Afra ko amrah complete - Chapter 31
Afra ko amrah complete Chapter 31: Afra ko amrah complete Chapter 31. Washe gari 6angaren su Afrah ,Afrah ce a kitchen Farhan yazo ya same ta ya rungumo ta…
4,012 words
Washe gari 6angaren su Afrah ,Afrah ce a kitchen Farhan yazo ya same ta ya rungumo ta ta baya tare da goga tsinin hancinsa akan gefen fuskarta yace"kin manta yau bana fita aiki rnr bacci ce? Ban manta ba uncle kasan yanzu abincin mu da gwaggo yake kuma banda saurin aiki, haka ne amma inaga sae na nemowa gwaggo yarinya mai aiki ko ba komai tana cire mata kewar bacci ita kad'ai ,gsky kam uncle ya kamata dmn bacci mutum d'aya akwai had'ari. Qara matse ta yayi a jikinsa har sae da ta saki er qara yace"ashe kinsan da haka kwana hud'un nan kika barni ina bacci ni kad'ai ko me zai faru dani ba ruwanki ko?juyowa tayi tare da kai hannyenta ta bayan wuyan shi ta jingina bayanta a drainboard tace"uncle ai kai ke fushi dani a lokacin ko gani na ma baka sonyi"wa ya gaya miki?turo baki tayi tace"har sae an gaya min bayan gashi a zahiri"cike da sha'awa yake kallon d'an bakinta yace"sae nayi maganin bakin nan naki mai tsiwa har sae yayi jini"hannu ta kai ta rufe bakin tace"yi hqr uncle" wannan kam kin iya fad'in shi haquri ba,to uncle me kake son nace? Yace"kinga zo na koya miki aiki a sauqaqe,uhm uncle kenan ,kina mamaki ne ai daa da ina yaro ina matuqar son naga ana girki shiyasa duk lokacinda gwaggo take kicin ina tare da ita,sae kawai naga na iya girki cikin ma ban cika zama ba sae idan anyi hutu. Dan haka sai kisa ido kiyi kallo yau, yaje ya d'ebo Arish ya d'auko peeler had'e da chipper da kuma sauran kayan aiki ya d'auki peeler ya fara ferewa byn ya gama ya wanke shi ynda ya dace ya fara chipping saura qwara biyar ya gama chipping ya d'auko frying fan ya d'ora kan gas cooker ya zuba mai ya yayyanka albasa er dai dai ta yanda man zai yi dad'in qamshi snn ya kunna gas cooker ,ya koma ya qarasa chipping d'in sauran potato ya zuba gishiri d'an dai dai ta yanda ba zai yi yawa ba kuma ba zai yi kad'an ba, koda yaje ya zuba, mansa yayi zafi dai dai yanda yake so ba tare da albasar da ya saka ta qone ba sbd manyan yanka ne sosai . Ya juyo gun Afrah yace"yanzu ba wai sae na jira har potato d'ina ya soyu ba ,zan d'auko plantain na fere na yankata slice by slice snn na barbad'a d'an gishiri ina yi ina duba potato d'ina kar ya qone kasancewar jimawar da yake yi bai soyu ba gashi kuma har zubi biyu zanyi kinga har qwaina zan iya had'awa shima na ajiye shi ba tare da na kad'a ba dmn kar yaje ya tsinke. Nan ya had'a plantain har da qwai ,da ya gama suyar potato ya kwashe snn ya zuba plantain byn tayi ya cire ya rage mai ya kad'a qwai ya soya,ya d'ora musu ruwan tea a electric kettle jug ,ya gyra kitchen ya dawo kan ruwan tean su da suka riga suka tafasa ya juye a flask. Suka d'auki break fast d'in zuwa dining bayan sun gama jerawa ya kalli Afrah yace"u see banyi minti 40 ina aikin nan ba amma ke har kusan two hours kke kwashewa,ya kike aikin ki ne hln? Nifa duk abinda na fara sae na kammala shi tukun nake d'auko wani , ta fad'i haka ne tare da kai hannu ta rufe fuskarta tana dariya ,yayi dariya yace"to haka kika ga anayi?Aa but ban kawo cewa aiki cikin aiki kesa kayi saurin kammalawa ba,na d'auka ko tsantsar wahala ce kawai ba wata riba, shiyasa duk abinda na fara sae na kammala snn nakeyin mai bi masa sbd nafi jin natsuwa na kuma fi ganin ban wahala sosai ba,hm ai naki ne mai wahala dmn kinga dai yanda nayi ynx shine easy way da zaki kammala abinci kan lokaci ba tare da kin wani wahala ba, sae ki kiyaye kuma duk weekend inshaAllah zan riqa koya miki har ki saba, Nagode uncle,most wlcm ,muje muyi wanka sae a kaiwa gwaggo nata breakfast. Bayan sun fito har sun shafa Vaseline ,Afrah tace"uncle kwanta na maka tausa kar jikinka yayi tsami kayi aikin da baka saba yi ba, hm Afrah kenan shi d'an wannan aikin zai sanya jikina tsami? Uhm Uhm uncle nidai ka kwanta nace, ba musu ya kwanta ta fara mishi tausa a iya guri d'aya yaji tana faman tausa mishi, yace"wai Afrah baki iya tausa bane sae guri d'aya nake jin kina tausa min"uncle kmr ya?kwanta na miki kiji yanda ake, nan ta kwanta ya shiga tausa mata jikinta ta koina sae fira yake mata can yaji shiru ta daina amsa mai, koda ya duba ashe tuni tayi bacci murmushi yayi tare da fad'in"lallai yarinyar nan kinji dad'in ki da yawa wato bacci kikayi kan dad'in tausa Tada ta yayi zaune takai hannu ta kama towel d'inta dake qoqarin zamewa ,cikin kukan shagwa6a tace"uncle bacci fa nake ka tashe ni" Dole na tashe ki Afrah ba muyi breakfast ba fa ,tashi ki shirya ki kaiwa gwaggo abinci ki dawo,kwanto mai tayi kan jiki tare da fad'in "to uncle bari bacci ya d'an sake ni,na bari, tayi minti 2 a jikinshi snn ta tashi suka shirya ta d'auki breakfast d'in gwaggo ta kai mata ta dawo . Bacci tayi mai isarta bny sun gama breakfast . Tana tashi bata zarce koina ba sae 6angaren gwaggo tace"gwaggo ina son zan qara gwada kiran Amrah ko Allah zai sa a sameta" Nan gwaggo ta miqa mata wayr ta shiga dialling.
6angaren Amrah kuwa duk da ba abinda ya shiga tsakanin ta da fu'ad ba qaramin kunyar had'a ido tayi dashi ba kan yanda yayi bacci rungume da ita, shiyasa yana tashshe ta ta fad'a bathroom ba tare da ta yarda sun had'a ido ba.
Bayan sunyi wanka sun shirya yaja ta suka je gaida iyayen sa snn sukayi breakfast su duka har iyayen. Bayan sun gama breakfast Baban fu'ad ya tashi tare da fad'in"fu'ad ka same ni a d'aki" Sae da suka shige umman fu'ad ta dafa kan Amrah tana murmushi tace"tashi kije ki kwanta ki huta kinji" Kunya Amrah taji sosai kaddai umman fu'ad ta d'auka ko wani abu ya shiga tsakanin ta da fu'ad shine tace mata hakn....ta katse ta da cewa kinyi waya da mutanen gida kuwa? girgiza kanta tayi tace"Aa waya ta ba caji amma nasa jiya da dare "ikon Allah ynz bakiyi waya dasu ba kuma shine kikayi shiru baki snr ba a kira suji cewa kun iso lafiya, ni sam hankali na ya d'auku fa, kuma shi fu'ad ko ya tambaye ki zancen kin kirasu bai yi ba ko? Tace"mama ai shima hankalinsa ya d'auku ne ga dukkan alamu, to shikenan , nan tayi dialling number gwaggo suka gaisa har tana bata haqurin kan rashin kiran da ba'ayi ba,daga bisani ta bawa Amrah waya tace"tashi kije d'aki kuyi waya,cike da jin kunya ta kar6i wyr ta tashi ta tafi. Sae da ta gama gaisawa da gwaggo snn aka bawa Afrah, cikin muryar kuka tace"Afrah i missed u, kiyi haquri nsn kin kirani wayata a kashe ban sami kaina bane sae da dare kuma koda na lalubo wyr ba caji,haka Afrah cikin muryar kuka tace"ba komai amma dan Allah ki riqa barin wayr ki kunne muna waya kinji, inshaAllah ki gaida uncle. Daga haka suka ajiye wyr dai dai fu'ad ya shigo ya sameta tana share hawaye, cikin damuwa ya jawota jikinsa yace"Amrah lafiya me aka miki? Ba komai waya nayi da Afrah, ajiyar zuciya ya sauke yace"shine kike kuka,ta gyad'a masa kai tare da janye jikinta daga nashi yace"to yi haquri ai sati biyu kawai zamuyi mu koma ku riqa kaiwa junan ku ziyara. Kuma kiyi haquri jiya kwata kwata har izuwa yau na nemi wayata na rasa amma sosai naso da isowar mu ki kirasu ki snr dasu mun iso lafiya,sae mutane suka d'auke min hankali, ba komai ,ga wayr mama ,kin gama ne?eh anijma zan kirasu a tawa wayr ,ya kar6i wyr yana mai kallonta snn ya fita.
6angare Afrah kuwa cikin yanayi na jin tausayin Amrah ta kalli gwaggo tace"gwaggo Amrah ta ban tausayi shike nan fa muda ita ko sun dawo nan garin sae dai ziyara "ai Afrah shi aure haka yake sae ka koma cikin wasu kana sabuwar rayuwa ,tun kana jin kewar mutanen gida har kazo ka saba, ni kam gwaggo ngde Allah da yasa uncle na aura da bansan ya zanyi rayuwa cikin wasu ba, ai dan bai fad'a kanki bane da dole zaki haqura kema.
*🏅89🏅* Suna nan zaune suka ji sallamar Farhan ,gaban Afrah yayi mugun fad'uwa ganin sa tare da wata duk da cewa er qauye ce hkn bai hana taji wani irin kishi ba,ta kalli wata mata da ta shigo da alama mhfyr yarinyar ce sbd suna da kama, bata iya gaida kowanen su ba ta tashi ta fita.
Tana zuwa 6angaren su ta ajiye kuka sae kace wani abu aka mata ,farhan ya shigo d'akin ya girgiza kai yana mai kallonta yace"ke meye haka daga na shigo da mutane kizo kina kuka?to uncle ina ka had'u dasu da zaka wani jero da wata ku shigo tare,Yace"kin manta er aikinda nace zan nemowa gwaggo, ai itace na samo ,ajiyar zuciya tayi tace"to ya nagansu su biyu? Mahaifiyar ynyr ce tazo dmn tasan gidan da er ta zata yi aiki ,oho yanzu naji magana. Afrah kenan kin fiye kishi ita wnn er qauyen kike tunanin akwai wani abu tsakani na da ita? Ko yaya dai ne ai ita mace ce dole kuwa naji kishin ganin ku tare da ita,tashi nidai d'auko min ruwa nasha qishi nake ji, ya fad'i haka ne tare da kwanciya kan gadon yana mai dubin silin. Tana kawo mai ruwan ya tashi ya kar6a ya riqe cup d'in had'e da hannunta kmr ita ke bashi ruwan,kuma sae sha yake yana kallonta byn ya gama tace"mene ne uncle? Kin rame Afrah amma dai sae haske kike qarawa, yace"wai tukuna me kika d'ora a yau?ban d'ora ba ynx nake shirin tashi ,Afrah wane irin abu ne 12 da rabi fa tayi, abu mai sauqi ne zanyi uncle shiyasa nayi zamana, keda kike jimawa gurin girki, kamanta ka koya min yanda zanyi komai a sauqaqe, shi sau d'ayan? Eh mana bari kuma ka gani koda zaka dawo sallar zuhur inshaAllah na kammala komai. Yace"to shike nan ni zan fita by 2 zan dawo inshaAllah. To a dawo lfy.
Tare suka fito ta raka shi har gurin motar shi snn ta koma daga ciki ,ba inda ta nufa sae kitchen ta shiga d'ora girkin da take ganin xai yi sauqin dafuwa.
Koda aka gama sallah ta gama girkinta wato spaghetti da taji yankakkin kayan lambu da kuma qoda,sae farfasun kifi, taje ta jere kan dining ta d'auki abincin gwaggo ta kaimata.
Kan hanyarta ta dawowa ne taga an bud'e gate motar Farhan ta kunno kai ,cikin murna sosai ta isa gurin shi ta qanqame shi tana fad'in"uncle har na gama girki wlh ashe zan iya ,ta ware tafukan hannyenta tace"kaga kuma hannaye na ba inda na yanke ,murmushi yayi tare da bata peck kan goshi yace"sannu da qoqari kinci kyauta"dad'i taji har ranta tace"dgske uncle ?lumshe idon sa yayi tare da gyada kansa yace"muje daga ciki amma sae munci abinci tukun"
Suna gama cin abinci yaja ta zuwa d'akin shi yaje ya d'auko wyrta ya miqa mata yace"ga wyr ki na mayar miki tukun "yeah!nagode uncle!ta bashi Peck tare da zama kan cinyar shi. Ya riqo yatsanta ya sanya mata zobe mai kyau na zinari yace"wani abokina na raka shagon zinari na hango zoben nan ya min kyau sosai shine na saya miki!ihun murna ta saki ta qanqame shi dmn zoben akwai kyau ya kuma yi mata kyau sosai a yatsanta gashi kallo d'aya zaka yi masa kasan tsadadden gske ne. Ta kalli yatsan cike da murmushi ta shafi zoben tare da d'ora kiss akai haka shima Farhan ta sake rungume shi tare da bashi kiss tace"nagde sosai uncle, yace"to a min deep kiss mana, rufe fuskar ta tayi tana dariya yace"bazan samu ba kenan? sosai ma zaka samu amma sae ka rufe idonka tukun ,to na rufe cike da natsuwa ta kai bakinta kan nashi ta had'e inda da qyar ta samu ta qwaci kanta daga Farhan sbd shima ya shiga yi mata kiss d'in ba ita ba. Sun kwanta kan gado suna sauke numfashi su duka dmn sun bal'in jimawa had'e da bakin juna ,can Farhan yaje kan jikin Afrah yana kallonta still sauke numfashi take, ya shafo lips d'inta tare da fad'in"sorry na wahalda ke sosai ko? Idanuwanta da ke lumshe ta bud'e tana kallonshi tace"zaka kashe ni uncle?kan me? Kayi min nauyi, birginawa yayi ya maida ita smn shi ,shi kuma yana qasa ,kwantar da kanta tayi kan qirjinsa, zip d'in rgr ta taji ya bud'e yakai hannu yana shafa bayanta yace"ya naji ba bra a jikin ki?baka ga rigar ba breast curve ne da ita kuma ta kamani yanda ya dace,shafa bayanta kawai ya ci gaba da yi, Afrah tace"uncle wai dgske kake sae na haifu ko zanje school?eh mana,meyasa uncle byn cikin nan baya bani wahala ?sbd karatun medicine karatu ne da sae kin ajiye natsuwar ki gabad'aya ina gudun kar azo lokacin haifuwar ki yayi dai dai da exam ,ai zan iya uncle,kuma inshaAllah hkn ma bazata kasance ba?to naji sae nayi shawara dai, yes! Allah yasa ka yarda amin,ta tashi tayi zaune tare da juya masa baya acewar yasa mata zip,a maimakon taji ya rufe zip d'in sae hannunwansa duka biyu taji ya shigar dasu cikin rgrta ya d'ora su a hankali kan qirjinta tare da kwantar da kanshi a bayanta, wata wasa ta daban taji yanayi da hannuwansa a qirjin nata inda ta rasa Farhan wane irin mutum ne da yasan salon wasanni kala kala haka, duk tana tunanin nan ne lumshe da ido,cikin hikima ta dakatar dashi dmn bata jin zata iya jure wasar ta mata nauyi sosai,zip d'in rgrta ya rufe mata ya sake maida kansa a bayanta ya lafe. Ta jikin mirror ta hango yayi bacci ta tashi a hnkli tasa pillow ta kwantar dashi tare da gyra masa kwanciyar sa. Ta d'auki wyrta taje downstairs ta zauna falo ta kunna wyr ta kira Amrah suka jima suna waya sae fira suke kmr suna kusa da juna.
2weeks later Afrah ce a gaban Farhan cike da son tayi kuka sbd wyr da ta gama yi ynz da Amrah kan cewa sae kuma sun qara wasu sati biyu ko zasu dawo a cewar iyayen fu'ad ne suka buqaci haka. Lallashinta Farhan keyi Yace"Afrah kiyi haquri mana keda kullum kuna cikin waya da Amrah byn chatin d'inda kukeyi "Uhm uhm ni uncle banji dadi bane byn ance sati biyu zasuyi ynz kuma an qara wasu akai,tsoro ma nake ji kar iyayensa su samar masa aiki a can,to ai gaba ta kaishi ,haba uncle shike nan fa in hkn ta faru nida Amrah sae jefi jefi ba kamar suna nan ba, kwantar da hnklinki indai fu'ad ne ba zai yarda da yin aiki can ba dmn ko kad'an baya so.
Bayan sati d'aya cikin na biyu Afrah ce ta tashi daga bacci tana miqa sbd yanda jikinta ke mata ciwo ta koina dmn ba qaramin gajiyar da ita Farhan yayi ba yau. Tashi tayi ta gyran gadon ta feshe d'akin da Air freshener snn ta fad'a wanka.
Bata jima da shiga ba ta fara ihu cikin tsananin firgici tana kiran uncle ,a rikice Farhan ya shigo d'akin dai dai ta fito firgice daga cikin bayin ta shiga nuna mai cikinta tana fad'in "wayyo uncle wlh abu yana motsi a cikina!na shiga uku uncle ka cire min zai kashe ni! Da sauri ya jawota jikinsa dmn firgicinda ta shiga komai zai iya faruwa da ita,ya shafo cikinta tare da kai bakin sa saitin kunnen ta yace"Afrah ki daina ihu it's our unborn child ,d'agowa tayi kwalla tap a idonta hannunta na rawa ta ta6o cikinta tace"our unborn child?ya gyad'a mata kai yayinda ya cire suit d'in jikinsa yasa mata ksncewr ba komai a jikinta,ta koma da qarfi kan jikinsa ta rungume shi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya tace"uncle na manta da ina d'auke da ciki" Shima ajiyar zuciya ya sauke dmn firgicinda ta shiga ba qaramin firgita shi yayi ba kafin yasan mene ne, sun jima a haka Afrah ta d'ago a hankali tana kallon cikinta da ya sake motsa mata,bata ganin motsin sae jinsa take sbd a hnkil yake motsa mata,kmr ta ta6a sae kuma ta fasa ta koma jikin Farhan tana sauke ajiyar zuciya sbd still jikinta bai daina rawa ba. Sae da yaji jikinta ya daina rawa snn ya shafo bynta yace"kin gama wankan? girgiza masa kai tayi ba tare da ta d'ago ba yace"to tashi kije ki qarasa" riqe da gaban rgr ta tashi taje toilet . Bayan ta fito ko mai bata iya shafawa ba taje kusa dashi ta kwanta,frhn ya kalli yanda jikinta yayi very weak yace"Afrah kin tsorata da yawa ko?bata ce dashi komai ba sae hannun sa ta jawo ta rungume tare da lumshe idanuwanta , nan da nan bacci ya d'auke ta.
A qarshen satin su Amrah suka dawo,murna Afrah tayi ba kad'an ba inda ba don dare ba da sae taje. Tunda ta fito daga wanka take waya da Amrah har ta shirya tasa kayan bacci basu aje wayar ba, Farhan ne ya shigo d'akin yaje kan gado ya kwanta yana mai kallon Afrah ta jikin mirror da tun shigowar sa waya ke laqe a kunnenta amma bata cewa komai sae ma yanayin 6acin rai ya hango a tattare da fuskar ta,katse wayar yaga tayi tazo ta kwanta,ya kalle ta da kulawa yace"Afrah ya akayi na shigo na katse muku waya ko?"no uncle"iya abinda tace kenan takai hannu ta rage hasken d'akin" Jawota yayi jikinsa yace" gaya min to me ya 6ata miki rai?uncle ba komai kawai gobe da safe ina so zanje gidan Amrah ,meyasa bayan sunce su zasu zo, zan kirata su fasa zuwan sbd akwai abinda zai kaini,shike nan Allah kaimu gobe da safen. Tace "amin tare da gyara kwanciyarta ta shiga bacci.
Washe gari da qarfe goma sha d'ai ta tafi gidan koda ta shiga falon ta sami fu'ad zaune kusa da Amrah kmr wani mai lalla6a ta ita ko tana tirje mai,hkn yasa ran Afrah ya qara 6aci ,ta danne zuciyarta suka gaisa da fu'ad ya fita ya basu guri. Da taikaci Afrah ke kallon er uwar ta ta,ta fizgo hannunta suka haura sama zuwa d'akinta ,Amrah tace"Afrah lafiya kika shigo cikin fushi? kallon tufafin jikin Amrah take da basu da maraba da tsiraici tace"kin cuce shi wlh wad'anan wane irin kayane kike sawa haka bayan kinsan ba kya iya bashi haqqinsa! Wlh Afrah yau kad'ai na ta6a sa irinsu kuma shi ya matsa min ni kuma ina gudun 6acin ransa shiyasa na saka,but in kin lura a takure nake...qarya kike ba kya gudun 6acin ransa tunda har ya iya neman haqqinsa kika hana shi! Pls Afrah wai waya gaya miki ,nasan dai uncle fu'ad baya iya gaya kowa, kin manta kenan jiya muna cikin waya ya shigo d'akin ki ,baki kashe wyr ba kika ajiye shiyasa naji duk wata magiya da yake miki cikin lalama yana roqonki kan ki bashi haqqinsa kika qi,abinda ma ya qara qona min rai wai ace tunda aka yi aure baki ta6a bashi haqqinsa ba,wnn wane irin abu ne da cin zali,kinyi islamiya kmr bakiyi ba! kinzo d'aya da wacce tayi zaman banza a gida,kina kuma sane da tsinuwar mala'iku dake hawa kanki!kuma kinga tafiyata idan kinga dama ki gyara idan kuma kinqi ke kika sani....da sauri Amrah ta riqo hannunta tace"Pls Afrah ki tsaya kiji wlh tsoro nake ji sbd ban san yanda zanji abin ba,da qarfi Afrah ta fizge hannunta tace"sae kiyi ta jin tsoron tunda shi zai fishsheki. Nan tasa kai ta bar musu gidan.
Da Afrah ta koma gida gabad'aya Farhan ya kasa gane kanta sae tambayar ta yake me aka mata amma taqi ce mai komai yajata suka je gurin gwaggo nan ma bata ce dasu komai ba , da ma suka matsa mata tace bata jin dad'i ne.
Washe gari guraren qarfe 11 na safe Afrah na qoqarin rufe windown living room d'in farhan ta hango motar fu'ad ta kunno kai cikin gidan kallon sa take har ya parker mota ya zagaya ya fito da Amrah da yake lalla6awa kamar qwai. Ya jawota suna tafiya a hankali kmr masu tausayin qasa amma ba don komai suke tafiyar ba sae don Amrah wacce kallo d'aya za'ayi mata a fmhci cikin juriya take taka qafafunta yayinda fu'ad ke kallonta cikin tausayi da nuna so da kulawa.
Ganin ta daina ganin su yasa ta rufe window ta koma d'akinta ba jimawa taji knocking ta bada izinin shigowa ba tare da taje ta bud'e qofar ba. Amrah ta turo qofar a hankali ta shigo. Cikin rashin sakin fuska Afrah ke kallon Amrah tace"me ya sami qafar ki da ba kya iya tafiya sosai? Sae da Amrah ta kauda idonta da kallon da Afrah ke mata snn tace"haqqinsa na bashi shine hakan ta faru dani"
*Billy giro😊&Futha luv💅🏻* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 [10:23PM, 11/30/2016] Billy Geeero: [11/24/2016] 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅 *```AFRAH KO AMRAH ```* 🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅🏅
*```Na Billy giro 😊&Bilqis Sidibe💅🏻```*
*Futuhatulkhair.WordPress.com*
*```🏅90🏅```* Kuma shine kuka zo abin ki snr dashi sae kinji sauqi tukun, nice nace mai sae munzo sbd banajin zan iya qara kwana d'aya banzo mun sasanta nida ke ba tunda ko na kiraki a waya ba kya d'agawa. Amma amrah da gani kina jin jiki fa ,ai uncle yamin allura ya kuma bani magani nasha,, kin shiga ruwan zafi? Eh ya sani a ruwan zafi. Taja hannunta tace"to muje ki d'an kwanta ki huta ko" Ba musu Amrah taje ta kwanta sbd tana buqace da hutun. Afrah ta fito ta nufi d'akin Farhan ta same shi ya gama walha yana karatun qur'ani taje kusa dashi ta zauna, har sae da yakai aya ya juyo gareta yace"ya akayi ne Afrah ?murmushi tayi had'e da rungumo shi a hankali tace"uncle karatun ka da dad'i kmr kar ka daina, na ma d'auka fa kayi bacci naga na jima da barinka kana sallah, Yace"Afrah ai kinfi ni zaqin murya gun karatu dole ne fa in kinayi sae mutum ya tsaya ya bada natsuwar sa, hm uncle kenan nagode da zolaya... Au kenan nima zolaya ta kikeyi? Ah ah wlh kaima kasan da gaske nake, ni kuma kinsan da qarya nake, da sauri ta rufe mai baki tace"yi haquri ba haka bane wlh,murmushi yayi yace"to me ya kawo ki kika katse min karatuna?baqi mukayi uncle fu'ad da Amrah, shine nazo nagaya ma nsn uncle fu'ad na downstairs yana jiran fitowar ka, hannunta yaja suka tashi suka fito.
Banyan sun gama gaisawa da fu'ad yake cewa da Afrah taje ta kira Amrah su je su gaida gwaggo. Afrah taje ta dawo take snr dashi Amrah tayi bacci, Farhan Yace"ashe kun jima da shigowa kenan, cikin jin kunya fu'ad ya d'an sosa byn kanshi yace"bata samu baccin kirki bane bari naje na dubata,nan ya haura sama, Afrah ta wani riqo Farhan ta qanqameshi tana murmushi mai cike da nuna jin dad'i ,Farhan yace"ke lfyr ki wannan jin dad'in fa"uhm uncle ba komai. Fu'ad yana shiga d'akin ya zauna kusa da ita yakai hannu ya shafo gefen fuskarta a hankali ya furta"dear" Amrah ta bud'e idonta a hnkli ta sauke su akan nashi sae kuma tayi saurin kauda idonta tana qoqarin tashi, da taimakonsa ta tashi zaune ya d'an jawota jikinsa ,ya matsa fuskar shi gab da gefen fuskar ta har suna shafar juna yace"zamu je mu gaida gwaggo ne zaki iya?gyad'a masa kai tayi ,yace"to tashi kiyi tafiya nagani"kawai dai muje zan iya"to tashi muje ,cikin juriya ta tashi ta fara takawa sannu a hankali yana janye da ita a jikinsa har suka fito gurin staircase tayi saurin janye jikinta daga nashi sbd hango Farhan da tayi,taci gaba da takawa kmr ba wani abu har suka sauko ta gaisa da Farhan snn suka d'unguma su duka zuwa 6angaren gwaggo.