Kenza eBookz

ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 16

ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 16

ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 16: ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 16. "Yawanci ana yin wannan gwajin ne kwanaki kadan bayan mace ta gama al'ada (tsakanin rana ta 7…

4,413 words

"Yawanci ana yin wannan gwajin ne kwanaki kadan bayan mace ta gama al'ada (tsakanin rana ta 7 zuwa ta 10 bayan fara jinin al'ada), amma kafin lokacin da take yin kwan haihuwa (ovulation). Wannan don a tabbatar ba ta da juna biyu a lokacin gwajin." Shin yana da zafi? Mafi yawan mata suna jin dan ciwo kamar na ciwon mara (cramps) lokacin da ake tura ruwan maganin, amma ciwon baya dadewa." Rike hannun mijina nayi tare da cewa. "A'a na hakura wallahi na hakura ba zan iya wannan azabar ba." Gyada kai yayi yana faɗin. " Bata so ina ga a hakura da shi." " Tow shi kenan amma ku yi nazari dai!" Haka muka fito daga dakin muka bar asibitin. A hanya ya ce min. "Sorry na saka ki kuka!" Murmushi nayi na daura kaina a kafad'arshi. Haaka muka isa masaukinmu, bai kara min magana ba har ya fita abinsa. Kwanakin da muka na tsawon sati guda, ranar ya fita ina ga akwai wani abu me muhimmanci da ya fitar da shi ina kallo da laptop dinsa, na ga wani sako kamar ba zan bude ba, na buɗe. *Fisabiilillahi sai ka biye mata ta fasa ganin likitan? Idan ita bata son haihuwa kai zaka zauna ne naka biye mata tunda bata bukatar haihuwar shi kenan amma ka sani na gaji da dakatar da Daddah akan ita tana son ganin Yaranka* ...... Mujitafa Kumo Wani irin abu na ji ya tsaya min a rai, dama haka suka damu da rashin haihuwata, binciken laptop din nayi naga yadda Uncle Auta yake tambayarshi yana bashi amsar a sanyayye, hawaye ne ya zubo min. Da yawan kuɗin da ya kashe. Don na ga likitan, dafe kaina nayi cikin wani irin nadama, wani irin mutum ne da yake bin muradina? Duk abinda nake so kawai zai ko da blind eye, kuka ne ya kwace min domin na rasa wani irin so yake min da yake biye min haka, hada takardun nayi na wuce asibitin nayi sa'a kuwa likitan yana nan, ina ganinsa na fashe da kuka.. "Doctor bayan HSG babu wani hanya ne? Ka taimaka min mijina yana sona, yana kome domin ni, amma bana son ta fuskanci damuwa saboda ni. nasan yana jin ba dadi ina son na ga nashi babyn ne a tare da ni." Murmushi yayi ya ce min. "Dole sai mun san yanayin ciwon da maganin hana daukar ciki ya haifar miki, shi yasa nace ayi gwajin HSG," "Na amince!" Na fada bakina yana rawa, "Yaushe ne zaki fara Al'adarki?" "Nan da kwanaki uku!" Na bashi amsa. "Kuma kina Evolution?" Shiru nayi kafin nace wani lokaci ina yi wani lokaci bana yi!" Na fada ina kallon kasa. " Shi kenan, zan baki magani ya taimaka miki da evolution din sannan idan kin yi sai ki kawo mu san yadda za ayi." Murmushi nayi na ce mishi. "Sai me kuma?" "Ba wani abu ai Mijinki ya biya kome tun farko don har ana maganar za a tuntube shi don mai da mishi kuɗinsa." "Na dawo ayi aikin." Gyada kai yayi sannan ya bani takardar magani da wata takarda alamar daga wurinsa ne, ina zuwa aka bani. Koda na koma masaukinmu, na same shi ya zubawa kofar idanu. A hankali na nufe shi bude min hannu yayi ka shiga cikin hannun na durkusa a gabanshi, tare da daura kaina a kirjin shi. " Waye yake bada haihuwa?" Ya tambaye ni." Allah! " Na bashi amsa, "ina fatan idan aka yi aikin ba zaki yi fushi ba idan har aka samu fail?" Nodding kaina nayi alamar eh, shafa kaina yayi yana faɗin." Good gurl;" share min hawaye yayi s hankali ya shiga shafa bayana, har barci ya dauke ni, a daren na sha maganin har tsawon kwanaki uku. Kafin na fara period, wani nayi kwanaki biyar kafin ya dauke sannan muka shirya ranar Monday muka je ganin likitan anan ma aka kara bani wani maganin na kwana kwanaki biyar.

Kamar da wasa na sha na kwanaki biyar sannan muka koma a kwanakin na fara evolution, haka aka yi min aikin da na sha matuƙar azaba, koda aka fito da ni kamar bani da lafiya, haka ya tsaya a gefena har tsawon wuni guda. Lokacin da na farka na ganshi zaune ya kura min idanu. Sai ya bani tausayi na mika mishi hannu ya d'aga ni. Kuka na saka mishi. "Am sorry My Man, am really sorry!" Na fada ina kara rungume shi, shima rungume ni yayi yana shafa bayana, tare da sumbatar kaina ya ce min. "In sha Allah ko baki haihu ba, zan zauna da ke a haka ba kuskure ba ne, sai mu yi adopted din Yara biyu mace da namiji ko?"

Na sha kukana ni daya amma shima ya sha aikin rarrashi, kafin ya taimaka min nayi alwala da sallah, kafin ya kawo min abinci. "Ya aka yi nayi barci?" Kallona yayi kafin ya ce min. "Kina ta kukan maranki yana ciwo tunda aka yi aikin shi ne ya miki alluran barci." "Sorry!" Na ce mishi. Lakace min hanci yayi, na sake murmushi. Ya hade goshinmu wuri guda, "ina sonki!" Hannuna na kai bayanshi na lumshe idanuna. "Me too!" Bayan na nutsu ya kira Abba muka yi waya da su. Sannan ya kira Ubaid suka yi magana. Wunin ranar ina makale da shi, har washi gari sannan aka sallame mu. Sakamakon ya fito magani aka hada min, wanda ba san yadda zan yi da su ba, sati daya muka kara na warware sannan muka dawo Nigeria.

Cikin so da kaunar juna, wani irin yanayi nake ji na tausayinsa domin kuwa kwana biyu nan a gajiye yake dawowa daga nan zai fita, ni na zata ko don akan maganar rashin haihuwar ce, ashe wata kullaliya aka kulla min. Wanda ya tsaya kai da fata yake faɗa a kai. Watan azumi ne a gabanmu don haka kowani musulmi shirin azumin yake.

Ana saura sati azumi aka kawo sabbin kaya, aka kwashe tsofaffin aka fitar dasu. Matar Uncle Auta ce ta shigo muka gaisa ta min fatan alkhairi. Har zata fita ta ce min. "Lubnah kin san me ke faruwa kuwa?" Girgiza kai nayi ina kallonta. Shiru tayi kafin ta ce min. "Mijinki za ayi wa auren dole fa da kanwar Matar Ubaid. Wannan ba gyaran tarban azumi ba ne Alhaji ELYakub ya ce a kawo miki kayan fadar kishiya a fara da wannan." Murmushi nayi na ce mata. "Wallahi ban sani ba, Allah ya bada sa'a yasa a dace." "Amin Ya Allah! Don Allah kada ki d'aga hankalinki anyi haka ne don a bata miki amma kada ki damu;" murmushi nayi nace mata. "Wai ai na jima da sanin haka zai faru amma ban kawo ta bangarenta ba ne hankalinta ya kwanta Falilah kenan ina ga da Mijinta nake aure sai ta kashe ni, abokin Mijinta nake aure take kishi da ni wai 'Allah ya kyauta." "Amin Ya Allah!" Daga haka ban kara ba, ai kuwa ban san me aka yi ba itama Matar Uncle Auta ta juya maganar ne sai maganar sai ga case ina zaune sai ga Mahaifiyar Badriyyah tazo inda take shiga ba nan take fita ba, abin har da gorin haihuwa. Sai ranar na fahimci girman illar da Hafiz yayi min domin kamar xan mutu, haka suka tafi har da matar Ubaid din, bayan tafiyarsu Matar Uncle Auta ta shigo, yadda suka bar ni kaina yana ƙasa, haka ta gama surutunta ban d'ago kai na ce ci kanki ba,. Ta fita itama jikinta a mace. Har ya dawo ban nuna mishi abinda ya faru ba, domin shima bai da nutsuwa. Shafa kanshi nayi ina murmushi na ce mishi." Me yasa kake damuwa ne baka cin abinci sosai fa!" Jan kimatuna yayi muka saka dariya, yadda muke rayuwarmu haka muka yi kome sannan muka kwanta. Rike hannunsa nayi na ce mishi. "Me yasa ba zaka amshi tayinsu ba? Yanzu ana niman shekara daya kenan da aurenmu, ban ga laifin Daddah ba." "Wasu sun zo nan ne?" Buga kofar parlourn da ake yi ne. Na kalle shi. "Hamma Turaki?" Na ji muryan Falilah a tare muka fito da shi ina sanye da Hijab har kasa, yana budewa ta shigo ita da yarinyar da akace zai aura ta fashe da kuka. "Hamma Turaki, meye laifina don akan aurenka da Zakiya? Ashe Baban Nihla ya je yana niman auren kanwar Maman Husnah Yarinyar nan walidah kawar Zakiyah. Fisabiilillahi." "Kin san bakya son zama da kishi kika tafi har gaban Daddah kika hada min munafunci, ai ni na bada sadakin karma is bitch shine zai kashe ki, aure babu fashi." "Baby ka bani kudin hada kayan leffe please bana son wannan damar ya wuce ni, zan hada muku kai da ita in sha Allah." "Idan har rashin haihuwa ne kema me yasa baki kara wani haihuwar ba, Yan mata zan ki kudin kayan lefe!" Wani irin mutuwa jikinta tayi ta ja kafa ta fita, kallonshi nayi cike da Mamaki. "Dama aure Ubaidullah zai yi?" "Eh kai ya jima yana son yayi aure shegiya tana hanawa na rasa gane me kika tsare mata take jin haushinki, yanxu zata ga rashin mutumci ganin idanunta ba ita yar iska ba!" Rike baki nayi ashe haka yake da rashin mutunci.

Ai kuwa ba washi gari Ubaid yazo yayi ta bani hakuri Allah sarki sai ya bani tausayi. Idan baka samu mace ta gari ba rayuwarka tana cikin garari, wani ikon Allah ni da taso ganin nayi hauka. Da na gayawa Dangina addu'a aka yi ta min Allah sarki saii ga Yadiko tazo ta kawo min maganin wanke mahaifa, da sauransu. Satinta biyu ta koma, a lokacin har na gama hada lefen Ubaid ai yadda ta min kan kara haka zan mata na itacce. Kuma na shiga gaba aka kai kayan auren, muna dawowa tayi ta hauka da ihu zata dake ni. A raina na ce ko zaki mutu aure sai anyi shi...... [12/26/2025, 4:22 PM] Maman Walid: 30

Ihu da haukar da take yi, har cikin parlourn ina jinta, hankalina yana kan abinda nake haɗawa don na sha, "wallahi idan ina raye sai ga bayanki!" Ihu da hauka iri-iri tayi shi gashi an hanata shigowa gidan, a ranar dakyar ta koma gidanta, ina jin yadda yake ihu da tashin hankali.

Da yake mijina ya tafi wani meeting Abuja sai dare zai dawo haka na hada magani gyaran jiki, wurin karfe shida ya shigo a gajiye, karban jakan nayi kallonshi. Yayi laushi na tab'a goshinsa ina faɗin. "Anya yau lafiyarka lau kuwa?" Murmushi yayi ya wuce kitchen yana faɗin. "I need water!" Na biyo bayanshi na bashi ya sha, sannan ya sauke ajiyar zuciya can kuwa ya fara wani irin tari. "Me yake damunka?" Na rike hannunsa muka wuce cikin dakina, ina shafa bayansa.. sai da na taya shi wanka duk yayi laushi. "Me ke damunka!" Masallaci ya tafi bayan ya dawo ya kwanta sai dai dama mishi kunu nayi ya sha, ina rike da hannunsa. "Meke damunka?" "Bana jin dadi ne almost 3-days kenan." Sake tab'a wayarshi nayi na ji zafi rau. "Baby you're burning! Muje asibiti." Girgiza min kai yayi yana mai rike hannuna ya ce min. "Please sir na da sweater!" Haka na wuce dakin na kawo mishi, ya saka nace mishi. "Me kake so!" Girgixa min kai yayi yana faɗin. "Bana jin yunwa." "Fisabiilillahi haka zaka zauna da ciwo?" "Hmm!" Ya ce min na rasa me yake min dad'i, duk ya rasa kuzarinsa, haka yayi ta zazzaɓi a kwanakin ya daina zuwa office sai da yayi sati s gida, wanda ya janyo aka kai shi asibitin da baya so. Ruwa suka yi ta saka mishi, wani abin mamaki sai jikinshi ya rikice sosai. Wanda ya saka ni cikin wani irin tashin hankali.

Wanda ya kai aka tura shi ICU, dole Mama ta zo. A cikin kwanakin nayi wani irin rama domin bana cin abinci bana kwakwaran barci. Tunda Mama ta zo take nazarin yadda yanayin mu alamata da danginsa idan ya wuce Daddah da Alhaji ELYakub sai Uncle Auta da Ubaid. Kallona tayi ta ce min. "Kina cikin abinci kuwa?" Murmushi nayi na ce mata. "Ina ci!" Riko hannuna tayi ta ce min. "Kamar kina da ciki ko?" Da sauri na kalleta babu kowa a wurin, na ce mata. "Ciki Mama?" Gyada min kai tayi, nayi kasa da kaina. Tun last week ya dace period din ya dawo amma har yanzu shiru, sai ciwon gefen ciki da yawan kasala. Na zata ko don rashin lafiyarshi ce. Rufe bakina nayi da hannuna daya na kalleta. "Innalillahi wainnalihir rajoun! Mama!" Hannu ta saka min a bakina. "Mijinki ma kamar hannu aka saka mishi, bani da tabbas amma ki shirya mu koma gida!" "Mama!" "Ba zan barki anan ba, domin shima a nan din farautar rayuwarshi ake idan har shi ba a kyale shi ba, kema ai baki tsira ba. Waye kika yarda da shi a cikin danginsa!" "Tarik!" Na furta kai hatta Uncle Auta da Ubaid ban yarda da su ba,. Kiran Tarik nayi a waya.. "My boy ina son ganinka don Allah!" "Ina nan tafe gobe in sha Allah!" "Muje gidan Adamu!" Bata gayawa kowa dalilin tafiyarmu ba, haka muka isa gida, dai naji kamar nayi kuka, idan na tuna yadda na barshi. Kusan kwana nayi da zazzaɓi, washi gari Tarik ya iso ban san me Mama tayi ba amma da safe ruwan zam-zam ta mika min muka fita, Tarik ya zo ya dauke ni. Lokacin da muka isa Asibitin Uncle Auta da Ubaid muka samu sai Kakanshi.." Jiya ina kika tafi?" "Naga kamar tana bukatar hutu shine na tafi da ita ku yi hakuri."

" Ba kome Hajiya, dama mun damu ne." Inji Kakanshi. Wucewa nayi dakin da jakar zam-zam, na shiga na same shi a yadda na barshi. Ruwan addu'ar nayi Bismillah na shiga shafa mishi, shigowa Uncle Auta yayi ya ga ina shafa mishi ya zo ya taya ni. Har muka gama ya ce min. "Addu'a ko?" Gyada kai nayi, murmushi yayi ya ce min. "Mun yi da Baffa zaki koma gida zamu tafi da shi Russia!" "Zan bi ku!" Girgiza kai yayi na ce mishi. "Ni nafi dacewa na zauna a gefenshi." Na fada ina mai fashewa da kuka, fita yayi ya bar ni a dakin, dA sauri na juya gare shi, na riko hannunshi na kai kan cikina. " Please wake up ka ji feel your baby a marana, please ka tashi we need you." Na fada ina kuka. Na rasa yadda zan yi haka na fito na same kakanshi na ce mishi." Don Allah ka bar ni nan tafi da shi, don Allah ku bar ni, na biku. Mama ki ce su bar ni kin ji Mama ki roka min shi don Allah." Kallon su Mama tayi a nutse, ta ce musu. "Ku barta ta bi Mijinta!" A yadda suka tsara babu ni, amma da yake Allah ya mata baiwar iya sarrafa kanta sai gashi sun amince. "Shi kenan ta shirya!" Haka Tarik da Mama suka kawo ni gida na shirya tsaf, sannan na hada kayana na kashe kome na gidan abincin da yake frij na kai cikin gidan Uncle Auta, sannan na rufe gidan, muka wuce asibitin. A daren muka wuce Russia, lokacin da muka isa can Russia har da Uncle Auta. Yadda aka Karbe mu yafi kome dad'i, nima damuwa da rashin hutu yasa ina sauka a jirgin na yanki jiki na suma. Haka aka wuce da mu asibitin.

Sai da nayi kwana biyu ina barci na farka, koda na farka Aunty Herlim na gani a gefena. "Lunah sannu kin farka?" Gyada kai nayi ina murmushin karfin hali. "Ya Jikin shi?" Na tambaye ta ina kallon dakin, murmushi tayi ta ce min. "Yana dakinsa." Gyada kai nayi na rufe idanuna. "Kwanaki biyu kina barci!" Kallonta nayi na ce mata. "Kwana biyu?" Gyad'a kai tayi tana murmushi. "Amma babu inda yake ciwo na kira likita?" Gyada mata kai nayi, danna abu tayi sai ga nurse sun zo, tare da likita a bayansu, bayan an gama duba ni suka min tambayoyi, na basu amsa. "Ki huta zaa yi miki scan nan da dare!" Bayan sun fita na shiga wanka, na fito nayi sallah. Sannan na wuce dakinsa. Lokacin da na shiga naga sun daura mishi karfuna, zama nayi na dafe kaina. Ina kallon yadda ya koma lokaci guda, wani irin kuka nake ina kiran sunan Allah, tunawa nayi da kayan da nazo da shi, na kalli Aunty na ce mata. "Ina goran ruwan da yake jakata." "Yana gida zan saka a kawo miki!" "Ina so yanzu nan!" Haka ta bar Asibitin, bayan minti ashirin sai gata, dauka nayi na shafa miishi a jikinsa da ko ina. Da dare na je aka yi min scan sannan anan aka gano cikin sati biyar da kwanaki shida, hawaye ne ya zubo min, na koma dakin ina kallonshi yana barci. A bisa ka'ida ba za a zauna da shi ba, amma saboda yadda suka ga koma suka bar ni, sallah biyar sai na saka shi a cikin addu'a. Idan dare yayi kuwa sai gari ya fara haske nake komawa gefensa na kwanta ina kuka har nayi barci.

Ban sare ba, ban tab'a give up ba. Addu'a na saka Allah a gaba. Ruwan zam-zam din na karewa na gayawa Auntynsa suka nimo min har da ganye magariya, anan ne na ga ikon Allah, na kuma. Yarda akwai sihiri a tare da shi, tunda ya kwanta baya motsi numfashi ma da taimakon inji yake yi, amma ina fara ayatul shifa, ya fara motsi. Tunda na fara sai nima na fara jin wani irin abu yana yawo a kaina, idan na kwanta barci zan ga kamar aka bina da gudu. Sau biyu na ga haka, sai na kira Mama ina kuka na gaya mata. "Bar kuka haka, ki tuna akwai wanda yake bukatar kulawarki bayan Turaki, ki tuna da abin cikin ki ko ba don kanki ba, in sha Allah zan taya ki daga nan." "In sha Allah Mama!" Na fada ina kuka, tayi min nasiha sosai sannan ta kara min addu'a sosai.

Haka na kara kai mi, amma kuma idan na tuna akwai Allah sai na ji bana tsoro. Haka na cigaba da na shi, Turaki bai da Uwa bai da Uba, nice abu biyu zuwa uku. Jasminah tana Kano, bata san me yake faruwa ba. Nan kuwa dangin Uwarsa ba musulmai ba ne. Haka na tsaya ba dare ba rana, ina addu'a. Aunty Hindatu ta kira ni ta min jajje take gaya min anyi saukar Alqur'ani da yanka, Abba yasa an tara almajirai, sai na fashe da kuka. Sannan an raba namar sadaka gida gida, abinci kuwa har kofar fada aka kai aka rabawa almajirai. Sannan anan ware tsangaya uku akai abinci da ruwan sanyi aka raba. Nayi kuka kamar raina zai fita, sati daya aka dauka aka addu'a, sati na zagayowa ya fara farkawa, wani bin idan ta bude idanunsa har da tashi da karfi kamar zai tashi sama, sai anyi mishi allurai yake komawa barci, na kira Mama na gaya mata, ta ce min. "In sha Allah za a ci nasara!" Likitoci kuwa cewa suke miracles ne yasa ya dawo rayuwa domin sun fara tunanin a cire mishi abin numfashin ya tafi ya huta.

Alhamdulillahi ko kafin satin ya farka ya zauna da daram, ranar da na ga haka kuka na saka tare da rungume shi. Shafa bayana yake yana murmushin farin ciki. Ban kyale shi ya wartsake ba na daura hannunsa akan cikina. Na gyada mishi kai. "Alhamdulillahi!" Ya furta a hankali, hawaye na zuba a idanunsa yau na ga yana zubar da hawaye ya ce. "Zan zama Baba daga gare ki? Thank you for choosing me to be a Daada." Rungume shi nayi ina cewa. "Thank you for made me a mother!" Hade goshinmu yayi yana faɗin. "Thank you Lunah, thank you for saving me, thank you for protecting me. Na ganki a mafarkina, kin kare ni kin hana kowa ya cutar da ni, thank you for be in my side. Lunah!" Rufe mishi baki nayi ina faɗin. "Ya isa ka huta kayi sallah." "Jikina yana ciwo!" "Bari idan muka koma gida ayi maka hayakin habbatu saudat." Murmushi yayi yana shafa cikina. Haka na taimaka mishi yayi wanka da alwala, ya zo ta gabatar da sallah. Bayan ya idar ya ci abinci, sannan na bashi addu'ar da nake shafa mishi. Ya sha na kara shafa miishi, yans murmushi ya kwanta. Kwanaki hudu yayi aka sallame shi, muna zuwa gida na hada mishi ruwan addu'a yayi wanka sosai. Bayan ya fito na mishi hayaki da Habbatu saudat, ba sai gashi yana gurnani ba. Can ya tashi ya fara wani irin abu. Yana niman kamani amma yayi baya, na cigaba da zuba garin habbatu saudat, duk da na razana amma kuma aka na fahimci kamar abin da yake tare da shi yafi ni razana, tari yayi ta yi har ya zube a kasa. "Ki godewa Allah kina da shi a gefenki, Allah yana gefenki, ba wurinsa aka turo mu ba wurinki ne, wurinki aka turo mu amma muka kasa gane hanyar inda kike shine muka shiga jikinshi, shima abinda yasa muka shiga bai yi azkar din yammaci ba ne, ke kuma kina cikin addu'a koda ba kya ibada. Ni dai ki bar ni na tafi domin an daure ni ne da addu'ar da Iyayenki suke miki!" Kallon wulakanci nayi mishi na ce mishi. "Sai dai ku tabbata a haka kamar yadda ka bawa mijina wahala haka zaka kare ba zan kyale ka ba!" Ihu da kururuwa yayi ta yi har Auntynshi tazo, na cigaba da addu'a zata yi magana na ce ta je kawai. Haka na cigaba da addu'a da ruki'a, sai da na wahalar da shi har yana cewa zai mutu na kyale shi, ya fita ta atishawa. Yana samun damar barci na mishi alwala na gyara mishi kwanciya. Na kira Mama na gaya mata, ta ce min." Akwai abubuwan da aka hada muku dukkanku har da cikin jikinki ya za ayi?" " Kada ki damu zan turo Tarik."

(Kuyi hakuri na gaya muku gaskiya bani da lafiya wallahi gudun kada na tafi break ku ce ban kyauta muku ba yasa zan muku koda daya ne, ku yi hakuri kun san yadda nake typing amma wannan karon bana jin dadi sosai?! Arewa gobe xan kara muku update telegram maybe sai Sunday in sha Allah) [12/29/2025, 7:53 PM] Maman Walid: 31 Na fada mata tare da rike hannunsa, kwantar min da hankali Mama take tana gaya min magana me dad'i, hawaye ne ya zubo min, na ce mata "in sha Allah ina tare da shi, ba zan tab'a ja da baya ba." "Allah ya miki albarka, ya sauke ki lafiya. Ki kula da addu'a da azkar!" Daga haka muka yi sallama, na tsaya sosai da addu'a bs dare ba rana, a bangarenshi kuwa sauki ake samu, sati daya da muka yi magana da Mama sai ga Tarik, kusan nafi kowa murna, haka muka yi ta amfani da magani na fara mishi amfani da su, Alhamdulillahi sai gashi lafiya ta samu har an koma duty, bakiɗaya ya koma irin iyaye mazan nan masu matukar damuwa da Yaransu. Tun da yaji na shiga wata na uku ya tattara kaunar duniya ya daurawa cikin, da yake gani kamar bai da wani sama da shi. Tun daga nan na fahimci irinshi, da cikin ya shiga wata hudu nan na kara yarda da cewa zuwa yanzu Allah ya min arziki da ya bani shi a matsayin mijina, domin fita goma shiga goma, zai daura kanshi akan cikin yayi ta bashi labari, surutu kala kala. Ni kuwa motsi kaɗan zai tambaye ni me nake so.

Har ga Allah na gaji da zaman garin, don haka cikin da ya fara tasawa na shiga wani irin yanayi na son gida musamman abincin gida, tuwo, fate, dambu da kwadon zogale, ranar da na tashi da son taliyar murji ban samu ba da mai da yaji, karshe indomie na dafa na jikata tayi manya manya naci da mai da yaji, da dare kuwa ina kwance naji ina sha'awar awara da mai da yaji, kuka ne ya zo min ganin yada nake shiga damuwa Kakarshi da Auntysa suka saka shi gaba ya shirya mana dawowa gida, shi a lissafinshi kada mu dawo gida a kara cutar da abin cikin tunda sun ga ba nasara akanmu, murmushi nayi kawai nace ni dai gida.

Haka muka gayawa Mama zamu dawo na gaya mata ranar da zamu dawo. A bakinsa nake jin ta turo aunty Hindatu da Aunty Innah da Zakiyah aka gyara min gidan suna gari ma su zasu karbe mu, bai yarda ya gayawa kowa zamu dawo ba, sai dai ganinmu aka yi ranar wata Alhamis da safe muka iso. Uncle Auta da Ubaid sai da suka mishi tsiya, wani ikon Allah ko Yayuna Mama bata gaya musu ina da ciki ba, tace dan duma ne ba aboye shi. Nayi kiba daga sama da kasa, suka yi ta min tsiya ko ciki ne nace su taya mu da addu'a. Duk wani abinda muke bikatA an kawo a gidan babu abinda na rasa sai dare suka bar gidan,karfe tara ya shigo shi ɗaya. Ina daki na ji shigowarshi. Fitowa nayi na same shi yana zaune yana shan ruwan zam-zam. Murmushi nayi na bi kitchen na dauko dabino da ya'yan zaitun ka kwalba, Mama tayi recommended din akan ina ci, bude min jikinshi yayi na shiga cikin na zauna tare da kwantar da kaina a kirjinsa. "Baby ya My love yake?" "Idan na haifi Baby sai a koma Madam ko?" "Waye ya gaya miki haka?" "Kai mana!" "Kada ki min sharri!" Ni dai ban ce kome ba, na cigaba da cin zaitun din har na gama, muka shiga hira. Da yake bamu ta kowa ta kanmu muke ihun Falilah matar Ubaid muka ji tana faɗin matukar tana numfashi ni da Mijina da muka saka Mijinta aure zamu gani. "Ta gani akanta!" Ta kara da cewa. "Idan na haifu yar halak Lubnah ke da haihuwa sai dai wasu su gani!" Murmushi yayi bayan na kalle shi. "Allah ya bamu sai dai taji haihuwa!" Haka muka tattara ta muka zuba a gefe, sannan ya min kashedi na fita harkan Matar Uncle Auta itama munafika ce, kawai sai naji na samu nutsuwa hankalina kwance ba ruwana da kowa. Babu wanda ya san ina da ciki ma, satinmu uku da dawowa aka yi bikin Badriyyah ta auri wani senator a abuja, yadda bai je ba nima ban je ba, gidanmu baya rabuwa da karatun Alqur'ani, haka yasa muke kara samun kariya daga Ubangiji.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull