Kenza eBookz

Afra ko amrah complete - Chapter 20

Afra ko amrah complete - Chapter 20

Afra ko amrah complete Chapter 20: Afra ko amrah complete Chapter 20. Yace "yayi kyau na kuma dawo zancen doctor, kisani ko kad'an banji dad'in qaryar da…

4,295 words

Yace "yayi kyau na kuma dawo zancen doctor, kisani ko kad'an banji dad'in qaryar da kika yi masa ba, nasha gaya miki Afrah qarya ba kyau,qarya takan iya sa mutum wuta,tana kawo xubewar mutunci a kuma daina ganin kimar mutum da darajar sa, yanzu da ace na sanar da doctor cewa qarya kika masa ba zai qara ganin kimar ba ,ba kuma zai qara yarda da abinda zaki sake gaya mai ba koda kuwa ya kasance gaskiya ne. Kayi haquri uncle sharrin shaid'an ne amma zan roqi Allah ya bani ikon rinjayar shaitan ya kuma bani ikon tsalkake zuciyata, ,tada ta yayi kan durquson da tayi masa sbd ta fahimci ko kad'an abin bai masa dad'i ba. Share mata hawaye yake yace"shike nan ya isa na haqura amma kar ki sake aikata hakan kinji" "inshaAllah uncle" kimmin alqawari ko bayan idona ne ?nayi maka alqawari inshaAllah, amma uncle me kace da doctor ?ce masa kawai nayi na san waye mijinki ,zanje na masa magana. yace"amma Afrah dan Allah na roqe ki kar ki sake gigin cewa zaki zubar da ciki don kawai mai shi ya 6ata miki rai sam ba hujja bace,kuma ba qaramar wauta bace domin ba kisan irin alherin da ke tattare da wannan cikin ba wanda idan kika haifeshi Allah kad'ai yasan matsayin da zai kai shi tayu shine mai tausayin ki da taimakon ki duk baki sani ba. Don haka ko nan gaba koda bani ba,mijinki ya 6ata miki rai kiyi tsalkakakken hukunci ba irin wannan ba..... uncle me kuma ya kawo zancen wani mijin, Afrah idan na mutu ai dole kiyi aure baza ki zauna haka ba....cikin kukan shagwa6a ta rufe mai baki tace,"haka kawai ana zaune qalau ka d'auko zancen mutuwa,,ai ko banyi zancenta ba zata xo min sbd dole ce.....Aa ka daina uncle baza ma ka mutu ka barni ba " idan Allah ya rubuto tare mutuwar tamu take ba, amma idan ya rubuto ni zan fara mutuwa kinga dole na tafi na barki. Kuka ta ajiye mai sosai kan ya daina mata zancen mutuwa bata so,yace "to na daina sae kuma me?sae muyi bacci, wane baccin wai nikam ce miki akayi ni dtse ne da zan yi ta bacci kullum,bana rage sha'awa,kunya taji tayi saurin rufe mai baki had'e da 6oye fuskarta a qirjin sa, ya shafo cikinta yace"gobe zan sanar da su gwaggo qaruwar da muka samu...Aa uncle kunya nake ji dan Allah kar ka fad'a wa gwaggo ,to ai idan kika snr da Amrh dole gwaggo taji,ai ni bazan gayawa Amrah ba sae idan ta gani da kanta. To shi baban babyn fa? to ai ya sani ,um um da ace ban sani ba wai, tace"a rnr jy ko,da naje asibiti aka sanr dani ina d'auke da ciki tun kafin na baro asibiti nake ta farin ciki har ma na manta 6acin randa kasa min yayinda na tsara a raina cewa ina zuwa gida zan baka takardun na kuma rufe idona na fita da gudu, as i imagined idan ka krnta tkrdn zakayi farin ciki sosai sae kawai da dawowata ka ajiye min fad'a ka juyar da farin cikna izuwa baqin ciki. Cikin shagwa6a ta qarasa maganar yace"yi haquri ftr ki ba izini ce ta 6ata min rai dmn bana son mala'ikun Allah suna tsine miki,amma ai yanzu komai ya wuce" um um saura d'aya ,meke nan? Amai ne bana son inayi uncle,kaga yau na wahala sosai tun fitarka ban sake cin abinci ba da magana. Dama kuwa zan miki magana akai idan kika ji amai kiyi amn domin zai fi miki sauqi kan kice barin shi zakiyi, zai yi ta damun ki ne ba kuwa zai daina ba har sae kinyi shi,kinga yanzu da kika yi ,kinci abinci gashi yanzu har muna magana dake. Murmushi tayi tace"ni ina nasan haka ne"ya lakato hancinta cike da murmushi yace"ya zaki sani kina fama da rashin jinki" Yana kawo nan ya shiga cire buttons d'in rigar sa ,ta kai hannu a hankali tana shafa sumar qirjinsa tace"uncle yaushe sumar qirjin ka ya fito haka?ya zaki sani kin share mijinki d'an bawan Allah kin barshi da yunwa, d'an guntun murmushi kawai tayi ,yace"nikam meyasa kike son sumar qirji? tace"ba ita kad'ai ba har ma na nan ina so,ta fad'i haka ne yayinda ta shafo sajen fskrsa sannan ta koma kan qirjinsa tana ci gaba da shafa tace"luf luf dashi yana matuqar birgeni shiyasa kake matuqar birgine har bana so naga ka aske"qara rungume ta yayi yace"ni kuma a jikin ki ina matuqar son wa'anan har bana fatar ganin zubewar su shiyasa a duk lokacinda na gansu nake alfahari sbd Allah yayi miki su masu fad'i da tsayi ta yanda basa saurin zuvewa. Duk maganar nan da yake yi kanta a qasa tana d'an murmushi jin kunya sae kallon hannun sa take dake yawo a hankali kan qirjinta,daga nan ya kashe bedside lamp ya kwantar da ita tare da fad'in " yau a nan zamuyi yaqin kashe arna, anan d'in? Eh man kinga munyi a Oman mun sami ciki, munyi a d'aki na mun sami ciki,yanzu sae muyi a d'akin ki mu sami ciki, kinga mun sami 'ya'ya uku kenan, idan mun sake yi mu sami na hud'u... dariya tayi sosai tare da fad'in"cabd'i! idan haka ne da bone yaci matar jarababbe....kuf ta buge bakinta tayi saurin 6oye fuskarta a kirjinsa sbd wata irin matsananciyar kunya taji har dai da taga yayi mata kallon mamaki ,sae duk taji kmr ta 6ace 6at ta huta da kunyar . Lallai yaran zamani ba abinda baku sani ba"cewar farhan wanda ke kallon Afrah dake ta faman cusa fukarta a qirjinsa kmr zata fasa qirjin ta shige ,yayi2 ya d'ago fuskarta ya kasa yace"d'ago fuskar ki man ko so kike nayi fushi? a hankali ta girgiza kanta yace"to d'ago , da qyar ta iya d'agowa sae dai fuskarta rufe take da tafukan hannyenta ya jaye hannunwanta but still idonta a rufe suke . Nan ya sami damar qarewa kyakkywar fuskarta kallo musamman kan d'an qaramin bakinta da shima yake matuqar birge shi,fuskarsa yakai gab da tata ya goga hancinsa akan nata yace baza ki bud'e idon naki ba,kan tayi wani abu ya had'e bakinsu guri d'aya sae tsutsar lips d'inta yake kafin yake fara wasa da harshenta,yana kuma wasa da d'ayan hannunsa akan qirjinta yayinda d'ayan hannun ke shafar gadon bayanta ,daga haka ya shiga aika mata saqonni masu nauyin gaske da suka mantar da ita komai wato har Amrah,inda ta shiga nuna mai tata qwarewar ta hanyar mayar masa martani hakan yasa d'akin yayi tsit ba a jin komai sae numfashin su kad'ai.

"A hankali uncle kar naji zafi pls" shine abinda ta furta cikin kasalalliyar murya, sbd addu'ar da taji yayi yana qoqarin shigarta. Yace"olryt"

Da haka suka lula duniyar ma'aurata wacce tayi bala'in nishad'antar dasu.

Guraren qarfe uku farhan ya farka sae kallon Afrah yake da ta wani qudundune cikin jikin sa kmr mai shirin shan mamma cike da murmushi ya shafo fuskar ta domin yau ta faranta mai rai sosai ya kuma ji dad'in kasancewa da ita har dai yanda bata nuna gajiyawar ta ba. Tashi yake qoqarin yi domin zuwa toilet ya d'oro arwala yayi nafila sae kawai yaji wani motsin da bai kamace shi ba a harabar gidan, hakan yasa ya tashi a hankali ya bud'e window, sosai ya firgita da abinda ya hango , da sauri yaje gun wardrobe ya bud'e ya d'aukowa Afrah wata doguwar rigar bacci mai kauri da tsawo har qasa ,yayi kan Afrah ya tada ta zaune yana saka mata rigar sae innalillahi wa inna ilaihi raji'un! ke fita a bakinsa,sbd yanda yake jin motsin yazo gab da d'akin su,yana gama sa mata rigar kuwa aka turo qofar d'akin da qarfin tsiya har sae da Afrah dake cikin bacci ta farka a firgice ta daka uban tsalle ta koma bayan farhan ta qanqame shi tana kallon bakin qofar d'akin,cikin muryar firgici tace"innalillahi wa inna ilaihi raji'un!uncle su waye wa'anan"?

*Futha luv💅🏻&Billy giro😊* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 10/25/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*

*Futhalurv.WordPress.com*

*🏅62🏅* Uwayenki ne !ko kinada wata magana ne! saurin girgiza kanta tayi sbd bindigar da ta gani a hannun sa sae duk ta qara qanqame farhan tana kallon halitta irin tasu wacce bata ta6a gani a fili ba sae dai ko film domin girman jiki ne dasu sosai da kuma tsayi kmr samudawa ,haka ko maganar su abin tsoro ce kan kaurin muryar su wacce har vibrate kake ji idan suna magana. D'aya daga cikin su ya daka ma Afrah tsawa sbd amboton Allahn da take ta faman yi cikin muryar kuka,Farhan kuwa tunda suka shigo ya duqar da kansa yana ta addu'oi'n da duk suka fad'o masa a rai sbd kallo d'aya yayi musu ya fahimci sam ba irin wad'anda zai iya fafatawa dasu bane . Sbd shi kanshi ya bala'in tsorata da ganin yanayin su.

wanda ya dakawa Afrah tsawa ne yace"ki mana shiru ba tashin hankali ya kawo mu ba,don haka kajata ku 6ace mana da gani daga d'akin nan idan kuma kasa wasa mu fitar da ku daga duniyar nan gabad'aya, A rikice afrah taja hannun farhan tace"uncle muje dan Allah kar su kashe mu"

Suna xuwa downstairs farhan yace "Afrah yi sauri kije 6angaren gwaggo kafin su fito na samu na tada Amrah, pls uncle ni tsoro nake ji muje tare, da sauri kuwa farhan yaja hannun ta har yana had'awa da gudu gudu sae kawai suka ga an 6alla wutar falon suka ga mutane su uku sae tafi suke ga tulin 'ya'yan fruits da suka ciro a fridge suna sha ,d'yan su yace "weldone 6angaren gwaggo ko, kuje man ai itama tana da nata baqin sae ku tayata tarbar su." Koda yake Ku jira d'ayar sae kuje tare"rufe bakinsa keda wuya sae ga Amrah cikin kuka tana saukowa da gudu a firgice sae kama wuyan rigar baccinta take da ta yage wacce idan ta sake kai tsaye qirjinta ne zai bayyana ,wani daga cikin su ya kalli wanda ke bayanta yace"meye haka aikinda muka zo yi kenan? oga yarnyar ce da taurin kai taqi ta sauko ko kan gadon da take shine na jawota har aka sami akasi rgr ta yage. Yace"naji jeku qarasa aikin mu samu mu kammala da wuri, kar kubar komai da kuka sani na dukiya . Sannan ya kalli su farhan yace"malam bana son ganin mutum a tsàye idan ina zaune don haka ku zauna Ku taya mu shan fruit idan kuna ra'ayi. Idan ba kwa ra'ayi ku zauna kuyi shiru da bakin ku bana son sake jin maganar wani a cikin ku har mu bar gidan ,doka ce idan kuka taka muma zamu taka ,ba mu zo da niyar ta6a lafiyar kowa ba sae wanda ya taka mana doka.

Wannan kenan.

Sunyi kusan minti 20 ashirin zaune a gurin ba wanda yace qala domin kowa na gudun a ta6a lafiyar sa .

Bayan en fashin sun gma duk abinda suke a cikin gidan suka had'u falo d'ayan yace"oga a wancan 6angaren da mukaje matar ta sa6a doka hakan yasa muka harbe ta a qafa,da kyau amma ya akayi ka tausaya mata ai ba a qafa ya kamata ka harbeta ba ka mata harbin da zata bar duniya domin shine hkncin wanda ya taka mana doka, ai ko yanzu oga bata da maraba da matatta dmn tunda na harbe ta bata sake motsi ba har muka gama abinda muke muka fito. Ba qaramin tashin hankali farhan ya shiga ba har ya tashi tsaye yana qoqarin cewa dasu wani abu, ogan yace"wlh zan harve ka ynzu idan baka zauna ba. Cikin kuka da firgicin jin an harve gwaggo Afrah ta jayo shi tana fad'in "uncle dan Allah ka zauna kai ma kar su harbe ka"da qyar farhan ya iya durqusawa kan qafafun sa idanun sa sunyi jajir yana ji kmr ya fasa ihu. Wani daga cikin su yace "oga ai sai mu tafi kafin a fara kiraye kiraye,tkuna wani saqon ya riske ni a waya yanzu. Ya kalli farhan yace"Ku bani takardun kadarorin sa da kuka kwaso " Suna miqa mai ya miqa ma farhan yace"sa mana hannu a kan kowace takarda kuma bana son musu "ko kallon takardun farhan yaqi yayi ya kauda kansa gefe wanda shi kad'ai yasan abinda yake ji game da harbin gwaggo da akayi,ogan ya jawo Afrah da qarfin tsiya har sae da ta fad'a kan jikinsa, ya d'ora mata bindiga akai tare da buge mata baki kan ihun da yaga zatayi, yace"ka sa mana hannu ko kuma na harbeta idan kuma kaqi kaima na had'a da kai" A kan dole farhan ya sa musu hannu kan kowace takarda. Sannan ogan ya saki Afrah da ke ta faman kuka ciki ciki. Yace"then wace ce matar ka a cikin en matan nan? Kai tsaye ya nuna Afrah sbd sanin alqawarin da yayi ma Amrah na ba wanda zai san da auren su,,, Afrah kuwa kallon mamaki take yiwa farhan tace"uncle..... Shiiii!ba sai kince komai ba ai na fahimci ba gsky bane...da gaske yake yi oga domin tare muka same su d'aki d'aya, nop ai naga lokacin da ya leqo mu ta window ba mamaki shi ya sameta a d'akinta ya sanr da ita abinda ya gani. Ya kalli Amrah yace"ke baiwar Allah gaya min gaskiya wace ce matar sa a cikin ku"shiru tayi tana tunanin in ma mugun abu zasuyi wa Afrah gara kawai tace ita ce"tsawa ya daka mata yace"dake nake magana! a rikice tace"nice matar sa"da sauri farhan ya kalleta tayi saurin had'e tafukan hannayenta alamar don Allah kar yace komai,ogan yace"laifinta kake gani don ta fad'i gaskiya,ai kuruwa kayi dmn da ace munje da wannan muka samu ba itace matarka ba zamu kashe tane kaima mu dawo mu kashe ka mu kuma d'auke matar ka,duk yana magana ne yayinda yake nuna Afrah. Sannan yace da yaransa "kuja matar tasa kuzo mu wuce "a rikice farhan ya miqe ganin sunja Amrah yace"Dan Allah ku bar mu haka mana meyasa zaku tafi da ita wannan wane irin rashin imani ne..... qarasa zancen sa keda wuya yaji harbi ,ihu Afrah ta saki tayi kan farhan da ya fad'i tana kuka cike da firgici,da qyar ya iya nuna mata Amrah wacce har sun fita da ita daga cikin falon yace"Afrah kije Amrah na magana, da gudu ta tafi ta riqo hannun Amrah da take miqowa,kuka take sosai tana so zatayi wata magana ta fasa tare da saurin cewa"Afrah ki koma ki fitar da uncle sun saka wuta" gudu take har tana hard'e qafafu ta samu ta koma daga cikin falon tana jijjiga farhan da kad'an ya rage ya rufe idonsa tace"uncle don Allah kar ka rufe idonka ka tashi mu fita sun saka wuta uncle "Afrah ki fita kawai kinga wutar ta kawo a bakin qofa ki tashi ki fita !a rud'e ta kalli bakin qofa wanda hakan ya bata tabbacin zagaye gidan sukayi da wuta. Cikin kuka sosai ta juyo tana fad'in "uncle ka tashi mu fita kar wutar ta fara yawa" ta fad'i hakane yayinda take qoqarin tallaboshi yayi saurin dafe inda aka harbeshi yace"Afrah bazan iya d'agawa ba ki tafi kawai ,wani irin kuka ta fashe dashi tace"uncle ni bazan fita ba sae tare da kai,idan kuma baza ka iya ba sai dai mu mutu a tare"Afrah ko na fita ba lallai bane na rayu ,sbd sun harve ni inda bana tunanin zan rayu....a'a uncle zaka rayu ka tuna kaifa ka ce min ba a yanke qauna daga haramar ubangiji,,haka ne Afrah amma.... sae kuma ya kasa iyar wa sae idanuwansa dake qoqarin rufewa , murya can can qasa yace"pls Afrah ki fita nace"shine abinda ya furta na qarshe se idanuwansa suka rufe ruf..... Wayyo Allahna uncle dan Allah ka bud'e idonka kar ka tafi ka varni!. Kuka ta shigayi sosai tana jijjiga shi tàna kiran sunan shi amma ba alamar zai motsa ga wutar duk ta zagaye gidan tana ci gaba da ci.

*Billy giro😊&Futha Luv💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 10/25/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*

*Futhalurv.WordPress.com*

*```🏅63🏅```* Rungume sa tayi qam a qirjinta tana ta kuka a cikin kukan ne taji yayar mutane a waje sae taslima suke . Da hanzarinta ta tashi domin ganin wanda ke shigowa wato JB da mahaifin sa taje ta rungume Abban Jb tana kuka tana fad'in"Abba sun kashe min uncle ,sun kashe min gwaggo sun kuma tafi da Amrah, ta qarashe maganar cikin kuka sosai. Mahaifin jb wanda ba kowa ya sanar dasu halin da ake ciki ba face mai gadi da ya samu ya farfad'o kan wata powder da suka shaqa masa ya some shine yana farfad'owa ya lalubo er wayrs da en fashi suka manta basu kar6e ba ya kira mahaifin JB kasancewar yana da numbar sa ,sbd shike masa gadi da rana sannan yazo nan yayi na dare.

Komai Abban Jb ya kasa cewa sbd jimamin da ya shiga ciki,en sandan da ya kira ne suka zo suna fad'in Alhj kunyi gigin shigowa fa wutar tana ci sosai, yace "dole ne dmn duk na rud'e naga na ceto ran 'yayana. Yana gama fadar haka en sanda suka kama aka fitar da farhan wanda da qyar suka iya tsallake wutar suka fito sannan aka nufi 6angaren gwaggo wacce still tana nan yanda take, ita ma d'aukar ta akayi aka sata cikin mota.

Asibiti aka tafi dasu wanda cikin gaggawa aka kar6e su .

Bayan an shiga theater room dasu ne Abban JB ke waya da commissioner en sanda yana sanar dashi halin da suke ciki yayinda yake son ayi gaggawar tura motar en sanda a tare hanyar fita gari da ta shiga a kuma yad'a en sanda ta koina ko za'ayi nasarar gano su kafin su illata Amrah. Haka kuma yayi waya da en kashe gobara kan suje su kashe wutar da ke ci gidan farhan. Sannan ne ya samu er natsuwar kallon Afrah da JB keta faman rarrashi,shima ya saka nasa bakin suna kwantar mata da hankali.

Ba qaramin jimawa akayi ba domin tuni gari ya waye sannan aka fito daga theater room ,Afrah ta tashi da hanzarinta ta nufi gun fu'ad dake cire hand gloves tace"uncle dan Allah kar kace sun mutu"kwantar da hankalin ki dmn ba wanda ya mutu a cikin su ,zama ki iya zuwa gun farhan sbd har yanzu gwaggo bata farfad'o ba but anyi mata aiki an cire harsashin da ke cikin qafarta, haka nan bada jimawa ba inshAlh zata farfad'o.

Da gudu take zuwa d'akin da ya nuna mata farhan yake, sae dai ba qaramin tausayi ta bashi ba domin ko farhan d'in ba wai ya farfad'o bane.

Da shigar ta d'akin ta nufi gadon da farhan yake se ta tsaya cak duk wani kuzarinta ya rage, sae kallon sa take da tsoro sbd bashi da maraba da gawa,gashi duk a tunaninta zata zo ta same shi ya farka.

Wani tunani ne ya fad'o mata a rai wanda yasa ta fashe da wani sabon kuka, taje a hankali ta kwanta kan jikin sa tana ci gaba da kukan. Ta kalli fu'ad da ya shigo shida JB da kuma Abban JB tace"uncle fu'ad ya naga uncle bai farka ba kwata kwata baya motsi har yanzu?zai farka kinji... yaushe?shiru yayi sannan yace"idan allurar da aka masa ta sake shi,inshaAllah zai farka indai har aikin da aka masa bai zo da wata matsala ba, don haka ki daina ta6a sa hka sbd kinga kusa da zuciya ne aka masa aiki akwai had'ari sosai ga ta6a gurin. Tace"to zan iya zama kusa dashi ?eh ba matsala ,nan ta share hawayenta taja kujera kusa dashi ta zauna tana jiran farfad'owar sa.

*Billy giro& Futha luv😊* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [10/26/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*

*Futhalurv.WordPress.com*

*```🏅64🏅```* Tana nan zaune sae kallon farhan take har dai gunda aka masa aiki wato inda aka cire masa harsashi, haka tayi ta bin jikin sa da kallo sae tunanin rayuwar su ta jiya take kafin suyi bacci sae gashi yanzu shine a kwance komai baya iya yi wanda idan aka ce mata ya mutu bata san ya zatayi ba. Hawaye ne ke silalowa a hankali kan kumatun ta ,ta share hawayen tana tuna ko sallah bata yi ba gashi se tayi wanka wanda kan tunanin rayuwar su ta jiya ce ta tuna mata da hakan,sae kallon rgr jikinta tayi tasan ba wanda ya saka mata ita face farhan,Allah yaso ta farhan mutum ne mai yawan ibadah da bai maida dare domin bacci kad'ai ba, da ba don hakan ba da sun riske ta a yanda take, da baqin cikin zai fi mata yawa a rayuwa wanda har ta mutu bazata ta6a manta hakan ba ,still baza ta ta6a manta hakan ba domin ko a tahiri bata ji wanda irin wannan mummunan abu ya faru dasu irin yanda ya faru dasu kai tsaye ba,,haqiqa Allah mai jarabatar bawan sa ne ga wanda yaga dama ga kuma wanda yafi so domin ya qara gwada imanin sa,hakan yasa baza tayi kuskuren tunanin cewa don Allah baya son su ne ya musu haka. JB ta kalla wanda tun d'azu yake ta faman kallonta yayi saurin kauda idonsa sbd ba a son ransa ya tsare ta da ido ba. tace"uncle jB ina son nayi sallah amma bana da hijab kuma.....sae tayi shiru tana qarewa d'akin kallo ganin toilet yasa ta sauke ajiyar zuciya,yace"sae kuma me Afrah?ta duqar da kanta tace"sae kuma tufafi "yace "to"ya kama hanya zai fita Abban shi yace"gidan nasu zaka tafi ne?Aa wai da zan tafi gida na kar6o mata a gurin Nina ,Aa muje gidan nasu kmr wajen gidan kad'ai ya qone, shiyasa nake son a rufe musu d'akuna kasan wasu na zuwa da sunan taimako alhali ba haka bane, marasa imani ne wad'an da basa tsoron had'uwar su da ubangiji bare suji tausayin halin bayinsa da suka shiga ciki,sae ma qoqarin qara saka su wani halin suke na ganin sun qarasa kwashe d'an abunda ya rage musu.

Suna fita Afrah ta fad'a toilet tayi wanka tana fitowa ta nemi guri ta zauna jiran dawowar su,wanda bata jima da xama ba sae ga JB ya dawo ,ta kar6i kyn tana masa godiya, har zai fita sae kuma ya tsaya ya d'an juyo kad'an yace"shike nan kike buqata ko da wani abu? Aa bana buqatar komai,, but ya kamata kici wani abu Afrah,bana jin yunwa...Aa bari dai naje na kar6o miki a gida nasan sun isa kammala break fst. Bata iya ce masa komai ba ta barshi ya fita , amma sam ita bata jin zata iya cin wani abu, domin tashin hankalin da take ciki ko yunwa ma bata ji, fatar ta d'aya Allah ya farfad'o da farhan da gwaggo ya kuma sa a gano Amrah ba tare da sun mata komai ba. Bata damu da hawayen da taji suna sauka kan kumatun ta ba ta nufi toilet domin saka tufafi. Bayan ta fito tayi sallah, ta jima tana kai kukanta a gurin ubangiji wanda ako yaushe yana kusa da bawansa musmman mafi kusa dashi wato mai yawan ibadah da kuma yawan ambaton sa,wanda tasan yana jinta kuma zai share mata kukanta inshaAllah.

Bayan ta gama taje kan kujerar da ke kusa da farhan ta zauna tana tunanin ko ya Amrah take ciki yanzu. ** ** ** 6angaren Amrah kuwa tunda suka tafi da ita kuka take tana tunanin wane hali Afrah ,gwaggo ,Farhan suke ciki yanzu,ko Afrah ta sami fitar da farhan? shin ita gwaggo fa tana raye ko kuwa ta mutu?,ya mahaifinta zai ji idan yaji an tafi da ita a kasancewarta na 'ya qwaya d'aya tal a gunshi ?haka take ta yiwa kanta tambayoyin da ba amsa, sae kuma ta sake fashewa da wani sabon kuka wannnan wace irin musiba ce ta same su haka a lokaci d'aya.

Duk tana wannan tunanin ne a cikin wani d'an qaramin d'aki mai duhun gaske da komai bata gani hatta tafin hannun ta ,ga gurin very stationary , motsin komai ba a ji hakan yasa ta kame guri d'aya cike da tsoro har bata son yin wani dogon motsi.

Yini akayi zungur ba wanda ya farfado tsakanin gwaggo da farhan iya damuwa Afrah ta damu domin yinin ranar ko abinci taqi taci sae kuka take tana magana da fu'ad da ya shigo d'akin dmn ya qara kwantar mata da hankali bata bar yace komai ba ta tashi tana kuka cikin dasasshiyar murya tace "uncle fu'ad dan Allah ka snr dani gsky wai ko basa raye ne ake 6oye min"Afrah kiyi haquri ki kwantar da hankalin ki lokacin farfad'owar sune bai yi ba,uncle fu'ad wace irin allura ce da tuni an gama masa aiki amma har yanxu bata sake shi ba,gashi nan tun safe still bai motsa ko qaramin yatsan sa ba at all ma ko numfashi bana ganin yana yi,haka ma gwaggo har yanxu ko damar ganinta ba'a bani ba. Cikin kuka sosai ta qarashe mgnr. Shiru fu'ad yayi cike da tausayi domin tuni gwaggo ta farfad'o amma wani tashin hankali ne idan Afrah ta ganta sbd numfashi take sama sama kmr wacce zata mutu kan hawan jinin da yayi mata mugun kamu shiyasa aka mata allurar bacci. Da alamar rarrashi fu'ad ya kalli Afrah wacce kallo d'aya xakayi mata kasan a galabai ce take da jin yunwa duk ta wani hargitse ta fita hayyacinta kmr ba ita ba. Da sauri ta kai xaune sbd jirin da ya d’ebe ta ,ba shiri ta riqo hannun farhan gam sbd yanda take ganin komai na d'akin na juya mata. Sulalewa take qoqarin yi sae kawai taji hannun farhan da ta damqe yana motsawa a hankali.

*Billy giro 😊&futha lurv💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [8:36PM, 10/27/2016] Billy giro😊: 10/27/2016 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅

*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*

*Futhalurv.WordPress.com*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull