ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 15
ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 15: ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 15. Sannan ya juya ga Baban Jama'are ya ce mishi. " Na zata kasan yakana ne, amma na fahimci baka…
4,307 words
Sannan ya juya ga Baban Jama'are ya ce mishi. " Na zata kasan yakana ne, amma na fahimci baka fahimci haka na, idan na kara jin labarin Hafiz a bakin Lubnah ko mijinta da sunan ya shiga rayuwar aurenta, na rantse da Allah zan yi abinda zai baka tsoro. " Murmushi yayi kafin ya kalli dan uwansa ya ce mishi." Da gaske nake ba da wasa ba, rayuwarta da aurenta yafi min kome muhimmanci ban damu ba ace don tana auren mai kudi ne ba kome, na ji kuma na amince" yayi fadar ni kaina sai naji kamar an yantani daga wani kunci zuwa jin dadi, ya juya ga Turaki ya ce mishi. "Idan ba zaka iya zama da ita a haka, ka sake ta yanzu nan!" Ya ajiye mishi takarda da biro, ba Turaki ba hatta ni sai da gabana ya fadi, muka kalli Abba da yake wani muzurai. Alamar no mercy a cikin lamarinsa, kallon Turaki nayi da yake Allah bai mishi burbushin kunya ba, janyo ni yayi ya ce mishi."Wai Alhaji i love my wife, zan iya kome domin tayi farin ciki. Daga yau ka kuma ganin Lubnah a gidanka matuƙar ba dalili bane babba kayi karana kotu domin a nima mata hakkinta, Alhaji a dokar ƙasashen duniya idan tayi ƙarana duk abinda na mallaka sai an raba biyu, a nan kuma ka bani takarda da biyo, wai ina son Matata wallahi idan zan fada maka ita mace ta biyu mai daraja a rayuwata, ni ba gara ka fille min kai zai min sauki da na sake wannan abin!" Ya shiga rattaba bayani, zamewa nayi na barshi ya yi ta rashin kunyarshi, na rantse bai da kunya har cewa yake. "Ni fa naga ƙoƙarin Lubna da ta xauna da mai furfura irina, waye ya sani ko hakuri take da ni, amma Alhaji ina kula da kaina! Ina cin abinci me kyau ina. " Da gudu na shiga parlourn na riko kunnenshi, ya kuwa taso. " Ya zaa yi, ai haka zan bi Umarninki! " Muna fita waje na ce mishi." Wai kai baka da kunya ne?" " Da nayi me?" Ai ban yarda mun kara shiga cikin gidan ba, na ja shi muka bar gidan. Wannan tarin rashin kunya nashi. Sai da muka dauki hanya na ce mishi." Ba kyau rashin kunya, ba kowani magana ake fada ba, wani ana shiru a gaban manya ko mutane, ba laifi bane confessing yadda kake ji, but abin kunya ne kayi ta magana ina kunyarka ya tafi?" Shiru yayi yana saurarena kamar wanda yake daukar maganar da nake amma can ya ce min." Hmmm meye amfanin na fadi abinda yake raina ku dai Hausawa akwai ku da daukar aiki ja!" Jan kumatunsa nayi, ya sake murmushi muka cigaba da hiran. Wani lokaci baka sanin yadda kuke son juna, sai wani abu ya gifta tsakani zaka fahimci ai dama ashe irin wannan rayuwar akwai shi, koda muka dawo gida wani magani da Yadiko ta bani tun da muka isa na shiga kitchen ina damawa da madara ya shigo, zagaye cikina yayi da hannunsa yana sinsinsar hijab dina. "Me ake dama mana ne?" Share shi nayi na cigaba da abinda nake ya sumbaci kaina yace min. "Nima zan sha? Idan ta mallaka ce sai mu mallake juna." Murmushi nayi na ce mishi." Yanzu ma ban mallake ka ba, ake ganin haka idan kuma na mallake ka sai an hada da rokon Allah." Shiru yayi bayan na gama dama gumbar na ajiye, fruit da nake da shi ja ciro na yanka na nika mishi, kankana ds kokumba na saka madara da zuma, na fito ina mai tura mishi mug din, ya kurba. "Meye sirrin?" Dauke kai nayi ina sha muna kallon laptop dinsa da yake aiki. "Yaushe zan koma aiki?" "Ai na amshi takardan barin aikin da kika yi can baya!" "Ban gane ba ba ka yaga ba?" "Eh amma na saka kin ajiye aiki domin kin zabi zaman aure akan aikinki." Kura mishi idanun nayi kai tsaye nace mishi.." yaushe muka yi haka Sir?" "Sai dai saniya! Amma aiki kawai ki zauna a gida ki bautawa Allah da aurenki. " Naji haushi amma sai na share naki bawa maganar muhimmancin da zai ce ina jin zafi ne, can ya ce min. "Baki ji haushi ba ne?" Tab'e baki nayi ka ce mishi.. "ko kaɗan ban ji haushi ba!" Na fada ina murmushi, kallona yayi kafin ya ce min. "A'a Lunah kada ki yarda ki boye kin ga ni fada miki kome nake gara ki gaya min kada na fita na ji bakya garin nan!" Dariya nayi na ce mishi. "Ka tafi makera!" Daga haka na cigaba da shan gumbar bayan na gama na mike na nufi daki nayi wanka tare da saka humra, na zauna ina mai kunna wayata yau, tunda na bar Lagos na ga sakon mutane. Nashi na gani kusan sakon ban hakuri ne da ya tuba, girgiza kai nayi ina kallon wayar, fisge wayar yayi yana sanye da kayan barci. "Wayyo Allah na, kin gama ganin furfura na!" Saka hannu nayi na tallafi fuskarshi ina jin kamar kada mu rabu a hankali na ce mishi. "Har kayi wanka mijin Lubnah!!" Jan hancina yayi yana mai daura kanshi a hannuna. " Gani nan, na zata zaki zo ki taya ni ne?" Girgiza kai nayi ina faɗin. " Ba ka gaya min zaka yi wanka ba ai da nazo!" Matsowa yayi yana kallon cikin idanuna, rungume abina nayi. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ina shafa bayanshi har barci ya dauke shi a hankali.
Da asuba kuwa kafin a kira sallah shiga ya tada rigima, sai da na biye mishi a lokacin aka zauna lafiya, bayan mun gama a tare muka yi wanka ya tafi masallaci, ni kuma na cigaba da azkar din safe. Karfe bakwai saura ya shigo muka kara kwanciya. Bamu tashi ba sai sha biyu rana abin karyawa nayi mana, sannan na shiga wanka ni da shi duk muka shiga cikin manya kaya, ni riga da zani shi kuma jampa da wando, muka karya sannan mika dawo parlourn mukai ta hira. Har karfe biyu muka yi sallah azhar na ja shi zuwa kitchen na mana abinci mai sauki sai gasa nama da yayi da kanshi, yana yi yana faɗin. "Yarinyar kika ci abincina sai kin ce ashe haka na iya girki!" "Hmm inji me tsoron wanka!" Haka muka gama parlourn, ana kiran la'asar ya tafi masallaci don nashi bai gama ba, ni kuma na tafi dakina bayan na idar na watsa ruwa na fito.
Satinmu hudu, na gaji da zaman Bauchi duk da kusan kullum shi yana gidanmu. Amma ni ya hana ni fita, sai ana jibi zamu cika sati hudun ya kai ni na wuni a bakin su Mama nake jin labarin ai ana gina mishi wani branch na kamfaninsa a Bauchi ne tinda bana son lagos, kawai sai naji abin bai min dad'i, koda muka dawo gida. Ni da kaina na haɗa kayan mu. Da ya shigo ya samu ina hada kayan shi, daukata yayi sama yana faɗin." Matar Turaki lafiya ina zamu zaki biya mana kuɗin jirgi zuwa honeymoon." Ture shi nayi na ce mishi." Lagos zan koma!" Rike baki yayi yana faɗin." Ikon Allah yau kuma?" Ina gama hada kayan na ce mishi. "Yaushe zaka saka mana tafiyar?" Janyo ni yayi tare da rungume ni yana faɗin "ki saka duk lokacin da yayi miki!" "Gobe!" "Yayi kusa fa domin ina son na!" Kallon cikin idanunsa nayi mutumin nan bai gajiya da aikin lada. "Ni dai!" "Dama kin cewa Mama na kara aure ko?" Ya fada yana kaiwa hancina hakori da sauri nayi baya ina dariya. "Ji min mugunta don ka ga nawa yafi naka!" Na fara ƙoƙarin kwace kaina ya rike ni da kyau, aikin ladan nan dai ina ga sai na fara gudunsa, amma zan iya kiranshi da manniru.
Haka ya d'aga mana tafiya har zuwa wata sati. Ranar Monday na satin muka bar Bauchi da kaya niki-niki, amma Gombe muka je kwanan mu biyu a gidanmu na can har muka hadu da Mamansu Sarah wai Airah ta zo, kallo daya nayi mata na watsar da ita yadda take wani rawan jiki a gaban Turaki ko ya kula itama Uwarta sai da ta gwatsaleta a gabana tana faɗin. "Amma hauka kike da kike ta wannan rawan jikin, ki tsaya a matsayinki kada ki ce zaki kai kanki inda Allah bai kai ki ba, idan da Turaki yana da niyyar tara mata da ita kanta Lubnah a mata biyu ko ta uku ta zo, so behave yourself." Sannan ta juyo gare ni tana faɗin. "Ki yi hakuri, zaki ga abubuwa dayawa akan Mijinki ban sani ba ko kin sani amma akwai mata irin Airah da suke harin Mijinki, ki fahimci mijinki me yake so me yake bukata, zaki iya fuskantar mutane ta kowani fuska amma Mijinki yana da muhimmanci domin mata dayawa suna niman irin damar da kike ciki amma sun rasa yana da kyau ki rike Mijinki da muhimmanci ki bashi muhimmanci sama da kome, koda gaba zaa yake ki. Ba za a iya rusa ki kai tsaye ba sai dai idan wata hanya, Mijinki yana sonki sama da kanshi, amma ki sani shi dan adam ajizi ne kuma zai iya miki ajizanci a kowani lokaci. Allah ya baku zaman lafiya da zuria dayyiba ku yi hakuri ban zo bikinku ba." Matar ta burge ni for first time haduwarmu, sai na rasa a ina Airah ya gado mugun hali, ranar da zamu tafi har da ita Airah taci uban kwalliya da gashin doki ga wani shegen riga da wando da ta saka tare da wata Shaidaniyar rigar abaya, dauke kai nayi kamar ban ganta ba, shima Gogana ya fahimci haka. Tunda na fahimci waye shi sai na ji a raina ko bana tare da shi nasan babu Macen da zata burge shi sai dai idan ta shiga cikin littafin ƙaddaransa.
VIP Nan muka wuce ita kuwa ta shiga regular, irinta kowa da kowa. Tunda muka bar Gombe a garin Abuja muka sauka ya kwashi wasu fasinjojin yayi gaba ni da Mijina muka yada zango a garin Abuja. Unguwar Maitama nan muka wuce Taj yazo ya dauke mu, ba laifi gidan yayi kyau. Tunda muka gaisa bai kara ce min kala ba, haka muka shiga cikin gidan. Abinda na fahimta kasuwanci ya zo yi a garin Abuja, sai da muka samu kwanaki biyar kafin muka bar garin zuwa Russia, bai gaya min ba sai da muka je Airport ya mika min passport dina, kallonshi na tsaya yi kafin muka shiga cikin aka gama kome muka bar kasar.
Mutanen nan sun nuna min kara, sun nuna min gata. Yadda suka nuna nice nasu sai ka fahimci dabi'ar dan adam ce kyautatawa da adalci, son da suke yiwa nasu suka bani, lokacin da Aunty Herlim take gaya min ai kudin da aka biya bashin bankin Abbana ba dukiyar kowa ba ne na Granny ce, tun bata ganni ba take kaunata, da ta ji labarin ta ce zata biya. Sai na rasa kuka zan yi ko dariya, wato Hafiz ya ce min babu wanda zai kara shiga duniyata domin shi yafi dacewa da ya zauna a duniyata. Amma yau Allah ya bani mutane masu yawan gaske da suke tare da ni hagu da dama. Sannan ta kara min da cewa. "Kada ki damu a cikin abinda ta baki ba kome ba ne, ita me bukata take nima ma ta bashi, kin san mu nan har gajiya wasu suke da tara dukiya don ma muna tare ne. Kuma Mijinki ya ce bai yarda mu nisanta kanmu da ita ba, shi yasa da kare ko maguna da suke tare da ita a cikin gidan nan zata barwa kome nata." Ikon Allah wai nace ikon Allah ko nace masu yi domin Allah, ina wata miyar sai a makota.
Haka muka yi yawo wani bin su kai ni har shagunan Granny da wasu gidajen Mamarshi, wai ana haya ne. Shi dayansa dole yayi ta rayuwa tare da magauta. Kawai abin bani mamaki yake yana da kome da zai yi rayuwa irinta alfarma amma yafi gane yayi rayuwa tsaka tsakiya... [12/24/2025, 10:15 PM] Maman Walid: 28
Ban san wani irin mutum ne shi da bai dauki duniya da zafi ba, dafa kafadata Aunty Herlim tayi tana faɗin." Yana sonki yana matuƙar kaunarki mutanen nan suna sona da dukkan zuciyarsu, sun dauke soyayyar da suke mishi sun daura min, bakiɗaya, suna min kawaici da yakana akan dansu.
Haka Auntynshi zata dauke ni ta kai ni wuraren kakar da na Mamarshi har nayi ta mamaki. Idan har zan bude baki zan iya cewa Alhamdulillahi domin Allah ya bani Mijin nunawa sa'a, yau maganar Hafiz da yake cewa idan bashi ba, babu namijin da zai iya kula da ni, yau ina karyan babu wanda zai so ni. Ina zaune a bakin gado ya shigo ya zauna tare da cewa." Sanyi nake ji ko zan samu coffee! " Tura baki nayi ina faɗin. " Kai yanzu kana shan coffee zaka hanani barci karshe haka zamu kwana kana abu daya gaskiya sai dai ka sha tea!" Rike baki yayi yana faɗin. "Eyee wato ga mara gata zai sha tea? Ni coffee zan sha ki rike kayanki tunda ba zaki bani ba nima aiki zan yi!" "Atow tunda aiki ne ba kome!" Na wuce na hada mishi na kawo, sannan na wuce ban daki nayi wanka nazo na sauya kaya na kwanta. Ni a lissafina ai aiki zai yi sai da na kwanta har na fara barci shima ya watsa ruwa ya zo ya kwanta, ikon Allah ba sai labarin ya sauya ba, haushi kamar na ture shi haka nayi ta mishi mita, bayan kome ya wuce na sake wanka na fito ina hararansa ya koma bakin aikinsa, zungure keyarshi nayi ina faɗin, "Cheating is bad!" " Hakkina na amsa ba Cheating da nayi! " Tura baki nayi na cigaba da barci, a hankali kwanaki suka yi ta tafiya ashe wani aiki yake anan din sai da muka shafe wata uku sannan muka juyo Nigeria, kasar mu ta gado. Uncle Auta da Ubaid suka zo daukar mu, sai tsiya suke mishi har da ni, wani k'amk'ame hannuna yayi yana wani cin magani shi nan kada su min magana. Kallonshi nayi bayan na raba kaina a kafad'arshi, sumbatar hannuna yayi har muka isa gidan Nihla da Yaran Uncle Auta suka yi t rige-rigen hawa jikinshi, haka ya dauke su. Yana sauke su ko wancan satin na hango buƙatar Yara a tare da shi amma yana kokarin dannewa watanmu tara mun kusan na goma da aure amma mutumin nan yana iya samun kanshi a yanayin son Yara yayi ta dannewa. "Sannu da zuwa sannu kun sha hanya?"inji matar Uncle Auta "Alhamdulillahi da fatan mun same ku lafiya?" , Matar Ubaid tana gefe tana cin chew gum. Kallonta nayi na ga yadda take wani dauke kai na ce mata. "Sannun da fatan an same ku lafiya!" "Lau ya yaji?" Ta fada tana kallon cikin idanuna, ganin hankalin mazan baya kanmu na ce mata. "Alhamdulillahi, gamu nan dai mun yi yaji mai capacity.!"
Murmushi tayi tana yar dariyar renin hankali ta ce min. "Allah yasa ba wurin tsohon kwano aka koma ba, daga nan gida aka nufa." Kallonta nayi da kyau na fahimci maganar da ta min, sai na kallu Turaki da yake d'aga min gira. "Na wanke na bashi ya sha ko wurin tsohon kwano na koma ba zai iya tari ba, mace da ta isa bata kuka akan namiji bata bin namiji don ya zauna da ita shi yake binta don ta zauna da shi, ni ko ban zauna da Turaki don Allah ba zan zauna don kawunsa da amininsa." Ina gama fadar haka na wuce na barta nan, na je na fito na sami ko ina Tsaf, na fito na cewa matar Uncle Auta. "Sannu Maman Daddah, gidan yayi kyau. Ubangiji ya haka Uncle Auta hango wata." "Ke ya kamata ko fara yiwa kanki addu'a domin mun gaji muna son Yara a gidan Turaki!" "Eh tow ai ni ban hana Turaki auro wata mace ba, tabbas yana bukatar wata mace a rayuwarsa domin ya haifa mishi Yara, amma ban sani ba ko shi yana maraba da second wife don nasan ni dai ba raguwa ba ce sannan ba xan yi kukan don Turaki yana tare da wata mace ba, domin duk wacce zai aura sauran bazawara ce! " Na fada ina d'aga mata gira, duk Mazan suka juyo gare mu. " Wai me kike nufi da ni?" Matar Ubaid ta tambaye ni, dariya nayi nace mata. "Kamar ya? Magana muke cikin raha kuma na ga babu fada!" " Karya kike Lubabatu Usman Umar Jama'are, kina jin haushin don Turaki yana son Nihla ce!? Wato don kin lalata mahaifarki shine bari ki saka idanun akan Yarinyata da yake so!" Dariya nayi mata na ce mata. " Ni bana haushi akan yarki kuma ba zan fara ba, idan ta ni ce ki na gaya miki idan kin so saboda so ko bashi auren Nihla shine karshen soyayyar da zaki nuna mishi kenan na san kin isa." Cikin jin haushi ta ce min. " Shi yasa kika shiga kika fita aka fasa aurenshi da yar uwarsa ko!" Dariya abin ya bani na ce mata. "Allah ya min tsari, aure ai dole Turaki yayi aure wai tsaya akan me nake baki amsa ne? Dalla ja tsumman rayuwarki idan kin isa ki hana Mijinki aure mana idan ni na hana nawa, aure kuma ki rubuta ki ajiye turaki zai yi shi amma ba a yadda kike so ba!" Zata kara magana Mijinta ya ce mata. " Ya isa haka Falilah ya isa kada kuma cewa uffan. " D'aga mishi hannu Turaki yayi ya tako gabana ya riko hannuna ya ce min." Da gaske kina son na kara aure na haihu?" Na zata ya amshi maganar ne, cikin kwarin gwiwa na ce mishi. "Eh kai kana bukatar Yara ko ranar a can na ga yadda kake daukarsu kaima ya mata ace akwai a gidan nan." Wani irin kallo yake min ." Kina nufin bakya kishina!" Murmushi nayi na ce masa. " Ina kishinka kai, kawai ni dai ina son ka haihu!" " Ya Isa ban san bakya bukata na a rayuwarki har haka ba, kin fini idanun ganin mata ne ko kin fini zuciyar son Yara;" daga haka ya juya ya bar gidan, ina ganin yadda take murmushi na ce mata. "Ki yi dariya a fili, ni bana tsoron fushinsa, amma duk ranar da nayi fushi hatta Mijinki gashi nan bai isa yayi barci cikin kwanciyar hankali ba."
" Kyale munafuka akwai abinda take nufi!" Inji Matar Uncle Auta, Ubaid ma ya mata tas suka fito. Har dare bai dawo ba har na kwanta cikin dare na ji shi a bayana, juyawa nayi ina kallonshi, shafa kaina yana faɗin. " Shiiiiii;" tuni barci yayi gaba da ni, da asuba ina farkawa na ga baya nan, haka na farka nayi alwala. A hankali sai na fahimci fushi yake da ni kuma yaki yarda mu fahimci juna. Haka yayi ta jera kwanaki yana fita babu karyawar kusan sati biyu, ranar na tashi na ga not yayi tafiya zuwa abuja na kira bai ɗauka ba, sai dare ya kira ni, nan ma babu wani alamar ya huce, ranar da zai dawo ya turo min sako na shiga aiki na gama. Koda ya dawo ya fita ya dauko Nihla suka shigo gidan, wurin karfe shida sai ga wata yarinya budurwa kusan suna yanayi da Maman Nihla, ta shigo tana wani dan jiji da kai kallo daya nayi mata na watsar cikin iyayi da kwailanci take gaida shi yana parlourn sau daya ya amsa bai kara bin ta kanta ba, wai tazo daukar Nihla, amma ta zauna tare da saka shi. A raina na ce yau dai ga budurwa nan a gidan. Haka ta gama iyayi bai d'ago ya kalleta ba, yana gama cin abincin ya dauki yarinyar ya fita da ita, itama zuruf ta bishi, na gyara zamana.
Abubuwan sun min yawa, don haka na zauna jiranshi har karfe sha biyu ba dare, bai san ina parlourn ba, ya shigo na haska wayata. Cak ya tsaya a hankali na isa bayanshi, don ina ganinsa ta gaske da yake shigowa na waje, na rungume shi gam. "Ina sonka Bilal, ina sonka ina kaunarka ina kishinka, amma ka tambaye ni dalilin da na ce kayi aure? Kasan me yasa nake son kayi aure? Idan kace ba ka so ban isa nayi maka dole ba, amma ka sani ko ban saka ka kayi ba dole kayi domin Yara suna cikin jin dadin duniya, ka sani ba zan maka dole ba, amma wannan silent treated din yafi kome zane ni, gara ka gaya min gaskiya zai fi min sauki da sassauci. Ba zan kara maka magana ba amma ka daina azabtar dani da haka Please." Na fada ina kuka, janyo ni yayi yana faɗin. "Am curious da kika ce na kara aure, ni a ganina na auri mace ta haihu da ni ba ke ba, cin amanar kauna ce, ba adalci ba ce ba kome ba ne son zuciya ce. " Girgixa kai nayi ina kuka na ce mishi." Ba cin amana bane, adalci ne zaka yi don ka haihu da wata mace mace ba wani abu ba ne. Wallahi ba kome ba ne kyautatawa ce da adalci!" " Ba zan iya adalci akanki ba, zan auro mata nayi ta zaluntarsu, zan ta cutar da su saboda ke ina sonki da bana iya dauke idanuna akanki a kwanakin da nayi hakuri nake, amma ba zan iya son wata mace bayan ke ba. Zan cutar da ita su kuma zasu cutar min dake!" Rike fuskarshi nayi cikin kuka nace mishi. " I miss you baby;" na fada ina shashekar kuka, rungume ni yayi yana faɗin. "Bana da ra'ayin wata mace Allah ya gani amma idan wata tazo ba yadda na iya ke daya nake so!"
Shi kenan fa fada ya kare nayi alkawarin ba zan kara mishi maganar aure ko haihuwa ba, kwanaki biyar tsakani ya shirya mana tafiya zuwa ganin likita ni da shi, kasar Ingila. Dama nasan matsalata ban boyewa likitan ba, ya bamu test ya kai goma, kullum ana mana daya kullum sai da muka yi kwana goma aka tsaya jiran sakamakon. Sai da muka samu kwana hudu kafin aka kiramu likitan ya kalle ni ya kalle shi kafin ya ce mishi. " Kana da Chance sosai na haihuwa, amma ita gaskiya babu Chance sosai domin duk wani hanya da kwayar halittar zata shiga ta wuce har ta samu kwan halittar ta ya toshe. Don haka zamu iya cewa kai baka da matsala akai haihuwa matsalar ta Madam ce itama da a iya magance ta amma sai ta amince ko nace kun amince sai ayi mata. HSG" zuba mishi idanun muka yi kafin muka kalli juna yadda kuka san ana mana hisabi, saboda tsananin tashin hankali. Mene ne kuma HSG? Kamar yasan abinda muke nazari ya sake murmushi ya ce mana. " Ku kwantar da hankalinku ba wani babba al'amari ba ne!"
(Kuyi hakuri don Allah bana jin dadi amma da sauki sosai sannan masu kodai kodai 🤣😹 Wallahi bashi ba ne hmmm idan shine ai maganar rubutu ya kare wai wata Shekara zan cigaba idan da shine Nagode sosai Ubangiji ya karo zumunci) [12/25/2025, 10:02 PM] Maman Walid: 29 Sauke ajiyar zuciya muka yi lokaci guda, yana rike da hannuna. Wani irin tsoro yana fisgana. Na kalle shi murmushi yayi min irin na kwantar da hankalina, sannan na mai da idanuna kan likitan. Murmushi yayi ya fara zubo bayani kamar haka. "Da farko dai zan muku karin bayani akan yadda ake yin HSG" " A harshen Hausa, HSG (wato Hysterosalpingogram) wani nau'in binciken likita ne na musamman da ake amfani da hoton X-ray da wani magani mai ruwa (dye) domin duba mahaifa da magudanar kwai na mace."
"Ga daki-daki bayanin ma'anarsa da kuma dalilin da yasa ake yinsa" sai da ya sauke numfashi kafin ya kalle mu, ganin yadda na gama firgita, ya kalli Turaki yana murmushi ya ce mishi. "Na ga kamar kai kafi madam karfin zuciya ko akwai tambayar da zaka yi ne?" Jinjina kai Turaki yayi yana matsa hannua ya ce miishi, "Mene ne Ma'anar HSG?" Cikin nutsuwa da kwarewa likitan ya ce mishi. "HSG gwaji ne da ake yi a sashen hoton X-ray. Likita zai sanya wani siririn roba ta farjin mace zuwa cikin mahaifa, sannan ya tura wani ruwan magani. Wannan ruwan yana haskaka cikin mahaifar da bututun da ke kai kwai (fallopian tubes) domin a ga yadda suke a cikin hoton X-ray." Gyad'a kai yayi yana me kara kallona, jin irin azabar da za ayi min ban san lokacin da hawaye ya fara sauko min ba. Ya share min da hannunsa ya kara kallon likitan ya ce mishi " Me ya sa ake yin HSG? (Dalilai)"
"Likita kan bukaci wannan gwajin ne saboda manyan dalilai kamar haka"
* Binciken Rashin Haihuwa:
"Wannan ne babban dalilin. Ana son a gani ko magudanar kwai (fallopian tubes) a toshe suke. Idan bututun ya toshe, kwayar halittar namiji ba za ta iya haduwa da kwan mace ba."
* Duba Siffar Mahaifa:
"Don ganin ko mahaifar tana da wata matsala tun daga halitta, ko kuma akwai wasu abubuwa kamar fibroids ko polyps da ke hana juna biyu zama."
* Bayan Tiyatar Mahaifa:
" Idan an yi wa mace tiyata a mahaifa ko an toshe mata magudanar kwai don tazarar haihuwa, ana yin HSG don tabbatar da cewa tiyatar ta yi nasara."
* Binciken Bari (Miscarriage):
" Idan mace tana yawan yin bari, ana yin HSG don ganin ko mahaifar tana da rauni ko kuma tana da siffar da ba za ta iya daukar juna biyu ba." Ajiyar zuciya muka sauke lokaci guda, tare da rike hannun juna gam Turaki ya kara tambayarshi.
"Yaushe ake yin sa?"