Kenza eBookz

ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 9

ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 9

ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 9: ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 9. "Amma ina da hakki akanta? Idan aka cigaba da yin haka waye zai dauke ta da daraja. Duk wannan…

4,246 words

"Amma ina da hakki akanta? Idan aka cigaba da yin haka waye zai dauke ta da daraja. Duk wannan rawan kafar da kuke yi ku sani bare ne ba dan uwanta ba." Ya fada ranshi yana jin zafin abin, basu kula shi na can ya ce musu."idan har albarkata ce zata rike auren Lubnah ba zan saka mata ba." Murmushi Mama tayi ta ce mishi. "Tabbas rayuwar auren Lubabatu yana bukatar albarkanka amma ka sani ko ka saka ko kada ka saka aure babu fashi, kuma ka rike albarkanka ai naji Talatu da Uwani zasu bashi Jalilah da wannan nake son ka sani kamar yadda Lubnah tayi gaba har abada Hafiz da Jalilah ba zasu tab'a tarda da ita ba. " Daga haka ta wuce dakinta ba zata kara miishi magana, haka. Yayi ta fada har yana faɗin saboda abin duniya suka likewa turaki! Yadiko ta ce mishi." Eh kai tunda ya fitar da kai kunyar kallon mutane da bashin da Tsinannen Yaron can ya ciyo maka, dole ka samu bakin magana ko kunya baka ji ba. Ka zauna kana dabbawa kanka wuka. " Tayi tsaki ta cigaba abinda take yi.

A can Jamaare fa haushin Yayun Lubnah sun tsaya kai da fata ba zata koma gidan Hafiz ba, shine suka yi zuciya tare Da bawa Hafiz auren Jalilah, wannan shine mafarkin Jalila ta sami Hafiz kuma burinta ne gashi nan ya cika zata samu Hafiz yadda take so, sai dai Hafiz shi baya ta ita domin kuwa zuciyarsa bakiɗaya tana can ga son zuciya. Hatta hada auren bai san anyi ba domin ya je kulla nashi makircin.

*** Kwanaki goma sha biyu muka dawo daga Dubai a matuƙar gajiye da tarin tsaraba. Wanda muna isowa aka yi ta tura kayanmu wurin ɗinki, har gida matar ta zo tayi ta amsa tana, duk da ya cewa su Aunty Hindatu akwai kayan biki daga Russia za a kawo don kome booking yayi daga can, mun dawo da kwanaki uku. Wanda yayi dai-dai da bikin saura kwanaki,

Da safe Aunty Hindatu suka zo gidan ina zaune a daki ina karyawa suka shigo, kallonsu nayi na ce musu.. "Lafiya kamar an koro ku?" "Gobe zasu kawo kaya!" Wani zabura nayi tare da nufar daki suka biyo ni da yake Mama tana dakin Abba, daga nan ina jin yadda suke sa'in'sa da alamu maganar auren ne, sai da ta fito muka fahimci, ai akan auren ne domin kuwa ta ce ya bada abinda za ayi hidimar bikin ya ce shi ba zai bada ba, ya rigada ya tura Jama'are shi yanzu ya tura daurin auren Jama'are, shine take fada wai ayi bikin a can, ita kuwa ta ce ba yarda ba shine fa abun ya kai ga sa'in'sa. Shi ya ce idan ba a Jama'are ba sai dai a fasa auren ita kuma tayi tsalle ta tuma ta ce babu wnada ya isa ya mata wannan rashin adalcin. Karshe sai ga gidan ya cika da Yayuna dakyar aka lallaba Mama ta amince, amma kuma da Ya Umar ya zauna da Abban ya gaya mishi abinda yake faruwa domin har gidan Ango sun buga katinsu gobe za a kawo kayan aure, sai jikinsa yayi sanyi dama daga can aka zuga shi da yake bai da lissafi ya zauna a kai.

Dakyar aka kashe maganar a daura auren Hafiz a can, Lubnah za ayi bata a gwallaga, sannan shi Hafiz ranar juma'a ne yayinda lubnah ranar asabar ne. Wani ikon Allah a masu zuwa amsar kayan har da Jalilah tazo ganin kayan auren, da yake gulma da munafunci ya kawo su. Karfe daya na rana suka iso lokacin gidan ya cika a gidan nan Aunty Zakiyah da Aunty Munah basu nan, amma har Raliyah daga Jos sun zo yan kaduna ma sun zo, suna sallah dangin Mr Turaki suka iso wurin karfe biyu da minti talatin. Tun daga bakin kwananmu aka rasa inda za a ajiye motar yan kawo kaya, abinda nake gani a blogs yau shine a kaina, yadda aka yi ta fitar da kayan ana shiga da shi kai rakiyan kawo kayan har da yan sanda da civil defense, aka kawo kayan aurena. Wato ba iya jijjiga table nayi ba karya table din nayi, domin har daga makotan unguwarmu shigowa ake zuwa ganin kayan.

Ni kan tunda na shige uwar dakin Mama ban fito ba, a babban parlourn baki aka karbe su, koda yake ba abinda xan cewa Yayuna sun fitar da ni kunya ba zan iya cewa kome ba, a cikin waɗanda suka kawo kayan har da wata baturiya anan suke cewa kanwar Mamanshi ce ita ce autarsu wato Miss Herlim, bayan an karbi Kayan an kuma bude anyi addu'a, sannan aka yi addu'a, kafin suka ce. "Tow mu dai zamu wuce ba kwana zamu yi ba!" Ita Miss Herlim ce ta bukaci ganina, Aunty Hindatu ta ce mata tazo, ina zaune a dakin aka shigo da ita, ko bata gabatar fa kanta ba nasan Yar uwar Mamansa ce. Tana shigowa ta rungume ni, tare da kama hannuna ya saka min wani abun hannu. "Inji Mamanmu, tace a sakawa Labubu wannan." Shafawa nayi ina kallonshi murmushi na ce mata. "Na gode!" Murmushi tayi ta ce min. "Mafarkin Son zai tabbata, don Allah ki mishi adalci yana sonki so na hakika, mutumin kirki ne bai taɓa niman matan banza ba, na kirkin ma baya bi, bai taɓa shan giya ko wiwi ba, balle kuma taba. Mutumin kirki ne sosai. Zai kula da ne, ki rike mana shi amana maraya ne bai da Uwa bai da Uba sai kakanni. " Sai yanzu na tuna mun yi fada ashe bar muka bar Dubai a tare muka sauka a lagos, mu kuma sai muka sake bin wani jirgin zuwa Jos, bana son tuna abinda ya fada mu, domin raina bacci yake. Koda yake ba laifinsa ba ne na me hoton ne, da kuma nima, Kodayake ai ba wani abu bane, awurin daukar hoton ne ya min tashin ɗa'a, na kusan gaya mishi magana, amma ya dauko duk laifin ya daura min domin kuwa bai yarda yayi kuskure ba, har sai da Auntynshi ta shiga lamarin, nasan ya hanani saka turare mai karfi amma Aunty Innah ta saka nu sawa. Shine ya nime yayi min rashin mutunci.

Har yau mutumin nan ya ki kirana ya bani hakuri bayan yasan shi ne da laifi, murmushi nayi nace mata. " In sha Allah!" Haka ta fita duk wani abinda muka yi sai da aka hada musu tas suka tafi, bayan tafiyarsu Yadiko ta ja kofar ta rufe. Domin kuwa bata ji a ranta a bude parlourn ba, haka kowa ya gama son gani sai bayan tafiyarsu aka bude tare da zuba idanun akan kayan aka gama gani aka rufe parlourn, bayan isha aka tattara kayan sai gidan Ya Umar aka kai can, karshe aka bar gidan da kamshin yan gayu, wurin karfe tara Ya kira Mama suka sha hira yayi ta godiya. Tare da farin ciki an karbi danginsa da mutunci an karrama su..

Ni dai ban san yadda suka kare ba, domin barci ya kwashe ni sai wurin karfe biyu na dare na farka nayi alwala na gabatar da nafilla, ban kwanta ba sai karfe hudu saura na kwanta.

* Washi gari mota Ya Tahir ya kawo aka mai da yan jama're, suna barin gidan nima Aunty Raliyah ta kai ki saloon, muka je aka gyara min kaina, ana wanke min kai kalman Jalilah ya dawo min inda take cewa. "Na ga sai wani murna kuke kasa dai a zurma dayawa domin dai kaf duniya babu me iya miki kirkin da Hafiz ya Miki!" Ta fada tana murmushi, nima na ce mata.. "duk wnada ya goyi kare yasan yadda zai da bakinsa, Malama ina miki farin ciki, zaki auri abinda kika jima kina jira." Daga haka ba barta a nan.

Murmushi nayi kawai ganin Ya Hafiz take, haka aka wanke kaina da kafana aka gyara min farce na. A ranar da muka dawo gida. Mama ta bani ruwan zam-zam take gaya min cewa. Yadiko ta biya aka hada min daga can Belaye, aka kawo min. Shi dai bai ce musu kome ba, ya ce a cigaba da shiri aure za ayi shi kuma akwai haske d duhu amma hasken tafi yawa, Tunda ta fadi haka suke sadaka kome badawa suke sadaka, kamar zasu zauce saboda kawai Allah ya bada zaman lafiya, haka yasa kowa ka gani a hidimar da aka fara hankalinsa kwance.

Ranar Juma'a Goggo Alti tazo, ta ce ta bar Goggo Uwani da Talatuwa a can, musamman ita da zata yi auren yarta, amma wani ikon bayan isha sai fa Goggo Uwani, kamar an wurgota daga daka, abinda ya bawa kowa mamaki an daura auren Hafiz da Jalilah.

Ranar Juma'a daren saukar kur'ani aka yi, ba ayi kome ba. Washi gari kafin daurin aure aka yi walima wanda karfe goma aka yi shi, ana gamawa sha daya saura muka aka kara shirya ni. Tun daren jiya aka kawo mai lalle da asuba ta zana min yayi kyau ya zauna das a hannuna.

Da yake a masallacin gwallaga ake daurin auren, dubannin al'umma suka shaida daurin aurena.

Bilal Haris ElYakub kumo Da Lubabatu Usman Umar Jama'are, akan sadakin sisin gwal, guda ashirin da biyar. Lakadan ba ajalam ba. Idan ka ganshi a wurin kowa sai ya san an daura aurensa domin yayi wani irin zuru-zuru. Bayan an gama aka dauki hoto da manyan baki sannan aka wuce gidansu amarya. Ina sanye da wata farar doguwar riga wacce aka kawo daga wurin kakanshi a can Rasha, sai mayafin da na rufe kaina da shi aka fara guda alamar angwayen sun shigo sai da suka gaida aka yi addu'a, sannan aka kira ni parlourn baki, koda na isa gabanshi na je, wani irin rungume ni yayi kirjina yana buga tara-tara, ya ce min. "Finally Mrs Bilal Haris Turaki.....

(Allah ya gani page biyu na so baku amma ciwon do da gefen kaina zuwa goshina ciwo yake min sosai kuyi hakuri zuwa gobe don Allah) [12/16/2025, 1:37 PM] Maman Walid: 17 Yadda ya rungume ni naji haka a jikina, sai yanzu nake jin kamar ina safe place, he became mine, kara rungume shi nayi hawaye na zuba min tabbas mutumin nan yayi hakuri ya jira har Allah ya bashi, duk wanda ka gaya ya jima yana nima to kada ka ga dare daya ya samu kace ta wata hanya ya samo hakuri da juriya. Dakyar aka janye shi sai guɗa ake mana, kafin aka fitar da shi. Parlourn Mama suka shiga ya zube akan gwiwarshi, da sauran yan uwansa ta ce mishi. " Bilal ga Lubabatu nan na baka, Bilal idan ka gaji da Lubabatu kada ka wulakanta min ita ka kira Ado ko Tahir ka ce su zo su ɗauki Kanwarsu, Bilal kada ka tozarta min Yarinya idan tayi maka laifi ka kawo min ita ni nan nasan abinda zan mata, Bilal don Allah idan ba zaka zauna da ita kada ka kore ta, ka. Kira a zo a dauketa. Ku shaida na roke shi da kada ya wulakanta min Yarinya don Allah kada ka wulakanta min ita wallahi tana maka ba dai-dai ba, ka gaya, zan zo har gidan na iso kota. Ka yi hakuri ka duba rayuwarta na baya ka rike min ita da adalci. Zata maka biyayya ba zaka tab'a hanawa tayi ba, kayi hakuri don Allah."

"In sha Allah Hajiya babu abinda zai faru, idan yayiwa Lubnah wani kawunansa ni zan fara sare mishi kai." Inji Uncle Auta, Ubaid ya ce mata. "Hajiya in sha Allah haka ba zai tab'a faruwa, Hajiya ya iya zaman jiranta duk ya tsufa ya zama Kasungurmin tuzuru kafin baiwar Allah ta amince mishi ai kin san baba tsoho zai rike yar Matarshi da amana!" Ai kuwa aka yi ta dariya sannan aka yi addu'a. Suka nufi dakin Abba, kasancewar yana jin nauyin Turaki da irin abinda ya mishi, mika mishi hannu yayi Turaki ya riƙe ya cewa Ya Ado. " Kira min Auta!" Ya Ado ya zo, abokan wasa sun saka ni a gaba wai a bamu fili kawai tunda sun ga mijin ya gagara boye zallamarsa a fili nima har da wani cusa kaina kai Jama'a, wata abokiyar wasana yar kawuna kenan take min wannan tsiyar.." Hindatu fito da ita Abba yana kiranta?" Ya fada a gaggauce, bakiɗaya muka kalli juna, wani irin tsoro da tashin hankali muka shiga dukkanmu haka muka fito musamman yan uwana. Haka muka fito aka shigar dani har gaban Abba tsoro ya gama cika ni. " Bilal Turaki ga Lubabatu nan na baka ita, Bilal Turaki kada ka saka min Y'a kuka, idan ba zaka iya ba ka dawo min da ita don Allah, don Allah kada ka cutar da ita, ta sha fama da rayywarta na baya idan har bata maka ba, ka kira ni na tura Yarana su daukota. Y'ata yar dangi ce soyayyar da suke yiwa juna Allah kaɗai ya sani, idan har wani zai yi kuka tow kuwa dukkansu zasu yi, bakiɗaya suka goya min mata baya don tayi farin ciki, Yarana basa bayan abinda kake da shi, damuwarsu Kanwarsu tayi farin ciki, nasan suna son kanwarsu zasu iya tsayawa sun yake ka akan Kanwarsu don Allah ga amana mun baka." Ya turo kekenshi, nima ba matsa kusa da shi, ya dauki hannuna ya mikawa Mr Turaki, ya rike ya d'ago kai yana faɗin." Allah ya saka da alkhairi, in sha Allah ba zaka tab'a samuna da laifin akanta ba, in sha Allah ba zaka kama ni da laifi a kanta ba, idan ka ga wani abu ya faru tow a cikin kaddaranmu ce, Abba ni yar da ka bani kawai ka min gata, idan ka ga na dawo na butulce maka, ka girmama dalilin haka, Abba ni ba iya y'a ka bani, rayuwa ka kara min domin na kara akan nawa. Abba iya wannan alfarman fa ka min na bani abinda kuka fi so, yafi kome min dad'i nasan da Iyayena suna raye sai sun fi kowa farin ciki. Amma nasan Kakanina kowanni bangare suna cikin farin ciki. Na gode na gode!" Ya fada yana kara damke hannuna, hawaye ne ya shiga zuba min tun daga fara maganarshi, wani irin so yake min haka? Kamar yasan tambayar da nayiwa kaina ya cewa Abba.."Abba ni ba so ya kawo ni gare ta, gaba da kaunarta ya kawo ni gare ta! Abba ina kaunar Yarka ina kaunarta sama da kaunar da nake mata, ita din wata bangaren rayuwata ce." Addu'a Alhaji Sa'idu ya rufa da shi, haka Aunty Hindatu ta fitar da ni, mutumin nan yayi confessing yadda yake kaunata, ya faɗa abinda yake ranshi abinda na jima ina jira, da muka fito aka fara hoto, ban tab'a gani ko ji a rayuwata akwai irin kaunar da yake min ba, hatta a wurin hoton kowa ya shaida shin kaunar kauna yake min, haka yake kare ni, tare da kallona lokaci zuwa lokaci. Yana murmushi. Idan ya ga kamar xan yi kuka, rike hannuna yake yayi ta murzawa, murmushi yake min ko ya saka bakin shi a kunne. "Kada ki yi kuka!" D'ago kai nayi ina kallonshi, shima murmushi. Wani irin kuka ne yake zuwa min, amma haka nake shanyewa yaddA muke hoto da dangi, kafin nayi da yayuna mata, ina tsakiyarsu Aunty Munah tayi missing na Bauchi koda yake a lagos akwai dinner. Kuma ta ce zata ta can, haka ba koma aka yi min da Yayuna maza musamman Ya Ado da na kwantar da kaina arm dinsa ina kuka, sannan aka yi min da shi da Ya Ado, sun saka ni a tsakiyarsu. Kaina yana kafadar Ya Ado, shi kuma yana rike da hannuna. Murmushi yake. Sannan aka gama ya rike hannuna yana faɗin. "Sai yaushe zan kuma ganinki?" Ya fada yana murmushi, "Malam dalla sake ta bayan rungume ta da ka gama a gaban Jama'a." Inji Ubaid, haka ya kyale ni. Wurin karfe daya aka gama shirya ni cikin wata laffaya, danginsa da suka zo aka basu ni tare da tsaraba, Yadiko da take cikin tafiyar ta shiga parlourn Abba ta fito da ni,

Mama kin fitowa tayi don itama zuciyarta yayi rauni, a hankali na kwace na wuce dakin Mama da take uwar daki ta zauna tayi shiru, rungume ta nayi ina kuka. "Mama ki zo muje!" Murmushi tayi tana shafa bayana. "Kada ki damu zan zo na ga gidanki, idan turaki ya miki laifi ko gaya min zan ɗauki mataki akan shi."

"Ke bana son sakarci, Mama kyale ta mu tafi! " Inji Ya Umar, da hannu tayi mishi alama da ya tafi, ta cigaba da buga bayana, can Aunty Hindatu ta shigo ta mata alama ta tafi. Sai wurin karfe biyu saura sannan ta ce min. "Muje ki tafi gidanki in sha Allah!" "Mama!" Hannu ta saka min a baki tayi, tare da riko hannunta muka fito ta mikawa Yadiko ni, "Ubangiji ya baki zaman lafiya da zuriar dayyiba, ya albarkaci rayuwarku, Rahama da Ni'imar Allah ya lullube rayuwar gidanki, Allah ya shirya zuriar da zasu zo bayanki." Haka tayi ta min addu'ar har wurin motar da zan shiga, kafin a tashi motar na rike hannunta, murmushi ta sake, sannan ta cire hannunta tayi musu alama su tafi ina ji ina gani aka raba ni da gidan, ko aurena na farko ban ga wannan gatar ba, domin Ya Tahir mota guda ya dauka wa dangi bayan wanda gidan ango suka kawo, aikuwa dayawa sun bi motar domin kuwa sun zata a can zan zauna. Duk da akwai gida a can, amma ni da Gombe maybe sai ko sallah ko wani abu, ba ƙaramin kuka nayi ba, tafiyar awa biyu tare da rakiyar sojoji da yan sanda muka isa garin Gombe, an karbe mu da hannu bibbiyu, abinci aka kawo mana, muka yi sallah da ya wuce muna, sannan aka hada min ruwan wanka na shiga nayi aka kawo wani lace wanda aka yi mishi dinkin doguwar riga yayi kyau gashi fari tas, sannan mai kwalliya ta zo ta min kwalliya wurin karfe hudu da rabi aka fito dani zuwa kofar fadar Gombe, aka yi kilisa, domin an bashi dan malikin Gombe. Yadda aka tsara hawan yaji kyau ga shi ashe tun jiya aka bashi sarautar aka yi bikin, sai karfe shida muka dawo gidan. Anan Gombe sun yi yar karamar liyyafa, yayi kyau ba na wasa ba. Da na dawo dakin dakyar nayi barci domin bai taɓa min irin wannan abin ba, sai wannan karon magana yake faɗa min masu nauyi da saka jin kunya, don haka naki biye shi, karshe yaja can yana baro min magana har nayi barci, tun da muka yi sallah asuba, na kwanta na gaji sosai. Wurin karfe takwas muka tashi nayi wanka na saka wata Holland, sannan na shirya bayan na saka Aunty Innah ta daura min laffaya muka fito zuwa parlourn aka shiga dani cikin gidan na gaida manyan gidan suka saka min albarka, sannan muka dawo muna karyawa waɗanda suka rako ni suka fara shirin komawa Bauchi muka fita nayi musu sallama sai Godiya suke, bayan sun tafi Aunty Raliyah take cewa. "Gaskiya Mijinki nan yayiwa bikin nan shiri na musamman, kowani mutum daya ta samu kyautar dubu hamsin da jaka na kayan biki." Murmushi kawai nayi ba tare da nace kome ba, har zuwa lokacin da na gama karyawa, ya shigo sanye da wata yadin material na kasar Sweden sai daukar idanu take, yana shigowa ya gaishe su sannan ya ce min.. "ko zaki sauya kaya mu shiga kunyi hoto da yan gidan." Yadda ya tsare ni da idanun taya zan ce mishi a'a, haka na koma cikin dakin na saka wata shadda na fito, da babban mayafi sai takalmi da pose muka shiga cikin gidan aka yi ta hoto da manyan gidan har da kannen kakanshi, sannan ya riko hannuna muka nufi wani gida wnada ko bai gaya min na san nan ne wurin zaman mu, ashe akwai mutane a gidan mai kwalliya da mai taya ni sauya kaya, haka muka yi ya hoto har ya kira su Aunty Hindatu suka zo aka yi da su, sannan aka fita. Ina zaune a gefenshi har kafad'arshi yana gogan nawa, waya yake hannunshi yana cikin nawa. Yana gama wayar, zuba min idanu. "Wa na kama?" Ya fada yana sumbatar goshina. A hankali wasu abubuwan da zuciya ta jima da binne su, yau ita Mr Turaki yake tono min, tare da jefa min kwadayi da son na kasance da shi, tabbas kowani namiji da yadda yake daurawa mace karatunsa. A wannan ranar Mr Turaki ya daura min wani karatu me nauyin dauka. Domin sai yanzu na fahimci yadda mace take ji idan ta hadu da shu'umin namiji, musamman wanda ya san yadda zai zautar da zuciyar mace, dakyar na iya kame kaina tare da fara ƙoƙarin kwace kaina, ina hakki tare da niman mayafina hawaye na zuba min. Da sauri na dauki mayafina zan fita ya fisgo ni. "Ba jikinki nake bukata ba, amma na gaya miki kada ki zo gare ni da turarenki nan domin Allah ya gani duk lokacin da zan ji kamshin ki tow ina jin mafi kololuwar buƙatar kasancewa da ke, kada ki yi kuka kin ji domin akwai ranar da zaki roki na kyale naki........ [12/16/2025, 8:08 PM] Maman Walid: 18

Da sauri na bar parlour ina gyara zaman mayafina, ina zan iya irin wannan rashin kunyar, shi bai da kunya bakiɗaya da aka zo rabon ina ga nashi bawa wasu aka yi, " hi Mrs Turaki jira ni na kai ki ai baki isa ki tafi ki bar ni ba, salon wani dodo ya kama min yar Chika ta!" "Chika?" Na kara maimaitawa a raina nace. *Allah yasa ba wata kalmar batsa ba ce!* Domin shi duk abinda ya fito a bakinsa fada yake, sarkafe hannunmu yayi ya d'ago tare da sumbatar hannuna ya ce min. "Muje ko? Chika na!" A hankali nake binsa yana kallona yayi murmushi. "Sai naji kamar mu yi ta tafiya haka, babu kowa a tsakaninmu. Babu wnada zai dame ne mu, babu tashin hankali." Riko ni yayi na dawo gabanshi, ya hade goshinmu wuri guda. "Ina ji a raina ni nafi kowa sa'a a wannan rayuwar duniya, ina kuma rokon Allah yasa kada nayi danasanin akanki har karshen rayuwata." Hannunsa naji akan kuguna na bude idanuna. "Ke hakkina ne fa, da zaran na taɓa ki sai ki razana kamar wacce aka ɗoɗɗana mata wuta, ki sani Mijinki jarumi ne ahto ba zan yarda ina taɓa ki, kina zabura kamar wacce aka saka mata lantarki ba." Wayarshi ce tayi kara ya ɗauka yana faɗin. "Ok kuna airport kenan?" Take na ga fuskarshi ta sauya, a hankali na kai hannuna kirjinsa ina ɗan tab'awa, a hankali kamar rarrashi. Zuba min idanun, ni kaina ina jin abinda ake fada tsaki yayi ya ce mishi." As you wish!" Rigima suke da Kakanshi akan ya zauna a part din iyayensa musamman na mahaifiyarsa shi kuma yace ba zai zauna ba, shine ake ta kai ruwa shi ya nace sai gidansa. Kallon kwayar idanuna yayi kafin ya ce min. "Zaki iya zama a wancan jahannamar?" Lumshe idanuna nayi kafin na bude akanshi. "Duk inda ka kai ni zan zauna." Bakinshi ya kai tare da sumbatar goshina, "Muje su Auntynki sun tafi fa!" Zare idanun nayi ina faɗin, "me yasa suka tafi?" "Ji gulma da kika samu Mijinki, kika manta da wasu aunty a can!" "Ni ba ruwana kai ne ai!" "Amma yarinyar nan kin ga girmana, lallai ma dole na shiga lamarin nan ayi mana Shari'a akan wannan sharrin da kika min." Ya fada yana murmushi, har muka isa inda motar da xata mai mu airport an saka kome na mu, ya bude min na shiga sannan ya zagayo ya zauna a kusa dani. Rike hannuna yayi yana shafa lallen hannuna. "Kin yi kyau! Amma. Jiya don wulakanci kika yi ta kuka har naji tsoron kada Mama ta ce an fasa tarewar da sai na ce kowa ya tafi mun gode anan zamu cigaba da zama!" Kifa kaina nayi ina dariya, ashe haka yake da surutu, an kira shi ya kai sau biyar karshe kashe wayar yayi, "idan suka gama bidiarsu dole na dauke ki mu tafi honeymoon!" Murmushi nayi wato ina ga ko Radio sai zuba yake min, har muka isa airport ɗin Uncle Auta yayi ta mishi fada akan bata lokaci da yayi ya ce musu. "Ni fa bance a shirya wani biki ba, yawwa don da na san da wani bikin nan da na wuce honeymoon da matata ni bai dame ni ba, kowa ya zo ya kwashi gara yayi tafiyarsa ko Lunah!" Ya tambaye ni yana kallon fuskana, kasa motsi nayi Ubaid. "Amma kai dai daga dan iska sai kai, Allah yasa ka wuce bangon duniya ba honeymoon ba." "Tow ina ruwana, lunah kina jin yunwa na kawo miki wani abu?" Wato shi dai haka Allah yayi shi da bala'in niman magana, har muka shiga jirgin a wurin zama ne fa ni zan zauna da su Aunty Hindatu da Goggo Alti, sai Ummanmu, suka janyo ni na zauna a wurinsu. "tsayawa yayi ya ce musu, ku bani matata, ni na muku alƙawarin zuwa aikin hajji in sha Allah, muna sauka zan tafi da ita idan kafin a fara zan dawo muku da ita." Kallonshi nayi kamar zan yi kuka na dauke kai, yadda yayi ta tsara su har suka bada hadin kai, na sha mamaki. Kafin mu isa lagos ya shawo kansu, muna isa airport na lagos wata mota ta zo ta dauke shi da ni.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull