ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 12
ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 12: ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 12. Juyowa nayi a fusace amma kuma sai nayi ƙoƙarin gayyatar murmushi akan fuskana, na ce mata.…
4,231 words
Juyowa nayi a fusace amma kuma sai nayi ƙoƙarin gayyatar murmushi akan fuskana, na ce mata. "Na gode sosai, shima Arziki ne." Na barsu nan suka yi ta zagina da fadar wasu abubuwan da ni dai nasan iya shi ya sani wannan abin ya b'ata min rai, kofa ya dawo bai zo da mota kofar gidan ba, da kafa ya dawo jin hayaniyarsu yasa shi ya tsaya sai da ya ji me suke cewa ya shiga tare da zuba musu idanu. "Wai bana ce kada na ga kowacce mara kunya a gidana bane?" Ta tambaye su, bayan ya rufe gidan ya saka key a aljuhunsa ya nufi daki hango table din kaca-kaca, ya shigo ya same ni kwance, kuka nake son yi amma na danne. Zama yayi yana faɗin." Me ya kawo su gidan nan?" "Su da gidan dan uwansu, anan da kwanaki ita Badr ai amaryanka ce!" " Na sani amma me ya kawo su gidana?" Nan ne bani da amsar bashi nayi shiru. Tashi yayi ya nufi dakinsa ya shiga ya sauya kaya yadda ake buga kofar gidan nayi mamaki ashe tunda ya shigo suka ga ya shigo dakina ya zauna. Suka shiga kiran Iyayensu, ni dai ban ce kome iyayen suka yi ta buga gidan, amma ya fusata da ya fito da bulala a hannunsu ya tambaye su waye ya basu izinin zuwa gidansa? Suka nuna Badr, ya tambaye su waye ya basu izinin cin abincin da aka girka mishi, suka nuna ta. Murmushi yayi ya ce musu. "Gobe idan ta janyo ku, kada ku mata musu ku zo ni kuma zan tabbatar muku da cewa nayi rayuwa da kowani dan bariki!" Ya tara su wuri guda yayi ya zane su. Gajiya da ihun nayi na zo na fisge bulalar nayi na ce mishi. "Wannan ba zai hana su fasa abinda suka yi niyya ba, sannan ni ban ga wani fa'idar zane su ba domin ni kake janyowa kiyayya, don Allah ka bar kome ya wuce babu amfanin tashin hankali don Allah!" Na fada ina rike bulalar, sake min yayi ya nufi kofar ya bude yana faɗin. "Ni ban haifa ba balle ku ce nawa ne, ku rike Yaranku idan suka cigaba da shiga rayuwata zan gyara musu zama."
Haka yaran suka fita suna kuka, shi ko a jikinsa. Haka ya riko Badr yasa ta tattara abincin da suka bata ya juye mata a jakarta, me shegen tsada. Aikuwa bayan ya gama da su, ya biyo ni kitchen, sauran abincin da ban ci ba na bari a kitchen na saka mana cokali muka shiga ci muna hira, wayarshi ce tayi haske ya dauka ok naji ya ce, sai da muka gama sannan ya riko hannuna muka shirya muka fita tare. Gidan kakanshi muka nufa. Gabana ne ya fadi nasan tunda suka yi haka sai a hankali. Sai da aka fara magana na ga ya d'ago zai magana na rike hannunsa, ina kallonshi. Murmushi nayi ina faɗin. "Sanyi!" Ba karamin al'amari ya faru amma haka suka nuna nice da laifi ai kiransa nayi, ce min yayi. "Tashi Jasminah ta raka ki!" Kallon nayi ya ce min. "Jeki ba kome!" Haka muka nufi gidan muka barshi, tass ya wanke su tare da cewa ya dake su ko za a rama musu ne,ya daka gobe ma ya ga wata ta zo mishi ai shi kan ma ya gama zaman gidan. Sun zata wasa ne, sai dasuka ga ya bar parlourn, duk yadda dattijan nan suka so ya zauna yayi tsalle ya ce ba zai zauna ba, a ranar ya saka na hada wasu abubuwan muka bar gidan dama sanadi yake nima, sai kuma haka ya zo akan gabba, domin ba shi ya bar gidan da ra'ayinsa, mutanen gidan suka yi amfani da zuciyarshi domin ya bar gidan. Tabbas mun koma gidan mu a daren inda muka kwana a daki daya cike da damuwa shi fushi sosai yana faɗin me yasa naki gaya masa abinda ya faru, sai ya dauki fushi. Ni dai ban san yadda zanyi bayanin amarcin da na yi ba. Washi gari bayan ya fita, wurin karfe daya, aka ce ina da bako Adamu Jama'are. Cikin farin ciki, na ce a bashi ya shigo Yayana ne. Tunda na ji haka na wuce kitchen na hado mishi abin motsa baki, sai dai ji nayi kamar nasan muryan wanda ya shigo domin kuwa. Bai kama da na Ya Ado ba. A hankali na fito daga kitchen din, idanuna ne ya ɗauka akan na Hafiz. Ji nayi gabana ya buga kamar wanda zai fito waje. Idanuna suka cika da kwallah.. "Me kake nima a gidana!?" Takowa yayi na sake tiren hannuna, wukar da yake kan fruit na dauka ina nuna mishi. "Fita min a gidana!" Takowa yayi yana faɗin. "Ba zaki iya kome ba, ai na gaya miki ke tawa ce ba xaki tab'a tsare min ba." Ya rike wukar kamar wanda aka jefo shi haka ya shigo parlourn, wani irin daukar Hafiz yayi ta baya ya buga shi fa kasa, kishi ya rufe mishi idanu. Dukanshi yake kamar zai kashe shi, na rike shi ina faɗin. "Don Allah kada ka kashe shi!" Ture ni yayi na fadi akan hannun kujera. Shi kuwa Hafiz ganin yadda ya Turaki ya fita hayacinsa ya ce mishi. "Ai na gaya maka, indai ina raye ba zaka tab'a kasance da ita ba, bari ka ji sai da na taɓa kuma ita ta kira ni, shine na biyo ta. Kai baka isa ka ce zaka raba ni da ita ba, ko ka kashe ni nan Hafiz Ni ne mijinta wanda ya fara bude mata idanu!" Naushi ya kai mishi. "Don Allah ka kyale shi wallahi karya ne!" "Wallahi ba karya nake maka ba, ka duba wayarta da whatsp dinta da Email dinta, ni dai take bi." Wani irin kuka ne ya kwace min nayi ta kallonshi. "Allah ya isa Hafiz! Me yasa kake son lalata min rayuwata!" Kai mishi duka Turaki yayi a gabanshi sai da ya suma ya kalle ni. Kafin ya ja shi ya fitar da shi a gidan yayi wayawa yan sanda aka zo aka dauke shi. Ni kuwa madadin ya min magana sai ya saka kai ya bar gidan.
Haka na kwana na wuni, babu shi babu alamar shi, haka na kwanta washi gari. Mutumin nan baya nan, sai karfe biyu na yamma Ubaid da Matarshi suka kawo min ziyara, a bakinsa nake jin labarin business Trip din da yayi, haka na bawa kaina hakuri na shanye na cigaba da hakuri. Sai da ya shafe sati uku cib ranar na shiga gidan Uncle Auta. Na samu wani labarin wai ashe an d'ago da maganar aurenshi da badr, akan idanuna suke fadar zata shigo ta kwace mijinta.
Haka na fita na tafi gida, na kira Hindatu ina kuka, na gaya mata duk abinda yake faruwa. Nace mata. " Ni zan koma gidan Ya Ado ba ni da sa'a da aure!" Fada tayi min sosai sannan Aunty Hindatu ta shiga bude min sirrin zama yar bariki a gidan miji, sai nayi ta jin kunyar kuma maganar Allah gaskiya ta gaya min, haka muka yi sallama da ita, da safe Uncle Auta ya kawo min cefane, na yi girki don daga ganin haka nasan yana hanya, haka na shiga nayi aiki wurin sha biyu ya shigo gidan, kallo daya nayi mishi, na wuce na rufe kofar gidan na dauke key na saka a kitchen, sannan na gama abin da nake na shiga ban daki nayi wanka, wurin karfe daya da rabi na fito na daure da towel. Shigowa yayi na kalle shi fuskarshi a haɗe ga alamu yayi ya ce min. "Key nake bukata!" "Babu inda zaka sai ka gaya min me kake nufi da ni?" "Bani da lokacin magana bani key?" Ya nuna min hannu, gyara zaman towel din nayi na dauko baby oil dina na cigaba da shafawa a hankali cikin wani salon jan hankali. Yaki kallona, ne saboda baya son ya dauko amma kamar an ce ya d'ago kai idanunsa suka yi farin gani...... [12/19/2025, 9:58 AM] Maman Walid: 22 Da wani irin sauri ya dauke kai yana.. "Kin ga saura minti uku a shiga sallah ba ni!" Yana kallon yadda na mike, "Ya Ilahi." Ya furta a hankali, ya rasa me yake mishi dad'i. Turare na dauka nayi ta shafawa har aka shiga sallah, sannan na wuce na daki doguwar riga da abin sallah na shimfida mana na ce. "Zo ka jamu sallah, tunda na masallaci ya kwace maka!" Yadda nayi maganar a sanyayye tare da wata Ja'iran murya yasa shi, shiga gaban sallah. Haka ya jamu, amma zuciyarshi kamar ta fito don azabar karfin turaren nan dakyar yayi addu'a ya fita a dakin murmushi nayi ina bin shi da idanun. Oh dai.
Bayan na idar da addu'a, na nufi kofar dakinsa na buga, shiru yayi ya ki amsa min. Na kara buga kofar ina kiranshi. "Malammmmmmm!" Haka nayi ta bugawa har ya gaji ya buɗe, murmushi nayi mishi. "Food is ready!" Kallona yayi yana mamakin. "Ba zan ci ba!" Riko hannunshi nayi nace mishi. "Wallahi nan ne kan nace na zai yiwu ba, oya muje!" Na ja hannunsa, ina faɗin. "Oya muje ka ci abinci, ba zai yiwu a bani amanarka azo a ga wani abu ya same ka, na shiga uku ba." Na ja mishi kujera ya zauna sannan na shiga zuba mishi abinci kome daidai cikinsa. Sannan na ajiye mishi na saka cokali. "Ke yanzu baki ji kunyar kayan jikinki ba?" Kallon kaina nayi dress ne irin na yan makaranta, skirt da riga, ko gwiwa basu kai ba nace mishi. "Ina zan ji kunya tunda gidan mijina ne!" Na fada ina murmushi, tabbas yayi kewar abincinta, amma kuma fushin da yake da ita har yau ba daina jin zafi ba.
Sai da ya ci ya koshi sannan na bashi ruwa ya sha kafin ya mike. "Yawwa Goodluck;" na ce mishi sannan ya wuce abin dariya a fusace yayi tafiyarsa. Haka na gyara table din na kai kome kitchen, sannan na wuce dakina. Ina waya da Mama muka gaisa sosai har da Yadiko. Kafin muka yi sallama.. ina zaune wani idea ya fado min wata rigarshi na dauka na saka, yau ko da karfi sai mun shirya wallahi na gaji. Ni ko labarin Hafiz ban kara ji ba, ina zaune ina karanta wasikar jaki ya shigo ya shirya zai fita ya ce min." Bani key zan je KUMO FAMILY MANSION!" "Sai gobe yau lokacina Better go to your room, babu inda zaka na gaya maka." Daga haka na cigaba da wasa da kafana. Sake baki yayi yana kallon yadda take mishi tsirfa kala-kala. Abin ya bashi mamaki. Haka ya koma dakinsa can naji ana buga min kofar gida kofar na je na tsaya ya zuba min idanu ganin Hijab har kasa na ce. "Waye?" "Uncle Auta ne " aka bani amsa. "Ai sannu me kake bukata?" "Wurin Turaki na zo!" "Ayya sai dai gobe amma yau turaki nawa ne ni ɗaya." "Ki yi hakuri ki bani aronsa." "Ina ka je kawai da ya tafi har tsawon sati uku ka tambaye ni ya gama amarci ko bai gama ba, amma haka na zuba mishi idanun don haka sai ya biya kwanakin da yayi baya tare da ni wuce wurin Maman Daddah kafin na kira ta na gaya mata kun fara niman sabin yan mata!" "Tow haka abin ya koma!" Ya juya yana faɗin haka juyawa nayi na kalle shi yana rike da hularshi. Cike da mamaki yake bina da kallo. "Kayi lokacinka yanzu nawa ne!" Na wuce dakina.
Fitowa yayi da sauri daga ban daki, jin yadda aka shiga sallah, ya sa shi kara nufar kofa a zafaffe domin yana tsoron kada ta kara sashi rasa sallah Asr kamar yadda ya rasa ta Dhur, sai dai kash kicibs suka yi da ita cikin hargitsetsan yanayi da yake kara karayar mishi da wasu kwarin gwiwa da yake da shi, kin kallonta yayi domin haka na iya Dragging dinsa into wani part da bai shiryawa ba, cikin makirin muryanta da rabonsa da ya ji muryan kusan sati uku kenan, ta ce mishi. "Malammmmmmmmm!" Jin wani abu yayi ya tsaya a tsakiyar kansa ban da ita da tasan tasirin da muryanta yake da shi, da ba zata tab'a kiranshi da wannan yanayin ba, hade rai yayi ya cigaba da tafiya don baya son ya kara kallonta ba tare da ya nufi masallaci ba, ada idan aka ce mishi mata dangin shaidan ne baya tab'a amincewa, dawowarta gida yau a karo na biyu ya amince ita din tafi kowa sanin hanyar da zata kashe shi, kafin ya gama tunani ta kara cewa. "Malammmmmmmm yunwa nake ji!" Raka'a na biyu da aka kai ya saka shi dafe goshinsa tare da watsa mata harara, ai kuwa ta shiga buga kafarta. "Shi kenan kamar yadda ta min dazun ta kara yanzu dole nayi sallah a gida " ya rasa yadda zai yi da ita tare suka ci abinci amma yanzu tana kara mishi wani abu wai yunwa take ji. Zuba mata idanun yayi ya juya zai tafi, na bi bayansa har dakin ya shimfida abin sallah, nima na fito naje nayi alwala na dawo dakin na samu ya fara bin bayanshi nayi muka yi sallah tare. "Yunwa nake ji!" Na fada a hankali ina matsawa kusa da shi. "Malammmmmmm!" Juyowa yayi ya rufe min bakina. "Naji!" Tashi nayi a hankali zan fita daga cikin dakin ya ce min. Na yarda so halitta ce, ya ratsa zuciyata, amma ba zan jure abinda ya faru ba , ki min bayani Lulu... ina sauraronki ya aka yi Hafiz ya zo gidan nan?" Murmushi nayi tare da zuwa na zauna a gabanshi, hannuna na kai gaban rigarshi na shiga balle bottom din. Bai hana ni ba sai ma kallona yake. "You like it?" Gyada kai nayi a hankali ya cire rigar tarin kwanji da tsokoki suka bayana. Daga nan labarin ya sauya, wasu abubuwan dai sirrin Turaki ne da ni, domin na fahimci wata rayuwar daban take da lissafin mai karatu, shi bako ne a bangaren, yayinda ni yar gari na kasancewa wacce take rayuwa a wani bangare na garin, kamar yadda ake cewa mata suna suka tara haka ma mazan suna suka tara, a daren nan namiji gwarzon mijina, y goge min hadda bakiɗaya ya bude kaina ya zuba min nashi iya nashi shi dayansa. Ya daura ni a lissafinsa wanda iya ni kaɗai ya daurawa, akwai rana mai matuƙar daraja irin wannan ranar? Akwai wata rayuwa mai dadi irin wannan rayuwar? Mutumin nan ya wanke min duk wani abinda nake ji ko nake gani. Mutumin nan ya dasa min so da kaunarshi tare da buƙatarshi a kodayaushe.
Sai bayan kome ya lafa ya kara rungume, yana shafa bayana kamar za a kwace mishi ni! "Thank you Lunah!" Kwantar da kaina nayi a kirjinsa, ina jin wani irin yanayi yana ratsa tsakaninmu. Mun fi awa a makale da juna, kafin ya tashi ya haɗa mana ruwan wanka, kin shiga mu yi nayi amma haka ya tilasta min na shiga muka yi wankar muka fito. Kunyarshi kuma sai ya cika ni, riga da wandonsa ya dauko min na saka, ya gyara gadon ina kallonshi. Bayan ya gama ya janyo ni jikinshi muka kara kwanciya, kanshi ya daura a kirjina, na rungume shi. Furfura kanshi na kai hannuna ina tsige su ya ce min.. "Kin ga furfura ko? lokacin da na ganki ina talatin da wani abu, yau gani ina bawa arba'in baya, tunda kika amince kika aure ni, zan gaya miki, ina da lafiyar da zan jiyar dake farin ciki a ranan da muka kasance! kawai ki kaunace ni ki bar jin kunyana domin ni bani da kunyar!" Tabbas bai da kunya, amma sai na tsinci kaina da kasa magana na cigaba da wasa da gashin kanshi. Ina murmushi da jin wani farin ciki a raina ya ce min. "Ki ce min wani abu? ina jiran kalmanki ko da ta a'a ce." Murmushi nayi ya d'ago kai yana kallona, wani irin tartsatsin kauna nake hangowa a cikin idanunsa. He like me, sama da yadda nake tsammani. Chakulkuli ya fara min nayi ta kaucewa, daga karshe yayi nasarar daukata ya daura ni akan kafarshi yana faɗin. "Shi yaren soyayya ba ruwansa da yare ko kabila, ba ruwanshi da jinsi mace ko namiji, shi wata halitta ce da take wanzuwa cikin zukatan masoya imma mutane imma wasu halittun na daban, ya kike fahimci haka? Ni na fahimci haka ne lokacin da na hadu da ke." Akwai wani irin dad'i da nutswa idan ka ji namiji yana fitar da abinda yake ransa. "Ina sonka Malam, sai dai ina tsoron kada ka juya min baya, ina tsoron kada ina murnan na rabu da Hafiz!" Rufe min baki yayi yana girgixa min kai. "Allah ya min tsari na zama kamar Hafiz Allah ya rufa min asiri na zama irin Hafiz, Ubangiji ya hanani ranar da zan zama kamar Hafiz. Kai Allah ya nuna min mutuwata sama da ranar da zan ga na zalunci matar da nake aure ba." Kifa kaina nayi a goshinsa na ce mishi. "Na gode!". " Me yasa kike godiya! " " Ai kai mutumin kirki ne kuma me cika alkawari ne, shi yasa nake maka godiya domin zaka cika alkawarin da ka ɗauka. "
Haka kawai na zauna ayi min sakiyar da ba ruwa, mijina yana sona nima ina son mijina, akan me zan bar wani ya shiga tsakaninmu, a ranar duk a gida yayi salollin, wurin karfe tara aka buga gidan ya kalle ni, murmushi nayi na nufi kitchen na dauko key na mika mishi. Ya je ya bude Kofar. " Ka fito daga prison kenan?". Murmushi yayi sannan ya amshi ledar kafin ya kara magana ya banko kofar, Uncle Auta ya ce mishi." Ni ka wulakanta?". " Sorry Uncle!" Wato mu fa sai yau muke cin kazar amarci, muka ci muka yi nak, sannan muka baje a parlourn muna hira da kallon wani film.
Daren ranar dai dayawa zasu so jin labarin amma kuma, ai lamarin Babba ne fa. Domin ni kaina sai da naji kamar na gudu mutumin nan wayo ne da shi, amma kuma duk abinda zai yi tausayi yake ba ni domin ya jima bai yi auren ba, ni kuma sai na mishi uziri, sai da muka kwashe sati daya cib sannan ya fara zuwa office shima din dakyar na lallaba shi, har da cewa Uncle Auta da Ubaid zasu mishi dariya ya ce musu sai ya rama min kwanakin da baya nan, riko shi nayi nace mishi. " Wato bazani kayi kana gaya musu sai yanzu muke amarci! " " Ai ke kika gaya musu! " Zare idanun nayi na ce mishi." When?" " Kin manta kenan. " Yana tuna mun ranar na ji kunya ta kama ni da gudu zan fita ya riko hannuna. " Ban da gudu don Allah!" Kaina na daura a kirjinsa ina murmushi. "Kin yi kyau kullum kara kyau kike min!" Ya fada min wata katuwa magana a kunnena, kunya ta sa na kifa kaina ina faɗin. "Yaushe zaka fara jin kunya?" "Hala ranar da tsufa ya cimma ni!" Girgiza kai nayi na raka shi har wajen sannan ya shiga mota ta bar gidan nima na dawo parlourn, tunda na dawo na shiga aikina, karfe uku saura na wuce lokacin na kusan gama hada sobo, da yake yace zai zo da baki tuwan shinkafa miyar Egusi nayi, ina ta aiki na ji an buga gidan na zata shi ne ina zuwa na bude Matar Uncle Auta da Ubaid sai wasu mata biyu da yan mata uku. Murmushi nayi na ce musu.." Barkanku da zuwa ku shigo!" Na wuce kitchen na kawo musu ruwa. Na juya zan tafi na ji daya tana faɗin. "Dazun na ga posting din wata arewa dairy wai Yan Bauchi suna da rowa, basu iya baka kyauta daga ruwa sai ruwa." Murmushi nayi na wuce kitchen, na hado musu snacks da nayi na karban baki na fito musu da shi, sai lokacin juna suke. Na koma na hada abinci a kula guda, sannan na kawo musu na ce musu. "Don Allah ku yi serve kanku, bari na sauya kaya." Na koma dakina na watsa ruwa na sauya kayan jikina, ina kasa kunnena ko zanji dirin motarshi, amma ina sai ji nayi yana gaisawa da matan, kafin ya shigo dakin.. "ina ta son na maka oyoyo!" Zungure min goshi yayi yana faɗin. "Kin san dai da baki zan zo!" Na dauko wata hijab dina har kasa na daura akan riga da zanin da yake jikina. "Kina kyau da riga da zani." Haka ya riko hannuna ya ce min. "Waye dai taya ni shiryawa?" "Muje na gaishe su sai na raka ka, ka sauya kayan ko?" Haka muka yi na fito na gaishe su, sannan na cewa Matar Uncle Auta da Ubaid. "Kuci abinci!" Na raka shi dakinsa, ya watsa ruwa ina tsaye na fito mishi da wasu kananun kaya, ya saka sannan ya saka turare na riko hannunshi,. Muka fito a lokacin da su Uncle Auta da Ubaid suka shigo gidan, ashe matan biyun nan mazajensu ne da Yaransu, haka mazan suka koma dinner table, su kuma matan suka zauna a parlourn na koma kitchen na yi ta fito da kayan abinci, shi kuma yana karba idan na kawo sai ya sumbaci hannuna, ko ya ce min. "Sannu da ƙoƙari!" Ina kawowa zai sumbaci goshina. "Allah ya miki sakayya da gidan Aljanna!" "Amarya ko Falisha zata taya ki ne?" Inji daya matar. "A'a mu yan Bauchi, mun iya aiki da kanmu ko Malam?" Gyada min kai yayi bayan mun gama na wuce kitchen, sai gashi ya biyo ni da abincinsa. Ajiye min abincin yayi. Ya saba muci tare don haka na wanke hannu ya zauna a kan wani kujeran kitchen din nima haka, muka shiga ci tare. "Wani abu ya faru ne?" Ya tambaye ni bayan na tura mishi loma. "A'a babu abinda ya faru!" "Akwai mana baby gaya min." Murmushi nayi nace mishi. "Zance ne irin namu na mata." Gyada min kai yayi yana kallon yadda nayi ta tura mishi abinci, sai da muka gama ya wanke hannu ya taya ni wanke kwanon, muka fito ina cewa. "Dauko tissue please! " Wurin cin abincin ya nufa Uncle Auta ya ce masa. " Sai ka gaya mana matarka ce ta baka abinci a baki!" "Kai dai da baka iya romantic ba, a barwa newly couples kayansu!" Ya tawo lokacin har na shigo parlourn, yana zuwa ya mika min. Na amsa tare da goge mishi ina faɗin.. "Malam gashin baki da kasumbar nan suna bukatar gyara fa." Na faɗa kasa kasa. "Tow idan suka tafi ba sai ki gaya min ba, ai tun jiya nake bin ki, amma kika share ni." "Ok bari mu sallami baki!" Na fada ya koma wurin mazan. "Duk wannan soyayyar kafin a haihu ne idan aka haihu shi kenan sai ya zama tarihi." Murmushi matar Uncle Auta tayi ta ce mata . "Da don haihuwa ne, da tuni ya tara goma na yara. Kauna ce dai da bata tsufa ba, sannan bana jin idan zasu cika gidan nan da Yara zai fasa wannan halin shi ba bafulatani ziryan bane kuma ba bahaushe ba ne da mace na fara haihuwa zai zuba mata yaran ta ji dasu shi ruwa biyu ne....... [12/19/2025, 8:05 PM] Maman Walid: 23
"Mu kanmu mun yarda ƙabilar uwarsa tayi tasiri akanshi. Yadda ya iya jiranta ta dawo gare shi." Sai duk suka yi shiru, kasancewarta Babba a tsakaninmu sannan muna bata girmanta daidai gwargwado.
Tun da fadi haka bata kara magana ba, sai ta yi shiru,sai dai na fahimci wani abu a nan shine matar Ubaid kamar ban mata ba, da farko na zata matar Uncle Auta ne take min kallon gani gani amma daga bayan zuwan waɗanan matan sai ja lura da yadda Matar Ubaid take bina da idanu. Bayan tafiyarsu na gyara parlourn na tattara wanke-wanke, ya rungume ni ta baya yana me taya ni wanke -wanke. "Maza biyu da suka zo nan Alhaji Ahmed da Alhaji Mohammed, abokan kasuwancin Papa ne, Alhaji Mohammed yana Cotonou da iyalinsa, shi kuma Alhaji Ahmed yana abuja, tagwaye ne su." Gyada kai nayi na juya ina fuskarshi. "Su ma wadancan tsalla tsalla yan mata da suka zo da su dama an shirya proposal ne ban sani ba?" "Ni waye ya gaya miki an shirya haka?" "Amma ai a bakinsu naji ana cewa yana Bauchi na da rowa!" "Wallahi ni ban fadi haka ba sai dai ko su." Dan dagalgala nayi tare da sumbatar goshinsa ya saka hannu ya dauke ni cak, na sumbaci goshin sannan ya sauke ni na ce mishi. "Ina ga sai na fara saka maka abu domin na lura family dinka basu da buri da ya wuce su ga an yi min karin wata mace!"na juya na na zabga mishi mintsini. " Na gaya maka wannan shine kashedina da kai wata mace sai na fille maka kai!" " Tow ranki shi dade!" Haka ya fada yana dariya, a tare muka gama wanke kayan muka gyara kitchen din tas sannan ya riko hannuna zuwa parlourn nan ma muka gyara wannan na fito na samu yana jirana. Bude min hannu nayi na shiga da sauri ina sauke ajiyar zuciya. "Ina sonka dayawa!" " Ok bani labarin ranar kika fara sona!" Biye mishi nayi muka yi ta hira shi kuma ya zuba min idanun ina bashi labari ina dariya ko ina farin ciki.