Kenza eBookz

Afra ko amrah complete - Chapter 4

Afra ko amrah complete - Chapter 4

Afra ko amrah complete Chapter 4: Afra ko amrah complete Chapter 4. Da gudu farhan suka qaraso shida police, Sosai farhan ya shiga rudu ganin Alhj Sadiq…

4,259 words

Da gudu farhan suka qaraso shida police, Sosai farhan ya shiga rudu ganin Alhj Sadiq wanda a nan take idanuwan sa suka rikid'e zuwa ja,d'agowar da zaiyi ne ya hango wanda yayi harbin nan farhan yace da en sanda shoot him!ba wasa kuwa d'ayan d'an sanda ya kai maisa harbi wanda ba don duqewar da yayi ba da a qafa za'a same shi sae aka same shi a wuya ai kuwa nan take ya fad'i qasa matacce yayinda suka ji kururuwa mai qarfin gaske had'e da fad'in father!!sae duk en fashin suka fito a ma6oyar su, suka yo kan ogan su da aka harbe,cikin zafin nama d'ayan su ya aiko harbi wanda yayi dai dai da fitowar mahaifiyar Amrah sbd ihun Amrah da taji,nan harbin ya sauka akan qafar ta wanda hakan yasa en sanda suka tafi da gudun su, kan su qarasa har en fashin sun d'auke gawar ogan su suka saka a mota suka bar gurin a tsiyace ba tare da sun bi takan Amrah da ta fito a cikin motar ba, Amrah kam taje da gudu ta fad'a kan mamar ta tana kuka mai tsima zuciya.

Farhan kuwa hankalin sa ne ya rabu gida gida duk ya rikice ga Alhj Sadiq kwance cikin jini ga Afrah a some ga kuma mahaifiyar Afrah da aka harba.

Farhan na qoqarin tashi Alhj Sadiq ya riqo hannun shi yana numfashi a wahale ya riqo hannun Afrah ya had'a da na farhan yana mai cewa "Farhan ga qanwar ka na baka amana bana so ta rayu tare da kowa face kai,domin kai kad'ai ne wanda nafi yarda da shi a duk duniya, yana kawo nan kawai ya shiga yin Kalmar shahada sae kawai hannun sa ya saki komai nasa ya daina motsi. Nan farhan ya shiga jijjiga shi yana kiran Abba! Abba!!Abba!!!ina rai ya riga yayi halin sa,nan farhan ya shiga yin kuka kamar mace.

Da safe Farhan ya ajiye Amrah a asibiti wanda kallo d'aya zakayi mishi kasan yayi kuka bana wasa ba. Kudi ya zaro ya miqa wa Amrah da har yanzu kuka take yace"Amrah kiyi haquri takai ci na d'aya rashin nasarar cafko su da ba'ayi ba Amma in Allah ya yarda mama zata ji sauqi, tun da kinga yanzu za'a shiga theater da ita wanda naso ace da ni ciki amma bazan samu shiga ba sbd jana'izar da zanje. Gyada kanta tayi tare da yi mishi godiya sannan ya fice.

Sae da ya jima kafin yake dawowa jiki sa6ule ya qarasa gurin Amrah da ya hanga sae faman rusar kuka ta ke farhan yace"Amrah lafiya ina mama?cikin kuka tace uncle wai mijin mama yazo ya tafi da ita ba tare da an mata aiki ba, dama mama tana da miji ne?gyada masa kai tayi kafin yake cewa to meyasa bai je da ke ba?sbd ni ba er sa ba ce?farhan yayi shiru kamar mai son cewa wani abu sae kuma ya fasa, Sae tunani yake yanda abubuwa suka cakud'e masa lokaci d'aya ga mutuwar Alhj Sadiq ga shi an nemi en uwan Alhj Sadiq an rasa sun gudu gabakid'aya har matar shi da kuma dukiyar sa kaf,ba kuma wannan kad'ai ba yanzu kwata kwata Afrah bata ji tun lokacin da ta farfad'o daga doguwar sumar da tayi,kukan da Amrah ke ci gaba da yi ne ya dawo dashi daga dogon tunanin da yake yace"ki daina kuka nasan idan hankalin mama ya dawo zata dawo ta d'auke ki,yi shiru ki daina kuka kinji,nan yaci gaba da rarrashin ta wanda da qyar farhan ya samu Amrah ta daina kuka tabi shi gidan su.

Bayan sati daya da faruwar hakan Amrah kam sae bud'ar ido take mamar ta tazo amma shiru wanda hakan ne yasa ta qara shiga damuwa kullum cikin kuka bata cin abinci.

Ko yanzu kwance take cikin d'akin da aka bata masauki sae faman rusar kuka take.

Farhan ya shiga da sallama ta amsa yayinda take share hawaye ya samu guri ya zauna tare da Afrah dake maqale a kafad'ar shi. Yace"Amrah a gaban idon ki ne mijin mama yazo ya d'auke ta? Aa na d'an d'aga dana dawo ne likitawa ke sanar dani kan cewa ba yanda basuyi ba kan ya haqura har a mata aiki yace a'a, olryt inace kinsan garin da mijin mama yake ko? Eh na sani,that's gud ki shirya zanje na kai Afrah asibiti idan na dawo sai mu je. Nan ya fita daga dakin yayinda gwaggwo ke qoqarin shiga dauke da abinci.

Koda farhan ya dawo ya samu har ta shirya shi kadai take jira.

Sae dae zuwan su garin bai anfana musu komai ba sae baqin ciki,sabida labarin da suka ji kan cewa tuni mijin mama yabar garin yau kusan shekara d'aya kuma ko garin da ya koma baya can sbd kasuwanci yake baya tsayi guri d'aya.

Amrah kuka take tun kan hanya har suka zo gida sbd bata da wasu en uwa da zata je gurin su mahaifiyar ta kad'ai ce kuma yanzu ta rasa ta.

Farhan kuwa sae lallashin ta yake haka ita ma goggwo ta kama mishi.

Amma Amrah tamkar rarrashi qara mata kukan yake wanda har akayi kusan sati uku Amrah bata daina aikin kuka ba, ba dare ba rana kuma duk yadda akayi da ita bata cin abinci,wanda rashin cin abinci ne ta shiga ganin bishi bishi har tazo bata gani,koda akaje asibiti suka ce tabbas yunwa ce ta mata illa domin dama can tana tare da yunwa. Ba yanda farhan bai yi ba na ganin ta warke amma abu ya faskara kamar yadda ita ma Afrah abu ya faskara sae magani da suke ta faman sha kullum.

Kwanaki sun ja yayinda lokaci yake qara tafiya zaman da Amrah take a gidan su farhan ya kawo so da shaquwa tsakanin farhan da Amrah. Sae dai wani abu da kowa bai sani ba shine Kusan kullum sae Habib ya turowa farhan text na barazana akan sae ya d'auke Amrah da kuma daukar fansa kan ogan su da aka harbe. Farhan sae dai yayi tsaki,yayinda yake cike da son ya gano ma6oyar su ko hukuma zata yi nasarar cafke su.

Sanin cewa da gaske zasu iya sace Amrah domin har tare ta sun ta6a yi wani lokaci da ta je kasuwa wanda jin haka ne yasa farhan ya nemi a gaggauta d'aura musu aure ba tare da ta kammala secondary school ba.

Haka ko akayi domin cikin sati d'aya farhan ya angonce da matar sa Amrah.

Wannan kenan.

A nan muka kawo qarshen labarin.

sae ku biyo mu domin jin yanda farhan zai qarasa da su Habib.

*Billy giro😊 & Futha Luv💅🏻*

🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:20PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [7/19/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 ~*AFRAH KO AMRAH* ~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*Na* *Bilkeesu giro😊 &Bilqis Sidibe💅🏻*

🏅1⃣3⃣🏅 Farhan ya dawo daga dogon nazarin da yake ya kalli Habib yace"kayi haquri Habib a bisa rashin sani ne yasa na ce a harbe shi domin duk a tunani na shine ya harbi Abba...Farhan kenan tun farko da baka kira motar police ba da duk hakan bai faru ba. Kasani nasan cewa nine ka daukowa motar police sbd na dauke Amrah. Tun lokacin da ka fito gida kaje gidan su Amrah ku ka fice police station duk ina sane. Sa'a kawai kuka ci kai da motar police d'in, domin ba don Alhj Sadiq ya tare ku kan hanya ba,da kuna kawo wa saitin ma6oyar mu baza ku kai labari ba har abada,domin tarkon da muka had'a muku ba wanda zai rayu a cikin Ku. Kuma shisshigin da kayi na raba Amrah da J hakan zai sa bazan ta6a lamunta maka ba. Sbd tun lokacin da ka aure amrah ka lalata min rayuwar qane na, ya zamo ba yada wani amfani sae kwanciya, kwanciyar da bazai iya tada kan shi ba sae an tayar. Wanda ba don jinyar sa da nake ba da tuni na manta cewa na dauki fansa a kan ka. Ka had'a min zafi biyu a lokaci d'aya ka kashe mana oga kuma Amrah ta koma hannun ka, kasani J ya fika son Amrah fiye da yanda kake tunani!domin J bai ta6a son wata 'ya mace da har yaji yana son aurenta kamar Amrah ba. Domin ko dauke ta da mukayi ba muna nufin cutar da ita ba sae don a d'aura mata aure da J,sbd na fahimci da gaske yake sonta shiyasa na jajir ce na ganin ya mallake ta.

Amma sae kazo ka lalata mana lissafi.

Qyar farhan ke kallon Habib da yayi shiru alamar ya kawo qarshen zancen sa. Yace "naji J da aure yake son Amrah amma haka kawai kai tsaye ake d'aura aure ba yardar yarinya ba izinin iyayenta. Sannan kasan irin halin da Amrah zata shiga ita da mahaifiyar ta na aura mata yaron da baya da halin kirki kuma baya da niyar gyara hali,wanda idan ya aure ta lalata mata rayuwa kawai zai yi,domin Amrah yarinya ce wacce duk namijin kirki zai so ta kasance matar shi.

Habib koda ace ban auri Amrah ba,ba shi zai sa ka samu damar auradda ita ga J ba,domin indai ina raye bazan ta6a bari J ya auri Amrah ba.

Wani fari da ido Habib yayi yana mai ganin tirzawa irin ta farhan yace"lallai farhan wuyan ka yayi qwari kai da kake neman na haqura shine har ka sami damar gayan min wannan zancen.

Kauda kansa kawai farhan yayi yana mai cike da jin haushin Habib wanda har jin yake da yana jin qarfi a jikin sa da sae dae ya fafata da shi ba zancen bashi haquri,sae dae kash sun riga sun kashe masa qarfin jiki da sinadarin powder da suka shaqa masa. Hakan zai sa ya haqura yaci gaba da bashi haquri duk da cewa bada haquri ga azzalumin mutum baya daga cikin tsarin sa. Amma zai yi hakan ko don kare lafiyar Afrah da Amrah.

Maida duban sa yayi gun Habib da yaje kan sofa ya zauna tare da d'ora qafa kan qafa ya kunna sigari. Wanda sae da ya zuqi sigari ya busar sannan yace "farhan lallai yau zan nuna maka ni ba mai imani bane. Idan tantama kake to yau zaka fahimci hakan da gaske. Sbd ka ta6o ni inda ba a ta6o ni.

Farhan ya nisa ya lumshe idon sa cike da damuwa yace"na roqe ka Habib kar ka ta6a min lafiyar *Afrah ko Amrah*ko ma me zakayi ka aiwatar da shi akaina.

Cike da murmushin mugunta Habib ya sauke qafar sa da ya d'ora kan d'aya, yace "na yafe maka laifi d'aya amma bazan yafe maka d'aya ba. Gama fadar hakan keda wuya ya saita bindigar sa yayinda wutar gidan ta d'auke d'if wanda yayi dai dai da tashin qarar bindiga. Afrah da ke jikin farhan ta buga wani irin razanannen ihu.

Yayinda dariyar Habib ke fitowa.

A firgice farhan ke lalubar Afrah da yaji ta saki gabad'aya bata motsi,sae wani d'umi da yake jin yana sauka kan jikin sa.

*Futha Luv💅🏻&Billy giro😊* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:20PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 7/20/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 ~*AFRAH KO AMRAH* ~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*Na* *Bilqis Sidibe💅🏻 & Bilkeesu giro😊*

🏅1⃣4⃣🏅 Ga kuma wani nishi da yake jin yana fitowa ta bayan sa. Wanda hakan ya qara rikitar da shi,yayi yunqurin tashi domin neman fitila. Bai riga ya tashi ba haske ya bayyana a d'akin,ya kai duban sa cikin sauri gun Afrah da ke kan jikin sa, wacce ya shiga dube dube a jikinta ba alamar harbi, somewa ne kawai tayi domin tsorata da jin qarar bindiga har ta masa fitsari a jiki. Ajiyar xuciya ya sauke mai nauyin gaske, sannan ya d'ago idon shi domin kaiwa Habib duba sae yaga wayam ba kowa a d'akin duk sun fita,har Amrah ma bai ganta ba. A rikice ya tashi yakai Afrah kan sofa ya kwantar, juyowar da zai yi ne ya hango Amrah kwance dafe da gefen cikin ta. Kan bed ya hau tare da tallabo ta jikin sa, yakai hannu ya yaye mata sumar da ke kan fuskar ta tare da 6alle abin da suka rufe mata baki da shi, a hankali ta shiga bude idanun ta yayinda bakin ta ya fara motsi kadan kadan, wanda da qyar ta iya furta "un..cle" hade da fitowar hawaye zar a idonta. Cike da damuwa farhan yace"my Amrah"... sae kuma ya kasa cewa komai sbd hannun sa da yaji ta d'ora kan inda suka harbe ta,idanun sa ne suka ciko tap da hawaye yayin da ya tsure gurin da kallo sae jini ke fita a gun,bakin sa na rawa haka ma duk jikin sa ya d'auki rawa yace"my Amrah bari nazo muje asibiti kinji"riqo hannun sa tayi ta girgiza mishi kai tace"no uncle,ni fuskar ka kawai nake son gani" a hanzarce ya tashi ya nemo eyeglass d'in ta a tsakiyar d'aki ya saka mata, Kallon fuskar shi take ba ko qyaftawa,kamar yadda shima farhan ke kallon ta, a hankali ta d'ago hannun ta da ke dauke da jini sha6e sha6e,ta shafi gefen fuskar shi yayinda idanun ta suka fara lumshewa hawaye kuwa sae rigangan fitowa suke"forgive me uncle"shine abinda ya fito daga bakin ta. Saurin jijjiga ta yayi yace"no Amrah don Allah kar ki rufe idon ki, ki bari muje asibiti kinji"....ka yafe min uncle ni bazan rayu ba...waya gaya miki my Amrah zaki rayu har ma ki haifo min 'ya'ya...mutuwa zanyi uncle,kuma inaji a jiki na ummana zata zo nema na idan tazo kace ta yafe min,hawaye ne suka zubo sha6e sha6e a kumàtun sa, ta share masa hawayen tace"ba kuka nake so ba uncle,ni addu'a nake so ka min"ta fadi haka ne yayinda take kallon wani gefe dauke da murmushi a fuskar ta. Ashe Afrah ce ke qarasowa gurin su,tazo sae rarraba ido take tana kallon farhan da ke kuka, sae kawai d'an qaramin bakin ta ya bud'e a hankali tace"uncle meyasa kake kuka anti bata da lafiya ne? Da mamaki farhan ya kalli Afrah yace"Afrah magana kike yi please kice da Aunty kar ta tafi ta bar mu kinji. Afrah ta kalli Amrah da ke kwance, sae dae bata ce da ita komai ba face Amrah da ta riqo hannun ta ta had'a da na Farhan tace"uncle ina son rayuwar ka da Afrah,n i Luv u uncle I luv u so much!" daga haka bata sake cewa komai ba sae bakin ta da ke motsi kamar mai addu'a,ta rufe idonta ruf,sae kawai ta saki hannayen su, a rikice farhan yace "no Amrah I Luv u more please dont leave me! "Amrah!!Amrah!!!jijjiga ta yake sosai yana kiran sunan ta,wani irin kuka ne ya qara zo masa ya rungume ta sosai. "Uncle" cewar Afrah ganin mutanen da ke shigowa d'akin. Gwaggo ce,dasu Habib had'e da en sandan da ke bayan su. Gwaggo taje da qyar ta 6an6are Farhan daga jikin Amrah,tana mai lallashin sa, do'ra kansa yayi kan kafadar gwaggo yana kuka kamar qaramin yaro yana mai cewa"gwaggo kinga Amrah ta tafi tabar ni shike nan daga yau bazan qara ganin ta ba,gwaggo shike nan bazan sake jin sautin muryar Amrah ba. Hawaye ne suka zubo a idanun gwaggo yayinda take shafa kan farhan,tace "farhan kayi haquri dama haka rayuwa ta ke, idan kaine yau gobe ba kai ba ne.

D'aya daga cikin police ne ya qarasa gun gawar Amrah yayi dube duben sa yaga tabbas lallai ba rayuwa a tare da ita nan ya girgiza kan shi had'e da jawo bedsheet ya rufe gawar.

Sannan suka tasa qewar su Habib gaba wad'an da hannayen su har qafa duk an sanya musu sarqa gudun kar su gudu.

Tun da gwaggo ta fara lallashin farhan had'e da yi mishi nasifa, sae yayi shiru kukan ya daina zo masa gabadaya, sae kallon gawar Amrah yake wacce aka rufe da farin bedsheet ya kafe idon shi guri d'aya wato gefen cikin ta da aka harba wanda har jini ya 6ullo kan farin qyalle da aka rufa mata. Ganin baya da niyar daina kallon gurin yasa gwaggo ta jawo hannun shi dana Afrah suka bar dakin.

*Futha Luv💅🏻 & Billy giro😊*

🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:20PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 7/21/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 ~*AFRAH KO AMRAH* ~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*Na* *Bilkeesu giro😊& Bilqis Sidibe💅🏻*

🏅1⃣5⃣🏅 Washe gari bayan an dawo daga gurin jana'iza.

Mutanen da suka zo ma gwaggo gaisuwa sae jimamin yanda abin ya kasance suke. A nan gwaggo take musu bayani ko ita ta tashi sallar dare ne sae taji a ajikin ta gidan kamar ba lafiya,har tana jin kamar hayaniya a 6angaren su farhan koda taje sae taji duk irin abubuwan da ke shirin faruwa tsakanin farhan da en fashi,wanda hakan yasa tayi hanzarin komawa ta dauki waya ta kira police sae dae koda suka iso har sun aiwatar da nufin su.

A 6angaren farhan kuwa tunda aka dawo daga gurin jana'iza yaji komai ya dawo mishi sabo har ma ya kasa zaman kar6ar gaisuwa ya shige d'aki ya had'e kai da guiwa sae kukan zuci yake. Yana cikin haka ne sae ga JB riqe da Afrah,ya shigo da sallamar sa. Farhan ya d'ago idanuwan sa da sukayi jajir cikin raunin murya ya amsa sallama, yayinda JB ya sami guri ya zauna,yace"farhan kayi haquri kazo muje gurin zaman kar6ar gaisuwa bai kamata ace mutane na zuwa basa samun ka ba. Farhan ya kalli Afrah da ke kallon shi kamar wacce zatayi kuka,wanda tun jiya yake ganin yanayinta haka, duk da cewa yasan bata san meye mutuwa ba amma yanayin ta kamar wacce tasan mutuwa, yace da JB ka maida Afrah cikin gida sae kazo muje. JB yace "zarah zo muje gun gwaggwo"maqale kafada tayi tace"um um uncle ka tafi kawai ni gurin uncle d'ina zan zauna"farhan ya nisa tare da jawo hannun ta yace"ki bishi kinji,an jima zan je gurin gwaggo na d'auko ki. Nan ta gyd'a kanta JB yaja hannun ta suka fice.

Koda JB ya dawo ya sami fu'ad yazo gurin farhan a tare suka fice gurin zaman kar6ar gaisuwa.

Sae guraren qarfe goma farhan ya sami komawa cikin gida sbd sae a wannan lokaci en kar6ar gaisuwa suka watse. Yana zuwa ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito kenan ya sami Afrah tsaye cikin kayan baccin ta,tana riqe da d'an qaramin silver flask, d'ayan hannun ta kuma tana riqe da teddy. zuwa tayi ta miqa masa flask bata ce dashi komai ba sae cup da taje ta d'auko ta bashi, bud'e flask d'in yayi ya zuba mata tea mai kauri,sannan ya zauna ya dora ta kan qafafun sa, Ya kai cup a bakin ta,ta girgiza kanta, tace"uncle kamanta cewa kai ke fara sha kafin ni,farhan yayi shiru can yace"poppy luv" _*ya kan kira ta da wannan sunan ne sbd poppy sunan wani plant ne mai dauke da red flower wanda Afrah ke mugun so domin duk suka shiga garden bata da aiki sae tayi ta tsinko flower tana wasa da shi,har ma tana sawa a gashiñ kanta,shiyasa yasa mata poppy luv shine idan ta motsa masa wani lokaci sae ya kira ta da sunan*_

Farhan yaci gaba da cewa"poppy luv ni bazan iya cin komai ba yanzu"kallon shi tayi tace"uncle idan baka sha ba nima bazan sha ba"farhan yayi shiru yana kallonta,shi dai baya jin zai iya cin komai damuwar sa kad'ai ta ishe shi, sae dae baya iya barin Afrah da yunwa domin yasan idan bai sha ba,baza ta sha ba.

A hankali yakai cup a bakin sa ya kur6a kadan, sannan ya bata tasha,da yake shegen wayo ne da ita duk ya bata tasha bata yarda ta sake sha sae yasha domin ita ma ke riqa cup din ta kai a bakin sa,da haka har suka shanye tean gabad'aya har sauran da ke cikin flask basu rage ba sbd dukkan su yunwa suke ji.

Gwoggo ce ta shigo da sallamar ta dauke da abinci ta ajiye abincin tare da fad'in "nasan cewa yau duk baka ci komai ba, don Allah kayi qoqari ka sawa cikin ka wani abu kafin ka kwanta"ai yanzu muka gama shan tea nida Afrah"wannan d'an tean ne zai ishe ku"Allah gwaggo ba don Afrah ba da bazan iya sawa baki na komai ba,kuma tean kauri ne dashi sosai shiyasa ya ishe mu"ai dama tean ku biyu na had'a ma shi,sbd tana ganin zan had'a mata tace na had'a har da uncle"kawai dai nayi tunanin cewa ba zai ishe ku ba sbd kun yini da yunwa domin ko ita yau bata ci komai ba, duk nayi mata zancen abinci sae tace sae da kai zata ci, ba yanda banyi ba amma taqi ci, hakan yasa yau duk bata sha maganin ta ba,cikin sanyin murya wanda dama tun d'azun haka yake maganar sa yace"ai gwaggo a ajiye zancen shan maganin ta domin kinga taji sauqi,to idan ta daina sha baza a koma er gidan jiya ba?a'a gwaggo dama abinda na fahimta shi ne ihun da tayi tun a lokacin da aka harbi Abba(Alhj Sadiq) shine ya kawo mata matsala a cikin dodon kunnen ta har ta daina ji,sae gashi jiya tana jin qarar bindiga tayi razanannen ihun da nake sa ran shine ya kauda wannan matsalar farko ma'ana ya dawo mata da jin ta,amma duk da hakan zamu je asibiti a duba ta. Gwaggo ta nisa tace"ikon Allah ni kam tun jiya nake ta mamakin yanda take magana ashe haka abin yake,Allah yasa samun lafiyar kenan, kai kuma Allah ya baka ikon haqurin rashin da mukayi na Amrah, yace Amin kafin take fita daga dakin.

Sae da Afrah tayi bacci sannan ya kai ta gurin gwaggo. Ya dawo shi kad'ai cikin d'aki abin tausayi wanda kallo d'aya zakayi masa kasan shi kanshi yana jin tausayin kanshi, duk da cewa ba'a wancan d'akin yake ba,domin tunda aka fitar da gawar Amrah bai sake leqa d'akin ba. Sanin cewa ba zai iya yin bacci ba bai ko gwada kwanciya ba yaje ya d'oro arwala ya shiga jero salloli inda duk yayi raka'a biyu sae ya jima sosai yana karanto addu'o'i.

A 6angaren su Habib kuwa hukuncin d'aurin rai da rai aka yanke musu tare da horo mai tsanani a bisa rashin sanin iya adadin ran da suka kashe garin yawon su na fashi da makami.

Bayan sati 1

Haka rayuwar farhan ta dawo so lonely, sea dae sauqin sa d'aya yawan ibadar da yake da kuma addu'a duk sae komai ya fara masa sauqi wato damuwar da yake ciki ta fara rage mishi,domin yanzu har ya koma kan aikin sa wanda sae ya kai Afrah school ne yake ficewa asibiti.

*Futha Luv 💅🏻 & Billy giro😊*

🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:20PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 7/23/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 ~*AFRAH KO AMRAH* ~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*Na* *Bilqis Sidibe💅🏻&Bilkeesu giro😊*

🏅1⃣6⃣🏅 Sannu Sannu lokaci keta ta tafiya domin yanzu Afrah har tana primary 2 inda take tafka rashin ji a school son ranta ita da qawar ta Amrah (wato wacce JB ya had'a ta da ita tun a nursery) duk makarantar an san da zaman su kan rashin jin su,ga kwanya da Allah ya musu sae ma ka rasa wacce tafi qoqari a cikin su, hakan yasa suke zowa first position ma'ana bracket sukeyi.

Riqe take da towel d'an qarami dai dai ita pant kadai ne a jikin ta, tana tsaye a bakin qofar toilet sae kuka take cike da shagwa6a yayinda take kallon gwoggo da ke had'a mata tea ta sanya madara kenan sae ga farhan ya shigo,ya kalli Afrah tare da girgiza kanshi domin inda sabo ya saba sbd kullum idan za'a je school sae Afrah tayi kuka.

Sae da ya gaida gwaggo ya qarasa gurin Afrah da ta qara fitar da sautin kukan ta, farhan yaja hannun ta suka zauna kan sofa,ta wani narke masa a jiki tana ci gaba da kuka.

Farhan ya shiga lallashin ta inda yake cewa"poppy luv meyasa kullum roqon ki nake akan ki daina kuka amma kullum sae kinyi kuka"a shagwa6e ta share hawayen ta tace"to uncle kullum ni bana baccin safe tun bacci bai ishe ni ba ma ake ta she ni"kiyi haquri poppy luv haka boko yake sae da haquri,mararaicewa tayi tace "to uncle zaka bar ni yau kar naje?...no poppy luv kin manta yau friday saurin tashi ake?cikin 6acin rai mai d'auke da shagwa6a ta kalle shi kafin take tashi kan jikin sa tare da jefar da towel d'in da ke hannun ta, tace "oh no uncle! uhm uhm"nan ta shiga bubbuga qafafunta a qasa kafin take zama dirshan kan tiles ta had'e kai da guiwa ta fara rera sabon kuka, farhan yayi shiru yana kallon ta da alama kukan yana masa zafi a rai ,ya kira sunan ta kusan sau biyu bata amsa mishi ba,yace "ba ruwana dake idan baki zo mun shirya ba"yana gama fadar haka ya jingina a jikin sofa tare da lumshe idon shi. Afrah ta d'ago kanta tana kallon shi,wanda tayi 15 secnds a haka,jin ta daina kuka yasa farhan ya bude idon shi a hankali ya sauke su kan Afrah, kunnen ta ta kama tace "sorry uncle"sannan ta share hawayen ta tace "na daina kukan kar kayi fishi dani kaji, kaji uncle, murmushi farhan yayi yace"oya zo kiji wani albishir"da hanzarin ta taje inda yake rad'a mata abu a kunne Afrah ta daka tsalle cike da murna tace shike nan yau bazan tsokani kowa ba na maka promise uncle,farhan yace "yauwa my poppy luv ko ke fa to mu tafa ko,nan suka tafa tare da lotsa kumatun junan su, wanda hakan ke qara sa kowannen su ya qara fadada murmushin sa. Gwaggo dai sae murmushi take tana kallon su inda sabo ta saba,domin kullum haka ke faruwa sae da wayo ake samu taje school ba kuka.

Sae da tasha tea sannan gwaggo ta shirya mata suka fice.

12:20pm ya koma domin ya dauko ta sae sauri yake sbd a 12 ya kama ta yaje dauko ta se ya had'u da go slow kan hanya.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull