Kenza eBookz

ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 19

ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 19

ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 19: ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 19. Bayan tafiyarta sai ga ta tare da wasu mata kamar yan boko irin Lagos Alaja din nan, suka zo…

4,433 words

Bayan tafiyarta sai ga ta tare da wasu mata kamar yan boko irin Lagos Alaja din nan, suka zo yarbanci ta juya musu suka yi ta yin wasu abubuwan da ya sa na ce mata. "Hajiya hala baki da tarihin jahar da na fito ko? Ni yar jahar Bauchi ce, ina kuma alfahari da cewa ni namar kai ce ga kitse ga tauri, idan kika sake na saka ki a corner." Wani devilishly smile na mata, ina kallon cikin kwayar idanunta. "Kada ki saka na kai ki inda ba zaki ji dadi ba." Ina fadar haka ta bala'in shiga hankalinta, fita suka yi ita da kawayenta. Haka Yarta Mimi suka shigo kamar wani abin arziki, ta dauki Yarinyar sai da ta gama kallon yarinyar ta ce min. "Anya wannan jinin KUMO ce kuwa ban ga tayi kalar fatar Kumo Family ba."

"Ba mamaki an saba number ta yadda kika kasance daban a cikin kumo family, domin duk kumo muna da manyan idanun naki kuwa kamar ta kwad'i." Inji Jasminah tana kallon Mimi, sai tayi shiru, tana kallon yarta. "Yes kalle ni da kyau duk wani jinin kumo yana da dogon hanci dogon gashi, kai everything yaran kumo suna da shi hatta Boɗɗo da aka haifa jiya kalli gashi har yatsun hannunta sun nuna zata yi gashi, amma ke kuma ko goruba ys sallama miki rashin gashi, shima hasken fata baki ga lura cewa mai kike ta labtawa akanki ba." Duk Jarabar son ayi fada Jasminah ta sani, sai da ta kunyata yarinyar nan ta fita kuka, atow ka fada ne tsakani me baki mara kunya, haka ta fita daga parlourn, ni dai na zuba idanun ai kuwa can sai ga Hajiya Zeenatu ta shigo tana huci, kallonta Jasminah tayi irin kallon nan ne mara daɗi, zata yi magana na rike hannunta. Girgiza mata kai nayi ina murmushi, haka uwar ta gama zage-zage ta sannan ta fita a parlourn, abin bai yi dad'i ba domin Hajiya Khaulatu ta je ta ci mata mutunci wanda ya janyo katon tashin hankali a cikin gidan kamar zasu yi doke doke, dakyar aka gama lafiya Kannen Babanshi sun zo sun bani hakuri ni a lissafina kamar zasu kara biyo min ta baya ne, har muka dawo gida maganar ake nanatawa sai da Yadiko ta musu fada suka yi shiru, ashe wannan zuwan yadiko zama zata yi Umma zata koma Bauchi wai mijinta yana ta sintiri, duk sai naji ba dad'i. Haka na tura mishi sako, aikuwa washi gari sai gashi da akwati ya shigo da shi suka gaisa, da yake kayan da aka mana na sunar basu kawo ba, kome ayin parkage dinsa ne, haka ya kawo mata ya saka dubu dari biyu a kai, tare da da godiya, dukkaninsu da suka zo sunan sai da aka musu shatara na arziki, suna da kwana biyu suka bar Lagos, a ranar kuma aka kawo kayan Yadiko tayi ta saka albarka.

Yanzu nasan ina wanka wato Yadiko sosai take wanke ni, Umma ai ni nake yi da kaina, Yadiko kuwa haka ta saka shi nimo mata ganyen lim, tayi ta zane ni da shi da sunan tana min wanka, ai sai da naji kamar zan yi hauka domin wankan ya saka ni jin wani irin tsoro da damuwa, sati uku nayi wani irin kwari sai yanzu na fahimci wankar tana gyara min lafiyata, domin kuwa idan nayi barci sosai, yarinyar ma idan ta sha ruwan zafi tuni take barci sai dai kukan dare da rikici. Shima Yadiko take nuna min yadda zan yi, shima ganin Yadiko bata bada fuska sai ya kame kanshi ya daina nimana, abinci idan muka gama da ita xan jera zan koma daki yana dawowa zan zo na gaishe shi. Bayan nan zan koma daki shima haka ta ce min, sauran kuma yayi da kanshi.

Sakon kewar da yayi, wani abun da yadiko take kara burge ni da shi da ta fito kiri ta gaya mishi gaskiya tare da cewa idan aka gama wankar da kanshi zai fahimci dalilin haka. Sai bai kara nuna takura da yake ciki ba, haka muka cika wata guda, ranar Jasminah suka zo mana wuni ita da wata yarinya baka kyakyawa da ita anan take gaya min budurwa Taj ce, yarinyar ita ta yi mana abinci, da dare suka tafi gida, ya rage saura kwanaki goma yadiko ta sauke mana wanka. Haka yayi ta sayayya yana kawowa gidan, idan na tambaye shi dalilin haka sai ya ce ina ruwana ranar da na mishi magana ban gane me yake nufi ba, budar bakinsa ya ce min.. "aure zanyi ko akwai matsala ne?" Daga ranar ban kara mishi magana ba, ana saura kwanaki uku ta ce min. "Kina takure ko?" A kunyace na ce mata. "A'a Yadiko!" Murmushi tayi ta ce min. "Ki kula da kanki da Yarki, idan kin gama wanka jini ya dawo, ki kula da kwanakin kyankyasan kwanki, domin zaki kuma ciki. Ki kula da kanki da Yarki don kin ga tana da lafiya da kuzari don Allah kada ki dauko wani cikin saboda wannan rawan kan da kuke da shi zaku iya samun wani cikin nan kusa wallahi." Ni dai ban kara magana ba, kuma ban kara motsi ko wani abu ba, sai dai na kara fahimtar cewa shi fa kome na rayuwa yana tsarin Ubangiji, ranar da muka cika kwanaki arba'in, muka ajiye wanka, sannan shi da kansa ya ce mata. "Yadiko ki yi hakuri wata sati sai ki tayi don Allah!" Bata so ba, amma haka ta hakura.

Tafiya ce ta kama shi har na tsawon kwanaki biyar, a wannan lokacin yadiko ta shiga hada min wani hadin gyaran jiki da kanta ta shiga kasuwa tare da rakiyar Aunty Munah da tazo min, kamar nayi kuka haka tayi ta haɗa min magani har da tsumi tare da maganin sanyi ta hada min na fara sha, sai nayi ta fitsari na tsawon kwanaki uku, kafin ta bani gumba da zuma na cigaba sha, ranar da ya dawo tare da ita muka sha aiki da Aunty Munah, yana dawowa ya shigo suka gaisa, a daren ashe ta kira Ya Ado ya zo ya dauke su, sai gashi nan kuwa ya zo suka tafi sai da nayi kuka don takaici, shima bai san sun tafi ba, fitowa yayi ya ga ina kuka. "Lafiya?" "Sun tafi mana!" Shiru yayi kafin ya ce min. "Sorry zan bisu kin ji!" Gyada kai nayi ya wuce wurin da na ajiye yar ya dauke ta, yana faɗin. "I miss you Mommy." "Nifa!" "Allah ya baki hakuri duk nayi miss dinku." Ya rungume ni yana murmushi. Sai da naji ina ma rayuwarmu ya tsaya haka kada wani ya shiga cikin rayuwarmu, kada wani ya hana mu farin ciki.

"Muje kaci abinci, sai ta tafi sallah isha." "Bani tea na sha sai na fita, idan naci ba zan mori kaina ba!." Haka kuwa aka yi na wuce na cigaba da hada mishi, sannan nan kawo mishi na zauna ina kallonshi, ya sha yana kallon yarshi. Yana gamawa ya ajiye ya nufi masallaci, nima nayi a gidan bayan na idar, na kara gyara jikina na sha zuma na, na gyara jikina da turare. Dakinsa na wuce na gyara dakin kayan da ya dawo da shi, na shiga cirewa. A hankali na gama sai dai me lipstick na samu ban tab'a ba. Na mai da kome wurin zamanshi da zan wuce na ga wayarshi tayi haske. Ban yi niyyar dubawa ba, na hango sunan Adaa. Komawa nayi na shiga duba wayar ya saka mata security code yaushe ya fara saka security code a wayarshi? Abin sai ya bani mamaki nayi ta kallon wayar hoton yarshi ce a kai, nayi kasa da kaina ina mamaki. Kafin na sare ban kara magana ba, na ajiye na fita. Har ya dawo ya ci abinci, muna ta hira sama-sama. Tashi yayi ya shiga cikin dakin, bai fito ba nima kuma ban yi wani yunkurin zuwa dakin ba, na wuce zuwa dakina na gyarawa Yarinyata wurin kwanciya, na kwanta barci ya dauke ni. Har zuwa sha biyu ko zai zo wallahi ban Ganshi ba, karshe na tashi na rufe kofar na kwanta ina kuka, sai wurin karfe daya da yaji kukan yarinyar ya zo yana buga kofar ban bude ba, haka ya gama buga kofar ya hakura. Washi gari tun asuban fari na mata wanka na bata nono, na fita na hada kome na ajiye mishi nasan ba zai fita ba, amma sai na zabi shiru na zuba mishi idanun, wurin karfe goma na safe ina barci ya shigo dakin, ganin ko ina tsaf-tsaf sai ya sauke ajiyar zuciya sannan ya kwanta a baya, duminsa ne yasa na juya ina kallonshi. Ban wani damu ba amma zai san ya tab'a har mutanen Bauchi. Yadda nayi kuka shima haka zai koka........... [1/8, 7:41 PM] Maman Walid: Mikewa naso yi amma ya me da ni, kallonshi nake shima kallona yake. "Nayi miki wani abu ne?" "Me ka gani?" Shiru yayi yana kallon yadda na haɗe rai na fara ƙoƙarin tashi ya mai da ni. "Wai me ke damunki ne?" A gajiye na ce mishi. "Ban shirya wani haihuwar ba ne, kuma naga kai kana da damar karo wata macen ni dai oho!" Tun a zamanmu na fahimci shi mutum ne da bai maka dole akan abinka, shiru yayi yana cike da mamaki, ko yayi tunanin yayi amfani da karfi ne, ai kuwa dai gashi ya saka min karfi na ce mishi. "Don't try rape me!" Yadda nayi maganar ya kara kokarin aiwatar da abinda nake hangowa a kwayar idanunsa. Cikin rawan murya na ce mishi. "Ex dina bai taɓa using karfinsa a kaina ba, bai taɓa ba bai taɓa amma kai da yake kana da kudi kuma kana da kyau yan mata zasu iya bibiyarka har ka bibiye su, karewa har da lipstick a kayanka fine kayi yadda kake so da ni, kayi tunda godiyar da zaka min kenan a kwanakin haihuwar Yarka da take da daraja sama da kowa kayi min fyade kayi Bilal ka yi yadda kake so da ni!" "Ke wai meye matsalarki ne?" Watsa mishi harara nayi na dauke kai, haka ya mike tare da cewa. "Wai me nayi ne? Idan kuma akan abinda ya faru jiya ne sorry." "Sorry fa!" Na fada tare da fashe da wani irin kuka har cikin raina, naji wannan kalmar sorry Sorry wannan kalmar ya min ciwo, kuka nake har Nana ta farka kuka nake itama kuka take, haka ya fita zuwa kitchen ya dauko nonon da muke tarawa, ya dawo ya zo ya saka a abin dumama mata, yana yi yana kallon yadda nake kuka, wayarshi da take kusa da ni tayi ƙara naga Adaa, sake kallonshi nayi wani irin baƙin ciki. Dauka yayi saura kiris ya sake min yarinya ta fadi na fasa ihu. Ina cewa." Bani y'ata womanizer" shiru yayi yana kallon yadda nima maganar tayi affects dina balle shi da na gayawa, na kuma saka hannu na amshi yarinyata. "Ka je wurin budurwa wacce take da abinda bani da shi, ka je ita babu abinda ya ragu a tare da ita, tana da kome full options, ka je bata haihu tayi bellypot ba, ka je bata bude kamar ni ba ka je bana son ganinka, kuma ka sani tafiya zan yi gidanmu wallahi ba zan iya zama da kai ka kashe ni da yata ba." Tunda na fara maganar har na kai karshe bai ce min yi hakuri ba, bai tanka min ba bai kuma ji a ransa ko a fuskarshi abinda nake ya b'ata mishi rai ba, duk fadar da nake kallona yake, karewa abinda yayi min ya saka ni frozen shine tab'a goshina da wuyana, sai kaina jin babu inda yayi zafi, sai ya rungume ni tare da Yar. "Baki fita kaina da zan fara hango wata mace ba, na gode sosai da kika nuna min kishina, ban tab'a zatan zan ga kishina a ƙwayar idanunki haka ba." Wani irin kuka ne ya kara kwace min na ce mishi."Fita min a dakina!" Na nuna mishi hanya, a hankali ya nufi hanyar fita, kusan wannan yayi breaking duk wani zaman lafiyan gidana, duk yadda yaso na zaffafa shima ya tattara lamarin ya zuba min idanu. Nima haka da yayi sai ya kara tunzura ni. Na kara jin zafinsa.

Muna cikin wannan yanayin, ranar da muka cika sati daya da tashin hankalin. Yadiko tazo nayi ƙoƙarin boye kome, amma da yake wanda ya haife ka, ya fika wayon duniya sai da ta yi magana domin na zube sosai saboda rashin barci da b'acin rai, tayi ta tambayata ko da wani abu ne nace mata azumi nake kawai na bar zancen, haka ta wuni domin washi gari zata koma gida, sai da zata tafi ne na fara kuka ni kawai zan bita, haka da nayi yasa ta fahimtar akwai abinda nake boyewa, haka tayi ta kallona ta ce ko da wani abu ne nace mata Babu kawai zan bita gida ne. "Ki yi hakuri nan da kwana ashirin zai kawo ku, lokacin Nana tayi wata biyu kenan!" Wannan maganar da ta gaya min kamar na mutu, domin nasan ba zai kai ni gidan ba, haka nayi ta kuka har ta tafi. Shima da yake baya dawowa Sai wurin karfe sha biyu saura, haka ya same ni a parlourn ni da Nana na sha kuka har na godewa Allah, tunda ya shigo yaji ajiyar zuciya na a kai a kai, har ya wuce ya dawo ya ajiye jakarshi ya zauna bayan ya kunna wutar parlourn, idanuna ne ya sauka akan kwalar rigarshi shatin jan bakin mace, "Lubnah!" Tashi nayi na bar shi a wurin, ina shiga dakina ns rufe kofar dakin ban kara kula shi ba, na yanke duk wata hanyar da zai samu damar min magana.

Washi gari. Wurin karfe biyu na rana Hajiya Zeenatu suka zo ita da wasu mata sai wata very pretty lady, fara ce tas har kana hango koren jijiyar jikinta, tunda suka zo Hajiya Zeenatu take min murmushi, kallonta nayi a hankali na gaishe ta kafin na shiga kawo musu kayan tab'awa. Hango karfen da nake motsa jiki yarinyar tayi ta ce min. "Na ki ne ko na, Sir Turaki?" "Both!" Na fada ina kallonta, murmushi tayi tana magana da yarbanci. "Au da gaske ya saya miki irinsa, ai na gaya miki." Kawai sai naji kirjina tayi nauyi. Sai nayi kamar ban ji su ba, can yarinyar ya ce min. "Ina Yata?" Kallon gadon kwanciyar yarinyar da muka saka a parlourn nayi ta nufi wurin tana faɗin. "Alaja kin san da ni ce uwar Yarinyar nan!" Yanzu na fahimci abin sarai, na kuma kara hango abinda take nufi, sai na sarke hannuna a kirjina ina kallonsu. "Wannan ita ce Adaa yarinyar da Turaki yaso ya aura!" Murmushi nayi na ce musu. "Ina ta shiga na mata overtaken?" Na fada bayan na gyara zaman da nayi akan kujera. "Kamar ya? Bai gaya miki labarinta ba ne?" Inji Hajiya Zeenatu, "bai gaya min ba saboda ba ta da muhimmanci a rayuwarsa, da tana da shi da ba zai manta da ita ba,sannan da kowa yasan da zamanta." Yadda nayi maganar ina murmushi, ta ce min. "Yanzu ai ta dawo mai wuri tazo." "Hajiya ni sai nake ganin kamar kishin da kike da Uwar Bilal ne ya dawo kaina, domin dai na ga Bilal dan tsohon mijinki ne, sannan uwarsa ta tsamo ki daga duhun talauci ta kawo ki cikin hasken arzikin, yanzu babu ita babu wanda ya baki damar shiga kumo ni Lubabatu ina ruwa da ke? Ban ga dalilin da zai saka ki shigo min rayuwar gidana ba. Idan kuwa kuka ce zaki shiga rayuwata, zan takura miki zan kure miki gudu zan tabbatar kowa yasan yadda kika dame ni, ita wacce kika janyota gidana idan naso sai na rufe ku na watsa muku ruwan zafi, wannan fatar da take nunawa mijina, sai na kara toyashi yadda zata cigaba da bibiyar lamarin Mijina, Hajiya focus matsalarki ki fita hanyata da gidana, turaki bai shirya auren wata ba, idan mijina ya shirya auren wata ni da kaina zan tsaya mishi domin nasan ya shirya. "

Dariya tayi ta ce min." Yarinya kenan, ni da ke shege kafasa, Allah ya baki sa'a. Ita wannan yarinyar Uwarsa ce ta nime mishi aurenta, kuma akwai document na yarjejeniyar haka, aure zai yi domin nice a tsakiyar." "Hajiya kenan Allah ya baki sa'a, ya kuma bamu lafiya da nisan kwana. " Daga haka suka nufi hanya yarinyar ta ce min. " Da alamu baki ga sakona ba ko?" Murmushi nayi na ce mata. "Ba mamaki ni nawa sakon zai zo lokacin da ya dace." Daga suka fita, raina a idan yayi dubu ya b'aci.

--- " Alaja ni fa ba zan iya ba, Yarinyar nan tsoro take bani kin ga confidence da na hango a cikin idanunta?" Murmushi Hajiya Zeenatu tayi ita fa dole yadda tayi a gidan Uban turaki da Mijinta Alhaji Mudansir take so tayi a gidan Turaki, ta ce mata. "Kwantar da hankalinki, duk abinda take fada karya ne, waye bai san yadda ta samu Turakin ba, asalin asiri suka mishi. Idan har su bokonsu kasa yake bugawa zan nuna mata nawa akan dutse yake." Ita kan Adaa sai ta shiga damuwa domin kuwa bata son tashin hankalin da zai dagulawa ranta.

*** Bayan tafiyarsu na rasa yadda zan yi. Ko yan uwana bana son su san halin da nake ciki, don haka na kira Mama. Cikin kuka nace mata. "Mama Turaki!" Shiru tayi kafin ta ce min. "Ki dawo gida to! " Shiru nayi kafin na ce mata. "Ba fada muka yi ba, asalima narasa yadda xan yi ne?" Murmushi tayi, ta ce min." Gaya min me ya haɗa ku?" " Mace yake kulawa." " Kina sonshi?" Cikin shashekar kuka na ce mata. " Mama shine mahaifin Nana A'ishah Boɗɗo, shine ya so ni tun ban san ciwon kaina ba!" Murmushi tayi ta ce min. " Good to me kike so? Gaya min me ya faru?" A hankali nake gaya mata abinda yake faruwa, shiru tayi kafin ta ce min.. "Lubnah!" "Na'am Mamana!" "Mijinki ya shiga tarkon matar ubansa duba da yadda ta kawo miki yarinyar gidan. Mijinki babu wata mace a gabanshi. Domin ko juma'a da ta wuce yazo Bauchi. Kuma ya zo har gidan nan, abu daya nake son na gaya miki, Mijinki yana sonki yana girmamaki, kada damuwar wasu ta dame ki, sannan ita uwar Mijinki, zan gaya miki abinda zaki mata, amma ki nutsu da kyau. Ba mamaki mijinta bai san me take yi ba, idan kina son nasara akan mutane kaima tunaninka kake budewa sai ka tafi da daidai da kai, kishiya take so a miki. Mijinta Uban Mijinki ne ke kuma yarsa duba da yadda suka dawo jikin Mijinki, sai ki san hikima da dabara. Ba a ciwon mummuni sau biyu a wuri daya don haka ba zan kara barin wani ya cutar da ke a gidan aurenki ba." Cikin shashekar kuka na ce mata. " Mama to ya zan yi? Matar nan shaidaniya ce, na rasa yadda zan yi da ita!" " Ki hada da azumi zan miki sadaka anan, in sha Allah zata barki miji ai naki ne, idan Turaki ya tashi aure ko kina so ko bakya so mune nashi kuma zamu tsaya mishi, amma yanzu lokacinki ne da Yaranki ku samu soyayyarshi da kaunarshi, shine babban abinda nake nufi da fata, sannan kin san ni bana bin boka ko Malam Allah nake bi tare da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, don haka ki cigaba da addu'a mu nime tsarin Allah akan duk wani mai sharri!" Sai naji kamar nafi kowa dace a duniya da na samu Mama a matsayin Uwata, ta tsaya min ta kuma sa na daina kuka. Wani abun da ya kara bani mamaki yadda ya iya zuwa Bauchi bai gaya min ba, sannan kuma bai kamata karana ba, asalima abin da yake gabanshi yayi sai na ji tausayinsa............ [1/12, 1:52 PM] Maman Walid: 39 Bai kai karata ba, sannan bai nuna min ya damu da abinda nake yi ba, asalin adalci Yayi min domin ni dai ba san yadda zan yi da abin kunya ba, haka yasa nayi shiru ina sauraren Mama. Har ta gama min bayani sannan muka yi sallama, bayan isha da ya dawo ina kwance a dakina ya leko zai fita da gaggawar. "Zaka tafi wurin Adaa?" Cak ya tsaya yana kallona. "Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya." Shigowa Yayi min a zauna zai dauki yar nayi maza na kwace Y'ata. "Me yasa kike min haka? Ni ma fa y'ata ce, sai ki hana ni daukarta idan na zauna bakya kula ni gaya min me nayi miki da zafi?" Hawaye ne ya zubo min na ce mishi. "Ka damu ne da mu? Ai dmuwarka yana kan Adaa." "Ki tsaya mu yi maganar gaskiya." "Wani irin maganar gaskiya bayan na samu jan bakinta a cikin kayanka, na biyu na ga sakonta yadda ka mata a daren da kuke tare na ga layin jan bakinta a jikin rigarka, sannan ta zo gidan nan ita da Matar Kaduna tsohuwar Step mother dinka me ya rage da ban gaya maka ba? Akwai ko babu? Duk abinda na gani shima ba hujja ba ne? Zaka iya amfani da ita amma ka sani ni da kai Y'a mace muka haifa ka rufa min asiri kada a lalata min y'a wallahi ban tab'a zina...... " Ya dauke ni da mari wanda ya janyo nayi shiru tare da rike fuskana. "Marina ka yi?" Na tambaye shi, ina kallonshi hawaye na zuba min daga idanuna. "Na cancanci kyautar mari daga gare ka?" Kura min idanun yayi idanunsa sun yi jajjur, tashi yayi ya bar gidan bakiɗaya na sha kuka, kamar ya bana son na kira Ya Ado domin zan d'aga mishi hankali a daren na sayi ticket na Jos, kamar ya san abinda nake shiryawa, da safe sai gashi tare da Kakanshi, suka shigo na gaishe su. Na koma dakin na dauko musu yar da na gama shiryata na mikawa Kakar ita, sannan na koma dakin na cigaba da hada kayana na fito da su waje, na ajiye. " Y'ata ina zagi da wannan kayan?" "Baffa gidanmu zan tafi" shiru yayi kafin ya ce min. "Gaya min me suka miki shi da su?" Ai kuwa na fara kuka, na rasa yadda zan mishi bayanin wulakancin da yake, ganin har lokacin kukan ya ki karewa Ya ce mishi. "Allah sai ya bi mata hakkinta, domin ka zalunce ta sosai." Yadda yake mishi fada ba nan yake fita ba, har da cewa. "Ban da ita wacece zata zauna da kai tsakaninta da Allah ba tare da ta tuna cewa kai wani ne, tayi maka alfarmar zama da kai har da haifa maka zinariya me yasa zaka wulakantata?" "Datti rashin kunya take min wallahi ban mare ta don bana sonta ba, ranar ta kira ni manemin mata jiya kuma tana ƙoƙarin kirana da maxinaci kawai don ta samu wani abu da tabbatar mata muna tare Adaa!" "Ban rabaka da yarinyar nan ba?" "Amma Datti!" "And so what? Abubuwan da kake yi yasa take zarginka, ai nima ba yau na ce ka rabu da ita ba nayi karya? Bari ka ji idan ka sake ta bar nan ta je har gidan dan uwanta ko iyayenta wallahi ba zan je biko ba. Kuma ba zan tab'a shiga lamarinka ba, ba ruwana da kai, wallahi xan gayawa Kakarka. " "Datti don Allah kayi hakuri!" " Ita zaka bawa hakuri domin ita ka cutar matarka ta rufin asiri babu wanda ta kaiwa kukan kayi mata laifi bs kasan ana jiran a ga ta kuma kuka akanka ba ne a ce damar ba sonta kake ba." Sai naji bawan Allah nan ya biya ni, cikin shashekar kuka na kara kai min kukan na ce mishi." Baffa Mommy Zeenatu ta ce matuƙar tana raye sai ta aura mishi Adaa ni ba auren ne bana so ba, a zo a raba da Y'ata, ni na yafe mishi duk abinda yayi min Daada mutumin kirki ne, kawai ya je yaji auren shi ni ban damu ba kuma ban yi bakin ciki ba, abubuwan da yake yi kada wata rana a cutar min da ita tunda har gidanta yana zuwa da sunan soyayya duk anan suka gaya min. Kayi hakuri Alhaji amma lokaci yayi da dole na hakura da zama da shi." " Ita Zeenatu ta ce miki zai auri yarinyar ko? " "Eh tace akwai baiko da Mahaifiyarshi ta tabbatar za a yi aurenshi. Allah ya basu zaman lafiya gara na tafi wurin Iyayena sun fi kaunata ba xan zauna bakin ciki ya kashe ni ba tunda ta gaya min cewa budurwanshi ce tun fil azal tun Haihuwar Nana take gaya min bani da mazauni a cikin KUMO FAMILY, tunda na.fara da y'a mace, ni ina son abuna ganin haka yasa take tunanin gara ta haura mishi adaa saboda na haifi y'ace Mace Allah sarki ina son abina koda shi baya so kuma naga lamarin maganarta gaskiya ce domin ya sake min kula da yarinyar duk ya koma nawa wanda a baya tare muke kome Innalillahi wainnalihir rajoun ina jin zuciyata kamar zata buga." Kafin wani lokaci na tashi karamar bom ai daga shi har kakanshi hankalinsu ya tashi haka ya, kai kakan gida ya dawo yayi ta rarrashina da gaya min cewa babu wata mace after ni, daga karshe dai wannan abinda ya janyo rikicin aka janye ya min alƙawarin ya fita sabgar yarinyar,

A can Family house ɗinsu kuwa Alhaji ELYakub Kumo ya tara su yana tambayar su meye matsalarsu da Auren Turaki, domin ya fahimci ba turaki ne basu so ba, shine kawai suke yiwa kafar angulu. A gaya musu rayuwarsa suke bukata ko me? Ya kara cewa. " Nayi ƙoƙarin na muku adalci, amma Zeenatu kin saka kafa kin shure kun zata tsoronki nake ji da na kyale ki? Ba tsoronki nake ji ba, Yara mata biyu kika haifa mana bai saka mun miki gori ba ina ruwanki da rayuwar Matar Turaki da ita yanzu ta fara haihuwar? Ki jira idan ta kara yin mata macen sai ki ce ta gaje ki, da mace da namiji duk muna so, Mudansir ka gayawa matarka idan haihuwar maza banza ne me yasa ke baki yi ba? Ke ni da Dadda mun mijinki ya kara aure? Ina ga kin zo lokacin da dole ki fahimci kowani mutum da wanda Allah ya ke sakawa ya tsayawa Mudansir ka tafi Kumo akwai jikar Kawunka Alhaji Umaru ka aurota na musu magana yarinya ce shekarunta ashirin da daya, tana jami'a idan ta shigo Allah ya bata Yara maza sai mu ga yadda zaki yi."

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull