Kenza eBookz

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 62

Alkalamin kaddarata by sajeeda - Chapter 62

Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 62: Alkalamin kaddarata by sajeeda Chapter 62. Sosai ya yi mamakin yadda ta yi saurin yarda da abinda ya fada din…

3,333 words

Sosai ya yi mamakin yadda ta yi saurin yarda da abinda ya fada din Bai san lokacin da ya rukunkumeta a jikinsa da dan karfin da sai da ta yi dan karra kafin ya sasauta mata ya sake dago fuskarta yana kallon fuskar tata A fuzge ya ce" Ke fa idan kika tsufa a haka aljannar nan da kanta zata zabe ki Ibtin MUHAY, Allah ya yi ya matso min awanin nan na mika wancen hannun wancen na jaki mu je inda ya dace muryata ta bude hankali kwonce".....

Da sauri ta sake sada kanta tana cike da kunya ta juya da gudu ta shige ciki tana yar dariyar da ta saka Furera sake binta da kallo har ta karasa wajen da suke zazaune ta dauki jug din tsumin Nahidt ta kafa kai ta sha sosai ta ajiye tana yiwa Fauzy muzurai ta ce " Abinda ba zai barni ba gwara ya kasheni a huta!"

Haka suka tuntsure da dariyarsu sunna tafawa wanda hakan ya saka Malama sauke ajiyar zuciya tana cire tunanin cewa wai Malan ya kasa zama da hakurin har a mika masa ya zo gani? Aman gannin shiru bai shigo ba sai ya saka ta ware ta ci gaba da tsoma bakinta a hirarsu sunna shan dariyar tare, inda Furera take kutuntuma ashar kala daban daban a zuciyarta tana tsitainema kowa dake wajen, sai dai ba halin nunawa domin bata manta zaneta da wannan mai shige da baby dol din ta yi ba, zasu koma ne zasu zuba kishin da yayarta ba ita ba! Su zaaiwa karyar sarauta ?💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 7️⃣1️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Da wannan tarin taron farin cikin aka kusan wuni ana tarbar baku ta ko wani bangare, domin auren ba na Nahidt kadai bane aka daura, kowa daga bangarensa yana abinda zai gyara shi har lokacin tafiyarsu ya yi

A lokacin da akai masu rakiya aéroport ya kasance sun cike filin jirgin ne, domin Aba da yan rakiyarsa ciki harda su Dad da Mama, domin sai Mama ta mika Nahidt dakinta zata dawo, A daidai lokacin da zasu daga ne Shuwwa ta fashe da kuka, da kyar aka rarasheta domin tunda take bata taba rabuwa da yar uwarta na kasa da kasa ba sai yau sanadiyar darajar aure, ita kanta Nahidt din kukan take yi kamar ranta zai fita domin ta fi tausayawa kanwarta a kan kanta, sai dai yaya zata yi, dole zata tafi, idanma ta yi hakuri ai Shuwwa din ta ce Zasu dawo suma tare Da wannan suka dawo wajen da zasunna hangen tashin jirgin duba da ba'a bari a matse waje idan baka cikin masi dagawa, danma sojan dake tare da ita ne ta yi rakiyar ciki Tana jingine a kirjinsa har jirgin ya fara tafiya a doguwar hanyarsa , sunna hangensa har ya cida ya tashi, hakan ya saka ta fashe da wani kukan tana rungume tahi a jikinta hadi da fadin" Ta tafihhhhhhhhhh"

Ajiyar Zuciya ya sauke a sanyaye ya ce" Zan fa taya ki kukan nan, kuma kin san za'a shiga tashin hankalin kallo a wajen nan, ke na kula bama kukan su Aba sun tafi kike ba, na wancen y'ar kike, kuma ni du a banza ko?"

Kanta ta dago tana ta shashekar kukan ta kalle shi ta ce" Nahidt ce fa, Nahidt dina ce fa"

Fuskar ya kurawa ido yana ayana' Na shiga uku, wabilahilazi shagwababiya ce ta karshe, yanzun rarashi fa zan yi dole fa, ko ta ringa tale bakin nan har kartin cen su kalla'

A bayane kuwa sai ya riko hannayenta yana fadin" Kin ga in yauma kike so mu bisu kawai sai mu bisu, saima mu je mu yi waya da Aban naki tunda dai bangaren na Nahidht din dakunna hudu ne kawai a gyara mana daya gamunan zuwa ko? Share hawayen mana haba anmatana"

Yana maganar yana janta ne suka nufi cen balbalin da ake ajiyar motocin ya bude mata da kansa ta shiga ya rufe ya zagaya yana karra muzurai da gannin sojojin sun wani zuba masa ido da tarin mamakinsa

A hade ya ce" Kowa ya tafi gidansa ya huta tunda kun ga karshe" Sumui sumui kowa ya nufi motar da ya zo da ita ya shiga kowane na kunshe dariyar rigimar rigimamensu a gaban hajia babarsa, wai dama haka ya iya kula da Matarsa ne?

Bayan ya shige da aka bude masa ya sake janyota jikinsa ya kwontar , da gudu bodyguard din nasa ya zagaya da direban suka shiga jan motar

Shashekar kukan da take yake ta sauraro yana sake shafa bayanta Sunna isawa tun kafin Bodyguard din ya iya bude masa motar ya bude sannan ya duka ya taimaka mata ta fito Dauketa ya yi cimak a hannunsa ya juya ya shige ciki bakinsa daidai kunnenta yana fadin" Kukan nan kam saura kiris na saki nawa, saura kiris Ibtinah"

IBTISAM kam ta jima da dangana, ta dore da shagwabar ne dan ta ga ta karbu, shagwabar tata na sakata nishadi ita da kankin kanta, inda masu bashi tsaron suka sake mutuwa da mamaki kafin General Almustapha ya furta" Alhmdulilah, yanzu barikin sojoji ta yi Uwa, Allah ya sa ta kasance mai kwontarwa oga hankali, dan kar ta ringa tada masa mu kuma yana jijiga mu!"

Du da amen suka amsa sannan kowa ya koma bakin aikinsa, bi ma'ana masu hawa suka hau , masu sauka kuma suka sauka

Kasancewar cikinsu du a cike yake, haka kuma sun yi sallah sunna shiga da kansa ya yi bayi da ita yana cire mata dukkan abinda yake jikinta Ita dinma sai langwabe masa take yi a jikinsa, domin hanyar ce dama da bata budu ba bata gane irin nauyin mara da minsininta da ake shi ake nema ido rufe ba, a yanzu da ta gane tsoro ke dakatar da ita, a yau kuma yan uwanta sun sake ja mata kunne ta yadda gaskiya tsoron sai dai ta ce Allah ya karra cire mata ya bata ikon juriya da daukan nauyin mijinta ko yayane

Haka jikinsa ke rawa a wajen wankan , ya shige da ita ne dan ya wankota ya nadota, karshe sai ita ce ta wanko shin domin katabus ya kasa sai binta da ido tamkar wanda ya sha wani abu sun masa luhu luhu sun rine

Kasancewar tsakanin Magariba da isha'i ne sunna fitowa jiki ba karfi ya saka jalabiyarsa ya wuce masalaci, ya rigayi kowa zuwa ya zauna jiran sallar domin ita kadai zai yi ya koma ga iyalinsa wace ga dukkan alamu a yau zata bashi hadin kai ya maimaita irin abinda ya faru ranan, da kyar da adu'a ya iya cire tunanin ya ci gaba da salatil annabi yana kuma jiran Liman

____________________________________

A lokacin da suka sauka ba wani tsaye tsaye motocin da suka zo daukarsu aka ware wa'inda zasu nufi gidan amarya da ita, inda Malan ya wuce tuni da abokanansa abokannan arziki suka fara yin gaba, Furera ta wuce ta dauki taxi ba tare da kowama ya kula da ita ba, domin taron ya yi taro, talakawa sun zo tarban sarkinsu, ga masu bada tsaro sun zagaye an tatare ana ta kafa kafa, shi yasama suka yanke hukuncin a sadata da gidanta tun kafin a shige masarauta da ita fitowa kuma ta zama aiki, idan gidan ne zata zo tunda nasu yake yanzun

Ita kam a hankali ta dora kanta a gefen kafadar Mama dake ta yi mata nasiha, nasihar da akai masu a cenma ita ce ake sake jadada mata a cikin motar, nuna mata ake a duniya bata da masoyi irin Muhamadu, an nuna mata wannan bawan Allah da anaiwa mutun sujada da zata yi masa tsabar darajar da ya samu a yanzu a rayuwarta, ga rabuwa da kanwarta, gashi ita maganama basu samu sun yi da Muhammad din ba har yanzun, wannan ya hadasa mata kasalanda mutuwar jiki da sake dulmiya a halin tunani, bata taba sannin cewa wai irin ranar nan haka zata samu kanta a irin wannan halin, ashe dai shi aure ko na bazawara ce sunnansa aure? Ko nata ita NAHIDt sunnansa Aure? Haka aka shige tafkeken get din da shi kansa an cenza kalarsa an saka sabo mai sabon yannayi, kafin ake karasawa wajen ajiye motoci

Kamar yadda aka yi umarni, dogarai suka iyakantar da jama'ar anguwar da suka zo dan wanke kwalkwatar idannuwansu, iya matan nan hudu yan rakiya ne suka idasa shigewa baban falon da Uwar gidan malan ta shaida masu nanne falon Malan din cen ZA'A fara kaita a cen zai tara su ya masu nasiha kamar yadda yayi da Furera, suka bar mutanen da Furera ta gayata da budaden baki da hanci da tunanin me ya hada amaryar malan din da aka ce yarinyar nan ce da ta gama yawon ta zubar da dogaren gidan sabon sarkinsu mai daraja da mutunci sarkinsu wanda suke fatan ya kamanta halaya irin na mahaifinsa na adalci da tausayin talaka

A hakimtaciyar kujera Uwar gidan Malan ta yi masu jagora suka hakimtar da jinnin sarauta, y'arsa baba, y'arsa ta farko NAHIDHT UMAR ABDULAHI BINE MUTALAB

Bayan ta tabatar an gama wadatasu da dukkan abubuwan motsa baki ta nemi su bata dan lokaci kan tana zuwa

Tana fita bangaren Furera ta sake zuwa ta kuma fada mata cewar ta zo iyayen Nahidht zasu juya, kuma ta san du inda malan yake yanzu zai shigo domin baya zarce wannan lokacin bai shigo gidansa ba tunda an yi sallar isha'i

Rai bace Furera dake zaune da kanwarta sunna kitae kitsensu ta bata amsa kamar haka" Kar ki ce dan ya saba, ki dai ce dan yana zumudin zuwa ya idasa shanye sauran romon karti, ke kuma kai na rawa dan a samu gindin zama a gidan sarauta kina kai kawo tamkar ba kishiya akai maki ba, Allah ya tsareni da nuna fuska biyu ko a gaban waye!"

Murmushi ta yi ta dubeta da kyau ta ce" Haka ne, Allah ya tsaremu baki daya, aure dai an riga an yi an gama sai hakuri da fatan zaman lafiya, idan baki manta ba a lokacin da Laure kishiyar babarku ta rako ki i warhaka Malan na gida, haka na amshe ki, shi kishi ai ba hauka bane, ki huta lafiya!"

Tana gama fada ta juya ta yi tafiyarta , ita kuma ta ringa gunduma magangannu kunduma kunduma har sai da ta gaji dan kanta kanwarta na tirata sannan ta sake caka mata dauri tana fadin ta je ta jadada masa bata karbi amanar karuwa ba, idan ta masa ciwo ya dauki mataki

Da wannan hudubar ta fice ta nufi bangarensa, a lokacin da ya shigo din kennan shima bayan sun gama salamar bakin da suka yiwa Nahidt din rakiya harma ya yarda da maganar cewa masu yi mata hidima zasu zo nan da sati guda idan an gama tantance wa'inda suka dace a kawo mata in sha Allah

Tunda ya shigo falon da lalausar salamarsa yannayin gudun jinninsa ya fara cenzawa

A hankali ya ringa amsa gaisuwar Malama dake masa da murmushi kwonce a saman fuskarta, sai kuma ya juya bangaren da Nahidht din take wanda yake ta son kallo tun zuwansa aman ya hanna kansa dan yiwa mai adalci adalci

Idannuwansu ne suka sarke da junna, sai kuma ta yi saurin sada kanta hakan ya sa farar alkyabar dake jikinta sake sadowa ta sake tare gaban goshinta

Dan Murmushi ya sauke na fahimtar kamar wace take jin kunyar hada ido da shi ko menene? Sai kuma ya girgiza kansa yana ayana' Ba dai Yayar Y'ata ba, idan ta ga dama Yanzu ne zata ce min Muhamadu kamar wata gwogwona'

Shigowarta da doka kofar da ta yi ya saka shi waigawa da dan sauri ya zuba mata ido

Salama ta yi ciki ciki, haka kuma jikinta daga ita sai dan kwalin nan da ta yiwa dauri irin na birkitatun yan barikin nan tana taunar cingam, kana gannin yannayinta ta aro lamari ne irin na fitinanun mararsa jin magana irin wa'inda barikin bata karbe su ba suke mata cin karfi da yaji, watau mararsa nutsuwa a barikinma, irin masu ja da karfi da son nuna su din yan duniya ne ta kowani hali

A kujerar da ya dace ya zauna ta karasa ta zauna sannan ta dora kafa daya kan daya tana taunar cingan hadi da yin kas kas kas da cingan din

Har ga Allah ta ba Nahidt dariya, ta ba Malama tausayi, ta kuma ba Aban Shuwwa mamaki da tunanin ita kuma nata salon kishin haka ya sakata dawowa? Subahannalah a haka ta fito dan rashin sannin ciwon kai ta zo har bangarensa? Duda gidansa ba gida bane dake cike da maza, aman ko dan shedanun aljannu ai zaka kamanta rufe jikinka, bale masu aikinsu mata dake yi masu aiki sunna girmama su har sukan duka har kasa su gaishe su da kiransu malamansu, me take son nunawa a haka?

Ajiyar zuciya ya sauke, da yannayinsa na sanyi ya kai zaune a saman kujerar dake gefen ta Malama wace kuma take facing din su biyun

Sake zuba masu ido ya yi d💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥 *ALK'ALAMIN K'ADDARA TA* ‍💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥💔❤‍🔥

*The Hero writer*

*SAJIDA*

_Bismillahir rahamanir rahim_

PAGE:. 7️⃣2️⃣

*P͓̽R͓̽E͓̽S͓̽E͓̽N͓̽T͓̽*

*S̉T̉ỎR̉Ỷ ẢN̉D̉ W̉R̉ỈT̉ỈN̉G̉ B̉Ỷ*

*S͞͞A͞͞J͞͞I͞͞D͞͞A͞͞*

*T͞͞H͞͞E͞͞ H͞͞E͞͞R͞͞O͞͞ W͞͞R͞͞I͞͞T͞͞E͞͞R͞͞'S͞͞ 👇🏻*

1 *yar mahaukaciya* 2 *Banida zabi* 3 *Duk karyar kada* 4 *Baka ce* 5 *Daga tafiya daukar soja* 6 *Kutkale* 7 *Makauniya ce* 8 *Mage mai kwanciyar daukar rai* 9 *Duk nisan jifa* 10 *Dutse* 11 *Idan Ka Raina Inda Kake*. 12 *Neman Na Kaina* 13 *WATA KOKOWAR*

*The Latest Qualitative New Book ALKALAMIN KADARRATA*

*WANNAN BOOK NA KUDI NE BA FREE BANE, IDAN KINA DA RA'AYIN KARANTASHI KI GARZAYO KI BIYA KUDINKI YAR UWA ZAKI SAMU BONUS NA DUKAN LITATAFAINA CIKI HARDA NA KUDIN DA NA GAMA KWANAN NAN, KI GANE................ALKALAMI NA DORA, NA ZUBA RUBUTU......IN SHA ALLAH ZAKI NISHADANTU SANNAN KI KARU💓💓💓*

Zaku biya kuɗin ku ta wannan account numbern 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GTBank Naira 300 ne kacal zaku biya anyi araha an hana bashi.

Ko ku turo Recharge card ta wannan numbern wayar 08038856944 banda vtu hoton katin zaki ɗauka ki turo.

Sannan Sai ku tura shaidar biya ta wannan no din +22793811618

Ga ƴan Niger zaku biya kuɗin ku ta wannan layin +22793811618 katin sahelcom ko AIRTEL ta dala DARI ne ( 500 francs cefa) sai ku tura shaidar ta layin nawa sannan na saka ku a grup din

Sai kun zo🥰🥰🥰🥰🥰

Ajiyar Zuciya ya sauke, da yannayinsa na sanyi ya kai zaune a saman kujerar dake gefen ta Malama wace kuma take facing din su biyun

Sake zuba masu ido ya yi daya bayan daya kafin ya yi dan gyaran murya a tausashe ya furta" Asalamu alaikum wa rahamatullah wa barakatuhu yah ku iyalaina"

A ciki Malama ce kawai muryarta ta bayana a tausashen itama, Nahidht kam ta amsa aman a saman lebenta haka kuma a zuciyarta ta ayana' Toh fa Allah ya kawo mu' Inda Furera ta tabe baki tana ayana' Namiji munafuki algungumi macuci!'

Sake gyara zamansa ya yi ya ci gaba da fadin" Alhmdulilah, kamar yadda kuka sani harma kuka kasance sheda ga wannan rana, yau ta kasance rana ta farin ciki a garemu baki daya, ranar da Allah ya nuna min na sake kamanta sunnar ma'aiki ta hanyar karro maku yar uwa, abokiyar zama, wace nake fata da adu'ar Allah ya sa zamanku ya kasance alkhairi a garemu baki daya, koda da halin karro wata na cikashe hudun ya zamto ta tarda gidana irin gidan da ake koyi da halayan matan shugaban halita annabi muhamadu sallalahu alaihi wa salam, ta yadda sai dai ta zamto cikashin farin cikina in sha Allahu rabih"

A yanzun kam ido cikin ido Nahidt ta dube shi da duba irin na ka fa fara isata, ko ka fa fara kauce hanyar nan, wanda sunna yin ido hudu sai da ya boye murmushinsa domin karara ya gane tabin fadan da ya yi ya karbu ta yiwuma ya samu amsa wa martani a kusa kusa, sai kuma ya idasa da kallon Uwar gidansa wace ta yi murmushi ta sada kanta a nutse ta furta" Allah ya doraka a kan hanyar farin cikinka Yah Ustazzzzz" Wani tsadaden murmushi ya sauke mata yana sake gannin girmanta a kasan zuciyarsa A kasan zuciyar Nahidt kuwa fadi take' Kan balaki, Allah ka sa matar nan ba kililin kasau take min ba, wannan gaskiya itace kishi da ita Balaki ne, gwara ka fafata da mahaukaciyar nan da irin su uwar gidan Malan, yo fisabililahi ni kaina matar girmamata nake a zuciyata bale kuma mijinta, kai jama'a Allah ka saka mu a damshin malamar Aban shuwwa, ka bamu hali irin nata'

Furera kam Allah kadai ya san irin zagin da ta rawaito a yau a cikin zuciyarta ta kuma auna shi kan mai uwa da wabi, ba ogan bale makarabansa

Sake muzgutawa ya yi yana fadin" Hajia, da Furera Ga Nahidht, Nahidt ga Hajia da kuma firera, zan so ku yi zama na adalci a tsakaninku, ku kyautata kyautatawa junna sai ku ga Allah ya baku ikon kare hakin dan uwanku harma da ni kan kaina, ina fatan zan samu haka a wajenku?"

Tsakin da take ta rikewa ne ya bale daga bakinta, ta kuwa ja shi da karfin balakin da ya saka suka sake dubanta gaba dayansu Da sauri Malama ta dauke maganar da fadin" In sha Allah ya ustaz, Allah ya bamu ikon fin karfin zuciyarmu alfarmar annabi da alkur'ani"

A dole ya janye dubansa a kan Furera ya lumshe idannuwansa yana hadiye abinda take son hadasa masa, watau bacin rai, hakan ya sake kunnata da kona mata zuciya To a kan me zata zauna a mayar da ita kamar wata banza a waje ?

Shi kuma sai ya sake karkatawa garesu yana tuna ranar da aka kawo furerar, a ranar ita da kanta ta yanke cewa zasunna yin kwana bibiyu ne a gidan, da kanta ta ringa amsa adu'o'in nan tana ta rawar kai duda ya daukota ne a matsayin budurwa, sam a ranar bai fuskanci irin haka daga uwar gidansa ba, hasalima sai da ya je yi mata sai da safe ya samu kamar Idannuwanta sun yi ja, a nan ya gane cewa lalle Malama na sonsa irin son da ta kasa hanna shi son wani abin bayanta, harma ta taimaka masa, ta kuma yi da zuciya daya, a ranar sai da yaa dade yana rarashinta har ta dawo kyakyata daria kafin ya bar dakinta, sai ga yau gashi gaban sabon salo, wai shine har furera ta manta kalar horon da yake mata a gado take masa tsaki? Dan murmushi ya saki na gefen baki yana ayana' zaki yi bayani ne' A bayane kuwa sai ya sake fadin" Yaya kuka tsara sabuwar tafiyarmu ne? Zaku jone da kwana bibiyun da kuke yi kamar na da ko zaku cenza ne?"

Readers Also Read