ALAKAR ZUCI BOOK 2 - Chapter 20
ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 20: ALAKAR ZUCI BOOK 2 Chapter 20. " In sha Allah Baffa an gama zan je na dubata?" Wani irin dukar kirjinta tayi tana faɗin."…
2,096 words
" In sha Allah Baffa an gama zan je na dubata?" Wani irin dukar kirjinta tayi tana faɗin." Sai kayi Auren Baban Mimih?" " Ai ba yau na gaya miki, ki fita harkan iyalin Turaki, ban san me yasa kike son tashin hankali da rashin son zaman lafiya, tunda ni s matsayina na Mijinki baki ji maganata ba. Ina ga idan mahaifina saka ni ai dole nayi tunda bani da kamarshi, kuma ban isa ya gaya min na ki ji ba, don haka ki je ki yi yadda kike so, Baffa in sha Allah zan je ka ganta." Shima dama kamar ta ishe shi, hanyar hukuntata yake nuna, ai kuwa yan uwansa suka goya mishi baya, hauka tuburan tayi tana faɗin. Wallahi babu wnada ya isa ya mata kishiya. Ba wanda ya bi ta kanta kuwa. *** Alhamdulillahi da muka shimfida zaman lafiya s gidanmu, bakiɗaya ya tattara kome ya ajiye a gefe. Ya saka ni da yarshi a gaba yana bani wani irin kulawa, da ga na gaya mishi period ɗina ya dawo ya ce shi ba ruwansa idan na kara samun ciki yana so ko Yara dubu ne. Jin haka yasa na fara kaucewa tsarin domin kuwa ina lissafin kwanaki da Ovulation dina, a lokacin kwanakin ina kiyayyewa. Kuma Alhamdulillahi sai gamu har kusan wata shida lafiya lau. Sai a lokacin ya shirya mana zuwa gida, gashi yarinyar tabarkallah, ta Gombe muka isa, murna kamar Sarah da mamarsu dauke mu,. Kwananmu biyar anan naji labarin Auren Jasminah da Kawunsu. Nayi murna ai kuwa ka kirata ina ta tsokanarta. Tayi dariya anan Kano suka hadu da mijin. Yana da mata biyu ita ce ta uku, wani ikon Allah bai taɓa haihuwa ba sai tarin albarka da Allah yayiwa rayuwarsa sannan yana rike da Yaran riko a gidansa kamar nashi.
Kawunsu kuwa ina komawa Bauchi na samu labarin a bakin Daada ya gaya min ai sai na kwantar da hankalina, gidanmu can dutsen tanshi muka sauka. Yarinyar da muna isa aka dauke ta, basu dawo da ita ba sai La'asar likis, na sha kulawa wurin Mama da Yadiko, da nake bata labarin abinda ya faru mamaki take tayi tana jinjina al'amarin. Kafin muka samu natsuwa da Isha muka wuce gidanmu da aka gyara shi, anan muka kwana washi gari Ya Sani ya kawo mana abin karyawan daga gidansa, nan yake gaya min kamfanin Turaki na nan Bauchi shine yake kula da shi...... [1/12, 1:52 PM] Maman Walid: Ba zan iya cewa dukkanin halayen turaki nawa akwai na banza ba, amma zan iya bada labarin shi din mutumin kirki ne mai adalci, shi din Gwarzo ne jajjirtaccen jarumi ne, da yake tsaye akan gidansa. Bai yarda ni d yarshi mun yi kukan wani abu ba, alakulli halin yana tsaye har kan yan uwana. Danginsa ma suna matuƙar son ya zauna a tare su, satin mu biyu s Bauchi muka wuce Abuja inda Taj yake muka yi sati daya, sannan muka wuce wurin Dangin Mahaifiyarshi. A can muka fara azumi sannan muka dawo gida. Gida lokacin watan yarinyar tara, aka yi sallah anan Lagos muka yi, sannan aka yi bikin Alhaji Mudansir Kumo da yar danginsu mai suna Barakatu, yarinyar Fulani kyakyawar gaske.
Haka muka kasance s hidimar duk inda aka ganmu haka ake rige-rigen daukar Yarinayr da take kafad'arshi, wani ikon Allah dafa Hajiya Zeenatu da yarta Kowa jikinsa yayi sanyi, bayan bikin turaki ya biya min aikin hajji na tafi, lafiya lau na fara aikin hajji, sai dai kuma wani abun mamaki ranar arfa na fara wani irin zazzaɓi me zafi. Haka dai nayi aikin hajjin. A daddafe, har muka dawo gida, tunda a airport asibiti ya wuce da ni, sai da aka kara min ruwa da allurai na samu kaina. Ina bude idanuna muka yi ido huɗu da Yar Daada, sai dariya take min ya ce min. "Congratulations love kin sake daukar wasu yaran Turaki gaskiya ni jarumi ne, Mammy bata cika shekara ba, gashi nan kin kara daukar Yarana a womb dinki." Kura mishi idanun nayi ban san lokacin da na fashe da kuka ba, "yanzu kai wannan abin burgewa ne?" "Eh kai wallahi abin burgewa ne fa." Duk yadda naso na gaya mishi yadda za a ɗauki lamarin nuna min yayi shi bai ga wani abin muni ba, haka na kyale shi ba don na so ba, amma wannan karon na san nayi ciki don sau hudu ana min karin ruwa, sai da cikin ya cika wata biyar a lokacin Nana tana da shekara daya da kusan rabi, sannan na samu kaina. A lokacin aka yi bikin Almustaph babban dan Aunty Innah, haka na tafi gida da ciki a lokacin duk wanda ya hanni da cikin sai ya san ina da ciki domin yayi wani girma. Sannan duk tsawon lokacin nan anyi scanning har sau biyu daya ne kuma yaki nuna Gender. Haka nayi ta fama da shi, ai kuwa su Mama da Yadiko suka ta min fada akan me zan zo kada ka kara zuwa ko ina sai na haihu. Kusan anyi bikin ina kwance. Sai da na shafe sati kafin na wuce Jos, kwana ɗaya nayi a gidan Aunty Raliya, muka wuce lagos.
---- Tunda na dawo Alhamdulillahi, kulawar da nake samu a wurinshi ya wuce yadda nake tunani, haka muka yi ta lallabawa har na shiga wata tara, anan aka ce ba zan iya haihuwa da kaina ba. Dole ya saka hannu aka za ayi min CS'. Ya kira Mama ya gaya mata, aiki za ayi min ko zata zo ne, kwanaki uku a tsakanin sai gata tazo, kafin aka min aikin. Wani ikon Allah yara uku maza biyu mace daya ita ce kusa karama a cikinsu, haka aka fito dasu Mama tayi ta mamaki. Kafin na farka danginsa sun cika asibitin, sai murna da godiyar Allah da suke ta yi. Lokacin da na farka da surutu sai kuma kirga da nake yi, kafin wani lokaci ƙarfin maganin ya sake ni.
Alhamdulillahi a cikin kwanaki biyar na samu kaina, a kwanaki na bakwai aka sallame ni, yan uwa da dangi da abokan arziki sai fatan alkhairi ake mana, duk wanda ya ga Yaran sai a ce Turaki ya fini ƙarfi, domin yaran sak da sak suka yi da shi, sati na biyu aka yi suna shima walima kawai aka yi Mazan Haris sunan Abbanshi. Hassan ya ci. Husaini ya ci sunan Kakanshi Hassan Ajmal. Husaini Amjad, gambon kuwa aka saka mata sunan Mama,kiranta da Anum, Mama ta zauna da ni har muka cika kwanaki arba'in, a wannan lokacin kan sai da aka dauko min me reno. Mama bata kyale ni ba sai ta min biki ciki da wajena, sannan ta bar gidan. Inda muka buɗe shafin kauna ni da shi, kamar zamu cinye kanmu.
Wannan karon yarana suna samun kulawa dukkanmu uku haka matar Alhaji Mudansir ta haifi danta namiji, aka saka mishi sunan Alhaji ELYakub, suna kiranshi da Dady. Wannan abin da ya faru yasa kowa ya shiga hankalinsa. Hajiya Zeenatu bata da wani katabus, yarta Mimi da kyar aka yi aurenta koda yake wani gaye ta kawo wai tana so garin bincike aka samu dan safarar miyagun kwayoyi ne. Haka yasa aka fasa auren sai wani shima ba laifi amma dai ya fi wancan kusan irinta ne.
Rayuwa ta bani abubuwa dayawa, a lokacin da ban zata ba, a lokacin da naso abubuwan ban samu ba, yau dai gashi ni ce cikin Alkhairi da kwanciyar hankali.
*** Bayan shekaru biyar ..
Hafiz kuwa jinya ya sha kamar zai mutu don zai da ya kwanta a bayara can asibitin kutare da masu tarin fuka, anan ta sha jinya Jalilah da aka kashe auren guduwa tayi ta shiga bariki. Aka nime ta aka rasa, wannan abin yayiwa Goggo talatuwa ciwo, a cikin wannan yanayin Allah yayiwa Goggo Alti rasuwa, lokacin Yarana suna da shekaru uku, Nana taka da shekaru hudu da rabi, haka muka zo har Jama'are kowa ya ganni sai ya tambaya anya nice kuwa, murmushin gaske nake gani a fuskar dangina da yan uwana da suka tsaya min, mun hadu da Hafiz ganin yadda Ajmal yake tsalle a jikin Abba Amjad yana jikin Ya Umar da Nana a gefen Ya Ado, Anum a cinyar Ya Tahir abin sai ya sake shi jin kamar na shi ne Yaran, haka ya bar cikin mutane ya koma can bayan gidan yana kuka, domin idan da xai bada labari tow duk wnada ya gayawa Ya auri Lubnah ƙaryata shi za ayi, yau gata da Yaranta da Mijinta, da yau ace sun haifi ɗa da ita da yanzu ana alakanta shi da ita amma yanzu sai zai ace tsoho.
Ko wancan watan yaji labarin yadda Karima tayi mummunar hatsari tana can asibitin Mahaukata, yaran da kuwa an kwashe su ba a san inda aka kai su ba.
Kwanan mu goma sai ga Turaki a Bauchi, yazo yayi ta mita wa Mama da Yadiko. "Fisabiilillahi yaushe Lubnah zata girma ne? Sati daya na bata amma ta kara kwana uku, nasan yanzu kusan har magana sun yi da Hafiz yayi ta nunawa mutane ita as tsohuwar Matarshi." "Kai ai baka da matsala sai na kishi, idan bai nunawa jama'a ita tsohuwar matarsa da yayi wasa ya rasa ta, ai kai abun alfahari ne ace yau ga matar da ya rasa saboda sakarcinsa." Inji Yadiko sai kuma ya shafa kai yana murmushi. "Kuma fa haka ne fa!" Haka ya gama musu iyayi, sannan ya bar gidan ya tawo gida. Na gama abincin dare, ina wanka ya shigo har ban dakin.
Zan iya cewa zane ni yayi amma zanewar kauna, haka muka fito cike da kaunar juna. Sai da muka yi sallah isha sannan muka fito parlourn muka ci abinci da yaran, sannan muka yi hira na shiga da Yaran cikin dakinsu na kwantar da mazan gado daya matan gado ɗaya. Sannan nayi musu addu'a. Kafin na dawo dakin ibada wato dakin mijina, yana ganina ya kashe aikin da yake ya tashi ya kashe wutar dakin sannan ya muka bude wutar kaunar da take rura zukatarmu.
Washi gari. A group naje jin Hafiz an tura shi asibitin ƙwaƙwalwa na jahar Kano wato saboda halin da yake ciki da ake tsammanin hauka ce, ni da kaina nace damuwa ce, domin domin ita kadaice zata zarar da shi, haka, dayawa cewa suke hakkina ne y kama shi, don haka ya kare da hauka.
Satinmu uku muka wuce da Yara Lagos. Don ma yaran nan gidan Ya Ado suke tafiya hutu ko can KUMO FAMILY. Hankalin zuriar KUMO ya kwanta. Ita kuwa Falilah matar Ubaid an ce wai asirin da tayi kokarin yi min ne ya koma kanta ko ma Yaya ne Allah ya kyauta. Matar Uncle Auta muna shiri da ita. Domin ko lokacin bikin yarta Dada haka muka tsaya a matsayin kawayenta ni da Amaryan Ubaid, ai kuwa sai muka hade kanmu yadda kansu yake haka. Yarinyar daga Lagos muka kaita abuja, aka sha biki wata shida a tsakanin aka yi bikin Taj. Shekara biyu da auren Dada aka yi bikin Yar Ya ado a Bauchi a lokacin ina goyon mai sunan Ya Ado, wanda muke kiranshi Annur.
Ana gama bikin mijina ya sako ni gaba muka dawo Lagos. Wato idan Turaki yana bina a Sannu ji nake I'm melting domin ni kaɗai nasan gajiyar da nake samu a tare da Mijina, ni daya nasan waye shi. Ina son mijina ina kaunar Mijina kuma nasan shima yana sona Sosai. Dirin motar shi naji na fito ya shigo, isa gabanshi nayi na amshi jakarshi. Ina murmushi nace mishi. "Barka da dawowa ya hanya ya aiki?" Jan kumatuna yayi yana faɗin.. "Alhamdulillahi na same ki lafiya ina Yaran suke?" Murmushi nayi na yi nace mishi. "Naa tana gidan Ya Ado, Amjad yana gidan Taj, Anum da Ajmal suna can wurin Dadda dani sai auta ne a gida, janyo ni yayi yana faɗin. " Ke dai ki ji tsoron Allah ki daina kiran Auta domin wallahi akwai shida na zuwa na gaya miki goman nan dai sai kin dire min su! " Murguda mishi baki nayi nace mishi.." tunda a ruwan sha ne ai sai ka dura min. " Na shige dakin biyo ni yayi yana faɗin. " 'Aa ba a ruwa ake sha ba, amma bari na gaya miki yadda ake shan shi." Ya fada yana rungume ni ta baya na fasa ihu karami cikin jan hankali. Alhamdulillahi anan zan tsaya da labarin Lubnah. Da yake cike da alakar Zuci soyayya da rikita rikita, Na gode sosai da wa'danda suka biyo ni a labarin nan, Ubangiji ya kara hada mu a wani labarin mai sunan......... Fatan alkhairi son so Fisabiilillahi......