ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 13
ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 13: ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 13. Haka muka gina kanmu, kuma muka gina rayuwarmu. Zan iya cewa tunda na fahimci tarin alkhairin…
4,167 words
Haka muka gina kanmu, kuma muka gina rayuwarmu. Zan iya cewa tunda na fahimci tarin alkhairin da yake tattare da mijina, tafiya ta kama shi ina hada mishi kaya ya zauna yana goge kanshi ya ce min. " Ko zaki raka ni ne?" " Ka manta ina son zuwa gidan Ya Ado ne?" Shiru yayi kafin ya ce min. " Zaki iya min alfarman na dawo sai mu tafi tare?" Kallonshi nayi sai nace mishi. " Allah ya dawo da kai lafiya." Na fada ina murmushi, bana son ta ha kamar raina bai so ba, haka na shirya mishi kayansa, har na taimaka mishi ya sa kaya amma ina son zuwa na ga yan uwana, amma yadda ya nuna baya ra'ayi na share ban kuma magana ba. Bayan na gama shirya shi ya ce min. "Me zan saya miki?" "Kome ma ina so!" Daga haka muka fito ya shiga motar, bayan tafiyarshi ne nayi baki duk da ya hana su zuwa amma Amma saboda masifa sai sun zo. Na musu iso suka shigo parlourn. Na kawo musu abinda ya dace sannan muka kara gaisawa na ga sai dariya suke yan matan idan suka kalle ni, sanin zasu iya saka ni a damuwa yasa na barsu na wuce dakina. Kiran Aunty Zakiyah ta shigo ta ce min zasu zo in sha Allah gobe ita da Yaranta. Nayi murna sosai nace su zo da niyyar kwana yaran tunda basu gari. Ina gamawa na fito parlourn. Matar Uncle Auta ce ta shigo tana faɗin."ku wasu irin jakuna ne? Ku wasu irin jahilai ne? Kun dauka tafiyar da yayi Da badr wani abin arziki ne, shegu yan marasa kunya da mutunci." Tayi musu tas, "wai don Mijinki yayi tafiya Da badr shine zasu mai da shi babban al'amari." "Sune da wahala na yarda da Mijina sannan ni ba mahaukaciya ba ce bana saka karfi akan kome idan ya ce zai kara aure yayi wallahi bani da case da shi sai dai duk wacce zata aure shi ni ce na bude shi a leda babu Macen da zata gaya min waye shi." Tunda na fadi haka na ga sun yi wani firgita. Murmushi nayi na ce musu. "Ni saka kishi ne, ba ji kishi ba ce. Turaki da yana da buri da ra'ayin tara mata hala da nazo a ta hudu, idan kun iya ku kama kanku idan baku iya ba, ku cigaba ni bani da energy da zan yi fada akan namiji domin mijina mijin mace daya ce, idan kuka ga kaddaran wata mace ta ratsa to in sha Allah rabo ce ta kira ta, daga yau kada na ƙara ganin kafar kowacce yar iska s gidana idan ba haka ba, between ni da lu xa a damu matsala." " Ai ki kyale su sai na gayawa Turakin!" " Akan me zaki gaya mishi, sun yi na farko yayi musu fada na biyu ya dake su da yake jakuna ne, na uku na shiga cikin lamarin, kun zo ku hada mu fada tow ta Allah ba taku ba, wallahi kun yi karya ku shirya da kyau domin Allah ya bada sai dai ku yi Hakuri sai na kona fuskar yarinya idan ta kara shigo min gida idan kuna ganin wasa ne Allah ya dawo da ku gidana zaku gane baku da hankali!" Yadda na musu tass suka fita kamar munafukai.
Wannan yasa na samu sauki amma na dan shiga rud'ani da naji labarin yana tare da Badriyyah, har dare bai kira ni ba haka na kwanta zuciyata babu dad'i, gaskiya kishi masifa ce haka nayi ta juyi har sha biyu na dare, karshe na tashi nayi sallah nafilla ina addu'a na fara jin barci haka yasa na tattara na koma gado. Kafin barci yayi gaba da ni, karfe shida na safe kiransa ne ya tashe ni don kiran sallah asuba ban ji ba, haka na tashi ina mai amsa mishi bayan mun gaisa nace mishi." Ya hanya?" Ya amsa min da " lafiya lau!" " Nayi ta jiran kiranka jiya amma baka kira ba!" Na fada a shagwab'e. " Kin san Allah kada ki d'aga min hankali, kin san yadda na bar garin nan!" Tab'e baki nayi na ce mishi."Sallah zan yi!" Na katse kiran, haka kawai sai shaidan yana min wata huxubar tsiya, haka nayi sallah na yi azkar ya kara kirana. Dauka nayi ya ce min. "Please muyi video call;" kashe kiran nayi na bude datana. Na shiga imo shi ya sauke min apps din Wai yafi sauƙin kiran idan baka kasar. Can kuwa sai ga kiranshi. Dauka nayi ina kallonshi. Haka kawai nake jin haushinsa. "Yan mata nayi miki laifi ne?" Murmushi nayi na ce mishi. "Ba kome." Sai yayi ta kallona. "Da gaske ban miki kome ba?" Girgiza kai nayi, buga kofar dakin aka yi, na ji yana cewa. "Waye?" Abinda na ji kenan. "Hamma nice badr ban dakina ruwan ya tsaya ne!" Kallona yayi na dauke kai. "Tafiyar har da ita zata ga likita ne." "Ban tambaye ka ba!" Na gaya mishi. "Ki tsaya!" "Ni kitchen zan shiga ina da baki!" Na fada ina mai mikewa zan kashe wayar ya ce min. "Ki tsaya." "Me kake bukata? Ina ga ai na sallame ka sannan ita wacce take magana ai lokacinka take bukata." Na katse kiran, ba zan kara shiga damuwa akan wani namiji ba, haka yayi ta kirana amma naki dauka asalima kashe wayar nayi na shiga aikin gidana baji ba gani, kusan da yake raina a b'ace yake aiki kawai nake har da su wnki a washing machine, bayab na gama na koma dakina na kwanta ina da miya a frij. Shi na fitar idan suka zo sai na dafa shinkafa da dodo. Wurin karfe sha biyu Uncle Auta ya zo da Matarshi, Ni abin sai ya dame ni. " Ni fa ba fushi nayi ba, amma shi yana ganin kamar nayi fushi ne? Lallai fa ita ai yar uwarsa ce, sannan ko babu kome akwai aure a tsakaninsu akan me xan bawa kaina wahala kan namiji, ni zama da kishiya ba bako bane a wurina, idan zai kara aure wallahi ni ban isa na hana ba, shi yake ganin haka babban tashin hankali ne, na taso naga gidanmu mata biyu ne haka yasa na sakawa raina duk inda aure ya kai ni tow akwai wata ko na samu wasu, amma wallahi ni ban ji kome ba!" "Ok me yasa kika kashe wayarki?" Murmushi nayi na ce mishi. "Nasan halinsa yanxu zai ta ƙoƙarin sai ya gamsar da ni akan yana da gaskiya, bayan ni nasan yana da gaskiya. Idan ya cika son sai ya min bayani zan iya jin behind the scenes yana yin wani abu ne, shi namiji ne ya kamata ya tsaya akan kafarshi. Ba laifi ba ne ya gaya min gaskiya amma bana son a kan kaina na yiwa Mijina kallon wanda ya kasa." " Na gamsu da maganarki amma ki kunna wayarki wallahi zai iya hana iyayenmu zaman lafiya sai ya saka su zo na gaya miki gaskiya idan kin yarda. " Kunna wayar nayi sai ga kiran ina dauka ya ce mishi. " Yanzu nake shirin kiran Datti da Daddah! " " Da kuwa baka kyauta." Nan muka shiga hira su Uncle Auta suka bar gidan, muna gama wayar na kashe, sai ga kiran Aunty Zakiyah, wai suna kofar gida na zo an hana su shigowa, haka na fita na shigo dasu, muka zube a parlourn, muka yi ta hira a dauko musu abinci suka ci, sannan muka yi sallah La'asar bayan nan ya kira ya ce." Ya nake jin muryan Yara sun iso ne?" Nace mishi eh , daga nan suka yi sallah, zan iya cewa daga nan muka shirya dai dare Ya Ado ya zo ya dauke su, ya bar mun Takwaran Mama,har da uniform dinta na makaranta.
Na ji dadi haka na cigaba da kula da gidan, sai dai duk lokacin da muke waya sai naji muryan Badr, kusan kamar da gangan yake zama kusa da ita. Kawai sai na sakawa raina matuƙar zan ji muryanta zan kashe wayar. Shima kuma ya gane idan zai yi waya da ni, sai dai ya bar inda take. Ya ce min ganin likita take amma da na bude data na ga hotonsu ana ta sakawa a status. Ba karamin ƙoƙari nayi da na danne zuciyata, na zuba mishi idanu. Har ya dawo cikin ikon Allah ranar juma'a, suka zo gidana ta nuna min ta fita da mijina, dauke kai nayi kamar ban san me yake mun zafi ba, amma na san yadda nake ji. Tunda na tarbe shi ban kara bin ta kanshi ba, sai dare na rufe kofana. Tunda ya kaita bai dawo ba sai sha biyu saura da ya dawo ya samu kofata a buɗe. Yayi bugun duniyar nan nayi kamar ban ji ba, washi gari ban fito ba sai karfe tara, na wuce kitchen yana parlourn yana karyawa. Nayi kamar ban ganshi ba. Wallahi ba zan iya hakuri akan wannan ba, domin yadda tayi ta min iskanci tana kallona tana dariya. Yafi kome yi min zafi. Ina tsaye ina fitar fa abincin jiya da bai ci ba, ya bar min na zuba musu ruwa, shigowa yayi ya ce min. "Jiya ni daya na kwana!" Shiru nayi domin abinda yake bakina idan na fada sai ya kusan suma, haka yasa na ciza bakina sai da ya fashe. Sake bakin nayi a hankali na wuce na hado kayan tea na daura a tunkaya.. "Lubabatu nayi wani abu ne?" Murmusa mishi nayi ina faɗin. "Me ya faru?" Na tambaye shi. "Amma naga kamar kina wani abu da ban saba gani ba ne." "Ok ba mamaki kai kake ganin haka;" na fada a takaice ina nufar inda tukwane suke, na wanke na juye miyar na dumama. Sannan na wuce na dauki plat da cokali na jera abincin da kome da kome, sannan na nufi hanyar waje ya amshi tiren na koma na juye ruwan zafin, na nufi parlourn na zauna a hankali na fara ci. Da cokali ɗaya. "Ina cokalina?" Kallonshi nayi sannan na ce mishi. "Wannan abincin ba zai ishe mu ba;" "kamar ya? Naga abincina na ne na jiya." "Ai ya koma na kowa da kowa!" Na fara ci a hankali fir na hana shi. "Wai meye matsalarki ne?" "Kai ne?!" Na bashi amsa, "kai ne matsalata idan ina da wata matsala kai ne. Idan zaka auri Badriyyah lafiya lau, amma kawo min ita ko zuwa ka zauna sai sha biyun dare wallahi ba zan yarda ba, kashe nayi maka yasa na rufe kofar gobe ka kara dawowa min gidan rufe shi zanyi.;" na mike xan tafi ya dawo da ni na zauna yana murmushi, "kishi haka lunah........ [12/21/2025, 3:54 PM] Maman Walid: 24 Ya fahimci raina a fusace yake kuma a kufule nake, sai ya fara cin abincin har ya cinye yana murmushi. " Babu wata mace da zata shigo min! " " Waye ya sani ita fa virgin ce ni kuma fa?" Rike bakina yayi yana faɗin. "Ba ruwana da Virgin ko rashinsa, ke nake so ba budurcinki ba, ke nake so ba fuskarki ba, ke naso ba wani abu ba, soyayyarki halitta ce daga Allah, zan so ki zan kaunace ki zan kuma kare ki, sannan zan hana ki kuka, zan saka ki murmushi da farin ciki, hannuna kawai zaki rike na cika wannan alƙawarin da na miki" kura mishi idanu nayi a hankali naji hawaye na zuba min zuciyana ya karaya, tsoron kada shima ya min halin Hafiz na fara kuka wiwi karshe na bar mishi parlourn zuwa dakina ina kuka. Shigowa dakin yayi ya same ni ina zaune sai kuka nake, durkusawa yayi a gabana. "Tsoron me kike ji?" Girgiza kai nayi ina shashekar kuka. " Yar uwarka ce, ni kuma bare, akwai lokacin da Alakar zuci baya tasiri sama da dangantaka. Idan ba zaka zauna da ni ba ka gaya min na tafi ka ji, don Allah kayi hakuri ka ce min na tafi wallahi." Wato wani irin rungume ni da yayi tare da buga bayana. "Shiiiiii" yayi ta fada min sannan ya janye ni a jikinshi yana share min hawaye. Murmushi yayi yana faɗin. "Kin yi kyau, ina ganin mace tana kuka bata kyay amma ke kuka kyau yake miki? Ji wannan hancin don Allah!" Wato ba iya rarrashi ya iya ba, hatta dauko wani abun da zai mantar da ni fushin da nake yi sai da ya raba ni da fushin, sannan ya janyo hannuna muka fita parlourn, wani abu da na fahimta tun kwanakin da muka yi na sati ɗaya a gidan, Malamina ba mutu me yawan shan ruwa bane, idan ka ga ya sha ruwa to bukatar haka ce ya taso mishi, kuma idan dai sha ruwan yana sha dayawan gaske ne yadda idan ja shiga hannunsa bana marmarin sake fadawa hannunsa, domin duk sauran kwanakin da yayi da ya dawo daga tafiya bai wani damu da ya fanshe su ba. Wannan abin sai ya tsaya min a rai na daura mishi ayar tambaya. Me yasa bai damu da ya bukace ni ba. Domin ban san cewa haka tashi halayyar yake ba, ranar haka muka kwana duk da ina son ya bukatar shi amma sai na lura kamar shi yafi bukatar hutu, don gefena can ya je ya kwanta. Kuma yana kwanciya sai barci. Ban iya barci ba daren nan haka nayi shi ina juyi domin na sha abubuwa wai irin miji zai dawo nan na gyara jikina. Sai dai kash babu abinda ya faru, tashi nayi a hankali na wuce dakina. Kusan kwana nayi ina juyi da naga abin ba zai kare ba, na tashi zuwa ban daki nayi alwala na fito, na gabatar da sallah nafilla, har dai da na fara jin barci na koma gado na kwanta.
Da asuba da ya farka ya ga bana dakin, sai da yayi wanka sannan ya shirya ya tafi masallaci, bai dawo ba sai da gari ya fara haske. A lokacin da ya shigo ya same ni akan abin sallah, ina azkar zama yayi na ga fuskarshi kamar akwai damuwa da gajiya ya kalle ni. Na shafa addu'a, na gaishe shi bai amsa ba, ni kuwa na share na tashi na fara nad'e abin sallah. Ina tsaye naji ya rungume ni ta baya yana faɗin.. "Matar Turaki, jiya sai da kika saka ni barci sannan kika gudu wai me nayi ne?" A hankali na janye daga rikon da yayi min na wuce inda nake ajiye abin sallah na ajiye sannan na cire hijab dina, na nad'e shi sannan na koma gadon na kwanta, kafin na ce mishi. "Ka je ka kwanta ka huta gajiya akwai gajiya a tare da kai." Murmushi yayi ya biyo ni gadon yana faɗin. "Ai a wurinki zan huce gajiyar Matar Turaki tana fushi da Turaki na shiga uku na!" Ban kula shi ba, haka ya haura gadon daga nan kuma sai da ya tabbatar da fushin da nake ya kare duk wani rigimar da nake ji ya tafi kamar kura akan iska, muka dulmiya juna cikin duniyar kaunar juna. Daga ranar bai kara yayi tafiya ya dawo ya nuna min ya gaji yayi ta barci ba, yana dawowa zai huce gajiyarshi da ni, ni kaina lokacin zamana da Hafiz nasan ba haka nake ba, amma a yanzu na zama wata yar iska irin dai matar da basu gajiya da tattaunawa cikin dare nan, kuma ai maganar gaskiya ni bazawara ce, ta wannan wurin ai ina da hadda har da tartil taya ga katon mutum a gidana za a ce nayi hakuri da shi, ko shi ba mutum ba ne. A bangaren family ɗinsu ba karamin uzurawa suka yi akan ya auri Badriyyah ba. Shi kuma da yake dan duniya ne ya ce ba zai aure ta ba, ko yanka namar shi ake ana gasawa ba zai aure ta ba.
Badriyyah tana da wanda yake sonta amma bakar jaraba ta hana kanta hango haka. ** Hafiz Tun baya da Turaki ya mishi shegen duka, ya bar Lagos ya dawo ya shirya da kyau, sai dai Me yana isowa Jama'are, ya samu labarin Karima ta zo ta kwashe Yaranta, wani abin tashin hankalin Yaran da yake ta zargin na shine ta ce a gaya masa Yaran ba nashi ba ne, Yaran da ta haifa na tsohon saurayin ta ne, sannan kada ya ce zai nime ta domin ba zai same ta ba. Kusan hauka ne Hafiz ne bai yi ba domin sai da aka daura shi a gadon asibiti, daga karshe aka tura su asibitin Bauchi domin abin kamar zai saka shi hauka, kafin aka shawo kan matsalar, tun da ya dawo hayacinsa ya tuna ya kashewa Lubnah bata mahaifarta bayan shine baya haihuwa, ya wulakanta Lubnah akan Yaran kai duk abinda yayi na mugunta sai gashi yana dawo mishi, haka zai zauna yayi ta kuka. Domin yasan yanzu kan Lubnah ta mishi nisa,Ita kanta Jalilah da ta fahimci Hafiz din da ta sani ba shi ne yanzu, sai ta fara niman hanyar da zata rabu da shi, ranar wata Alhamis bayan isha yana zaune ya zubawa tv idanu. Ta zo ta zauna da takarda da biro ta mika mishi. "Ina son ka sake ni, domin kaima kasan naka haihu ana aure don a hayayyafa ne kai kuwa baka da wannan damar." Murmushi yayi sannan ya ce mata."lokacin da nake tare da Lubnah kina daga cikin mutanen da suka yi ta zuga ni na rabu da ita? Na kara mata kishiya, nayi yadda nake so amma yau an wayi gari don bana haihuwa ki ce zaki rabu da ni? Ina soyayyar da kike min Wanda yasa kika gagara zama da mazankina baya? Yanzu bani da amfani zaki guje ni. Ai ba zan iya rabuwa da ke ba domin sai na fanshe sadakina sai na rabu da ke." "A'a Hafiz ni bance ka rabu da Lubnah ba!" Murmushi yayi ya bai kara magana ba, yana kallonta tare da nazarin abinda zai mata yadda zasu yi balance. Haka ta bar parlourn yayi ta nazarin, ya rasa Lubnah har abada, ya sani kashedin da Mijinta ya mata kaɗai ya razana shi amma ya zai yi? Yana son Lubnah ko wani hali yana son ya rabata da kwanciyar hankalin gidanta. Yana son ta fuskanci halin da yake ciki, amma yasan ko me zai yi ba zata tab'a dawowa gare shi ba. Amma kuma yana da hanyar da zai dawo da ita gare shi ko bata dawo ba itama ta fuskanci yadda yake ji. (Labarin Hafiz ko ba zance muku kai tsaye gaskiya ba ne, amma kuma akwai maza ire-irensu da suke ganin idan basu sami yadda suke so ba, gara ayi ragas kowa ya rasa, sannan idan suka ga mace ta samu nasara a Rayuwarta bayan rabuwa da su, sai su fara jin ciwo da bakin ciki burinsu su ga ta wulakanta. Allah yasa mu dace!) Amma kafin ya zo ga Lubnah sai ya fara ta kan Jalilah.
** Allah ya gani ta kowani fuska Ni da mijina muna samun zaman lafiya. Sai dai kuma yadda wasu abubuwan suke faruwa da barazanar da nake fuskanta yasa na gayawa Mama, murmushi tayi tana faɗin. "Ai ko na kwantar da hankalina, miji mata hudu ne shi, ba xai yiwu ki ce ba zai kara aure ba, idan kika ga haka shine maslaha ki kwantar da hankalinki, idan kuma kika fara fuskantar matsala ki min magana nazo na dauke ki." Sai na samu nutsuwa ko ba kome Mahaifyata tana tare da ni, ko sun yi magana da ita ne naga ya dan damu da zuba mishi idanu da nayi, har ya kai ni gidan Ya Ado na wuni sannan ya dawo da ni gida.
Sannan wani abu da na kara fahimta, mutum ne da ba zai yiwu ya boye maka kome ba, amma dan zaman da nayi da shi sai na hango mutane biyu da suke tare da shi, kusan kamar shine yake kulawa da su. Akwai wani abu da na kara yarda cewa mutum ne shi mai matuƙar kishi, hana Ubaidullah shigowa gidansa. Haka idan ka ga Uncle Auta a cikin gidan nan, tow abu me muhimmanci ne ko tare suke, tsakaninsa da Ubaidullah parlourn baki ni kuwa bana tab'a shiga domin kai tsaye ya gaya min, Ubaid da Uncle Auta, suna da tsalle shi kuma yana da kishi, idan ya wuce gaisuwa don Allah bai yarda na sake da su ba. Sannan idan baya gari duk abinda zasu kawo min iya waje zasu tsaya su bada a kawo min cikin gidan. Wannan yasa ko gidajensu ban cika zuwa mazan nan ba.
A watan da muka cika wata uku da aure ne, wata makociyar mu ta haihu. Suka gaya min da yake yar arewa ce. Matar Uncle Auta ta gaya min ta waya, yana dawowa daga Office bayan ya ci abinci na gaya mishi. Murmushi yayi ya ce min. "Ok sai kin dawo!" "Na gode sosai! Ai sai gobe zamu shiga gidan!" "Tow Allah ya kai mu!" "Amin Ya Allah!" Bayan ya gama cin abinci muka dawo parlourn ina jikinshi aka buga kofar gidan, kallon juna muka yi ya mike ya fita can sai gashi da Matar Ubaid, Maman Nihla. Zama tayi na tashi na kawo mata ruwa na ajiye mata. Sannan na koma dakina. Ban san me ya faru ba amma yadda take kuka da mishi bayani da fulatancin yasa na fahimci rigima ce. Kwanciya nayi na cigaba da abinda nake yi da nake da Aunty Hindatu. Muryan Ubaid na ji sama-sama, fada kamar zasu daku. Har sai da na fita don na ji maganar da hausa Mr Turaki yana faɗin. "Ai gaskiya ne akan me xan barka ka shigo min gida, bayan nasan waye kai, na san halinka matarka baka tsaya a kanta ba, baka Musulmi baka Kirista, me kake son cimma? Idan ba rashin mutunci da rashin arziki ba." Fitowa nayi suka juyawa zuwa gare ni. Allah yasa da hijab har kasa, "Me kika fito yi?" Ya daka min tsawa, juyawa nayi na koma dakin. "Ai na gaya maka ni matata sirrina ce, har abada ba zaka tab'a samun damar kare mata kallo na, kayi focus din matsalarka. Idan ka rungume matarka zaka fahimci nimar da Allah ya maka, ita Lubnah da kake cewa matarka tayi koyi da ita ka manta yadda muka yi da kai ne? Don Allah kada ka lalata min aurena domin ni ban shiga rayuwar gidajenku ba." Da haka na fahimci idan matar shi tayi mishi wani abu yake huce haushinsa akanta bata iya kome ba, ga Lubnah nan tana yin abinda ya dace a gidanta, dama ba shiri muke da ita ba, ashe Mijinta ya kara a abubuwan da zai kara dagula lissafin kome. Kawai sai naji zuciyata bata min dad'i ba...... [12/23/2025, 12:47 PM] Maman Walid: 25 Don haka suka gama rigimarsu, ya shigo zai min masifa na saka mishi kuka. Ganin yadda nake kukan da gaske sai ya rungume ni yana shafa baya har nayi shiru. "Dayawan mutanen da suke kusa da ni idanunsu akanki yake ni kuma kishi ne da ni kamar na cire zuciyata na fitar da shi waje. Ina sonki dayawa don da na kasa boye shi, sorry idan nayi kuskure ki yi hakuri kin ji!" A hankali na janye kaina daga jikinshi, zuwa yanzu na fara jin tausayinsa be mess with everyone domin ni. "Kin yi shiru?" "Tsoro nake ji, tsoron kada kishi ya cigaba da ruguza zamanmu!" Na faɗa ina shashekar kuka. Murmusa min yayi tare da rike hannuna, ya ce min. "Tabbas ina kishinki, ina kishin wasu mazan su kalle ki. Ina kishin idan na tuna duk tarin ni'imar da Allah ya miki kafin ni wani ya fara ɗanɗanawa ina ji kamar na mutu, a duk lokacin da na tuna Hafiz ya fara samun kusanci da ke kafin ni sai na ji ban cancanci haka daga kowacce fuska. Look ina da zafin kishi wallahi ina ji kamar ni ɗaya Allah ya halitta da kishinki." Ya d'ago kai yana kallona idanunsa sun jajjur murmushin karfin hali yayi kafin ya ce min. "Ina da kishi sosai!." A hankali na janye a jikinshi, na cigaba da kuka, zama yayi a kusa da ni yana faɗin. "Amma ba ina bin abinda zuciyata, ta saka ni ba ne,. Kawai abu daya na san ina yi shi ne kaurace miki, dole na ke saka kaina a tare da ke, nayi ƙoƙarin danne haka amma ina." Aure wata uku zuwa hudu yau Turaki yake gaya min yana kishina, kishin da yake yasa shi kaurace min? Kallon kasa nayi ta yi ina jin kamar zuciyata zata buga. A hankali na matsa daga kusa da shi na koma can gefe. Nayi shiru na rasa me zan yi na huce idan nace ya sake ni ma ba zai sake ni ba. Don haka nayi shiru ban kara magana ba, sai dai shi a lissafinshi ai ya fada min abinda yake ranshi ne, don na daina jin zafinsa, ni kuwa sai nake ganin gara mu rabu kowa ya kama gabanshi. Idan ba haka ba, a banza zan ta cuta da sunan kishin da yake ji da shi.