ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 11
ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 11: ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 11. Yana sonta yana kaunarta amma baya son ta ga kamar don jikinta, baya son ta ga kamar bai da…
4,158 words
Yana sonta yana kaunarta amma baya son ta ga kamar don jikinta, baya son ta ga kamar bai da hakuri akanta. Ko dama can yana kwadayinta ne. Zama ya kara yi ya daura kafa daya akan ɗaya, ya janyo ni jikinshi. Haka yasa na daura kaina a kafad'arshi. Murmushi yayi. "Na jima ina addu'ar wannan ranar, yau ni ne Matata ta daura kanta a kafadana! Alhamdulillahi alakulli halin." Ya furta yana murmushi, ina gama sha ya amshi kofin ya fita da shi, can ya dawo ya kashe wutar dakin, sannan ya zo ya riko hannuna muka kwanta. Janyo ni yayi kan pillow shi, ya kuma ja bargo ya rufe mu, ya ce min. "Ki yi barci domin nima barci zan yi!" Daga haka na sauke ajiyar zuciya, "ki yi barci hankalinki kwance domin kina tare da Mijinki ne." Gyara kwanciya zan yi ya gyara min tare da daura kaina a kirjinsa. "This is your place, wurin naki ne ke ɗaya!" A hankali ya cigaba da shafa bayana, tun ina jin wani irin yanayi har barci yayi gaba da ni, sosai wunin ranar muka yi barci, da alamu kowa ma yasan cewa muna hutuwa, karfe daya na rana muka tashi saboda yadda ake buga kofar gidan daga waje, sake lumshe idanuna nayi na bude a hankali, zame jikina nayi daga nashi na nufi ban daki fitsari nayi sannan na wuce waje bayan na saka doguwar hijab har kasa, bude kofar nayi yan matan nan ne, na zuba musu idanu. Ban ce musu kalla ba, sai jin shi nayi ya rungume ni ta baya."uban me kuka zo yi?" Hannunsa ya sakalo shi ta kan cikina. Daura nawa hannun nayi akan nashi. "Maybe sun zo ganin wuri ne, su shigo mana!" Na fada ina juyawa cikin gidan. "Before na je na dawo na ga wata Yarinya sai na mata rashin mutunci." Ya fada tare da banke kofar, ai kuwa bamm kofar tayi kara. Wato shi dai kome na shi daban ne. Kitchen na nufa ya biyo ni, cire hijab din yayi yana faɗin. "Yanzu da zance mu yi wanka!" Rufe mishi baki nayi da hannuna ya shiga sumbatar hannun na kwace ina faɗin. "Me yasa baka jin nauyi ne?" Kallon sama yayi kafin ya kalli gefe da gefe yana niman wani abu can ya ce min. "Nauyin wa zanji? Naki?" Ya nuna ni da yatsa sai kuma ya janyo ni yana faɗin. "Gaya min yadda ake jin kunya sai na fara akanki?" Na jima ban ga tantiri irin wannan mutumin ba. "Ina wayata take ne ma? Na ji su Aunty Innah zasu shigo ne?" "Eh kai zasu shigo da karfe biyar na yamma." Sake baki nayi na ce mishi. "Au kasan da haka daman?" Na tambaye shi, jingina yayi da wall din kitchen din, yana faɗin. "Eh kai na sani hala sai kuma ki yi kuka?" Ya fada yana jan hannuna zuwa waje dakin da nake tsammanin shine nawa ya kai ni, ya ce min." Ki yi wanka ga Ni nan zuwa." Ban daki na wuce nayi wanka da alwala, sannan na fito ina daure da towel, shigowa yayi sai kuma ya juya ganin nima na diririce, ai kuwa yana fita na yi maza na saka kayana, sannan na fito na same shi yana tsaye, murmushi yayi min ya ce. "Muje mu yi sallah." Haka na bishi har dakinsa, muka yi sallah. A lokacin yunwa ya dame ni. Riko hannuna yayi muka bar gidan bayan na koma dakin na gyara fuskana, hannuna cikin nashi muka isa har gidan kakanshi, tun da muka shiga ake min sannu har na samu wuri na zauna ina gaishe su, abinci aka kawo mana na ji yana ta fulatanci, ai kuwa Daddah ta rufe shi da fada aka shiga kawo min abinci, kafin wani lokaci an cika min gabana da abin karyawa. "Kayi hakuri Turaki bata jin magana ashe haka ya barka da yunwa har yanzu." Murmushi nayi ina kallonshi, hada min abin karyawa yayi ya mika min tea din na fara sha, da zafi na ajiye mishi ina hura bakina. Dauka yayi yana d'aga min har yayi huce na dauka na fara sha ina murmushi. "Sha Chika!" Haka na karya shima ya ci kaɗan, kusan sai da naci na bar mishi sannan ya ci. Ganin yadda na zaɓi wasu abubuwan wasu kuma na bari ya sake murmushi yana faɗin " kina loss weight ko?" Ci yayi yana faɗin "cigaba da rage kiba, kin ga ni na ci Abinda kika bari ina laifi." Haka muka gama sannan aka kwashe ya riko hannuna muka tafi dakin da Kakarshi ta wurin Uwa take, ina shiga ta rungume ni tana faɗin. "Labubu kin ji sauki kenan?" Gyada mata kai nayi ya ce mata. "Granny meye matsalarki da ni yanzu bayan na yi aure kina min kallon banza ko kishi kike ne don nake na yi ba?" "Allah ya rufa min asiri." Ta fada tana buga mishi sanda ya kauce yana dariya sannan ya fita ya barmu a dakin, mun sha hira da ita kafin ta ke gaya min "an jima zamu koma gida ma yaushe zaki zo mana!" Murmushi nayi na ce mata "Sai ya kawo ni!" Haka muka yi ta hira jife-jife har na tayata hada kayanta, ta dauko kudi me yawa ta bani, nayi ta Godiya. Shigowa yayi ya ce mata. "Ki fito gashi an zo ɗaukarki!" Ai kuwa na rakota zuwa waje, a lokacin suke gaisawa da sauran mutanen gidan, haka ya rakata har wurin motar ta kira ni. A hankali na isa wurinta na tsaya, riko hannuna tayi ta saka min abu a cikin hannuna. " Ki kula da Mijinki da kyau, ki kuma kula da kanki." Ta rike hannuna alamar tana bani abu me muhimmanci, sannan ta sake hannuna yazo gefena ya rufe mata kofa yana faɗin. "Granny yarinyar nan ta kwace min ke!" Murmushi tayi tana faɗin. "Ka taimake ni ka rike musu yar mutane!" "In sha Allah!" Ya fada, bayan ya ja hannuna baya, suka tashi motar suka bar gidan, yana d'aga musu hannu. Sannan ya mai da ni can parlourn Alhaji ELYakub Kumo, muka zauna a rough carpet din parlourn, mika min wani album yana faɗin. "Wannan hoton zuriarki ne!" Amsa Yayi ya mika min, a hankali na fara bude shafi zuwa shafi. Hoton Babanshi ne na farko ya matso kusa da ni. "Wannan shine Papa!" Juyawa nayi ina kallonshi. "Kuna kama!" Bakin shi na ji a kan hancina. "Sosai kai!" Ya fada bayan ya sumbaci hanci. Sosai ya matso kusa da ni, kamar zai boye ni a jikinsa. Wani hoto na bude, hoton Mamanshi ce. " Mammy ko?" " Ya aka yi kika san Mammy nake kiranta?" Ya fada yana sumbatar kuncina. " Bari mana Chairman yana nan fa?" "Tuni ua gudu parlourn wurin Matarshi." Da mamaki na kalli wurin da yake babu alamar shi. Gira ya d'aga min. "Ai na gaya miki, ni lamarina mai karfi ne!" Tura baki nayi, yayi maza ya rike bakin da yatsarsa guda biyu. "I like this lips!" Ya fada yana sakewa. "Kika kara tura min baki sai na ciza!" Hoton bikinsu ba buɗe. "Lokacin ina zero kafin na zama plus." Shi dai bai da kunya ya more, ture shi nayi ina hararansa. "Me yasa kake da matsala?" "Saboda ni ne gidan haya!" Murmushi nayi ya kai hannunsa yana tab'a ni, "don Allah kada ka hanani kallon!" Ihun da muka jiyo a waje yasa muka kalli juna sannan muka kalli kofar, Badriyyah ce sanye da wasu kananan kaya a jikinta. "Idan ka ce ba zaka aure ni ba it's ok, but ka auri wannan karuwan yafi kome disguise a cikin wannan Familyn wallahi sai na kashe ka na kashe ta, sannan na kashe kaina. " Ya fada tana nuna mu da wuka. Mikawa yayi ya nufe ta, ta fasa ihu tana faɗin. " Kada ka matso kusada ni" ta fada da karfi zata yanka hannuna, kafin ta d'ago daga kallon inda ya dace ta yanka ya rike hannunta. " I don't care idan kika min wani abu, kuskuren da kika yi shine involved din Matar turaki cikin lamarin shine kuskurenki!" kwaɗa mata mari sai da ta sake fitsari, ai wannan katakon hannun nashi nasan za ayi haka.......... [12/18/2025, 3:54 PM] Maman Walid: 20 " Bilal kashe ta zaka yi?" Inji Uwarta, ta fada da hargowa. Bawan Allah nan ya shafawa idanunsa toka yana faɗin. " Kika sake riko wani abu da sunan matata don ubanki sai na binne ki da ranki ina wasa da ke? Mara kunya ni nayi maka da wadancan sakarkarun da suke bin ki ne? Na kara ganinki da sunan kin zo gidana ko wurin Matata da sunan hauka sai na rufe tarihinki!" Ya hankad'a ta can, t faɗi tana kuka. Kallon Uwarta yayi ya ce mata. "Ba ita ba ke kanki, ki fita idanuna wallahi idan wani abu ya samu matata sai na baku mamaki." Ya dawo inda nake ya zauna ya barsu da bakin ciki kallonshi nayi ya sake murmushi. "Yi kallonki kin ji ai namiji na gefenki babu karen da ya isa ya miki haushi na kyale shi." Ya fada yana rike min habba na. Sai da suka fita ya ce min. "Lubabatu?!" Na sha mamaki da ya kira sunana domin bai taɓa yin haka ba. " Dangina ne, kada ki rena min su. Zan yi iyakar kokarina na ga sun miki adalci. Tun ina yaro na taso bama shiri da su, sai Uncle Auta." Murmushi yayi ya kwanta tare da daura kanshi a cinyata yana faɗin. "Ina kewar Mammy sosai!" "Papa fa?" "Not yet!" Kallonshi nayi na tuna abinda Granny ta gaya min, wato ba iya fusata yake da kowa hatta mahaifinsa bai bari ba, Innalillahi wainnalihir rajoun, wallahi sai naji ya ban tausayi. "Papa ya bata abubuwa dayawa." "Bai bani ba, ya bani ya kwace je betrayal me." Sai na rasa bakin magana, nayi shiru lokacin da aurena ya mutu Abba fushi yayi da ni ya kuma zare hannunsa a kaina, a lokacin ni kaɗai nasan yadda nake rayuwa. Ganina ake but ina matukar shiga damuwa. Dakyar ya fara amsa gaisuwar da nake mishi. Shafa kanshi nayi na ce mishi. "Ba kyau fushi da iyaye! Kowani irin Yanayi zaka tsinci kanka kada kayi fushi da su, ba ina son na ce kayi hakuri ba ne, amma ina son na tuna maka hakkinsu akanka ne. " Wato akwai wani abu da na fahimta a rayuwa ba zuwa Islamiyya ka haddace kur'ani ake buƙata ba, yaro ya san waye Allah da hakkin Allah shine ake bukata, sannan yasan soyayyar Allah da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, kafin ahalul Baitu da Sahabbai, har zuwa kan iyaye. Mafi kololuwar daraja na wannan matakai uku ne, kafin zuwa ga Iyaye. Shafa kanshi nayi ina jin tausayinsa har cikin raina, duk yadda aka yi yana da trauma akan Iyayensa. Hawaye ne ya shiga zubowa daga idanuna yana d'iga akan fuskarshi. "Me kuma aka yi?" "Ba kyau fushi da iyaye!" Cike da mamaki yake kallona bayan ya tashi zaune. "Me ya kai ki personal life dina?" Rike hannunsa nayi, kuka na saka mishi.. "ka janye fushinka akan Mahaifinka ba haka yake bukata ba!" Zuba min idanu yayi ina iya hango yadda fuskarshi tayi ja. "Ke idan aka miki haka zaki ji dadi? Ko da yake kema ai kin yi min karya na rashin gaya min baki da aure me yasa rayuwarku take cike da karerayi ne?" Kallonshi nake na kai hannu zan rike shi ta kwace hannun. "Na gaya miki gaskiya, kada ki kara tab'a ni! Kannena uku da mahaifiyata hudu suka mutu bai iya kiran Makarantar ya gaya min ba, ya boye min haka bai ishe shi ba sai dawowa nayi na samu yayi adding another wife, gaya min me kike so nayi?" Baya na ja musamman yadda ya hayayyako min, na kara fashewa da kuka. "Matar da ya aura sakatariyar Mahaifiyata ce, taya ba zan tsane shi ba waye ya sani ko sun kashe mahaifiyata ne don su cigaba da abin!" Da sauri na kai hannuna bakinshi. "Allah yana ganinka kada ka yi mishi kazafi, kada ka tozarta shi. Sadauki ne da yayi kokarin baka kyakyawar rayuwa. Yayi maka adalci ta hanyar ka fuskanci abinda yake gabanka. Bai d'aga maka hankali ba sai da ya tabbata ka sami abinda yake ganin zai gyara maka gobenka, iya adalci ya maka ya maka adalci bai lalata mutuncinsa da kimarsa ba, ya aurota duk da bata addininsa da ta same ka ta amince da addininsa, ta kuma zauna da shi ba tare da ta hango gazawarshi ba, shi din jarumi ne da babu irinsa har ya koma ga Allah yana son ya zauna da kai ya fahimtar da kai waye shi, ya gaya maka yadda yake jin ka. Amma baka fahimce shi ba. Yayi kuskure wurin auren yar dakinta amma kuma rabon Jasminah kike tsammanin bai isa ya dauki rayuwarta ba ne." Rike hannunsa nayi tare da matsawa kuwa da shi, kafin na rungume shi ina kuka. Na janyo kanshi na rungumar a kirjina ina shafa bayansa. " Nasan anyi maka laifi amma kada hukunta shi ta haka, wata rana kai Uba ne da sannu zaka fahimci me yasa iyaye suke hakura da wani abu domin Yaransu. Zaka gano yadda suke tsoron kare yaransu daga wani abin da zai shafi bayansu. Wallahi ban tab'a ganin jarumin Uba irin Papa ba je did him best to protect you! Kuma har yana kan kare ka, ya cusa maka kiyayyarshi domin ka zama dodonsu, kuma yayi haka ne domin ka tsaya da kanka. Yaki nuna maka soyayya domin kada ya saka maka soyayya da kawazuci kamar yadda Mammy tayi yake damunka, ba nan kulawarsa ya tsaya ba, ya bude maka idanunka ka fahimci mutanen da suke zagaye da kai, ya cusa maka niman na kanka domin kada ka jira abinda Mammy da shi suka tara maka. Idan har haka dai saka na zama Uwa ta gari zan yi tsalle na rungume wannan halin nashi. Domin ya nuna min ba koda yaushe ake tafiya a yadda ake so ba." Kai ya d'ago yana kallona da idanunsa da suka yi jajjur, ga Daddah a kofar shiga parlourn. " Dubi ka ga mahaifiyarsa ce, kalli yadda take kuka danta ne fa, and kasan yadda take ɗaukar abin a ranta? Kasan yadda Uwa take girmama me kaunar danta? Balle kai son da take yiwa mahaifinka ya shafe ka, shafar da takai har ta rufe idanun ta ki yarda da shi ta baka dukar yarda. Kaf duniya ita ta san waye danta. Wadanda bayin Allah ba iya tausayin dansu suke ba kai ne abin tausayi domin kai ne kake raye kaine kake bukatar kome shi na shi ya ƙare yana can amma addu'ar iyayensa dukka biyu yana riskanshi kai fa? Baka da wanda ka ajiye zai maka baka da wanda zai maka addu'a kana fushi da shi! Bayanshi ya kama dahir wani lokaci ba kukan mutuwa muke ba, kukan namu ya zai riske mu muke kuka. Duk wanda ya rasa iyaye shine abin tausayi ba su iyayen da suka tafi ba! " Ina kai nan na mike na bar shi a wurin, tabbas rayuwarshi a juye take yana bukatar wanda zai d'aga mishi rayuwarsa. Ban daki na shiga nayi kuka nayi kuka wannan shine abinda ba zan manta a rayuwata ba. Ganin har lokacin ban fito ba, Daddah ta ce mishi."Matarka yaki fitowa, kizo ki san yadda zaki yi da shi!" Jiki a mace ya zo ya buga kofar. " Lunah kada ki kirkiro mana wani scenes please ki fito muje gida!" Haka na bude kofar ina kallonshi. Yayi wani iri, bude mishi hannu nayi ya shiga cikin hannun, na rungume shi. " Sorry ba zan kara maka magana ba ka ji, amma be a good boy!" Gyada min kai yayi na shiga shafa bayanshi, ina jin wani irin tausayinsa a raina. Mijina ne dole na taya shi yaki da zuciyarsa ya san darajar iyayensa. Wucewa Daddah tayi ta bar parlourn. Sai da na ji yadda yake jin zafi na janye jikina na saka mayafina muka koma gidan mu, aka yi sallah la'asar. Ina dakin ya shigo ya same ni. Kallonshi nayi murmushi nayi mishi tare da bude mishi hannu. A hankali ya tako, wani lokaci namiji ya maka lakar shagwaba wani cinyewa ne, yana zuwa ya durkusa a gabana na rungume shi, ina shafa kanshi. "Kayi hakuri ka ji!" Zagayawa yayi da hannunsa bayana ya rungume ni. "Thank you, Moon!" Shafa bayanshi nayi a karo na biyu. "Is ok, ka godewa Allah da sauran lokaci bai kure ba." D'ago yayi yana kallon yadda nake kallonshi, murmushi yayi a hankali ya d'ago fuskarshi ya haɗa da nawa, akwai wani lokaci da zaka yi mafarki a zahiri amma kuma irinshi bai cika tabbata ba, but today My Man ya cika min mafarkin fiye da yadda ban zata ba, domin ni dai nasan nayi aure amma ban san cewa akwai wani tafiyar da iya yarda da abokan arziki mijin na gari, sai dai kuma yadda labarin zai kasance ne aka samu matsala. Domin ana ta buga kofar gidan. Janye jikinshi yayi yana kallon yadda na lumshe idanuna. "Ina ga su Auntynki ne ko?" Ban iya amsa mishi ba, amma kuma na gyada mishi kai wani irin kunya da girmansa suka cika min idanu. Sai da ya fita ka sauka da gudu na bude kayana na dauko riga da skirt na saka sannan na yafa mayafi. Daurin dankwalin a parlourn na karasa shi, shine ma kayansa yayi wani irin squeezing, shigowa suka yi ya musu barka da zuwa sannan ya fita. Ganin yadda yake raba idanu Aunty Zakiyah ta ce min. "Auta ba dai mun katse muku!" Wucewa kitchen nayi kunya ya gama lullube ni. Dakina suka shiga yadda suka ga gadon a yamutse Aunty Hindatu ta shigo kitchen din ganin yadda na tsaya a gaban sink ina murmushi, wannan shine first time da aka yi kissing dina. Sai nake ji kamar ina yawo a sama ne ko a iska ne, abin akwai armashi wanda a da can Ya Hafiz bai yarda da kiss ba wai shi baya son kazamta, amma yau abubuwa dayawa sai suka sani jin kamar bani ba, yatsuna na kai bakina. "He kiss You ko?" Kallonta nayi a razane domin ta razana ni. "Wallahi kin bani tsoro!" Zungure min goshi tayi tana faɗin. "Kina imagination na abinda ya faru, ki sani babu amfanin hasashe domin kuwa shi naki ne." Aunty Hindatu kenan bata san yadda na sha mafarkin irin wannan ranar da rayuwar ba, daukar tire din da na saka drinks din nayi na wuce na kai musu na dawo na duba firj na ga namar jiya kasancewar yayi sanyi sakawa nayi a microwave nayi na dumama, sannan na kawo musu yadda nake dan dingishi yasa suka fara min tsiya wai tun shigowarsu nake raba kafa. "Innalillahi wainnalihir rajoun, gocewa nayi fa jiya! Allah ku tambaye shi!" Na fada musu kamar xan yi kuka. "Au don mune yan iska sai muce mishi wai da gaske gocewa tayi?" Shiru nayi ina share zancen, daga gidan Daddah aka kawo mana manya kulolin abinci, har da fura da nono. Ai kuwa sun ci abinci sosai. Aunty Zakiyah ta ture tare da miko min wata jaka wai muje daki Aunty Innah ta ce. " Bana son bakin munafunci gaya mata anan!" Kayan Mata ne na Maman Hidaya da Khairat ne, hadi na musamman ta ajiye min ga turaren tsuguno da na humra, duk kunya ta kama ni tsuminta ta sa nayi ta sha har bayan Magariba suka tafi, bayan fitarsu na gyara gidan na saka turaren wuta, na shiga ban daki nayi wanka na gyara jikina da kyau. Sannan na fito a hankali, na shiga turare jikina ta ko'ina sannan na nufi wurin kayana, na dauki kayan barci masu kyau. Na saka na kara gyara jikina sannan na nufi ban wurin abin sallah na daura sallah isha da shafa'i da wutir, ina cikin addu'a ya shigo gaba yayi ya tare da tadda kabbara, sallah da ma'aurata suke na sunnah shi ya ja mu. Sannan ya dafa kaina yayi ta zuba addu'a kafin muka shafa. Janyo hannuna yayi muka fita parlourn, zaunar da ni yayi sannan ya nufi kitchen, wayata da take hannun kujeran yayi kara, ɗauka nayi. *Kina ta rawan jiki! Tow in sha Allah wannan daren da kike gani shine na bakin cikinki...........* [12/18/2025, 7:27 PM] Maman Walid: 21 Sake wayar nayi ya fadi kasa, daidai isowarshi parlourn ganin yadda na razana tare da zubawa wayar idanu cike da tsoro. Ajiye tiren yayi ya zauna tare da ɗaukar wayar ya kalli rubutun, kallona yayi ya ga yadda duk na firgita. Kashe wayar yayi tare da cewa. "Oya muci babu abinda zai faru." Ya fada yana mika min hannunsa na rike tare da saukowa daga gadon, a hankali na mika mishi hannuna. Ya riko ni sannan ya zaunar da ni a gefenshi muka ci abincin wanda ni kaina nasan ba wani abin arziki na ci ba, amma shi ya ci kai. Kallonshi nake na ga shi ko a jikinsa. Bayan ya gama ya ce min. "Taya ni kai kayan kitchen," haka muka kai kitchen, sannan ya ce min. "Mu wanke!" Ya fada yana me kallona, ganin nayi shiru ya dafa ni a dan razane na kalle shi. "Tunani kike?" Girgiza miishi kai nayi, ya janyo ni gefenshi ya shiga bani labarin da ya mantar da ni abinda ya faru, ba a gama wanke wanken , ma samu sauki daga tunanin da nake. Muka gyara kitchen din sannan muka dawo parlourn muka yi ta hira. Sai goma saura na wuce dakina na wanke baki na cire hijab din na kwanta sannan can sai gashi ya shigo, ya zo dakin kunna wutar dakin yayi ga yadda na rungume pillow, kashe wutar yayi ya nufi gadon ya zauna yana kallon yadda nake kwance lumo. Kwanciya yayi a gefena. "Ya ce min yau ko bani labarin da na jima ina son sani da bakinki!" Bude idanu nayi a hankali na zuba mishi kafin na lumshe idanuna, na fara bashi labarin irin zaman da muka yi da Ya Hafiz, sai da na gama bashi tas kafin ja gyara kwanciyar da nayi na sauke ajiyar zuciya janyo ni yayi jikinshi yana faɗin. "Sorry ban san irin rayuwar da kika yi ba kenan, amma me yasa kika manta da ni?" "Saboda ban tab'a tsayawa na duba waye kai ba, sannan ban tsaya na kalli fuskarka ba, balle har na san cewa kana tare da adalci. Duk lokacin da na tuna na kwari kaina sai na ga kamar ban yiwa kaina adalci ba, sai dai ni fa mahaifata ya lalace bai zama dole na haihu da kai ba, amma kofa a bude take idan zaka kara aure Allah ya baka zuriar dayyiba." Hannu ya saka bakina yana faɗin. "Shiiiiii! Nima ban damu da lallai sai na haihu ba, shekaru sun ja!" Ya janyo ni karo na biyu ya rungume ni da kyau, a hankali yake shafa bayana yana rarrashina. Har barci yayi gaba da ni.
A hankali muka yi wani irin sabo da shi har na tsawon kwanaki uku cib, duk da bai tab'a niman wani abu ba amma na ga alama kamar shiri yake yiwa kansa. Sai dai ranar da na cika sati da yake su Aunty Hindatu sun tafi washi garin ranar da suka zo. Ranar da na cika kwanaki bakwai a ranar ya shirya min gagarumar tarbar na musamman, don tun safe yake nuna min tsaf y shirya min, da yamma da ya fita ma haka ya kawo kayan lambu da duk wani abu na zabe fruit na hada mata hadi na musamman, da yake ya hana a kawo mana abinci da kaina nake girki, hidimar da nayi ranar y saka min gajiya haka ya sa ina gamawa na jera a table na wuce dakina nayi wanka da alwalan isha, bayan na yi sallah na fito parlourn don ina ta jin kamar maganar mutane. Abin ya bani mamaki taya ya dawo na san zai shigo. Haka na fito na samu yan matan family din ne a kan table sun saka abincin da nayi mishi suna ci, murmushi nayi na wuce kitchen na tsaya sai na ji raina yayi azabar ɓaci, koda na fito na samu ba iya cin abincin suka yi ba wulakanta abincin suka yi, kallona Badr tayi tana faɗin. "Gidan dan uwanmu ne kuma mijina ni nan ni ce kishiyarki da kika danne aurena ya auro ki." "Sannu da kokari!" Na ce mata sannan wuce dakina. "Waye bai san labarinki ba? Sai dai shi wanda aka yiwa asirin da yake ta rawan kai akanki!" Juyowa nayi ka kalle ta nayi ƙoƙarin danne fushina da b'acin rai na ce mata. "Sai me don kin san labarina? Tayu ki bada labarin da kika sani, amma ko gidan giya akwai babba." Na juya zan wuce ta ce min.. "Mahaukaciya wacce tayi jinyar hauka." Ji nayi raina yana b'aci, "kun ga ni ba ai na gaya muku tayi jinyar hauka yanzu ma Mentioned din sunan haukar yasa ta tsaya, yar kwaya kawai."