Anwar and ayman complete - Chapter 9
Anwar and ayman complete Chapter 9: Anwar and ayman complete Chapter 9. Aneesa sosai take farinciki nandanan ta kirawo feena ta gayamata haka feena ta taya…
4,181 words
Aneesa sosai take farinciki nandanan ta kirawo feena ta gayamata haka feena ta taya ta murna sosai tace amma da xarar anyi aure an aje harka ko? Hhhm ay baxan iya ba dole ina tabawa dan rabuwa da Faisal a gurina ba abu bane mai sauqi hhhm kefa kikace Anwar 100% a mekuma xaki da wani faisal gwara ki xauna ki tuba kiyi bautar aure shiii ta katseta feena yaushe kika fara wa'axi bansani ba to barakiji ni saina muri rayuwa kuma baxam iya rabuwa da Faisal lokaci daya ba kema da kike xancenam baki taba damdanasa kinjiba shiyasa Allah fenna tambaya kedai bari xan aramiki shi da bikina banaso keni yanxu na rage harka sonakema nadaina dan wlh in dad yaji abinda nake xai iya kora ta kema dakanki kinsan a boye nake indai yana gida dama mom ce ba ruwan ta dankinwo friend dinki gida ko kinje birthday dinshi ko kindan fita ita ba matsala but dad.... Kedai ayi shiru nandai sukaci gaba sa hirarsu
Tunda abinan ya faru Abba yadaina shiga harkar junior gaisuwa ce kawai ke hada su Anwar kuwa ko gidan yaxo tsakininshi da iyayen harara inya gaishesu su amsa sutashi su bashi guri saidai suyi ta hirar da junior abin yana matukar da munsu amma sunsan wani lokacin xasu sakko
Ayman tunda taji labarin ansawa Anwar da aneesa ranar aure ga badaya hankalin ta ya tashi tarasa yadda xatayi kuka kuwa ta shashi yanxu Mamy tabar yaya yayi aurenan Allah sarkin ta tasan xata wulaqan ta yanxu waxata gayawa kukan ta waxai sharemata batasan kowa ba sai Mamy ita tasani matsayin mahaipiya to itama tanuna mata danta tapi so tayi kuka mai isarta gashi ba ta da waya da takira Mamy ga merry shiru ba alamun ta kwatakwata tadaina jin duriyar ta da tayiwa safeeya magana tace itama so daya sukayi waya da ita intakirata sai ace switch off kai Ayman nandan ta fara rama ko abuncin kirki ta denaci Anwar yanzu baxaman gida yake ba karpe 6:00am yake fita wani likacin saima 12am yake dawowa ayki yaci wuta danhaka besan wanne hali take ciki ba dawani lokacin saiyayi 2days began ta illa yasan tana gidan direbane yake kaita makaranta Wanda yasamomata dan yanzu shikanshima veda lokacin kansa Aneesa ma sai suyi 4days basuyi waya bata damu ba tunda ita aganin ta ta sameshi
Mamy ce tace xataje taga Ayman amma Abba yace kartaje xuwan ta baxaiyi amfani ba kawai tayi mata addu'a yanxu ta daure amma inta ganta saitasa damuwa a ranta amma yanxu dole ta hkr tunda bamai lallashi Allah ya riga ya rubuta ba yanda ta iya dole ta hkr
Yau weekend bayanda basuyi Anwar yaxo aiki ba yace wlh hutawa xaiyi gobe yaxo gannin baxaixo ba suka hkr suka kyaleshi bamatasan be futa ba saida ta gaji da xama ta fito sakamakon yunwar da takeji duk da bawani abincin kirki takeciba yanxu ko kwalliya tadaina iyakacin ta tayi wanka tasa kaya ta feshi cikinta da perfume sai powder da white lipstick kawai ta fito tana tapiya kamar kwai ya fashe mata aciki a dainnin ta sameshi yana breakfast taja kujera ta xauna cikin sanyi murya tace yaya inakwana dagowa yayi suka hada ido tayi saurin yin qasa da nata karemata kallo yayi tsaf ganin yadda duk ta sauya harbaki ta qara taxuba abinci tanaci kadan kadan batawani ci na kirki ba ta miqe inaxaki na koshi ne harara ya watsamata xauna ki cinye abincin saiki tafi Allah yaya nakoshi nace ki xauna ki cinyemin shi kapin ranki yayi mutuqar baci dole taxauna ta kama ci ganin ya tsareta da manyan idanun sa inxaki saki jiki ki saki aure ne dai baxanfasa ba kasa daurewa tayi tace toni nace kafasane saikuma tasa kuka shiru yayi yana kallon ta hartayi me Isar ta ta koma daki ta kwanta tana mamakin damuwar ta itadatake murna xaiyi aure yasake ta to meye na damuwa hhm to basai inxai sakekin ba kina ganin mamyn ma taqi taxo ta duba halin da kike ciki saitaji xuciyar ta qara duhu gashi bata da hanyar Neman merry balle tasan halin da ake ciki.
Kwanci tashi ba wuya Anwar har ya gama hada lepe akwati 24 kowa 12 ba abinda babu komai kai daya ba banbanci ko dayake ay itama Amaryar ce tunda be mata ba ta fara sakin jikin ta taga abin bana wasa bane merry kuwa ko labarinta bataji har lokacin Mamy bata xo ba kuma basuyi waya ba duk yanda Mamy tayi taxo Abba yace akwai lokacin xuwa ba yanxu ba gadan gadan Anwar da Aneesa ke shirin biki dan dad dinta yace ba ruwan sa bare kuma mammy feena kuwa dad dinta na gari danhaka xuwa bikinma saitayi sa'a ya barta tunda yace sai yayi 4month a gida ya huta itama kuma yanxu ta fara gane gaskia, yau saura kwana hudu biki yaune event xasu fara gaba ta a farbs event center a rumfar magaji nan kano ta saci kudin Abban ta sosai na haukama besan ta dibaba Anwar kuwa har yanxu begama aykin ba sunqara musu 2month dukwani kudinshi sunk are ga iyayenshi sunce ko sisi ba xasu taimakamai ba Mamy cewa tayi in ya gayyaci danginta bata ya peba Ayman bawani taro xatayi ba, Aneesa ce taxo da wani abu akan ita baxata xauna da Ayman ba kuma ko iya gidan yayi mata kadan da kyar da lallashi ya lallashe ta ta yarda akan insungama ayki yasamu kudinsa xaimata Sabo wanda yafishi Abban ta cewa yayi ko cokali baxaisaimata ba hankalin ta yayi matuqar tashi kuma duk kudin datasata tayi schedule dinsu gurin event dinta guda uku farbs, meenah the efficient event sanda indaxatayi kamu, lauchng da kuma dinner, danhaka ta matsa Anwar yabata kudi yace bashi dashi xagi ta uwa ta Uba ta xageshi tana mataulauci kawai tundayake ba ataba cimaimutunci irin haka har kuka saida yayi lefenta dad hanawa yayi akai gidansa yace intaxo ya bata abokin ta jacson ne yaxo ya tarar tananeman kudi a fujajan danhaka yace ga million 3 in antashi da lunchng sukama hotel tabiya mishi wata bukatarsa dayayiyai da ita abaya ta qi yarda sukwana acan ana I gobe daurin aure bamusu ta yarda bayan antashi daga lunchng suka dau hanya.
Merry ce taxo afujajan gidan Anwar tanaxuwa taga Ayman a kwance waya ta miqamata samun number yaya Anwar lapia ta tambaya lapia kedai kawai sa yauxancika alkwarin da naiwa kaina batare da tagane metakenupi ba tasamata kasancewar ta haddace tana miqamata saitafice daga gidan harfaduwa tayi batadamu ba ta karkade jikin ta ta miqe abaya take binsu har suka isa central hotel daki na 106 tanaganinsu suka shiga dakin suka rupo batare da sunsan da ita ba gefe ta koma ta kira Anwar tace kaxo central hotel daki 106 xakasamu Amaryar ka da kwarto ba jira mexaice ba ta katse taja niqaf dinta ta rupe fuskar ta reception ta koma tace mukulin daki na 106 takeso yace mata ankama tace nasani yace yasabawa doka nabaki karkadamu taciro 500,000 ta ajiye sannan tace cajeni bawani makami a tare dani ga jakatama riqe wani abu kawai xan tabbatar ganin xunxurutun kudi albashin na watanni ya karba yabata extra key din dakin a kofa reception din ta tsaya yakika tsaya nan bedameka ba tunda kagama naka tace da gudu motar Anwar tashigo me dauke da number DANMASANI gaba daya bayacikin hankalin sa duk ya rude tanaganinshi ta rupe fuska har yaqaraso tace barka da isowa muje nakaika dakin tayi gaba ya bita jinshi yake kamar mafarki tabude dakin suka fada lokaci guda suka saki innalillahi wa,inna ilahirraji'un sakamakon abinda idonsu yaga nemusu jirine ya fara daukar Anwar yai saurin xubewa yana maimaita Allahumma ajirni fi musibati was aklifni khairan minha.....
🍎🍇 MUJE ZUWA 🍎🍇
Taku har kullum Dr Rahmacy
For comments 08067450913 [4/10, 7:43 AM] Dr Rahmancy: [ 4/42017 6:12am ]
🍎🍇 ANWAR $ AYMAN 🍎🍇
Written by Rahma A Danmasani
Dedicated to Danmasani family
107
Gabadaya ya gama fita hankalin sa tunda yake beta shiga irin wannan tashin hankalin ba shin mafarki yake ko ido biyu yake ne meyasa Aneesa xataimai wato ita saqo kan saqo innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ya dape kai motsin da sukaji ne ya juyo dasu shiya juyo da Aneesa bayan ta tafi wata duniyar aykuwa wata gigiyarciyar qara ta saki ta na neman kwace kanta shikuwa gogan ko ajikin da da matse ta yake yana toshe mata baki da nasa yaja ayki itakuwa dukanshi take tana neman kwace kanta ina besan me'ake ba shi ganima yake dadi ne ya isheta Anwar wanda ke tsugune kanshi na qasa ya runtse ido yayin da kwakwalwarshi ta tsaya da ayki addo'in kawai yake ja ya kama wannan ya saki wannan ya dau wannan merry ita kanta wacce ta qame ta kasa sarrafa komai sai runtse ido tana kuka tana bariki ba tayi a rayuwa ba shin me karuwa takenema a dunia take sayar da mutuncin ta kai dunia inazaki damu nuni Aneesa tayiwa jacson ya tsaya sannnan ya fara masifa who permitted to you to........ Aneesa ta katse he's my husband sai ya tsaya sororo shikuwa Anwar ficewa yayi yayin da yanayin sa gabadaya ya chanja merry ce tayi qarfin hanlin daga liqaf dinta ya janyo murmushin yaqe ta daure ta kalli Aneesa tace kinyi asara ke a bariki ma jakar jahilace da shugaban karuwan dunia xaiganki sai yakusa ka sheki kira mexaki sai bawa namiji duburar ki ya sadu dake tanan sannan washegarin aurenki kuma namijin ma kafiri mara tsarki, hhhm ko dayake ba abin da yakowoni ne ba alkawarin da Na daukarmiki na cika tayi saurin barin daki taja kofa gap2 ba taga Anwar a gurin ba ta jingina da kofar dakin tasa wani irin kuka mai tsuma xucia tana Allah ka yafemin rayuwar da nayi a baya Allah na tuba Allah ka karbi tubana nasan kai ubangiji ne mai yawan afuwa da rahma kayafemin banyiwa kaina adalci ba nacuci kaina meyakaini wannan rayuwar ta qara fashewa da kuka ta dape kanta da yake sarawa a haka ta rupe fuskar ta nupi kofa dakin ta daya Anwar bega fuskar ta ba kuma tana da tabbacin begane muryar ta ba haka ta pita ta hau motar ta bayan ta bayar da key din da ta karba lokacin yayi dai2 da dagawar motar Anwar a guje da gani Kasan ba a hankalinshi yake
Aneesa mikewa tayi tana saka kayan ta jacson fadi yake ki bari kawai mukarasa tunda aykin gama yagama wannan aybaxaisa yafasa aurarki ba haushin ya kamata duk shi yaja mata ta bangajeshi ba tare da tace komai ba tai ficewar ta ba tare da tasan inda ta nupa ba
Anwar be tsaya ko ina ba saigidan su yashiga ko sallama babu Mamy bata falo sama ya hau direct bedroom din ta ya nufa danbegan ta a falo ba nanma be gantaba saukar ruwan da yakeji ne yasa kwakwalwarshi ta bashi wanka take ya xube kan carpet ya sunkuyar da kansa qasa hartapito besan ta fito ba har ta shirya batasan dashi ba kasancewar ba motsin sa tana shirin fita falo taga mutum turus tayi saida tadan tsora ta ma qafa tasa a tsorace ta dan bugeshi yayi firgigit ya miqe ya riqo ta Mamy Mamy Mamy gabadaya ta rude batasan sanda ta riqoshi ba lapia ta tambayeshi shiru yayi ta,qarajeho mai tambaya wani abu ne yasamu Ayman kai ya girgixa to mene Mamy Dan Allah ki taimakeni dame ta tambaya cikin kosawa Mamy nafasa auren xabura tayi ta sakeshi indai maganar auren ka ce kai saurin barin gidannan tana nuna masa kofa nixakayiwa munafunci gobe ne fa daurin auren sannan kaxo ka rainamin hankali ni na hadama shi da nixakayiwa barikanci ga gaugauta barmin daki ga mamakin ta saitaga yasa kuka ya xube kan gadon ta kuka yake sosai ta qara fadin katashi kafita nace amma kamar tanayi da dutse abin ya fara konamata rai taja hannunshi amma ko motsi beyi ba saima dadacewa yake wlh nafasa auren ta baxan aure ta ba dana aure ta gwara Na mutu wlh Indai kuka auran ita mutuwa xanyi karamar kanwata ita ta dace dani ta isheni ya miqe ya durqusa a gabanta yana fadin Mamy ki taimakeni nasan Abba baxai saurareni ba ajanye daurin aurennan nafasa wlh nafasa mari ta sakarmai yai saurin dagowa nanma taqara sakarmai amma kodamuwa beyi ba abun tunyana da bata haushi yadawo mamaki tace metayima amana taci kamar ya runtse ido yayi yana hango yadda ya gansu aynan da nan numfashin sa yafara daukewa maganar ta tsaya da sauri ta riqoshi wai mejefaruwa ne Aneesa Aneesa Aneesa kawai yake fada can nunfashinshi ya dauke gabadaya Anwar Anwar amma shiru gigicewa ..........
🍎🍇MUJE XUWA 🍎🍇
Taku had kullum Dr Rahmancy
For comments 08067450913 [4/10, 7:43 AM] Dr Rahmancy: [ 4/4/2017 10:8am ]
🍎🍇 ANWAR $ AYMAN 🍎🍇
Written by Rahma A Danmasani
Dedicated to Danmasani family
108
Girgixashi ta shiga yi amma ina shiru waya ta dauka cinkin gigita ta kirawo Abba yana dauka cikin kidima tace wai meke faruwa ne game da me? Ya tambaye ta Anwar ne yaxomin kamar ma ba acikin hayyacin sa yake ba yana ta fadin shi yafasa auren intemakeshi indai aka auramai ita mutuwa xaiyi xance dai mara kan gado da na dauka wasa ne na koreshi wlh kaga yanxuma ya suma ko motsi ba yayi numfashin shi yayi sama, mmttsssswwww...... Tsaki Abba ya ja dallah ki rabu da shi waimu xaimayar abokan wasan sa yana sane rainin hankali ne daxufa suka tashi daga gurin luchng jia sukayi kuma gobe naji anacewa xa'ayi dinner daganan akai amarya yanxu kice yace ya fasa gobe ne fa daurin auren ay ko da gaske yake be isa ba muxaimayar yan iska muce karyayi yace sai yayi muce yayi yaxo yace ya fasa kuma saura kwana 1 daurin aure aybe isa ya xubarmin da mutun ci ba ki rabu dashi APRILFOOL xaimiki tace dan Allah kaxo ba alamun wasa a tare da yaronan katse wayar yayi tabi wayar da kallo takoma gurin Anwar yadda ta barshi haka tassmeshi girgixashi ta kuma yi amma ina memakon ya farfado sai numfashin shi da ya ringa fixga yana sama kamar me asma nan da nan hankalin ta ya qara tashi bala direba takira tace yaxo da mota sukai Anwar asibiti ko 3mt ba ayi ba yaxo su biyu ne suka kamashi da baba megadi da bala suka sashi a bayan mota mamy ta hau gaba suka nupi malam Aminu kano da shi a mota ta kira Abba tace suntapi asibiti
Merry tunda taje gida ta shiga dakin ta tana rusa kuka tana danasanin rayuwar ta ta baya da Neman Allah ya yafemata shirun da yayi yawa yasa ummiey ta shigo tasame ta xube tana sujja tana Neman gafar Allah saidatagama Mamy ba kallon ta taxo ta rungume ummiey tana dan Allah Mamy kiyafemin kuncin da nasaki a baya nayi nadama kuka ya kwacemata ita ummiey kukan take tana nidama nadade da yafemiki Maryam fatana Allah yadada shiryaki nagode was Allah daya ganar dake gaskia ta rungumeta duk abinda suke Abu na kallo shima yaji sheshekar kukan ya fito amma ummy ta rigashi shigowa ji sukayi ya tapi sujjada yana yiwa Allah godia duka suka juya yana dagowa merry ta tashi ta durkushe gabanshi kapin tayi magana ya dago ta yace nayafemiki dunia da lahira nidama ban rikekiba kullum addu'ata Allah ya shiryeki da duk al ummar musulmi Allah maji roqon bawa ya amsa min Alhamdulillah nima gatawa addu'ar Allah ya amsamun(Allah ga Rahma 'yar Abdulrahman Allah ka fito mata da sakamakon jarabawa mekyau dan sayyadul mujaheedunah Annabi Muhammad (SAW) ameen Allah) Allah yai miki albarka yabaki miji nagari da 'yaya nagari duka suka amsa da Ameen
Ayman gaba daya hankalin ta ya tashi ganin 9pm na Neman yi Anwar bedawo ba tunda suke be taba kai haka ba ko yadawo da yamma ya fita da magriba duk inda 8:30/40pm ya dawo amma yau shiru hakanan jikin ta ya bata ba lapia ba
Abbah shikanshi da yaga yanayin Anwar saida ya shiga xulumi da tashin hankali Mamy kuwa kuka tasa tace Allah ya isa tsakanin ta da Aneesa ita tasamata da a wannan yanayin baxa ta yafe mata qarfe 9pm dai2 likitan ya fito suka tareshi suna tambayar sa yace ba komai kwakwalwarshi ce kecikin tension da ya samu hutu ya farfado komai xaixama nml sukace Allah yasa cikin sanyi murya amma wani tashin hankali ya sameshi ne Dr ya tambaya wlh bamu sani ba suka hada baki sukace yace bakomai Allah ya bashi lapia
10pm Mamy ta kira faruk ta gayamai yace gashinan xuwa meyasameshi tace ita batasani ba gida ya shigo yacewa ummey ya tapi asibiti su kulle gidan acan xai kwana Anwar ne bashi da lapia meyasa meshi ummiey tace cikin tashin hankali yace bansani ba tace ba gobene daurin auren ba yace eh gobe ne yanayi yana tapia kayimasa sannu yanxu dare yayi gobe da sape maje yace toh lokacin yakai kofa merry kuwa hankalin ta yayi kololuwar tashi gani take itace sila
Aneesa ta gama gararambarta ganin ba sarki sai Allah dole ta koma gida dan bata gun xuwa ba inbanan ba Abba tagani a falo yasa mammy a gaba yana wlh ta fito masa da kudinsa a dankinsa ya ajiye dan duk wanda ya daukudin ko iyaye nane da suka mutu suka dawo suka dauka wlh saina daure su karshe kenan ni ina da mukulin dakin kane yarka xaka tambaya ita kadai ka yarjewa a gidanan shiga dakinka ana haka ta qaraso falon ta wuce su dad yace ke xonan taxo ta tsaya ba tare da tace komai ba yace uban waye ya shigarmin daki ya debi kudina ta yatsine fuska a xuciyar ta tace baxan dauki duka biyu ba ga na rasa Anwar ga na daurin prison donhaka dole wani ya dau daya nadade inason fanshe wulaqancin da kikayimin na cutata ki karben kudi kice kinaxuwa gurin boka ki kashe danhaka dole na rama dad ya katsemata tunani tambayarki nake cikin isa da gadara tace mammy ce mammy ta xare ido nikuma ta ina xandauka ayba yau kikasaba ba bare kice ammiki sharri kaida kanka ayka taba kamata da dollars kace ina tasamu takama qinqina qarshedai takasa fadar gaskia ka rabu da ita ba adade ba kanemi dollars dinka karasa ko ba haka tanayi tana karkada kugu wlh hakane dad yace mammy tace idan ba wadannan hajia saratu ce takawomin ajia lah dad kaji qarya me wannan kudinne xaikasa bude account a banki ya kawowa dangin talauci ajia kuma dad da bakin ta tace dankudinka take xaune da kai tabbas hakane ta taba fada magana xarar bunu idantafi batakomawa gashi ta fadi magana anxo anmata sharri da ita wacce bata da mafita sai gurin Allah nandanan dad yakira police yace sutapi da ita harsai ta fadi inda takaimai kudinsa inbata fada ba suyi ta dukan ta tanaji tana gani akasamata ankwa a katura keyar ta ta bude baki tace insha Allahu yanda kikaimin sharrinan saikingani a kwaryarki
Ayman ganin har 12am shiru ba Anwar ba alamunsa duk masu aiki sunkulle gida suntapi sunkwan ta kuka tasa karurus tana shesheqa
Qarpe 1:00am dai2 Anwar ya farka su Mamy sukayo kansa har suna rige2 Aneesa kawai yakecewa kincuceni na amince miki kin yaudareni ko dayake ni na yaudari kaina naga alamar hakan tun a china kuma amfadamin duk nashare ashe ba sharri akayimiki ba kinfi abun da akefada hannu Abba yakama lokacin da suka isa yace kayafemin kinbin umar ninku da nayi Ku kamin xabi na alheri na raina ban godemuku ba naimusu sakayya da nunamuku Baku isa dani ba gashi na debo sillar ajalina mudum aka auramin Aneesa ganin ta kadai xai iya kasheni domin na tsaneta na tsane ta I hate her toooo ya fashe da matsanancin kuka.......
🍎🍇 MUJE ZUWA 🍎🍇
Taku har kullum Dr Rahmancy
For comments 08067450913 [4/10, 7:43 AM] Dr Rahmancy: [ 5/4/2017 6:07am ]
🍎🍇 ANWAR $ AYMAN 🍎🍇
Written by Dr Rahmancy
Dedicated to Danmasani family
109____110
Mamy ce tace masoyiyar ta ka kuma,harara Abba ya watsa mata tayi saurin shiru ya riqeshi yace ya isa kayi hkr baxu auran ita ba Abbah yace aydama bamu muka ce xamu aura ma ita ba kaikace kana son ta aure a hannun ka yake amma fasashi xaiyi wuya an riga angama komai tunran gini tun ran xane xaiyi magana Dr yashigo yace ya tashi suka ce yaxo ya dan gwagwadashi yace yana bukatar hutu sudan barshi ya samu relief ya fita Abba ne ya kalli Mamy yace ki bi faruk ya ajiyeki gida dare yayi faruk yai saurin cewa ayni a nan xan kwana Na fada a gida ma su rupe kofa to shikenan ba mumu tapi Abba yace suka tapi bayan ta piyar su Dr yaxo yayimasa allura bcc ya daukeshi sai sha biyu ya tashi idon faruk biyu yace sannu yawwa danxo ka taimakan natashi inyi sallah wlh banyi magriba ga isha'i faruk ya kamashi yayi alwala yayi sallah
Da asuba Abba ya kirawo baba Alhaji ya sanar mai halin da ake ci Alhaji baba yace ay bkm larura ce xaije ya lallaba mahaipin ta a daga, ko da baba yaje ya fadawa dad ransa be baci ba dandama shi be wani gayyaci manyan abokansa ba qananan ma ba kowa ba makota kawai ya fadawa dan ya tura afadamusu an daga Abba dama be gayyaci kowa ba dan shima ta gurinshi badamuwa ' yan rimin gado kuwa a kayi musu waya ta wadatar
Bayan sunyi sallar asuba Anwar ya kalli yace jiya kaga Ayman a asibitin nan yace a,ah Dan Allah je gida ka dauke ta ka kaita gidan mu itakadaice a gidan faruk yace ina masu aykin yace suna bangaren su wasu kuma gida suke kwana faruk yace ka bari gari yayi haske yanxu innaje tana daki kaga baxai yiwu Na shiga ba intapi to naje Na dako ta shiru yayi be kara cewa komai ba
6am dai2 su Mamy suka xo da breakfast bayan sunmai ya jiki ya amsa da sauqi su Kansu sunga saukin bakamar jiya ba dan Mamy bccin ta rabi da rabi tayi sai lokacin Ayman ta fado mata tai saurin kallon Abba tace Ayman fa na gida ita kadai yace maxaisame ta ba gidan ta ba ne amma dai aybaxa taji dadi ba wannan babban gidan ace kwakwana kaikaday to mene Abba yace a,ah da komai kasan ta da tsoro Abba dawanan Dan wannan Anwar ne ya kalli faruk ya gane nupin shi yace bana dauko ta dama mijin ta yace a dako ta duka suka kalli Anwar amma ko kallon su beyiba faruk ya dauki ya fita da kyar mamy ta lallabashi yasha tea
Ayman yadda ta ga dare haka taga rana saida asuba barawon bcc ya sace ta shima ba ta dade ba ta farka faruk yana xuwa yayi sa'a yaga su haule suna hada breakfast a kitchen dan haka yace suyi mata magana ta pito bayan sungaisa kafin yayi magana tace ya faruk Dan Allah yaya yana gidan ku ne yace a,ah Dan Allah aramin wayanka inkirashi aygurin sa xamu tace yana ina inmunje kyagani tace muje yace a haka xaki baxaki yi kwalliya tace eh yace a,ah je ki shirya ba musu ta koma damatayi wanka kasancewar yaxame mata jiki ko wanne safiya saitayi wanka hakama yau doguwar riga tasa baka Arabian gown har qasa tayi tolling da dark blue din qaramin mayafi simple make up tayi ta fito dukdahaka tayi kyau yace ko kefa suka tapi ganin sun shiga asibiti tace bashi da lapia ne shiru yayi kamar beji ta ba tace no wonder nasan lapian yaya baxaiqi kwana a gida ba yai parking suka nupi dakin tana shiga ayko su Mamy bata kalla ba taje kusa da gadon ta xauna shikuwa Wanda tunda ta shigo yake kallon ta da murmushi hannunta ta dora kan fuskar sa tace yaya meyake da munka shiru yayi bece komai ba jin hannun ta gurin bakinshi yasa ya faketa ya dan cije ta aykuwa ta kwalla qara daria yayi tace muguntar ma har agadon asibiti sai anyi ta wani turo baki daria sukasa wannan yasa tagane ashe su mamy na dakin tace lah Mamy na ashe kinan ta taso Abba ina kwana lpia lau daughter Mamy baxan gasheki ba fushi nake dake konaima na ba kyayi Mamy tace kaina bisa wuyana tuba nake tasa daria tace wasa nakemiki yaushe xan iya fushi da ke bakiga gaisuwar labarawa xanmiki sabahul khair ya ummiey har Abba saida tabashi daria yanxu komawa gefen gadon tayi ta xauna tace ya kuma kana kwance xa'a daura auren nandanan ya tamke fuska mamy ce tace ki rupemana baki ke ba kya gajia da surutu ganin ba wasa fuskar mamyn tayi shiru can ta fara gyanyadi2 Anwar yace bcc kikeji kai ta gyda ya matsa yace hawo ki kwan ta ganin da gaske hawa xatayi faruk yace xo kikwan ta akan kujerar nan ya tashi Anwar ne ya riqeta aykuwa ta fada kirjinshi ta kwanta ya dora hannun sa kan bayan ta faruk komawa yayi yaxauna ya ganin ikon Allah a hankali bcc ya dauke dagota yayi ya kwantar akan gadon kusa da shi ya makale ta shima nandanam yayi baccin