Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 59

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 59

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 59: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 59. Da sauri ya yarda abin dawisun ya idasa hayewa saman gadon gaba daya…

3,352 words

Da sauri ya yarda abin dawisun ya idasa hayewa saman gadon gaba daya yana fadin" Oh sorry, I'm sorry an mata , in ga wajen in ga nan din naki.......?"

Matse kafar ta yi tana zarro ido tana kallonsa hadi da turo bakinta ta sake matse kafafuwan tana fadin" Me zaka gani? Allah sawaka"

Wani murmushin ya yi yana duba agogon hannunsa ya ce" Kin ga, karfe goma ce ta gota kina ta barci, bayan na ji tsare tsarem dake gabanki na aurar da babar yaya, me zai hanna a matsayinki na matar soja ki murje ki ba marada kunya ki ci kazarki gatanan tana kallonki sannan mu shiga rubuta abinda ya dace mu yi a bikin nan? Nine fa baban amarya......" Ya karashe yana kanne mata ido daya

Hannunta ta dora a saman bakinta da mamaki ta ce" Muhamadu rasululahi sallalahu alaihi wa salam, a ina aka taba yi kai mijin kanwarta kuma ka zama baban amarya? Hana dai "

Idasa zama ya yi gannin ta fara sakewa da magana ya sake rike damar ya ce" kin ga, ko dai ranki ya kiya ne da Allah ya daukaka ni? Nine baban amarya baki ga Abanki a bayana yake buya bane?"

Ai kam tino ranar da abanta ya yi wuf ya boye a bayansa ya sakata kyalkyalewa da dariyar da bata shirya bashi a kwana kusa ba, har tana dan dafe cikinta da ya tuna mata yinwa take ji matsananciyar gaske kuwa sannan ta dan girgiza yatsarta a hankali ta ce" Nahidt bata da kirki, a bainar nasi ki saka ubana gudu kuma ki ce ke ba haka kika zo yi ba?, Allah shirya min ita......."

Ita na dariyar Nahidt ne, shi kuma yama kallon fuskarta da yadda take yi din, har ta dire ayar maganarta sannan ya saki lalausan murmushi ya juya ya dauko kwanon wajen mama da kuma ledar kazar ya sake dawowa yana bubudewa a hankali yana ajiyewa a gabanta

Tukakiyar tebar da ta sha miyar markadadiyar gyada ta zubawa ido yawunta na tsinkewa, sai kuma ga kaza wace tana yin ido hudu da ita jiya ne ya fado mata a rai Cike da kula da yannayinta da dan sigar tsokana ya ce" Kumama ai akoy ta frij ta jiya ko ita zamu ci mu adana wannan?"

Da sauri ta kalle shi tana zarro ido a zuciyarta kuwa ta shiga ayana' waye babana, ai daya ake yi da Allah in ji kuturu, ni na ci kazarka kai kuma ka kasheni? Ka je ka ci abinka Allah zai bani nima'

A bayane kuma sai ta kiya ta ja tebar tana sake kallon kazar a hankali ta saka cokali hadi da yin Bismillah ta dan diba ta fara kaiwa bakinta Ai kam ta sha hadi yadda take sonta hakan ya sa ta sake kaiwa bakinta still tana hankalce da lamari na leda mai dauke da kaza, shi kuma yana kallonta kamar ya samu wata TV har sai da ta masa alamu na abin jika makoshi kafin ya mike a sanyaye ya dauko ya sake ajiye mata ya kuma zuba mata ido yana kallon dukkan motsinta har wayarta ta kuma daukan vibration din da ta yi ta yi a dazu aman bata sani ba

Shine ya dauki wayar da sauri, hakan ya sa ta zuna masa ido a lokacin da ya daga kiran ya saka a handsfree bai ce komai ba

"Wayo Allahna kanwata, fada min fada min Shuwwan Abanta shafa min an yi ko? Shikenan Shuwwan Abantama ta san abin? Fada min sumanki nawa" Zuuuuu haka Nahidt ke maganarta tana kyakyata dariya, a lokacin da suka yi ido hudu ita da shi suka kumakin cire dubansu wajunnansu

A hankali ta fashe da kukan tabarar da ya saka shi lumshe idannuwansa ya dauki wayar ya karra a kunnensa a hankali ya ce" Bana tunanin zaki iya biyan kukanta gaskiya, sai dai ko mijin ki!" Yana gamawa ya katse kiran ya janyo matarsa jikinsa ya shiga dan rarashinta yana aukin maimaita Nahidt ce ko? Ta yi shiru zai yi tafiya mai digi tata ta kanta ya bata abinda ta nema! A haka ta lafe a jikinsa ta idasa zuba tabararta tamkar ba ita ba, tana zile zile ana tarota tamkar wata yar goye.................................

Ita kam Nahidt wayar ta cila da ihu ta ringa kwaso shokiiii tana aukin fadin ta aurar da y'arta ta kai daki, y'arta ta kai dakinta............ (🥺😔), Sai kuma ta idasa da silalewa tana zama bakin gadon a lokacin da ta tuna jibi i war haka fa ta yiwu har an daura nata auren itama da nata mijin, shin me ta tamadar masa wanda zai saka shi nishadi harma ya gasata? Ita fa tausaya masama take yi, anya malan zai iya wani katabus kuwa??????takan ji tausayinsa a zuciyarta sosai, yana cen ya kasa zaune ya kasa tsaye sai shiri yake abin har mamaki yake bata, sai dai kuma idan ta tuna Allahu gafurun rahim ne sai ta sake rike carbinta ta kuma sake kadaice kanta wa bauta masa da fatan ya sanyaya kaurin rubutun ALK'ALAMIN KADARARTA

A wannan rana Shuwwa ta ga tatali irin na soja, bama a wannan rana kadai ba har dare ya shigo idan ya matsa to fa dan ya leka masalaci ne, a nan a tare da ita ko kiransa aka yi yake amsawa, a nan a tare da ita ya baje ya ringa sakata magana da yawan nuna mata kular da ta sakata sake baje kolin tabararta, baci take yi da shagwaba son ranta kai da za'a bartama sai tace a sabata a baya Tunda dai Allah ne ya yi abinshi ta samu mai tarota ai sai yi............

_____________________________________

A gidan Malam

Karfe shida na yama

Dago kansa ya yi yace..................ALK'ALAMIN KADARATAH

Na

*Sajida*

Page

6️⃣8️⃣

Dago kansa ya yi daga ware hular da zai hadawa dinkin shadar da aka watsa masa fari kalll wanda ya sha zubi gari da yar ciki ya zunawa rigar da ta ajiye ido yana kallo sannan ya sake maida kansa dan cire abin balawa a hannun rigar da kuma safar da Matarsa uwar gidansa watau Malama ta ce ita ta fi dacewa da hawa dinkin ba tare da ya furta mata ci kanki ba

A harzuke ta sake kaiwa saman kujerar tana zama ta ce" Ka rasa wace zaka kawo ka jera ni kishi da ita Malan sai warce ba'a san asalinta ba? Y'ar ina ce ita su waye iyayenta?, Malan du irin yadda nake zuba maka karya tabaya a abincinka kana ci dan kar munafukar nan ta cin maka sai da ta cin maka ashe? Du tarin azhkar dinka da adu'o'in neman kariyar da kake yi ba dare ba rana sai da har dandi ta cin maka? Malan yau kaine kake murnar zaka je daurin aurenka da yar barikin da ta tare a gidan kanwarta har ka yi mana dinkunnan shada ka ce sai mun je? Da ni za'a tafi daurin auren yar iskar y'ar ? Malan ai ya dace ka yi min adalci ko dan zaune da nake da kai a hali na rashin jin kukan yan jarirai da yawon yan dagwai dagwai a gefena, Malan haka zaka wulakantani a anguwa a ce du abina ka kare da auren karu........"

Hular da ya dauko ce ta kubce a hannunsa ta fadi lokaci daya kuma ya sake zuba mata ido da idannuwansa da suka fara daukan launin ja dan bacin rai

A cen kasan zuciyarsa ya ringa astgfari da hailala dan samun sasaucin bacin ran dake tuko shi

A sanyaye ya karasa wajen da take zaune yana kallonta ya ce" Furera, ai ke kin san cewa an auna kwayoyin haihuwata an kuma aunawa likita dai bai ga matsalar da ta hanna ni baki ciki ba, kuma ke kin san wanene ni a saman shinfidarki wanda koda baki zauna da ni dan komai ba na gabata dan hakin da nake ba gaban jikinki kamar yadda na karanta a koyarwar adinina kadai na isa ki zauna da ni, bale ban san abinda Allah ya boye a hanna min haihuwa ba, Furera a kulun kece mai tino min cewa ban ajiye ba kuma hakan damuwa ce a tare da rayuwata, kin ga na hakura na kuma barawa Allah shi yasa nake burin ajiye wace zuciyataa ta yabama, Allah fa ya halata min shikenan ke sai ki fitineni?, Ki sani idan takamarki baki haihu ba y'arki ba zata kasance cikin jarabtar furucinki ba ki kiyaye lamarin ubangiji a kan hannin da ya yi, domin bawa baya tinkaho da halitarsa da yannayin tukin rayuwarsa har sai ya jishi a kabari, hakan na nufin ke din nan hakita ce da Alllah ke iya juyawa lokacin da ya so, kar ki manta sai idan ya so zaki shiryu idan ya ki ba zaki taba shiryuwa ba, in ba abinki ba meye riba a cikin zubar da mutunci ne? Ba zaki yi koyi da yar uwarki bane? Nan fa aka kawo mata ke ta kuma amsa ta yi min biyaya, kina tunanin akoy matar da zan yi ta tureta a kima d adaraja a cikin zuciyata ne? Furera Zuciya na son mai kyautata mata, ba kuma zan karra aure dan na tsane ku ko kun gaza min bane, zan karro ne dan halin hakan ya kama, shin ke bakya tsoron Allah ne? Kuma da kike magana a kan wai rashin asali ki wanke idannuwanki ki kuma nemi majinginin bayanki, domin ina tsoron ki tsinci keyarki a kasa a lokacin da kika ji cewar kadara ce ta rigayi fata har kika sameta a bagas kike son wulakantata, ki sani ba'a wulakanta dan Adam ko waanene domin yanzunta na iya kasancewa gabanki, ita kuma yanzunki ya dawo nata, ko a yanzu gaskiya du wanda bai yiwa NAHIDT dina adalci ya yabeta ba bana jin zamu shirya, tunda ai ta yi kokari ta zubar da komai ba tare da an saka mata wuka a wuyanta ba, sai dan mai shiryawar ya shiryeta ne, sauran kuwa zan tayata da daga hannuna na hada da kama kafa da fiyayen halita kan aya kar ta kasance a kanta , kunya da soyayar maaiki ta sa Allah ya karra yafe mata sannan ya saka Matar malan a gidan aljannah, zuwa kuwa da ki dauki shadar nan ki saka ki je da ita, ko kar ki saka ki saka wace ta maki dama so na yi mu yi ankon farin kaya tunda murna muke, ni dai na san sai kin halarci daurin aurena tare da yar uwarki, idan kuwa ba haka ba......Furera idan kuwa ba haka ba ina tsoton kanki ya kasa rike asalin wanene ni!" Yana dasa aya ya juya ya fice a falon nasa yana ta karra tausar kansa da magangannun cewa wannan ba ranar bacin ransa bane, dan haka ya nufi bangaren da aka gama gyara komai da irin dukiyar da aka zuba mata wadda daga MUHAY ne ya bada wannan mamakin , kaya fa an zuba ko yar waye kaya kuma sun yi ko a gaban waye, shi da kansa sai da wajen ya ringa bashi sha'awa

Murmushi ya yi yana girgiza kansa da tunanin wai da gaske Shima goben nan zai kilaceta kamar yadda ya jima yana fata?, Tabas bawa kar ya cire rai da rahamar ubangijinsa duk rintsi, komai nisan dare gari zai waye ne, mai hakuri kuwa shi ke dafa dutse.

Tunda ya fice ta mike da gudu ta yi bangarenta, tana zuwa ta dauki wayarta ta kile bangaren nata ta shiga dokawa

Ta jima tana ringin ba'a daga ba hakan ya sa ta yi wurgi da wayar ta fashe da wani kukan mai tsananin gaske a bayane tana fadin" Walahi walahi walahi ba zai yiwu ba, ina ji ima gani na san kana sonta na yarda ka aurota ka kawota gidana ta yada zata idasa janye min kai daga duniyata? Malam idan taa rabani da kai na shiga ina da raina? Walahi ba zan yarda ba , uwar gidanka ai dole zuciyarta ta mace ita din kanta shekararta hamsin ne ta girmeka da shekaru bila adadin, me ya raage mata? Tama ce zata yi kishin mana ai da ta kwashi abin kunya, ni dai nice daidai da kai ba wata karuwa ba walahi, wayo Allahna ba zan iya yarda wata ta zo ta kwacen mijina da mutanen anguwata ba!"

Ajiyar zuciya malama da ta yi niyar zuwa ta ce da ita ta kira masu mai kunshi ta sauke ta juya tana girgiza kanta da nemawa Furera sauki a wajen Allah, dan ta kula ta matukar daukan abin da zafin gaske, bata san gwara ta yiwa kanta da kyau ta rufawa kanta asiri a kan lamarin auren nan na malan ko zata kankarowa kanta daraja da mutunci a zuciyarsa, to in bandama shirme irin nata abinda baka isa ka hanna ba menene na tada jijiyoyin wuyan? Aure dai nan da yan awani an daura da ikon Allah, gwarama ta ba kanta hakuri ta sha ruwan sanyi

Komawarta ta yi ita akai mata kunshinta da kitsonta sannan ta ci gaba da gyaran bangarenta, domin kayan daki na kasa da kasa Malan ya masu da kayan fitar kishiya, ita kam ai gaba ta kaita , fatanta ta zamo alkhairi a garesu baki daya, dan ko hajiyarta har nan ta zo ta masu fatan alkhairi da nasiha mai ratsa jiki sannan ta yi mata gargadin kar ta saki kishin yarinyar ya sa ta zubar da ladan shekara da shekarun da ta dauka tana yi, domin shi kishi halal ne kuma halita ne, aman idan ka yi hakuri ka daidaita komai zai zo maka da sauki ne bi izinillah Da wannan ta karra samun kwarin gwuiwar kawar da kanta a lamarin, duba da shima yana yin iya kokarinsa dan ya kiyaye abinda zai iya hasalasu a kan maganar auren nasa Tana gamawa ta shige wanka dan ta shirya da wuri domin jirgin karfe takwas zasu bi na dare su kwana a cen da sasafe a yi komai da su.

____________________________________ Sosai yanzu ta samu kanta da zafin dake adabarta, tunda wannan abu ya kasance tsakaninta da shi take fuskantar wani sabon mutun mai naci a gareta, yakan yi mata nacin cin abincinta sannan ya mata nacin sakin fuskarta Bai kuma nuna zai je wajen da ya ki fita da dadin rai ba, aman jikinta ya zamana ne filin wasansa ba dare ba rana, haka kuma lebenta ya kasance har ya saba da tsotsarsa A haka ta zabi gadajen da za'a zubawa y'ar uwarta da kanta, ta zabi kayan da za'a jera mata, ta zabi labulaye ta kuma zabi kalar da ya dace a sakawa yar uwarta sannan ta shiga rigimar da yaushe zata je gidan ne? A nan ya ringa yi mata kwana kwana da fadin idan an jima har ya samu kanta dare ya tsala sosai barci ya kwasheta tana kan rigimar ita fa atafau a gida zata kwana ta yaya auren NAHIDT gobe gobe aman ace sai gobe zata je? Shi dai yakan shafa bayanta ne ta ciki na ciki, a yanzu kuma da ta yi barci a jikinsa sai da ya saki ajiyar zuciyar da bai shirya saki ba, a sanyaye kuma ya ringa murmushi kasa kasa ya furta" Idan kika tafi ni kuma na yi yaya? Da kin a yadda nake kwana da abu a hannu da kin tausayaminma ni kin karra min tunda dai ai mun warke ko?, Ni kam na zan kuma nesa da ke ta maganar raba gado ba gaskiya, sai dai kowamaa ya yi hakuri......"

(Ga gaisuwa mijin Shuwaa baban Nahidht😍😂🥰🥰🥰a)

Tunda ta farka sallah ta yi dakinta a guje ta rufe ta shiga shirya jikinta ga kuma waya a gefe sai yi suke yi da yan uwanta a nan take ji wai Matan malan sun sauka tun jiya

Baki ta rabe ta zauna gaban madubi ta tsatsara Mak'up dinta sasauka mai fitar da sirrin fuska, sannan ta sake komawa wajen kayanta dake shan turaren wuta ta sauke su ta saka pant da breziya sannan ta kade doguwar Bubu din ta shada dakakiyaa da akai masu aikintaa a waje mai ruwan copee wanda ya ciza sosai ta saka a jikinta

Rigar ta zauna mata a jikinta, sanann ta bude ta yi masifar kyau, haka ta dauko sarkarta ta saka da abin hannu da dan kunne da zobe Daurin nata mai tsole idon sarakuwa ta kashe ta kuwa kashe shi ya nadu ya yi dassss a kanta Takalminta mai dan tudu ne da jakarsa ta fitar da su da mayafinsu dake hawa da su farare ne su kuwa gaba dayansu ta dauko wayar tata ta bude jakar tana kokarin sakawa cikin jakar ta fito

Da sauri ya juyo sai kuma ya juya wajen manyan sojawan da suka zo falon suka gama tsara irin zagaye wajen daurin auren da zasu yi dan abinda zai faru wanda basa so a kai ga saka karfi a wajen Da sauri ya ce" Kunna iya tafiya"

Du sara masa suka yi sannan suka juya da saurin summa suka bar falon

Sake juyowa ya yi dan sake bama idannuwansa kalaci

A lokacin ita dinma shi take kallo da yannayi na matsanancin begen ganninsa cikin manyan kaya , wanda bata taba ganninsa da su ba

Yana tsayen ya kasa motsawa dan ta gama summar da shi da ruwan kyan da ta yi ta karaso a hankali ta tsaya tana dan murmushi tana kallonsa

Fuskarsa ya shagwabe a dan rikice ya ce" Anya kuwa zaki je wajen nan? Ko kuma mu je mu samu katon hijab da nikaf ne? Ni ni ni......"

A hankali ta langwabar da kanta tana murmushi da son jin ya furta soyayarta da kishinta zasu iya saka shi hannata zuwa wajen daurin auren yar uwarta, sai kuma ya yi shiru yana sake takwakwabe fuskarsa

Dan murmushin ta kuma yi a sanyaye ta ce" Ni na ce me?"

Sake kallonta ya yi shima yana so ta bashi haske, aman yar mutuniyar tasa sai ta tsaya iya nan Hakan ya saka shi fadin" Nine a wahalce, nine zan fi jigatuwa....... IBTISAM kin yi kyau har kamar na ce kin fi kyau kyau"

Kwarai ta yi mamakin jin furucinsa, sai dai kwanakin nan ta gama gane yana da magana a gaban abinda ya yarda da shi, dan haka sai ta yi luuuu da idannuwanta ta ajiye mayafinta tana fadin" Dan haka bara na lulubewa maza gannina a bagas......."

Kyakyawan murmushi ya kasheta da shi yana kallon bayanta har ta shige dakinta kafin yake juyawa ya yi nasa dakin da gagawa shima Bindigarsa ya daure a jikinsa da alburushi sannan ya rufe ya dauko hularsa ya sake bade jikinsa da mahaukacin turarensa ya fitowa fito yana kanga waya a kunnensa dan jin idan sarkin rawanin ya karaso yana yiwa Aba kuwa?

Sake zuba mata ido ya yi, ta saka abaya bak'a sidik ta nada mayafinta a kan kayan da ta saka , abayan bata da ado ko diz a jikinta sannan budadiya ce sosai, haka kuma nadin da ta yiwa dan kwalin abayar ya amsheta harma ya so ya fi shigar ta dazu kyau

Ajiyar Zuciya ya sauke yana ayana' kyanki ki yi zamanki a dakina na yi ta kallonki ba dare ba rana, idan na fita na dawo na tardo ki, ni kuma sai na je na maki neman dan walahi ko dako zan yi ba zan yarda ki fita ba IBTISAM zan yi na faranta maki mudin raina'

A bayane kuwa sai ya gyara tsayuwarsa ya daga hannunsa wajen kansa ya sarra mata, wanda hakan sai da ya saka ta saki murmushin ba shiri kafin ta sara masa itama Hannayensa ya bude mata ta zo da dan sauri ta fara ciki, ya mayar ya rufe ruffff a hankali ya furta" Mu je mu daura auren y'armu"

Itama a hankalin ta ce" Aa mu je mu daura auren Abanmu da y'armu"

Murmushi sukai suka fice dan an jima da gyara abin daukansu su din kadai ake jira

Sai da ta shiga ya rage tsayinsa ya gyara mata abayarta sannan ya rufe ya zagaya ya bude ya shiga shima kafin suke dagawa

Tun daga kan kwanar gidan Dad ta ringa gannin tarin sojawan da suke shawagi aka zuba ta ko'ina, sannan lamari na bikin manya tunni baki sun fara yiwa gidan caaaa

Readers Also Read