Afra ko amrah complete - Chapter 18
Afra ko amrah complete Chapter 18: Afra ko amrah complete Chapter 18. Amenity ward ta nufa ta shiga room number 2 wato d'akin da Amrah take Tana shiga ta…
4,446 words
Amenity ward ta nufa ta shiga room number 2 wato d'akin da Amrah take Tana shiga ta sami gwaggo sai dai ko zama bata yi ba gwaggo ta bar d'akin kallon gwaggo take har ta fita sannan ta d'an qirqiro murmushin dole ta zauna tana mai kallon Amrah ta d'an qara sake fuskar ta kafin take cewa "Amrah InshaAllah a cikin kwanakin nan za'ayi auren ki da uncle,..... Zumbur Amrah takai zaune wacce tunda aka kawo ta asibiti bata ta6a tashi ba sae yanxu, bata san lokacin da tace" da gaske? Da gaske nake Amrah,,, amma meyasa, bayan yanxu ba wani zancen binciken da zakiyi? Haka kawai nake son mu auri miji d'aya nida ke sbd amintakar mu ta qara qulluwa. Wani irin farin ciki Amrah taji kamar wacce akayi wa bushara da gidan Aljannah har ma ta nemi ciwon da ke jikin ta ta rasa,sae kuma nan take taji farin cikin ya ragu har tana magana a ranta cewa _"meyasa zanyi farin ciki don xan auri mijin aminiya ta wacce a duk duniya bani da kamar ta“_
Kamar Afrah taji me take fad'a tace " kar ki ta6a tunanin don kin auri uncle kinyi abin kunya ga auren mijin aminiyarki, ko d'aya babu kunya a ciki domin ni na buqaci hakan ba snatching kika min ba,don haka don Allah daga yau ki cire a ranki cewa kinyi rashin kyautatawa kuma ki daina tunanin zamu iya samun sa6ani don kin auri uncle kisa a ranki cewa wata shaquwa ce zata qara qulluwa a tsakanin mu. Komai Amrah ta kasa cewa sae hawaye da suka silalo a hankali kan kumatun ta. Nan suka ji sallamar Farhan wanda sau d'aya ya had'a ido da Afrah ya kauda kai, hawayen da ke qoqarin zubo mata ne yasa tayi saurin tashi ta bar musu d'akin. Farhan ya nemi guri ya zauna wanda sae da yayi gyaran murya kafin yake cewa "nasan Afrah ta sanar da ke abinda ake ciki,sae dai nasan zaki ji zancen wani iri sbd tun a Oman naji kina sanar da ita baza ki amince ba amma ina so kiyi haquri wannan karon ki amince sbd na samu ta daina damuna akan zancen auren nan,duk da cewa nasan kina da wanda kike so, haka kuma baza ki so ki auri wanda ba kya so ba,idanun ta ne suka ciko da qwallah yaci gaba da cewa,sbd shi so wani abu ne wanda in baka yiwa mutum shi baza ka ji dad'in rayuwar aure da shi ba shiyasa nake son wannan auren ya zamo na wata biyu ne kacal tsakina na dake ba tare da Afrah ta san da hakan ba, sannan ba wani abunda zai shiga tsakanin mu na auratayya sbd na yarda da yin auren ne a bisa sanin halin Afrah kan idan taso abu hankalin ta baya ta6a kwanciya har sae an mata,haka kema nasan baza kiso wani abu ya shiga tsakanin mu ba. Sosai nake guje mata wannan auren ba don komai ba sae don sanin irin halin kishin ku na mata wanda komai amintakar ku da mutum idan kuka had'a miji d'aya sae kun sami sa6ani har ma kuzo Kuna nuna qiyayya wa junan ku,gashi sam bana fatar amintakar ku da Afrah ta koma qiyayya, amma nasan kona snr da ita hakan baza ta gane ba sae idan anyi auren ko zata fahimta. Then kar ki samu damuwa domin auren za a yi shi ne a asirce ba wanda zai sani sae waliyan mu kad'ai wanda koda mun rabu ba mai tunanin cewa ke bazawara ce. Amma don Allah Amrah idan har da takurawa a cikin al'amarin nan ki sanar dani. Hawayen da suka cika mata ido ne suka gangaro kan kumatun ta tace a ranta _" ba abinda zance sae godiya ga ubangiji na da yasa zanyi rayuwa da kai har ta tsawon wata biyu a matsayin miji da mata,koda kuwa ba abinda zai shiga tsakani na da kai bani da wani sauran baqin ciki a duniya, fatana d'aya Allah yasa har na gama wata na biyu ban kawo sa6ani a tsakanin ku ba_.
*Billy giro 😊&Futha lurv 💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [20/10/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```~AFRAH KO AMRAH ```*~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*NA Billy giro 😊& Bilqis Sidibe💅🏻*
*Futhalurv.WordPress.com*
*🏅57🏅* Tana zuwa d'aki ta fad'a ruf da ciki tana kuka tana kuma mamakin halin d'a namiji, ita fa ta nemi ayi auren don taimakon aminyarta har yana zillewa baya so amma shine ana yin auren ya wani zaqe har yana nuna wani abu ya shiga tsakanin su a gaban ta "lallai ma uncle " shine abinda ta fad'a yayinda take share hawayenta wasu na sake fitowa . Shigowa yayi d'akin tayi saurin share hawayen ba tare da ya lura ba, yazo gab da ita tayi saurin matsawa sbd qamshin turaren da taji a jikin Amrah, shi taji yanayi, nan take taji ya qara bata haushi. Kwanciya yayi kan gadon da take zaune yace "waih Alhmdlh ashe dai mata biyu ni'ima ne ban sani ba sae a daren jiya"ya jawota jikin sa yana wasa da tsorayen kalbar da ke saman kanta yana ci gaba da cewa," sae yanxu naga ashe ba qaramin taimaka min kika yi ba da kika sani nayi auren nan,kinga duk byn kwana biyu se mutum ya riqa canji idan yau nasha kankana gobe sai naci Apple domin kinsan shi yanayin rayuwa komai idan ana yin canji yafi,ryt haka ne ? Wani irin abu take ji kmr ta cije la66ansa dake maganar sae dai bata nuna masa komai ba se ma murmurshi ta qirqiro tace "ai shine nake son ka fahmta uncle kaqi ka gane sae yanxu wanda naji da d'in hakan sosai daka fara fahimta" ransa ne ya d'an 6aci sbd ya xaci taji haushin maganar da yayi, amma yaga akasin haka sae dai zai ci gaba da yi mata irin hakan dole yau da gobe ta fara kishin sa har taji haushin auren da tasa yayi. Haka ya raya a ransa. Sannan shima yayi murmushi yana miqa yace "waih kina da maganin ciwon jiki? da kulawa ta kalle shi ta fahimci gayya ce tace "eyyah uncle sannu bari na maka tausa domin kmr maganin zai yi wuya" A hankali ta yunqura zata fara masa tausa sae qoqarin danne xuciyar ta take, yaje gun wata amma ita ce da tausa , ya dakatar da ita da cewa"barshi kawai zan nemi magani domin tausa baza ta min magani ba"yana gama fad'ar haka ya fita cike da tunanin abubuwan da zai riqa yiwa Afrah wad'an da zasu sanya ta kishin sa har ta nemi rabuwar auren da kanta kafin wata biyun da ya d'iba suyi sbd shi ko kad'an baya ra'ayin mata biyu.
Yana fita Afrah ta rufe qofar da key ta hau wani sabon kuka sae kace mutuwa aka mata. ** ** ** Leesa ce zaune da mom Farida suna cin abinci kan dining leesa ta ajiye spoon ta d'auki lemu ta kur6a tayi sassanyar ajiyar zuciya kafin take cewa " mom Farida lokaci ya kusa da zan tura en fashi a gidan Farhan su kwashe duk wata dukiyar dake cikin gidan tun daga kan 6angaren gwaggo har 6angaren sa, takardun kadarorin sa,keys d'in motors, gold, diamond, ke duk dai wani abu da kika san dukiya ne, indai akwai shi a gidan baza'a bar masa ba,har ma phone d'in hannun sa bana son su barshi da ita domin ita ma kud'i ce After that sea kuma nasa a kore shi daga gurin aikin shi......ke kuwa tayaya zaki iya sa a kori Farhan a gurin aikin sa?Abu mai sauqi wai cire wando aka, zan sa ayi kisan kai ne a cikin office d'in sa na kuma san yanda zanyi a laqa masa wannan kisan, ba kuma kowa zansa a kashe ba sae na nemo mafi kusanci dashi a office wanda ko yaushe yana cikin yi masa hidima,na masa zafi biyu kenan domin wlh tuggun da zan qulla a wannan kisan ba mai iya fitar da Farhan sae ni dana qulla, kinga kuwa har abada ba zai ta6a fita ba.
kuyi haquri da wannan.
*Billy giro 😊&Futha lurv 💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```~AFRAH KO AMRAH ```*~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*NA Billy giro 😊& Bilqis Sidibe💅🏻*
*Futhalurv.WordPress.com*
*🏅58🏅* Bayan kwana d'aya da faruwar hakan Afrah ce a kitchen tana girka abincin yamma duk tabi ta yanyanke hannun ta sbd har yanxu bata wani gwane sosai a girki ba son jiki tasa a koyon abincin sbd a Oman maman Amir na koyar dasu duk suka je 6angaren ta. sae dai sauqin ta d'aya abincin na dad'i amma sae ta wahala sosai kafin take samu ta kammala. Kmr tayi kuka taga ta kammala abincin sae ga Farhan ya shigo kitchen d'in yace "ina ce ke kad'ai kika girka abincin bada mu ba? Meyasa uncle? to me amarya zai zauna ne basu je yawon shaqatawa ba ai sae zaman gidan ya fara isar ta,gashi ni kuwa bana son aminiyar taki ta fara jin haka har dai yanda na fahimci kina matuqar sonta shiyasa nake son faranta mata sbd kema kiyi farin ciki,ryt?ya fad'i haka ne yayinda ya rungumota ta baya ya riqo hannuwan ta yana wasa dasu ta samu da qyar ta danne kukan da take ji na takaici tace "yanxu uncle har abinci kunci a can? Qwarai kuwa duk wani abin marmari da kika sani sae da muka ci shiyasa cikin mu yayi tap.....kash at all na manta fa mu d'an riqo miki wani abu but kar ki damu zan bawa mai gadi ya sayo miki, bai tsaya jin me zata ce ba ya fita sae dariya yake a ransa sbd ba wani gun suka je ba face asibiti domin qara duba lafiyar Amrah idan zuciyarta tayi sauqi ba sae anyi aiki ba sbd sunyi tunanin yi mata aiki kafin ciwon ya sake tasowa sae suka ga ta fara jin sauqi shine suka sallame ta acewar bayan kwana biyu ta dawo. To shine fa suna dawowa suka je 6angaren gwaggo ya samu tana yanka kayan marmari yayi zaune yasha son ransa ya bar Amrah tana taya gwaggo qarasa aikin sae dai sae sauri take ta samu tazo ta taya Afrah aiki sbd tasan yanda Afrah ke wahala gurin aikin abinci.
Tana shigowa ta samu Afrah zata fita da basket d'in abinci Amrah tace "wai har kin gama abincin ne ina ta sauri nazo na taya ki" har na gama kuma har zan kyautar wa masu gadi , meyasa? kuda kuka sha 'ya' yan marmari me kuma zakuyi da abinci? A sanyaye Amrah tace " Afrah kayan marmari dake narkewa kai tsaye" Cikin tsiwa taso yi mata magana sae kuma ta fasa da ta tuna xancen ta na asibiti kan baza su sami sa6ani ba. Ta danne 6acin ranta tace "gashi idan kina buqata sae ki d'iba, sauran se ki kaiwa masu gadi, da kulawa Amrah tace" ke baza kici bane " d'an guntun murmushi tayi mai ciwo ta wahala a girki amma baqin ciki ba zai iya bari taci ba tace" uhm a'a ni freshmilk zan sha "tana gama fad'ar haka ta haura sama wanda har taso ta tamvaye ta uncle fa sae taga ita da mijinta baza ta so ta mata shisshigi ba ,domin shisshigi nasa a fara jin haushinka har azo a sami sa6ani ita kuwa duk wani abu da tasan zai iya kawo sa6ani a tsakanin su guje masa take.
Afrah kuwa kan ta qarasa d'aki kuka ya fara zo mata tana shiga taji sallamar Farhan ya shigo tayi saurin zuwa gun wardrobe ta bud'e tana qoqarin had'iye kukan ta sbd ko kad'an bata son ya fahimci tana kishi domin kunya zata ji amatsayin ta na wacce ta tursasa ayi auren. Bata iya d'agowa jikin wardrobe ba har ya qaraso gurinta, ya rungomo ta a hankali ta baya yace "kuka kike ko? uncle hannu na ne ya yanke , ya riqa hannun yana dubawa yaga tabbas ta yanke d'in amma ysn ba kukan yanka kawai take ba, yasan ko bata ji ciwon fitar su ba zata ji haushi kan wahalar girkin da tayi ba a ci ba, sbd yasan yana d'aya daga cikin abinda tafi tsana, Afrah kuwa ita ba abinda ma yafi qona mata rai irin yawon shaqatawar da yace mata sun tafi . Yace "sannu amma ba cutting board ne da ba kya using dashi gurin cutting d'in abubuwa? to uncle ai da shi nake aiki kawai dai dana zo yanka albasa ne na rufe ido na sbd yaji shine na yanka hannu na., Sannu ya qara yi mata sannan yaja hannun ta suka zauna kan bedside sae hura mata iskan bakin shi yake kan gurin da ta yanke, taji dad'in hakan har tana qoqarin qwanciya kan jikin sa sae Kuma ta fasa sbd duk ta matsa kusa dashi sae taji qamshin turaren Amrah wanda ba komai kesa yana qamshin ba sae don yanayin turaren da Amrah ke sawa wanda duk yanda kaje kusa da ita ko kad'an ne sae ka kwashi qamshin kuma ba wai sae kunyi very close kake kwasar qamshin ba. Yace "tashi ki d'obo mana abinci muci" turo baki tayi tace "wane abincin kaida kace baka ci har na kyautar wa masu gadi " amma ke kinci kafin ki kyautar? Aa ni banci ba,Amrah kawai nace ta d'iba, meyasa bayan daji yunwa kike ji gashi d'an zaman nan da nayi har inajin yanda cikin ki ke qugi. shiru tayi dmn qara mata takaici kawai yake yace" yi haquri laifi na ne, yanxu kisha freshmilk kafin na fita na siyo miki wani abinda zaki ci kinji ,gyad'a masa kai tayi sbd bata jin zata iya d'ora wani girkin, gashi su ke kaima gwaggo abinci bare ta nemo gurin ta, na marecen nan ma ba ayi da ita ba sbd tace kar a girka da ita dmn kona ranan ta bata cinye ba.
Shi ya tsiyaya mata freshmilk da kansa ya bata tasha sannan ya wuce zuwa masallaci jin anata kirayen kirayen sallar magrib.
** ** ** Yau kusan sati biyu da yin auren, sosai Amrah ke kiyaye duk wani abu da tasan zai iya kawo sa6ani a tsakanin su. kuma yanxu kullum ita ke aikin gidan da dutyn ta, da ba nata ba, sbd ita ta buqaci hakan ganin yanda Afrah ke wahala gun abinci gashi ita nan take da ta d'ora abinci bata wahala kuma ba jimawa ta kammala shine duk rnr girkin Afrah take taya ta, Afrah da son jiki sae ta sake mata aikin gabad'aya iyakar ta taje ta mata zaune a kitchen suna fira har ta kammala wanda in sun gama abincin, sake zama suke a falo suna ci gaba da fira amma duk yanda firar tayi ma Afrah dad'i da Farhan ya shigo gidan zata tashi ta koma d'akin ta ne sbd cikin azanci yake sake mata maganar da kesa kishin ta ya motsa sosai har taji kamar ta had'iye zuciya ta mutu, wani lokacin ma har hawaye ke qoqarin zubo mata sae tayi saurin danne su, tana faman wayencewa kmr ba komai . Farhan kuwa tashin da takeyi ganin yake kmr tana yin haka ne don ta qulla wata shaquwa tsakanin sa da Amrah, domin shi har yanxu bai fara ganin alamun Afrah na kishin sa ba, duk da cewa yanxu ko kad'an bata bashi damar ya kar6i haqqin sa a gurinta , ita kuwa har ga Allah ko taso bashi da ta tuna cewa fa yasan wata bayan ita kuma still yana ci gba da mu'amalar aure da ita, sae taji baza ta iya ba, akan dole yake haqura ya barta.
A cikin sati na uku ne Afrah ta fara jin jikin ta ba d'adi sae wani nauyi yake mata da ke sa taji bata iya aikin komai domin ko wanka da ba dole bane da sae dai tayi kwanciyar ta.
Yau koda ta tashi da safe taji abin sae qaruwa yake yafi na kullum, da qyar ta samu tayi wanka ta je d'akin Farhan ta same shi kwance kan bed ya rufe jikin sa da blanket. A iya bakin qofar d'akin ta tsaya , sai da ta mishi ina kwana sannan tace "uncle so nake naje asibiti a duba ni bana jin dad'i" hm Afrah kenan gani kuma sae kinje asibiti, zo naji jikin naki may be ma malaria ce da ta addabi mutane, um um nidai nafi so naje asibiti, kin fara rigimar ki kenan gashi ni yau jikina ciwo yake min bana son damuwa,takaici maganar shi ta bata sbd duk girkin Amrah haka yake ce mata sae dai shi a gurin shi da gaske jikin nasa ciwo yake masa sbd gajiyar aikin da yayi jiya a office, yace "zo kinji na duba ki, ki daina zancen zuwa asibiti, nifa uncle nafi so naje asibiti sbd ni kad'ai nasan yanda nake ji, kin fara ko, ni kuwa gsky yanda jikina kemin ciwo bazan iya driving yanxu ba but zo a nan bedside drawer xaki ga malaria tablet kisha qwara d'aya kinga zuwa anjima dai dai jikina ya sake min sae muje, jin tayi ya soma kawo ta iya wuya da ciwon jikin nan da yake amvata mata tace"ai bance maka malaria ke damuna ba kuma ni ixini nake so kaban tunda yanxu na iya driving sae naja kaina, rufe idanun sa yayi a hankali sbd kansa dake sara masa sosai haka kuma surutun Afrah ya fara isar shi yace "wai ma na tambaye ki da izinin wa kika shigo d'akin nan? uncle ka manta sae da na maka sallama ka amsa min ka kuma bani ixini kafin nake shigowa, ba wannan nake nufi ba, sanin kanki ne u are not on duty , kuma kinsan yanda tsarin komai yake domin na sanar da ku don haka koma gun Amrah ki nemi izinin ta idan har ta baki damar zowa kiyi magana dani wannan ba laifi bane, bcs in yanxu ta shigo ta ganki baza taji dad'i ba , ba izini kin shigo mata d'akin maigida kuma da sassafe haka,komai kasa ce masa tayi domin baqin cikin da take ji ma baza ta iya magana ba ta yaya ita da mijinta ace sae ta nemi izinin wacce ta la6a har ma yana kiran kansa a maigidanta. Tsawa ya daka mata ta fita cikin kuka, tana zuwa d'aki ta d'auki mayafi da makulli ta fita sae kuka take tana jan mota har hawaye nasa ta ganin hanya bishi bishi Allah ne ya nufa zata kai asibiti lafiya .
Ba yabo ba fallasa ta dawo gidan taci karo da Farhan yana saukowa kan staircase sae faman dafe kansa yake dake masa masifar ciwo. Tsayawa tayi cike da fargaba sbd wani kallo da taga yana yi mata, qarasowa yayi yazo gab da ita, gabanta sae dukan uku uku yake tana tunanin matakin da zai d'auka, a natse cikin yanayin muryar da rai ya 6aci yace "Afrah yanxu fita kikayi without my permission shin ko kinsan tun fitar ki har dawowar ki mala'ikun Allah na kan tsine miki, kuma tabbas kin sani amma kika take sani sbd rashin ji irin naki,kunnen ta ya kama riqo ba mai zafi ba yace" ki saurareni da kyau kiji daga yau kinyi na farko kinyi na qarshe idan kuma kika sake zan d'auki matakin da baki ta6a tsammani ba, ture hannu sa tayi cike da kukan shagwa6a tace "to shine sae ka wani riqe min kunne" yace "wai meyasa yanxu duk kin rainani ko ce miki akayi duk mutuncin ki da mutum da girman sa idan ya zamo mijinki kika san sirrin sa sai ki raina shi, nan ya shiga yi mata fad'a sosai domin ko kad'an ya tsani raini,ita kuwa ko kad'an ma bata ga wani laifi da tayi ba kan ture masa hannu, sae duk taji ranta ya qara 6aci, tayi saurin ra6ewa ta gefen sa zata bar gurin domin bata son 6acin rai yasa ta masa wani abun da zai sa ya qara mata fad'a. Kiran sunan ta ya shiga yi ita kuma sai sauri take zata hau staircase wanda garin saurin ne ta zubar da takardun asibitinta dai dai Amrah ta sauko ta gani tayi saurin d'auka ta kira sunan ta domin ta bata, wani gigitaccen mari taji ya sauka akan kuncen ta wanda ya fitar mata da hawaye kai tsaye, Afrah wacce ita ce tayi marin tace "meye ruwanki dan ya kirani naqi na amsa mai! uncle d'inki ne ko nawa!daga yau kinyi na farko kinyi na qarshe kar ki sake ganin muna abu nida uncle kisa bakin ki, ki bari har idan an kasa dake! Daga nan ta fashe da wani irin kuka ta tafi d'aki tana fad'in " wlh bazan sanar da kai wannan cikin ba zubar da shi zanyi tunda ko na bar shi baqin ciki ba zai bar shi. Nan ta shiga yamutse d'akin ta ko'ina tana neman abinda zata sha kai tsaye cikin ya xube.
*Billy giro 😊&Futha lurv 💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*
*Futhalurv.WordPress.com*
*```🏅59🏅```* Sosai Farhan ya shiga bawa Amrah haquri sannan ya haura sama zuwa d'akin Afrah. Ya samu duk ta yakuce wata er kit da yake ajiyewa nan d'akinta ta magunguna, sae duba magungnan take tana karanta qa'idojin su ko zata sami wanda keda qarfin da mai ciki bata shan shi. Hannun ta ya riqo ta fizge hannun tace"ni ka rabu dani" qarfi yasa ya jawota ya manna ta a jikin sa, sae kuka take sosai tana son qwace kanta, ganin ta kasa yasa tayi tayi mai kuka kan jikin sa tana dukan qirjin sa. Hannayenta ya kama ya riqe tana ta fizgar jikinta kmr wacce tayi qaramar hauka, ya qara matseta gam a qrnsa yace"Afrah ki daina jijjiga mu haka kaina ciwo yake sosai ki natsu ko kuma wlh na hukunta ki"wani marayen kuka ta fashe ta sulale qasà kàn guiwoyinta, ta kama qafafun sa ta rungume kmr wacce ke shirin roqon sa gafara sae kuka take tana ambatar iyayenta da suka rasu, a sanyaye farhan ya durqusa bakinsa na rawa ya kama kumatun ta yace"me na miki haka da kike ambatar su Abba da suka jima da rasuwa?, ni ka rabu dani baka sona ai dole na kira su,kuma duk abinda kake min baka gani ne Allah ma yasa na bisu na huta da takaicin da kake d'ura min kullum,wani abu yake ji marar misaltuwa wanda yafi kuka ciwo sae dai kuma kai tsaye yayi d'an guntun murmushi yace"au wai dama duk abinda nake miki yana 6ata miki rai kenan,yaushe kika fara kishi na ne ban sani ba Afrah?.....ni Allah ya tsare ni nayi kishin wanda baya sona ,murmushi kawai yayi ya bar d'akin yana tuna marinda Afrah tayiwa Amrah wanda ko kad'an bai ji dad'i ba domin shi baya da nufin had'a su fad'a.
Afrah kuwa yana fita ta tafi 6amgaren gwaggo cikin kuka, gwaggo tace"oyo oyo zo naji wa ya ta6a min ke "sae da ta fad'a kan jikinta sannan tace"ba uncle bane tunda akayi auren nan kullm sae yayi ta 6ata min rai har ya guma min wani a yau wai daga naje d'akin shi ina so ya bar ni naje asibiti bana jin dad'i shine yace na bari ya duba ni nace masa nafi so naje,da qarshe wai ma na fitar masa d'aki tunda bani keda duty ba sae naje na nemi izinin Amrah sannan ko zan dawo muci gaba da magana"eh mana Afrah ai haka abin yake...kmr ya gwaggo uncle d'inane fa la6ata kawai nayi sae ace sae na nemi izinin ta,, da kika la6ata ai ta zama mata, kun zama d'aya keda ita a gurin uncle d'in naki don haka dole ne ya bata haqqinta na matar sa ya kuma yi adalci a tsakanin ku.....wai ni Allahna gwaggo wai baza ki fahimce ni bane shike nan don na taimaka na la6ata aka ce bazan je gun uncle d'ina ba sae da izinin ta don ita ce mai duty,wai kuma shine ma har da raba kwana daidai daidai nida ita, Allah ya kawo mu yau nida Afrah,to da duk a tunaninki don kin la6a ta kinfi ta kaso agun miji ne.... Eh mana, dariya gwaggo tayi tace "Allah ya shirye ki Afrah"uhm uhm wato ma gwaggo haka zaki ce sae kace wani abu nake yi mara kyau, bayan akan daidai nake ,tashi tayi tana fad'in "inda ma nasani banzo gurin ki ba tunda ba kya d'ebe min takaici sae ma qara min da kike. Tana kawai nan taga farhan tsaye a bakin qofa yana kallon ta, tayi saurin kauda fuskar ta gefe cikin fushi,yayi dariya yace"wai ashe yarinyar nan kishi ne da ita haka gashi har takai ga marin Amrah don kawai ta d'auki takardu zata bata.....ta mari Amrah fa kace.... Wlh kuwa,,,Afrah da hankalin ki kuwa? to aini gwaggo bansan abu zata bani ba.... Ina zaki sani kishi ya rufe miki ido...wane kishin byn duk kaine kamin fad'a da dawowa ta asibiti baka ko tambi me akace yana damuna ba,,Aa farhan ba kyauta ba...gwaggo haka kawai fa ta fita ba izini na,lallai baki da gaskiya Afrah kuma ko kad'an banji dad'in yanda kika mari Amrah ba ,tun farko abinda ake duba miki kenan kan auren nan amma kinqi ji gashi tun ba aje koina ba kun fara samin sa6ani... To gwaggo ai 6acin raine yasa na mata haka ba wai da niya ba.... ba wani tun da da kuna yara har girman ku ko kunyi fad'a ba kwa dukan junan ku amma sae yanzu zaki sa mata hannu don kina ganin kin taimaka mata ta auri farhan ai inace itama taimakon naki tayi sbd tana da wanda take so ba kuma ita tace tana buqatar auren farhan d'in ba kece kika tilasta ta amma har kike ikirarin la6a ta kikayi ,to ai wanda take so d'in bai fa san tanayi ba,shine naga gwara ta auri uncle domin wancan zai iya mata walaqanci ba lallai bane ya riqe ta da daraja..... ai gwanda shi d'in da ace tana tare da aminiyar ta tana sata baqin cikin da gwara ace wanda bata taso tare dashi bane yake mata hakan.....oh oh gwaggo na gaya muku ba a son raina bane kuma ni shike nan bani da inda zanje naji sanyi uncle fad'a ke fad'a,nan ta fita tana ci gava da cewa"Allah yasa yau yau d"in nan ma na mutu na huta da takaici, duk tana magana ne cikin kukan shagwa6a har ta fice daga 6angaren tana mitar ba a sonta .
Farhan yayi murmushi ya sami guri ya zauna yana fad'in "Afrah iyayen rigima ni na rasa a ina ta kwaso rigimar nan gwaggo" shine fa ga kuma saurin fushi kuma nan take ne idan an mata abu ranta ke 6aci "naga dai ba haka mahaifiyar ta marigayiya hajiya maryam take ba "ai kinsan gwaggo sae ka haifi d'a baka haifi halin shi ba" haka ne fa.