Kenza eBookz

Afra ko amrah complete - Chapter 19

Afra ko amrah complete - Chapter 19

Afra ko amrah complete Chapter 19: Afra ko amrah complete Chapter 19. Sai da suka d'anyi shiru gwaggo ta katse shirun da cewa shin wai ta sanar da kai…

4,476 words

Sai da suka d'anyi shiru gwaggo ta katse shirun da cewa shin wai ta sanar da kai abinda ke damun ta? Ai rigimarta baza ta bari ba kawai dai zan duba ta da kaina koda bata so ko kuma na kar6i takardun da ke hannun Amrah na gani. To Allah yasa muji alheri ,da jin kunya yace"Amin "sannan ya fita yana tunanin ko ciki ne ba zai kai wata d'aya ba"amma sae ganin yake kmr ma malaria ce da zaman banzan da take yi bata aikin komai .

Afrah na komawa 6angaren su ta tu6e zata yi wanka sae ga Amrah tazo ta same ta har d'aki tana bata haquri kan cewa "Don Allah Afrah kiyi haquri wlh ban miki magana don komai ba sae don na baki takardun ki da kika zubar a rashin sani kuma ni ban san wani abu kukeyi ba dmn saukowata kenan,amma kiyi haquri inshaAllah hakan ba zai sake faruwa a tsakanin mu ba. Afrah komai ta kasa cewa sbd kunya ta cika ta har ta matsu Amrah bata var d'akin ba,Amrah kuwa na ganin ko kallon ta Afrah taqi ta ajiye takardun a kusa da ita zata fita, Afrah taji kmr ta mata magana idan bata bud'e takardun taga meke ciki ba domin ita bata son kowa ya sani har sae ta zubar da cikin, sae dai kuma tasan halin Amrah baza ta bud'e takardun ba amma duk ta haka hankalin ta bai kwanta ba,tace"kinga ina fatar baki bud'e min takardu ba? Ko d'aya Afrah kinsan ba hali na bane, sae duk ta qarà jin bata kyuata mata ba domin da gani tasan Amrah taci kuka kuma ko yanzu kukan take ji. Afrah tace"kiyi haquri Amrah nima ba a son raina bane dan Allah kiyi haquri kinji"ba komai Afrah ya wuce. Daga haka ta fita Afrah kuwa ta yiwa takardun 6oyon qwarai sannan ta shiga wanka.

Da fitowar ta wankan d'aure da towel taje d'akin Amrah ta nemi izinin ganin farhan Amrah ta bata dama.

Tana shiga d'akin shi ta same shi yana shan magani bayan ya gama yazo har inda take nan bakin qofa yace"ya akayi ne? na nemi izininta kafin na shigo,to ina ce kin bata haquri ?eh ,yaushe? da tazo d'akina ta ban haquri, to kema kije har d'akin nata ki bata haquri, kuma wlh kar na qara ganin irin haka a tsakanin ku, idan kuma kika qi wlh Afrah zan miki huknci mai tsanani,kayi haquri uncle nima ban so haka ba sharrin shaid'an ne, naji Allah ya mana katangar qarfe da sharrin sa, Amin yauwa ina jinki me ya kawo ki?,dama ina so anjima zan fita ne da yamma ,,zuwa ina? nidai kawai kayi haquri ka bani izini,keda ba kya da lafiya kike zancen fita bayan kuma d'axu kinje asibiti ,don Allah uncle kar kace " Aa",,naji amma ina so zanga wani abu a jikin ki, bani fa keda duty ba,, ai na sani dmn aikin da zanyi ba zancen duty bane, idan kuma kince Aa fitar ki ce Aa, ba yanda ta iya tace"to shike nan duba abinda xaka duba. Qara matsawa yayi kusa da ita har suna shaqar numfashin juna sannan yakai hannu a hankali yana yaye towel d'inta ,tayi saurin kallon shi yace"ba dole kina iya tafiyar ki amma ki sani ba fitar ki, kmar zata yi kuka tace "to uncle me zakayi?nima gaya min inda zaki je sae na gaya miki abinda zanyi,, um um duba kawai, wani shu'umin murmushi yayi sannan ya qarasa bud'e towel d'in wanda hakan ya bayyanar da kyakkyawan qirjinta a fili har sae da yaji wani abu kasancewar ya jima bai gansu ba,haka ya dake yaci gaba da kallon qirjin nata da kyau sannan ya riqo hannayen ta yana kallon en yatsunta daga nan ya kalli fuskar ta wacce taqi yarda ta kalle shi yace"ur eyes "a hankali ta d'ago suka had'a ido,yace"yayi kyau sae ki rufe qirjin naki ki bani guri"a sanyaye ta rufe qirjin ta tace"to ka bani ixini? Sae da ya lumshe idon sa yace"eh na baki u are free to go" cikin jin dad'i ta fita d'akin ba tare da ta kawo tunanin abinda yasa ya mata binciken ba.

Bayan ta saka tufafi taje har d'akin Amrah kamar yanda yace, ta qara bata haquri cike da nadamar abinda ta mata , Amrah tace "wlh har ga Allah Afrah nasan a yanda muke yin kanki ba zai sa kimin haka ba sae dai sharrin shaid'an wanda nake fatar Allah ya shiga tsakanin mu dashi kar ya sake bashi cin nasara a tsakanin mu, amin Amrah ako yaushe ina alfahari dake sbd haqurin ki da kuma tunanin ki shiyasa nake son ki a rayuwa wlh, amma ai nafi sonki domin ni bazan miki yanda kika min ba, tayi maganar ne cikin wasa, Afrah ta rufe idonta cikin jin kunya ,ta kama kunnen tace"gsky ne yi haquri dan Allah ,Amrah tayi saurin d'auke hannayen Afrah da ta kama kunnuwanta ta rungumeta ,tace"kefa da wasa nake miki. Daga haka sukayi zaune suna fira cike da nishad'i kmr basu ba.

Sun kwashe awanni suna fira har Afrah taji sat kmr bata da wani sauran baqin ciki har tayi tunanin fasa zubar da cikin da tayi niyya.

Sea dai yamma nayi tayi tunanin zuwa ta zubar da cikin ba don komai ba sae don ganin idan tayi haka zata rama takaicin maganganun da farhan ke saka mata domin idan yana mata maganganun ji take tamkar wata wuta ce mai kaifin bala'i yake rura mata a zuciya.

Shirinta tayi tsaf ta fita sae dai tafiya mai nisa tayi zuwa wata asibiti inda bata sa ran wani ya santa ko ta had'u da wanda ta sani.

Har ta isa wani abu take ji kmr ta fasa,amma bata bawa zcyr ta dmr hakan ba.

Cikin sauqi ta samu ganin likita kasancewar private asibiti ce,da shigarta office d'in taji wani dad'i ganin likitan ba musulmi bane a cewar idan ta had'u da musulmi zai tsaya ja mata aya ko hadisi tafi son kai tsaye ayi mata abinda taje nema. "Hajiya have a seat,ko kina da lalaura zama ne"kallon sa tayi had'e da girgiza masa kai tana mamakin yanda ko kad'an bai yi kama da mai jin hausa ba amma sae gashi yana hausa kamar jakin kano. Basarwa tayi ta nemi guri ta zauna tana tunanin qaryar da zata shirga masa ya mata aikin ta kai tsaye. Yace"Uhm meye matsalarki? sae da ta qirqiro hawayen qarya suka cika mata ido tap ta fara magana cikin murya kmr wacce ke cikin matsananciyar damuwa tace"doctor juna biyu ne dani kuma wanda a bisa qaddara na same shi ba wai ina nufi banyi aure ba na same shi, a'a ina da aure, amma miji na baya son mu sami haifuwa da wuri shiyasa yake bani pills ina sha amma kwatsam sae gani d'auke da ciki wanda na tabbatar idan yaji kashe ni ne kawai ba zai yi ba domin nasan zan sha dukan tsiya sbd zai d'auka ko bana shan pills d'in da yake bani,kuma kullum ce min yake idan na yarda na d'auki ciki mun rabu dashi kenan har abada ,ba zai qara waiwayata ba,cikin kuka sosai ta qarasa maganar tace"gashi ni kuma ina mutuwar son shi bana son mu rabu kuma shi kad'ai ne gare ni a duniyar nan bani da kowa duk iyayena sun rasu, share hawayenta take wasu na sake zubowa,ta zame kan kujera ta durqusa kan guiwoyinta tace"pls doctor ka taimaka ka bani abinda zan sha cikin nan ya zube cikin gaggawa pls and pls am begin u" Ajiyar zuciya dr ya sauke ya cire eyeglass sannan yace"ya isa haka Hajiya zauna muyi magana"

Bayan ta zauna yace"mijin naki yasan kin fito?eh amma bai san asibiti zan zo ba shiyasa nake son nayi sauri na koma,shike nan zan taimaka miki dmn matuqa kin bani tausayi,amma ina fatar ba kwata kwata bane baya son haifuwa? Aa yace da mun shekara biyu yana son mu haifu,ok cikin naki wata nawa ne?ko wata d'aya ma bai qarasa ba, that's gud domin abu ne mai sauqin zubarwa. Nan ya tashi ya d'auko mata wani magani tablet ya zauna kafin yake cewa"zaki sha qwaya d'aya tak by 30mint cikin zai zube tas"bai kai ga miqa mata ba wayar sa tayi qara ,ya d'aga wayr cikin fara'a, yana cikin wyr ya shiga kallon Afrah bcs ba da kowa yake waya ba face farhan wanda duk zunzurutun tafiyar nan da Afrah tayi yana biye a bayan ta haka kuma duk abinda ta fad'a yana ji a bayan window. Amma sae da ya bar kusa da window sannan ya kira Dr wanda ba komai yake snr da shi face"ka canza mata wannan maganin ka bata na bacci dana qarin jini da qarfin jiki ga masu ciki,amma ka bata su a matsayin na zubar da ciki ne idan ta fita zan shigo muyi magana."

Nan Dr ya katse wyr ya kalli Afrah kafin yake cewa bari dai na baki wanda yafi wannan qarfi, kmr kuwa kasan tunanin da nake yi kenan ka bani wanda koda 15 mnt keyi cikin ya zube tas, ok to cewar Dr sannan ya tashi ya d'auko mata magungnan da farhan yace a bata ,ta kar6a tana godiya yace"kowanne kisha qwaya d'aya "ok to, nawa ne kud'in nan ya fad'a mata kud'i ta biya shi ta fita sae murna take a ranta.

Tana zuwa gida bata wani duba qa'idojin magungunan ba bare ta fahimci na mene ne ,sha kawai tayi,taje ta dauko pad ta saka a cewar koda yazo mata da matsanancin ciwon mara ta shirya,taje ta nemi gado tayi kwance sae jin wani abu take cikin cikinta na tsoro kmr wacce tayi babban laifi tana tunanin idan aka kamata ya zatayi ,haka take ji sosai har ma ta kasa samun natsuwa ta yanke shawara zata je 6angaren gwaggo koda yazo mata da mutuwa sae tayi wasiya kafin ta mutu. Nan ta garzaya sae 6angaren gwaggo ta haye gado ta rufa jikin ta da blanket fuskar ta kad'ai ta bari.

Farhan kuwa tafe yake hanyar dawowa sae mamakin Afrah yake a ransa ,yayinda ya yanke shawarar ba zai nuna mata yasan komai ba zai zuba mata ido yaga iya haukarta tukun.

Yana shigowa gidan 6angaren gwaggo ya nufa koda ya shiga d'aki ya sami Afrah idon ta qyar kan agogon bangon d'akin sae qidayar lokaci take ,dariya ta soma bashi wai a haukar ta zubewar cikin take jira har tana wani qidayar time baki sae motsi yake kmr wata mai salati.

*Billy giro😊 &Futha lurv💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*

*Futhalurv.WordPress.com*

*```🏅60🏅```* Gyaran murya yayi domin ya fahimci bata san da shigowar sa ba. Da fargaba take kallon shi abu ga marar gaskiya. Shi kuma ya sake mata fuska kmr ba komai yace"ina gwaggo take ne? koda na shigo ban ganta ba may be tana bayi tana wanka,yace"OK" kafin yake fita. Ajiyar zuciya ta sauke ta qara shigewa blanket sae ga gwaggo ta fito daga bayi tace"assha kaddai ciwon ne yakai ki ga kwanciya,ina farhan yake ne bai duba ki ba? Aa gwaggo amma yanzu ya fita, to qoqarta kiyi sallah kinji an fara kiraye kiraye ,ba musu ta tashi amma ta fara mamaki da har yanzu bata fara jin komai ba sae bacci, may be yanayin maganin ne sae idan tayi bacci koda zata tashi ta samu cikin ya zube. Haka tunanin nata ya bata.

Da qyar taga ta samu tayi sallar magrib sbd bacci ,tana kammalawa ta maida pant d'inta da ta cire mai d'auke da pad taje ta hau gado ta sake qudundunewa cikin blanket daga haka bacci yayi awon gaba da ita.

Sai bayan sallar isha'i farhan ya sake dawowa 6angaren ya sami gwaggo tana lazimi ya nemi guri ya zauna ta taqaita tace"inaga fa kmr Afrah na jin jiki sosai ka duba ta kuwa? eh gwaggo, to me yake damun ta ne? shiru yayi baya son snr da gwaggo ciki ne da Afrah wanda ya fahimci haka ne kafin ma yabi bayanta wato lokacin da ya duba qirjinta da yatsunta da kuma idanuwanta ,yafi so ko zai sanar da gwaggo sae ya gama ganin haukar Afrah tukun. Yace"d'an zazza6i ne"to Allah ya mata sauqin shi yace amin "ya tashi ya fita.

Koda Afrah ta farka daga bacci ta ganta d'akin farhan yana zaune a bedside yana wani aiki da laptop bayan sa kad'ai take gani hakan yasa tayi saurin sa hannu ta ta6a pant d'inta bata ji alamar komai ba ,ta shiga dube dube akan gadon ma haka, ta tashi domin zuwa toilet ta qara duba kanta ,farhan yace"ki d'oro arwala kafin kike fitowa kiyi sallar isha'i"kallon agogon d'akin tayi qarfe 9:40pm ta shiga tunanin ko dai cikin ya zube har farhan ya mata wanka bata sani ba, to idan haka ne ai ba zai ce tayi arwala ba kuma ai kayan jikin ta ne a saye da ita farhan dai se kallon ta yake har ta qaraci banzan tunanin ta ta shiga toilet. Tana shiga ta ciro pant taga shi d'in dai ne ba wani canji kanta yayi mugun d'aurewa ya akayi cikin bai zube ba ko dai doctor ya manta ba guda guda ake sha ba lallai zata je ta duba qa'idar maganin ta gani.

Sae da ta watsa ruwa sannan tayi arwala ta fito taje d'akinta tayi sallah tana gamawa ko azkar d'in da take bata iya yi ba ta tashi ta jajimo jakarta da ta fita da ita sae dai kaf ta zazzage jakar bata ga maganin ba, tunani ta shiga yi to ina takai maganin ko ta bar su a mota,no nazo dasu tunda har nasha kawai dai nasan ina da niyyar musu 6oyon qwarai ban kuma riga nayi ba amma zan bincika . Ta kwashe kusan rabin awa tana neman maganin duk ta wahala amma bata gan su ba nan ta yanke shawarar zata je cikin motarta ta bincika. Sum sum take tafiya kmr wata 6arauniya har ta sauko downstairs ta murd'a key tare da riqo handle d'in qofar taji farhan yace"ina zuwa da dare haka? wani irin abu taji na fad'uwar gaba duk la6a6en nan da take don shi kawai take amma sae gashi ya kamata dumu dumu zata bud'e qofa, ynx me zata ce masa ,har ya qaraso gurinta ta kasa ko qwaqqawaran motsi kanta qasa cike da fargaba sae 6al 6al zuciyar ta keyi kmr zata fito, yace"ina magana wani abu kike so ne? Da qyar ta iya bud'e bkinta tace"dama wani abu zan duba a mota"mene ne wannan abun da baza ki haqura har da safe ba koda yake jeki ,kallon sa tayi ta kuma yi saurin duqar da kanta yace"jeki man ko so kike na raka ki ? saurin girgiza kanta tayi tace"Aa zan iya zuwa ni kad'ai" Tana kawowa nan ta bud'e qofa ta fita farhan ya girgiza kansa domin yasan ba komai take nema ba face magungunan da ya d'auke ,wanda ya d'auke su ne sbd yasan da zarar taga cikin bai zube ba sae ta nemi ganin qa'idar su.

Sosai take jin tsoro duk da hasken da ke harabar gidan haka taje ta bud'e motarta,tayi iya binciken ta bata ga komai ba. Jin take kmr tayi kuka duk takaicin kanta take da ta manta inda ta sa su, domin a tunaninta tasan ba wanda yasan da su bare tayi tunanin d'auke su akayi. Ba yanda ta iya ta rufe motar ta koma daga ciki ,sae dai bata sami farhan ba ya komawar sa d'aki . Tana shiga d'aki tayi zaune qasan tiles bayanta na manne a jikin gado ta had'e kai da guiwa ta fara rera kuka tana tunanin yanzu ya zata yi idan bata ga magungunan ba gashi cikin bai zube ba tasan da kmr wuya farhan ya sake bari ta fita nan kusa. Bud'e qofa taji anyi tayi saurin d'agowa dai dai hawaye na zubowa kan fuskar ta, tayi saurin share hawayen farhan yazo yana taya ta yace"kukan na me"cikin muryar kuka tace"ba komai"amma kike kuka ko yunwa kike ji?girgiza kanta tayi byan kuwa tana jin yunwa sosai amma bata jin zata iya cin abinci a yanayin da take ciki yanxu. D'aukar ta yayi suka je d'akin shi ya zaunar da ita kan bed yaje ya bud'e frigde ya d'auko fresh milk ya tsiyaya a cup yazo ya zauna kusa da ita,ya jawota jikin sa yana shafa bayanta a hankali yace"Afrah yi haquri kisha wannan kafin ki kwanta kinji" girgiza masa kai tayi, nan dai ya lalla6a ta ya shiga bata har sai da tace ta ishe ta,tana gama sha ba jimawa bacci ya kwasheta,wanda shi ya saka ta baccin ta hanyar qwarewa gun shafar jiki dmn bacci. Kallonta yake yanda ta wani lafe a qirjin sa, yakai hannu a hankali ya shafo cikinta,sae kawai hawaye suka silalo kan kumatun shi yana mai jin baqin cikin yanda Afrah ta tashi zubar mai da cikin,ya rasa meyasa take da niyar hakan da har ta shirgawa doctor uwar qarya haka byn kusan ko yaushe yana nuna mata illar qarya amma sae gashi ta gwane a gurin. Motsin da tayi ne yasa yayi saurin d'auke hannun sa a kan cikinta .

Washe gari ta gama sallah kenan taji amai da sauri ta nufi toilet ta saka key sbd d'akin farhan take bata so ya shigo yaga amai take ya fahimci ciki ne da ita, sauqin ta d'aya ammanta baya da sauti, ta kintsa kanta kmr wani abu bai faru ba ta fito.

Da ta fito komai bai ce mata ba , nuna ma yayi bai lura da yanayin da ta tashi ba . Sosai taji dad'in da bai fahimta ba ta zauna tana yin azkar.

Zaune suke suna break fast su uku guraren qarfe goma spoon d'aya Afrah tayi taji alamar amai hakan yasa bata sake saka wata lomar ba gudun kar tayi aman. Magana farhan ke musu yana tambyar abinda zai dawo musu dashi sbd fita zai yi,komai Afrah taqi yarda tace domin tasan tana bud'e bakinta za a sami matsala. Amrah kam tace"bata buqatar komai, Farhan ya kalli Afrah domin yasan duk zai fita sae ta fad'i kalar chocolate d'in da take so, yace"kefa"girgiza mishi kai tayi wanda ya duk san dalilin kasa maganar sbd yana lure da ita tun lokacin da ta saka loma. Fita kawai yayi abin shi ba tare da ya ske cewa komai ba yasan dai tana da aiki domin duk yanda taso 6oye cikin yau da gobe sae ya bayyana dmn ba zai ta6a sakacin barinta ta zubar dashi ba.

D'aki Afrah ta shige domin ta samu taci abinci amma da taje zuwa bud'e baki sae taji amai ,ta sake gwada bud'e bakin taji still ta kasa , kuka take sonyi sbd yunwa take ji sosai ,nan dai ta danne kukan tayi ta gwadawa ko zata samu ta bud'e bakin bata ji amai ba wanda tayi hakan kusan sau biyar taga duk d'aya,kuka ta shiga yi ciki ciki ta rasa yanda zata yi taga dai ba wai amai ta bari a cikin bakinta ba kawai dai yunqurin amai kezo mata da zarar taje zuwa bud'e baki.

Haka ta yini ba ci ba magana ko gwaggo da tazo dubata da hannu take bata amsa idan na gyad'a kaine ta gyd'a kai in kuma girgizawa ne ma haka. Hakan yasa hankalin gwaggo duk ya tashi domin ganin take kmr matsalar Afrah ce ta dawo mata wato kurmanci,sae duk ta kasa zama ta kasa tsayi tana kiran wayar farhan da taqi shiga, tace da Amrah"tun yaushe ne rashin maganar yazo mata ?nima gwaggo ban sani ba sae yanzu sbd tunda safe ta shige d'aki bata sake fitowa ba kawai dai d'azu da safe da uncle zai fita, as usual tana fad'in abinda take so a dawo mata dashi amma sae naga ta girgiza masa kai wanda hkn ya ban mamaki amma sae na basar.

Afrah da ko kad'an bata son a kira farhan ta kar6e wayar gwaggo tana nuna kar a kira shi ita fa lafiyar ta qalau, gwaggo tace "to Afrah kimin magana mana naji" Shiru Afrah tayi domin bata jin zata iya yiwa gwaggo magana . Suna cikin haka sae ga farhan ya shigo , gwaggo tace "yauwa farhan dama kai nake son kazo ka duba Afrah idan ba matsalar tace ta dawo ba,dmn bata magana sae dai tayi wa mutum maganar kurame,yace"Afrah yiwa gwaggo magana mana taji,girgiza mai kai tayi yace"me yasa?shiru tayi ,yace"gwaggo jeki abinki kawai lafiyar ta qalau kar ki damu"farhan ina fa lafiya bata mgna nikm ba inda zanje sae naji tayi min magana,,rau rau Afrah ke kallon Farhan dake kallonta ko kad'an bata son tayi magana tayi amai har su fahimci ciki ne da ita ,shi kuwa farhan ransa ne yayi mugun 6aci dmn sak ya fahimci irin laulayin da take d'auke dashi ya kuma gano dalilin da yasa bata son yin magana,wanda hakan ya qara bashi tabbacin tana kan bakar ta na ganin ta zubar mai da ciki, duk da yaso ya basar har sae yaga iya gudun ruwanta amma 6acin rai ya mantar dashi har bai san lokacin da ya daka mata uwar tsawa tare da jawota jikin sa yace"kiyi magana aka ce !Afrah da gabad'aya ta rud'e bata san lokacin da ta bud'e baki zuwa magana ba kan tace komai ta shiga kwara amai kan jikin farhan.

*Futha lurv&Billy giro* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```~AFRAH KO AMRAH ```*~ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*NA Billy giro 😊& Bilqis Sidibe💅🏻*

*Futhalurv.WordPress.com*

*🏅61🏅* KO kad'an ransa bai 6aci ba kan amman da take kwara masa sbd yasan sae tayi aman ne zata ji sauqi, da qyar ta samu ya tsaya mata duk tabi ta galabaita sae numfashi take fitarwa. Qoqarin zamewa take daga jikin sa sbd tsayuwa na son gagararta hannun ta yaja ya tafi da ita d'akin shi suka je bayi, ya riga ta tsaftace jikinsa ya fito ya barta ya dawo downstairs ya samu Amrah ta gyare gurin tsaf gwaggo tace " anya farhan baza ayiwa yarinyar nan test ba kuwa" zan gwada hakan, haka ya fad'a a taqaice sbd 6acin randa yake ciki baya ko son yin magana sosai.

Da dare Afrah ce kwance sae tunani take Farhan bai ce mata komai ba har yanxu kuma tasan ya fahimci abinda kenan. Bud'e qofa taji anyi ta tashi a hankali tana kallon Farhan wanda fuskar sa ba alamar annuri yaje ya zauna kan gadon da take , ta matso gab dashi tare da jinginawa a jikinsa ta kwantar da kanta kan kafad'ar sa wanda tana yin komai ne tsoro tsoro yace "gaya min meyasa kike son zubar min da ciki,na miki wani laifi ne ko kuwa ra'ayin cikin ne ba kya yi? fad'uwar gaba taji sosai ta san bone ya cita tunda ya gano ta amma ya akayi ya sani shine abinda take tamvayar kanta, tace "uncle wa yace maka zan zubar da ciki? Ki bani amsar tambaya ta tukun,ba zai yu na miki tambaya kimin ba,shiru tayi ta rasa me zata ce masa sae qoqarin kuka take yace" Afrah ba kuka na tambaye ki ba don haka kar ki soma" shiru tayi yace"Afrah kar ki bari 6acin raina ya yawaita ki bani amsar tamvaya ta ina saurarenki " cikin muryar kuka sosai,tace "uncle ni abinda kake min ne bana so" name kenan? na maganganun da kake gaya min, sosai suke qona min rai shiyasa naga ba abinda zan maka na rama face zubar da cikin "tsantsar wauta ya hango a tare da ita , dmn shi ya d'auka ko qatoton wani abu ne sae dai ya tuna cewa Afrah yarinya ce she is only seventeen yrs bata kammala hankalin kanta ba tukun, Yace" amma Afrah ai ni na miki laifin ba cikin ba meyasa baza ki d'auki mataki a kaina ba, kuma kin manta cewa kwata kwata kin daina bani kulawa akan haqqina ai ko shima wata axaba ce kike min,uncle kana fa da wata mata, Afrah dan ina da wata matar sae aka ce ki share ni,ko kuma haka aka ce miki idan ana kishi har haqqi daina ba miji ake...turo baki tayi tace"ai ni ba kishi bane kuma nida nace a auro ta sae kuma nayi kishi", naji ba kishi bane gaya min dalilin ki naqin bani haqqina,to ni uncle ba komai,kenan yau zaki bani? maqale kafad'a tayi tace "ni bazan baka ba tunda d'azu kamin tsawa don kawai naqi magana" ai kad'an ma kika gani don banzo gun zancen qaryar da naji kin shirgawa doctor ba "da sauri ta tashi kan jikin sa har tana hard'e qafafu sae wani soshe soshen rashin gsky take. Tace " uncle waya snr da kai nayiwa doctor qarya? Ni naji da kunne na ko Kuma kina tunanin haka kawai zan barki ki fita ba tare da kin sanar dani inda zaki je ba,, kenan uncle baka yarda dani ba,yarda ma kuwa amma ke ke shirin 6arar da yardar sbd tun da kika zo nemn izinin fita na fahimci ba kya da gaskiya na kuma sami kaina da jin fad'uwar gaba kmr wani mummunan abu zai same ni shiyasa na kasa haqura sae da nabi bayanki wanda tabbas 6arna ce ke shirin afkuwa dani se Allah ya kare ni da sharrin shad'aninki,,kuka ta fashe dashi ko kad'an bata ji dad'in kalmar ba tace"me yayi zafi haka uncle? Au to ba shaid'anin naki ya ingizaki ba, wani kukan ta sake fashewa sosai kuwa ,farhan yace"baki fahimce ni ba fa zo na fahimtar da ke. Nan ya jawo hannun ta ya zaunar da ita yace"ba ina nufin ke shaid'an bace ,kuma shaid'aninki da kika ji nace kowa na duniya Allah ya halicce sa dashi haka ma Annabi Muhmd( s . a. w), amma shi Allah ya taimake shi ya musulntar mai da nashi baya sashi aikata munanan ayukka, mu kuma namu da ba a musulntr ba shike ingixa mu wani lokaci muna aikata abinda ba dai dai ba,haka kuma idan muka biyewa son zuciya tana sa mu aikata munanan ayukka ,ma'ana kinsan abu marar kyau ne amma kika yi don kawai biyan wata buqatar ki,shine kinyi son zuciya shiyasa ake son mutum ya tsalkake zuciyar sa idan kikayi hakan to kin gyara dukkanin jikin ki, Idan zaki iya tuna a cikin arba'una hadith, a cikin qrshen hadith na shida inda annabi Muhammad (S.A.W)yake cewa sahabbansa _"Ala,Ku saurara,wa inna fil jasadi mudgatan izan salahat salahal jasadu_ _Kullihi,wa iza fasadat fasadal jasadu kullihi_. _Haqiqa a cikin jiki akwai wata tsoka idan ta gyaru dukkan jiki ya gyaru._ _Idan kuma ta lalace dukkan jiki ya lalace._ _Yace"Ala ,Ku saurara ,wa hiya qalbun ,ita ce zuciya_" Buhari da muslim ne suka ruwaito shi.

Kinga kenan abinda hadith yake fahimtar damu anan shine idan muka tsalkake zuciyar mu ,mun ku6utar da ga66an jikin mu ne daga aikata miyagun ayyukka,sbd dama duk wani abu daga zuciya ne yake fitowa sannan ga66an jiki su aikata. Ina fatr kin fahimta? Na fahimta uncle kasan mnyi wannan hadith a islamiyya....ai ba yi ba aiki dashi, inshaAllah zan kiyaye.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull