwai addu'ar da yayi kafin yaci,hakan yasa maganin bai yi tasiri a jikin sa ba. Tace"lallai farhan idan kasan wata baka san wata ba"nan ta jefar da turaren hannun ta ya tarwatse ta shiga mota ta tafi hasale.

*Futha luv 💅🏻& Billy giro😊*

🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:20PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 7/28/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *~AFRAH KO AMRAH*~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*Na* *Bilqis Sidibe💅🏻 & Bilkeesu giro*😊

🏅1⃣9⃣🏅 Leesa na komawa gida ta shiga d'aki had'e da jefar da d'an yalalon gyalen ta,ta shiga rawayar daki tana tunanin mafita. Farida ce tazo ta same ta tace"tun jiya nake sauraren kije min da kyakkywan labari amma naji shiru. Shiru Leesa tayi tana tunanin me zata ce da ita. Ya kinyi shiru ba amsa kinsan fa ni aiki na ba wanda za'a tsaya wasa bane so nake na kwashe dukiyar nan kafin Hjy luba da 'ya'yanta su ankara.

Idan baku manta ba Hajiya luba ita ce kishiyar uwar Alhj Sadiq (wato baban Afrah,) kuma ina fatar kun fahimci farida ita ce matar da Alhj Sadiq ya auro bayan rasuwar Hajiya Zarah (wato mamar Afrah)🤔

Farida taci gaba da cewa sanin kanki ne ba abinda ya dawo da mu garin nan sae don mu samu sauran kadororin sa su koma hannun mu,sbd wannan karon baza mu iya yin yanda mukayi gurin mallakar sauran ba, sbd da sa hannun sa ne,wanda don na iya sa hannun sa ne yasa muka mallake su,har ma muka kwashe kud'ad'en sa da ke banki,amma wannan karon hakan ba zai yiyu ba sbd takardun filayen sa da gidajen sa duk da sunan Afrah ne kuma dole sae da sa hannun farhan muke iya mallakar su,kuma ni kad'ai nake son na mallake su bada wad'an can munafukan mutanen ba,shiyasa bana son ku jima kuna wata soyayya da farhan so nake da ya fara sonki kiyi qoqarin ganin yasa muna hannu sbd kinsan da maganin ya kama shi duk abinda kika ce yayi zaiyi ne ba tantama.

Rai 6ace leesa ke kallon farida"tace mom farida ni fa gaskiya kallo d'aya nayi ma farhan naji ina son shi kuma da aure ba guntuwar soyayya nake sonyi da shi ba,,hm amma leesa kin san dalilin da yasa na zo da ke ko, sanin kanki ne da zan iya wannan aikin ba abinda zai sa nazo da ke,domin ko giyar wake nasha bazan yi soyayya da farhan ba,asali ma bazan ta6a yarda ya ganni a cikin garin nan ba. Don haka idan baza ki iya ba tun wuri ki gaya min na nemo wata. Shiru leesa tayi tana tunanin fa matsayin 'ya take a gurin farida wato farida qaunar mahaifiyar ta ce da suka fito ciki d'aya amma tasan indai akan dukiya ne ba ruwan mom farida da dubin hakan zata iya nemo wata ta fita batun ta,kuma ko ta nemo wata shawo kan farhan zai yi wuya sbd addu'ar da yake yi,ko ba hakan ba ma baza ta ta6a yarda wata mace ta ra6i farhan ba domin ko Afrah yau d'in nan zata raba ta da farhan....da ke fa nake magana, amsar ki nake jira. Leesa ta nisa tace"mom farida baza ki gane bane farhan fa ya tsare kansa da addu'oi wanda ba kai tsaye ake shawo kansa ba,shiyasa nake so ki bari abi abun a hankali ba sai an saka gaggawa a ciki ba sbd kinsan cewa da yanzu kun mallake duka kadarorin bcs kunyi aje da 'yan fashin da kuka tura gidan Alhj Sadiq kan cewa sae Alhj Sadiq ya saka wa kowace takarda hannu kafin su bashi damar fita daga gidan,sae suka yi komai a gaggauwa ce har suka manta da zancen sa hannu,kuma koda suka tuna har ya fita, binshi da sukayi baiyi wani amfani ba sbd jin motar police yasa suka harbe shi ya mutu ba tare da sun sami abinda suke so ba, that's y yanzu nake son nayi komai a natse amma ina mai tabbatar miki da cewa yau yau d'in nan zan raba farhan da Afrah sbd ita ce babbar matsala ta domin na fahimci kulawar da yake bata ne kesa ba ya kula mutane, kin ga idan na raba shi da ita dole sannu sannu zai haqura ni kuma sae na fara qoqarin cusa soyayya ta agare shi. Idan har ma taqama yake da addu'a to aiki na na yau ba boka ba malam. Kamar ya leesa? Leesa taja hannun farida tace "mom farida zauna kiji"ina son ki bani number mutanen ki domin da yamma zanje gidan su farhan na d'auki Afrah muje yawo in yaso daga can na miqa musu ita suyi gaba da ita wanda har abada baza a qara ganin ta ba, ni kuma zanje asibiti gurin Dr Bilal yamin aikin da duk wanda ya ganni zai zaci naji rauni da gaske,acewar kidnappers na hadu dasu kan hanya suka kar6e Afrah ni kuma suka min rauni, kinga kuwa dole farhan ya haqura da qaddara domin ta tafi kenan ba zai sake ganin ta ba, nan farida ta ba leesa hannu suka tafa tace "ashe dai 'yata mai kwanya ce,, au duk a tunanin ki zaman da nayi a bariki na banza ne,,hmm to ke kina ganin Dr Bilal ba zai tona mana asiri ba..ya ma isa! shine fa gayen da nace miki mun had'u har kullum yana zowa muna d'ebewa juna kewa, jiya ne fa kawai bamu had'u munyi ba sbd hankali na ya karkata kan Farhan,farida ta bugo leesa cike da dariya tace dad'i na dake baki da kunya,to meye abin kunya mom farida koke fa kina damawa da naki Alhazzan.

" wa iyazu billah ya Allah ka shirya bayinka"

Da marece kuwa leesa ta shirya tsaf ba ta zarce koina ba sae gidan su farhan.

6angaren gwaggo taje ta shiga da sallamar ta,ta gaida gwaggo sannan ta gaida farhan da ke zauna kan sofa, ita ma ta nemi guri ta zauna ta kalli Afrah dake kwance jikin gwaggo wacce kallo d'aya ta yiwa leesa ta kauda kai, leesa ta ce"Afrah me aunty ta miki da baza ki tarbe ta ba? gwaggo tace"ita da uncle d'in ta ne,koda yaje d'auko ta makaranta ya samu tana fad'a da wani yaro,shine ya mata fad'a ya hana ta rama dukan da yaron ya mata,to fa tun sannan take faman fishi da shi taqi ta haqura taqi cin abinci taqi yarda na mata wanka,,, oh my dear Afrah zo qyale uncle muje yawon mu bada shi ba ko, zo kinji. Afrah da shegen son yawo tazo da murnar ta,nan leesa ta cire mayafi kamar wata er gida taje ta mata wanka gwaggo ta bata tufafi ta shirya ta tsaf.

farhan dai sae kallon su yake wanda ya dauki fitar da wasa sae yaga ashe da gaske ne.

Har mota farhan ya rakasu ya riqo hannun Afrah ya d'an rage tsawon sa kadan yace"puppy luv haka zaki fita baki ci abinci ba... Kar ka damu idan mukaje zan samar mata abinda zata ci.

leesa tayi maganar yayinda Afrah ta fizge hannun ta daga riqon da farhan ya mata, sbd har yanzu fishi take dashi,dan guntun murmushi farhan yayi ya kama hanya yana mata bye bye yana mai jin kewa kamar wacce zata tafi guri mai nisa, Afrah kam kallon sa kawai take dauke da fishi a fuskar ta ba tare da ta mishi bye bye ba.

Har zasu shiga mota Afrah ta juyo yayinda farhan ya juya,tace"uncle! ta kira shi ne cikin"daga murya sbd ya dan yi nisa da su,hakan yasa farhan ya juyo,nan Afrah ta sake masa murmushi tace"bye uncle"shima yayi mata murmushi yace "bye my Afrah"kallon su yake har suka fita daga gidan,bai koma daga ciki ba sae da yace"Allah ya tsare min ke my Afrah".

