Afra ko amrah complete - Chapter 26
Afra ko amrah complete Chapter 26: Afra ko amrah complete Chapter 26. Afrah na nan still jikin window tana jiran fitowar sa ,taga kuwa da gaske tafiya zai…
3,923 words
Afrah na nan still jikin window tana jiran fitowar sa ,taga kuwa da gaske tafiya zai yi ganin travelling bag a hannun shi, da sauri take saukowa har tana hard'e qafafu sae dai koda ta fito tuni ya tada motarsa har an bud'e masa gate a nan tsaye ta fashe da kuka tana kallo har ya fita ta sulale nan jikin qofa ta had'e kai da guiwa tana ci gaba da kuka. Ta jima sosai a gurin tana kuka sae kawai taji qamshin turarensa tayi saurin d'agowa ta ganshi ai kuwa ta rungume shi tana fad'in "kayi haquri uncle kar ka tafi dan Allah,bazan sake fushi da kai ba idan shine" Hannun ta yaja suka je daga ciki yace"ni kuma yanzu na fara fushi dake dn haka tafiyata zanyi na barki kuma baza ki qara gani na ba,pls am really very sorry uncle wlh kasan allurar ka zafi ne da ita dmn har yanzu fa bata daina min ciwo ba kuma gurin har yayi lolo shiyasa bana iya kwanciya da kyau, ai dole ne tunda ba kya bari a murza miki kuma ba kya murza ma kanki gashi kuma kinsan halin jikin ki yanda yake. Pls nidai uncle kar ka tafi,komai bai ce mata ba sae hannunta yaja suka je d'akin shi. Ya shiga cire mata komai na jikinta ,kallonsa take tana kame kame cike da son tayi masa magana amma ta kasa sbd yanda ya fuske kmr bai ta6a dariya ba, tana kallo ya rage hasken d'akin ya kwantar da ita ruf da ciki,ya cire suit din jikinshi yaje ya d'auko ice block a freezer. Afrah sae binsa take da ido bata san me zai mata ba, jin yana shafa bayanta duk ta tsorace ta d'auka ko wata allura zai mata har ta soma bashi haquri sae ta fahimci yana murza mata gurin ne yana sa qanqara , qam ta rungume pillow sbd sanyin da take ji da ciwo , bai kulata ba sae da ya tabbatar gurin ya murzu sosai sannan ya d'agota yaga idonta a rufe sae numfashi take sosai yace"mene ne?ta bud'e idonta nan hawayen da ke cike da idon suka gangaro ta kwanta a hankali kan jikinsa yayinda yake share mata hawaye, ta shafo bayanta tare da fad'in ciwo uncle " Hannun sa yakai yana shafa gurin a hankali yana mata sannu se ta qara lafewa jikin sa sosai sbd jin dad'in shafar da har ta soma jin bacci, murya can qasa tace"uncle ka fasa tafiya ko?um um tfyr ta dole ce fa ko yanzu an d'age time d'in tafiyar ne shiyasa na dawo,hln wane gari ne uncle? Abuja, pls uncle kaje dani, um um cikin da ke jikin ki da had'ari sosai idan kika shiga jirgi dmn ko tashin jirgi kad'ai zai iya 6arar dashi,to uncle muje da mota sae muyi ta tafiya a hankali har mu isa kaji, um um haquri zakiyi Afrah ai ba wani jimawa zanyi ba . Kuka ta shiga yi sosai tana roqonshi shi kuma sae lallashinta yake haka yaja har ya fara romancing d'inta ba a son ransa ba sae don ya samu tayi shiru. Banyan sun gama ne ya rungumeta qam a qirjinsa yana kallon Afrah da bacci ke qoqarin d'aukar ta, a hankali yake son zame jikinsa daga nata tace"uncle ina kuma xaka tafi?wanka nake son nayi kafin lokaci ya tafi,wankan me uncle? Hm Afrah kenan har ma kya tambaya bayan kema wankan ya kama ki, saurin duqar da kanta tayi ta daina kallon sa, yace"ko kin d'auka ko dole sae ta hanyar kusanta wanka ke kama mutum?um um uncle na sani,to tashi muje muyi wankan,6oye fuskar ta tayi a qirjinsa tace"nifa wankan bai kamani ba"murmushi yayi yace"to naji er wayo muje ki tayani wankan nida ya kama"
Bayan sun fito yake cewa ya akayi keda wankan bai kama ba amma naga kinyi? Uhm uhm uncle nifa saboda tsaro kawai nayi, dariya yayi yana qoqarin sake wata maganar tayi saurin marairaice mai dmn ta katse zancen tace"uncle xaka tafi dani ko?wai baki daina zancen ba bayan nace kiyi haquri? To uncle.... Sae kuma tayi shiru ganin ya jawo wata jaka yana zuba kayanta a ciki ,mantawa tayi da ciwon jikinta ta fara tsallen murna,yayi saurin hana ta tsallen tare da zaunar da ita yace"ki natsu fa kar ki 6arar min da baby, ta ya zan iya natsuwa uncle bayan ina murnar za a tafi dani ,nan tayi zaune kusa dashi ta cika shi da surutu tana nuna mai kayan da take so, tace"is ok uncle kayan hausawa biyu sun isa sauran duk ka samin Arabian gowns sbd sunfi dad'in sha'ani,nan ya koma 6angaren Arabian gowns yana zarowa tace"yes kmr kasan ina mugun sonta wlh sbd tana min kyau... wow!nyc uncle ita wannan ban ta6a sata ba ashe haka take da kyau, wuuhuuu! blue black d'in nan ma ta had'u a had'a min da ita, Yes!um um bana son kalar red d'in nan ga dai wasu can guda uku d'aya blue 2 baqake,yauwa ga wata peach in colour can ita ma a had'a min da ita, then.....sae tayi shiru tana qare ma tufafin kallo dmn ta samu wacce zata qara za6owa, Farhan dake kallon ta ya riqo yatsanta da take fmn wasa dashi kan dimple d'inta yace"my Afrah kayan fa sunyi yawa ynx fa zasuyi kala goma kenan, turo baki tayi tace"to uncle kana nufin da kun gama abinda kuka je yi dawowa zamuyi baza mu yawata mu d'an shaqata ba na samu ma na ziyar ci wad'an da na sani a can....yeah har ma naje gidan su umman uncle fu'ad ko uncle? dariya ta bashi sosai amma haka ya danne dariyar yaci gaba da sa kayan da ta nuna mai. Bayan sun shirya sun fito yaja hannunta sae 6angaren gwaggo suna kaiwa bakin qofa wayarsa ta shiga ruri bai d'aga wayar ba sae hugging dinta da yayi ya d'ora mata kiss gefen fuska tare da riqo hannunta ya bata jaka , yaje saitin kunnen ta yana fad'in "dama na had'a miki kayan ne don ki zauna 6angaren gwaggo har na dawo sbd bana son kiyi wahalar zuwa 6angaren mu yawon d'aukar kaya . Nan ya sake d'ora mata wani kiss kan lips yace"pls ki kula da kanki n my unborn child" ya fad'i haka ne had'e da shafa cikinta, ya tafi cikin sauri yana mata bye bye. mutuwar tsaye tayi jakar hannunta ta sa6ule sae qasa dai dai lokacin da hawaye ke gangarowa kan kumatunta, ta kalli irin dressing d'inda tayi mai kyau na zuwa garin Abuja sae kawai taji ta fashe da kuka.
*Billy giro 😊&Futha Luv💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:22PM, 11/30/2016] Billy Geeero: ```[11/13/2016]``` 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*
*Futhalurv.WordPress.com*
*```🏅79🏅```* Amrah ce ta fito a rikice tace"Afrah lafiya me yake faruwa? Cikin kuka Afrah ta fad'a jikinta bata iya ce mata komai ba, Amrah ta d'auki jakar da ta gani qasa suka shiga daga ciki. Gwaggo na ganin su ta shiga tambayar lafiya? Afrah ta qara fashewa da wani kuka ta fad'a jikin gwaggo, cikin kuka sosai har ba ajin wata kalma in ta fad'a tayi ma gwaggo bayanin abinda Farhan ya mata. Gwaggo tace"yi haquri lallai bai kyauta miki ba dmn ya kamata da yaga kina zumud'i yace bafa dake zai tafi ba, ai ni gwaggo ba ruwana dashi ko ya dawo, ai banni dashi kuma kima daina kuka kina wahalda kanki kar kija ma kanki wani ciwon. Ba musu kuwa ta share hawayenta taja hannun Amrah suka shiga daga ciki. Gwaggo ta jawo wayar ta tana neman layin Farhan ta shiga amma ba a d'aga ba,bata koma gwada kiran ba ta ajiye.
Bayan sun shiga daga ciki ne Afrah tace da Amrah"shin wai ya ake ciki zancen uncle fu'ad? yace ma uncle yana so yazo shine uncle yake tambayata yazo d'in shine nace eh,but ke ya kika gani? Eh mana yazo but ke kina son shi?gsky bana jin bazan so shi ba,but ni auren ne bana so ayi da wuri....why? sbd gwaggo kinga har yanzu bata qarasa jin sauqi ba na fison sai taji sauqi gabad'aya ko za ayi bikin bcs bikin zai fi dad'i ,huh! haka ne amma ai ko cikin satin nan zata iya jin sauqi...da kamar wuya,meyasa baki ga uncle bane gurin ya samu sauqi sae harakar gaban sa yake kmr ba abinda ya faru ,uncle daban ne kuma jikin sa daban haka kuma harbin sa baiyi munin na gwaggo ba bcs ita gwaggo fa da harsashin ya shiga sae da ya karya mata qashi while uncle bai yi nisa a cikin jikin sa ba kuma da gani wani abun kinsan juriya ne kawai yake,uhm uhm nidai Amrah ki yarda kawai ayi bikin nan da wuri ,meyasa?sbd ina so musha biki......wai ba kwa ji nane ina ta magana ,lah!gwaggo yi hqr wlh ba muji ba gamu zuwa.
Riqe da hannun juna suka je falon kowaccen su ta zauna gefen gwaggo suka sata tsaka,gwaggo ta kalli Amrah tace"kinsan fu'ad yace zai shigo gashi ko shiri banga kin fara ba sae surutu da kuka zauna ma yi, gwaggo ai bai ce ga time d'inda zai shigo ba ,yanzu ya kirani ya gaya min zai shigo ba jimawa.....yes!muje kiyi wanka ki shirya,Afrah taja hannun ta suka shiga daga ciki. Sun kwashe kusan awa d'aya da rabi ana shiri bayan sun kammala sukayi sallah ,Afrah tace "hm ke kinga yanda kikayi kyau kuwa, may be ma ba zai gane ki ba in yazo, kinji ki da zolaya, wlh Allah da gaske nake kinyi kyau sosai, gwaggo ta shigo tace"wai kunje falon baqi kun duba ko baya buqatar gyara ?Aa gwaggo kinsan ko jiya sae da na share shi,cewar Amrah, gwaggo tace to shike nan.
Bayan yazo Amrah ta shirya zata fita Afrah tazo tare da rad'a mata magana a kunne ,Amrah ta bugota suna dariya tace"baki da kunya ko? nidai dan Allah ki amince ayi auren nan cikin time,maqale kafad'a tayi tace"naqi d'in ,a shagwa6e Afrah tace"koh yayi" Murmushi kawai Amrah tayi ta wuce.
Ba qaramin kyau fu'ad yaga tayi masa ba ai kuwa sae kallonta yake yayinda kanta yake qasa tana wasa da zoben dake jikin yatsanta ,kiran sunan ta yayi ta d'ago ta kalle shi ya sake mata lallausan murmushi yace"kinyi kyau" Sae da ta duqar da kanta kafin take cewa "nagode, kasha ruwa mana uncle,to nida kaina zan zuba, cikin natsuwa ta taso ta tsiyaya mai lemu a cup ta bashi ta koma ta zauna,yasha ba sosai ba ya ajiye sae fira yake d'an janta da ita har yazo kan zance aure yake tambayar ta me ta gani ayi aure cikin watan nan ko kuwa, sae yanda kika ce ina sauraren ki? Dake nake kimin shiru ,uncle fu'ad ni nafi son sae gwaggo taji sauqi tukun ko za ayi zancen aure. Ya nisa tare da fad'in "shikenan Allah ya qara mata sauqi" amin.
Bayan sun gama firar ne ta koma tana shiga Afrah ta qanqame ta sae rawa take da qafafunta tace"wayyo Allah zance da dad'i ko dan Allah gaya min kinsan ban ta6a yi ba, kinji ki fira ce fa kawai ake, kmr ya fira ?kmr yanda muke yi da gwaggo mana.... No gsky ban yarda ba firar masoyi da ta gwaggo dole su banbanta,dole cikin firar masoyi a d'an kamo gefen gyale a rufe fuska ace"uhm honey kenan ai kaima kasan babu wani bayan kai" Da gwaggo har Amrah sae da sukayi dariya sbd yanda Afrah tayi acting d'in tsaf kmr tana gaban saurayi, Gwaggo tace"oh Allah ya shirye ki Afrah, sae da ta rufe fuskarta tace"amin gwaggo sannan taja hannun Amrah tace"nidai muje naji bayani yanda ake zance. Amrah ta sa6ule hanunta q hankali tace"gara ke ni ina da abinyi dmn girki zan d'ora la'asar tayi. Daga haka taje ta miqawa gwaggo ledar da ke hannunta ta wuce. Afrah da ta cika fam taje gurin gwaggo cike da shagwa6a tace"gwaggo kinga irin wulakncin da tamin ko? Afrah ai da gaskiyar ta lokaci fa ya tafi kinaji har an fara kirayen kirayen sallah idan kuka zauna ma fira za a makara gun girkin dare ne,, shine kika kama mata ko gwaggo, ai nima zowa zanyi nayi saurayi na san ya ake zance a daina min wlknci,Amrah tayi dariya tace"cabd'i ai kuwa kashe ki ne kawai uncle ba zai yi ba,ya kashe ni man ina ma ruwansa dani nida nake fushi dashi, haka kema meye ruwanki dani bayan kimmin wlknci,ni kima rabu dani....hhhh yarinya cezin ya riga da ya wuce ki sae dai wata ba ke ba . En qana nan pillows dake kan cushion Afrah ta d'auka tana jifan Amrah dasu ,haka ma Amrah ta shiga ramawa,tuni Afrah ta gaji sbd jikinta har yanxu bata jin dai dai taje jikin gwaggo ta qanqameta tace"gwaggo ce ta daina ramawa haka nafa daina dukanta. Amrah barta haka kuje ma kuyi sallah Amrah ta miqa ma Afrah hannu sae sauke numfashi take tace"zo muje daga ciki muyi sallah ,Afrah ta miqa mata hannu tana fad'in"waih Amrah kin fiye mugunta wlh wannan ribiti haka, to ai ke kika fara. Dai dai sun shiga daki Afrah ta kwanta tace"waih jeki fara yin arwala kafin ki fito na d'an huta"nifa fashin sallah nake shiyasa nace girki zan d'ora, Afrah ta tashi tana fad'in"aga aga aga wacce ke fashin sallah" Amrah ma tace"aga aga aga er qararrama mai ciki da bata fashin sallah"a shagwa6e Afrah ta juyo tace"ki daina fa ai kema kina da ciki ba gashi ba, ta fad'i hakane tare da lakato cikin Amrah,Amrah tayi wuf zata rama Afrah tayi saurin d'ora hanneyenta kan cikinta ta kame guri d'aya tare da runtse idonta tana fad'in "wayyo don Allah yi haquri kar ki ta6a ciwo marata keyi" Allah sarki sannu ,murgud'a mata baki tayi tace"bana so tunda baki gaya min yanda ake cezin ba" Nan ta shige toilet Amrah dake dariya tace"idan kinyi sallah zan gaya miki amma sae na gama d'ora girki.
Bayan ta gama sallah tayi kwance tare da kunna wayarta da ta d'auko,kunna wyr keda wuya ta shiga ruri,ganin Farhan ke kiran ta ajiye wyr tare da juya mata baya tana ji har ta tsinke. Tayi saurin d'aukar wayar ta kashe ta balle battery ta saka ta a drawer ta koma ta kwanta. Tana ji gwaggo na waya dashi ,tana fad'in ni bazan rarrasheta ba kai dai ka rarrasheta kaida ka mata laifi, to bara na bata wayar, nan ta shiga kiran Afrah,Afrah ta yi lamo abinta kmr mai bacci har da su rufe ido. Sae da gwaggo tayi wahalar tasowa tace"ashe ma bacci take"ah to gwaggo ki barta kawai kar ki tashe ta dan Allah. Shine abnda taji kasancewar ana d'anji,nan sukayi sallama da gwaggo a cewar sae anjima zai sake kira. Afrah kuwa tun daga gurin bacci yayi awon gaba da ita.
Yau kwana biyu kenan da tafiyar Farhan duk yanda yaso yayi wayq da ita taqi yarda ko mgnr sa ma bata son anayi ,maganar ta d'aya ce yanzu cezin dai cezin ita dai cezin ina ma zata sami saurayin da zai zo suyi cezin, Amrah tace"wlh Afrah ki kama bakin ki kina matar aure kina ambatar saurayi in ma uncle yaji ki ba kwa yinta da dad'i wlh, Amrah wlh so nake na ganni ina cezin naji me ake ji wane shauqi masoya keji, nace ki bari na la6e naji yanda kuke yi gwaggo ta hana ni, kuma ke kinxo kina hana ni zancen saurayi nida bakina ,wai ke kar uncle yaji ko yaji ai ba ruwansa dani tunda fushi nake dashi. yau da safe ko naji gwaggo na waya dashi yace ba zai dawo ba sae jibi,da gaske!? Wlh,,hm ai ko ya dawo ma ba ruwa na dashi tana gama fadar haka ta tashi ta shiga daga ciki sbd kukan da ke qoqarin zo mata, tayi kwance taci kukanta mai isar ta ,daga nan sae bacci.
Bayan kwana biyu tana kwance sae game take da wayarta. Farhan ne ya shigo gidan ba kowa sbd Amrah na can falon baqi ita da fu'ad, gwaggo tana bayi tana wanka ,yayi tsaye yana kallon Afrah dake game gashi ko yanzu kafin ya shigo gari sae da ya kira wayar ta yafi a qirga aka ce mai tana kashe. A nan tsaye ya sake gwada kiran still layin yana a rufe hakan ya bashi tabbacin flight ta saka wayar . Afrah kuwa cak ta tsaya da game d'inda take sbd qamshin turaren sa da taji ,ta jikin screen d'in wayarta ta hango shi tsaye bakin qofa,taci gaba da yin game d'inta kmr bata san dashi ba. Tako yake a hankali har ya iso gurinta ,zama d'aya taji ya rungumeta yana shinshinar qamshin jikinta tayi saurin fizge jikinta tare da fad'in "meye haka!qara rungumeta yayi,tace"ni ni ka rabu dani ,wlh zan maka ihu, wayyo gwaggo...gam ya rufe bakinsa da nata sae da ya gama kashe mata jiki ta hanyar tsotse mata lips sannan ya zare bakinsa yana maida numfashi, yace"so kike ki tsorata gwaggo dake bayi ta d'auka ko wani mugun abu ne ya faru da ke, cike da takaici take kallon sa tana faman murza lips d'inta da yasha tsotsa ,ta yunqura zata tashi ya maida ta da qarfi kan jikinsa ,kuka ta fashe mai dashi tare da kai hannu kan qasan cikinta da taji ciwo kan janta da yayi da qarfi,sbd har yanzu idan tayi dogon motsi sae taji gurin ya mird'a mata. Cike da ganin rashin kyautatawar sa yake qoqarin rarrashinta se yaji qarar bud'e qofa gwaggo zata fito hakan yasa ya zame jikinsa daga nata , Afrah kuwa tashi tayi taje jikin gwaggo tana kuka, gwaggo ta kalli Farhan tace"me ya had'a ku kuma? haquri nake son bata gwaggo amma taqi saurara ta. Gwaggo taja hannun ta suka zauna tana fad'in yi haquri rabu dashi, ai tunda ya tafi ya barki muma zamuyi tafiya bada shi ba. Nan Afrah ta share hawayen ta ta qara lafewa jikin gwaggo, gwaggo tace"Farhan ya hanya?Alhmdllh gwaggo ina Amrah take na shigo ban ganta ba? Tana can falon baqi ita da fu'ad,ok akwai lemu mai sanyi gwaggo? Eh Afrah tashi jeki d'auko masa,kina jina fa kinyi shiru,still tayi shiru bata ce da gwaggo komai ba, Farhan yace"barta kawai bari na tashi da kaina. Da sauri Afrah ta tashi har tana hard'e qafafu dmn ta samu ta riga shi isa gun fridge amma duk da haka ya riga ta isa ita kuma tana isa ta riga shi bud'ewa ta zira hannunta zata d'auko mai hollandia yoghurt ya riqo hannunta yana kallon qafarta da kulawa tare da fad'in"baki ji ciwo ba?girgiza mai kai tayi ba tare da ta kalle shi ba . Ta d'auko cup ta tsiyaya mai ta bashi ,ta koma jikin gwaggo ta kwanta. Gwaggo tace"ah ah wai lemu kawai kika bashi ba abinci haba Afrah yi haquri tashi kinji"no gwaggo barta gsky bana jin yunwa zan dai tafi na watsa ruwa na dawo.
Yana fita Afrah ta sauka kan jikin gwaggo ta kwanta kan bed sbd baccin da take ji,gwaggo tace"ah ah na d'auka ko raka shi zakiyi? um um gwaggo akan me nida ma kejin bacci. Da haka gwaggo tayi shiru sae ga Amrah ta shigo d'akin, nan baccin da Afrah keji ya watse tace"yeah Amrah ta dawo daga gun zance nazo ki bani lbr?um um jeki raka uncle tukun,mtsw kinga kawai kice min baza ki gaya min ba shike nan ,ai da ana maida rayuwa baya da baza ki min walaqanci ba ,don wlh da sae na maida rayuwata baya nayi cezin nima naji me ake ji da har ake ma mutum walknci don ya nemi a bashi lbr...Uhm uhm wai ni gwaggo meyasa kuka min auren wuri tun kan nasan meye zance gashi yanzu sae wlqnci Amrah keta min. Ikon Allah wai da gaske kuka kike yi? Ba dole ba yanzu fa ko taruwa akayi ana firar zance da saurayi ni sae dai nayi ta rarraba ido ina kallonsu bazan saka bakina ba bcs i have no idea"ta qarashe mgnr cikin muryar kuka, gwaggo tace"yau dai rigima kike ji qarin ma kinga Farhan ya dawo"bata tanka gwaggo ba sae kukanta da taci gaba da rerawa.
Mamaki ya cika Amrah ta ma kasa cewa komai ta tashi tana rage kayan jikinta dmn ta samu tayi wanka tayi shirin bacci.
Koda Farhan ya dawo ya sami Afrah kwance an ajiye kukan rashin dalili ana game , yaje a hankali kusa da ita ya zauna ya kar6i waya yace"tashi muje 6angaren mu dare yayi" ni a nan zan kwana, meyasa?sbd nan nake son ci gaba da kwana har ko yaushe...at all? Eh man... Hm Afrah kenan yi haquri tashi muje kinji , fafau Afrah taqi tashi yayi lalla6a har ya gaji . Ya nisa tare da fad'in ni zan tafi, na tafi da gaske baza ki je ba? Gyad'a masa kai tayi tare da qara gyara kwanciyar ta. Ba musu ya fita gwaggo tace"wai Afrah kin kuwa san darajar aure ?eh mana gwaggo, qarya kike baki sani ba don da baki barshi ya tafi ba,ni ba inda zanje sae yazo munyi zancen kmr yanda kowa keyi kafin ayi aure. Kinga bana son shashanci maza tashi kiyi wanka ki koma 6angaren ku! Cikin kuka Afrah ta tashi ta fad'a toilet tayi bala'in jimawa kafin take fitowa sae ga Amrah ta shigo da murnarta tace "zo kiga wani abu" A hankali Amrah ke yaye labulen dakin, tace duba kiga uncle yazo zance,Afrah ta saki baki tana kallon Farhan da yayi wani irin mugun kyau cikin kaftani da hula ta kasa kunne dmn jin abinda zai ce ma gwaggo, yace"gwaggo gun Afrah nazo zance ko za a bani damar na ganta"murmushi gwaggo tayi tace"kaji abinda take fad'a kenan?naji kuma ina son nayi mata ita ma kar a barta baya,to ai sae ka koma motar ka tunda zance kazo yi ni kuma bari naje na sanar da ita. Afrah da Amrah sukayi saurin sakin labulen qofar gwaggo ta shigo tace"to Afrah ai sae kije uncle d'inki yazo zancen dan haka kar ki 6ata masa lokaci daga haka ta fita. Afrah ta qanqame Amrah tace"yes uncle ya fanshe fushin da nake dashi tunda yamin abinda nake so ,amma fa sae naja class kamar yanda kowace budurwa ke jama saurayinta har dai idan tana fushi dashi, za ayi qara'i yau kenan?ah kema kin sani.
Cikin minti ashirin ta gama shirinta tsaf cikin arabian gown ta kawo big eye glass tasa ,karan hancin ta ya qara fitowa da kuma hasken fuskarta kasancewar glass din mai duhu ne,ta tsuke d'an qaramin bakinta da yaji pink lipstick tana kallon Amrah sai wani juyi take,tace"na had'u ko kuwa da saura na?Allah kin had'u ,ryt kina ganin gayen ba zai raina ajina ba kuwa?shi uncle d'in? Dariya sukayi har da tafawa Afrah tace"a wani film naji haka, bye zan tafi sae na dawo kisha labari.
Tafe take cikin tafiyar qasaita kmr da gaske zance zata tafi gun saurayi sbd ita haka take ji kmr dagaske.
Haka taci gaba da tafiya cikin taku d'ai d'ai tana tauna orbit a hankali wanda ba lallai bane ka iya gane tana cin chewing gum kai tsaye sae idan ka kalle ta da kyau. Hango shi tayi cikin mota ya hakince kmr wani governor tana qarasowa yayi saurin bud'e mata gambun motar ta ciki, ta shiga a hankali ta zauna ta rufe, Action! shine abinda ta furta a ranta. Hakan yasa ta sha toka ta d'orà qafà kañ qafà tare da juya masa baya tana kallon wajen motar ta jikin glass, sae ci gaba take da tauna chewing gum cike da natsuwa.
*Futha Luv💅🏻 &Billy giro😊* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:23PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [11/14/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*
*Futhalurv.WordPress.com*