ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 10
ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 10: ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 10. Ina kallon yan uwana cike mamaki su kansu lamarinsa kara basu mamaki. Duk jikina ya ɗauki…
2,151 words
Ina kallon yan uwana cike mamaki su kansu lamarinsa kara basu mamaki. Duk jikina ya ɗauki rawa. Haaka muka isa wani gidanshi a can victory Island, gidan yayi kyau, ya riko hannuna muka shiga avinda muka fara shi ne sallah, muna idarwa ya fita can sai gashi da abinci, kusan a tare muka ci yana bani ina kauda kai karshe ya janyo ni kamar yarinya karama haka yayi ta dura min, har na ji na koshi. Kafin ya riko hannuna zuwa parlour ya zaunar da ni akan kujeran parlourn, sannan ya fito ya zo ya zauna ya saka ni a gaba yayi ta kallona. Kafin ya kwantar da kanshi a cinyata, hannuna ya ja ya daura akan kirjinsa, tun yana min hira har barci yayi gaba da shi. Zama nayi ina kallonshi. A hankali nima na daura kaina kan kujeran na cigaba da nazarin rayuwa, kafin barci yayi gaba da ni. Wasa-wasa sai karfe shida saura muka farka, shi ya fara tashi ya zuba min idanu. Ji nayi an sumbaci hannuna, a hankali na ji dumin lips dinsa, bude ido nayi na kalle shi na ce mishi. "Kin tashi?" Gyada mishi kai nayi ya ce min. "Sorry ko ni na tashe ki?" Murmushi nayi na tashi zuwa dakin da muka cin abinci a cikin na shiga ban daki biyo ni yayi, zuba min idanu yayi da yatsu biyu ya nuna min abinda zai yi. Juyawa nayi zan fita ya riko hannuna na tsaya, ya gama yayi duk abinda Muslunci ya shara'anta sannan ya fito nima nayi nawa na fito na zo na samu yana jirana, a bayanshi na tsaya ya jamu sallah, bayan mun idar ya dauki Babban rigarshi ya ce min. "Muje kin ji suna can suna ta Bala'i!" Ya fada yana murmushi, gyara zaman mayafina nayi yana gamawa ya riko hannuna muka fita, har waje ashe dA mutane a gidan a harabar gidan na gansu suna taya shi murna. Motar ya bude min na shiga, sannan ya zagayo ya shiga yana zama muka bar gidan kafin mu isa har an kira Magariba, muna shiga can cikin gidan. Ya bude min na fita ya riko hannuna sai da ya ja min mayafina ya rufe min fuska, sannan ya rike ni gam, muka shiga tafiya kasancewar gidan ana ta hidima ga mutane sun taru, hotonmu da muka yi aka saka a wurin da za ayi taron, a hankali muke tafiya saboda tun da muka shigo gidan ake daukarmu hoto, lokacin da muka fito aka mana caa, sai da na ji bakiɗaya kome ya tsaya min har cikin gidan muka shiga hannun shi rike da nawa, gam lokacin da zamu shiga yan matan family din sun fito, hannunsa ya kai kuguna, ya kara janyo ni jikinshi, kallonshi nayi murmushi yayi min da wani karamin murmushi, haka muka shiga cikin gidan ana rangad'a gud'a, kaina a sunkuye har gaban Kakarshi ta wurin Uba wato Daddah tare da Kakarshi ta wurin Uwa. Guɗar da ake yasa ko ina na gidan ya amsa, riko mishi kunne wata babbar baturiya tayi tana mishi fada. "Aunty Mom barci nake ji. Idan na ce ku bari mu yi barci ba zaku yarda ba, amma gata Lunah bayan barci akwai wani abu da na.." ture keyarshi tayi tana faɗin. "Allah ya shirya ka wuce masjid;" ta tura shi waje, daga nan ta riko hannuna ta kara kawo ni gaban Mamarsu. "Mum ga Lubnah!" "Labubu!" Kaina a kasa ta rike hannuna, ta rasa bakin magana sai kuka, Daddah tsabar dad'i wani abun wuyarta na gwal ta cire ta saka min, "tunda turaki ta kawo ka da sunan tana sonka, nasan bai yi zabin tumin dare ba." Ba ta kara cire warwaronta, ta saka min a hannu. Yan uwan Mamanshi da suke zaune da kawayensu ba sai gashi anata zuba min kudi fa kyauta kamar ana hidima. Da yake an tura a kira su Aunty Hindatu, sai gasun nan, haka suka d'aga ni zuwa vangaren da xan zauna aka hada min ruwan wanka Aunty Zakiyah ta hada min kayan kamshi nayi wanka na gyara jikina na fito nayi sallah, sannan na gabatar da sallah da ya wuce min, sannan nayi isha domin za a yi min kwalliya, bayan na gama aka kawo min wani kaya irin na mutanen Ethiopia, haka saka min kayan tare da mayafinsa sannan aka gyara min gashina, ban ji dadin wannan kwlliyar ba. Ana cikin kwallyar ya shigo yana ganin gashin a bude ya ce bai san wannan zancen ba, hular da aka daura akan gashin ya kara fitar da ni, kasancewar Kakarshi Kirista ce har yanzu don haka kayan akwai Cross amma sai aka cire na kan hular, sannan muka fito bayan an gama shirin, su Aunty Zakiyah sun jima da barin gidan domin tas zai kunyata su.