Suna cikin tafiya hadari ya had'u sosai suna isa Temako Super market ruwa suka fara sauka kamar a bakin qwarya, leesa ta sami guri ta Parker mota. Lema ta dauko ta kalli Afrah tare da shafo gefen fuskar ta tace"my dear Afrah kinga ruwa ake yi sosai ki zauna zanje na siyo miki ice cream,chocolate,biscut har ma da kayan wasa kinji,maqale kafad'a tayi tace"um um duk ina da su a gida ni yawo kawai nake so"oh Afrah bana son ruwa su ta6a ki kije kiyi rashin lafiya kinga uncle ba zai ji dad'i ba. Turo baki tayi tace Allah anti sae kinje dani ai ga umbrella nan a hannun ki bazan jiqe ba. Leesa taji kamar ta shaqe wuyan Afrah kan takaici ta dake tace"ok ina zuwa kinga an kira ni a waya bata jira me Afrah zata ce ba tabar gurin da nisa sannan ta d'aga waya tace"yauwa dama kuwa yanzu nake qoqarin kiran ka,nayi nawa aikin saura ku, kuzo ga yarinyar nan a cikin mota ku tafi da ita kuma motar ta zama taku hade da dubu dari biyar d'in da ke ciki. Ajiye wayar keda wuya ta hango shi tafe cikin kaftani kamar na kirki bai zarce koina ba sae cikin motar da Afrah take zaune yana shiga ya ja gambu ya rufe.

*```Futha luv💅🏻 & Billy giro😊```*

®NAW✍🏻 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:20PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 7/31/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 ~*```AFRAH KO AMRAH```* ~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*Na*

*Bilkeesu giro😊 & Bilqis Sidibe💅🏻*

🏅2⃣0⃣🏅 Yana shiga ya dorawa Afrah bindiga a goshi, ta juyo tana kallon shi a tsorace har tana qoqarin fara kuka yace"shiiii!ba abinda zan miki ni abokin uncle din ki ne yawo xamu je na siyo miki kayan wasa daga nan mu wuce gurin uncle. Da yake Afrah mugun tsoron bindiga ne da ita bata bi ta kan abinda yake fada ba ta shiga kuka tana kiran "Anty" Leesa kam tuni ta 6uya sae dae tana hango duk abinda ke faruwa. Ganin yanda Afrah ke kuka har tana qoqarin tona mai asiri yasa ya 6oye bindiga domin ya fahimci ya yi babban kuskuren nuna mata ita. Ya jawo ta jikin sa domin ya samu ya lalla6ata ya gudu da ita cikin kwanciyar hankali. Afrah kam ta riga ta tsorata da shi sae fizgar jikin ta take yayinda sautin kukan ta ke qara fitowa,ta manna masa uban cixo a hannun sa da ya rufe mata baki. Cikin zafin nama ya kai mata mari sbd jin zafin cizo. Nan tayi baya kanta ya bugi gambun mota sae kawai gambun motar ya bude ta suntu6a waje, da yake dama gambun motar a bude yake shine bai san da hakan ba. Sosai ya shiga rudu bcs Afrah na faduwa wata mota ta tsaya close to Afrah. Rudun sa ne ya qaru hango wanda ke ciki, ai ko ba shiri ya rufe gambun motar ya tafi agurguje. Farhan ne ya fito daga motar ya nufi Afrah cikin hanzari ya dauke ta sae kuka take yayinda jini ke fita a gefen bakin ta. duk ta rikice ta qanqame farhan sosai tana ci gaba da kuka. Idanun farhan sukayi jajiri sae kallon motar da wuce yake ko zai gane wanda ke cikin motar. Leesa ce tazo da gudu yayinda farhan zai saka Afrah a mota, sbd ko kadan baya son ruwan sama su ta6a ta sabida zazza6i suke sata. Bai saka Afrah a mota ba sae wani mugun kallo da ya bi leesa da shi har sae da yasa hantar cikin ta kadawa ta saki lemar da ke hannun ta. Yace"wane irin shashanci ne zaki bar min Afrah gurin wani bnza can har yana qoqarin hallaka ta! Wata irin ajiyar zuciya ta sauke a 6oye sbd ta fahimci bai gane ainihin abinda take shirin aikatawa ba.

Nan ta shiga fitar da hawayen munafurci wanda duk ruwan da ake kelawa kana hango gangarowar da suke kan kumatun ta.

Cikin murya kuka tare da qara marairaice murya tace"wlh farhan ita kadai na bari a mota sbd ruwan da naga anayi,sai na tafi ni kadài, ban ko qarasa ba na hango wani ya shiga motar yana qoqarin guduwa da Afrah shine nazo da gudu, amma wlh *Ban sanshi ba*gashi ya gudu da mota ta da kuma maqudan kudin da ke ciki. Sae dae ba damuwa ta bane tunda anyi sa'a bai je da Afrah ba,amma don Allah kayi haquri da nasan hakan zai faru da bamu zo ba. Farhan yayi shiru yana son gasgata zancen leesa har dai yanda take kuka tana ci gaba da roqon sa. Nan yaji ta bashi tausayi ya zaro kudi a aljihu ya bata yace kiyi haquri a halin da Afrah take ciki bana jin zan iya biya wa wani guri.

😂zo kuka leesa a wannan lokaci sororo tayi ta saki baki tana kallon farhan ko godiya ta kasa mishi har ya shiga mota ya tafi ya bar ta nan tsaye ruwa na faman dukan ta, ga lema tabi iska kuma gurin ba alamar zata sami taxi sbd ruwan da ake.

😂zafi biyu kenan buqata bata biya ba tasha kashin ruwa.

Farhan na isa gida ya dauki Afrah dake kuka tana rawar sanyi ya tafi da ita 6angaren gwaggo ya cire mata kayan jikinta da suka jiqe, gwaggo tace"lafiya me yake faruwa da ita naga jini a gefen bakin ta kuma sae kuka take tana rawar sanyi? Cike da damuwa farhan ya bawa gwaggo Afrah yace don Allah gwaggo a gasa mata jikin ta da ruwa masu zafi tukun.

Nan gwaggo ta shiga da ita toilet, farhan ya tafi ya canxo tufafi ya dawo yana da sintiri a bakin qofar toilet kyace wanda yakai patient asibiti yana jiran fitowar doctor. Sae da gwaggo ta d'an jima kafin take fitowa dauke da Afrah dunqule cikin towel, farhan ya amshe ta yana kallon fuskar ta da ya fahimci marin qwarai aka mata dmn yatsu sun kwanta tsaf kuma har gurin ya kumbura. Sosai yaji ta bashi tausayi yaje da ita kan bed ya zauna ya shafa mata mai ya saka mata tufafi sannan ya shiga yiwa gwaggo bayanin abinda ya faru. Gwaggo tayi taslima tace"ni har naga rashin haqurin ka da kace zaka bi bayan su hankalin ka bai kwanta ba, ashe wani mummunan abu ke shirin faruwa, oh Allah ya qara tsare ki Afrah,,amin gwaggo,na rasa meyasa yanzu mutane ba tsoron Allah a ransu,, ai zamanin yanzu sae addu'a, gwaggo ta fadi haka yayinda take miqowa farhan tea mai zafi sae qamshin ginger ke tashi a cikin sa. Sae da farhan ya kur6a yaji zafin dai dai sannan ya shiga lalla6a Afrah har ya samu tasha ya kuma bata magani. Nan bacci mai nauyi ya kwashe ta farhan ya shiga shafa magani a hankali kan gefen fuskar ta da ya kumbura.

A 6angaren leesa kuwa akan ta ruwa suka qare tayi yawon neman taxi har ta gaji, ga cajin wayar ta ya qare bare ta kira mom farida azo a dauke ta. Sae da ruwa suka dauke tsaf sannan ta sami abin hawa,ta tafi cike da tunanin wata mafita kala kala a cikin ranta.

Tana shiga gida ta hadu da mom farida tana saukowa kan staircase ta kalli leesa da jiqe sharkaf da ruwa duk ta galabaita kamar kazar da tasha kashin ruwa.

Farida tace"ya haka keda nake ta sauraren kiran ki na aika miki mota....bari kawai mom farida gayen ya mugun hallakani ashe kwata kwata bai san aikin sa ba wlh! ban san me yasa yazo shi kadai ba ya kuma tsaya er qaramar yarinya tana ja'inja da shi har ta bude gambu mota ta fado,wanda hakan yayi dai dai da isowar farhan, dole ya gudu buqata bata biya ba. Kuma wani abin takaici nan farhan ya barni,duk da irin kukan da na mishi ina bashi haquri abinda ban ta6a yiwa wani d'a namiji ba, amma ya tafi ya barni wai shi ba zai iya biya wa wani guri ba sbd halin da Afrah take ciki,shine ya wani bani kudin taxi bayan ba alamar taxi a gurin. Amma lallai farhan din nan shi bai lura da ba abin hawa ba ko kuma ya manta cewa idan ana ruwan sama abin hawa wuya yake....mom farida Ta ya zai fahimci hakan bayan gold dissa na cikin matsala. Gashi shi kuma dan iskan gayen can nayi kiran shi a waya yafi a qirga akan kiran sa ne ma cajin wayata ya qare bai d'aga ba, daga qarshe ma sae yayi rejecting, wanda hakan ya nuna min ya gudu da mota da kuma kudi ba tare da ya biya min buqata ta ba. Hm ai mutanen basu da kirki domin tunda naji kince shi kadai yaje nasan bai sanar da sauran ba don kawai yaci kudin shi ka dai. Hake ne man,gashi yanzu zafi uku uku kenan bana ga mota da kudi bana ga biyan buqata na kuma sha kashin ruwa a banza, ,kuma wai duk akan er qaramar yarinya hakan ta faru dani,amma na rantse... Mtsw mom bari kawai na watso ruwa na dawo na gaya miki wata mafitar!

Hm ko ce mata akayi idan Allah ya kare bawansa akwai wani mahaluqi da ya isa ya cutar da shi. Muje zuwa dai muga abinda leesa ke shirin yi wanda take tunanin Allah zai bata sa'a.

*```Futha Luv💅🏻& Billy giro😊```*

®NWA✍🏻 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:20PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 7/31/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 ~*```AFRAH KO AMRAH```* ~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*Na*

*Bilkeesu giro😊 & Bilqis Sidibe💅🏻*

🏅2⃣0⃣🏅 Yana shiga ya dorawa Afrah bindiga a goshi, ta juyo tana kallon shi a tsorace har tana qoqarin fara kuka yace"shiiii!ba abinda zan miki ni abokin uncle din ki ne yawo xamu je na siyo miki kayan wasa daga nan mu wuce gurin uncle. Da yake Afrah mugun tsoron bindiga ne da ita bata bi ta kan abinda yake fada ba ta shiga kuka tana kiran "Anty" Leesa kam tuni ta 6uya sae dae tana hango duk abinda ke faruwa. Ganin yanda Afrah ke kuka har tana qoqarin tona mai asiri yasa ya 6oye bindiga domin ya fahimci ya yi babban kuskuren nuna mata ita. Ya jawo ta jikin sa domin ya samu ya lalla6ata ya gudu da ita cikin kwanciyar hankali. Afrah kam ta riga ta tsorata da shi sae fizgar jikin ta take yayinda sautin kukan ta ke qara fitowa,ta manna masa uban cixo a hannun sa da ya rufe mata baki. Cikin zafin nama ya kai mata mari sbd jin zafin cizo. Nan tayi baya kanta ya bugi gambun mota sae kawai gambun motar ya bude ta suntu6a waje, da yake dama gambun motar a bude yake shine bai san da hakan ba. Sosai ya shiga rudu bcs Afrah na faduwa wata mota ta tsaya close to Afrah. Rudun sa ne ya qaru hango wanda ke ciki, ai ko ba shiri ya rufe gambun motar ya tafi agurguje. Farhan ne ya fito daga motar ya nufi Afrah cikin hanzari ya dauke ta sae kuka take yayinda jini ke fita a gefen bakin ta. duk ta rikice ta qanqame farhan sosai tana ci gaba da kuka. Idanun farhan sukayi jajiri sae kallon motar da wuce yake ko zai gane wanda ke cikin motar. Leesa ce tazo da gudu yayinda farhan zai saka Afrah a mota, sbd ko kadan baya son ruwan sama su ta6a ta sabida zazza6i suke sata. Bai saka Afrah a mota ba sae wani mugun kallo da ya bi leesa da shi har sae da yasa hantar cikin ta kadawa ta saki lemar da ke hannun ta. Yace"wane irin shashanci ne zaki bar min Afrah gurin wani bnza can har yana qoqarin hallaka ta! Wata irin ajiyar zuciya ta sauke a 6oye sbd ta fahimci bai gane ainihin abinda take shirin aikatawa ba.

Nan ta shiga fitar da hawayen munafurci wanda duk ruwan da ake kelawa kana hango gangarowar da suke kan kumatun ta.

Cikin murya kuka tare da qara marairaice murya tace"wlh farhan ita kadai na bari a mota sbd ruwan da naga anayi,sai na tafi ni kadài, ban ko qarasa ba na hango wani ya shiga motar yana qoqarin guduwa da Afrah shine nazo da gudu, amma wlh *Ban sanshi ba* gashi ya gudu da mota ta da kuma maqudan kudin da ke ciki. Sae dae ba damuwa ta bane tunda anyi sa'a bai je da Afrah ba,amma don Allah kayi haquri da nasan hakan zai faru da bamu zo ba. Farhan yayi shiru yana son gasgata zancen leesa har dai yanda take kuka tana ci gaba da roqon sa. Nan yaji ta bashi tausayi ya zaro kudi a aljihu ya bata yace kiyi haquri a halin da Afrah take ciki bana jin zan iya biya wa wani guri.

😂zo kuka leesa a wannan lokaci sororo tayi ta saki baki tana kallon farhan ko godiya ta kasa mishi har ya shiga mota ya tafi ya bar ta nan tsaye ruwa na faman dukan ta, ga lema tabi iska kuma gurin ba alamar zata sami taxi sbd ruwan da ake.

😂zafi biyu kenan buqata bata biya ba tasha kashin ruwa.

Farhan na isa gida ya dauki Afrah dake kuka tana rawar sanyi ya tafi da ita 6angaren gwaggo ya cire mata kayan jikinta da suka jiqe, gwaggo tace"lafiya me yake faruwa da ita naga jini a gefen bakin ta kuma sae kuka take tana rawar sanyi? Cike da damuwa farhan ya bawa gwaggo Afrah yace don Allah gwaggo a gasa mata jikin ta da ruwa masu zafi tukun.

Nan gwaggo ta shiga da ita toilet, farhan ya tafi ya canxo tufafi ya dawo yana da sintiri a bakin qofar toilet kyace wanda yakai patient asibiti yana jiran fitowar doctor. Sae da gwaggo ta d'an jima kafin take fitowa dauke da Afrah dunqule cikin towel, farhan ya amshe ta yana kallon fuskar ta da ya fahimci marin qwarai aka mata dmn yatsu sun kwanta tsaf kuma har gurin ya kumbura. Sosai yaji ta bashi tausayi yaje da ita kan bed ya zauna ya shafa mata mai ya saka mata tufafi sannan ya shiga yiwa gwaggo bayanin abinda ya faru. Gwaggo tayi taslima tace"ni har naga rashin haqurin ka da kace zaka bi bayan su hankalin ka bai kwanta ba, ashe wani mummunan abu ke shirin faruwa, oh Allah ya qara tsare ki Afrah,,amin gwaggo,na rasa meyasa yanzu mutane ba tsoron Allah a ransu,, ai zamanin yanzu sae addu'a, gwaggo ta fadi haka yayinda take miqowa farhan tea mai zafi sae qamshin ginger ke tashi a cikin sa. Sae da farhan ya kur6a yaji zafin dai dai sannan ya shiga lalla6a Afrah har ya samu tasha ya kuma bata magani. Nan bacci mai nauyi ya kwashe ta farhan ya shiga shafa mata magani a hankali kan gefen fuskar ta da ya kumbura.

A 6angaren leesa kuwa akan ta ruwa suka qare tayi yawon neman taxi har ta gaji, ga cajin wayar ta ya qare bare ta kira mom farida azo a dauke ta. Sae da ruwa suka dauke tsaf sannan ta sami abin hawa,ta tafi cike da tunanin wata mafita kala kala a cikin ranta.

Tana shiga gida ta hadu da mom farida tana saukowa kan staircase ta kalli leesa da ta jiqe sharkaf da ruwa duk ta galabaita kamar kazar da tasha kashin ruwa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull