Afra ko amrah complete - Chapter 30
Afra ko amrah complete Chapter 30: Afra ko amrah complete Chapter 30. *```π 87π ```* Hijabin jikinta ya shiga cire mata ya share mata hawaye wasu suka sakeβ¦
3,982 words
*```π 87π ```* Hijabin jikinta ya shiga cire mata ya share mata hawaye wasu suka sake zubowa yace"ba nace kukan ya isa ba"cikin yanayi na rashin ganin sa sosai kan qwallar da ta cika mata ido ta d'ago tana kallon shi tace"uncle shikenan Amrah ta tafi ta bar ni ni kad'ai"mugun tausayi ta bashi yanayin yanda tayi magana,da kulawa ya kwantar da kanta kan qirjinsa yace"yi haquri daina kuka kinsan ai zasu dawo ne ku riqa kaiwa junan ku ziyara tunda anguwar da zasu tare ba ko wani nisa ne da ita ba" Nan yayi ta rarrashinta har ya samu tayi shiru ,daga hk bacci ya kwashe ta a jikinsa, ya kwantar da ita ya fita zuwa 6angaren gwaggo ya same ta zaune shiru ita ma da gani tana jin kewar Amrah sosai. Sallamar da yayi ne ya dawo da shirun da tayi ta amsa mai sallamar tace"sae na shigo da Afrah koda na shiga bayi na fito ban ganta ba nsn 6angaren ku ta koma tana ta kukan ko?eh wlh amma dai yanzu na samu tayi bacci, to shikenan idan ta tashi ka samu abinda ka bata taci sbd tun jiya rabon su da abinci ita da Amrah kan kukan da suka sama gaba. Yace"to shikenan in ta tashi zan bata d'in. Nan suka ta6a er fira snn ya tashi ya fita.
Koda ya dawo ya sami Afrah toilet sae amai take kwarawa wani irin kala rod'i rod'i, ya kalli rgr jikinta duk ta 6aci da aman yace"sannu ko ya akayi haka? Ina cikin bacci ne kawai naji na tashi ina amai, rgr ya tayata cirewa ta kuskure bakinta tayi brush da taimakon sa ta d'an watsa ruwa snn suka fito ya had'a tea mai kauri ya bata tayi saurin kauda fuskarta tace"uncle wani abu nakeji a cikina har zuwa zuciyata ka bari na daina ji tukun" Afrah yunwa ce fa ba komai ba kisha tean zaki ji kin daina jin abinda kike ji ,ai ko aman da kika yi duk na yunwa ne, da qyar dai ya samu tasha yace"nemi tufafi ki saka kiyi sallah ni zanje masallaci" Daga haka ya fita byn ya dawo ya sameta kwance ta gama sallah ya ajiye food flask d'inda ke hannun shi a kusa da ita yace"tashi kici abinci, mene ne uncle? Bud'e kular yayi dmn shima bai san abinda ke ciki ba , mayen mayen shinkafa ne da yayi ruwa ruwa yaji ganyen sure ,Afrah ta tashi da hanzarinta tace"ina ci ina aka samo shi? Gwaggo ce ta dafa miki , wani dad'i taji har ranta ta kasa haqura tana qoqarin saka hannu ta fara ci, ya riqe hannun yace"zaki qona hannunki fa"pls uncle loma d'aya zanyi,to bari na baki da kaina ,nan yakai ya d'ebo ya rage masa zafi da iskan bakinshi snn ya bata taci,tace "pls uncle a qara min loma d'aya ba musu ya qara mata yace"ynz bari a d'auko plate a zuba akai kinji zai fi sauqin ci,ta gyad'a masa kai kawai amma bata jin zata iya haqura har a d'auko plate bata qara wata lomar ba.
Koda ya dawo da d'aukar plate ya sameta sae yarfi take da hannu qwallah cike tap a idonta yaje da kulawa ya riqo hannunta yace"Afrah meyasa kika sa hannunki bayan kinga zafi ne da abincin sosai? Kayi haquri uncle na kasa haqura ne,zama yayi tare da jingina ta a jikin sa ya riqo hannun ya lashe abincin da ke jikin hannun snn ya shiga hura mata iskan bakinshi akai,a shagwa6e tace"pls uncle a zuba muci" Nan ya zuba abincin ya bata spoon tace"um um da hannu yafi dad'i" Da hannunsa ya shiga bata abincin tana ci har tayi loma uku taga baya ci, tace"uncle kaifa ?kici tukun, um um nidai muci tare,na baka? Um um bari na bawa kaina kar ki qona hannunki, um um uncle zan iya ya rage zafi kasan, nan ta shiga bashi yana bata har suka kammala cin abincin. Da dare bayan isha'i Farhan ya fito daga wanka dai dai Afrah ta shigo dakin sanye da hijabinta har qasa da ta gama sallah ,suna had'a ido tayi saurin duqar da kanta yazo gab da ita ya riqo hannyenta yace"me kike so ?kallon sa tayi cike da son gaya masa abinda take so har ta fara magana sae kuma tayi saurin katse kanta"yace"Afrah gaya min mana kinji"um um ka bar shi kawai zan tambayi gwaggo, daga haka ta zare hannyenta daga nashi tayi saurin fita d'akin tana ji yana kiranta tayi kmr bata ji ba tayi tafiyar ta 6angaren gwaggo ta sami gwaggo tana lazimi sae da gwaggo ta d'an taqaita tukun tace "ya akayi ne Afrah ko Farhan ya fita ne? Gwaggo so nake ki aramin wyr ki ina so zanyi waya da Amrah, je kan dressing mirror ki d'auko, tashin da zata yi ne sukayi ido hud'u da Farhan, tayi wucewarta zuwa d'aukar waya shi kuma ya shigo yace da gwaggo"zan fita koda akwai abinda za'a siyo ?eh to fruits ne kawai,yace"to kafin yake tashi ya fita. Afrah kuma ta kira wayr Amrah taji ta a kashe sae duk taji ba dad'i sbd sosai taso tayi waya da ita kafin a shiga bacci,kan dole ta haqura ta ajiye wyr. Suna nan zaune suna fira Farhan ya dawo Afrah tayi saurin tashi ta kama mishi kayan da ke hannun shi. Yace"je da ledar hannunki ki cire na ajiye wa store sauran ki wanke kixo ki zuba a fridge. Afrah ta tashi taje tayi kmr yanda yace ta dawo tana qoqarin kwanciya sbd d'an aikin da tayi har ta gaji yace"kar ki kwanta dare yayi zo mu tafi ,nan yaja hannun ta sukayi sallama da gwaggo suka tafi. D'akin shi ya tafi da ita yace"ke wannan hijabin baya takura ki ne kina zama dashi a cikin gida haka"cire hijabin kije kiyi wanka kiyi shirin bacci, a sanyaye tace"ina so zansha fruits tukun" Yace to cire hijabin dai . Byn ta cire ta jawo fruits tayi zaune tana sha ya bita da kallon da yasa ya fahimci har rama tayi a en kwanakin nan. Tace"zaka ci ne uncle? Um um gama dai ki had'o min coffee nasha.
Tana gamawa ta had'a mishi coffee ta shiga wanka koda ta fito bata ganshi bedroom ba ta leqa living room ta hango shi zaune kan sofa ya jingina bayanshi tare da d'ora qafafun sa kan footstool ya gama shan coffee yana kallo. "Zo" shine abinda yace yayinda take qoqarin komawa bedroom tazo ta zauna kusa dashi ta sadda kai kmr wata baquwar shi yace"d'azun kin sami yin waya da Amrah? Girgiza kanta tayi tace"wyr ta a kashe take" To me yake damunki ne naga kinyi suku suku? Ba komai,kallonta kawai yayi yace "shike nan tashi muje daga ciki"da shigar su ta nemi guri zata kwanta yace"ya haka ba kayan bacci? Tashi tayi zata d'auko kayan baccin yace"zo ,byn tazo yace"gaya meyasa kike son kwanciya da towel?sbd nsn zafin jiki zai tashe ni anjima idan na tashi nayi wanka sae nasa kayan baccin, yace"yi hqr kisa su a yΓ±z bana son kina kwanciya ba kaya a jikin ki. Tace"to"snn ta tashi ta nemo riga ta saka ta kwanta nesa dashi kmr wata mai shakkun shi "yace"Afrah bana jin dad'in yanayin nan naki fa, zo kan jikina ki kwanta ,jiki sanyaye taje ta kwanta kan jikin sa ya shafo bayanta a hankali yace"fad'an da mukayi ne yasa kike baya baya dani ko?kin kai ni maqura ne Afrah ko kad'an banji dad'i ba,kinsan photon ba qaramin kyau mukayi ba da dole duk wanda ya ganshi ko bai san mu ba zai yi sha'awar ajiye photon a wayr sa,dmn a gabana naga JB yayi saving din photon byn na bashi wyr shi, shi ba d'an uwanki bane ta koina ta yaya zai ajiye photon matar wani a wyr shi, gashi ba mayafi a jikin ki ko ma kina da mayafi ni banga dalilin ajiye photon ki a cikin wyrshi ba, ya ajiye na yarintar ki ai hkn ya isa. Snn kuma idan ba kya kishin kanki ai ya kamata ace ni kina kishi na kar wata ta ganni ta qyasa har taje ta fara tunanin yanda zata mallake ni. Daga hk yayi shiru Afrah tace"dan Allah uncle kayi haquri kuskure ne da rashin tunani" Ya d'ago ta yana kallonta yace"ba komai ya wuce sae ki kiyaye nan gaba"ta gyad'a masa kai tana wasa da en yatsunta ,ya kai hannun ya rage hasken d'akin ya gyara musu kwanciyar su suka shiga bacci. ** ** ** ** A 6angaren su Amrah kuwa ba qaramar tarba ta samu ba a gun dangin fu'ad tunda sukaje en uwansa keta tururuwar zuwa ganin ta kaf cikin su ba wanda bai ji dad'in ganin ta a matsayin matar fu'ad ba inda cikin qaqanin lokaci suka sata a jikin su kmr wacce suka saba da ita, hkn yasa ita ma ta sake dasu kmr ta sansu. Yinin rnr duk bata sami kanta ba gashi taso ta kira gwaggo tayi magana da Afrah.
Zaune suke bayan isha'i kan dining ita da fu'ad da kuma iyayensa wanda kallo d'aya zakayi musu kasan sunyi matuqar jin dad'i da samun Amrah a matsayin sirikarsu. Bayan sun gama taje masaukin su ita da fu'ad ,suna shiga fu'ad ya fita ya bata guri dmn ta samu ta watsa ruwa. Ta jima a gurin wankan kafin take fitowa suka yi kici6is da fu'ad da ya shigo d'akin, ba shiri ta koma bathroom sbd d'an guntun towel ne a jikinta,shi kuma fu'ad yayi saurin juyawa tare da fad'in "sorry" snn ya fita ,bai dawo ba sae da ya tabbatar ta shirya ,bathroom kawai ya fad'a zuwa wanka. Amrah kuwa sae a lokacin ta samu damar lalubo wayarta cikin jaka, tsaki tayi ganin wayar ta mutu ba caji sae duk taji wani qunci dmn ko yaya taso tayi waya da gwaggo da Afrah,amma haka ta haqura taje tasa caji. Koda ya fito har ta kwanta tayi lamo kmr mai bacci har da su rufe ido, har ya gama shirinsa bacci bai d'auketa ba,yaje kan gadon ya kwanta tare da rage hasken d'akin. Ba zato ba tsammani taji ya jawota ya rungume sae duk ta nemi natsuwarta ta rasa,sbd sosai ya shigar da ita qirjinsa har suna jin saukar numfashin juna, komai kasa ce masa tayi amma cike take da son qwace kanta daga gareshi, yaje saitin kunnenta yace"Amrah ki natsu mana ba abinda zan miki nasan kin gaji da yawa kina buqatar hutu, ki cire fargabar komai kiyi baccinki a jikina kinji shi kawai nake buqata daga gareki,ajiyar zuciya ta sauke a hankali tana tunanin yanda zata iya bacci kan jinkin d'a namiji abinda bata ta6a yi ba,da dai qyar ta samu bacci ya d'auke ta, sae a lokacin fu'ad ya shiga qarewa kyakkywar fuskar ta kallo musamman en lips d'inta masu kyau kmr ta shafa janbaki ,a hnkli ya kai babban yatsan sa yana shafa lips d'in, can ya daina tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya ya qara rungume ta yana gode ma Allah cikin ranshi da ya bashi Amrah a matsayin mata kuma uwar 'ya'yansa nan gaba kad'an in Allah yace.
*Billy giroπ&Futha Luvπ π»* π π π π π π π π π π [10:23PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [ 11/20/2016] π π π π π π π π π *```AFRAH KO AMRAH ```* π π π π π π π π π
*```Na Billy giro π&Bilqis Sidibeπ π»```*
*Futhalurv.WordPress.com*
*```π 86π ```* Ta jima a gurin zaune tana kuka da gwaggo har Amrah ba wanda yace da ita qala sbd gabad'aya ta cika su da tausayi. Can gwaggo tace" zo Afrah "kmr jira take taje kan jikin gwaggo ta fashe da wani sabon kuka"gwaggo tace "kukan ya isa haka bari zuwa anjima dai dai ya sauko kije ki basa haquri" Afrah dai bata ce komai ba sae kukanta taci gaba dayi a jikin gwaggo,gwaggo na fmn rarrashinta. Har ta koma 6angaren su kuka take ganin dare yayi ta tashi ta fad'a toilet tayi wanka tayi shirin bacci taje d'akin Farhan cike da fargaba , ta same shi ya gama shirrin bacci zai kwanta ,suna had'a ido gbn ta yayi mugun fad'uwa ta rasa ma ta yanda zata bashi haquri har ta gaji da tsayuwa bai ce da ita komai ba ,hasali ma kwanciyar sa yayi ya rufe idonsa kmr mai bacci ,sum sum ta fita ta bar mai d'aki bata zarce koina ba sae 6angaren su gwaggo sae Allah Allah take idan basu rufe 6angaren su ba sbd da goma ta gota rufewa suke. Tana isa kuwa dai dai Amrah zata rufe 6angaren ,Amrah ta dakata tana kallon Afrah wacce ta shigo ,Afrah tace "ki rufe kawai nan zan kwana"
Taje ta sami gwaggo ta gama wutiri ta zauna kusa da ita cike da son tayi kuka,gwaggo ta jawota jikinta tace"yaya ne yaqi ya haqura? Girgiza kanta tayi yayinda qwallah suka cika mata ido tace"gwaggo na kasa masa magana tsoro nake ji kar ya dake ni har yanzu ransa 6ace yake" to tashi ki koma da safe sae ki bashi haquri, hawaye suka zubo mata ta share hawayen tace"gwaggo dan Allah ki barni na kwana a nan wlh bazan iya bacci ni kad'ai a d'aki ba kuma nsn in na kwana a d'akin sa qila zai dake ni sbd ko gani na baya sonyi rufe idonsa ma yayi da naje ynx" Gwaggo ta numfasa tace"Shike nan jeki hau gado ki kwanta amma ki daina kukan nan da safe zan bashi haquri da kaina kinji. Ta gyad'a mata kai tare da qara share hawayen fuskarta ta tashi taje ta kwanta.
Washe gari tun da asuba ta koma 6angaren su tayi kici6is da Farhan da ya dawo daga masallaci yana batun shiga ,saurin shigewar sa yayi ,yayi kmr ma bai ganta ba. Jiki sanyaye ta shiga taje d'akinta ta fad'a kan bed tana kuka marar sauti daga hk har bacci ya kwashe ta. Firgigit ta tashi ta nufi kitchen sbd yau rnr aiki ce Farnhan na fita. Cikin sauri sauri take aiki sbd lokaci ya tafi so take ta kammala kafin Farhan ya fito. Da qyar taga ta samu ta kammala sae dai duk ta yayyanke hannun ta babbar yanka kuwa dmn sae bleeding hannunta yake jinin yaqi tsayi tayi zuba ruwa tana wankewa amma a banza,sama ta haura zuwa dakinta dmn nemo first aid kit. Bata jima da shiga ba Farhan ya fito zai wuce sae da ya kusa saukowa idon sa yakai kan jinin Afrah da ya d'id'd'ga kan hanya ,bin jinin yake har ya tafi kici bai ganta ba, hklnsa ne ya tashi ganin jinin kitchen d'in yama fi yawa, sama ya haura zuwa d'akinta dai dai ta gama dressing hannun zata fito ,yanda ta ganshi kai tsaye sae da gabanta ya fad'i ta dake ta gaida shi bai amsa ba yace"jinin mene ne nake gani akoina?na yanke ne kan saurinda nake zan fere doya, kinga illar ana koya miki aiki kina sa son jiki da wasa ba kya maida hkli,ai kinga Amrah duk saurin da takeyi bata yanka hannunta kmr yanda kike , yana magana ne rai 6ace. Daga haka yasa kai zai fice tace"uncle abincinka fa? Ai koda kika d'ora girkin sanin kanki ne lokaci ya tafi, to uncle pls kaje dashi office,ko naje dashi bani da lokacin cin shi asali ma ban saba yin haka ba, nan ya wuce bai jira me zata sake cewa ba ,tabi shi da ido cike da qwallah a idonta bai qarasa fita ba ya juyo yace"kar ki girka na rana baxan dawo da wuri ba idan kina buqata sae kije 6angaren su gwaggo kici. Hawaye masu zafi ne suka zubo mata lokacin da ya gama maganar ya fita ba abinda yasa ta hawaye sae don wa shi kad'ai ta soya doyar sae gashi yaqi ci yaqi kar6a yaje da ita. D'aukar break fast d'in tayi taje ta kaiwa mai gadi daga nan ta wuce 6angaren su gwaggo.
Sae da yamma Farhan ya dawo gidan bai zarce koina ba sae 6angaren gwaggo da shigar sa ya sami Afrah kwance a kan tiles tana bacci ga plate d'in fruits a gabanta.
Sallama yayi ya shiga daga ciki ya sami gwaggo ya nemi guri ya zauna snn suka gaisa gwaggo tace"Farhan kayi haquri ka bawa Afrah wyrta tunda tace zata canza photon kuma ka daina fushin da kake yi da ita ka ganta tun da safe komai ta kasa ci sae kuka ta sama gaba" Yace"Afrah bata ji gwaggo kin sani ,kuma wyr nan dama tayi girma da ta riqe ta don kawai ta matsa tana son irin wayata ne shiyasa na saya mata amma sam bai kamata ace tana riqon tsadaddiyar waya sosai ba a yanda take da sakaci" ka dai yi haquri Farhan kasan Afrah yarinya ce sosai, gwaggo ki barta kuma ki daina biye mata dan Allah, daga haka ya tashi ya fita. Afrah wacce tun shigowar shi ta farka taji sak abinda yake fad'a taje jikin gwaggo murya raunane tace"gwaggo ni ba sae ya bani wayar ba, so nake yayi haquri ya daina fushi dani" Afrah kije da kanki ki lalla6a shi kinji, ai ke matar sa ce kinsan hanyoyi da dama da zaki bi ki shawo kan mijinki sae kiga har wayr ya baki ba tare da kin nemi ya baki ba. Gwaggo tsoro nake ji kar ya min wani fad'an,um um ba zai miki fad'a jeki.
D'ari d'ari Afrah ta nufi 6angaren su tana tsara yanda zata bashi haquri har ta isa qofar d'akin shi tayi knocking ,kanta qasa ya bud'e qofar tayi qarfin halin shiga ba tare da ya bata izini ba. Taje kan sofa tayi zaune ta kame guri d'aya tana kallon Farhan da ya bud'e frigde ya jawo plate d'in fruits da fresh milk ,Afrah tayi saurin jaye idonta ganin yayo gurinta dasu ya d'ora kan coffee table d'inda ke gurin ,ya nemo stool ya zauna yana mai fuskantar ta fuska d'aure ya kalleta yace"feed my unborn child"kallon sa tayi ta kuma saurin d'auke idonta ta kai hannu ta fara ci ,yace"kaf plate d'in zaki cinye kar kiyi tunanin ragawa dmn baki ajiye mai cinye sauran ba" ta kalli tulin fruits d'in da ke kan plate tace"uncle ya min yawa" Na dai baki 15 mnt ki gama cinye shi kaf idan kuma kika qara koda minti d'aya ne zan qaro miki wani plate . Haka Afrah tayi ta d'ura fruits sauri sauri har ta kusa cinye wa,ta d'an tsaya ta huta sbd yanda cikinta ya cika,snn taci gaba daci har ta cinye ya tsiyaya mata fresh milk ta kar6a kmar zata yi kuka sbd tasan ba makawa idan tasha sae tayi amai dmn bata jin yanda cikinta ya cika akwai gurin fresh milk,amma kan dole ta kai cup a bakinta ta shanye ta kaf ta ajiye cup had'e da yunqurin amai, yayi saurin zaro handkerchief ya riqo hannunta ya d'ora mata yakai hannun izuwa hancinta ,wani irin qamshin dad'i taji na daban ya daki hancinta da ya mantar da ita amman da yake qoqarin xo mata, sae da sukayi minti uku a haka snn ya zare handkerchief dinsa tare da kallon yanda take numfashi sama sama kan cikinta da ya cika da yawa yace "fiye da hk zan miki idan kika sake zama baki ci abinci ba" Ya 6are wani magani yana mai kallon hannun ta da ta yanke ya miqa mata yace"kar6i kisha ,ba tare da tasan na mene ne ba ta kar6a tasha, yaja hannun ta suka fita suka zagaye gidan kusan sau uku ,ga gidan daidai gwargwado yana da fad'i,ai kuwa tuni Afrah ta gaji har zufa na karyo mata, cikin ba jogging suke ba tafiya kawai amma ji tayi kmr tayi tafiyar 20 kilometers,hkn yasa take taji wani irin zafin jiki ya taso mata ,Farhan yace "kije ki watsa ruwa ki nemi guri ki kwanta" Daga haka ya saki hannunta yayi tafiyar shi.
Taje ta watsa ruwa tana fitowa d'aure da towel ta fad'a kan gado sbd wani bacci mai dad'i da taji yana fizgar ta ga d'akin ya d'au sanyin Ac sosai nan take kuwa bacci ya tafi da ita. Har akayi sallar magrib bata farka ba can cikin baccinta mai dad'i taji farhan na mata knocking tare da fad'in"ki tashi haka lokacin sallah yayi" Ta tashi a hankali ta kalli towel d'inta da ya rabu da jikinta ta jawo ta d'aura ta nufi bayi ta d'auro arwala ta fito tasa er duguwar riga mara nauyi ta zuba hijabinta har qasa ta fara sallah. 6angaren gwaggo ta nufa bayan anyi sallar isha'i ,gwaggo tace "inace kin samu kin lalla6a shi ya sauko? Kan ta ba gwaggo amsa aka kira gwaggo a waya hkn ya ma Afrah dad'i sbd bata son a karo na biyu tace ta kasa bashi haquri ,koda gwaggo ta gama waya hnklinta ya d'auku kan abubuwan hidimar biki da aka shiga shigowa dasu gidan, sae sauri take ta bada makullin store a zuba a ciki.
A washe garin rnr aka sama amarya ruwa tunda asuba da yamma kuma aka yi yinin qawaye,d next day a washe garin suka je saloon da dawowar su sukayi zaman qunshi kasancewar da yamma za'ayi wankin amarya. A can kusa da garden suka tare da qawayen su gurinda yafi iska da dad'in zama sae fira suke cike da nishad'i yayinda ake zana ma Amrah lalle ,Afrah kuwa tuni an gama mata sae jiran bushewar sa take. Fitsari ne ya tashe ta ta tafi cikin sauri zuwa 6angaren su sbd shine mafi kusa, cin karo tayi da Farhan dake saukowa cikin sauri zai fita, a rikice ta bud'e ido ganin yanda ta 6ata mai fararen kaya, tace"dan Allah kayi haquri uncle wlh bansan da kai ba, komai bai ce mata ba ya juya zuwa sama ,ta bishi da ido tana tuna rabonta dashi yau kwana d'aya cikin na biyu kenan sbd 6angaren gwaggo taci gaba da kwanan ta haka ko tazo d'aukar kayan sawa bata had'uwa dashi sbd shima hidimar biki bata barshi ba. D'akinta taje tana tunanin yanda zata yi fitsari da lalle a hannunta ,sae kawai taga farhan ya shigo ta samu da taimakon sa tayi fitsarin cikin sanyin murya ta masa godiya bai kula ta ba ya d'auki abinda yazo d'auka ya fita ya barta tsaye tana mmkin irin fushi nashi da har yanzu bai sauko ba.
kuka take ji amma ta hana kanta kukan ta fita.
Da yammacin rnr akayi wankin amarya d next kuma akayi walima da safe da dare kuma akayi dinner ,bikin ya qayatu ba kad'an ba dmn ba qaramin kyau amarya da ango sukayi ba kowa na d'aukar su photo banda Afrah da bata da waya hkn yasa ta d'anji ciwo a ranta amma dole ta haqura ko ba komai akwai photunan kati dmn an d'auko en camera ba ko guda ba. Gobe da safe ne amarya da ango zasu bi flight su tafi abuja sbd iyayensa suka buqaci haka amma a iya sati biyu zasuyi su dawo sbd a nan bauci akayi wa amarya jere.
Tunda dare da aka dawo dinner Afrah da Amrah sae kuka suke kan rabuwar da zasuyi wacce sae zumunci zai sake sada su ba dai suyi irin zaman da sukayi da ya riga ya wuce ba. Haka ma washe gari sunci kuka mai isar su a filin jirgi kmr wad'an da akayi wa mutuwa, da qyar fu'ad yaja amaryar sa suka tafi. Afrah kuwa gwaggo ce ta jata.
Bayan sun koma gida ta tafi 6angaren su tana ta kuka ita kad'ai a cikin d'akinta tana tunanin yanda zata yi rayuwa ba Amrah ga Farhan na fushi da ita wanda har yanzu yaqi ya bata fuska bare ta bashi haquri. A hankali taji an turo qofar d'akin ta d'ago manyan idanuwanta masu kyau da sukayi jajir kan kuka tana kallon Farhan dake qarasowa cikin d'akin, ganin kawai tayi ya zauna kusa da ita ya jawota jikinsa ya rungume tare da fad'in "yi haquri kukan ya isa haka" ajiyar zuciya ta sauke ta qara shigewa jikinsa yayinda wasu sabbin hawaye ke gangarowa a hnkli kan kumatun ta.
*Billy giro&Futha luv* π π π π π π π π π π [10:23PM, 11/30/2016] Billy Geeero: *[ 11/22/2016]* π π π π π π π π π *```AFRAH KO AMRAH ```* π π π π π π π π π
*```Na Billy giro π&Bilqis Sidibeπ π»```*
*Futhalurv.WordPress.com*
*```π 88π ```*