Tunda aka ce zamu fito aka haska wani fitila da camera wanda suke can baya suna hango mu a majigi, sai suka huta da mikewa, flower girls dinmu Yaran Jasminah ne da Yaran mazan Uncle Auta, suka bude mana hanya muka cigaba da tafiya, Nusaiba yar Aunty Nuratu Kafaya ita ce da wasu yan Gym dinmu suka fito a bridesmaids, suka take mana baya a mazan da suka rufa mishi har da Ubaid. Haka muka isa wurin zaman muka zauna. Gashi an saka wakarsu ta can wanda suke yi da kafada, wasu daga cikin danginsu na can, sai wurin yayi kyau. Haka akayi ta gabatarwa har aka gama kafin aka kira Ubaid ya bada labarin abokinsa, a hankali yake bada labari har ya gama sannan aka kira Nusaiba ta bada labarina, tun daga bude taron da Addu'a zuwa yadda take ba da labarina, kallon Aunty Zakiyah da ta d'aga min hannu nayi murmushi, bayan ta gama aka saka waka musamman namu na yan arewa, kafin aka saka wakarsu na Fulani. Kallona yake yana murmushi, bayan an fito da ni da shi. Aka yi ta zuba mana kuɗi, daga shi har ni ba gwanayen rawa ba, haka muka tsaya musamman inda ya ɗan saka hannunshi a kuguna da kuma rike hannunsa ina kallonshi. Wani abun da ya kara tashin hankalin a wurin masu adawa da aurenmu, musamman Badr ban ganta ba, na samu kyautar abin arzikin da abin duniya baa tashi ba sai karfe daya saura sannan aka raka su Aunty Hindatu zuwa gidan Ya Ado ango da yan uwansa, ni kuma aka wuce da ni bangaren fa aka gyara shi tas, aunty Innah har da cewa. "Yanzu ba mamaki fitar nan har kin bashi hadin kai ko? Tow wallahi ba wani ɗoukin da zai yi akanki." Tura baki nayi ina faɗin. "Wallahi ba abinda muka yi barci kawai yayi fa!" Na fada ina jin haushi ko me na bashi ai hakkinsa ne, tun da muka dawo take fada, kamar nayi wani zunubi, bayan sun tafi Aunty Mom ta bani wasu abubuwan har da tarkacen mata irin na turawa, muna nan zaune da ita har suka dawo da yake har da Matar Ubaid da Uncle Auta, ana ta hira sama-sama, na lura matar Ubaid tana jin kanta ita wata shegiya ce, nima na nuna mata ni iyaka ce, suna shigowa kai tsaye wurina ya nufo ya cire min mayafin yana faɗin.. "zaki cutar fa fatarki da wannan uwar bargon wanda ko ita Momma bata isa yafa wannan abin ba." Ya wurga da shi can kasa ya maza ya duba kafana da yake muna dawowa na goce da kafar, yana d'agawa yaga yayi ja. Rike baki yayi tare da dama a kujeran ba juyawa Kanwar Uwarsa baya yana faɗin. "Yanzu kin san kafar tayi haka shi ne baki kira ni kin d'aga min hankali ba, Innalillahi wainnalihir rajoun, wannan wacce irin masifa ce da tayi min asarar daren amaarci." Zuba mishi duka Kanwar Mamarsa tayi tana faɗin.. "kai dai baka da mutunci sai ka san yadda zaka yi da kafar." Wallahi tsakaninsa da Allah ya kore kowa a gidan. Ya kuma nace sai ya cire gocewar. " Yanzu Lunah hakuri zaki yi na cire wannan abin domin wallahi ba zai hana ni sakat ba."zare idanun nayi na ce mishi."" Ban isa ba wallahi ba zaka cire min masifa ba, ina zaman lafiya. " Ai kuwa ya dauki wayarshi ya dokawa Kakanshi kira akan akan me zai shirya taron da na goce. Kafin wani lokaci tsofaffin nan sun iso gidan, ba sai gashi Uncle Auta ya dawo ba aka je a daren aka dauko me gyaran karaya, yayi tsalle ya tuma ya ce musu.. "Malam gayan mun yadda ake cirewa amma ba zaka taba min matata ba!" Sai da Uncle Auta ya ce mishi.. "ka rungume ta domin idan kai ne waye zai rungume ta, haba don Allah." Gyada kai yayi yana dawowa kusa da ni ya zauna, tare da rungume ni mutumin ya kama kafar ya latsa da kyau kafin ya ja wallahi ban san lokacin da na gantsara mishi cizo ba.......... [12/17/2025, 7:29 PM] Maman Walid: 19
Shafa bayana tare da ce min. "Shiiiiii!" Sake fatar nayi tare da cewa. "Don Allah ka ce ya bari na huta don Allah ka gaya mishi ya bari na huta;" "Sake kafar ta huta!" Ya fada yana bubuga bayana, "sannu." "Boy dare yayi fa saura minti hamsin a kira sallah farko kai da matarka kun hana mu barci wallahi!" "Look at my eyes bari ya ja!" Zare idanun nayi zan girgiza mishi kai, ya saka kaina a kafad'arshi, yana buga bayana, mutumin na jan kafar na fisge kaina zan yi ihu ya cilla min wani sweet a bakina na fashe da wani irin kuka. Tare da rungume shi. Kuka nake yana shafa kaina. Har aka gama jan kafar ina kuka, Daddah tayi ta min sannu, anan barcin wahala yayi gaba da ni.
Haka suka watse a gidan kowa yana tausaya min. Cak na ji kamar ina yawo a iska na bude idanu me cike da barci na kalle shi, murmushi yayi min sannan ya ce min. "Yi barcinki, my chest is your special bed, don haka rufe idanunki." Ya fada yana tafiya a hankali har dakinshi, ya kwantar da ni a hankali, ajiyar zuciya na sauke ya shiga ban daki yayi wanka da alwala sannan ya fito, ya ja min bargo yayi sallah. Kafin ya kwanta. Sai da yayi sallah nafilla kafin ya ɗan kishingida, yana addu'a gyangyadi yana fisgar shi ya ɗan kwanta. Ai kuwa barci ya dauke shi, sai jin shigar sallah yayi da sauri ya shiga yayi alwala ta nufi masallaci, bai fito ba sai da garin ya fara haske. A hanya ya hadu da Kawunsa da Mijin Goggonsa kallo daya ya musu ya shiga shafa gemunsa cikin murmushi irin na tantiran yan duniya, ya d'aga musu gira irin tow ya nima haka nake, don iskanci goya hannu yayi a baya ya cigaba da tafiya yana murmushi. Tabbas yana shiga musi hanci da kudundune. Yasan su ne suka shirya aka dawo da shi gidan don haka sai ya fitine su da rashin kunya da rashin mutunci yadda da kafarsu, zasu zo su ce ya bar musu gidan. Duk yadda aka tsara ya sani amma yafi son su fuskanci guilty din tare da shi, yadda suka yi amfani da damarsu. Sai da ya isa kofar gidansa ya fara wani iyayi irin na zumudin sabon ango.
Ai ko da ya shiga cikin gidan, dakinsa ya wuce ya samu tana barci abin ya burge shi, amma ya zauna a bakin gadon yana wani murmushi yana jin wani irin dad'i da nutsuwa. Kayi mafarkin kai Gwauro ne ba karamin masifa ba ce, shafa kaina yayi sau biyu na bude idanuna. Da suke cike da barci a hankali ya ce min. "Good Morning Queen!" Murmushi nayi na tashi zaune kafin na ce mishi. "Kayi hakuri ban yi sallah ba." Na dauko a hankali na daura kafar a kasa, sai naji babu zafin sosai zan mike naji ya janyo ni, sumbatar goshina yayi yana faɗin. "Kin yi kyau!" Murmushi nayi na kara mikewa, ya dawo da ni na zauna ina kallonshi. "Lokaci yana kurewa!" "Ok muje na raka ko!". Ya fada na mike a hankali, zai dauke ni na ce mishi. "Don haka ka yi hakuri wallahi xan tafi da kaina." Murmushi yayi ya ce min. "Nayiwa Mama alƙawarin kula da autarta!" Haka ya dauke ni har ban daki. "Ni dai ka fita xan iya kome da kaina." "Tow!" Ya fita ni kuwa nayi wanka da alwala a gurguje, na fito nayi sallah. Ina idarwa ya shigo da mug na tea, mika min daya yayi ya ajiye na shi ta fita can sai ga shi da Pjym riga da wando ya mika min." Kwanta muyi barci!" Kallon kayan nayi sai kuma na amsa na nufi ban daki na saka, ina fitowa ya zubawa kofar ban dakin idanun kuri, kunya ce ta rufe ni na saka hannu bibbiyu na rufe fuskana. Tasowa yayi ya balle gaban rigar yana murmushi ya ce min "haka nake son ganinki!" Ya janyo ni zuwa bakin gadon ya zaunar da ni.