Afra ko amrah complete - Chapter 17
Afra ko amrah complete Chapter 17: Afra ko amrah complete Chapter 17. Sai da ya maimaita maganar sannan ya shiga nazarin ta lokaci mai tsawo. Nan ya sami…
4,360 words
Sai da ya maimaita maganar sannan ya shiga nazarin ta lokaci mai tsawo. Nan ya sami kansa da tashi ya nufi 6angaren gwaggo ba tare da ya dubi daren da ake ciki ba spare key d'in da ya riqo ya sa ya bud'e 6angaren, yayi turus cikin mamaki da fargabar ganin Afrah waje bakin qofar falo ta had'e kai da guiwa tana ta kuka ji yake kamar mafarki yake amma haka yaje gab da ita ya zauna inda a tsorace Afrah ta d'ago, tana ganin shine ta qanqame shi tana kuka tana fad'in "Dan Allah uncle ka amince na samu na fara binciken nan wlh kullum sae nayi mafarkin Abbana yazo yana ce min " na tashi naje gare su kafin suzo gare mu "haka yake ta fad'a kullum sae dai a yau cikin tsawa ya min maganar har sae da na firgita ,, ta qarasa maganar cikin muryar kuka mai ban tausayi ,,,,jikin sa ne yayi sanyi ya qara rungume ta tsam a qirjin sa yana shafa bayan ta cike da nazarin maganar da ta gaya masa.
*Billy giro 😊&Futha lurv 💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 10/18/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*
*Futhalurv.WordPress.com*
*```🏅53🏅```* Ya jima yana nazari akai , ya sauke numfashi a hankali,sannan ya d'ago Afrah yana share mata hawaye yace"daina kukan ya isa tashi muje 6angare na in yaso gobe da safe mayi magana. Ba musu ta tashi suka tafi sae dai kwata kwata ta kasa bacci sbd yanayin firgicin da ta shiga. Farhan ya shiga yi mata addu'a daga nan bacci ya fara fizgar ta sae kawai ta tashi firgigit da d'an kukan ta na shagwa6a, farhan ya kunna dim light kafin yace komai ta matso gab da shi ta shige jikin sa ta bud'e buttons d'in rigar sa ta 6oye fuskar ta a ciki, shidai farhan sae kallon ta yake yana shafa bayan ta,har ya zaci ta koma bacci se kawai yaga ta fitar da fuskar ta a hankali tace"uncle bacci nake ji amma bazan iya ba ina gudun kar Abba yazo min a mafarki"insaAllah ba zai zo ba kinji,yi baccin ki kawai , da qyar ya samu ta koma bacci daga nan shima ya samu yayi.
Da asuba sae da farhan ya raka ta toilet sannnan ta iya yin arwala.
Zaune suke sun gama sallah tana maqale a jikin sa tana kuka marar sauti . Farhan yace"Afrah me kika fahimta a maganar da Abba yake gaya miki? Uncle na fahimci so yake naje gare su kafin su zo gareni wata qil idan suka zo zasu cutar da ni ne "ba haka bane Afrah abinda na fahimta shine ba kya qiyamul laili domin ita qiyamul laili ba qaramin bakami bace dake hana duk wani maqiyi cin galaba akan ka da yardar ubangiji,haka ma yawaita yin zikiri wato ambaton Allah wanda na fahimci sam ba kya yinsa gashi kuwa manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace _"misalin wanda ya ke ambaton ubangijinsa da wanda baya ambaton ubangijin sa,kamar misalin rayayye da matacce ne. Haka kuma yace "Allah mad'aukakin sarki yana cewa"Ni ina tare da zaton bawana dani, kuma ina tare da shi idan ya ambace ni.Idan ya ambace ni a cikin ransa zan ambace shi a cikin raina, idan ya ambace ni a cikin jama'a zan ambace shi a cikin jama'ar da tafi su alheri,in ya kusance ni taki d'aya zan kusance shi kamu guda, in ya kusance ni kamu guda zan kusance shi tsawon gaba guda, in yazo min yana tafiya zan zo masa ina gaggawa_ To kuwa kinga idan kina yin zikiri Allah yana tare da ke a duk inda kike ,zai kuma kare ki da duk sharrin maqiya.
Haka kuma ki yawaita karatun qur'ani wannan nasan kina yin sa sosai don haka kici gaba ki kuma qara da yanda kike yi. yanzu ina ftr kin fahimci cewa ba dole sae kaje wa maqiyanka gaba da gaba ba Addu'a kad'ai ta ishe su domin ita ce takobin mumuni. To haka Abba yake nufi ki tashi ki daina bacci ki duqufa gurin Allah kina mai neman kariyar sa. Domin su maqiya ako yaushe cike suke da son ganin bayan ka amma idan ka riqe Allah ba abinda zasu iya maka wanda Allah bai ma ba.
Don haka daga yau kiyi qoqari ki kiyaye yin qiyamul laili da kuma zikiri ,da kuma neman kariya a gurin ubangiji,to inshaAllah idan har hakan Abba ke nufi baza ki qara ganin sa a cikin mafarkin ki ba.
Ajiyar zuciya ta sauke ta qara rungume shi cike da fahimtar abinda ya sanar da ita tace"inshaAllah uncle zan kiyaye "to Allah ya bamu ikon kiyaye wa,Amin. Nan ya d'auke ta suka koma kan gado sae shafa ta yake a hankali kmr yana shafa qwai tana jin shafar tasan cewa ga yanayin da yake son kasancewa ciki ba wai don tayi bacci yake mata hakan ba, haka ta lafe tana sauraren duk abinda yake mata,har yakai inda bata jin zata iya jurewa wato nipples d'in ta da yake muzarwa cikin wani salo da qwarewa yayinda take jin wani abu na ratsawa tun daga kan qwaqwalwar ta har zuwa babban yatsan ta na qafa ,daga nan ne ta qara shigewa jikin sa tana mayar masa da martani har suka lula duniyar ma'aurata sae dai iya wahala tasha domin har kuka sae da ta masa fiye da wanda tayi masa na farko sbd wannan karon buqatuwar da yake ciki bata bar ya tausaya mata ba domin har second round sae da yayi.
Lallashin ta yake tayi har ya samu ta daina kukan ya kuma samu bacci mai nauyi ya d'auke ta nan shima yabi bayan ta hakan yasa d'akin yayi tsit baka jin komai sae ajiyar zuciyoyinsu.
Sae guraren qarfe goma suka tashi ,Afrah ta tashi tana son taje toilet farhan sae kallon yanda take taka qafar ta da qyar yake sae duk yaji wani abu ba dad'i had'e da mutuwar jiki,ya tashi da hanzari ya qarasa gurin ta ya rungumo ta yana fad'in"Afrah ashe naji maki ciwo? Cikin muryar kuka tace"ai na gaya ma amma kaqi ka saurare ni,in kana min haka gaskiya gurin gwaggo zan riqa bacci na,,, yi haquri muje na duba ki idan ba sosai bane,um um nikam bazan iya bari ka duba ni ba kawai ka bani magani nasha,,, to muje ayi wanka tukun .
A tare suka yi wanka har suna cud'anya jikin juna da qarshe ya nemi ya gasa mata jikin ta sae dai yana tsunbula ta a cikin ruwan zafi ta tuma ta d'ale kan jikin sa tana kuka akan dole ya fasa mata gashin.
Kamar mai koyon tata yaje da ita 6angaren gwaggo Afrah taje a hankali jikin gwaggo tana mata ina kwana, bata iya kar6awa ba sae farhan ta shiga yiwa tambaya wata kan wata na ganin yanda Afrah ke takawa da qyar,sosai yaji kunya har yana sosa bayan kansa yace"gwaggo wlh ba da qarfi na mata ba ,,,haba farhan kai fa likita ne ya zaka mata haka bayan kasan Afrah qarama ce kuma kasan yanayin jikin ta,kuma alamu sun nuna wannan shine na farko,shiru yayi yaqi yace bana farko bane domin yasan fad'a zai sha sosai idan taji bashi ne na farko ba amma ya mata hakan,haquri kawai yayi ta bata har kuma ya bata tausayi domin tasan Farhan mai tausayin Afrah ne sosai. Tace"to inace ka gasa mata jikin ta ko?gwaggo kuka take bata bari, oh ni na rasa me ruwan zafi suka yi ma Afrah da ta tsani shigar su sae kace tare suke da mutuwar ta ,to nikam bazan bar ki haka ba sae kin shiga ruwan zafi, cike da son tayi kuka ta kalli gwaggo tace"gwaggo uncle ya bani magani, gwaggo kam bata saurara mata ba taja ta sae toilet .
Duk wani kuka da ihun da take da kuma yanda take ta faman kiran shi, farhan naji amma haka ya dake nan gurin da suka barshi zaune ko motsin kirki baya yi sbd abinda yake ji game da kukan da take.
Sae da aka gama gwaggo ta bar ta ta fito tazo gun farhan ta zauna tana kallon idonsa da suka cika tap da qwallah kmr nata . Kauda idon sa yayi ya jawo ta ya rungume Yace"to ya isa haka tunda an gama.
Bayan kwana biyu da faruwar hakan. Cikin ikon Allah Afrah bata sake mafarkin Abbanta ba sbd kwana biyun nan tana qiyamul laili tana kuma yin zikiri sosai haka kuma takan yi karatun qur'ani ko wace sallah idan ta gama yayinda ta duqufa da roqon Allah ya kare ta da sharrin duk wani mai sharri mutum da Aljan.
Amma kuma suku suku take yin komai sbd wani tunani da tasa a ranta.
Zaune take kan bed ta had'e kai da guiwa cike da tunanin da tasa a ranta har tana fitar da en silalin hawaye . Farhan ya fito daga gurin wanka ya same ta a haka ya zauna kan bedside drawer tare da dafa kanta yace"my Afrah wai tunanin me kike yi a kwanakin nan? A shagwa6e ta d'ago tana kallon shi tace"uncle wani abu nake so"mene ne? Ni bana son na gaya maka kace a'a,,, fad'i kawai ina jinki.
*Billy giro😊&Futha lurv💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [10/18, 9:50 PM] Billy giro 😊 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```~AFRAH KO AMRAH ```*~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*NA Billy giro 😊& Bilqis Sidibe💅🏻*
*Futhalurv.WordPress.com*
*🏅54🏅* Wayar sa ce tayi qara koda ya duba Abban Amrah ne da kulawa yace "pls Afrah yi haquri na d'aga wayar kinji , gyad'a masa kai tayi tare da jinginawa a jikin sa, yanayin yanda yake waya cikin damuwa yasa ta d'ago tana kallon shi miqar da ita yayi tsaye suka je jikin wardrobe ya zaro riga ya bata ta saka mishi sannan ya d'auko wando dai dai ya qarasa waya ya saka wandon yace"yi haquri Afrah har na dawo sae muyi magana, Abban Amrah ne ya kira ni Amrah ba lafiya unconsciously har anyi addmitng din su a asibiti. Dan Allah uncle ina zuwa.... Aa Afrah...sae kuma yayi shiru tuna cewa ta had'a shi da Allah amma yaso ya fara zuwa shi kad'ai tukun . Yace "shikenan d'auko hjb d'inki muje.
Koda suka je asibiti likitawa ne kan Amrah zasu yi su biyar suna qoqarin ganin sun ceto ranta, Farhan ya cike na shidan su wanda kafin ya shiga sae da ya bawa Afrah makullin office d'in shi yace taje ta zauna kafin su fito.
An kwashi kusan awanni kafin ake ciyo nasara sae dai hana kowa shiga akayi sbd patient d'in ta wahala sosai shiyasa aka yi mata allurar bacci.
Iya kuka Abbanta yayi domin ya firgita sosai da yanda yaga ciwon yazo mata karaf d'aya.
Su Farhan na fitowa ya tafi sauri sauri office d'in sa ya sami Afrah sae bacci take rufe qofar sa ne ya farkar da ita. Bai zauna ba sae da ya bud'e fridge ya d'auko mata fresh milk ya tsiyaye mata a cup ya bata , bata sha ba sae da taje toilet ta wanko bakin ta, tace "uncle ina son zanga Afrah tukun" Amrah bacci take sae anjima ko za a bada damar shiga a ganta "to uncle me yake damun ta ne? ciwon zuciya ne......ciwon zuciya uncle, kallon yanda ta fitar da hawaye kai tsaye yake kmr wacce tasan abinda ya haifar da hakan yace" ko kin san me yake damun ta ne? ni ban sani ba amma dai Abban ta bai sanar maka ba? Shi kansa bai sani ba amma ba makawa ta jima tana sa wani abu a ranta tana kuma yawan tunanin koma mene har ta kai ga ya haifar mata da ciwon zuciya , to uncle ya kenan? Ba yanda zamuyi sae idan ta farka aji mene ke damun ta idan da yanda za'ayi sae a mata wannan abun domin tunanin abun yaci mata zuciya sosai wanda ci gaba da tunanin sa tamkar tana kusanto lokacin mutuwar ta ne , duk da cewa rai a hannun Allah yake amma akwai sanadi, kuka ta fara yi cike da tausayin Amrah tace "uncle kenan idan bata sami abinda take so ba zata iya mutuwa ? zai dai zama sanadi mutuwa kuwa sae Allah yace,shiru tayi inda ta dai fahimci rashin samun abinda Amrah ke so zai iya zama sanadin mutuwar ta. Hakan yasa taci gaba da rera kukan ta kamar wacce aka ce yau yau d'in nan Amrah zata mutu, bai hana ta kukan ba domin cike yake ta tausayin Amrah da kuma mahaifin ta wato lebaran sa.
Bata ma iya shan fresh milk ba suka koma gida a cewar zasu koma anjima sae dai har suka isa gida Afrah kuka take. Gwaggo keta rarrashin ta tana bata baki tana fad'in ta daina kukan mana kar taja ma kanta ciwon kai tace "gwaggo ki bar ni nayi kuka domin wlh ni kad'ai nasan yanda nake jin Amrah a cikin raina" duk yanda kike jinta a cikin ranki ai ba kuka zakiyi mata ba addu'a ya kamata , domin kuka baya magani, nan tayi ta rarrshin ta har ta samu ta daina kukan Da dare bayan sun koma sun samu Amrah ta tashi daga bacci sae dai kallo d'aya zaka yi mata kasan tana jin jiki sosai domin ko magana bata cika son yi ba sae dole take yi . Kuma ba irin tamvayar da likitawa basu yi mata ba kan me ta sa a rai da yawa har yake neman illata ta amma ta nuna sam ba abinda ke damun ta ciwo ne kawai, likitawa basu yarda da hakan ba sbd sun san dole akwai abinda tasa a ranta yaja mata wannan ciwon amma ba su takura ta da tambaya ba sae mahaifin ta suka snr cewa ya lalla6a ta ko zata snr da shi.
Afrah ce kad'ai da Amrah a dakin, su gwaggo da farhan duk sun fita dama kuwa haka Afrah taso domin tana son tayi wa Amrah wasu tambayoyi. Kallon Amrah tayi wacce tun shigowar su tana kwance bata ko iya wani motsin kirki. Matsawa tayi kusa da ita tare da riqo hannun ta tana qara yi mata sannu kafin take cewa"Dan Allah Amrah me yake damun ki ne da kika qi sanar da kowa hatta Abba da ya tambayeki naji kince da shi ba abinda ke damun ki,bayan nasan ba gaskiya bane wanda ina fatar zaki sanar dani domin nasan idan kin 6oye ma kowa ni baza ki 6oye min ba sbd mu abokanan shawara ne wata qil idan kika snr dani zan iya shawo kan abinda ke damun ki. Shiru Amrah tayi tana kallon ta cike da qwalla a idon ta domin bata jin zata iya sanar da Afrah cewa tunanin farhan ne da take ba dare ba rana da kuma ywan kukan da take akan tsananin son shi dake azazzalar ta mnt by mnt. Afrah tace"ina jinki Amrah ki sanar da ni kinji,kauda kanta tayi tana faman danne hawayen da ke qoqarin zubo mata amma duk da haka sae da suka fito tayi saurin sa hannu ta share hawayen,ta qara jimqe hannayen su da ke riqe da juna tace"ba komai Afrah......saurin rufe mata baki Afrah tayi tace"kinsan ba ma haka dake sanin kanki ne ba ma 6oye ma junan mu komai don haka ki cire ba komai a cikin bakin ki,ki sanar dani komai,hawaye ne suka sake cika ma Amrah ido har suna qoqarin zubowa tace aranta _"kiyi haquri Afrah duk da na d'auke ki tamkar er uwa ta jini bana jin zan iya sanr da ke abinda ke damuna,domin abu ne dani kad'ai nake son barwa kaina har na koma ga mahlicci na"_ Afrah dake kallon ta take taji ita ma nata idanun sun ciko tace a ranta _"lokaci mai tsawo na fahimci abinda ke damun ki amma na dake akan ban sani ba,sbd son da nake yiwa uncle so ne dani kad'ai nake son zama mallakin sa yayinda nake jin ni kad'ai na dace dashi,but jin da nake miki tamkar er uwa shi yasa na fara jin bazan iya barin ki cikin damuwa ba wanda don haka ne yasa nace ki aure shi ba wai don binciken da nayi niyya ba sae gashi kmr kar wani abu ya shiga tsakani na da uncle naji na qara son sa wanda duk matsa ma san da nake kan ya amince ya aure ki ina jurewa ne kawai but still inshaAllah sae naga cewa kin sami abinda kike so dmn jin da nake miki tmkr er uwa bazai bar na iya ganin mutuwar ki ba kan abinda nasan zan iya taimaka miki ki mallake shi_.
Daga haka suka rungume juna sae kuka suke ba wai don d'aya taji abinda d'aya ta fad'a ba.
*Billy giro😊&Futha lurv💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [18/10/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```~AFRAH KO AMRAH ```*~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*NA Billy giro 😊& Bilqis Sidibe💅🏻*
*Futhalurv.WordPress.com*
*🏅55🏅* Haka suka ci kukan su kmr wad'an da akayi ma mutuwa sai da suka gaji don kan su suka daina.
Sae guraren tara da rabi suka bar asibitin. Farhan da gwaggo duk sun fahimci yanda Afrah jikin ta yayi sanyi ko magana bata cika son yi ba wanda duk a tunanin su rashin lafiyar Amrah ne ya sa ta hakan , eh haka ne amma ta had'a da tunanin yanda zata tunkari Farhan da zancen ya amince ya auri Amrah ba tare da ta sanar da shi cewa Amrah na son shi ba kan wani dalili nata .
Bayan sun isa gida sukayi wanka sannan sukayi shirin bacci, Farhan ya kalli Afrah wacce har yanxu akwai damuwa a tare da ita cikin muryar lallashi yace "Afrah nasan dole ki damu sosai akan ciwon Amrah sbd na fahimci kina jin ta ne kmr sistar ki ta jini wanda ba komai ya kawo hakan ba face yanda kuka taso tare tun kuna yara, kuma kukayi matuqar shaquwar da kesa idan d'ayan ku ya shiga wani hali dole d'ayan ya shiga,amma ina son kiyi haquri ki rage wannan damuwar ki mata addu'ar samun sauqi domin ita ce mafita .
Marairai ce fuska tayi cike da qwallah tap a idon ta tana kallon shi tace "uncle pls zan roqe ka wata alfarma wacce bana son sautin a'a ya fito a bakin ka na fiso kawai kace min ka amince pls and pls uncle" Ina jinki Afrah gaya min indai har bai fi qarfina ba InshaAllah zan miki amma kuma ya kasance ba sa6on Allah bane domin kinsan babu d'a a ga abokin halitta a gurin sa6awa mahalicci. Uncle ko kad'an ba sa6o a cikin abinda nake son kamin, to fad'i ina jinki, inda inda ta shiga yi ganin yanda ya tsure ta da kallo ta samu da qyar ta fara da cewa "dama ba komai bane uncle maganar dai da ka sani ce ta xancen auren Amrah da nake son kayi" qyar yake kallon ta har ta gama zancen, yayi d'an gutun tsaki had'e da girgiza kansa yace "akan wannan maganar ne kika sa na 6ata lokacina na saurare ki" Hawaye ne suka silalo a hankali kan kumatun ta, da kulawa Farhan ya riqo kumatun ta yana kallon cikin idon ta yace "Afrah kuka kike yi bayan kinsan baki da gaskiya a cikin zancen nan ina ce dalilin da yasa kike son na aure ta yanxu babu shi an wuce gun, ryt? gyad'a masa kai tayi sbd yanda ya tsure ta da ido yana son yaji amsa tace "amma uncle.....rufe mata baki yayi ya kwantar da ita tare da ja musu blanket yana fad'in "har yanzu baki san lokacin da zaki fara rigimar ki ba muyi bacci haka ya isa, duk yana maganar ne rungume da ita yana share mata hawaye yace " idan kuma so kike zuciya ta ta fashe sae kiyi ta kukan. Akan dole tayi shiru ya kashe dim light suka shiga bacci .
Washe gari bata yi masa zancen ba har suka je asibiti koda suka je ciwon Amrah ya tashi sosai da qyar aka shawo kai, ba Abban ta kad'ai ba har likitawa sun fara sarewa da yanda ciwon keyi mata wanda har suna tunanin idan ya sake motsawa sae dai wata ba ita ba amma basu sanar da Abban ta haka ba domin so suke suyi iya qoqarin su na ganin hakan bai faru ba.
Kuka Afrah keyi sosai duk tabi ta katse har bata iya tsayuwa da qafafun ta sbd duk wanda ya kalli Amrah baya tunanin zata qara scnd a duniya. Amma cikin ikon Allah har ta iya kama hannun Afrah ta zaunar ta samu da qyar ta bud'e baki tace "Afrah ki daina min kuka addu'a nake so kimin Allah ya yaye min abinda yasa nake fama da wannan ciwon idan kuma na mutu shikenan Alhmdlh domin ina ganin kmr za tafi zama hutu a gare ni .... Hava Amrah dan Allah ki daina zancen mutuwa zaki tashi InshaAllah har ma ki sami abinda kike so.......da kmr wuya Afrah shiyasa nafi son na mutu kan na rayu domin kamar zanfi wahala wahalar da ban san lokacin da zata yaye min ba. Kuka ne yazo ma Afrah sosai ta tashi ta fad'a jikin Farhan dake tsaye akan su tace "uncle kaga Amrah ko ce ta daina gaya min haka wlh bana son tana fad'in zata mutu, ta qarashe mgnr cikin kuka sosai , Farhan ya kalli Amrah wacce kejin kmr zuciyarta ta fito ta had'e da ta farhan su zamo guri d'aya ko xata ji sassaucin abinda take ji, yace" Amrah ki daina zancen mutuwa kinji ai ciwo ba shine mutuwa ba domin sau nawa zaki ji an kwanta da mutum lafiyar sa qalau amma a wayi gari ba tare da shi ba amma sae a wayi gari da marar lafiyan da yayi nisa nisan da ba a ta6a tunanin xa a wayi gari da shi sbd lokacin sa bai yi ba domin ita rayuwa sae idan lokacin ka yayi ne ake zare ta. Hawaye ne suka cika mata ido har ma bata ganin shi sosai tace "na gode uncle zan kiyaye" Ya kalli Afrah wacce har yanxu ke kuka tace "uncle dan Allah ina so muje gida" meyasa Afrah ? Baza mu jima ba zamu dawo. Ba musu sukayi sallama da Abban Amrah suka kama hanya. Suna zuwa gida suka sami gwaggo har ta rufe 6angaren ta zata fito tace "A'a lafiya kuka dawo gashi sai sauri nake har na kammala abinda nake zan ja tawa motor na tafi" Afrah ce ta nemi mu dawo ban san me yasa ba, to ga makullin sae ku shiga domin ya kamata naje na qara ganin ya jikin nata yayi,, Afrah tace "gwaggo dan Allah magana nake son zamuyi mu duka.
Bayan sun shiga sun zauna Farhan da gwaggo sae sauraren Afrah suke suji maganar da zata sanar da su wanda kafin ta fara sae addu'ar samun nasara take sannan tace "uncle, gwaggo , zan so kuyi haquri da maganar da zanyi zan kuma so kuyi haquri ku amince da buqata ta kuma kuyi haquri da yawan naci na domin magana ce wacce kuka santa wato mgnr ita ce, " ina son uncle yayi haquri ya janye ra'ayin sa na zama dani kad'ai a matsayin matar sa zan so ya taimaka min ya had'amu mu biyu wato nida Amrah wanda ina son haka ne a bisa wani dalili ba don wancan dallin farko ba amma don Allah kar a tambaye ni wane irin dalili ne . Farhan yace "Afrah kin fiye naci , kin fiye naci sosai wanda na kasa fahimta shin so na ne ba kya yi da har ba kya jin komai idan kina amvatar na auri wata keda kanki,kuma haka kawai zan auri Amrah bayan naji ta sanar da ke tana da wanda take so,kuma me ya kawo zancen nan a cikin wannan yanayi da Amrah ke fama da rashin lafiya ? Kayi haquri uncle rashin lafiyar ce tasa na damu sosai akan ka aure ta....sbd me? Shiru tayi tana tunanin a yanda ta fahimci Amrah sam bata son a san tana son uncle tunda har ta iya ciwo kmr ta mutu amma taqi fad'a, hakan yasa ita ma zata ajiye mata sirrin baza ta sanar da kowa ba.....dake nake ki gaya min meyasa? Sbd ina ganin kmr kad'ai ci ne ke sata yawan tunani har ta kai ga ciwon zuciya, kad'ai ci? Eh uncle kasan cewa Amrah ita kad'ai ce gun Abban ta Kuma ba ya tare da mahaifiyar ta sannan kuma bai yi wani auren ba gashi tun safe idan ya fita aiki sae dare yake komawa, shiyasa nake son ka aure ta ta dawo cikin mu da zama ko zata ji sauqin kad'ai cin da take ciki,babu wata hujja a cikin zancen ki... Niko nake da hujja uncle sbd wanda tace tana so bai ma san tana yi ba bare a tuntun6e shi da zancen aure Kuma idan yaji ita ke son shi ba zai riqe ta da wata daraja ba amma nasan kai zaka iya tausaya mata ko don Abban ta, don girman Allah uncle kar ka ce a'a ina son ayi ayi auren nan ne tun kafin ciwon ya illata ta don Allah uncle kaji. Nan ta shiga kuka tana roqon sa tana Kuma had'a shi da sunayen ubangiji kala kala sae duk ya rasa ma me zai ce mata domin ji yayi kmr ta d'aure shi tamau da sunayen ubangiin da ta had'a shi, sae dai qwarai yayi baqin ciki na ganin kwata kwata Afrah bata kishin sa. Ke kuwa Afrah..... A'a gwaggo barta kawai na amince zanyi auren! kuma a cikin kwanakin nan wata qil Amrahn ma zata fi sona domin na fahimci sam ba sona a tare da Afrah bare har ta iya kishina! Nan ya fita cikin 6acin rai. Haka ita ma gwaggo ta tashi tare da jefo mata keys tace idan kin tashi ki rufe min 6angare na, ya zamo ita kad'ai suka bari sae kuka take mai cin rai ta rasa inda zata sa kanta taji sanyi tasan har ga Allah tana matuqar son uncle kuma tana kishin sa, haka kuma tana matuqar son Amrah bata iya barin ta cikin damuwa ko don kasancewar su aminan juna tun suna yara. Sae da taci kukan ta har ta gode Allah sannan ta tashi ta rufe 6angaren gwaggo ta fita ta nemi napep taje asibiti.