Afra ko amrah complete - Chapter 23
Afra ko amrah complete Chapter 23: Afra ko amrah complete Chapter 23. Koda ta shiga d'akin farhan ta samu ya shiga toilet nan ta wuce d'akinta ta fad'a…
4,410 words
Koda ta shiga d'akin farhan ta samu ya shiga toilet nan ta wuce d'akinta ta fad'a wanka. Bata jima sosai ba ta fito ta shafe jikinta da turarukka taje ta bud'e wardrobe zata nemo kayan bacci ,taji an rungumota ta baya qamshin turaren da taji ne ya fahimtar da ita farhan ne,yace"my Afrah tuni ke nake jira har na qagu gashi tunda na fito wanka nake fama da towel ina zaman jiran ki. Bata ce masa komai ba sae towel d'inta da ya zare take kallo yana sauka a hankali kan jikinta ,bata damu da hasken da ke d'akin ba sbd tana sanye da pant, ta jaye hannun sa da yake wasa dashi kan qirjinta tasa hannuwanta ta kare qirjin sannan ta juyo ta manne qirjinta da nashi kafin take zare hannunwanta ta d'ora su kan kafad'un sa tare da goga hancinta akan nashi sannan ta d'ora masa kiss a hankali kan lips tace"uncle kasan fa ya kamata na ajiye duty na bama Amrah , ya kamata kayi tunani ka kuma sa adalci a tunanin ka, wani abu yaji kmr yayi kuka dmn tsananin buqatuwar da yake ciki,,rgr bacci ta jawo ta saka tace"me kace? "haka ne" shine kawai abinda ya iya ce mata, yana ji ta masa bye bye kan zata je 6angaren gwaggo ta kwana. Binta kawai yayi da kallo har ta fita yana mai tunanin makomar sa a yau da kuma mamakin kansa da yanzu yake saurin jin buqatuwa kmr wani jarababbe akasin da da baya da haka. Inda yau har jin yake kmr komai zai iya faruwa dashi idan bai sami mace ba.
Afrah kuma tana fita taci karo da Amrah zata fita taje 6angaren gwaggo tace"wlh gwara ma ki koma dmn na sanar da uncle yace shike nan kinga kenan ni zan kwana a 6angaren gwaggo ,Amrah tace"pls Afr....kafin ta qarasa tuni Afrah taja musu qofa ta rufe,Amrah tayi tsaye sororo tana kallon qofar d'akinta,tana tunanin yanda zata kwana ciki ita kad'ai,kan tsoron abinda ya faru dasu da kllum cikin mafrki take har jiya d'in ma da tasan an kama su.
*Billy giro &Futha Luv* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [11/1/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*
*Futhalurv.WordPress.com*
*```🏅71🏅```* Farhan yaje d'akin shi ya saka jallabiya ya nufi downstairs dmn kashe wutace nan ya hango Amrah sae safa da marwa take tana tunanin yanda zata kwana ita kad'ai ,tana hango farhan tazo cikin sauri tace"pls uncle dan Allah kace Afrah ta dawo wlh bazan iya bacci ni kad'ai a d'aki ba, nafi so na riqa bacci a gurin gwaggo har lokacin tafiya ta yayi" shiru yayi kafin yake cewa "kinsan fa....no uncle baza ta gane ba inshaAllah kawai dai a nuna mata ni zan riqa kula da gwaggo ita kuma ta riqa kula da kai, pls uncle kaji wlh yanzu bazan iya bacci ni kad'ai ba tunda abun nan ya faru sae mafarki nake kullum, ta fad'i maganar ne kmr za tayi kuka, sae duk yaji ta bashi tausayi da kuma tausayin kanshi idan Afrah ta kwana gun gwaggo yace"shikenan jeki sae kicewa Afrah tazo. Sosai taji dad'i har tana mishi godiya.
Ba 6ata lokaci sae ga Afrah ta shigo gidan tuqun tuqun da rai tace"uncle wai da gske ne kai kace na dawo ?eh ni nace.....Uhm Uhm amma ba a kyauta min ba ni shike nan bazan riqa bacci a gurin gwaggo ba,duk gidan nan kowa ana masa abinda yake so amma banda ni. Cikin kuka sosai take maganar sae doddoka qafafunta take a qasa tana tafiya kmr wata mai matching song da haka har ta haura sama zuwa d'akin ta. Sae a lokacin farhan ya d'auke idon sa a kanta ya kashe wutace ya rufe qofa ya haura sama ya same ta kwance ruf da ciki tana kuka, yaja hannunta tare da fad'in "yi haquri tashi muje d'akina" ni bazan je ba ai bani keda duty ba ,ai yanzu ba a dawo kan duty ba tukun sae gwaggo taji sauqi, meye had'in gwaggo da dutyn mu,koma yayane yi hqr muje kinji, maqale kafad'a tayi tare da matsawa nesa dashi nan ya tankwahe hannayen jallabiyar sa yaje ya d'auke ta cak tare da fad'in "Afrah wannan rashin nauyi haka sae kace ba kya cin abinci kulum. Zizzille masa ta kama yi har suka isa d'akin shi ya kaita kan bed sae abubuwa yake mata tana kukan shagwa6a tana tirje mai har ya samu ta bada kai bori ya hau sbd irin girman abubuwan da ya shiga yi mata masu gusar da hankali kai tsaye.
Washe gari da asuba ya dawo daga masallaci ya same ta kan sallaya yaje ya zauna kusa da ita ta kwanta kan jikinsa kmr wata mara lafiya ,tausayin ta yaji ya d'ago fuskar ta yace"my Afrah lafiya ?qara lafewa tayi a jikinsa tare da fad'in "ba komai uncle"um um Afrah jikinki ya nuna ba kya jin dad'i gaya min gaskiya kinji,a sanyaye tace" ni bacci kawai nakeji" Nan ya cire mata hijab d'in jikinta ya kaita kan bed ba jimawa bacci ya d'auke ta.
9:30am A 6angaren Gwaggo sukayi break su dukan su har ma fu'ad da yazo duba gwaggo.
Bayan sun kammala ne Afrah ta tashi tayi taga taga zata fad'i farhan yayi saurin kama ta yace"Amai zakiyi? girgiza masa kai tayi had'e da dafe goshin ta,tace"jiri ke d'iba na shine nake son naje na kwanta. Yace"ok to muje daga ciki. Nan suka shiga bai fito ba sae da tayi bacci.
Fu'ad yace"ni zan tafi, farhan yace "idan asibiti zaka je jirani muje bcs ina son na shiga office na duba wasu abubuwa.
Tafe suke cikin mota fu'ad yace"me yake damun Afrah ne haka da har take jin jiri ka dubata kuwa"ai ba abunda zan duba ta bane, yau ma da amai ta tashi sosai bayan kwanciyar mu sallar asuba,da farko ma na d'auka gajiya ce se tace min bacci take ji, wanda na tabbatar har da gajiya ta dai 6oye min ne,gajiyar me ke nan? hm sirri ne fa wannan , yauwa dama ina son na tambaye ka, wani abu ke damuna sosai wato desire na rasa meyasa bayan da ba haka nake ba ,gashi duk abun ya motsa min bana iya haqura sae nayi ta wahalarda er mutane, kmr ya matar ka ce fa, haba fu'ad ko mata ta ce ai akwai tausayi ina saurin lalubo ta.... To meye ciki kasan fa sex qarin lafiya ne shiyasa ake so atleast a sati mutum yayi sau biyu,,,but duk da haka Afrah nawa ce kawai don tana da haquri ne wlh amma sam bana jin dad'in hakan dmn bana son ina takura ta. Farhan kenan to ya zakayi tunda baka iya haqura sae kuma idan aure zaka qaro sae ka rage mata wahalar, kaji ka dan Allah bari wannan zancen tun kafin nasan meye aure kasan bana ra'ayin mata biyu,to ya zakayi? Magani kawai zan nema nasha ko kuma na yawaita yin azumi ,hm lallai to kai ya akayi ka dawo haka bayan kace da ba haka kake ba, but ya ma za'ayi ka fahimci ba haka kake ba bayan marigayiya Amrah baka wani jima da ita ba ta rasu?na fa sani amma wlh ba haka nake ba dmn yanzu haka bani da wata buqata da ta wuce na kasance tare da mace bayan kuma yesterday night i slept with her,kuma fa not only one round, kaga kuwa akwai matsala don ni bana son kaina haka wlh,,hm farhan nafa gano inda matsalar take ina wannan allurar da kace min kana yi ta kashe desire tun kafin dawowar ku da Oman, eh na fahimta ,yauwa to ai kasan tana da nata effect ga wanda bata kar6a ba. Kaga kai yanzu bata kar6e ka ba shine kana daina yin allurar duk wata desire da tasha kwantar ma a baya sae ta dawo tana yawan motsa maka anyi ba ayi ba kenan, but ai kasan tablet d'in da ya kamata ka kasha komai ya dawo maka nrml,,off course na sani ,amma kasan sam banyi tunanin wannan allurar ce keta wahalda ni ba se yanzu,ashe Allah ya so ka dana fahimtar da kai, wlh dana wahala na kuma whlda er mutane in ta kasa haqura azo ayita samun sa6ani. Yanzu alhmdlh matsalata da nake tunani ta kau inshaAllh har dai idan naci sa'a maganin yayi saurin kar6ata. Fu'ad yace"ni yanzu farhan matsalata d'aya shine nayi aure", to ba dai kaine ba sae kace wani wanda aljana ta aura kaqi kayi aure kuma ko mgnr sa baka yi, hm bari kawai kai dai wlh yanzu sosai nake son aure sbd a cikin en kwanakin nan na kamu da soyayyar wata silent gal wlh ba ruwanta gata beauty n cutie kmr ita tayi kanta, dry farhan yayi yace"koma yayane nasan baza ta kai my Afrah ba don babyn Allah ya mata kyau ksn...hm yanda kake taqama da Afrah nada kyau haka ita ma yrnyr akwai kyau wlh,amma gaskiya Afrah ta fita haske,, to wace ce ita?kasan ta amma ba zan gaya maka ita ba yanzu ,dmn ko ita bata sani ba na fison sae komai ya daidaita tukun,to Allah ya kaimu, amin,, but idan ka samu yarnyar nada wanda take so fa? Banga alama ba haka kuma inshaAllah zata soni bcs tun rnr da na fara jin sonta na fara roqon Allah yasa ta soni ko bai kai nawa ba dai.
To amin. Ya fad'i haka ne dai dai sun iso asibiti fu'ad ya parka mota suka fito kowannen su ya nufi nasa office.
Da dare Afrah ce sanye da er finkcikar rgr bacci kwance a jikin frhn sae kuka take yana murza mata bayanta da yayi mata allura,yayi rarrashi har ya gaji taqi shiru sbd bata so allurar ba ya matse ta yayi mata. Sae da ta gaji don kanta ta daina kukan ta tashi a hankali tare da share hawaye tana kallon farhan da idanuwan sa suke a rufe, tace"pls uncle ka bud'e idon ka muyi magana" a hankali ya bud'e idanun shi yace "eheem ina jinki "sosai ta marairai ce fuska tace"dan Allah gobe uncle kar aje dani kotu sbd tsoro nake ji,dmn duk na tuna da zuwa kotu sae naji fad'uwar gaba,,Afrah zuwa dake dole ne fa, um um nidai a bar ni gurin gwaggo na kula da ita,idan ana son magana dani sae a kira ni ta waya kaji uncle, jawota yayi ya kwantar yace"lokacin bacci yayi Afrah yi bacci"uhm uhm nida bani ma da lafiya kuma sae ace wai sae an tafi dani" cikin kukan shagwa6a sosai ta qarashe mgnr. Farhan yace" kiyi bacci nace Afrah ki daina zancen nan yau bacci nake ji sosai ki bari da safe mayi magana kinji,gyad'a masa kai tayi tana mai share hawayenta,ya d'ago ta ya qara share mata hawayen tare da d'ora mata gud nyt kiss kan lips sannan ya rungumeta yana shafa bayanta da haka har sukayi bacci abinsu.
*Billy giro &Futha Luv* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [11/2/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*
*Futhalurv.WordPress.com*
*```🏅72🏅```* Washe gari Farhan ne ke nmn Afrah saqo saqo har da su bud'ar wardrobe don yasan ba qaramin aikin ta bane , zata iya 6uya a ciki dn kawai kar a ta tafi da ita kotu. Haka kuwa akayi dmn yana bud'e wardrobe ya hango ta can lungu ta qundundune cikin blanket kmr wani tulin wanki sbd har fuskar ta ba a gani amma abinda bata sani ba shine babban yatsanta na qafa ya fito.. A hankali ya tallabota ta buga ihu a firgice sbd har ta fara bacci nan gurin da take ,tana ganin farhan ne ta fara kukan shagwa6a tana kai masa duka a qirji wai ita ya sauke ta, bai direta koina ba sae kan bed yana ta fmn dariya dmn ta mugun bashi dariya,sae qoqarin riqe mata hannaye yake amma taqi bari sae ci gaba take da dukansa dmn tayi mugun jin haushin gano ta da yayi. Da sauri ya riqe mata hannu tare da daka mata tsawa sbd ta dake shi a jikin aikin sa duk da cewa dukan shagwa6a ne amma yaji zafi,kuka ta fashe dashi tana roqon yayi haquri ta manta,bai yi fushi da ita ba sbd yasan sosai tana kiyayewa dn duk wani rungumo shi da take da kwanciya a jikin sa da kulawa take yin komai bata yarda ta ta6i gefen, Sauke hannayenta yayi da ta riqe kunnuwanta kan haqurin da take bashi,ya matsa gab da fskrta ya kama kumatunta kmr wanda zai share mata hawaye ta lumshe idonta a hankali sbd bakin su da taji ya had'e guri guri d'aya. Basu fi minti biyu ba ya d'ago yana share mata hawaye da babban yatsan sa,snn ya kwantar da ita gefen qirjnsa yana shafa bayanta sae d'akin yayi tsit kmr ba kowa can Afrah ta katse shirun da cewa"sorry once again uncle"
Yatsun sa yakai ya lotsa kumatun ta, yace"ba komai" murmushi tayi ita ma takai hannu ta lotsa kumatun sa tare da d'ora masa kiss, murmushi yayi tare da kai yatsan shi yana shafa lips d'inta sae matsawa yake qarayi kusa da ita cike da son ya had'e bakinsu , Afrah tayi saurin kauda fuskar ta ta tashi tana fad'in "bari nayi wanka uncle". Binta yayi da wani kallo har ta shige toilet ya sauke ajiyar zuciya ya kwanta tare da lumshe idon sa.
Sosai ta jima gurin wanka tana cikin wankan ne taji ihun Amrah,a gaggauce ta qarasa wankan ta zaro towel ta d'aura ta fito.
Tana shiga d'akin Amrah ta samu farhan ya gama rufe buttons d'in rgrsa zai fito ta bishi da kallo ya fita sauri sauri, ta maida dubanta kan bedsheet d'in Amrah da ta hango d'igo d'igo jini,nan ta shiga tunanin kaddai ace rashin haqurin uncle ya fara yawanda har baya iya bin mace a hankali har sae yaji mata ciwo,fitowar Amrah daga toilet ne ya katse mata tunani,jiki sanyaye ta qarasa gurin Amrah tana kallon yanda jikin amrah ke rawar tsoro tace"uncle ne yaji maki ciwo ko? tayi saurin girgiza kanta tace"ciwon me ,me kika gani?ta nuna tace"wancan jinin da ke kan bed d'inki na gani,,, da sauri Amrah taje ta yaye beedsheet din ta dunqule tana fad'in"can't u see it clear it's just red lipstick fa" ta fad'i haka ne tana faman qirqiro murmushin da bai kai ciki ba. Afrah fita d'akin kawai tayi ta nufi d'akin farhan bata ganshi ba sae muryar sa take ji yana waya a toilet corner. Kan ta qarasa har ya gama wyr ya fito taje ta riqa hannayen sa tana mai kallon cikin idon sa tace"uncle mene kake fad'in a bisa qaddara ne hakan ta faru kuma har kana fad'in baka san yanda zaka yi ba yanzu? My Afrah am sorry wannan ba mgnr ki bace kinji,to uncle meyasa ka ma Amrah haka? me tace miki nayi? Bata gaya min komai ba amma...sae kuma tayi shiru tana kallon shi sae yi yake yana share gumi kmr wanda ke cikin tsananin tashin hankali, ta marairai ce fuska tace"wai uncle me yake faruwa da kaine? Ba komai Afrah kuyi sauri ku shirya ku same ni 6angaren gwaggo amma ki tbbtr kun rufe 6ngrn kafin kuke fitowa.
Yana kawowa nan ya fita ya bar Afrah da tunani.
Bayan sun shirya suka nufi 6angaren gwaggo,suka samu farhan na cewa fu'ad "kasan abinda ya faru yanzu ya xama dole muje da gwaggo sbd had'ari ne barinta a nan"gwaggo wacce ta fito daga d'akin qurya tana tura kanta cikin wheelchair tace"farhan ni kuma meye sai anje dani ko kuma ganin kake idan aka barni bana iya yin komai shi ne kake cewa barina had'ari ne? Gwaggo sam ba haka bane wlh...to mene ne farhan? shiru yayi ya ciro handkerchief ya share gumi ya kalli Amrah wacce ke tsaye kusa da Afrah yace"ba komai gwaggo kawai dai mu tafi. Afrah ta kalli Amrah ,Amrah tayi saurin kauda fuskar ta tana kame kame kmr wacce bata son aga wani abu a jikin fuskar ta, hakan yasa Afrah ta tsure fuskar da kallo sae ko ta hango gefen bakin Amrah ya fashe har ma yana ftr da jini still ,a hankali Afrah ta kai yatsanta ta shafo jinin tace"Amrah wannan jinin fa ko shima red lipstick ne? Komai bata ce mata ba se riqo yatsan Afrah tayi tana share mata jinin, grn haka ne Afrah taga wuyan hannun Amrah jajir har ya kumbura da gani damqar qwarai aka yiwa hannun, ta shafo gurin tace "Amrah me ya same ki ne wai kike 6oye min? Ba komai ,shine abinda ta fad'a cikin muryar kuka har ma hawaye na d'iga kan hijabinta tayi saurin share hawayen ta 6oye hannun ta cikin hijab . Farhan ne yazo kusa dasu Afrah tayi shiru ta fasa tmbyr da tayi niyyar sake yima Amrah sbd duk maganar nan da suke qasa qasa ce ba mai jin su . yace"Afrah bani makullin gida,ta miqa mai suka fito su dukan su har gwaggo da fu'ad ke turawa kan wheelchair.
Tafe suke cikin mota Afrah sae yi take tana kallon farhan da still fmn share gumi yake ga damuwa sosai tattare a fuskar shi. Ta riqo hannun sa qasa qasa cikin muryar kuka tace"Dan Allah uncle ka gaya min me yake damunka kaida Amrah na ganku cikin damuwa sosai ita Amrah har ma kuka take yi". Kallon ta yayi cike da qwalla a idon sa ,se kuma ya kauda fuskar sa gefe hawaye na gangarowa a hankali kan fuskar sa.
Sorry 4 dis one am too busy.
*Billy giro *&Futha luv* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 11/4/2016] Billy giro😊: 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*
*Futhalurv.WordPress.com*
*```🏅73🏅```* Uncle kuka kake yi kaima. Share hawayen yayi sannan ya juyo tare da girgiza mata kai alamar kar tayi kuka dmn ya fhmci cike take da son tayi kuka. Ganin yanda ta le6ace baki zuwa kukan yasa yayi saurin nuna mata kotu yace"kinga mun iso kotu kuma da kinyi kuka ke za'a fara kira shaidu,sannan kuma bazan gaya miki abinda ke faruwa ba, da qyar ta iya had'iye kukan ta riqe hannun sa gam har suka shiga kotu.
Bayan an hallara gabad'aya gurin yayi tsit ana sauraren tambayoyinda lauya keyiwa leesa kmr haka: Baiwar Allah kotu tana son jin ainihin cikakken sunanki. Sunana Khaleesat muktar mai dala.
Khaleesat rnr juma'a guraren qarfe 12 da wani abu an ganki cikin mota tare da Amrah wacce aka sha nema kan sace ta da akayi a dalilin fashin da akayi a gidan farhan. Sae gashi an ganki tare da ita kin shiga da ita cikin wani daji mai nisa kika faka mota had'e da kiran wani a waya inda ba jimawa ya fito tare da mahaifin Amrah wanda shima ya kwana ba a ganshi ba. Sannan bayan kin saki Amrah ita da mahafin nata sae kika yi tafi , hakan yasa gardawan en fashi suka shiga firfitowa ba adadi har kina yaba qoqarin su da cika aikin su,at d end baku bar gurin ba en sanda suka kama ku aka tafi daku police station,inda bayn an tuhume su sukayi bayanin cewa fashin da akayi a gidan frhn kece kika tura su, amma ke kince sam ba haka bane. Shin idan hr ba haka bane a ina kika samo Amrah, ko zaki iya yiwa kotu bayanin inda kika samo ta ? Shiru leesa tayi kmr baza ta ce komai ba can tace"Bazan 6oye komai ba zan fad'i duk abinda na sani. Tabbas nice na tura en fashi gidan farhan ban kuma yi haka don komai ba sae don sani akayi. Shin ko zaki iya snr da kotu waye ya saki?eh wata mata ce mai suna hajiya Aysha wacce ynz hk tana zaune a cikin kotun nan. To da wane dalili ne yasa ta tura ki ita bata je tayi aikin da kanta ba? Zan so ta fito kuji bayani daga bakinta sbd zaku fi fhmta. Lauyan ya kalli aqali da ke rubuce rubuce ya nemi alfarma kan a bashi dama ya fitar da matar.
Bayan an kirata ne gwaggo na ganin ta ta miqe zumbur cikin tsananin mamaki har tana qoqarin fàduwa sbd qafarta da ke ciwo da alama ta manta, se fu'ad ne ma yayi saurin kamata kar ta fad'i. Farhan da Afrah ko se mamakin suke ko gwaggo tasan ta ne.
Sae da lauya ya tambayi sunan mtr sannan yace"shin abinda malama Khaleesat ta fad'a gaskiya ne? Eh gaskiya ne ni na tura ta,sbd na jima ina son kar6ar dukiyar d'ana amma hakan ya gagare ni a bisa cin amana da kuma qiyayyar da en uwan mijina keyi min kwata kwata basa sona shine suka rabani da dukiyata da kuma d'ana bayan rasuwar mijina. Nayi baqin ciki sosai dmn har kotu naje amma ba a bi min haqqina ba shiyasa ni kuma nayi abinda nake ganin shine dai dai wato na kar6a ta qarfi. Ikon Allah Hajiya Aysha sosai na fahimci zancen ki amma kuma waye d'an naki ko kuma kina son ce mana ke mahaifiyar farhan ce?tabbas ni mahaifiyar farhan ce.....qarya ne ke ba mahaifiyar sa bace! tuni mahaifiyar sa ta rasu,lauya yace da gwaggo ki yaye kotu ba guri ne da ake sako magana haka kawai ba sea idan an umarci mutum, sannan ya juya gun mtr da ya kira hajiya Aysha wacce ke magana cikin muryar kuka tace"ka gani ko tana d'aya daga cikin dangin mijina da basa qauna ta ko kad'an shine har suka laqa min mutuwa har d'ana ya d'auka cewa dgske bana raye dmn tun yana d'an qanqani aka rabani da shi.
Sosai farhan ya shiga rudu da mamaki yana kallon gwaggo . Lauya yace"hajiya Aysha da wane dalilin en uwan mijinki suka tsane ki har suna laqa miki mutuwa? Ba wani dalili haka kawai tunda aka auro ni basa sona amma mahafin farhan sosai yake sona dmn har ya mutu baya da burin da wuce ya faranta min rai. Shine yana mutuwa en uwan shi suka min korar walaqnci inda da kukana da komai nke roqoñ su barni naje da d'ana amma suka qi haka na tafi ban san inda zanje ba dmn bani da kowa a duniya sae Abban farhan kuma ya mutu ya barni. Mutum d'aya ya tausaya min wato abokin sa marigayi Alhj sadiq ya taimaka min da masauki ba tare da kowa ya sani ba inda akai akai yana zuwa muna gaisawa kuma duk wata lalura shike yimin har akayi shekaru . Ranar kwatsam ina cikin bacci naji mutum akaina da rana tsaka a firgice cikin tsananin mamaki na tashi ina kallon Alhj sadiq wanda kwata kwata kmr baya cikin hayyacin sa. Duk yanda naso na kauda abinda yaso aiwatarwa dani hkn ya gagara sbd qarfi ya nuna min ya biya buqatar sa. Kmr kar ya kammala abinda yake dani sae kawai ya tashi firgigit kmr wanda ya tashi daga mumumunan mafarki ,yana kallon yanayin da muke ciki nida shi ya shiga tsannanin tashin hankali da rud'u da kuma matuqar mamaki , ya jima dafe da kai yana furta kalmar "innalillahi wa inna ilaihi raj'iun!" yayita ba adadi snnan cikin kuka ya shiga tmbyta kan me ya rage ni dashi da zan masa haka,ashe taimako na zama haka ,meyasa na manta Allah na bi rud'in shaid'an,haka yayita fad'in maganganu da suka qara tabbatar min akwai abinda yasha kafin yazo gareni wanda ya gusarmai da hankali dmn nasan shi mutum ne mai matuqar tsoron Allah da yake gujewa aikata sa6o,wanda ko a mafarki banyi tunanin zai aikata haka da wata mace ba bare ni. cikin kuka sosai nake masa bayani ba laifina bane shine ya afka min amma sam yaqi yarda da hakan har ya kai ga ya furta Allah ya isa akaina sbd ganin yake da yazo ne na basa wani abu yasha ya gusar mai da hankali ya biya mn buqatata. Bayanda banyi ba kan ya saurare ni ya kuma yarda dani amma yaqi ya tafi cike da baqin ciki fal a ransa A rnr yasa aka kore ni daga masaukin da ya bani na tafi cike da tunanin ya zanyi da rayuta yanxu ina zan dosa. Nayi kwana biyu ina wahalar neman gurin da zan fake ban samu ba sae tasha nake kwana nake yini a rana ta uku ne Allah ya taimake ni wata mata ta d'auke ni ina mata wanke 2 a gidan abinci ta nan nake d'an samun abinda nake ci. Haka na ci gaba da rayuta cikin qunci sae kwsatam rnr bayan wasu watanni da baza wuce biyu ba na tsinci kaina da ciki,wanda hakn ya qara tayar min da hankali sosai duk nabi na rasa inda zan sa kaina naji sanyi, na d'aya dai vazan iya zubar da cikin ba, na biyu ko giyar wake nasha bazan jewa Alhj sadiq da wannan zancen ba duk da nasan ya jima yana nmn haifuwa. Haka na haqura ina renon cikin da ko yaushe na tuna dashi sae na zubar da qwallah. Bayan cikin ya cika wata tara naquda ta taso ni sosai wacce nakeyiwa aiki ce ta kaini asibiti sbd duk a tunaninta cikin mijina ne da ya rasu ya barni dmn na snr da ita wani abu daga cikin labarin rayuwata sae dai bata san iya tsawon shkrun da mijina yayi da rasuwa ba. Gurin haifuwa ne na had'u da matar Alhj sadiq ita ma taje haifuwa banyi mamaki ba dmn na sami lbrn tana da ciki,na rigata haifuwa dmn ita haifuwar tazo mata da wahala da qyar aka samu ta haifu ta sami 'ya mace kmr yadda nima na sami 'ya mace. Cike da tunani nake kallon y'ata wacce na fi son ta rayu a gidan mahaifin ta sbd ina guje mata talaucin da nake ciki,shiyasa na yanke shawar kai er a d'akin da aka kai hajiya zarah,na kai er na ajiye ina kuka na koma bayan windown d'akin ina kallon su ,su biyu kan gado kmr en biyu. Ina tsaye ne hajiya Zarah ta farka sae murna take tana kallon yaran dmn duk a tunanin ta ita ce ta haife su gabad'aya kasancewar koda ta haifu bata san inda take ba . Tana cikin kallon yaran ne ta hango ni jikin window na kasa tafiya kan jin son 'yata da nake tace min"baiwar Allah lafiya kike kuka? Banyi mamakin yanda bata gane ni ba a matsayin mu matan abokai dmn na rame nayi baqi duk kammani na sun canza da ba lallai ne don ka sanni ka iya gane ni kai tsaye ba, hakan yasa nace 'ya'yanki ne kawai suka bani shawa daga haka na bar gurin da sauri dmn bana son ta gane ni.