Afra ko amrah complete - Chapter 25
Afra ko amrah complete Chapter 25: Afra ko amrah complete Chapter 25. 6angaren Farhan kuma ba qaramar wahala yasha ba kafin yake tsaida jinin amma duk iya…
4,403 words
6angaren Farhan kuma ba qaramar wahala yasha ba kafin yake tsaida jinin amma duk iya qoqarin sa na ganin Afrah ta farfad'o ya kasa. Jiki sanyaye ya fito ya sami su gwgaggo wato uncle Basheer ,JB,Abban Amrah,da kuma Amrah wacce tun kotu take ta kuka ganin halin da Afrah ta shiga ciki . Zama yayi ya dafe kansa cike da damuwa gwaggo tace"ya ake ciki ne Farhan? Sae da ya d'an rage damuwar da yake ciki sannan yace"Alhmdlh da sauqi " Cikin yana nan kuwa?shiru yayi kmr ba zai bata amsa ba sae can yace"sae wani ikon Allah zai sa cikin yaci gaba duk da na tsayar da jinin amma still cikin gab yake da lalacewa musamman idan ta farfad'o a cikin yanayin tashin hankali" Ke nan har yanzu bata farfad'o ba? Eh gwaggo yayi maganar ne kmr wani qaramin yaron da keson yayi kuka yayi saurin tashi ya bar gurin ya nufi d'akin da Afrah take sae kallonta yake . JB ne ya shigo dakin tare da dafa shi yace"kayi haquri Farhan inshaAllah komai zai yi dai dai" Saurin share hawayen sa yayi yace"JB ina son cikin da ke jikin Afrah sosai ya shiga raina ba kad'an ba sbd ban ta6a tunanin zata sami ciki da wuri haka ba bcs ciwon marar da take fama dashi mai tsananin gske ne da ko an sami ciki ba lallai bane ya iya zama,wanda ko wannan ba makawa farfad'owar ta shi zai 6arar da cikin kai tsaye sbd nsn xata tashi ne cikin yanayi na tashin hankali,idan har ma ina son cikin kar ya zube to fa sae idan na mata allurar hana farfad'owar ta har cikin ya daidaita yayi qwari but bazan iya haqurin haka ba dmn za a dauki lokaci sae dai na haqura da cikin ko kuma na mata allurar da ko ta farfad'o baza ta iya tuna abinda ya faru kai tsaye ba inda da taimakon Allah cikin ba zai zube ba amma nasan zata wahala sosai kafin cikin yayi qwari ,gashi ni kuma bana son wahalar da zata yi sae dai kawai na haqura na qarasa zuvar da cikin. JB ya nisa yace"um um kar kayi haka pls dmn nima haka my wife Nina tayi fama da cikinta kmr baza ta rayu ba har nayi tunanin a xuvar dashi sae kuma nayi tunanin idan kuma Allah bai sake bamu wani ba fa hkn yasa na haqura cikin ikon ta haifu yanzu kmr ma ba'ayi ba. Wato JB jinin Afrah na daban ne da komai qanqantar ciwo a gurinta babba ne shiyasa nake jin tausayinta wlh, but idan har ta farfd'o cikin bai zube ba zan bar shi.
Daga haka sukayi shiru sae ga su gwaggo sun shigo duba Afrah.
Har washe gari Afrah bata farfad'o ba hakan bai hana aka hallara kotu ba dmn yanke hukunci wa su leesa . Leesa, mom farida, Hjy Aysha duk kan wheelchair aka turo ko wannen su jikin su gabad'aya ya kumbura kan dukan da suka sha jiya har ma ba a gane su kai tsaye ga wanda ya san su. En fashi aka fara yankewa hukunci dai dai dasu, Sae dai kafin hakan sae da aka kira er uwar Abban Afrah da tayi bayani tsakanin ta da Allah me ta sani game da Afrah da Amrah. Tace"haqiqanin gsky abinda kawai na sani shine,Hjy Farida (Mom farida)ta kirani dmn na taya ta d'auke yaran ta kuma gaya min irin yawan kud'in da zata biyani gashi a wannan lokacin ina buqace da kud'i sosai shiyasa kai tsaye na amince da buqatar ta, amma kafin na aiwatar da hakan nayi matuqar jin tausayin hjy Zarah har naje bayan window ina kallon 'ya'yanta ina kuka, shiyasa tun a wannan lokacin nayi tunanin idan muka d'auke yaran zan kaiwa d'an uwana dake matuqar son haifuwa wanda kan rashin haifuwar sa ne yasa duk yayi aure matan basa tsayi har ya gaji ya daina yin aure. Bayan mun shiga dakin da hajiya Zarah take dmn dauke yaran sae da Hjy farida ta kashe ta tukun kafin muke d'aukar 'ya d'aya ba mu iya daukar su duka biyu ba sbd ni da ita duk mun rikice kan kisan da tayi musamman ni ban san da cewa kashe hjy Zarah za tayi ba duk a tunani na bayi ta shiga shine tace muje mu d'auke yaran.
Bayan mun bar asibitin ta biyani kudina na nemi alfarmar ta bar min er ba musu ta bar min , naje na kaiwa dan uwana acewar gidan marayu na kar6o masa ita yayi farin ciki sosai sbd yasan wacce nake aiki a gidan ta gidan marayu take aiki shiyasa baiyi wani tunani ba. Ni kuma sam hankalina ya kasa kwanciya ganin nake kmr asiri na zai tonu kan tsananin binciken da naga anayi a asibiti shiyasa na garzaya gun wacce ta kar6i haifuwar hjy zarah wato qawata wacce dama ita na kaiwa ziyara asibitin har na had'u da mom farida. Roqon ta nayi sosai kan ta rufa min asiri ta fad'i cewa 'ya d'aya hjy Zarah ta haifa ba biyu ba dmn na samu a daina neman d'ayar ko hankalina zai kwanta. Da qyar nasha ta amince da buqatata. Amma tun daga lokacin ta daina ganin mutunci na haka kuma ita hjy farida tun daga lokacin ba mu qara sa juna a ido ba sae a kotu. Nan ta kawo qarshen zancenta lauya yace"to kina nufin duk tsarin da hjy Aysha tayi na qarya bada sa hannun ki ba? Aa tsakanin su ne ni ban ma santa ba sbd tunda na bawa dan uwana er da na dauko ban yarda na qara zama garin nan ba sbd ganin nake asiri na zai iya tonuwa ko ynx dalilin zuwana garin nan d'an uwana ne ya kirani yace nazo bai kuma gaya min daliliba sae da nazo yake nuna min matuqar 6acin ransa kan jin gskyr yanda aka d'auko er da na bashi ,ya kuma gaya min irin case dinda ake ciki nan naji akwai makirci a ciki shine na yanke shawar zan zo kotu na fad'i gsky duk da nasan dole nima za a yanke min nawa hukunci. Lauya yace"yanzu kenan Afrah da Amrah en biyu ne? Ba makawa en biyu ne,yanzu haka ma wacce ta kar6i haifuwar tana cikin kotun nan dmn ta qara tabbatar muku da hakan. Nan lauya ya nemi izinin Alqali kan a bashi dama ya kirata . Bayan ya kirata tazo tayi cikakken bayani na cewa tabbas Afrah da Amrah en biyu ne. Nan lauya yace suna iya komawa su zauna. Aka koma kan mom farida yace"kinji bayanin da malama Fatima tayi( cewa da er uwar Abban Amrah) Ko kinada abin da zaki ce wanda kina ganin tayi qari ko qarya a ciki?Duk abinda ta fad'a gsky ne amma a tausaya a duba min bayin kaina bane sharrin shaid'an ne " ta qarashe mgnr cikin kuka. Lauya ya koma kan Hjy Aysha kafin yace komai ta nuna mai mom farida da leesa tace"wlh sharrin su ne sune suka iza min police d'in da suka had'a baki yaje har gidana ya sanar dani yanda zan tsara komai idan nazo kotu amma wlh duk makircin da nkeyi ban ta6a irin wannan ba ban kuma ta6a yin nadamar irin sa ba. Yaje kan leesa wacce tunda suka shigo kotu sae kukan nadama take ba qaqqautawa yanzu ta koina tasan bata da mafita ta kuma sàn idan ummanta taji yanda komai ya qara hargitsewa sae hawan jini ko ta mata ala gwai sbd tasha hanata aikata miyagun ayukka taqi ji, mahaifinta dake biye mata yana hana mahaifiyarta kan ta daina takura mata ya mutu yanzu bata da wani gata sae abinda ta shuka. Bai ce da ita komai ba ganin yanda take kuka na ftr rai kuma laifinta bayyanan ne ne ba sae ya mata wasu tambayoyi ba. Gun su Hjy luba yaje game da tuhumar su da ake na kashe mahaifin Afrah.
Wannan karon kai tsaye suka amshi laifin su dmn sun tsorata da ganin yanda su leesa suka sha duka. Sae dai cikin bayanin su sun nuna cewa ba kashe shi suka ce ayi ba kawai sunce a kar6e dkyr sa a kuma kore sa daga gidan shine en fashi suka bishi suka harve shi kan mantawa da sukayi bai sa hannu a takardu ba. Bayan kotu ta gama jin bayanin su Alqali yayi en rubuce rubucen sa sannan ya fad'i hukncin da ya yankewa kowa dai dai yanda shari'a ta tanadar. Da leesa da mom farida duk suka haukace suna roqon kotu ta yafe musu sharrin shaid'an ne,musamman mom farida da taci hukuncin kisa ba irin kukan da bata yi ba.
Fitar dasu Alqali yasa akayi dmn kukan su na nemn hargitsa kotu. Bayan kotu ta sami natsuwa Alqali yake snr da Farhan cewa "a bisa shaidu da kotu ta gamsu dasu na cewa Afrah da Amrah en biyu ne, ya zama dole tsakanin *Afrah ko Amrah* ka saki d'ayar su sbd baya hallata jini d'aya su auri miji d'aya a lokaci d'aya ba tare da d'ayar ta mutu ba. Nan Farhan ya rubuta saki wa Amrah. Inda Cike da tsananin tausayi fu'ad ke kallon Amrah dake kusa dashi wacce ke fmn zubar da qwallar farin ciki jin cewa en uwan juna ne na jini ita da Afrah.
Bayan sun koma asibiti suna zaune jugum a d'akin da aka kwantar da Afrah kowa sae saqe saqe yake a cikin ransa. A hankali Afrah ta shiga motsa babban yatsan ta na qafa sae dai ba wanda ya lura sae sautin muryar ta suka ji tana ta kiran uncle. Cikin hanzari Farhan ya tafi gurinta yaga ashe kiransa kawai take ba tare da ta bud'e idonta ba . Daina kiran sunan nasa tayi ta fara kuka tare da dafe qasan cikinta dake mata masifar ciwo,sae qoqarin shiga jknsa take ba tare da ta bud'e idonta ba. Farhan bai damu da taron da ke cikin d'akin ba ya rungumeta kmr yadda ta buqata sae kuka take da sautin sa ke fita da qyar, tana qara shigewa jikinsa.
*Billy giro😊&Futha luv* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: _```[ 11/11/2016]```_ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*
*Futhalurv.WordPress.com*
*```🏅77🏅```* Tun tana fitar da sautin kuka kad'an kad'an har ta fara ftr da sautin sosai sbd yanda take jin ciwon na qaruwa. At all Farhan ya rasa ta yanda zai rarrasheta dmn cike yake da jin tausayinta har ji ma yake kmr ya taya ta kukan. Amrah ce tazo tana mata sannu tana kuma rarrashinta ,firgigit ta jaye kan jikin Farhan sbd tuna abinda ya faru a kotu sae kallon kowa take d'aya bayan d'aya ta fashe da wani sabon kuka tana qoqarin zamewa kan gadon,Farhan na ganin haka yayi saurin fara mata bayanin komai tun fad'uwar ta har yau washe gari da aka yankewa kowannen su hukunci,farin ne taji marar misaltuwa sae kuma ta fashe da kuka tace "to ita Amrah bata da ciki ne? Murmushi yayi tare da duqar da kansa sbd sanin abinda zai gaya mata na cewa ba abinda ya shiga tsakaninsa da Amrah inda yayi mata bayanin yanda auren yake da kuma dalilin da yasa baya son kowa ya sani. Cikin mamaki tace"but uncle rnr da naga ka fito d'akinta ba komai ne ya faru tsakanin ku ba? A wannan rnr kinsan kin shiga toilet kin barni a kwance to a nan naji er hayaniya shiyasa na tafi koda naje d'akin Amrah na sameta da wani suna kokawa sae marinta yake har ya kai ga fasa mata baki shine yana gani na ya shaqeta yana qoqarin kasheta ,nayi iya qoqarina na ganin ya sake ta amma na kasa kuma gashi gab yake da hallaka ta hakan yasa na nemi wani qaton silver flask na daka masa aka sae kawai ya fad'i ba tare da ya sake motsawa ba,koda na dudduba shi ba alamar rai sae duk na rikice sbd bada niyyar kisa na dake shi ba sae don ceto ran Amrah. Sanin Amrah tayi ihu a lokacin da suke kokawa kuma ihun ya fita sosai nasan tabbas wani zai zo ko ke ko masu gadi shiyasa nayi saurin d'auke shi na tura a wardrobe , ina qoqarin fita ne kika shigo. Kuma wyr da kike je kika samu ina yi, da JB ne wanda shi na bawa kula da mutumen kafin mu dawo kotu . Bayan mun dawo ne naje dashi asibiti na qara dubashi naga tabbas yana da rai ,naji wani irin dad'i a raina dmn duk a tunanina ya mutu har ma na shiga tunanin tq yanda zan bayyana kaina na kuma san dole zaki shiga damuwa idan kika ji abinda ya faru shiyasa damuwa ta ta qara yawa har na kasa 6oyeta. To tun a wannan rnr da abin ya faru sae jiya gayen ya farfad'o sae dai still bai san inda yake ba,wanda naso ace ya samu kanshi kafin a gama shari'ar nan dmn ba makawa su leesa ne suka turo shi ya kashe Amrah. But still kotu tasan da zaman shi jiran samun lafiyar sa kawai ake aji wane ne dmn dad'a hukunci ga wanda ya turo shi haka shima baza a barshi ba sai an hukunta shi. A nan ya kawo qarshen zancen sa Afrah ta sauke ajiyar zuciya suka qanqame juna ita da Amrah sae kukan murna suke nan Abban Amrah ya bawa Amrah haquri kan rashin snr da ita gsky komái tun tana yarinya ,ko kad'an Amrah ranta bai 6aci ba sae godiya ma ta masa kan irin riqon da ya mata tamkar er sa ta cikin sa. Shi kuwa fu'ad baki baya rufuwa sae kallon Amrah yake yana jin wani irin sonta na qara fizgar shi sae controll din kansa yake na son sae ya ke6e da Farhan dmn ya sanar dashi ita ce fa yarinyar da yace yana so,amma sam ya kasa haqura dmn nan gaban kowa ya bayyana abinda ke ransa na game da Amrah har yana fad'in tunda ba sae tayi idda ba shi ama yi musu aurensu cikin watan nan idan har ta amince tana son shi, kunya Amrah taji tayi saurin fita daga d'akin yayinda kowa ya washe baki da jin dad'in zancen fu'ad.
Nan fu'ad ya sace jiki yabi Amrah dmn yaji nata ra'ayin. Farhan ya kalli Afrah wacce sae murmushi take cikin juriya sbd ita kad'ai tasan bala'in da take ji ,ai kuwa a shagwa6e ta kalle shi cike da son tayi kuka,yace"sannu ko"gyad'a masa kai tayi ta zame daga kan jikin sa ta kwanta ko zata d'anji damar ciwon.
6angaren fu'ad da Amrah kuwa magana yake mata amma ta kasa ce masa komai kanta qasà sai murmushin jin kunya take da qarshe ma guduwa tayi ta barshi nan zaune ya bita da kallo had'e da girgiza kansa cike da murmushi yana jin kansa sae shillo yake cikin duniyar so dmn alamu sun nuna mai Amrah zata kar6i tayinsa.
Bayan sun koma gida haka Afrah ta yini kwance bata iya wani dogon motsi wanda ji take ina ma tana da lafiya da har rawa sae tayi yau kan farin ciki amma ina ciwo ya kwafsa mata.
Da dare farhan ne ya fito da ita toilet gurin wanka yayi mata shirin kwanciya ya had'a allurai zai mata ta ajiye masa kuka bana wasa ba dmn tasan ko tashi bata iya yi bare ta nemi guduwa. Ajiye alluran yayi yace"is ok na fasa miki allurar amma fa zaki sha magunguna"share hawayenta tayi tace"sae dai haka" Nan ya bata magunguna tasha ya kunna mata MBC Bollywood kmr yanda ta buqata har sai da aka qare film d'in da ta samu anayi sannan ta iya bacci. Washe gari Amrah ce ta kawo musu break fast bayan sun gama ci ta nemi ya kaita 6angaren gwaggo nan ya d'auketa ya kaita.
Har guraren qarfe d'aya tana 6angaren sae fira gwaggo keyi ita da Amrah ita dai jin su kawai take sbd ko magana bata cika son yi ba. Suna cikin firar ne suka ji sallamar fu'ad sum sum Amrah ta miqe zata bar falon ta shige qurya ,fu'ad da kafin ta shiga har ya shigo kuma sak ya fahimci shigowar sa ne yasa ta tashi yace"sannu Amrah ina yini" Duqar da kanta qasa tayi sae wasa take da en yatsun ta duk kunya ta isheta,gaisawa yayi da gwaggo yayi ma Afrah sannu da jiki sannan ya miqa saqon da ya shigo dashi wa gwaggo inji mtr uncle Basheer. Kmr wanda zai fita sae kuma ya fasa yaje kusa da Amrah wacce still tanà tsaye kanta a qasa yace"Amrah pls kije ki zauna kinji tsayuwar nan zai sa ki gaji ,ki fasa shiga inner room dmn 6uya ni fita zanyi,kuma bazan sake shigowa gidan nan ba sae da izinin ki tunda ba kya so,haka ne ko?ya tsare ta da ido cike da son jin amsar ta hkn yasa ta girgiza masa kai , yaji wani irin dad'in da ya rasa dalilin sa, nan kawai ya fita ,Amra ta koma kusa da gwaggo ta zauna ,gwaggo sae kallonta take da murmushi yayinda Afrah kejin dad'in ganin yanda soyayyar Amrah da fu'ad zata yi kyau.
Da dare bayan sallar isha'i Farhan da Afrah ne a 6angaren su zaune a falo sun gama cin abinci suna jingine jikin cushion, Afrah ta kwantar da kanta kan kafad'ar Farhan suna kallon labarai. Farhan ya shafo gefen fuskar ta yace"am sorry Afrah ina zuwa"sae da ya jayeta a hankali kan jikinsa kafin yake tashi. Afrah ta riqo hannun sa tare da fad'in "pls uncle kar ka jima" bazan jima ba inshaAllah.
Ya jima sosai kafin yake fitowa gudu gudu sauri sauri yake saukowa kan staircase yayi kicimis da Afrah zaune a bakin staircase sae kuka take ta kasa hawa gata zaune sharkaf cikin wani abu kmr ruwa. Yace"Afrah fitsari kikayi?hannu ta d'ora a fuska tana qoqarin sake fashewa da wani sabon kuka. Yace"no Afrah kar kiyi kuka bafa laifin ki na gani ba, I'm just asking" Uhm Uhm sae ma ka tambaya ko fitsari ne bayan gashi a zahiri ,bayan kuma kaji yanda nake ta kiranka uncle amma ka shareni, cikin kuka sosai ta qarashe maganar tare da fad'in "shike nan don mutum baya iya yin komai sae ayi ta masa wlknci" Ba haka bane Afrah bayi na shiga kuma ina fitowa aka kirani a waya kuma sam wlh banji kiran da kike min ba ,yi haquri kinji my Afrah, ya fad'i haka ne tare da share mata hawaye sannan ya mata peck kan kumatu ,a shagwa6e takai hannu ta share peck din da yayi mata alamar bata so ta d'ora da cewa"ni dai gsky idan cikin nan ne ke wahaldani gwara kawai a cire shi kowa ma ya huta dmn wlh bazan iya ci gaba da wahala haka ba har na haifesa wataqil ma ban ko isa d'aukar ciki ba shine yake wahaldani , dama leesa ta gaya min idan yaro ya d'auki ciki mutuwa yake gashi kuwa na fara ganin alamun haka,kallonta yayi dmn bai san yaushe ne leesa ta gaya mata haka ba , amma ya basar sbd baya son maganar leesa. Tace"Pls uncle dan Allah ka cire min cikin nan kaji,wlh ni kad'ai nasan wahalar da nake sha" kallonta yayi da mugun tausayi sbd yanda tayi mgnr cikin marairaicewa sosai, ya share mata hawaye tare da fad'in"to shike nan daina kuka yau yau d'in nan zan cire miki" Yana gama fad'ar haka yaje ya saka key a qofa ya dawo ya cire mata kayan jikinta ya barta da inner wears ya d'auke ta ya d'ora kan d'ayan stair ya zaunar ,yaje ya d'auko mofa da ruwa ya goge gurin tas,ya maida kayan sannan ya dawo ya d'auke ta suka haura sama zuwa d'akin shi,bai xarce da ita koina ba sae toilet yayi mata wanka ya fito da ita ya ajiyeta kan bed tare da zare towel d'in jikinta ya shiga shafa mata Vaseline . Afrah sae kallon sa take yanda yake komai nasa very weak jiki mace wanda tunda tace ya cire mata ciki taga yanayinsa ya dawo haka. A hankali ta riqo hannunsa dake kan qirjinta yana shafa mata Vaseline, ta matsa lallausan hannun nasa da taji ya qara mata laushi , d'ago fuskar sa yayi suna kallon juna ta cikin ido tace"uncle baka so a cire cikin nan ko? Bana so Afrah amma nafi buqatar ganinki cikin qoshin lafiya, um um uncle tunda baka so a cire a barshi kawai zan iya ci gaba da haqura har na haife shi.
*Billy giro 😊&Futha Luv* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: _*```[11/12/2016]```*_ 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*
*Futhalurv.WordPress.com*
*```🏅78🏅```* No Afrah ki bari kawai a cire tunda yana wahalda ke sosai, um um uncle nidai nace a barshi tunda baka son a cire,,Afrah dama fa nayi......hannu takai ta rufe masa baki tare da shigewa jikin sa tace"pls uncle gardama ba naka bane dan Allah a daina zancen ni bacci ma nakeji,towel yasa ya rufe mata jikinta sannan yace"shike nan bari asa kayan bacci ko,ta gyad'a masa kai kafin yake tashi ya d'auko kayan bacci ya saka mata.
Washe gari da asuba koda ya dawo daga masallaci ya sameta durqushe kan sallaya sae kuka take dafe da qasan cikinta. A rikice farhan ya qarasa gurinta yana fad'in "lfy Afrah me yake faruwa ko fitsari kike ji? Da qyar ta iya girgiza masa kai tana yarfi da hannu, ta kuma qanqame shi sosai tana kuka mai wahala hawaye wani nabin wani, ta samu da qyar tace"wayyo Allah uncle cikina zan mutu "to Afrah ki bari a cire cikin kinji ,no uncle a barshi tunda kana so kawai dai mantawa nayi da bana iya tashi tsaye shine ina tashi maràtà ta wani tsinka min kmr zata tafi da raina, sorry sorry ki bari na miki allura ciwon zai rage sosai ,uhm uhm uncle bana so kawai dai zan sha magani. Ba yanda ya iya haka ya bata magani tasha duk da yasan alluran da zai mata sun maganin sau goma. A nan jikin sa bacci yayi awon gaba da ita ,ya cire mata hijab tare da zanen da ta d'aura kan rgr bacci ya kwantar da ita yana qare ma jikinta kallo ganin yanda ciwon ya ramar da ita lokaci d'aya . Nan ya shiga tunanin ko dai ya bata maganin zubar da ciki ba tare da ta san wane irin magani bane. Wata zuciyar tace"yanda nake son cikin nan bana son zubar da shi sae dai na tursasata na mata allurar rage kaifin ciwon.
Guraren qarfe biyu da rabi da taimakon Amrah gwaggo take taka qafar ta har suka zo 6anfaren su Farhan. Sun same su a falo Farhan na had'a allura, Afrah kuwa na kwance rabin jikinta kan cusion rabi a qasa, sae da suka gaisa gwaggo tace "farhan wannan kwanciyar da Afrah tayi ba dad'i baza ka gyra mata ba" ganin ya had'a allura tace"ok allura za ayi? eh to kwanciyar dai ce ta kama mata haka sbd ta kasa kwanciya ta kasa zama shine tayi haka bata ko san zan mata allura ba ai sbd bacci take, amma kasan dole ta farka idan taji an soka mata allura, Aa niyata sae na tashe ta in yaso na matse ta sbd ba ko wani motsin kirki take iya yi ba. Yana gama fad'ar haka ta farka sbd jin surutun mutane smn kanta. Ta had'e tafukan hannyen ta tana kallon allurar da ya had'a tace"pls uncle ko magani d'ari ne ka bani nasha amma kar ka min allurar nan wlh yanzu haka bayana ciwo yake kan alluran da aka min kwanakin nan"yi hqr qwara biyu ne kawai za'ayi"a rikice tace"har biyu uncle? To Afrah alluran nan fa suna kawo sauqi kai tsaye ba tare da kinyi doguwar jinya ba da taimakon Allah,um um nidai bana so a bar ni haka. Gwaggo tasa bakinta sae lallashinta suke amma taqi yarda hakan yasa Farhan ya matse ta ya mata alluran sae kuka take duk ta 6ata mishi riga da hawaye .
Nan zaune taja jikinta ta tafi nesa dasu ta manne jikin bango ta had'e kai da guiwa tana ta rusar kuka. Cikin damuwa sosai Amrah ke qoqarin zuwa gurinta ta rarrasheta Farhan yace"kar kije rabu da ita kinsan halinta ba saurarenki zata yi ba. To Farhan a barta tayi ta kuka ai ko don cikin jikinta a tasauya mata, zan rarrashe ta gwaggo so nake na had'a kayan nan tukun. Yana gamawa ya tafi gurin Afrah da niyyar ya rarrasheta ta qara matsawa nesa dashi tana fad'in ita kar ya ta6ata. Tashi yayi ya bar gurin sbd duk wani lallashi da yake ganin zai sa tayi saurin saukowa ba ya iya yinshi a gaban su gwaggo. Gwaggo tace"yau kuma kaida ita " Murmushi yayi yace"to gwaggo kinga fushi take bata so na rarrasheta,gwara kawai na bari zuwa anjima dai dai ta sauko. Nan suka ajiye zancen suka d'auko wata firar koda suka gama tuni Afrah ta 6ingire a gurin tayi bacci . Bayan su gwaggo sun tafi ne ya d'auketa ya kaita d'akinta.
Bayan kwana biyu Afrah taji sauqi dmn har tana iya miqewa tsaye sae dai tun a lokacin Afrah fushi take da Farhan sosai inda shi abin mamaki da dariya yake bashi shiyasa yasa mata ido har ta gama kumburen2 ta.
9:30am Farhan ke fmn knocking a d'akin Afrah tana ji amma tayi banza dashi yace"pls Afrah ki fito muyi magana tafiya zanyi kuma zanyi two days kafin na dawo, gyara kwanciyar ta kawai tayi tace"hm wai ni uncle zai ma wayo. Farhan ya gaji da knocking ya ajiye kud'i da d'an short note a nan bakin qofar d'akin ya tafi . Tana nan kwance taji ftr sa ta tashi tana leqensa ta window sae dai kad'an take iya hango gefen sa har ya shige 6angaren gwaggo.
Sae da suka gaisa yace"shi xai tafi "gwaggo tace"tafiyar kenan? InshaAllah daga haka ya tashi zai fita sae ga Amrah ta fito daga ciki tana mishi ina kwana yace"yauwa dama kuwa inaso na ganki kafin na wuce. fu'ad ne yace yana son ki bashi dama yazo kuyi magana ta famhtr juna sbd shidai dagaske yake kuma da wuri yake son ayi auren me kika ce?shiru tayi ta kasa cewa komai yace"Amrah say somting sauri fa nake"a sanyaye tace"ba komai uncle yazo" tana gama fadar haka ta koma ciki da sauri gwaggo tayi murmushi tace "Amrah iyayen kunya, Farhan yace"ai ana son haka a gun mace, nan ya zaro kud'i masu yawa ya ajiye yace"to gwaggo Ala hairan ni zan tafi "to na gode qwarai Allah kiyaye hanya" amin amin.