Kenza eBookz

Afra ko amrah complete - Chapter 14

Afra ko amrah complete - Chapter 14

Afra ko amrah complete Chapter 14: Afra ko amrah complete Chapter 14. D'aki yaje yayi zaune kan sofa ya dafe kan sa yana tunanin lallai ya zama dole ya…

4,312 words

D'aki yaje yayi zaune kan sofa ya dafe kan sa yana tunanin lallai ya zama dole ya ajiye duk wani tsari nasa wato na barin Afrah sae ta kammala high school ko zai nuna mata ainihin mene ne Aure. Domin baya jin zai iya sake ganin wani watan da Afrah zata sake shan wahalar period pain bayan yana da hanyar da zai taimaka mata sae dai matsalar sa d'aya har yanzu Afrah bata son a ambata mata kalmar aure wanda a da ya dauka yarinta ne amma se yaga har yanzu wanda ya rasa me ke damun ta. Haka ya qaraci tunanin sa kan cewa zai lalla6a ta idan tayi wankan tsarki ya kar6i haqqin sa ba don buqatar kan shi ba sae don ya samu wahalar period pain ya rage mata. Domin buqatar hakan bata fara zo masa ba tukun sbd wata allurar rage sha'awa da yake kar6a duk wata da kuma azumin da yake yawaita wa duk da cewa yawaita yin allurar na iya bashi matsala amma hakan yake yinta duk da yasan shi ba mabuqaci bane sosai amma yasan yau da gove sae Allah domin sanin cewa Afrah matar sa ce kan iya sa ya sa6a tsarin sa ba tare da yaso ba.

Bayan sati d'aya Afrah taji sauqi sae shirye shiryen tafiya Nigeria suke sbd sun kammala secondary school haka kuma farhan zai koma Nigeria da aiki sbd mutum ne mai matuqar kishin qasar sa akan lalura ne ma yasa ya yarda yayi aiki wata qasa wacce lalurar bai ko jima da ita ba Allah ya yaye masa ita wanda ganin Afrah ta fara school ne yasa ya hqr yaci gaba da aikin domin yana son ta gina foundation mai kyau, yanzu da suka kammala yayi hamdala ga ubangiji ya kuma rubutu takardar ajiye aiki.

Zaune yake a falo sae dubin agogo yake kan su Afrah da suka je saloon tun safe har yamma basu dawo ba gashi haka Afrah ta fita bata ci abinci ba kan zumud'i shiyasa duk ya damu.

Yana nan zaune ya yanke shawara kan zai je duk saloon d'in da ya sani ko zai gansu. Tashin sa keda wuya yaga an bud'e qofa su Afrah ne suka shigo a gajiya, Afrah da bata iya jira ya basu hnya ba tabi ta gefan sa ta zubar da ledojin da ke hannun ta taje kan seater jagwab ta kwanta sae maida numfashin gajiya take tace"wayyo uncle qafafu na kamar zasu sonce. Nan Farhan yaje yana mata tausa inda cikin kulawa da nuna damuwa Yace"my Afrah me ya tsaida ku haka bayan kinsan baki ci abinci ba? Uncle shopping muka je kasan ba mu qarasa sayayyar mu ba, amma Afrah ai cewa nayi ku bari har gobe tunda ba gobe ne tafiyar ba yau rnr saloon ce kawai. Ni uncle bana son na rasa wasu kaya da na gani jiya shiyasa nace ma Amrah muje,,, to naji tashi kuje kuci abinci...waih sae nayi wanka tukun sbd na gaji da yawa. Nan ya dauke ta cak suka haura sama Amrah dake leqen su ta jikin window tayi saurin sakin labulen tagar, ta jingina bayan ta a jikin bangon dakin tare da fitar da numfashi a hankali tace a ranta _"haqiqa rayuwar mata da miji abin sha'awa ce har dai idan ka sami miji mai sonka da gaske,ya rabbi ka bani miji na gari irin farhan ka kuma bani damar cire son wanda bai san ina yi ba wanda akan sa naqi kula kowa bayan nasan ko yace zai aure ni bazan yarda ba sbd bana jin zan iya kasancewa butulu koda kuwa zan mutu akan son sa._

Knocking d'in da akayi ne ya katse ta tayi saurin goge en sirarin hawayen ta sannan ta bud'e qofa. Farhan yaje ya dire Afrah kan gado tace"sannu uncle baka gaji ba? Hancin ta ya lakato yace "da me zan gaji wannan jikin naki da ba nauyi bare yinin yau duk baki ci abinci ba" Murmushi kawai tayi yace"oya je kiyi wanka ko kuma a d'aki na zaki je sbd kinga Ko Amrah tana so tayi.... Ai tun a mota nace nice first d'in wanka don karma tace ta riga ni,,,Uhm Afrah kenan ki wahalda ita kuma kice kece first d'in wanka to ke Amrah kin yarda da hakan?hm banni da ita uncle wai ita shegen wayo ne da ita amma zan rama....yanzun ma kuwa zan taya ki ki rama domin zan riqe miki ita ne sae kinyi wanka kafin tayi, Afrah najin haka ta tafi da gudu sae toilet wanda da shigar ta ta jefo doguwar rigar jikin ta tare da fad'in"wlh kar ki shigo na tu6e" Farhan yace"nidai ke shirin shigowa yanzu" nan ya nufi hanyar toilet , Afrah tayi saurin saka key tana bashi haquri kan kar ya shigo, sae da ya d'auke rigar da ta jefo yace"to yi sauri kiyi ki bata guri kuma da kun gama ku tabbatar kunci abinci after that kizo d'aki na ina son ganin ki"tace"tom"kafin yake fita. Bayan sunyi wanka sun ci abinci still Afrah na jin jikin ta cike da gajiya, hakan yasa ta koma bayi ta shiga ruwa masu zafi domin gasa jikin ta ko zata rage jin gajiyar, da haka ne bacci ya kwashe ta a cikin ruwan.

Ta d'au lokaci kafin take fitowa a gurguje tana d'aura towel tace "Amrah ashe bacci nayi.....au haba? Allah kuwa gashi nasan uncle na can yana jirana Allah yasa kar yayi fushi" tana gama fad'ar haka ta fita.

Koda ta shiga d'akin farhan ta same shi ya gama waya kenan kallo yabi ta dashi sbd wani musulmin kyau da ta mishi kan gyaran gashin da ke saman kanta irin gyarn nan da ake mimmird'e suma wato curly hair style wanda duk da hakan bai hana gashin ya sauko har kan kafad'un ta ba. yayi scnd 10 yana kallon ta inda kai tsaye ya fara jin wani abu shiyasa yayi saurin kauda idon sa a kanta.

Afrah da ta zaci fushi yayi ta kama kunnen ta tace"sorry uncle bacci ya d'auke ni shiyasa kaga banzo kan lokaci ba" ta qarasa gurin sa sbd murmushin da ya mata yace "ba komai" Zaman ta keda wuya ya shiga shafar sumar kanta yana tura hannun sa a cikin gashin sae yaba gyaran yake tace"thank u"tare da kwantar da kanta a kafada'ar shi tace"uncle ka fad'a min dalilin kirana ina so na koma bacci"da yamman nan Afrah... ta wani marairaice fuska tana kallon shi tace"dan Allah uncle ka bar ni nayi ko na 20mnt wlh na gaji sosai bana jin na ta6a wahala irin ta yau"ai bazan hana ki ba domin na fahimci yanda kike ji akan shi ne nace ki zo domin na miki tausa,,,,tace"ni kuma uncle bayan kayi min a d'azu"ai wannan soma ta6i ne don haka kwanta na miki tausa kiji dad'in bacci kafin ayi magrib, wai ma tukuna kunyi sallolin da ake bin ku?ai ba a biyo mu ko d'aya ba bcs a shagon wata balarabiya muka samu mukayi sallah,, ok to kwanta na miki tausar ya fad'i haka ne yayinda ya kwantar da ita sae duk taji kunya ganin yanda yake mata wani kallo ta rufe fuskar ta da tafukan hannayen ta tace" nidai uncle ka bar ni kawai naje nayi bacci na ai na gasa jiki na da ruwan zafi" ba dai dana fara ba, ya fad'i haka ne yayinda yake tausa mata qafafuwan ta har izuwa cinyoyinta . Afrah kuwa duk ta qara jin kunya har dai idan yaje kan conyoyin ta sae taji kamar wani salon yake mata hakan yasa taji dad'in tausar sosai wanda daga haka tayi bacci. Ganin tayi bacci farhan ya jaye mata hannunwan ta da ta rufe fuskar ta sannan ya juya mata kwanciyar ta sbd yana son ya tausa mata bayan ta,sae da ya jaye sumar da ta d'an rufe mata baya sannan yaci gaba da yi mata tausa a hankali, ita kuwa sae sauke ajiyar zuciya take.

Sae gab da magrib ta tashi daga bacci ta shiga miqa a hankali cike da jin dad'in d'an baccin da ta samu tayi inda a hankali take ziro en qafafun ta a kan gadon wanda yayi dai dai da fitowar farhan kan ya qaraso wani qamshi ya daki hancin ta kan wani body mist da yake shafawa a qirjin sa. saurin d'auke idon ta tayi sae kuma ta sake kallon qirjin sa da taga ba suma ko qwaya a d'aya qirjin very smooth akasin wani lokaci da take ganin qirjin dauke da suma luf, kauda fuskar ta tayi ta d'an 6ata fuska tace"ni uncle ka daina aske suman jikin ka yana min kyau"su6ul taji fitowar maganar kai tsaye ai kuwa duk taji mugun kunya tayi saurin tashi xata var d'akin yayi sâurin riqo hannuñ ta da qrfi har sae da ta fad'o masa kan qirji, ya d'ora hancin sa akan nata suna shaqar numfashin juna ya kalli yanda taqi yarda ta had'a ido da shi yace"meye abin kunya dan kin fad'i ra'ayin ki kan mijinki" Qoqarin jaye jikin ta take yace"sorry na daina,amma zan tambaye ki yanzun qirjin nawa bai yi kyau bane?komai kasa cewa tayi yayinda taqi yarda ta kalli qirjin sa kamar yanda ya buqata, sae body mist d'in da ke hannun shi ta kar6a tana kallo sbd qamshin sa yayi mata dad'i sosai, yace"kema kina so na shafa miki?sae a lokacin ta kalle shi tace"ina dai son ka saya min" ya kar6i turaren tare da d'ora hannunta akan qirjin sa yana yawo dashi sannan yace"zan saya miki amma sae kinji idan yayi miki dad'i a jikin ki,, kmr ya uncle?kamr haka , ya fad'i haka ne yayinda ya kai hannu kan qugun ta ya qara manna ta a jikin sa yana shafa mata shi kan cikin ta,da mamaki Afrah tayi saurin kallon shi domin kai tsaye taji hannun sa cikin towel d'in ta sae duk ta tsorace sbd shi kad'ai ne a jikin ta gashi hannun shi sae yawo yake kan cikin ta sae Allah Allah take kar ya wuce gun domin ta fara jin alamun haka ta yanda yake qara zuwa da yatsan shi sama yana wani salo kamar mai zana mata wani abu a jiki har dai da yakai kan tsakiyar mammanta wanda hakan yasa qirjin ta ya shiga up and down kan wani irin fad'uwar gaba da take ji kuma ta kasa yin komai sae kallon yanda hannun sa ke yawo take cike da tsoro da mamaki wanda cikin hikima taso ta qwaci kanta amma ta kasa sbd yanda ya matse ta sosai. Muryar ta na rawa tace"uncle meye haka kake min? qara rungume ta ma yayi ya fara zuwa da hannun shi qasan cikin ta, ai kuwa ba shiri ta ture shi daga jikinta ta shiga ja da baya kmr wacce taga zaki tafe, farhan kuwa sae qarasowa yake kusa da ita yana mata wani kallo d'auke da idanun shi da suka soma canza kala. A rikice ta kame jikin qofa sbd yzo gab da ita hakan yasa wasu hawaye masu zafi suka sauko a gurguje kan kumatun ta tace"na roqe ka uncle dan girman Allah kar ka ta6a ni"cak ya tsaya domin yana girmama sunan Allah" Nan ta samu ta fita a gurguje, farhan ya shiga kiran ta amma ina tuni ta kai d'akin su. Tana shiga ta saka key ta xube nan bakin qofar tana kuka mai ciwo . Amrah tazo a rude tana fad'in "lafiya me yake faruwa ne? Knocking dinda aka shiga yi ne yasa Afrah tayi saurin kallon qofar taja Amrah sukayi quryar d'aki"da mamaki Amrah tace"ke uncle ne ke knocking ba kowa ba. ba kiji muryar shi yana kiran ki ba?nasan shine amma don Allah kar ki bud'e masa....fizge hannun ta tayi tace"akan me! Allah ni bazan iya masa haka ba,bata jira me Afrah zata ce ba taje ta bud'e masa qofa sae dai tana bud'e qofar ta kauda idon ta sbd bata ta6a ganin shi d'aure da towel ba. Nan ta bashi hanya ya nufi gun Afrah wacce wannan karon bata yi tunanin guduwa ba sbd tasan idan ba hauka yayi ba bazai ce ya mata wani abu a gaban Amrah ba sae dai fatar ta d'aya kar Amrah ta fita ta bar su. Saurin noke hannun ta tayi da yake son riqowa ta maida su baya wacce still hawaye na sauka kan kumatun ta, yace"haba Afrah meye na kuka nifa mijinki ne ko kuwa don ban ta6a miki irin haka ba"please uncle ka daina cewa haka, ta yaya na kasance matar ka idan aure kake so ba sai kaje kayi ba"ba wani kin fa san cewa ni mijinki ne kawai dai ki gaya min idan sona ne ba kya yi! da farko yayi mata tsawa sae kuma ya sassauto muryar sa kmr zai yi kuka yace" pls Afrah ki gaya min kinji wlh bana so na takura ki" ni fa uncle ba wani aure da ke tsakanin mu,qarya zan miki ne Afrah? Baza ka min qarya ba uncle sae dai zan gaya maka gaskiya bana son ka a matsayin miji domin bana jin zan iya,sbd ina da wanda nake so nayi rayuwar aure dashi. Tamkar saukar guduma yaji maganar ta dirar masa a kunne yayinda komai nasa ya daina motsi domin har numfashin sa neman d'aukewa yake sae kallon Afrah yake wacce tun kafin ta furta maganar ta runtse idunun ta gam hawaye se wasan tsera suke akan kumatun ta.

*Billy giro😊Futha lurv* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:21PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [10/13/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*

*Futhalurv.WordPress.com*

*```🏅47🏅```* Tafukan hannayenta ta had'e ba tare da ta bud'e idanuwan ta ba. Tace"dan Allah uncle kayi haquri ka fita" Da qyar farhan yaga ya iya jan qafafun sa ya bar d'akin. Yana fita Afrah ta durqushe ta fashe da wani sabon kuka tace"am sorry uncle! Har sau uku tana fad'in haka. Sannan ta kalli Amrah wacce tun lokacin da Afrah ta furtawa farhan bata son shi a matsayin miji take mata kallon mamaki ba ko qyaftawa. Afrah tace"Amrah wlh qarya na yiwa uncle ni ina son shi a matsayin miji kuma bana jin zan iya rayuwa da wani d'a namiji face shi, amma kuma ina da wani buri da nake son cikawa wanda na fahimci auren nan yana son ya hana min cika burina, shiyasa nafi buqatar ya sauwaqe min in yaso idan na cika buri na sae na dawo ma auren. Cike da rashin fahimta Amrah ta qarasa gurin ta, tace"ni kuwa wane buri ne wannan da yafi aure muhimmanci a gurin ki? Ba wai yafi aure muhimanci bane,asali ma muhimancin auren yasa nake jin idan inada aure bani da lokacin komai,domin aure abu ne mai matuqar muhimanci a gurina da bana son had'a shi da da duk wani abu, kan hakan yasa nake son auren ya fita a kaina har sae na cika burina. Hm Afrah kenan wannan wane irin buri ne haka? Buri na shine na nemo wad'an da sukayi sanadiyar raba ni da mahaifiya ta tun ina jaririya na kuma nemo wad'an da suka raba ni da mahaifina tun ina er shekara biyu,wato en uwan mahaifina da kuma matar sa ta biyu. Nayi baqin ciki sosai a lokacin da uncle ya sanar da ni wannan labarin duk da cewa bani da wani wayo sosai amma tun a lokacin na qudur ta a raina sae na nemo su indai har ina raye haka suma muddin suna raye wlh bazan bar su ba sae nasa an musu hukunci dai dai da su. Iska mai zafi Amrah ta furzar kafin take cewa"Amma Afrah na tabbatar a labarin da uncle ya baki ba zai rasa sanr da ke cewa shima yayi bincike akai ba" Haka ne Amrah ya sanar da ni amma ni ban gamsu da binciken da akayi ba sbd ba a gano su ba sun gudu, daga haka kuma aka daina zancen neman su kinga haka da akayi yana iya qara bawa azzalumi damar yaci gaba da zalunci sa. Sae dai Dan Allah Amrah bana son kowa yasan dalilin da nake son aure na ya rabu da na uncle sbd ko kad'an bai so sanr dani labarin iyayena ba nice na matsa masa sbd yanda nake ji a school kowa na fad'in "daddy mommy" amma ni bani da su bare nayi zancen su, shiyasa na nemi naji meyasa ni banda su , wanda kan irin kukan da nake ina matsa masa da tambaya yasa ya sanar da ni. Sannan kuma ina so kimin wata alfarma guda d'aya wato ita ce,don Allah Amrah ki auri uncle"zumbur Amrah ta miqe tace"me kike cewa? Abinda kika ji dai shi na fad'a kan cewa ki auri uncle sbd na tabbatar idan na rabu da uncle ba zai zauna haka kawai ba zai yi aure sbd a yau yayi matuqar bani tausayi,domin na fahimci aure yake so,ni kuma ina baqincin uncle ya auri wata mace amma ke zan iya haqura ya aure ki sbd kusan nace tare muka taso mun san halin juna......ki dakata da zancen ki haka domin bazan ta6a amincewa da hakan ba, kuma ni ina da wanda nake so bana jin zan iya rabuwa da shi! Wane ne wannan wanda ban sani ba keda nasan ba kya kula kowa. Shiru Amrah tayi, Afrah tace "baza ki sanar da ni wane ne ba? Bazan iya sanar da ke ba..... Sbd me? sbd uncle Farhan ne ba kowa ba wanda na taso da son shi tun ina qarama kan yawan taimakon da yake kaiwa mahaifina a matsayin sa na lebaran uncle,sae gashi ya kasance mijinki hkan yasa dole bazan iya auren sa ba ko a mafarki kuwa,kuma koda shi kad'ai ya rage cikin maza bazan iya auren sa ba sae dai na mutu banyi aure ba kan na had'a kishi da ke. Duk maganar tana yin ta ne a cikin zuciya. Afrah tace"dake nake nace meyasa? sbd ko shi wanda nake so bai san ina yi ba ,shiyasa bana jin zan iya sanar da ke,,,ni bana ma buqatar naji wane ne tunda naji bai ma san kinayi ba duk da cewa banji dad'i ba domin nasan ba qaramar azaba keda hakan ba kana son mutum bai san kana yi ba,amma dan girman Allah Amrah ina son ki girmama sunan wanda na had'a ki da shi ki taimaka min ki janye son wanda bai san kinayi ba ki saka na uncle koda kad'an ne,ki kuma yarda cewa zaki aure shi,to wlh idan kika min haka bani da wata babbar masoyiya a duniyar nan face ke.....idan kuma naqi fa? Baza ki zamo maqiyiya ta ba amma wlh tamkar kin rugaza min tsarin rayuwa ta ne sbd idan uncle ya auri wata ba ke ba bana jin zan iya sake auren sa. Afrah ki ma daina kuka da durqusa min kina roqo na sbd a gaskiya ke ke shirin ruguza tsarin rayuwar ki muddin kika yarda auren uncle ya fita akan ki zai auri wata ce bani ba domin a gsky bazan aure shi ba don haka ki ma daina zancen rabuwar auren ku sbd ban fara mafarkin mun sami sa6ani da ke ba domin idan na auri uncle nasan yau da gobe sae Allah. Da mamaki Afrah tace"yanzu a yanda muke har kina tunanin don kin auri uncle zamu iya samun sa6ani.....hm bari kiji in gaya miki Afrah koda ace mu hanta da jini ne idan muka had'a miji d'aya dole watarana muyi fad'a sbd shi kishi abu ne da yakan rufe ido da kunne baji ba gani.....naji Amrah kuma na fahimci akan kar mu sami sa6ani ne yasa kike gudun auren uncle.....bashi kad'ai ba ne har da kunya ina ji ace duk amintar mu na aure miki miji....haba Amrah dan Allah ki daina d'auko wani banzan zance ni dai dan girman Allah nake roqon kimin alfarma idan kuma ba kya dubin girman Allah shike nan,,, Afrah rashin amincewa buqatar ki bashi zai sa ya zamo bana girmama Allah ba, amma kuma..... Sae tayi shiru tana wani nazari, bayan ta gama ta tayar da Afrah dake durqushe a gaban ta,ta share mata hawaye kafin take cewa"nima ina da wata alfarma wacce sae idan kin min ne zan yarda da taki,,, fad'i ina jinki,, Alfarmar ita ce ba wani abu bane face kije ki bawa uncle haquri kan abinda kika masa ki kuma snr dashi gsky kina son sa a mtsyn mji ,,meyasa Amrah?bazan baki amsa ba sae idan kinje kin dawo to kuwa duk kika dawo min da zancen na auri uncle zan amince na aure shi, nayi miki alqawari,, da gaske? Da gaske...na gode Amrah kar ki sake min godiya domin mun wuce yiwa junan mu godiya abin kunya ne ma don na miki abu kice kin gode sbd mun riga mun zama d'aya. Yanzu sae ki tashi muyi sallah sae kije ki bashi haquri.

Bayan sunyi sallah Afrah taje har d'akin farhan sae dai bata same shi ba,bata yi mamaki ba sbd tasan yana masallaci.

6angaren Amrah kuwa Afrah na fita ta fad'a ruf da ciki kan bed tana rusar kuka, sbd tsananin sonda take yiwa farhan wanda ko muryar sa taji sae taji wani abu kmr fad'uwar gaba,bare idan ta ganshi kai tsaye take jin bugun zuciyar ta ya canza, duk akan son shi amma bata jin zata iya amincewa buqatar Afrah duk da wani 6angaren zuciyar ta nace mata wata dama ce ta same ta a sauqaqe da zata mallaki abinda take matuqar so,amma haka ta dake tana hana zyr ta.

Tana cikin kuka ne taji shigowar Afrah cikin sauri ta share hawayen ta ba tare da Afrah ta lura ba. Tashi tayi zaune tace"ya akayi kika dawo da sauri haka? Baya nan yana masallaci kinsan sae bayan isha'i yake dawowa" Amrah tace"dama so nayi sae kinyi wanka kafin kije kinga dama ta samu sae kije kiyi wankan ko" Amrah shi bawa uncle haquri har sae nayi wanka? nidai kije kiyi indai har kina so na amince da buqatar ki, ba musu Afrah taje ta fad'a wanka wacce ta jima sosai kafin take fitowa.

Amrah ce ta shiga shirya ta da kanta duk d'akin ya qamsashe sbd turaren da ta mata wanka da shi. Ta kuma nemo wasu kayan bacci masu kyau ta bata ta saka sae dai kafin tasa sae da tace"Amrah nifa ban gane ba shirin bacci tun yanzu kuma kin wani shafe ni da turare"ai inace kinji ana sallar isha'i da kinyi sallar ba wani abu zakiyi ba face cin abinci sae shirin bacci kinga ai banyi sauri ba. Amrah dai bata ce mata komai ba domin ita to 9 take shirin baccin ta. Nan ta zuba hijabin ta har qasa domin tayi sallah.

Tana gama addu'a kenan taji shigowar farhan . Amrah tace"tashi kije gashi nan ya dawo. Da qyar Afrah ta iya miqewa ta cire hijabin jikin ta sae fad'uwar gaba take ji da tunanin yanda zata ba farhan haquri kan abinda ta masa da bata ji dad'in sa ba ko kad'an. Ta fara tafiya suku suku kamar wacce aka cirewa lakka hr ta kai bakin qofa ta tsaya tace"Amrah ina tsoro domin ji nake kmr wani abu zai faru da ni"name kenan Afrah keda zaki bawa uncle haquri me kike tunanin zai faru da ke?nima ban sani ba. To zo muje na raka ki ba abinda zai faru da ke sae alhairi.

Bakin qofa ta kai ta ta juyo.

Afrah ta shiga knocking a hankali cike da fargaba. Kanta a qasa koda farhan ya bud'e qofar yayinda ta shiga jin kamar ta nutse cikin qasa kan abinda ta masa wanda ta fahimci ya girgiza sosai sbd kallo d'aya zaka yi masa kasan yana cikin matsananciyar damuwa, domin in ma a kace mata yayi kuka bata musu sbd yanda taji muryar sa yana cewa"ya akayi ne Afrah?kasa ce masa komai tayi yace"shigo daga ciki idan magana gare ki" Bata musa masa ba ta shiga taje kan sofa ta zauna ta kame guri d'aya kmr wata munafukar baquwa.

Tayi kusan minti hud'u zaune tana tunanin kalmomin da zata had'a ta bashi haquri can tace"Dan Allah uncle kayi haquri da abinda na maka wlh fad'a kawai nayi ni bada gaske nake bana sonka ba, dan Allah kayi haquri kaji bazan sake ba"kallon ta kawai farhan keyi domin tun lokacin da ta furta cewa bata son sa a matsayin miji yaga sai da ta rufe ido kafin ta furta hakan,tun a wannan lokacin yasan cewa bada gaske take ba, sae dai tunanin sa me ya d'ebe ta ta furta masa hakan. Jin yayi shiru bai bata amsa ba ta sulale qasa ta fara masa kuka tana bashi haquri. Shi da kanshi ya tayar da ita ya shiga share mata hawaye kafin yake cewa"amma Afrah meyasa kika min haka, ko kuwa dan ina shafa jikin ki ne, ko kowa dan kinji hanuna a qasan cikin ki ne shi yasa kikayi tunanin zan kai hannu inda bai dace ba. Duk tamboyoyin nan da yayi mata guda uku tana girgiza masa kai amma sae ta qarshen tayi shiru taqi cewa komai ,yace "Afrah ba ina nufin na kai hannu na inda kike tunani ba domin nasan shiyasa kika ture ni daga jikin ki",,,yi haquri uncle wlh na tsorata ne sbd ba komai a jiki na sae towel kad'ai kasancewar na fito daga toilet kenan nazo d'akin ka. Ba komai Afrah ya wuce, kunci abinci ko kuwa? Aa ,to tashi kuje kici abinci sae Ki dawo kinji? Nan ta gyad'a mishi kai ta tashi ta fita.

Bata jima ba ta dawo take sanar da shi Amrah tace fresh milk kawai zata sha ta kwanta, yace"to kefa?nima bana jin zan ci wani abu sbd kasan ba mu jima da cin abinci ba...um um ke kam zaki ci wani abu ,meyasa uncle? Kawai dai nace zaki ci kuma banda musu, ai bazan maka ba,, sbd kina gudun na zane ki ba... ai nasan kana sona baza ka zane ni ba,ko baka sona... Aa qaunar ki dai nake,ya fadi haka ne yayinda ya lakato hancin ta yace "je ki debo abinci muci.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull