Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 60
Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 60: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 60. Kasancewar da kansa ya dora dokar duk wanda ya zo ko waye daga bakin…
3,129 words
Kasancewar da kansa ya dora dokar duk wanda ya zo ko waye daga bakin gate din da suka saka zai sauka ya karasa gidan a kafa a dole doka ta hau shi Dan haka ya zagaya ya bude mata a hankali ya furta" Bismillah Madam MUHYIDEEN MUHAY"
Idannuwanta ta lumshe sannan ta dora hannun nata saman nasa ta fito lokaci daya ya saka hannunsa yana rike mata jakar tata ,ya kasance hannunta na dana na cikin hannunsa na hagu datan hannun nasa kuwa yana rike da yar pos din tata suka ringa takawa a hankali, shi ya saka farar shada ne kal ita kuma da abayarta a saman shadarta, a jikinta tafukan hannayenta da fuskarta ne kawai ba a lulube ba, ga sojojin dake sanye da kaki sun zagaye su a dole ko baka san da zuwansu ba yadda ake kakauda mutane zai sa ka juyo dan gannin ko su wanene , hakan ya sa kallo ya dawo kansu, aka kuma yi mamaki da kuma rakasu da kallon sha'awa da adu'a , masu daukansu hoto na watsawa haka maroka na ta kokarin kawo gaisuwa , shi kuma burinsa ya kaita ciki ya cireta daga dumbin kartin nan ko zai samu nutsuwa
Sai da ya sadata da cikin gida har kofar baban falon Mahaifiyarsa wanda ya tabata a ciki suke ya ja ya tsaya ya nemi izinin shiga
Ana basu dama ya fara shiga da salama a bakinsa kasa kasa da kuma miskilancinsa Sai dai mutanen da ya gani da irin shigarsu ta alkyaba ta saka shi dole sakin murmushi yana karra kallon su
Nahidt dake rike da Alkyabarta tunda garin Allah ya waye ce ta mikawa mamansa da ta miko hannu idannuwanta na cika da kwalar farin cikin gannin yau MUHYIDEEN ne ya shigo da macen dake tasa ya yi mata jagora ya rakota da dukan alamu na yana kishin a tatare da shi! Lalle d'anta ya zaka cikaken namiji baban burinta kuma ya cika ita kam, domin haihuwa ai ta Allah ce idan ya samu kafin ta mutu alhmdulilah idanma bata gani ba alhmdulilah, ita kam da ta ga cewa yaronta ba abinda take tsoro bane yake damunsa ta fi kowa farin ciki, yanzu haka yar uwarta na gidan tunda safe ta zo itama tana dakinta barci take bata farka ba, bata nuna mata komai ba aman kuma bata nuna mata yannayin da take nuna mata a da na kaka naka yi da lamarin yaron nata ba, ko da ta kwatanta rabonta da shi tun a asibiti sai ta yi murmushi ta ce ai kin san yaron naki yanzun sai a hankali, bale an shiga babi na iyali? Kin san sun tare da matarsa ga baban matsayin nan da ya sake hawa kansa, dole sai da auzuri wani lokacin......... Ai kam tunda ta ji haka ta yi gummm ta shiga barcin karya, domin ba barci take ba tana fama da tukukin zuciya da tuna kamanin yarinyar da shayinta a zuciyarta, ita tsoroma take kar ta fito su hadu da yarinyar ta yi mata wani abin daban.....aman ta ji wani iri jin wai ya tare da wata? Du irin abinda ta kula? Me kennan? Tana son samun informations na abinda ya faru
Alkyabar dake hannun Maman MUHYIDEEN ta mika masa tana murmushi hawayen dake cikin idannuwanta suka zubo Daidia maman Shuwwa din ta fito daga bangaren kicin ita kam ba Alkyabar a jikinta domin an ce ba yanzu ba mijinta ne zai dorata a kan matsayin da yake nata nan ba da jimawa ba, itama bata damu ba ta baki take yi iyayen Hamza sun zo, danginta sun zo, duda basu yi wani zama ba aman du kowa kokarin kamanta kyautatawa dan uwansa yake yi
Murmushi ta saki gannin MUHYIDEEN ya yiwa mahaifiyarsa murmushi sannan ya shafa gefen fuskarta ya share hawayen dake neman zubo mata sannan ya lumshe mata idannuwansa dake nuni da rarashi yake yi
Juyowa ya yi wajen Shuwwa a hankali ya kama Abayar dake jikinta ya shiga balle mata Itama shi take kallo har ya gama balle mata sannan ya yaye dan kwalin na saman kanta shima ya mikama Mamansa
A nutse ya daga Alkyabar ya saka mata ita harda hular Hakan ya sa ta dago dara daran idannuwanta tana kallon fuskarsa Murmushi ya sakar mata zuciyarsa na dokawa ya furta" Asalamu alaiki ur excelency Princess nd mrs CHIEF OF ARMY IBTISAM MUHAY.........." Yana gamawa ya kamo fuskarta cikin shaukin kauna da dumbin soyaya ya kawo lebensa daidai............
Daidai m? Kai daidai me ka kawo lebe ne? Ka manta inda kake ne?😌
Akoyta fa, rigiji gabji, me zai faru ne? Ga sarki ga sarki ga saraki ga hukumahhhhhhhh🥰🥰🥰 ALK'ALAMIN KADARATAH🥰🥰🥰🥰💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* 💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥💔❤🔥
*The Hero writer*
*SAJIDA*
_Bismillahir rahamanir rahim_
PAGE:. 6️⃣9️⃣
*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*
*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*
*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*
*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*
1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*
*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*
*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*
Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.
Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.
Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618
Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din
Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰
A hankali ya dora lebensa saman goshinta ya mana mata kiss sannan ya dago yana kallon fuskarta
Tabatuwar abinda suke zargi ya saka iyayen kawar da kawunnansu cike da farin ciki, Hajia Nahidt kuwa gyada kai take a ranta tana ayana' Lalla su Shuwwa an fandare, sai kashe shi take da kallo kamar zata cire masa babar rigar, kai jama'a'
Kasa kasa sosai Shuwwa ta ce" KATONA, yaushe ka san babanmu sarki ne"
Yar daria ce ta kubuce masa wace ta sake kashe mamansa da mamaki harma ta sake juyowa da matsanancin farin ciki tana kallon ikon Allah Hancinta ya dungure kasa kasa sosai ya ce" Zan maki bayanin ranar da lokacin harda hours din, ba yau ba na san babar yarinya nake tare da ita"
Nahidt ta aniya tafa hannu tana matsowa sosai ta rage muryarta ta ce" Inaga ya dace a je daga wajen nan yalabai ka ga fa lokaci kuma na ga kamar kaine uban amaryar kau?"
Yar daria ya yi mata itama yana girgiza kansa ya kalleta ya kalli Shuwwa sai kuma ya kashe mata ido daya ya juyaa ya barsu nan ya koma wajen iyayen nasa
Kasa kasa sosai ya yi kokarin fada masu ko me suka ji kar wanda ya fito idan halin rikicewar wajen ta kama zasu iya jiyo hayaniya, su yi zamansu in sha Allah idan har ya yi aiki da dan hankalin da ya rage masa koma wanene mugun zai rufawa kansa asiri ne ya bada kai da kansa, idan kuma ya ki aikata hakan ne dole za'a samu matsala, domin dukkan wasu datawan da suka isa sunna wajem, haka kuma mataimakin shugaban kasa na wajen da takardar saka hannunsa kan a sauke wanda yake sama a dora mai wajen, so su dan saurara a dakin nan
Daga haka ya fice ya tafi,
Yana tafia mamansa da farin ciki ta karaso ta rungume Shuwwa dake ta bayani da Nahidt a sanyaye ta ce" Allah ya yi maki albarka y'ata, ni na tabata ke din alkhairi ce a rayuwarmu, Allah ya kare min ke yarinyata"
Shuwwa kam kunya ce ta hannata kwakwaran motsi, sai sada kai da ta yi tana jin wani iri abin mamaki kunyar Maman take ji har ga Allah har cencen kasan zuciyarta Daria maman ta yi ta karasata ciki ta zaunar da ita sannan ta koma wajen mahaifiyarsu suka ci gaba da shige da ficensu na tarban bakinsu
____________________________________
Cike da iza Sarki ya juyo yana sake bin manya manyan mutanen dake zazaune a wajen daurin auren nan,aman kuma abin mamaki har yanzu ba'a gabatar da daurin auren ba, shi abindama ya fi bashi mamaki irin yadda ya ga mutanen kasarsa datijan da rabonsa da ya saka su a idaannuwansa yana iya cewa har ya manta, domin ko wasan sallah ake basa cikin wa'inda ke halarta, tsofafin datijan da suka yi zamani da mahaifinsa, uwa uba yaron wajen dan uwansa da ya gani shima a Wajen bayan a fada bai ji maganar cewa zai zo daurin auren ba, sai a nan din ya ganshi, kuma tunda ya gaishe shi sai ya ga ya koma wajen datijan nan ya zauna
Dogarin dake yi masa fifita ne ya dan duko da kansa gannin alamun sarkin na son yon magana
Yana duko da kan nasa sarkin ya ce" Menene musababin jinkirin daurin auren bayan magabatan yaren sun gabata a wajen?"
Kansa a kasa sosai ya furta" Allah ya karra maka lafiya, mahaifin yarinyar ne bai fito ba"
Da mamaki ya kalle shi a ransa yana ayana mahaifin yarinyar kuma? Bayan CHIEF OF ARMY din da aka nada wanda aka ce shine mahaifinta? Sai dai kuma bai kuma furta komai ba ya yi shiru yana tunanin idan aka sake daukan lokaci tabas zai tashi domin yana son komawa kasarsa a yau, rabonsa da karagar mulkinsa da yake ji har bargon jikinsa tun jiya, bayan rabon da kujerar da ga haka har ya manta, ko bashi da lafiya sai ya zauna
Kusan minti tara tsakani aka zo aka sake gyara kujerar dake gefensa na dama, wace shi du a tunaninsa shugaban kasa aka tanadarwa ita Kuma sai bai zo ba, domin an bambabtata sosai an kuma kawatata sosai da shinfida irin ta kilishi a saman kanta
Da ido ya sake raka sojan da ya gama gyaran , yana bacewa ganninsa sai ga murya, murya ce irin ta baban bafade, duda muryar a yanzu bata da kaifi irin ta da kuma bata da zaudi irin ta da aman murya ce wace tun sunna yara suke jiyota a fadar gidansu, domin bafaden dan uwansa ne wanda bayan nadi aka neme shi aka rasa Hakan ya saka shi zubawa tsohon da ya shigo da rawani irin na sarautar gidansu da kuma rankwafa ta tsohuntaka ga kuma karfin hali na kirari uwa uba abinda baakinsa ke fadi kirari ne ziryan na dan uwansa wanda ya goge ya dora nasa
A kausashe, gabansa na neman faduwa ya ringa karfafawa kansa gwuiwa da ture tunanin dake shigo masa, domin kuwa ya tabata ko a mafarki abu ne da aka yiwa tufka hanci aka lula nesa, ba dai mutun ba walahi
Wata muryar mai iso da shigowar sarakin ta saka shi sake maida dubansa kyam a kan wanda zai shigo A tarihin masarautun kasar nan, masarautar gidansu ce kadai aka yiwa zamanin iso da mai shigowa, a zamanin sarautar dan uwansa ya goge wannan, bayan ya rasu shi ya dawo da ita aman kuma ta wata siga daban, sai ga tsohuwar sanarwar tana shiga dodon kunnensa, wanda hakan ya saka shi sake neman zurmuwa a wani tunani daban Shin wani karamin kwaron sarki ne ya dauki wannan sanarwa ya maida ita kasarsa? Da kuwa ya ga ikon Allah domin idan takamar kasar cewa an dade da juya babin yaki da kuwa sun tsogalo rigima da aljani, dan kuwa shi da kansa zai dauki takobi ya sare kan tsageran sarkin da ya dauki busa da kuma kida irin na masarautarsu!
Hanya aka buda, sandarsa ta fara bayana a wajen a hannunsa, sanda mai ruwan ta mahaifinsa sak, wace take da ado irin ta mahaifinsa Mutane da yawa wa'inda suka rayu da mahaifinsa suka kuma san adon rawani irin na mahaifinsa ne suka mike hankali tashe sunna zuba idannuwansu a saman mutumen da ya bayana a lokaci daya da tsayuwa da mayar da kai gefe tak irin na sarkin garinsu marigayi Allah ya jikan rai
Da kakarfar muryar wannan tsoho jikinsa na daukan tsuma ya bude bakinsa yana fadin" GYARA KIMTSI MUTANEN GARINA, GYARA KIMTSI GA NADIN ALLAH, GYARA KIMTSI BANDA HAYANIYA, GYARA KIMTSI GA JINNI NA SARAUTA, SARKIN GARINA MAI TAUSAYINMU, MAI KAUNARMU, KAWUNNANKU A KASA DOMIN MAGABACINMU NE TAKAWARKA LAFIYA SARKI DAN SARKI JIKAN SARKI *UMAR ABDULAHI BINE MUTALAB*, Ga da a wajen IBRAHIMA DA KHAMISSSSSS, ........" Watau tunda aka ambaci sunnan nan sarki Khamisss ya daina fahimtar abinda yake faruwa, haka kuma idannuwansa suka dawo kallon gabansa tarrrr ya ringa fitar da numfashi ta bakinsa, har sai da UMAR ABDULAHI BINE MUTALAB ya zauna a kujerar dake hade da tasa, sannan CHIEF OF ARMY MUHYIDEEN MUHAY ya zauna a dayan barin da a da wani ne a sama aman a yanzu ya tashi
Yana zama ya sauke ajiyar zuciya hadi da sake ambaton sunnan Allah da fatan Allah ya bashi dama kar ya fashe da kuka a zaunen nan da yake a gaban mutumen nan da ya wulakantar da rayuwarsa, yana fata yadda ya ga dare ya ga rana to ya jure wannan moment din
Dogaren da suka zube a gabansa, datijai wa'inda suka yo zamani da mahaifinsa ne yake kallo, da kallo irin na soyaya mai tarra kwala a cikin idannuwa Sai kuma a hankali ya daga masu kai dake nuni da ya amsa gaisuwarsu baki daya
A zabure sarki KHAMIS ya juyo a lokacin da baban shehin limamin Yah sheik ya amsa wannan gayata da dumbin kauna bayan an masa bayani a boye ya kuma zo da dukan kwarin gwuiwarsa duda matarsa bata jima da haihuwa ba ya zamto shine wanda zai daura auren a wannan lokaci ya yi gyaran murya a nutse ya shiga gabatar da dukkan abinda ya dace , ga kuma mai amsa kuwa a gefe yana fadin komai a cikin amsa kuwar ta yadda yan cikon gida ke ji da kunnayensu haka kuma yan nesa da nesa
Cikin kankanin lokaci aka daura auren MUHAMMAD da NAHIDT UMAR ABDULAHI BINE MUTALAB bisa sadaki kwakwara mai motsi wanda ana gama sanarwar daurin auren mai amsa kuwa ya sanar da babar murya sannan ya sake buda muryarsa ya sanar da sako kamar haka" SUGABAN Sojojin kasar nan watau MUHYIDEEN MUHAY yana mai sanar da dukan wani farar hula cewa ya ja ya koma , yana godiya da halartar daurin auren da aka yi yana fatan alkhairi"
Ana fadin haka sojojin suka shiga bada kokari ta wajen janye mutanen da suka tabata babu su a cikin hurumin maganar cikin mutuntatawa ba cikin wulakantarwa ba har suka idasa janye su gaba daya sannan suka sake zagaye wajen da iya wa'inda abin ya shafa
Ajiyar zuciya Muhammad ya yi yana sake sadda kansa, haka dukkan yawancin wasu manya manyan wajen kawunnansu a kasa suke a sade ciko harda shi din da kansa sarki Khamissss
Sosai ya iya controling din kansa a sanyaye sosai ya furta"Zaka iya hakuri da goyar dake son kaika wuta ka adana tsufanka ka rufawa kanka asiri ka yi aiki na ilimi ka mika kayan aron dake hannunka kuwa Papah ba tare da an wulakantar da junna da tashin tashina ba? Domin shi rufin asiri dadi gareshi koda a wajen mai laifi ne, ina fata alfarmar rufa maka nima Allah ya rufa min"
Kamar yadda ya dauki maganar haka shima ya dago da dogon kallo jikinsa na bari Zufar dake tsago a jikinsa mai tarin yawa ce, hankalinsa a tashe ya furta" Ta yaya? Ta yaya ka rayu bayan irin ukubar da ka gani? Ta yaya ka warke daga cutar haukan da kake ciki?"
Idannuwansa ya saka cikin nasa tarrrrr a kausashe ya ce" Ta hanyar wanda ya busa maka numfashi, Khamiss Mutalab ta yaya ka kwaci hakin da ba naka ba, ka tura wajen da baka da masaniyar fadawar kafafuwa, ka bi da bita da kulli kuma ka ki kyautatawa kasarka? Ka yi kokarin yin komai da murmushi domin kasarka na kallonka, ana haskaka ne!"
A firgice ya juyo wajen da masu dauka suke, bayanan da suke ne ya sake saka zuciyarsa neman tsayawa Juyowa ya sake yi a birkice ya ce" Kana nufin na baka kujerar da a kanta na aikata shirka? Kujerar da na fitar da kai sannan na haukata dan uwana? Kujerar da nake mulka da dukkan karfina? Kana so ka ce ni zan baka kujerar nan? Mema zai sa na baka ne?"
Ajiyar zuciya ya sake saukewa yana fadin" Bama so ka tona mu sai ka tona mu?, Khamiss a yanzu ace a barka a saman kujerar nan da shekara goma zai zamto ne idan ranka bai fita daga gangar jikinka ba to fa tsufa irin sosai din nan zai kama ka wanda zaka dawo baka fahimtar komai dake gabanka, haka ka zaba ne? Kuma ka san ko da karfin Allah zan iya amsa, bale talakawana suka ce ka sauka ka bani abinda yake nawa!"
Zai kuma yin wata maganar a gigice Muhyideen ya karkato kadan shima ya make murya sosai, sai dai ina, muryar tasa ba zata fita a hankali sosai din ba ya dan dube su ya dan yi murmushi ya ce" Allah ya karra lafiya a gaskiya idan aka amshi kujerar nan ta laluma ni aka cuta, inaga fa har rantsuwa na yi kan sai na yi wasan kura da azalumin da ya aikata haka dan na zubar da sheda ta kasance izina ga mai son aikata irin haka, ka ga fa......" Sai kuwa ya mike ya kwabe babar rigar dake sama hadi da hular dake saman kansa ya zubar, cikin lamari na ikon Allah sai ya kwabe dayar rigarma wace daga ita sai farar ciki kadai ta rage ta cen ciki mai siraran hannaye irin rigar nan dai ta maza sai ko wandon shadar da yake sanye da shi, hakan ya bayanar da bindigar dake jikinsa da manyan damatsunnansa Hankali kwonce ya juya wajen su Aban Shuwwa da ya yu mutuwar zaune ya wangale baki da hanci yana kallonsa ya karasa a nutse ya dan yi murmushi ya ce" Siriki dan bani Alkur'anin mana"
Ido ya kyafta da sauri, sai kuma ya dan zabura ya bashi alkur'anin da aka zo da shi dan hakan Ya amsa da hannu bibiyu ya koma gaban sarakan da dukkan wasu masu kallo Wajen camerar ya juyo ya ce" Ku kashe daukan zaku dauki wajen nadi" A yadda ya yi maganar a dole suka kashe sunna kyamewa da takaicin rashin daukarwa al'uma wannan rahoto mai dumi dumi