Afra ko amrah complete - Chapter 12
Afra ko amrah complete Chapter 12: Afra ko amrah complete Chapter 12. JB ne yazo gidan ya sami Farhan yana shirin zuwa Abuja cikin sakin fuska suka gaisa.…
4,398 words
JB ne yazo gidan ya sami Farhan yana shirin zuwa Abuja cikin sakin fuska suka gaisa. Farhan ya kalli JB da yayi matuqar ramewa wanda kallo d'aya zaka yi masa kasan yana cikin damuwa yace"JB rashin lafiya kayi ne? dan guntun murmushi yayi mai cike da damuwa yace" ba komai "wanda ya fad'i haka ne kawai amma ciwo ya darza kamar ba zai rayu ba sbd jin an auradda Afrah ga farhan sae dai ba yanda ya iya sbd mahaifin sa ya sanar da shi yanda auren ya kasance shiyasa kullum yake qoqarin ganin ya haqura da son Afrah amma kuma ko yaushe sonta qaruwa yake. Farhan yace"kace lafiyar ka qalau amma sae qara ramewa kake ko dai aure kake so baka da wacce zaka aura gaya min yanzu kaga aiki da cikawa muje gidan su husna mai awara zuwa yamma a d'aura maku aure, murmushi kawai yayi yace"ai husnah kai take so ba ni ba,farhan yace"ai kasan tace idan har bazan aure ta ba duk wanda na kawo zata aure shi sbd ta gefena ya fito zata ji sauqin sonda take min"ya fad'i haka ne yayinda JB ya shiga tunanin kaddai ace farhan lafiyar sa qalau son aure yasa yayi haukar qarya aka masa aure da Afrah....no akan me zai yi haka in aure yake so ai ba wanda zai ce ya hana shi bare yayi haukar qarya,,,farhan ya katse shi da cewa zo muje muyi break fast ka raka ni Abuja daga nan muje school d'in su Amrah na ganta naji yaushe ne zasuyi hutu domin na samu na cikawa Afrah alqawarin ta na son na maida Amrah Oman. Ba musu JB yaje sukayi break fast bayan sun gama sukayi wa gwaggo sallama suka tafi.
*Aftar 3 days* Duk wani bincike da farhan yayi bai sami leesa ba sae qawar ta suka samu a school wacce cikin hikima suka shayo kanta ta sanar da su leesa bata dawo Nigeria ba ta tafi qasar China inda kafin ta sanar da su garin da taje aka kira wayar ta wacce ta zamo tashin hankali a gare ta domin mutuwa ce aka sanar da ita wanda kan tsananin rud'un da ta shiga bata bi ta kansu ba ta wuce a gurguje.
*Leesa*
Waya take da mom farida inda take ta bata haquri ita baza ta sami dawowa nan kusa ba har sae farhan ya ajiye zancen nemanta domin duk abinda farhan keyi tana sane wanda ko qawar ta da suka zaci mutuwa ce aka sanar da ita ba duk mutuwa ba ce leesa ce ta kira ta tace tayi pretending as mutuwa ce aka sanar da ita kar ta qarasa sanar da su inda ta ke bcs they are kidnappers wanda hakan yasa qawar ta qara rikicewa.
Farhan ne a gaban gwaggo yana sallama da ita zai koma Oman a cewar zai koma kan aikin sa indai leesa ce zai ganta ko ba yanzu ba. Nan gwaggo ta masa Allah ya tsare tare da bashi saqo ya kaiwa Afrah.
*```Oman```*
Farhan na shiga gidan bai zarce ko ina ba sae 6angaren su Maman Amir , ya sami Amir da Afrah zaune ana mata assignment. Sau d'aya Afrah ta kalle shi ta kauda kai su Amir kuwa da murna suka tarbe shi.
Har suka koma 6angaren su Afrah bata ce da shi komai ba da suka shiga ma d'akinta ta wuce, iya damuwa farhan ya damu bcs tun tashin Afrah bata ta6a fushi mai tsawo da shi haka ba.
Sae da yayi wanka ya nufi dakin ta sanye da bathrobe a jikin sa. Ya same ta ta fito daga wanka kenan riqe da d'an qaramin towel gashin kanta sae tsiyayar ruwa yake wanda ya sauko har kan kafad'un ta. A hankali ya qarasa gab da ita tayi sauri jayewa gefe ta bar shi tsaye yabi ta da kallon mamaki yayinda ta fara tsane gashin kanta. Sake matsawa yayi kusa da ita ya riqe towel d'in da take tsane gashin kanta nan ta sake mishi towel d'in,ta kuma qi yarda su had'a ido kamar yanda yake buqata, hakan yasa ya kai hannu ya d'ago fuskarta yana kallon qwayar idon ta da ke son cikowa da qwalla,yace"Afrah kar kiyi kuka domin wannan karon idan kikayi kuka zan iya taya ki sbd na azabtu da fushin da kike yi dani, idan kuma kina son ganin kuka na ne to bisimillah"
Bata iya had'iye kukan ba sbd ya riga yazo gab hakan yasa ta fad'a kan jikin sa inda ta kama wuyan bathrobe din da yake sanye da ita ta cusa fuskar ta a cikin qirjin sa tana qoqarin hana kanta kukan.
*Billy giro😊&Futha lurv💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [11/3/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*
*Futhalurv.WordPress.com*
*```🏅42🏅```*
Amma ta kasa domin kai tsaye farhan yaji hawaye na sauka kan qirjin sa har izuwa cikin sa,qara 6oye fuskar ta tayi tace"dan Allah uncle kayi haquri kar ka yi kuka Allah bana son ganin kukan ka na kasa controlling kaina ne. Bai ce mata komai ba face sunan ta da ya kira , murya can ciki ta amsa. Ya d'ago fuskar ta yana share matq hawaye yace"naji bazan yi kukan ba amma ki daina fushi da ni kinji,,, na daina uncle amma meyasa baka zo da Amrah ba. ta fad'i haka ne yayinda take kallon cikin idon shi kafin yace wani abu tace"pls uncle dan Allah ka maida mu school d'aya kàji" InshaAllah Afrah i will. Tace "da gaske uncle? da gaske bcs har makarantar su naje naga idan sun kusa hutu amma basu kusa ba shine nace zan cire ta kawai wanda har mun kammala zancen da Abbanta kuma ya amince dis coming week zai kawo ta inshaAllah. Cikin murna sosai ta daka tsalle ta qara qanqame shi tana mishi godiya. Cikin jin dad'i farhan ke shafa bayan ta domin a duk duniya bashi da wani buri irin yaga Afrah cikin farin ciki. Da haka ya fara yaye towel d'in ta domin yana son yaga yanda bayan ta yayi, bata ji tsoro ba domin ta fahimci me yake son gani, kawai dai ta qara manna jikin ta da nashi sbd kar towel din ta ya zame ta qirjin ta. Haka shima bai zare towel d'in gabad'aya ba a iya inda zai gani kad'ai ya bud'e yana kallon yanda gurin yayi sauqi sosai, nan ya kai hannun sa yana shafa gurin a hankali ,Afrah da ke jin dad'in shafar sae qara lafewa tayi bcs dama gurin qaiqayi yake mata tana buqace da a sosa mata gurin. Sae d'akin yayi tsit kamar ba kowa. Afrah ta katse shirun da cewa "uncle kaga yanda gurin yayi saura kad'an ya qarasa warkewa shiyasa a kwanakin nan duk ina zuwa school wanda kafin naje sae Maman yaya Amir ta shafa min magani haka idan zanyi bacci ma ta kan shafa min, kuma kullum idan taga ina kuka ta kan rarrashe ni tace nazo muje yawo,daga gurin yawon take saya min sweets kala kala har sae nace ya ishe ni haka, kuma ko Abban yaya Amir kullum sae ya kawo min ice cream da chocolate, shi kuma yaya Amir kullum sae ya aramin wayar sa nayi game amma idan ina da Assignment sae ya koya min nayi ya kuma qara fahimtar dani karatun da aka mana sannan ko zanyi game. Nan ta kawo qarshen zancen ta farhan yayi murmushi yace"iyayen surutu wai ke ba kya gajiya ne? Turo baki tayi ta jaye kan jikin sa tare da buga qafafun ta cikin tsantsar shagwa6a tace"uncle wane surutu baka ji me nake gaya maka bane kace wani abu man"farhan da ya fahimci me take son yace, yace"to Afrah kin gode sosai Allah ya saka musu da alhairi"tsalle tayi taja hancin sa tare da fad'in "amin uncle haka zaka ce ba wai kace ina da surutu ba" Nan ya d'auke ta cak suka je dakin shi. Ya d'auko mata saqon gwaggo koda ta bud'e dambun nama ne da yayi shegen kyau, wani irin dad'i Afrah taji bcs tana mugun son dambun nama, farin cikin ta ne ya qaru yayinda farhan ya miqa mata ledar wani sweet yace"inji Amrah tace a kawo miki"ihu ta saki tana tsalle kan gado, farhan ya kishingid'a yana kallon ta se fadin take"wayyo uncle wlh ina mugun son sweet d'in nan gashi a school d'in mu kad'ai na ta6a ganin shi..... towel d'in jikin ta ne ya kunce kan tsallen da take wanda ba shiri ta fad'a kan jikin farhan ta cukuikuye shi,shi kuma farhan yayi saurin bude bathrobe din jikin sa ya rufa mata jikinta ya kasance sun rufa da abu d'aya shiyasa suke jin had'uwar fatar jikin su , sae dae Afrah bata yarda qirjin ta ya had'u da jikin farhan ba hannu tasa ta kare qirjinta, ta kuma qi yarda ta dago fuska ta kalle shi domin duk ta cika da jin kunya. Sun jima a haka farhan yace"Afrah wakeup mana a ina towel d'in naki ya fad'a? shiru tayi ta kasa ce mishi komai kuma ya fahimci cike take da son ta tashi yace"ok zan rufe ido na sae ki tashi kinji, ba musu ta gyad'a kanta ya rufe idon sa a hankali tare da fad'in "oya wakeup kinji" Bata iya tashi ba sae da ta kai hannuwan ta duka biyu ta qara kare qirjin ta,inda sauqin ta d'aya akwai pant a jikin ta.
Sae da ya tabbatar da ta d'aura towel sannan ya bud'e idon shi ya tashi zaune tare da d'aure bathrobe ya kalli Afrah wacce ke zaune bedside kanta qasa sae duk ta fito cikakkiyar marainiya. Farhan ya matsa gab da ita tare da dambun naman da ta ajiye kan drawer ya d'ebo kad'an yakai a bakin ta yace "kar6i kici kiji yanda dambun yayi dad'i sosai"cikin muryar kuka tace"uncle Allah yasa baka ganni ba?ban ganki ba Afrah,, da gaske uncle? da gaske nake,,,to ya akayi baka ganni ba bayan kallo na kake?sbd koda towel d'inki ya kunce an kira ni a waya hakan yasa na d'auke ido na kan na d'aga wayar sae kawai naji fad'owar ki kan jiki na",murmushi ta saki tare da kwantowa kan jikin sa tace"thank God da baka ganni ba da bazan qara iya had'a ido da kai ba"hancin ta yaja yace kinji ki da iya yi, wane dare ne jemage bai gani ba da har kike jin kunya ta yanzu, ko kina nufin har kin manta ni ke miki wanka, hm uncle kenan to ai wannan da ne kuma da da yanzu ba d'aya ba, to ai ko nan gaba zan miki,kallon sa tayi tace"idan na mutu? koma yaushe ne zaki gani, ya fad'i haka ne yayinda ya saka mata dambun nama a baki ita ma ta de'bo ta saka mishi haka suka ci gaba da cin abin su cikin natsuwa har suka kammala.
Bayan sun gama ne farhan ya d'auko wani magani yana shafa ma ta a bayan ta tace"uncle wannan kuma wane irin magani ne naga ba irin wanda ake shafa min kullum ba ne? Maganin da yake 6atar da tabo ne bcs bana son ganin zanen bulalan nan a jikin ki.
Yana gama shafa matà suka yi shirin bacci suka kwanta suna kallon wani horo film sbd irin finafinan da Afràh keso kenàn amma kuma sae ihu take tana qanqañme farhañ kumà idan yace zai kashe ta ajiye mishi kukan shagwa6a a kañ dole yake fasawa. Suna cikin kalloñ ne akayi wani guriñ dà yayi mugun firgita ta ai kuwa ba shiri tà saki ihu ta 6oye fuskar ta a qirjin farhan tana fad'in"wayyo Allah uncle a kashe"yace"bazan kàshe ba tunda in na kàshe kuka kike min. Hakan yasa taqi yarda ta d'ago wanda daga haka tàyi bacci, burin fàrhan kenan domin baya son tayi doguwar fira sbd akwai school gobe. Yace"iyayen rigima anyi bacci" Ya fad'i haka ne yayinda ya gyara màta kwanciyar ta, ya kashe kayan kàllo da hasken d'àki shima ya shiga bacci.
MAKARANTA AFRAH KO AMRAH DON ALLAH MUNA SON KOWACCE TA MIN MAGANA TA WANNAN NUMBAR *08140674366* *(Billy giro)* *A whatsApp chat ta sanar da ni sunan ta bcs ina son zan had'e ku a grp d'aya kasancewar ba wani yawa ne da ku ba kuma hakan zai fi mana sauqi a gurin posting* *muna fatar zaku ba mu had'in kai*
*Futha Luv💅🏻&Billy giro😊* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [10/10/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*
*Futhalurv.WordPress.com*
*```🏅43🏅```* Washe gari, Afrah da kuka da komai farhan ya samu ta tashi wai ita bacci bai isheta ba wanda tana zuwa toilet corner ta zaro towel ta shimfid'a tayi kwanciyar ta taci gaba da bacci. Sosai farhan yaga ta jima bata fito daga wankan ba gashi sauri yake shima yayi wanka kasancewar sunyi lettin tashi. Tashi yayi ya nufi hanyar toilet domin ya qwanqwasa mata tayi sauri, sae kawai ya had'u da ita toilet corner sae sharar baccin ta take,bai yi mamaki ba sbd yasan halin ta ne wanda yanzun taga damar idan ya tashe ta ko ta shiga toilet d'in zata ci gaba da baccin ne . Ransa ne ya 6aci wanda dama ransa a 6ace yake kan lattin sallar da yayi. Nan ya durqusa inda kai tsaye ya shiga cire mata rigar bacci, Afrah ta tashi firgigit ta kalli kanta daga ita sae pant da half vest sae duk ta 6ata fuskar ta tana kallon farhan wanda taga 6acin ransa yaci uban nata dole tayi shiru har yaja hannun ta suka tafi toilet ya shiga da ita gurin wanka tare da sake shower , sannan ya nad'e hannun jallabiyar shi, Afrah tace"yi haquri uncle zan yi wankan da kaina wlh bazan koma bacci ba. Bai kula ta ba ya shiga yi mata wankan ba tare da ya cire pant da half vest d'in da ke jikin ta ba amma duk da haka ta kasa sake jiki sae kame kame take tace"don Allah uncle ya isa haka zan qarasa da kai na" cikin kakkausar murya yace"idan kika sake min magana Alllah sae na raba ki da komai na jikin ki! ba yanda ta iya dole tayi shiru har ya gama yima mata wanka yace"oya sae ki cire pant da half vest ki wanke guraren ni zan fita kuma kar ki 6ata min lokaci idan kuma kinsan zaki 6ata min lokaci zan miki da kaina. Saurin girgiza kanta tayi tace"Allah zanyi sauri" Bai ce mata komai ba ya fita. Bata jima ba ta fito ta same shi yayi shirin shiga wanka ya fitar mata da uniform. Yace"kiyi zaman ki kinji har na fito toilet baki yi komai ba" Afrah ta bishi da ido har ya shige toilet tace"yau meyasa uncle yayi fushi haka" Tana cikin fad'ar haka idon ta yakai kan agogo saura 30 mnt 8 tayi gashi ko sallah bata yi ba bude ido tayi ta jefar da towel d'in jikinta ta saka uniform sannan ta d'auko Vaseline ta shafa taje ta kabbar ta sallah. Koda farhan ya fito ya samu har ta gama salla ta saka takalmi ta d'auko school bag zata goya. Zuwa yayi jikin wardrobe ya nemo wata jallabiya yasa, yaja hannun Afrah suka je 6angaren Maman Amir aka basu break fast had'e da lunch box. Cikin mota Afrah tayi break fast sae kallon farhan take d shakku, duk da ba kallon ta farhan ke yi ba amma ya fahimce ta ta gefen ido. Sae da suka kawo school sannan ya kalle ta cikin sakin fuska yace"yaya kin gama break fast d'in? Eh uncle saura kawai ka daina fushi dani,hugging d'in ta yayi tare da d'ora mata kiss gefen fuska yace"shike nan na daina fushi da ke" Cikin jin dad'i ta d'ora mass kiss kan goshi tace"thank u"tare da d'aukar lunch box in ta tana mishi bye bye har ta shige. Ajiyar zuciya ya sauke ya samu da qyar yaja motar sbd wani irin zazza6i da yake jin yana fizgar shi. Yana zuwa gida ko break fast bai samu yayi ba ya kwanta. To 10 yayi shirin zuwa asibiti inda a daddafe ya samu yakai asibiti.
Guraren qarfe biyar Amir ne yaje ya d'auko Afrah wacce da shigar ta taje d'akin farhan ta hango shi qudundune cikin bargo. Ajiye school bag tayi ta cire takalmi da socks sannan ta hau gadon tare da yaye blanket tana neman gurin kwanciya kan jikin shi. Sae da ta gama shigewa jikin sa sannan ta fahimci jikin nasa da zafi sosai,a hankali takai hannu ta ta6a goshin sa wanda hakan yasa ya bud'e idon shi a hankali yana kallon ta tace"uncle baka jin dad'i ne? Am fine kawai ina yin bacci ne,amma uncle kaifa ka gaya min baccin bayan sallar la'asar baya da kyau amma shine kake yi"sorry na kasa control in baccin ne"to meyasa naji jikin ka da zafi,sbd na jima a kwance...uncle kaifa kace min qarya ba kyau. haka ne Afrah... to amma shine ka min,, meyasa kika ce qarya na miki? sbd na fahimci baka jin dad'i da gaske,,yes Afrah haka ne amma naji sauqi ba kamar d'azun ba kuma don bana son ki shiga damuwa ne yasa nace miki am fine,kafin tace wani abu idanuwanta suka ciko tap da qwallah inda cikin muryar kuka tace"me yake maka ciwo ne uncle?it's just headache...don't callit just bcs nasan yana maka ciwo sosai...kinga ki daina kuka shiyasa bana son ki san bana jin dad'i sbd kin dinga yin kuka kenan har sae kema kinxo ba kya jin dad'i se duk ki kamu da zazza6i wanda har naji sauqi ke baki ji sauqi ba sbd yanayin rashin qarfin jinin ki don haka stop it pls sbd idan kika fara ciwo baki iya ba.... ai kaima haka ne uncle shiyasa bana son naga kana rashin lafiya....ai wannan karon ciwon yazo min da sauqi tunda har kika ga na samu nayi bacci. Nan yayi ta rarrashin ta har ya samu tayi shiru. Ta tashi taje tayi wanka ta d'ebo musu abinci suka ci.
Haka farhan yayi ta fama da zazza6i har kusan sati d'aya sae faman 6oyewa Afrah yake wacce kullum cikin ta6a jikin sa take taji idan ba zafi in taji zafin kuwa ta nemi yi masa sae ya samu da qyar ya rarrashe ta.
Yaune Amrah zata zo inda ranar ta kasance weekend shiyasa Afrah ta ca6a kwalliya sae murna take ta kasa zama ta kasa tsayi ko abinci bata ci ba kan cewa sae Amrah tazo zasu ci tare, se damun farhan take da fad'in "uncle wai har yanzu basu iso ba"shi kuma yana bata amsa kan ta qara haquri sun kusa. Sae da ya kwatanci lokacin saukar jirgin su ya kusa sannan yaja Afrah suka je air pot. Suna isa kuwa jirgin ya sauko Afrah ta shiga rarraba ido ta inda zata hango Amrah,ai kuwa tana hango su ta tafi da gudu suka rungume juna inda gabad'aya su murnar ganin juna suke kamar wad'an da sukayi shekaru basu had'u ba.
Bayan sunje gida Afrah ta kawo ma Baban Amrah Abinci da lemu sannan ta ja Afrah suka je d'akin ta ta zuba musu abinci suka fara ci sae fira suke.
Sae washe gari Baban Amrah ya koma.
12:00am Afrah ce ta shigo d'akin farhan sanye da rigar bacci iya guiwa rumgume da teddy a qirjin ta . Ta yi tsaye tana kallon farhan da ke juyi cikin bacci yayinda yake fitar da addu'a a hankali _" la'ilah ha ilallah wahidul qahhar, rabbus samawati wal'ard wama bainahumal azizul gafoor"_ rufe bakin sa keda wuya yaji mutum tsaye a kansa kafin ma ya bud'e idon shi yace "Afrah lafiya" Wanda yana gama fad'ar haka ya tashi zaune yaja hannun ta ya zaunar da ita kusa da shi ta kwantar da kanta kan kafad'ar shi tace"uncle na kasa bacci haka ko jiya ban iya yin bacci mai kyau ba" Haquri zakiyi Afrah ki fara koyon bacci ba ni bcs kinga baza ki bar Amrah ita kad'ai ba,,ai bazan iya barin Amrah ita kad'ai ba kawai dai na kasa baccin ne,,to naji zan koya miki wata addu'a yanzu inshaAllah idan kika yi ta zaki samu kiyi bacci. Zan fara sae ki saurare ni da kyau,,, ok uncle. _A'uzu bi kalimatil lahi tammat min adabihi wa iqabihi,wa sharrah ibadihi, wa min hamazaati shaid'an wa'an yahdurun._
Sau uku yana maimata mata sannan yace zai karanta ta riqa amsawa, haka suka yi har sau biyu ana ukun yaji shiru ba amsa koda ya duba tayi bacci abinta bai yi mamaki ba sbd tun amsawa ta biyu ya fara jin alamar tana son tayi bacci. Sae da baccin ta yayi nisa ya d'auke ta yakai ta d'aki,inda cikin hikima ya zare jikin sa daga nata sae wani qara qanqame teddy take a qirjin ta. Sae da yayi mata addu'a sannan ya fita. wanda duk abinda yake Amrah na kallon shi har ya fita sannan ta kalli Afrah long time kafin take komawa bacci.
*44*
On Monday tare Farhan ya kai su school yayinda yake jaddada musu kar ganin suna kusa da juna su sa wasa a karatu ko suyi rashin ji idan kuma kuka sa wasa to lallai zan raba muku school ne.
Wannan kenan.
Sosai kuwa suka maida hankali sbd ba wacce ke son a raba musu school musamman ma Afrah.
6angaren leesa kuwa duk inda take tare take da er qwaryar tsafin ta wacce duk abinda ke faruwa tsakanin farhan da su Afrah tana gani tamkar video shiyasa hankalin ta ya kwanta taci gaba da yin harkokin gaban ta har dai da taga kwata kwata farhan baya da niyyar kusantar Afrah nan kusa.
Sannu sannu rayuwa keta tafiya wanda yanzu su Afrah har suna j .s .s 3 girma ya qara zo musu dai dai yanda ya kamata yayinda kyansu ke qara fitowa, haka kuma shaquwar su ta zarce misali.
Ranar Wednesday da safe su Amrah ne ke shirin zuwa school . Amrah har ta kammala shirin ta tsaf amma Afrah Vaseline kawai ta iya shafawa sbd jin take jikin ta ba dad'i,har tana jin bata iya ta6uka wani abu. haka farhan yazo ya sameta wanda kai tsaye ya fahimci bata jin dad'i amma ta dake kan cewa lafiyar ta qalau. Bai ce mata komai ba ya taya ta saka uniform d'in jikin ta domin ya fahimci ba wani abu take iya yi ba. Tsaf ya shiryata Amrah dai sai kallon su take. Bayan ya kaisu school ne yace da Amrah"pls idan kinga ciwon yai tsanani a kira ni bcs na fahimci bata jin dad'i amma kinji tace min lafiyar ta qalau.....nifa uncle ba abinda ke damu na....naji ai bada ke nake zancen ba da Amrah nake yi.
Daga haka bata sake cewa komai ba Amrah taja hannun ta suka wuce. Farhan da ya fahimci abinda ke damun Afrah wato period pain sae tausayi take bashi da kuma roqon Allah yasa kar abun yazo mata a school ta rasa yanda zata yi kasancewar bata ta6a yi ba yanzu ne zata yi na farko.
Afrah kuwa tunda suka shiga class ciwo ya hana ta zama sae kuka take sbd yanda cikin ta ke mata ciwo wanda ko magana akayi ji take ciwon ya qaru.
Farhan ne yazo ya d'auke ta suka je gida kasancewar an kira shi a waya. suna shiga gida ya wuce da ita dakin su ya kwantar da ita sae kuka take wanda ji take kamar ace zata iya hana kanta kuka sbd yanda take kuka haka cikin ta ke qara tsinka mata, gashi tayi zufa zufa ,hakan yasa farhan yaso ya rage mata kayan jikin ta amma taqi bari,sae da yayi ta rarrashin ta kan ta bari man tunda akwai inner wears a jikin ta, nan ya samu da qyar ta yarda ya cire mata uniform ya barta da half vest da d'an guntun wando iya cinya. Sannan ya shiga kicinyar ganin tasha magani . Bayan ya samu tasha ya d'ora ta kan cinyar sa ya kwantar da kanta kan kafad'ar shi yana share mata zufa da handkerchief nan bacci ya fara fizgar ta kasancewar maganin bacci yake sawa amma kuma still cikin ta yaqi daina ciwo shiyasa ta kasa yin bacci,nan farhan ya d'ora hannun sa kan cikin ta yana mata addu'a wanda ya jima kafin yake samu bacci ya dauke ta,shifid'e ta yayi ta juya zuwa ruf da ciki nan yaga wandon ta ya staining kad'an haka ma wandon jikin sa inda ya zaunar da ita. Bedsheets yasa ya rufa mata jikin ta ya tafi zuwa d'akin shi ya canza tufafi ya fita.
Bai jima ba ya dawo dauke da leda wanda pad ne a ciki da kuma panties . Tunani ya shiga yi ya tashe ta ko kuma ya barta sae dai baya son jikin ta ya lalace da yawa haka kuma baya son ya tashe ta daga bacci. Nan dai ya barshi akan ba zai tashe ta ba sbd wani tunani da yayi a matsayin sa na likita.
Laptop ya d'auko ya zauna kan gadon yana wani aiki wanda yayi kusan awa biyu yana abu d'aya Afrah kuwa sae sharar bacci take.
A hankali ta shiga motsawa hakan yasa farhan ya cire eyeglass d'in da ke kan idon shi ya rufe laptop yayinda yake kallon Afrah wacce da qyar take moving har ta samu ta zauna sae kuma ta yunqura ta tashi sbd sanyin da taji a qasan ta , hankalin ta ne yayi mugun tashi ganin jini duk ya 6ata farin bedsheet d'in da ke kan gadon,ta kalli farhan cike da son tayi kuka tace"waye yaji ciwo a cikin mu?tashi yayi yazo kusa da ita tare da jawo ta jikin sa inda ya shiga mata magana a natse kasancewar komai nasa a natse yake yinsa yace"Afrah ba wanda yaji ciwo a cikin mu girma ne ya qara zo miki baki ji a jikin ki bane?kasa ce masa komai tayi bcs ta fahimci me yake nufi sae duk ta kasa d'ago ido ta kalle shi. Yace "je kiyi wanka kizo ki shirya kinji " Nan ta gyad'a kanta ta shiga tafiya a hankali wanda ita kad'ai ta san zafin bala'in da take ji idan tana tafiya amma haka ta samu har ta je toilet. Farhan kuma ya d'auki bedsheets ya tafi da su d'akin shi ya wanke. Koda ya dawo ya same tq bakin qofar toilet tsaye yaje tare da miqa mata ledar pad da panties tace"uncle ai da baka siyo panties ba ina da su da yawa wad'an ban ta6a sawa ba yace"ba komai ai basu 6aci ba but inace kin iya saka pad? Eh an koya mana a school yace"ok"kafin take komawa daga ciki.