Kenza eBookz

Afra ko amrah complete - Chapter 5

Afra ko amrah complete - Chapter 5

Afra ko amrah complete Chapter 5: Afra ko amrah complete Chapter 5. Da shigar sa makarantar sai dube dube yake ya ga sauran yaran da ba a zo daukar su ba…

4,390 words

Da shigar sa makarantar sai dube dube yake ya ga sauran yaran da ba a zo daukar su ba sae dae ba Afrah a cikin su ,qarasawa yayi guraren classes,Afrah ya hango da gudu duk hannuwanta ca6a2 suke da wani abu kamar kala har ma fuskar ta duk shine, cin karo tayi dashi yayinda ta 6ata masa fararen kaya tayi saurin dago kanta domin ganin waye,tana ganin shi ne ta rufe fuskar ta da tafin hannun ta tare da fad'in"oops sorry uncle"ta kuma qanqame shi tana mai cusa fuskar ta a jikin sa sae duk ta qara 6ata mishi kaya,a maimakon ranshi ya 6aci sae ma yayi dariya yace"Afrah meye haka a jikin ki har kika 6ata min kayan juma'a? Dariya takeyi yayinda ta dago fuskar ta kafin tace wani abu sae ga JB wanda shima dariya yake, JB yace kasan me wai fa Auntyn su ce suka je suka tarar a staffroom sae bacci take tare da birthday cake kusa da ita,wai ni take jira nazo muyi celebrate d'in birthday ko meye dalilin ta oho,shine fa suka ci mai isar su sannan sauran suka ya kuta shi,ita kanta ma basu bar taba domin duk sun 6ata mata fuska har cikin gashin kanta duk cake ne, ita kuwa wai duk bacci take bata san meke faruwa ba,hango ni da sukayi ne yasa kowa yabi tashi hanya suka gudu,, Shine kake dariya abin ka musu fad'a,,,wlh farhan abun ne da dariya domin kallo d'aya nayi wa Auntyn se na ganta kamar black monkey shine abin ya ban dariya sosai,farhan ya kalli Afrah yace"Afrah ashe har anti kike tsokana ko, turo baki tayi tace "uncle ita ce kullum idan tazo class din mu sae ta kar6e mana sweets da chewing gum d'in mu nida Amrah,wai mun fiye ciye ciye a class, kuma shi ke nan baza ta bamu ba,,jan hannun ta kawai farhan yayi sukayi sallama da JB. Da shigar su mota Afrah ta hango Aunty ta fito a hargitse sae neman su take domin tasan ba wanda zai mata aikin sae su. Afrah ta kwashe da dariya tare da nuna ta tace"uncle see d way she look like crazy bird!sosai abin ya bawa farhan dariya domin tabbas tayi kama da mahaukaciyar tsuntsuwa sae dae saurin 6oye dariyar sa yayi yaja motar, yana mai kwa6ar Afrah da kar ta sake yiwa auntyn ta haka ba kyau, amma tamkar ba da ita yake zancen ba sae kallon antyn take tana ci gaba da dariya har tana duqewa qasan seat wai duk dariya ce. can tayi shiru ta kalli farhan da ya maida hankalin sa gun driving tace"uncle zaka koya min mota"poppy luv yanzu kinyi qanqanta sae idan kin girma na koya miki,um um uncle ni yanzu nake so ka koya min, kaga ita Amrah da mashin Abbanta ke zuwa d'aukar ta kaga idan na iya mota,sae na riqa kawo kaina school har ma na riqa maida Amrah gida ba sae Abban ta yazo d'aukar ta ba,kaji uncle ka koya min bazan yi rashin ji ba ...yauwa uncle ina alqawarin da kamin yau da safe? Ai kin 6arar da alqwarin tun da dama cewa nayi sae idan baki tsokani kowa ba.....Allah uncle ba wanda na tsokana a yau indai a class d'in mu ne,other classes ne kawai sae Aunty,ta fadi haka ne yayinda ta turo baki, farhan yace "oh poppy Luv I mean gabad'aya school kar ki tsokani kowa,cikin muryar kuka tace"to uncle kai ne kace min class baka ce min school ba,ok naji ni nayi kuskure don haka daga yau kar ki sake tsokanar kowa a school kinji, ya fadi haka ne yayinda Afrah tayi saurin bude glass d'in motar sbd wata er makarantar su da ta hango kan gaban mashin da alama yayanta ne a tare da ita,yarinyar sae gyangyadin bacci take, nan Afrah ta bud'e murya sosai tace Sleeping sickness!firgigit yarinyar ta farfad'o tana ganin Afrah ba shiri ta jefo mata facing cap Afrah tayi saurin rufe glass d'in motar, ji kake qwal hular ta bugi glass,Afrah "tace kai! kai!....farhan yayi saurin riqe hannun Afrah ganin tana qoqarin sake bude glass,tace Allah uncle sae na rama... kafin farhan ya riqo d'ayan hanun ta tuni ta bude glass har ta cire school facing cap din ta, ta jefa sae a goshin yarinyar,yarinyar ta wangame baki zuwa kuka Afrah kuwa ta kece da dariya hade da yi mata gwalo. Tuni wanda ke tare da yarinyar ya harzuqa ya sauko a mashin sbd duk abin nan da ke faruwa tsaye suke bcs of traffic calming. Kan ya qaraso har farhan ya fito daga cikin mota ya samu da qyar ya lallashi mutumin. Sannan ya koma ya tada mota ya fice sbd traffic light ta basu dama. Kallon Afrah yayi wacce har yanzu bata daina yiwa yarinyar gwalo ba,yace Afrah!!da murmushi ta juyo tare da fad'in sorry uncle, girgiza kanshi kawai yayi sbd ya riga yasan idan tayi nasara gun fad'a to ko tsawar me zai mata ranta ba zai ta6a 6aci ba,shiyasa ma ya gwammaci ya mata a lalama. Yace Afrah meyasa ba kya iya zama baki tsokani kowa ba?langwa6ar da kañtà tayi tace "idan ka koya min mota zan daina uncle. Allah ya shirya min ke my Afrah ya fadi haka ne dai dai sun iso gida.

Da shigar su gida yakai Afrah 6angaren gwaggo ya tafi nashi 6angare domin ya canza tufafi.

Koda ya dawo ya samu har an ma Afrah wanka sae jiran shi take suci abinci. Suna gama cin abinci ya d'auki makullin mota,Afrah ta marairai ce tace"uncle inazuwa"no Afrah masallaci zanje ki bari idan na dawo sae muje inda nace miki kinji,"uncle please" ta fadi haka ne yayinda idanun ta suka ciko da qawalla,durqusawa yayi ya riqo hannun ta yace "to shike nan amma a mota zan bar ki kin yarda?da sauri ta gyada mishi kai domin ganin take da ya fita ba zai dawo suje yawon da yace ba.

Tafe suke kan hanya sae surutu Afrah ke mishi ita sae ya kowa mata mota har tana fad'in uncle ai na ma ga yanda kake yi zan koya da kaina,,farhan jin ta kawai yake har suka zo masallaci.

Bai riga ya parker mota ba sae ya hango wani abokin sa da suka jima basu had'u ba yayi saurin fita ba tare da ya kashe motar ba bare zancen cire key. Yana wuce wa Afrah ta koma seat din driver da murnar ta inda ta shiga ta6e 2,tana kwatan ta duk yanda taga farhan nayi, ta dora qafafuwan ta inda taga yana dora nashi tare da danna gun da qarfi,wanda hakan yasa motar ta tafi ba shiri, Yayinda farhan ya gama gaisawa da abokin sa,abokin ya fice shi kuma ya juyo,ai kuwa ya tafi da sauri har yana had'awa da gudu,yayi nasàrar riqo gambu,yakai hannu cikin sauri ya kashe motar,a tsoràce Afrah ta fad'a kan jikin sa cikin kuka dafe da goshi da alama buguwa tayi a gurin,cike da damuwa farhan ya jaye hannun ta yaga gurin har yayi lolo yayi ja,nan ya shiga murza mata, sautin kukanta ne ya qaru ta rirriqe hannun shi tare da cusa fuskar ta a qirjin sa, jikin ta sea rawa yake sbd ta tsorata sosai da jin yadda motar ta tafi da qarfi, bubbuga bayan ta ya shiga yi a hankali, ya kalli mutane sae sauri suke zasu shiga masallaci. Nan ya shiga dube dube yana tunanin yanda zaiyi da Afrah gashi ana qoqarin tada sallah. Kamar daga sama yaji "ance idan ba damuwa ko zaka bani ita na riqa ma, Farhan ya kalli inda maganar ke fitowa wata er matashiya ya gani ba laifi akwai kyau sae dae ba shape, kafin yace komai tace"ganin nayi kana ta faman dube dube ni kuma zan wuce kan hanya naga ya kamata na tsaya na taimaka maka,farhan bai kawo komai a rañsà ba yace "haka ne gasky na gode fa" ya fadi haka ne yayin da ya miqa mata Afrah,wani lallausan murmushi ta mishi tace" ai ba godiya a tsakanin mu sbd tamkar qanwa ta ce, nan farhan yayi murmushi ya dan kai bakin sa saetin kunnen Afrah wacce bata ko dago ta kalli wacce ta kar6e ta ba yace"my poppy Luv zan tafi na dawo kinji" ya shafi bayan ta tare da yi mata peck a gefen fuska, wanda duk abin nan da yake yarinyar sae kallon shi take da alama komai na farhan birge ta yake, domin bata daina kallon shi ba har ya shiga masallaci,sannan ta iya daga qafafunta taje cikin motar ta ta zauna yayinda Afrah ke maqale a qirjin ta, a hankali takai hannu ta shafo dai dai inda taga farhan ya shafa a jikin Afrah ta kuma dora lips dinta a dai dai inda farhan ya ma Afrah kiss,bata dago ba sae da tayi nata kiss, tace "Luv u guy"

*Futha Luv 💅🏻& Billy giro😊* ®NWA✍🏻 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:20PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [7/25/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *~AFRAH KO AMRAH ~* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*Na* *Bilkeesu giro😊 & Bilqis Sidibe💅🏻*

🏅1⃣7⃣🏅 Cike da murna ta d'auko wayar ta tayi dialling number yayinda mom farida ya bayyana a screen. Ringing daya biyu aka d'aga tace"mama yau akwai labari mai d'adi sae dae naxo zaki ji. Ta kashe wayar tana saqe saqe a cikin ranta har aka fito daga masallaci. Farhan ne yazo ya same ta tayi nisa gun tunani sallamar da yayi ne tayi far da ido,ba tare da ta amsa sallama ba tayi murmushi tare da fadin har kun fito,gyada mata kai farhan yayi yana mai kallon afrah sbd koda ya shiga masallaci cike ya ke da damuwar ganin yanda goshin ta yayi lolo yayi ja,har ma ya qagu ya fito. Yace tayi bacci ne? Bazan iya ce maka eh ko a'a ba sbd tun lokacinda na kar6e ta bata d'ago kanta ba har yanzu, Eyyah my poppy Luv inaga gurin yana matà zafi sosai,nan ya kai hannu ya kar6e ta, ya dago fuskar ta yana mai kallon gurin cike da damuwa yace"oh poppy luv meyasa kaudin ki yakai har kika jiwa kan ki ciwo haka,that's y bana son rashin jin da kike wlh just bcs of irin wannan ranar, yarinyar dai sae kallon farhan take wacce ta fahimci har cikin rai yake jin zafin jimuwar da Afrah tayi,ta d'an kauda kanta kad'an tana mai jin haushin yanda yake kula Afrah ita ya bar ta a tsaye...."wash uncle zafi ka daina murza min"maganar ta fito a bakin Afrah yayinda tayi ta cike da alamar zata yi kuka. Yarinyar ta juyo a hankali ta kalli Afrah wacce taji sautin muryar ta mai taushi da dad'in saurare like flute, domin tun da take bata ta6a jin murya mai dad'in sauraro irin wannan ba,duk da tasan qaramar yarinya ce amma ta jinjina ma zaqin muryar ta, Farhan kuwa kukan da yaga Afrah na qoqarin yi ne yasa ya daina murza gun,sae iskan bakin sa da yake d'an hura mata a hankali, yayinda Afrah ta wani lafe a qirjin sa,sae yarinyar ta gansu perfect match kamar su tabbata a hakan,amma tafi son ya kasance ita ce a qirjin farhan ba Afrah ba.... Farhan ne ya katse ta da banzan tunanin da take,yace"am sorry pls nagode fa"sauke ajiyar zuciya tayi mai nauyi had'e da gyad'a kanta,ta shiga mota shima ya nufi tashi mota ya shiga,tare da bud'e drawer mota ya bude er qaramar first aid kit dake ciki,ya dauko magani wanda da qyar ya samu Afrah tasha sannan suka bar gurin.

Sannan ita ma ta iya tuqa motar ta ta wuce,

Tana isa gida jiki sa6ule ta zauna kan kujera, matar da ta fito ce ta bamu mamaki sosai domin kuwa Farida ce matar marigayi Alhj Sadiq wato Baban Afrah. Zama tayi tare da fad'in leesa lafiya kin shigo jiki mace bayan kin kira ni da murna har ma kina ce min akwai labari mai dad'i,hmm mom farida na tsorata da ganin yanda yake bawa qaramar yarinya kulawa, ba ma shi ba mom ko suna na fa bai tambaya ba,,, mtsw wannan ne kawai na ma zaci wulaqan taki yayi,inace dai kin samo number sa..mtsw mom gayen fa bai ko sake min fuska ta yanda zan sami damar tambayar sa wani abu ba,domin kwata kwata hankalin sa na kan wannan qaramar yarinyar, wai kan d'an wani qaramin jin ciwo da tayi duk yabi yasa kansa a damuwa...hmm ai indai farhan ne kadan kika gani, yanzu abinda nake so da ke shine gobe zan miki kwatàncen gidan sae kije a matsayin kinje dubata, to na tabbatar in yaji kan Afrah kika je zai fara sake miki fuska har ma ki sami damar samun number sa,ni kuma a cikin kwanakin nan zanje qauye domin na kar6o mana maganin da nace miki za'a turara ma wani abun da zai ci,sae dae maganin yana da sharad'i domin a ranar da aka turara shi a ranar ake so aci wannan abun,idan ba a ci a ranar ba ba kuwa zai yi aiki ba, amma idan yaci to ina mai gaya miki zai ji a duk duniya ba wacce yake so kamar ki domin ko Afrah da kike gani ba zai qara kallon ta ba sae da izinin ki.... Au haba mom!Allah kuwa domin ko bacci ba zai iya yi ba har sae yazo ya ganki, nan leesa ta ba farida hannu suka tafa cike da murna suna shewa.

A 6angaren farhan kuwa duk yabi yasa kansa a damuwa sbd tunda suka koma gida Afrah take kwance har zuwa marece tama daina zancen zuwa yawon da ta qwallafa a ranta sbd jikin ta duk yayi zafi.

Farhan ne zaune a bedside yana kallon Afrah cike da damuwa... Gwaggo tace"ni kuwa meyasa baza kayi mata allura ba, d'an guntun murmushi farhan yayi ya d'an kauda kansa gefe yace"wlh gwoggo kukan ta ne bana son ji,ko fa bata magani ya na qarasa bare allura,gwaggo dai kasa cewa komai tayi ta rasa mene ne farhan keji idan Afrah na kuka wanda tun tana jaririya har yanzun bai daina ji ba.

Da dare farhan na kwance yana bacci Afrah ta shigo dakin riqe da er teddy, tana sanye da rigar bacci peach in colour iya guiwa,ta hau kan gadon taje nesa da farhan tana wasa da teddy. Cikin baccin sa yake ji a jikin sa kamar Afrah na kusa dashi hakan yasa ya bud'e idon shi a hankali yaga ashe da gaske tana kusa da shi, ya tashi da hanzarin sa tare da jawo ta kusa dashi yace"my poppy Luv kinji sauqi?eh uncle,gwaggo ta baki magani kinsha?eh,ina ce bakiyi kuka ba ko?shiru ta mishi, wanda shima yasan tambaya kawai yayi amma kuka kam ba fashi,yayi murmushi tare da shafo gashin kanta yace "to me yasa har yanzu baki koma bacci ba?shiru ta mishi domin ita kanta bata san dalilin da yasa ta kasa komawa bacci ba bayan tana jin sa sosai. Haka shima farhan yayi shiru yana tuna cewa Afrah bata iya bacci fa sae kan jikin sa,nan yace "sorry my Afrah ban san zaki farka ba da na jira ki har ki sake komawa bacci,kuma nima baccin yazo min ne ba shiri,, hmm farhan kenan sae magana yake da Afrah kamar wata babba, nan ya jawota jikin sa,yana shafa jikin ta a hankali yayinda yake ta kallon fuskar ta harde zara zaran eyelashes din ta da ya qure da kallo kamar mai wani tunani,cikin minti biyar tayi bacci abin ta,sae da ya tabbatar baccin ta yayi nisa sannan ya maida ta gurin gwaggo.

Da safe guraren qarfe 11 farhan ne da Afrah cikin qananan kaya riga da wando three quarter kala d'aya,riga black wando fari, sai sukayi kyau sosai sbd kayan sunyi dai dai da jikin su,ga qamshi mai dad'i da ke fita a jikin su,yayinda suke zaune kan resting chair farhan na karatun jarida Afrah na jingine a jikin sa tana riqe da poppy flower guda biyu sannan ta soka d'aya a gefen gashin ta sae tayi kyau kamar ba indiya har dai yanda gashin kanta yasha gyara aka zubo shi a baya.

Fresh air ke bugo musu cike da natsuwa gurin yayi tsit ba mai magana a cikin su sae kukan tsuntsaye da ke tashi kasancewar cikin garden suke,Afrah sae kallon tsuntsayen take yanda suke shawagi a cikin d'an kejin su,ko kad'an bata yarda tayi wani dogon motsi ba sbd duk rashin jinta idan ta fahimci farhan na buqatar natsuwa to kuwa shiru take yi da bakin ta. Suna cikin haka ne suka ji sallama farhan ya fara dago idon sa ya sauke su kan leesa ya amsa sallama yana mai son ya tuna inda yasan fuskar,leesa ta fahimci haka yayinda take qoqarin zama kan dayar kujerar da ke dubin su had'e da sakin murmushi tace"suna na "Khaleesat amma anfi kirana da leesa nice wacce muka had'u jiya har na kar6i Afrah ka shiga masallaci, farhan ya sake mata murmushi na alamar ya gane ta, tace "dama tun jiya na biyo bayan ku da niyar na ga gida domin na samu nazo naga ya Afrah taji da jiki, abin na raina tun jiya har ma naso ace nazo kafin yau. Sosai farhan yaji dad'i domin shi dai ba abin da yafi masa dad'i irin ka nuna damuwar ka akan Afrah. Yace " naji dadi na kuma gode sosai da kulawar ki..ah ah ba komai ai yiwa kaine,ta fad'i haka ne tare da fad'in Afrah zo muga gurin"Afrah ta kalli farhan, yace jeki kinji,nan ta tashi ta nufi gurin leesa, leesa kuwa sae magana take a ranta" _yarinya zaki gane kuren ki ne,domin kin kusa zama shara a gun farhan sae yanda nayi dashi_ Ta tsaida zancen yayinda Afrah ta qaraso,ta jawo Afrah jikinta tare da shafo kan ta,ta kalli goshin Afrah tana mai nuna damuwa a fuskar ta, tace "Allah sarki Afrah sannu kinji,Afrah ta gyada kanta tana mai kallon leesa,kafin leesa ke tambayar farhan abinda yaji wa Afrah ciwo, nan farhan ya sanar da ita, tace "Allah ya tsare gaba"sannan ta furta a ranta " _ina ma ace kin mutu a cikin motar_" Kamar Afrah taji me tace ta jaye kan jikin ta ta koma gurin farhan, Yayinda leesa ke ci gaba da magana tana mai kallon Afrah da taje kan jikin farhan ta lafe _kin kusan yin na qarshe yarinya domin kwanaki kad'an ya rage ki daina zuwa ko kusa da shi bare zancen kwanciya a jikin sa_ Nan ta daina zancen ta koma jan farhan da fira,har ta samu ta kar6i number shi.

Sae da ta d'an jima kafin take barin gidan tare da bawa Afrah sweets,chocolates & Biscuits cike da wata er matsakaiciyar leda.

Haka ma washe gari sae da taje gidan inda ta qara zuwar ma Afrah da kayan maqulashe ciki har da ice cream. Gidan ta yini a 6angaren gwaggo wanda hakan yasa Afrah ta sake da ita sbd Afràh yarinya ce mai saurin sabo.

Bayan ta koma gida ne farida ta tarbe ta da Albishir d'in cewa ta kar6o magani yanzu aiki ya rage nata, leesa ta kar6i maganin cike da murna tace"in Allah ya yarda gobe muna zaune zaki ga dan aike farhan yazo nema na,domin gobe Leda biyu zanyi ta chocolates naje har makarantar su Afrah na bata.....ha a! wannan shirmen fa leesa?mom farida ba shirme a ciki zuwan nan da nayi na kwana biyu a gidan su na fahim ci bata fara cin wani abu sae farhan yaci....to ai ba su biyu ake so suci ba shi kadai ake so yaci,eh ai shiyasa nace leda biyu zanyi dayar ita ce wacce zan turara ma magani wato ta farhan,dayar wacce bata da komai ita ce ta Afrah,idan naje school d'in su ni nasan yanda zanyi mata bayanin cewa ga nata ga ta farhan..... Hmmm amma dai akwai ki da shirme... Ba wani shirme mom, yarinyar tana da ganewa sosai domin zuwan da nayi na samu farhan yana koya mata karatun islamiya sae kinji yanda qira'a ke fita a bakin ta, kuma duk tambayar da yayi mata kai tsaye take bashi amsa.... Naji tana da ganewa amma meyasa baza ki bashi da kanki ba? Mom baki ga yanda ya dauki abin da ya fito hannun ta da muhimmaci ba, shiyasa nake so ta bashi domin na tabbatar idan ta bashi zai ci. To shike nan ke kuma ki tabbatar kin turara maganin da kyau. To mom farida.

Washe gari kasancewar ranar Monday ce Afrah na school yayinda suke ta guje guje ita da Amrah kasancewar lokacin break fast ne. Leesa da ke tsaye sae kallon su take,ta dan ya mutsa fuskar ta kadan tare da fadin abin tausayi Afrah daga yau ba kya da wani sauran nishad'in da zaki ci gaba da wasa da qawaye sae dai wasu suyi ba ke ba. Nan ta qarasa gurin su tare da bayyana murmushi a fuskar ta,Afrah ce ta fara hango ta tazo da gudu ta tarbe ta,tace "Aunty ina uncle"Afrah ai ke zan tambaya uncle,ko tunanin kike tare muka zo?a'a yace idan ban tsokani kowa ba zai zo ya kawo min ice cream, kuma yau ban tsokani kowa ba nida Amrah kawai ke wasan mu,,uhm to ki ajiye zancen ice cream ga chocolate & Biscuit na kawo miki, ta fadi haka ne yayin da ta fitar da Leda biyu, tace wannan ledar wato white colour itace ta uncle, pink colour ce taki,kar kici yanzu ki bari sae kinje gida, idan kika bawa uncle nashi sae kici naki,amma ki tabbatar kunci a yau domin zai iya lalacewa idan ya kwana....Aunty yaushe biscuit ya fara lalace wa a kwana da'ya, nifa wanda uncle ke saya min yana kwanaki bai yi komai,, _kaih! yarinyar nan akwai baqin wayon tsiya_ta fadi haka ne a ranta kafin take fitar da biscuit wanda da gani zai yi dad'i da tsada ta nunawa Afrah tace"uncle d'inki ya ta6a saya miki irin wannan? Turo baki tayi tace"wanda uncle ke saya min yafi wannan girma da kyau.

Duk da leesa taji haushi hakan ta dake tace"nima zan riqa saya miki irin wanda uncle ke saya miki, amma kici wannan a yau kinji, haka shima uncle,ok Anti zamu ci a yau,yauwa Afrah to je ki adana su a cikin jakar ki but wanne ne na uncle? White one na uncle pink one nawa... That's gud my dear je ki dawo sae na baki wani keda qawar ki. Da gudu Afrah taje har tana had'awa da tsalle. Ba jimawa ta dawo, leesa ta dauko sweet ta ba Afrah sannan ta ba Amrah, Afrah tace"anti Amrah bata shan sweet,chewing gum take ci, ok ina da chewing gum bari na bata,bayan ta bata ne ta wuce tana mai yi musu bye bye sae fatan nasara take a cikin ranta.

Da dare farhan ya fito daga wanka ya sami Afrah sae game take da game tab,tana jin ya fito ta watsa mishi idanun ta masu shegen haske da kyau, tace"uncle har yanzu ba muci biscuit d'in da Aunty ta ba mu ba"tayi maganar ne a shagwa6e bcs tana gudun kar yace dare yayi baza su ci ba, ba musu yace ok je ki d'auko mana kafin na gama shiri sae muci. Da murnar ta taje ta d'auko ta kawo, ta bashi white leda ta d'auki pink. Sae da ya gama shirin sa sannan yayi lokacin bud'e ledar ya dauko biscuit ya bude yayin da ya tsure biscuit d'in da ido yana mai jin baya son saka komai a bakin sa sbd yayi brush amma haka ya zaro d'aya ya saka a bakin shi.

*Billy giro😊 & Futha Luv💅🏻*

🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:20PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [7/26/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *~AFRAH KO AMRAH ~* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*Na* *Bilqis Sidibe💅🏻 & Bilkeesu giro😊*

🏅1⃣8⃣🏅 Amma hakañ ya zaro d'aya ya saka a bakin shi had'e da yin "bismillah" Bai wani ci da yawa ba ya ajiye sbd baya son zaqi sosai. Haka ita ma Afrah ta ajiye nata sbd bacci take ji. Har tana qoqarin kwanciya farhan yace "tashi muje muyi brush. Koda suka dawo suka sami wayar farhan sae ruri take, farhan ya dauki waya yaga leesa na yawo kan screen, yace "Afrah zo ga Antin ki" Sae da yayi receiving ya bata,bayan sun gama gaisawa ne,leesa tayi shiru tana tunanin ta yanda zata gane cewa sunci biscuit,can tace"Afrah inace biscuit d'in da na baki akwai dad'i sosai ko?eh shine ma muka gama ci yanzu nida uncle se mukayi brush zamu kwanta, shi kad'ai yaci nashi ko har da ke? Shi kadai yaci nashi nima naci nawa, yauwa inace baki masa canjen leda ba, fara kika bashi ko?eh Anti, that's gud!haka nake son ji,bye my dear,,, ok bye Aunty. Ta juya ta kalli farhan da yayi kwance kan bed idanun sa a lumshe da alama bacci yake ji sosai. Jin ta gama waya yasa ya bud'e idon shi tare da sakar mata murmushi yace "zo kiyi bacci na maida ke gurin gwaggo kafin nayi bacci" Nan ta hau kan bed ta shige jikin sa,sae ta dawo er fincika a cikin faffad'an qirjin sa, da yake dama bata da girman jiki sililiya ce.

A 6angaren leesa cike da murna ta daka tsalle,taje da gudu ta fad'a wanka,ta fito tayi zaune ba tare da tayi kwalliya ba acewar ta sae yazo sannan zatayi kwalliya ta nemi tufafin sawa sbd taja nata aji.

Farhan kam tuni bacci ya kwashe su shida Afrah.

Tun abin qarfe goma leesa ke sauraren zuwan farhan har 11:30 ba alamar farhan sae duk hankalin ta ya fara tashi wai ko da gaske yaci biscuit d'in. Tana cikin haka ne sae ga farida ta shigo tace "ya naji shiru ko har yazo ya tafi?bai zo ba tukuna amma nayi waya da Afrah tace min sunci" yauwa dama wasu turarukka nake son baki ki shafa kafin kije,to shike nan zanzo na kar6a.

Gwaggo ta gama sallah tana lazimi ta kalli agogon bango har sha biyu tayi farhan bai kawo Afrah ba, tashi tayi taje 6angaren shi,ta samu sae bacci suke shida Afrah ta wani qara shigewa jikin sa kamar wacce ke shan mamma, girgiza kan ta tayi tace"Afrah akwai aiki in kin girma domin bansan ya zakiyi da wannan sabo da farhan ya miki ba. Nan taje sannu ta jaye Afrah kan jikin farhan ta d'ora ta a kafad'a,, da sauri ya bud'e idon shi yace"gwaggo keda kanki bari na kai miki ita, a'a yi zaman ka kawai dama so nake ka rufe 6angaren ka kar ya kwana a sake. Nan farhan yabi bayan ta ya rufe 6angaren shi yaje ya kwanta kafin yake addu'ar shiga bacci.

Leesa kuwa rabon ido take har safe ba farhan ba alamar sa😂.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull