ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 14
ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 14: ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 14. Duk yadda yaso ya rarrashe ni, zan ture hannunsa ina murmushi. " Na fahimce ka ai! " Daga…
4,183 words
Duk yadda yaso ya rarrashe ni, zan ture hannunsa ina murmushi. " Na fahimce ka ai! " Daga haka na datse duk wani abin da yake tsakaninmu, daren ranar ban shiga dakinshi ba da ya zo yana tambayar ko abinda ya fada ne ya saka ni ware kaina daga gare shi na girgixa kai nace mishi, ga "period nake bana son Magana!" Kuma nayi dace period din ya zo, don na samu sauki na bar shi, haka yayi hakuri ya koma dakinsa, na kyale shi ya zauna shi ɗaya. Washi gari, ban tashi nayi abin karyawa da wuri ba, ina tashi na hada mishi tea da bread da egg, na koma na kwanta. Lokacin da ya shigo dakin ina juyin ciwon ciki, "ko za mu tafi asibiti ne?" Girgiza mishi nayi tare da cewa. "Ba damuwa ka je ai ba kome." Haka ya bar gidan da kyar shima sai da ya makara. Wurin karfe biyu na gama abincin dare da na rana, don ya ce zai zo duba ni. Haka na gama kome nayi wanka, da ya tashi zuwa sai gashi tare da Airah. Yadda take wasu abubuwan yasa na kai zuciya nesa. Murmusa mata kawai nake, har ya ci abincin ya kalle ni cikin kulawa ya ce min.. "Ya jikin naki?" Murmushi nayi kawai na cigaba da cin apple. "Da sauki ko?" Lumshe idanuna nayi ina gyad'a mishi kai. "Allah ya baki lafiya." Tura mishi sako aka yi ta wayar ya duba, tare yanayinsa ya sauya. Ya kalle ni da kyau sai ya cire hannunsa a cikin abincin yana faɗin. "Na koshi!" Ya fada yana ture plat din, murmushi nayi na tashi na hada juye wanda ya ci na gyara wurin, ya ce min."mu koma!" "Allah ya kiyayye hanya!" Na shige kitchen a bisa ka'ida raka shi nake, amma na barshi ya fita shi kanshi sai da ya juyo ya kalle ni, sannan ya bar gidan. Sai da na shiga kitchen hawaye yayi ta zubo min. Haka na sha kuka na ban gayawa kowa ba, shima kuma ban san dalilinsa nayi haka ba,
Wurin karfe hudu da rabi, na fita gidan Uncle Auta, muka tafi gidan barka a can muka hadu da Matar Ubaid, kamar yadda ta yi kamar bata ganni ba, haka nayi kamar ban santa ba, na cigaba da danna wayar ita kanta mai jegon da yake kawarta ce da kyar ta amsa min, ban yi karambanin a bani yaro ba, daga kan cinyar Matar Uncle Auta na kalle shi, daga nan na cigaba da uzurina. Ba zaka fahimci yadda abin yake ba, kusan kowa a gidan sai na fahimci kamar baya maraba da ni, har muka fita daga cikin gida, bayan mun dauko hanya ne matar Uncle Auta take tambayata. "Wani abu ya haɗa ki da Maman Nihla ce?" Girgiza kai nayi ina kallon kasa. Na d'ago na ce mata. "A'a." "Tow shi kenan!" Daga haka muka isa gidanta na zauna kadan sannan na wuce gida, ina shiga na same shi yana aiki, "sannu da dawowa!" Ya ce min, murmushi nayi na yi nace mishi. "Yawwa!" Na wuce dakina na barshi a parlourn yana aiki, kiran sallah Magariba yasa shi lekowa ya samu ina tattara wasu takardun, zuba min idanu yayi kafin ya ce min. "Me zaki yi da su?" Murmushi nayi mishi, na ce mishi. "Ina shiri ne in case." Daga haka na cigaba da aikina. Kai wasa wasa sai da muka shafe sati uku zuwa wata guda hala har ya manta ya gaya min bakar magana, tafiya ta kama shi Russia, mutumin nan na zata zai ce min na shirya mu tafi amma ya wani hada kayansa yayi gaba, ni kuwa na hada nawa kayan na wuce Bauchi don tsabar masifa mota na bi, balle har ya bincika ya ji labarin inda naje, zuwa yanzu watanmu hudu da sati biyu, a cikin watannin nan bai wuce a kirga hada shimfidar da muka yi, haka na shanye duk wani b'acin rai.
Kwana biyu me kyau muka yi a hanya, muka iso Bauchi kafafuna sun kumbura. Sai da na wuta sannan na dauki keke napap, zuwa gidana da yake G. R. A. Ya samu me kula da gidan yana waje, na isa cikin farin ciki ya amshi jakata yana tambayar ya hanya? Na ce Alhamdulillahi, na shiga bayan ya bude min, sannan na shiga cikin gidan. Kasancewar isowar safiya ce mika mishi atm nayi na ce mishi. "Don Allah ayi min cefane, sannan ka haɗa min da dankalin turawa, kome dai ka kawo min and ina niman alfarma kada wani ya tambaye ka, nazo kace na zo don Allah!" "In sha Allah Hajiya."
Daga haka na wuce cikin gidan na shiga aiki, nayi wanka na gabatar da Sallah da ban samu ba asuba, kwanciya nayi wurin minti arba'in ya dawo da kayan abinci, na amsa na kai kitchen ya ce min. "Hajiya nayi karambanin saya miki nama gasu nan!" Na ce mishi. "Na gode sosai!" Daga haka na y fita na duba kayan na kai kitchen na duba kudin da ya cire na ciro 5k na kira shi na bashi, sannan na koma na kwanta, wani sabon aiki na ga ba gas haka na kira shi ya fita ya sayo min gas sannan na yi abinci na saka mishi, da daren na kwanta nayi barcin gajiya, wayata a kashe babu yadda zaa same ni. Lagos. Kwana biyu me kyau Mai kula da gidan yayi ya ga bana ko fitowa, haka yasa shi zuwa gidan Ubaid don ya ga fitar Uncle Auta, da yake ya san gidan ya shiga ya samu yana shirin tafiya aiki. Bayan ya gaishe shi ya ce mishi. "Oga Iyawo yau kwana biyu bana jin motsinta, ban san me ya faru ba, ko zaka zo la ga jiran ne?" "Kuma lafiya?" "Ni dai kwana biyu kenan bana jin motsin ko karatun da take sakawa bana ji." Gyada kai yayi kafin ya ce mishi. "Jeka ina zuwa!" Ya koma cikin gidan, ya samu Matarshi tana bawa Nihla abinci.. "kin san inda Matar Turaki ta tafi ne?" Wani shewa ta saka tana faɗin. "Ni kuma zaka tambaya? Waye ya san inda take bayan kai tunda abokiyar harkallanka ce." Bai kulata ba, ya fita zuwa gidan Uncle Auta, ya tambayi Matarshi, ta ce mishi. "A'a bata zo!" Kanshi ya shiga duhu sosai. Don haka ya zo gidan ya duba bana nan babu alamar inda nake, kasan kiran Turaki yayi ya kira Uncle Auta suka shiga tattaunawa. " Haka kawai Lubnah ba zata tafi haka ba, akwai abinda shegen ya mata wallahi ba zata tafi ba. " Haka suka yi ta jajjantawa, kai karshe Uncle Auta ya kira Alhaji ELYakub ya gaya mishi amma ya ce kada ya gayawa Turaki. Haka dattijon yaji abin kamar saukar aradu, kwanakin da suka biyo baya. Abin ba dad'i Uncle Auta ya je gidan Ya Ado ya tambaye shi ko na zo ya ce mishi a'a. Bai yi saurin fitar da maganar ba, zuwa gida abu daya Ya Ado ya gaya masa.." Lubnah ba yarinyar ba ce, sannan tunda ta bar gidan Turaki da kafarta imma tayi haka don ta fahimtar damu cewa tana zaune amma bata jin dadi, ko kuma an je har gida anyi mata abu ta ji haushi ta fita. Idan baka manta ba, da aka bashi ita mun gaya masa idan ba zai iya ba ya dawo mana da ita, idan har gazawar tashi ce tow tabbas Turaki yayi abinda ba xamu iya yafe masa ba, idan kuma ita tayi kuskuren zamu hukutatta daidai da laifinta."
Uncle Auta ya shiga tashin hankali, domin zarginsa akan family ɗinsu ne, don haka yasa hukuma cikin lamarin, a wannan lokacin zuriar KUMO suka fahimci girma da darajar Turaki baya nan amma yadda Mahaifinsu yake barazanar tsine musu albarka. Suka yi ta rantse rantse. Al'amarin da ya janyo suka ji a ransu lokaci yayi da zasu bar Turaki tunda na da zinari aka halicce shi ba, gwanin har kwashe sati daya ba labari kawai aka kira shi aka gaya mishi. Duk abinda yake ya dawo gida fa, lubnah ba a san inda take ba, wani abin yafi kome tsaya mishi a raina.
Cikin abinda bai wuce 10hrs ba, sai ga Turaki a lagos, kamar wani zarrare. Haka ya zauce aka yi ta nimana, Ya Ado ya hura mishi wuta ya nimo ni, shi kuwa ya rasa inda zai saka kanshi. Haka ya je Airport ds taimakon shugaban airport ɗin ba a samu wani labari ba. The next abinda yayi shi ne fara binciken ta ina zai samo ni. Ya kira Mama yayi shiru kafin ya gaya mata gaskiyar abinda ya faru, shi a tunaninsa ya fadi haka ne don ya rage wani wage da yake tsakiyarmu, amma ina abinda ya fada a wannan lokacin Mama ta ce mishi. "Idan ka samo min ita ka haɗa da takardar shaidar saki ka kawo min, na zata kai me hankali ne ashe sakarai ne, ok idan ka samo ta ka dawo min da ita don ta gama aure da kai." A lokacin da ya tafi gidan Kakanshi ya gaya mishi, abinda ya faru. Kifa mishi mari yayi har sau biyu. "Mutumin banza kawai gata hauka ne, a shekarunka idan baka yi hankali ba yaushe zaka yi hankali ga matar Kanin Ubanka, matar Ubanka ya aura har da albarka a aurensu, kai kuma mara kunya kana kishin jahilci, Iyayenta sun kira suna bukatar yarsu da takardar shaidar saki." Hankalinta ne yayi mugun tashi tare da jin kamar yayi gagarumin kuskure amma taya zai gyara? Idan har ya ce zai gyara taya kenan? Kiran Granny yayi ya gaya mata halin da yake ciki itama ta ce mishi.. "amma baka da kunya, Allah yasa su karɓe yarsu tunda baka da mutumcin mutumin banza kawai." Cin mutuncin sosai dattijon nan yayi mishi, shi kanshi ya rasa ta ina zai fara. Ina zai fara zuwa, kakaninsa sun juya mishi baya, domin kuwa sun samu labarin irin zaman da nayi a baya, sannan kuma shi da bakinsa ya gaya musu abin da ya gaya min , kuma na bar shi ba tare da wani alama ba. Wannan abin ya tsaya mishi a rai.
Kusan ana niman sati uku kenan, babu wanda yayi tunanin zuwa Bauchi ko Gombe as ko na tafi can!
*** Yau Laraba, yadiko da Mama sun gama abin sadaka kenan, Yadiko ta kalli Mama yadda tayi shiru wanda ya bata damar cewa. "Ina ga Lubnah tana kusa tunda bata wurin Yan uwanta, ina ji a jikina tana matukar kusa damu, wallahi naji haka a jikina. Tayi haka ne domin wani dalili mai karfi. Kai bari na je gidanta na G.r.a." Ta shiga daki ko minti biyar bata yi ba, ta fito Mama ta ce mata. "Bana jin tana nan kusa." Girgiza kai yadiko tayi ta ce mata. "Bari dai na dawo!" Ta fita.
Sai da tayi tafiya sosai kafin ta samu keke napap, ta fada mishi inda zai kaita. Ya fada mata kudin ta ce su je. Bakinta dauke da Addu'a zuciyarta na bugawa saboda tsoron kada ta samu, bana nan har zuwa unguwar da yake tazo lokacin da ake kawo kaya, kofar gidan ba kowa da alamu me kula da gidan ya shiga cikin gidan, don haka ta shiga gidan kai tsaye tana sallama. Muna tsaye da shi ina mishi lissafin abinda zai sayo min, kawai na ga Yadiko akanmu, jikina ne ya dauki wani irin rawa, abinka wacce bata saba laifi ba, kallonshi nayi taya ya bar gidan A buɗe? "Hajiya lafiya? " Ya cewa Yadiko, " Uwaki Lubnah! " Ta min dakuwa da hannu bibbiyu, " Nace kin ci gidanku! Haka muka miki tarbiyya?" Idanuna ne ya cika da kwalla shima mai gadin ya ce min. "Kiyi hakuri Hajiya mantawa nayi da gidan a buɗe!" "Maza dauko Hijab dinki mu je gida mara mutunci!" Kiran wayar Mama ya shigo wayarta. Sai da ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce mata. "Tana nan bata je ko ina ba gamu nan zuwa da ita." Daga can Mama ta ce mata. "Ki tawo min da ita!" "Tow shi kenan." Haka yadiko ta saka ni a gaba muka nufi gidanmu, kunya duk ya kama ni. A lokacin da muka iso gidan, wani matsiyacin kallo Mama ta min tana faɗin. "Allah ya ganar dake!" Sai bayan isha suka min fada sosai, kafin Yadiko ta gayawa Ya Ado shi kuma ya kira Uncle Auta ya gaya mishi, a ranar labarin ya tafi kunnen Turaki..
Har dare Yadiko fada take min, sai da lokacin kwanciya yayi ta ce na je dakin Mama, haka na wuce dakin na je na kwanta, duk da haka bata tambaye ni ba, nima ban gaya musu kome ba, sai washi gari ina karyawa ta ce min."idan bakya son auren ina ga ku rabu mana?" Kallonta nayi kafin na ce mata. "Ai ni dashi bamu yi fada ba!" "Amma ya gaya min dalilin barin gidan ko?" "Wannan ai ra'ayinsa ya fada ni dai Bauchi nake son zama yayi aikinsa a can ni na zauna nan, sannan ki roka min shi yayi aure don Allah............ [12/23/2025, 7:46 PM] Maman Walid: 26 "Kin san illar haka kuwa yayi aure fa?" Kallonta nayi, kafin ka dauke kai ina tura kosai bakina. " Ko dai yana miki wani abu ne?" " Ba kome!" Na fada mata, na cigaba da cin kosai na har na gama bata kara magana ba, " yanzu ya kike so nayi?" Juyawa nayi kamar zan yi kuka na ce mata. " Ki ce mishi yayi aure na amince!" Murmusa min tayi irin na manya, ta ce min. "Shi kenan!" Na ci gaba da karyawa bata kara magana ba, ina jin suna magana da Yadiko na zata maganar auren ne amma bata mata ba, wurin karfe daya ina barcin rana, gidan ya kaure da hayaniyar da ya tilasta min farkawa. Na sauko daga saman gadon Mama na fito parlourn kaina babu dan kwali. Shine zaune a parlourn yana waya kamar ba zai yi magana ba, kallo daya nayi mishi, duk ya fada kamar mara lafiya. Kurawa juna idanu muka yi. Daga yadda ya motsa lips ɗinsa na fahimci abinda ya ce min.. wato "kin kyauta min!" A hankali na juya zan bar parlourn. "Ok! Sannu!" Ya fada har zan shiga cikin dakin ya ce min. "Haka ake amsar bako?" Juyawa nayi ina kallonshi, komawa ciki nayi na saka hula na fito na samu Yadiko ta shigo suna gaisawa, Mama da su Uncle Auta suna parlourn Abba. Fita nayi na kawo mishi ruwa da sauran abin karyawa, ya sauko daga kujeran ya fara ci yana faɗin. "Ayi hakuri!" Tashi tayi ta fita, ta barmu a parlourn shiru ya wanzu a parlourn. D'ago kai yayi yana kallon yadda nake danna wayata hankali kwance. "Nasan nayi kuskure amma me yasa ba zaki fahimtar da ni ba? Kowa ya daura min laifi eh nayi kuskure amma barina a wannan lokacin kin san illar da kika min?" "Saboda ba ni ba ce na gaya maka maganar da ya fito bakinka ba, Yes nasan haka kake baka iya boye abinda yake ranka, shi zaman da zaa yi shi babu yarda meye amfaninsa? Ni da ce min kai yi je ki na sake ki zai fi min sauki, amma ka gaya min don waninka ya aure ni kake gaya min magana ba zaka iya kasancewa da ni ba, tow me kake so na maka yanzu? Na rantse da Allah kai da kanka na gaya maka haka sai ka ji kamar babu amfani na cigaba da rayuwa da kai!" Daga haka na mike zan tafi dakin ya ce min. "Idan ke ce kika tsohuwar matata take kiranki tare da tura miki hotuna da bidiyo dinmu da wanda muka yi tarayya ya zaki ji?" Juyawa nayi na kalle shi murmushi nayi na ce mishi. " Shi yasa nace mu rabu kowa ya kama gabanshi, ai babu amfanin zama da zargi, har na gama zama a KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY, wani ya tab'a yunkurin keta min haddi ne bayan cousin dinka? Ba laifi bane idan ka ce ba zaka zauna da ni ba, zuwa yanzu na fahimci waye kai! A da can ina kallonka a matsayin wanda ko a gidan karuwai ka dauko ni zaka iya aurena a haka ka zauna da ni, tow tsaya idan bai cusa maka bakin ciki ba, taya zai fahimci nayi mishi nisa, ku dai maza kullum abinda ya muku kawo kuke ɗauka akanku wanda bai kai a dauka ba, ba zaku dauka ba." Na wuce na barshi, waya na ji yana yi sannan ta fita, can Mama ta zo ta kira ni na isa parlourn. Ya fadi abinda yayi min ya ce shi yasan abinda ya kawo na bar gidan kenan, Kallona Abba yayi na ce mishi. "Ni bai min kome ba!" "Karya ne wallahi nayi miki, don Allah ki fada kome wannan shirun naki gara azaba da shi, Abba nasan nayi laifi amma naso na dauke kai amma Hafiz ya dame ni, Hafiz ya takura min zuwa yanzu hatta email din Lubnah yana da iko da shi. Hafiz hatta wurin aikina ya tura sako marasa dad'i, Hafiz ba yaro bane na saka hannu a jikinsa amma kamar bai san inda yake miishi ciwo ba, nayi ƙoƙarin gano me yake bukata, sai na gano kawai Lubnah ce da take tsakaninmu, har ga Allah nayi kuskure da nake jin haushinsa ina kauracewa Lubnah, wallahi. " Tashi nayi na bar parlourn, domin da gaske bature ne bai da kunya yanko magana yake kawai, sai da Uncle Auta ya dakatar da shi, daga Abba har Mama sai aka rasa me magana domin ya fada musu shi fa rayuwar aurenshi lafiya lau kawai Hafiz yake mishi kutse har hukuma ya shigar Hafiz ya ki dainawa, yana gudun abinda zai taba mutumcinsa da kimarshi ce. "Har yau Hafiz bai rabu da Lubna ba dama? Ka dauki Matarka ku je gobe da bayan sallah isha ku dawo da ita. " Inji Abba, haka Mama ta fita daga parlourn ta saka na hada kayana, tunda na ga haka haushi ya kama ni hijab dinta na saka ko kaya ban ɗauka ba, muka wuce Uncle Auta sai hakuri yake bani, ya kuma hada ni da Alhaji ELYakub. Ya bani hakuri sosai sannan ya kara min nasiha, har muka isa gidan na wuce kitchen na gyara na fara ƙoƙarin daura abinci, ya shigo. "Ki bari nayi takeaway. Don jibi zamu wuce lagos." Wani irin kallo na mishi, "me zan ya a can? Ka daina ma tunanin xan kara binka, ka je ka auri Virgin ka ajiyeta a Lagos." Shiru yayi yana tuna Kalaman Abba da ya ce mishi. "Kana da Chance da zaka gyara alakarku, ka tafi da ita kishi kuwa kowa yana da ita, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya auri Khadijah yana da shekaru ashirin da biyar ita kuma arba'in sannan ya zaune da ita har ta haifa mishi Yara, kana kuma ita bazawara ce da ta girme shi. Don haka idan kana da ra'ayi kafin gobe ka goge kuskurenka da laifinka, idan kuka dawo bata iya goge laifinka, Hafiz yayi nasarar juya maka lissafi domin ya fi ka sanin wacece ita, ya kuma san zaka dauki kishi da zafi ita kuma zata ga babu amfanin aurenka." Fisgo ni yayi ya saka hannunsa bibiyu a kafadata. "Look at me? Me kike so?" " Zaman Bauchi!" Na fada mishi haka kai tsaye, "ok! " Ya fada bayan ya rungume ni, shiru nayi a hankali na ji kwalla yana zubo min, sake rungume ni yayi ya ci-gaba da bani hakuri. A hankali na fara kuka mara sauti, yana bubuga bayana, daga nan ya dauke ni cak, zuwa dakina. Sauke ni yayi ya daura ni a kan kujerar dakin ya gyara dakin. Kafin ya janyo ni gadon muka zauna, a hankali yayi ta rarrashina har labarin ya sauya na rasa wani munafuncin ne ya janyo ni na bashi damar yin abinda na ce ko me zai min ba zan kara yarda da shi, na kuwa san nayi yaji domin har barkono sai da ya gaya min yadda ake nomarsa, kiran sallah la'asar ya saka ni mikewa zuwa ban daki nayi wanka koda na fito yayi barci, dama da Alwala na fito na shimfida abin sallah, na shiga gabatar da sallah. Bayan na isar nayi addu'a, zuwa inda yake nayi na tashe shi yayi sallah, ya janyo ni na fada kanshi yana shafa fuskana. "Tashi nayi sallah" "hmm but ban koshi ba!" "Cab yunwa nake ji!" Na fada ina kwace kaina na fito na daura abinci, ina ta aiki ya shigo da Jallabiya. Sumbatar wuyana yayi ya zagayo da hannunshi kan cikina, ina aiki yana hana ni sakat. "Ka rufa min asiri kada na kone, dama ina bazawara kaga sai ka auro budurwa Virgin!" Shiru yayi ya daina sumbatar ya dawo gefen firj din yana kallona. "Allah ya baki hakuri." Ban kula shi ba, na gama girkin sannan na fito zuwa waje yana biye da ni na shirya abincin, kiran sallah Magariba ya fitar da shi, wurin karfe takwas suka shigo sanin halinsa yasa na ki fitowa, sai da ya zo don kanshi ya fito dani, na zuba musu abinci, haka dai na gama abinda ya dace musu na dawo dakina na kwanta, har wurin ƙarfe tara sannan Uncle Auta ya mana sallama gobe zai wuce Jos. Ya koma lagos. Ba kunya ya ce mishi. "Allah ya tsare ka gaishe su ni kan sai kun gani." Daga haka ya mishi sallama, tunda ya shigo daki wurin karfe goma saura, ya haura gadon da nake zaune ina karanta hisnul Muslim. Ya kwace ya fara kallona kamar zai hadiye ni, a hankali labarin dai fushi na rasa inda na kai shi, dazun na zata ina masifar kewarshi amma a yanzu dai na gane bakiɗaya rayuwata zan bada saboda shi, domin yadda kome ya wakana ya kasa barin cikin kaina da zuciyata, abin ya tsaya a idanuna ba zan tab'a mantawa da wannan daren ba, ina kwance a jikinshi shafa kaina yayi ya ce min. "Kin hakura zamu koma Lagos idan muka huta anan?" Kwantar da kai nayi a kirjinsa, nayi shiru kafin na d'ago ina kallonshi."idan muka koma ka cigaba da ƙyamar wani ya taba kwanciya da ni? Kayi ta gaya min ni ragowar wani ne?" Rufe min baki da yayi da nashi, sannan ya kashe zancen babu yadda zaa yi na kara tunawa da mun yi wani rigima, kusan a tare muka yi wanka muka dawo ina kwance a jikinshi. Har barci yayi gaba da mu, kusan washi gari makara muka yi, ya zuba min idanun ina barci. "Tashi gari ya waye!" Da sauri na bude idanun, muka shiga muka yi alwala sannan muka fito a tare, bayan nayi sallah na fita waje, fitowa yayi shima yana waya bayan ya idar ya shigo ya samu ina ƙoƙarin kunna gas, riko hannuna yayi ya ja ni zuwa daki, anya mutumin nan lafiyarshi kalau kuwa? Kusan ranar yana manne da ni, bini bini, abu daya da na fahimci zai lalata min lokacina na tuna mishi zamu tafi gida yau, sai ya hakura ya kyale ni na huta, har muka ci abincin rana, don sai karfe biyu muka karya abincin rana kuwa sai yamma la'asar likis.
Karfe shida yayi mana a gida, da yake ana sallah Magariba da wuri sai da ya bude min kofar na fita don muna isa cikin harabar gidanmu muka hadu da Hafiz. Haka muka shiga cikin gidan yana rike da jakata, ni kuma ina lafe a kafad'arshi, don bana son kallon Hafiz ma. A tsakar gida muka sami Mama da Yadiko, kasancewar ranar juma'a ce ranar, muka gaishe su. Daga yadda muka tawo Mama ta fahimci mun shirya, haka ma Yadiko sannan ya ce min.. "Bari na je sallah ko?" Gyad'a mishi kai nayi, yana fita suka hadu da Hafiz sai shigo murmushi suka yiwa juna. Kowa ya wuce. Dakin Yadiko na wuce na shiga nayi alwala.
Bayan na idar da sallah, na cigaba da azkar har bayan isha, sannan na na fito saboda Yadiko ta min magana, muka shiga ban tab'a sanin haka Abba yake faɗa ba, sai da ya saka Baban Jama'are a gaba ya wanke shi tas, sannan ya koma kan Hafiz ga Ya Umar ga Lauyar da aka dauka da yarjejeniyar kada wani abu ya kara shiga tsakaninmu da Hafiz, Abba ya ce mishi. "Banda rashin kunya da rashin mutunci, yarinyar nan har hauka ta kusan yi kai nima sai da ka kusan kashe ni, a haka ban rabu da kai ba, ka lalata min suna ka ciyo bashi da sunana duk na rabu da kai Hafiz idan kai ba Tsinanne asararre bane ka fita hanyar Lubnah idan na kara jin wani abu ya kara tasowa akanka, zan ajiye zumunci da kara na daure ka sai igiya ya saura mara kunya, Ali yau na dawo maka da karar danka, idan ya lalata min auren Y'a wallahi zan dauki matakin da sai an rasa mai bani hakuri, ka ja mishi kunne idan ya har dan halak ne shi ya kara bibiyar rayuwarta sai na lalata mishi nashi rayuwar maciji da bai da ramin kanshi sai na wasu." Tass Abba ya mishi tare da buga mishi kashedi........ [12/24/2025, 10:15 PM] Maman Walid: 27