Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 61

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 61

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 61: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 61. Da kyau ya ajiye alkur'anin saman kujerar ya tsaya a gabansu sosai ya…

3,374 words

Da kyau ya ajiye alkur'anin saman kujerar ya tsaya a gabansu sosai ya bude muryarsa ya ce" Allah taimaki Baba KHAMIS, inaga ya dace mu yi mu gama dan walahi kade kade nake ji a cikin gidan cen da busa kar aje harda kartin makadan nan aka shiga kuma ita kuma tana wajen, da wahala ta kasa yabawa, Gaskiya ka san kun san abinda ka aikata shi yasa aka sameka a nan, to ba yadda ban yi da su ba kan a yaku masarautar taka a tube maka rawanin ta balbalin balaki suka ce aa, ai kawai a barka da halinka, an cuce ni sosai , sai dai bani da yadda zan yi gaskiya, aman inaga an fara gabatar min da bidi'a, tunda dai sai kwana kwana kuke yi gashi shi kuma d'anka ne ko yayane zai sasauta, ni kuma HUKUMA ne, akoy hakkin ma bima al'uma hakkinta, gashi kuma aban namuma al'umar ne, kawai ka dan fahimta a gama tunda ga takardar saka hannun shugaban kasa ya tuge ka, kun yarda sarauta ta shiga siyasa har ya gama aiki fa, kawai zoben nan ne zaka ciro ka bamu a saukake jirginka na jiranka ka koma ka hada dukkan abinda ka ga zai gyaraka dan bama ja baya da balaki ko na waye da izinin Allah, idan ba haka ba kuwa gaskiya zan Shure komai na fara dankara maka Alkur'ani mai tsarki watau ka rantse ta yadda zaka kuturce, sannan na gabatar da hukunci a kanka a kan laifinka, dan shara'a tana hawa kan tsohon da baya iya motsawama bale kai da karfin kaunar mulki ya sa har yanzu ka iya irgen kudi!" Da karfi ya idasa maganar wadda da yawa sai da suka rintse idannuwansu ciki harda sarki Khamisss sannan ya sake fadin" Alkalan na wajen, sun auna sun kuma ce kai nawa ne, Baba ka fa aikata kidan sake tashi yake!"

Aban Shuwwa ya lumshe idannuwansa yana godiya da Allah da har yanzu MUHAY bai shaki Khamisss ba, a yadda MUHAY ke tsaye shi da kansa sai da ya sha jinnin jikinsa, yaron ya gama ginna jikinsa ne daidai da zamaninsa sai fatan Allah ya kiyaye ya karre, gashi sam bashi da tsoro, idan kuwa abu ya gamo shi da mai laifi kawai sai fatan Allah ya sanyaya, bale mai laifi irin na Khamiss? Gaba daya ya mayar da kasar tamkar ta yan daba, a cikin kasar baki daya har kwatance ake da rashin mutuncin yan garin, a bayane ake fadin shaye shaye ai sai garin, lalata sai garin uwa uba ya ba karuwai dama sunna yin lamarinsu harma ya hanna a yi kamu, shi din nan da tsufansa da komai yana sana'a ta miyagun kwayoyi ne a cikin kasarsa, y'ayansa kuwa harda wanda ya yi kisa bai jima a gidan yari ba aka fitar da shi ya fitar da shi waje, matayen kuwa sun bude waje waje na holewa a bayane ba a boye ba, kuma yana zaune shine magabacin wajen ya yi mirsisi yana wulakanci, ga hakkin d'an zumu da ya so salwantarwa, ga ta d'an uwansa da ya salwantar ya hada da hauka...............sosai MUhay ya so a hau kotu a bayana komai, sai manyan suka ci karfinsa , a yanzu kuma ana salamar kowa aka shiga wannan dan tataunawa kunnayensa suka fara jiyo masa busa da kida irin na bare bari a cikin gidansu, an kuma tabatar masa ai iyaye na taka rawar murna da yan mata, gidan ya dauki harami, baban tashin hankalinsa a yanzun kam ba zasu gane ba gaskiya, ya dace a ba kowa hakinsa kawai a watse ina dalili wai?!

"Menene hujarku ta cewa wannan din jinnin ABDULAHI ne? Me me yasa za.....mmmm mmnnmnmnmn!" Da karfi Muhay ya kaiwa kujerar dake gefe duka hakan ya saka sojojin nan gaba dayansu kwasar ihu irin na sarawa suka sarra masa sannan du suka sake maido hankalinsu wajen, ciki harda Dad da bai san lokacin da ya mike tsaye jikinsa na tsuma ba

Da karfi ya ce" So kake mu raba naman jikinka a Wajen nan ne ko so kake mu nuna maka namu salon kwayar ba tare da mun sha komai bane!"

Da sauri Aba ya mike yana kokarin sanyayar da ahin ya ce" MUHYIDEEN ka ga yarona, ka san taurin kai ne da Papah, kawai ka barshi ya tafi ai aikin gama ya gama bai san yana barin wajen aka shiga gyaran wajen ba, ko ya koma yanzu ba mutanen da ya bari zai tarda ba bale ya samu shiga fadar da take tasa, ba sai an kai ga haka ba kar ka manta uwa daya uba daya suke da mahaifina, ko ba komai akoy zumunci"

D'an IBRAHIM ne ya karaso yana hawaye da muryar kuka ya shiga fadin" Zumunci YAH UMAR? YA UMAR idan akoy wanda ya wulakantar da zumunci ai bayan Papah Khamiss ne, nima dan aikin gidan nan nake ba kowa ba, da bakinsa ya fada min cewa na yiwa matarsa biyaya ko na koma tsince tsince irin na ubana, Innalilahi wa inna ilaihi raj'une idanma aka tausayawa wannan mutumen ai an tafka kuskure mai girman gaske wanda sai Allah ya kama mu, cikin da Gimbiya ta haifar ka san ko na wanene?.........." Ya juya wajen sarki khamisss da zuwa yanzu burinsa daya ne ya bace battt ya samu kansa koda a dokar jeji ne da wannan balakin dake gabansa, shi fa tsoronsa daya kar su sake shi daga shi sai wannan mutumen, idan hakan ya tabata bai san me zai faru ba, dan yana gudun ya karya masa wuya a nan Yana hawayen ya ce" Papah na fadi ko cikin waye y"arka ta cikinka ta raina ta kuma haifa?"

Wajen ne ya sake daukan tsitttt, yar jaridar da har jikinta rawa yake ne ta samu bakinta da fadin" Kar dai ace nasa ne?" Sai kuma ta saka hannayenta tana rufe bakin nata tana zarro idannuwanta domin kamar wace ta saka aka juyo kanta du anna kallonta

Jikinsa na rawa ya saka hannunsa yana jan zoben dake hannun nasa ya sake dagowa da wani irin tukukin bakin ciki yana kallonsu ya ce"💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 7️⃣0️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

A rikice jikinsa na rawa ya ringa kallon Sarki Umar, sai kuma ya kalli MUHAY , haka kuma ya kalli jama'ar da ya zo da ita, wace yawanci karara ya fahimci a yanzu da suka ji ainahin abinda ya rufe su da shi shekara da shekaru karara kamar masu jira a miko masu shi su yi yaga yaga da namansa, mutun biyu ne kawai suke cikin hali kwatankwacin wanda yake ciki, watau halin rudani da tashin hankali ya ce" Wa ya ciro shi daga dakin da na rufe shi? Da hannuna na shake shi yana barci aman bai mutu ba? Dogari salau ya ce da hannunsa ya aikashi kiyama ashe bai kashe shi ba? Shi rai nawa ne da shi da zan ringa hada shi da hatsari kala daban daban aman yana mikewa yana Rayuwa?........... Shi shi wani irin................ "

Tsittttt kake ji wajen ya dauka , harta da muryar Zarki khamiss din lokaci daya ta yi shiru , haka kuma du aka zazaro ido sanadiyar bindigar da MUHAY ya ciro a kugunsa ya damko gaban rigar Khamiss ya dorata a saman kansa Idannuwansa sun karra rinewa a kausashe ya ce" Sai da na ce Kar a bi ta haka, irinku basu hau kan decision dinsu ba sai da suka yarda da taurin kansu, da biahewar zuciyarsu, suka nuna min ba sai an kai haka ba, domin irinku yadda suke son abin duniya haka suke son duniyar kanta, domin sun riga sun daukaa cewa matabata ce koda sun mutu babu tsatuwa a gaban Allah bayan mutuwar, sai dai ni gaskiya a yanzu ba zan iya ci gaba da raka shirmenka ba Allah yafe maka zunubanka!" Kunamar bindigar ya danna, a haukace Wajen ya dauki kabara wanda hakan ya sake tarwatsa zuciyar Khamis, har bai san lokacin da ya fara magana a haukace kamar haka ba" Wayyo Allahna wayyo kar ka kashe ni, kar ka min kissa irin na bindiga, kar ka kashe ni na aamsa laifina, na aikata nine nan na aikata dan Allah ka yafe min na aikata ba zan kuma ba, wayo Allahna na shiga uku ga zoben gayanaan zoben gashi na cire gaya nan, kar ku kasheni tunda ban kashe kowa ba, na san na aikata asiri na fitar da shi daga kasar, kuma na haukata kanina aman bayan wannan ni ban kashe kowa ba"

Muhyideen ya amshi zoben yana sakinsa ya ce" Damar kisan ne Allah bai baka ba, aman ai ka dauki niya" Ya juya wajen yarensa ya basu umarnin a tafi da shi da dukkan wasu masu take mada bayan da bai yarda da su ba, idan aka gama bincikw kotu ta yanke masu hukunci daidai da laifukansu su dukansu

Sai da suka gama watsewa sannan ya fuskanci yan jaridar ya kuma basu damar yi masa taambaboyin da suka shafi hawan sabon sarki, inda ya bada amsoshin a takaice sannan a bude, yana gamawa ya yi masu salama sannan ya koma wajen da sojojin ke idasa daidaita wajen domin ci gaba da wunin biki

Ido cikin ido suka yi da Malan dake tsaye yana binsa da kallon al'ajabi

Dan murmushi ya yiwa Malan din yana fadin" Ni wollah idan na ganka sai zan gaisheka sai na tuna ashe nine Aban Nahidt har a saman takarda"

Ido Malan ya karra warawa kafin ya samu kansa da sakin murmushin shima yana girgiza kai, kasa kasa sosai ya ce" Wai yanzun shikenan ni mijin NAHIDT ne?"

MUHAY ya dan kankance idannuwansa sai kuma ya gyada kai yana fadin" to mu je ka gani eh ne ko aa ne, ka ga kidan cen yana sakawa du hankalina tashi ina son shiga ina tsoron abinda zan tarar"

Yar daria ya yi yana fadin" Ka amso rigarka ko ta cikin ce ka saka mu je ai da kunya ka shiga a haka ko?"

Sai a lokacin ya waiga wajen da ya zubar da rigar, sai ya rigunnan a saman cinyar Aban Shuwwa sunna zaune da shi da mutanen dake gefens sai Dad

Ajiyar zuciya ya sauke ya tafi amsa hankalinsa kwonce

Yana zuwa ya duka kasa kansa a kasa, a sanyaye ya ce" Ku gafarceni na zarce abinda aka tsayar, na san abu ne mai matukar wahala hadiye irin haka, aman da ba'a yi haka ba ba zai taba mika wuya ba, ku gafarta min"

Sai a lokacin hankalin Aban shuwwa ya sake kwonciya, domin shi du jira yake ya ga an ririke Muhay a yadda idannuwansa suka kade lokaci daya ya ringa surfa tashin hankalin nan kwarai ya tsoratar da shi, shi da kansa Dad a lokacin da yaron nasa ya danna kunamar harbin nan sosai ya tsorata dan tabas ya dauka zai yi harbin ne, duda ya san da wahala ya dauki doka a hannunsa kai tsaye ya tsartar, aman kuma irin yadda abin ya nuna na ci masa tuwo a kwarya kowa ya sare , da wannan suka sake yi masa nasiha da fatan Allah ya tsare shi kafin ya amshi rigar tasa ya saka abinsa ya yi gaba

Shi kam dama Malan tuni ya fara yin gaban yana jiransa, dan shi kam ba zai iya gwa da gwa da sirikin nasa ba, kunyarsa yake ji fa sosai da sosai

Baban get din suka nufa, duda irin yadda wajen ke hargitse suka kutsa sannan suka dauki dayar hanyar da sun tabata a cen ne kidan nan haka kuma ba shaka matan nan na cen

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce" Allah ka bani ikon hukuntata idan na sameta a cikin filin rawar cen, ya Allah kar ka sa na zamto tamkar gabo a gabanta maimakun nai mata fada sai dai na rarasheta ya Allahna"

Aban SHUWWA ya yi murmushi yana girgiza kansa ya ce" MUHYIDEEN, yanzun idan sunna wajen cen ke zai faru? Kai fa da dama kanama iya yin ido, ni kam sai yadda Allah ya yi da ni, tsorona daya kar ta maimaita kwatanta aikata aikin da ta aikata a asibitin nan"

Me Muhyideen zai yi banda daria, dariar da sai da Malan ya ji mahaukacin mamaki har ya dan tsaya yana kallonsa Sai kuma shima ya yi dariyar suka ci gana da tafiya Malan ya ce" Idanfa matan mutane ne a wajen cen da muke nufa?"

MUHAY ya tabe baki ya ce" Inaga ai muma mazan mutanen ne, ka ga fa a gaskiya idan zaka koma ne ba damuwa aman ba mai sajani juyawa bayan ina ji a jikina tana wajen cen, kuma mai kwasarwa makadan kudadensu namiji ne! Ni na ganshi namiji ne!"

Ai kam shima yana jin hakan ya samu kansa da yin gumm ya bi bayansa suka karasa wajen

Daga nesa kadan suka tsaya sunna kallon ikon Allah, wajen ba zai shigu ba domin mata ne sun zagaye wajen ana kidan da aka kira na sarautar masarautarsu Ji ya yi hankakinsa na neman sake tashi dan haka ya laluba aljihunnan jikinsa domin a sanninsa akoy karamar wayar da ya saka dan kira

Kira ya tura ya koma gefe ya saka a kunnensa Ta jima tana ringin kafin aka daga

A hankali ya ce" Mamah, kunna ina ne?"

Mamansa dake cen wajen nadin gimbiya ta sheda masa ai sarkin ya shigo ana nadin gimbiya

A dan gagauce ya sake tambayar su IBTISAM fa?

Mama ta ce" Sunna bangarenka dan jama'ar ta yi yawa sai na tura su cen harda matan MUHAMMAD "

Ajiyar zuciya ya sauke yana dan murza gaban goshinsa a hankali ya kashe ya juya yana fadin" Sun tsira, sunna bangarena"

Muhammad ya sauke ajiyar zuciyar shima ya ce" Ko dai mun tsira ba"

Da wannan dan barkwoncin suka kuma nufar bangaren nasa, ba dan komai ya nace kan sai ya je ba sai dan ya dan kwatanta mata kar ta je cen din, dan ya kula wajen karra daukan harama yake yi, matan zuwa suke kansu da kafarsu

Shi ya fara shiga bayan ya yi salama an bashi damar shigowar

Kasa kasa Shuwwa ta furta" Katona ne" Nahidt dake zaune taa hakimce Shuwwa din na mata gyaran akaifu ta yi dan murmushin da ya sake yanke gaban Furera ya fadi kasa kasa itama ta ce" Allah ya sa banda Abanki, Shuwwa sai nake ji kamar ina jin kunyar Abanki, kar dai an shiga gabana ban sani ba"

Shuwwa ta yi yar dariya ta mike tana rike dan kwalinta dake son faduwa ta wuce ta gaban Furera dake zaune kauyenta daban bata cikin mutane, fuskar nan tata tamkar an aiko mata da sakon mutuwa, tabas da Malan ya ce ta nemi abinda zai tareta bai yi karya ba, domin a lokacin da jarababiyar makeriyar ta budi baki take fadin maganar da kowa sai da ya girgiza ita kasa ta yasu, tun daga lokacin kuwa du inda suka nufa idannuwanta a kansu, a kasan zuciyarta kuma fata take yi kamar haka.....inama idan aka dauki amarya a motar rakiyarta motar ta juye da su su kone kurmus ta yadda labarinsu zai shude a doran kasa? Ota ta san wani hadi ne dan a wulakantata, ta san wannan maganar karyar karya ce, ina hadin biri da gada ? Wulakantatun nan ne za'a nemi rufawa asiri a wani hada magana tamkar saukar aradu? Sarautar garinsu mai karfi a africa itace ta hayo kan wadinnan?, Tana kallonsu ne dan ta ga iya gudun ruwansu

Tana karasawa daga wajen da yake ta zubawa fuskarsa ido da kuma jikinsa

A hankali ta ce" Ina babar rigar?"

Jikinsa ya bi da kallo sai kuma ya kalleta, itama ba abayar sai doguwar rigar kadai a jikinta ta cake daurin nan na tsokana Dan gyaran murya ya yi irin zai yi kasa kasa sosai din nan ya ce" Tana wajen Aba, ina abayarki?"

Dan murmushi ta yi ta ce" Ka daina yin kamar zaka yi rada, ana jinka ko a hankali ko da karfi MUHYIDEEN"

Kikifta ido ya yi yana kallon bakin da ya ce MUHYIDEEN din, kasa kasan ya sake fadin" Ba ko sakaye, irin sunnayen nan da ake fadawa ababen kauna?"

Kunya ce ta kamata, ta dan sada kanta sai kuma ta dago ta kashe ido daya ta ce" Irin su my kankanar saudiya? My atarugun italiya? My fari masar Parissss?"

Daria ce ta subuce masa har sai da ya saka hannunsa ya rufe bakin nasa ya dan dara a cikinsa kafin ya saka hannun nasa ya dangwale hancinta ya ce" Kece kankanatah..........."

Ido ta zarro tana fadin" Ana jinka fa"

Bakinsa ya sake tabewa ya ce" Inace matan Abanki ne a ciki ko da wasu bakin ne?"

Kai ra girgiza dan haka ya sake tabe bakinsa yana fadin" Je cen kurya ki labe da katon Nahidt muke , ban san me yake so da ni ba, ba zai iya hakurin na kika masa matar bane ko menene? Sai na ji kamar na hanna masa anya wannan ba zai yi zalammmmmmm......." Dif ya dauke wuta sanadiyar hade bakinta da ta yi da nasa bayan ta yi dadage sosai ta cafke lebensa ta rike damatsunnan hannunsa kafin a hankali ta shiga tsotsar bakin nasa, wanda hakan ya saka shi yin baya baya kamar zai kifa sai kuma ya damke bayanta da hannunsa daya ya cika duwawun a hannun nasa ya matsa da dan karfi yana sake rintse idannuwansa

Da sauri ta cire bakin nata tana shigewa kirjinsa tana maida numfashi sannan kasa kasa ta ce" Aban nawa kake cewa zalamame? Kuma fa matansa duka sunna ji, idan suka kulaci abin fa? Ka san mata abin kishi baya masu kadan, kai kuma muryarka bata da sirri My alawar gwongwaninah......."

Idannuwansa dake rintse ya ringa hadiye yawu da kyar ya iya fadin" Mu tafi gida Ibtinah kin ji?"

A hankali ta dago fuskarta tana kallonsa, a sanyaye ta ce" Da gaske kake ba zan raka Nahidt dakinta ba?"

Shima kurre fuskar tata ya yi da kallo yana tunani yana cewa sun gama maganar nan kau? Sai kuma ya maida kanta saman kirjinsa ya dora a hankali yana shafawa ya ce" Kin ga jirgin da zai kaisu nan da awa daya zai sauka , zasu juya da yan rakiyarta mutun hudu da Dad ya wakilta kuma a dawo da su a yau yau, Ibtinah muma a jibi zamu koma na koma bakin aikina, sshikenan gaki gata, za'ina kaiki da kaina gidanta ina dauko abina, aman yanzun ki min uzuri ki zauna da ni itama ki ba Abanki daman ya zauna da ita na yau da gobe kawai.............." Ya karashe a hankali yana sake kallonta, ya kuma dago habarta ya ce" Na kamu, na kamu da yawa.......ba zaki fahimta ba, aman baban tashin hankali motsawa daga kusa da ke, aman idan hakan zai tayar maki da alkhairi hankali zan yi hakuri"

Idannuwanta ta lumshe a hankali tana kallonsa na yan dakiku, ya kamu da me? Ya kamu da mene? Sai kuma ta saki murmushi a sanyaye ya sake maida kanta saman kirjinsa tana fadin" Allah ya nuna mana jibin in sha Allah"

Readers Also Read