Kenza eBookz

Arman maleek book 1 complete - Chapter 26

Arman maleek book 1 complete - Chapter 26

Arman maleek book 1 complete Chapter 26: Arman maleek book 1 complete Chapter 26. Gyara ƙafafunsa yay daga inda ya ajiye ys matsar ds su gefe, haksn kuma…

4,363 words

Gyara ƙafafunsa yay daga inda ya ajiye ys matsar ds su gefe, haksn kuma ne ya bata damar ajiye abun da yake hannunta a gefensa, komawa tsyi gurin dining din plates daa cups sai spoons wanda zai ci Abin cin da su ta dauko , a ƙasa ta zauna tare da fara haɗa masa Abin cin a cikin plate.

"Mai a flask .?", ya fada bai kalleta ba, a hankalin tace "Ƙunun tsamiya", "zuba min" ya fada yana ci gaba da Aikinsa, cikin natsuwa ta haɗa masa kunun a cikin wani dan babban cup, kaɗan ta sa mishi Sugar ta miƙa masa kunun da yake ta kamshi ya sha kayan yaji sai kamshi kanunfari da citta yake, cike da kulawa ya ƙarɓi cup din yana mai haɗawa da hannunta, a hankali ta dan kallesa sai kuma ta sun kuyar da kanta ƙasa, a hankali cikin natsuwa ya fara shan kunun tsamiyar sbd dadin da ya mishi har bai sam lokacin da kunun ya ƙare ba, dan kallonta yay kafin yace "ya yi dadi. ƙara min", ya fada yana kallon fuskarta.

cikin jin dadi ta ƙara zuba masa kunun tare da gyara zamanta a gabansa, a hankali ya zuba santi, sai gashi har da yar dariyarta, don a rayuwarta bb abun da take kauna irin tayi abu a yaba mata, har in tama ka yaba mata, to gobe za ta yi ƙoƙari ta linka abun da ta maka saboda ka yabeta.

"Waya koya miki Kunun tsamiya haka ?, gashi dai ke ba wani Abin cin hausawa kika iya ba sosai Amma kunun ya yi dadi", ya fada yana tsareta da mayun idanuwansa , rausayar da kanta ta dan yi cikin tarin jin dadi tace "na iya mana, in Umma Jakadiya nayi ina kalla", ta fada a hankali, "Iyeee Yan matan ba", ya fada cikin yar raha, dariya tayi bata ƙara cewa komai ba, bayan ya gama sha ya dauki plate din da ta zuba masa Special Arish y fara ci a hankali, bayan y gama ya kora da Mango jus, sanyayyiyar gyatsa ya yi, kafin yace "Allah ya yi miki Albarka, y kuma shiryaki, sannan ya baki ikon gane dai dai da ba dai dai ba", "Ameen ", ta Amsa tana kallon zara-zaran yatsun ƙafarsa da wata kyakyawar kumba tawa ƙawanya.

Rurrumtse ƙafaffun yake yana dan jujjuyasu alama sun gaji, zuciyarta ce ta raya mata ta dan daddana masa ƙafafun ko yaji dadin su, jaan ye stool din tayi ta daura ƙafafun nasa akan cinyarta ta shiga dan jajja mishi su a hankali yarda ba zai ji dadi ba, lumshe idanunshi yay yana jin yarda laushi da ɗumin hannunta suke saukar masa da kasala irin mai lalata jikin nan kaji baka iya yin komai.

"Abieh!", ta furta cikin karya murya, ido ya tsareta da shi bai Amsa mata ba, "yau she zan ci gaba da zuwa School ne", watsa hannayensa yay alamar shima bai sani ba, hawaye ne suka zubo mata, hakan yasa ya tattara hankalinsa gareta yana kallon fuskarta, "e-learning though Computer", da sauri ta dago kanta, sauke idanunta tayi ƙasa tace "bana son sa na fi son wanda zan ga lecture shi ma ya ganni zan fi fahimta", ƙureta da idanu yay na wasu seconds kafin yace "kin fi son wanda za ki ga lecture shi ma ya gan ki ?", da sauri ta ɗaga kai.

jinjina kai yay kafin yace "to duka na hana", da sauri ta dago idanunta ta kallesa, "ko ban isa ba ?", ya fada cikin gatsali da jin haushinta na cewa wai ta ma fi son ta ga lecture shima ya ganta, wato SBD a gama kalle masa ita, shi bai kalla ba wasu ƙattin banza su kalleta , "Don....!", tsawar da ta firgitata ya kwatsa mata , da sauri ta kifa kanta a cinyoyinsa ta saki kuka mai rauni, lumshe idanunshi yay a lokacin da ya fara jin saukar hawayenta cinyoyinsa, da suke a fili.

Duk sai ya ji bai ji dadi ba, bai kuma kyauta ba, cikin sanyin jiki ya dago fuskarta, ganin ta rumtse idanunta ga hawaye na zuba akan fuskarta sai ya ji wani abu na masa yawo a zuciya, kafaɗunta ya dago , ya miƙar da ita tsaye, a cinyarsa ya daurata tare da kwantar mata fa kanta a kirjinsa, da sauri ta ƙara manna kanta saitin zuciyarsa tana jin yarda take duka da sauri da sauri, a firgice ta dago idanunta da suke jage-jage da hawaye ta kallesa, hannunta ta daura a sautin zuciyarsa inda take jin yana dukan kamar zai fashe.

Cikin rawar murya tace "Abieh zuciyarka!", ta fada tana kallonsa, idanunshi da sukw cike da kwalla shima ya zuba mata, a hankali yace "mai kika ji", ƙara saurarawa tayi kafin tace , ''na ji tana duka fiye da so Hamsin a cikin second , tana duka da sauri sauri, alamar kamar baka da lafiyar zuciya", jujjuya kansa yay kafin yace , "Uhmmm", ya fada tari na dan taho mishi da sauri ya miƙe ya shiga toilet din da yake cikin palon da sauri ya kuskure jinin da ya zubo masa a hannu sanadin tarin da yay, gulamar da ta faɗo a hannunsa ya wanke, idanunshi da suka cika da hawaye ya mayar, zufar fargabar da ta zubo masa ya share, a hankali ya fito daga toilet din yana dafa bango.

"lafiya Abieh ?", ta fada tana kallonsa, jujjuya mata kai yay tare da zama a ƙasanta, hannayenta biyu y riƙe yana kallon cikin idanunta, a hankali yace "mai yasa ba zaki so ni ba ?, mai na miki ?, mai zai sa ba zaki ƙarɓi aure na ba ? ko na miko tsufa ne da baza ki iya zama da ni a matsayin miji ba, ko kuwa ina da wata Ɗabi'ar da bata miki ba ?", jujjuya kanta tayi tana ƙara kallonsa, don bama zaka taɓa dauka ya yi shekarun da yake da su ba, don ba dai a kirashi da tsoho ba sai dai magidanci sbd tarin ilhama da haiba tare da kwarjin da Allah y zuba masa, bada ban su ba ma da sai dai a kirasa da saurayi, sbd sam bai yi kalar tsufa ba, ko kuwa dai kyan jiki da Allah ya basa ne yasa sam ba'a ganin tsufansa, wanda kuma a ƙalla ba a ƙasaru ba zai bawa 50 baya yama doshi 60.

"Abieh ni fa ina da wanda nake so kuma shi nake son aure pls leave me ", ta fada tana wanchakalar da hamnayensa ta miƙe ta fice da sauri idanunta na fitar da hawaye,bayanta ya bi da kallo, tare da kifewa akan kujera yana dafe saitin zuciyarsa da yake bugawa da sauri-sauri ga wani zafi da gurin yake masa yarda kasan zata fito haka take masa zillo.

9pm taji ring dib wayarta, a hankali ta miƙa hannunta ta dauki wayar, karawa tayi a kunnanta, cikin sanyi da damuwar da ta addabi zuciyarta yi Sallama, yarda ya Amsa mata sai da ta ji gabanta ya faɗi, cikin sauri ta tambayesa lafiya, don ta ji muryarsa ba yarda ta saba jin ta ba, yau din ta mata kama da ta marar lafiyan da ya kusan shekara yana ciwo, tayi wani cool sosai, "lpy lau . ina son ganinki kizo parking space na gidanku", ya fada bai bari ta yi magana ba ya kashe wayar tasa.

jikinta a matuƙar sanyayya , ta dauki babbar Hijab ta daura akan Kayan da suke jikinta, takalmi ta dauka da wayarta tayi waje, tunda ta fara takawa gabanta yake wani irin dukan lugude, a hankali take tafiya tana wawwaga bayanta, don dare ya soma yi, ban da hasken fitilu bb wani haske a gidan, gashi ta chan din bb wani wadataccen haske sosai .

Tun da ta fito daga cikin part dinsu y tsareta da idanu yana kallonta, hijab din jikinta ta yi mata kyau sosai, tana tafiya a hankali cike da natsuwa, sai da ta kusa ƙarasawa parking space din ta tsaya tana kallon tarin matocin da duk suka zama mallakin Abieh'nta, ita sam bata hango wata baƙuwar mota ba, hasken wayarta ta kunna ds niyyar kiransa, ta ga an dalleta da fitilar mota.

cikin natsuwa ta dago idanunta ta zubawa motar da aka haskata da ita idanu, ba ƙarya motar ta haɗu ita zata iya cewa ma bata taɓa ganin kalar motar ba don da gani least one ce, hijab din ta dan tattara ƙasan da yake ƙoƙarin fadar da ita ta fara tafiya zuwa gurin motar, a ya yin da duk tayi taku daya sai ta jo fargaba da dukan da zuciyarta yake mata ya ƙaru har ta ƙarasa gurin mota.

handle din mota ta jaa ta shiga, zamata tayi a gurin mai zaman banza ta zubawa sumar kansa wadda ita kaɗa take iya hangowa idanu , ya kwantar da kansa a jikin sitiyarin motar, hannunsa na dama da ya riƙe sitiyarin ya daura kansa a sama, yana manne da kanula da alama dai bashi da lafiya sosai, tun da gashi har da kanula, shiru cikin motar ya dauka na tsawon minti 20 bb wanda ya cewa kowa uffan , kowa da abun da yake saƙawa a cikin zuciyarsa.

A hankali ya dago kansa da ta zubawa idanu, lumshe ido tayi don a rayuwarta tana kaunar namijin da yake tara suma ballan tana na shi da yake kamar na mata har bayansa, kuma baki siɗik sai sheƙi yake alamar yana jin gyara, kallo daya zakawa sumar da kuma kalar fatarsa kasan ba Asalin Nigeria bane sai dai ko half case ne.

gashin kanshi da ya rufe nasa fuskarsa ya sanya zara-zaran yatsun hannunsa ya yaye gaba daya sumar da ta rufe masa fuskarsa, tare da zuba mata jajayen lumsassun idanunsa......... [5/31, 3:54 PM] (P.R.O) ƳAR LELEN ROYAL: PART 5. CHAPTER 1.

*P. 54.*

A tsorace tayi baya tare da mannuwa a jikin glass din motar tana zazzare idanu, shina idanunshi fes a kanta, cikin wata iriyar murya yace ''hankalinki ya kwanta ?. ni ne dai yanzu za ki iya Amincewa da ni ko kuma har yanzu din ba zaki iya ba ?", ya fada a fusge numfashinshi na wani fusga kamar zai fita daga gangar jikinta, da hannu ta fara nuna shi, bakinta na ƙyarma take furta "J.j...j..Jaaa...Jahan!", ta furta tana zazzare idanunta cike da mugun firgici da tashin hankali.

"Yes i'm Jaahan!", ya fada cikin confidence , jijjiga kanta tayi cikib tarin ɓoyayyan mamaki mai kashe mutum, "ban yi mamaki ba, dama tuni na yi tunanin hakan, ka sani ja cutar da Rayuwataa,ka mata taɓon da har Abada ba zan manta ba, ka sa na yi zurfi akan soyayya wani da kamin basaja, ba zan ce Allah ya isa tsakanina da kai ba, ba kuma zan ce ban yafe ba, Amma haƙiƙanin gaskiya ka cutar da zuciyata, in ma kuma kayi hakan ne domin na soka.." jan numfashi tayi, sai da ta kalli cikin idanunsa kafin tace "Shehi Maleeq ba zan taɓa son ka a matsayin miji ba faƙat sai ka bar min rayuwata na huta", ta fada tana kiciniyar buɗe mota.

Da sauri ya riƙe hannunta, cikin fidda numfashi da kyar yace "ki taimakawa Rayuwata, in kika min haka haƙika kin yi butul ci, sannan Ɗan halak baya manta Alkhairi, ko dubban Alkhairai na a kan ki ya kamata a ce kin sassauta min", kallon tara saura kwata ta mishi kafin tace "kana min gori ne akan abun da ka min ?, rainona da kayi kake son A biyaka ko kuwa Abubuwan da ka min a rayuwa ?, duk abin da kake so ka faɗa a biyaka, kasan zan iya biya domin ni ba matsiyaciya bace, " ta fada tana balle murfin motar.

kwantawa yay akan sitiyarin idanunshi na yin sama yace "zan iya mutuwa in har baki amince min ba", cikin fushi tace "to ka mutu mana Maleeq na hana ka mutuwa ne ? mtswwww!", ta fada tana ficewa A motar.

cikin tsananin baƙin ciki da tashin hankali ya riƙe kirjinshi ya fara tari sosai kamar wanda zai mutu, sai shsheƙa yake, da ƙyar ya fito a mota, yana dafe da kirjinshi ya nufo cikin palo bakinshi duk jini ga shi kuma yana ci gaba da tarin wani jinin na zuba, dakyar ya iya kai wa ƙofar palo, yana kai wa nan ya zube a ƙasa bb numfashi a jikinsa.

Misalin ƙarfe 1am Zayn ya sauko palon ƙasa zai dauki wayarsa, da ya manta a palo, daga chan upstairs ya hangi ƙofar shigowa palo kamar a buɗe, dafe kanshi yay tare da furta "oh god ina ga Hamma ya manta da rufe ƙofan ne yay barci bai rufe ba ", ya fada yana dosar gurin ƙofar , tun da ya fara zuwa gurin ƙofar ya ga kamar mutum a kwance, sai dai bai gasgata abun da idanuwanshi suke gane masa ba, sai da ya ga dagaske dai mutum din ne akwance, da sauri y ƙarasa gurin, ware idanunshi yay tare da cewa "Hamma!", ya furta yana dago kansa, Abun da ya gani ya yi mugun razanar da shi , da mugun kar fi ya furta "Hamma! Hamma!! Hammaaaaa!!!", ya fada tana jijjagasa amma shiru.

"Ayyana! , Umma, Sayyid, Abdul"ya fada da iya karfinsa wanda gaba daya maganar ta karaɗe cikin masarautar da kewayenta" da gudu suka fiffito don dama ba wai irin barcin nan bane sosai ya daukesu don dududu 1pm.

Tun daga chan bakin ƙofar part din Ayyana take furta "lafiya dai Zayn, me yake faruwa ?, mai a hannunka ?", ta fada tana doso gurin, cikin tashin hankali yace "H...h...Ha..Hamma!", da gudu ta ƙaraso gurin, haka Umma Jakadiya da su Sayyid.

Itama da tun ɗazun ta kasa barci sai tunanin halin da ta barsa cikinsa take, ta miƙe da sauri jin ana ta kwala kiran Hamma! Hamma!! babu ƙaƙƙautawa, da dugu ta sauko daga kan bed din , ganij bai kamata ta fita a yarda take bane yasa ta jaa hijab din da ta fita da ita ta zunbula a jikinta, ko shoes bata tsaya sawa ba ta fice da gudu sosai, har kamar zata faɗi, lokacin da zata fito har sun fitar da shi waje suna ƙoƙarin sashi a mota , da gudu ta nufi gurin, tana zuwa suna gama sashi a mota, Ayyana zata shiga, da sauri ta bankaɗa Ayyana baya ta zura kan cikin motar, bata wani jira ba ta ja ƙofar ta rufe, da sauri ta daura kansa akan cinyarta, tana hawaye take kiran sunansa, "Abieh! ,Abieh!! Abieh!!!", ta fada tana kuka, wanda tun yana mata dadi har ya kwi ga yanzun bata ma kaunarsa don in tana yi idanunta kamar zasu zazzago bata jin dadinsu gaba daya Alamar dai basu da lafiya.

da gudu Zayn ya jaa motar bai bari wani ya shiga ba, dole suka shiga wata motae suka biyo baysnsu, "Uncle Zayn numfashinsa fa ya tsaya", ta fada idanunta hawaye sosai.

Da sauri yace "maza ki danna masa kirjinsa numfashi ya dawo kafin mu isa", ya fada yana ci gaba da driving dinsa, da sauri ta daura duka hannayenta a kirjinsa ta fara danna masa, amma shiru, ganin wankin hula yana niyyar kai ta dare, gashi an ƙi ƙarasawa Asibitin yasa ta ware, lips dinta ta daura kan nasa, ta buɗe bakinsa da hannunta ta shiga fesa masa iska, tana fiffitasa da hijab din da take jikinta, SBD ya samu iskar shaƙa.

duk ta bi ta ruɗe, tama rasa ya zata yi, har suka kai Asibiti kuma bai farfaɗo ba, tun kafin Zayn ya gama parking mota ta fito ta shiga Asibitin da gudu, tana kiran Dr da Nurses garin gudu har tuntuɓe ta yi amma bata damu ba ci gaba da ƙwala musu kira kawai take, da sauri suka taho suma, kasantuwar labarinta ya biɗe duniya , kusan kowa ya santa yasa suka dauko keken tuƙa marar lafiya da sauri wai taho , kallonsu tayi tace "Patient din na waje kuyi sauri pls", ta fada a ruɗe, da gudu suka fita da keken.

bin bayanau tayi kafin ta ƙarasa sun daukosa, haka ta biyosu da gudu suka dawo, aka shiga da shi cikin wani room , nan waje ta fara zirga-zirga ta kasa natsuwa sai kuka take, gashi ta ji ciwo sosai Amma ta ƙi natsuwa a yi treat dinta , sai yawo take , ita kam in wani abu ya samesa bata jin zata iya yafewa kanta, tana cikin matsananciyar damuwa, roƙon ta daya Allah y tashi kafaɗunsa, ita kuma a yanzu ta dauki Aniyyar Lelenta sa, za ta bari ya samu kulawarta, zata yarda ta karɓesa a matsayin miji, don bata taɓa dauka yarda ya dauketa a ransa har ya kai haka ba, sai yanzu, da wannan tunanin take ta zirga-zirga ko zafin uban ciwon da taji bata ji.

Awa biyu suka dauka chasss kafin su fara fitowa daga cikin ɗakin, da sauri ta tari gaban Likitan da ya fara fitowa, cikin firgici tace "Dr ya jikin nasa ?", ta fada idanunta ha tsiyayyar da ƙwalla, "ke wace ce din sa ?", ya tambayeta, a hankali tace "Matar sa kuma Ƴarsa please wani hali yake ciki ?", ta fada tana haɗe hannayenta biyu, cike da matsanancin mamaki yace "to biyo ni", ya fada yana yin gaba, Juyawa tayi tana neman in da zata ga Zayn Maleeq Amma bb shi a gurin, da sauri ta biyan Likitan don kar ya ɓace mata.

Shiga suka yi Office din ya bata gurin zama ta zauna, ya dan jima yana kallonta kafin ya fara yan Rubuce-rubucen su na Likitoci mai tsinkawa Ahlin duk wani marar lafiya zuciya, sai da ya gama tas kafin yace "kin san Abun da yake faruwa da shi kuwa ?", da sauri ta girgiza kanta tare da furta "a'a!", kara kallonta ya yi, yay wasu rubuce-rubuce kai ka ce Dan sanda ne yake tambayar wanda ake tuhuma yana rubuta statement , "to yana fama da ciwon zuciya chronic", "Dr ciwon zuciya!", ta fada cikin mugun kaɗuwa.

"Yes, yama dauki tsawon shekaru masu mugun yawa yana tare da shi don a binciken da na yi ya nuna ya kai kusan shekaru 20 yana fama da shi", "innalillahi wa`inna`ilaihi raju`un!", ta furta cikin wani ƙarin fargaba don da har ta fara tunanin ko ita ce ta sa masa mugun zuciyar at one time .

"Dr mai ya kamata yanzu mu yi kenan don sama masa lafiya ?", ta fada tana kamewa, "to dole dai a kiyaye masa duk abun da zai ɓata masa rai , sannan a basa abun da baya so, duk abun da baya so a yi ƙoƙarin nisantar masa da shi, a basa kulawa sosai, sannan ayi ƙoƙarin ɗebe masa kewa kar a barsa shi daya, a ko wani lokaci ayi ƙoƙarin sa shi cikin farin ciki, da wannan nasan in sha Allahu komai zai zo da sauƙi", ya fada cikin tausayawa halin da yake ciki, "to mun gode sosai Dr, yanzu zan iya ganin sa ?", ta fada a hankali jikinta a mugun sanyaye.

"zaki iya Amma ke daya kawai don ba'a son ayi hayani a kusa da shi, please ku yi ƙoƙari ku kiyaye", ya fada cikin dan bada umarni "in sha Allahu!", ta fada tana miƙewa da kyar Sakamakon ƙafarta da tayi tsami sosai .

Dakyar take takawa har ta fice daga cikin Office din, A hankali take tafiya tana dafa bango har ta isa gurin ƙofar, buɗewa tayi ta shiga, chan ta hangesa kwance kan gado, fuskarsa ta ɗashe sosai, ya yi wani fayau, ya dan rame , idanunshi sun shige ciki, tausayin kansu ne ya kamata, tana tafiya tana jin zuciyarta na bugawa, wata irin kaunarsa take ji tana linkuwa a cikin zuciyarta, har ta ƙarasa gurin da yake kwance , zama tayi kan kujerar da take kusa da kansa, idanunta na zubar da hawaye ta kwantar da kanta a gefen nasa kan, cikin wata Cool voice, ta furta "Abieh'na ka yafe ni, na tuba in sha Allah ba zan ƙara ba, zan riƙeka na tarairayeka, in sha Allahu ba zan gujeka ba, zan yi ƙoƙari na rama Alkhairanka gare ni, ina son ka Abieh! ina Son ka Abieh!! ina Kaunarka ba zan taɓa Rayuwa babu kai ba I love you with all my heart , you're my life, you are my Everything , I love you My one and only mine , I love you More A............ [6/1, 6:46 PM] (P.R.O) ƳAR LELEN ROYAL: PART 5.CHAPTER 2.

*P. 55.*

"I love you more Abieh", ta fada tana sakar masa light kiss a lips, a hankali ya dan fara ware idanunshi, wanda suka yi jaa , alamar yana jin ciwo sosai, da sauri ta rike hannunsa mai drip, a hankali tace "Abieh!", bai ce mata komai ba sai idanunsa da ya mayar ya rufe alamar baya ma son ganinta, hawayenta da suka kasa tsayawa, ta fara shareww cikin karaya tace "Ayya Abieh don Allah ka yafe min, Wlh bazan kara cewa ka mutu ba, in ka mutu nima zan mutu ka taimaka ka min rai don Allah ka dai na fushi da ni, fushinka a gare ji babban bala'i ne, na yarda zan Amsheka a matsayin miji, duk rintsi duk wuya zan riƙe ka bazan taɓa barin ka ba har Abada, please Abieh for give me, " ta fada tana daura kanta akan kirjinsa.

hannunshi da yat mishi nauyi ya sa ya dago kanta daga kan kirjinsa ya daura akan kafadarshi, cikin wani irin sanyi da yake dan zubo mishi cikin jiki yace "Ouch!", da sauri ta daga kanta, cikin tsananin kulawa har lokacin idanunta basu dai na zuba da hawaye ba, ta kallesa tare da cewa "lafiya ?, mai yake maka ciwo ? ko na kira Dr ne ?", ta jera masa tambayoyin cikin tsananin kula , yakice hannunta yay daga jikinsa kafin yace "ke da kika ce na mutu babu ruwan ki , mai damuwarki da ciwo na ki matsa min anan bana son ganin ki tunda baki damu da damuwata ba", ya fada yana rufe idanunshi ruf.

zubewa tayi a ƙasa muryarta na kyarma alamar kuka ta durƙusa akan ƙafafunta cike da matsananciyar damuwa, tace "don Allah ka min Afwa, nasan tun bayan Haihuwata kake min Uzuri, duk abun da nayi akan sani ko rashin sa ka kan yimin Uzuri, ka yafe min, don Allah ka yafe min", ta fada tana daura kanta akan gadon muryarta a tsananin karye.

Zuciya da soyayya, tuni ya ji duk wani baƙinta da yake gani ya washe, cikin natsananin kauna, ya daura hannunsa wanda yake daure da drip a kanta, tare da cewa "na yafe miki, Allah ya yafe mana gaba daya", ya fada da a hankali, cikin tsananin farin ciki ta miƙe tsaye, faɗawa tayi kan kirjinsa ta rungumesa , cikin tarin murna tace "thank you Abieh , and I LOVE YOU", ta fada tana mishi kiss a kumatu, fuskarsa ce ta yalwatu da wani ƙasaitaccen murmushi,a kunne ya raɗa mata "love you more and more Cutie pie", ya fada shima yana sakar mata kiss a kunnanta.

Sauka tayi daga kan jikinsa, ta zauna a gefen kansa, kansa ta daura akan cinyarta tana shafa tulin sumar kansa, da take matuƙar daukar mata hankali, idanunshi ya lumshe, tuni wani barci mai dadin gaske da ya jima bai yi kalarsa ba ya daukesa.

sosai yake barcin wanda yake ƙara saukar masa da natsuwa da wani irin kwanciyar hankali na musamman, ita kuwa idanu ta zuba masa, cike da tausayawa, da kuma wata zallar kauna wadda bata san iyakar yarda take masa ba, ranar haka ta kwana kanta na kan cinyarta tana shafawa, fara kiran Sallah Asuba akan kunnansa, sai dai ya kasa zare jikinsa daga nata, sai yay luf yans shaƙar kamshin turarenta mai dadi, sai da yaji ana niyyar shiga Sallar Asuba kafin ta miƙe a hankali, gyara mata kwanciyarta ya y, yarda zata ji dadin barcin, shi kuma ya wuce Bathroom a hankali yana dafa bango.

Ruwa ya watsawa jikinsa, kafin ya dauro Alwalla, ko da ya fito ya kalli inda take har lokacin barci take bata farka ba, da alama bata samu barcin dare ba, sai yanzu take samun yinsa.

sanyayyan numfashi ya fesar, kafin ya fara dudduba in da zai ga Sallayar yin Sallah, bai wani sha wahala gurin nema ba ya hangeta chan kan fridge din da yake gefen gado, a hankali ya tafi ya dauka, shimfiɗawa yay , ya fara Sallah, har ya idar bata motsa daga inda take barcinta ba.

Gefen gadon ya ƙara matsawa, a hankali ya kama ƙafarta ta dama ya dan jaa, A hankali ta dan motsa ƙafar ta gyara kwanciyarta, sai a lokacin ya ga ciwon da yake ƙafarta, da sauri ya jaawo ƙafar yana dubawa, dan lumshe idanunshi ya yi, ganin wani irin ciwo da ta ji amma ita vata damu ba, gashi da alama ma zai yi zafi, amma ita ta lafiyarsa take, ɗakin ya shiga hangawa ta inda zai ga First aid box , kasantuwar a irin ɗakun nan ana samun kayan taimakon gaggawa.

dakyar ya miƙe ya ƙarasa gurin, daukowa ya yi, ya dawo inda take ya zauna gyara mata ƙafarta yay, kafin ya fara wanke mata ciwon, Sprit din da ya sanya mata ne da Hydrogen yasa ta bude idanunta, a hankali ta shiga motsa ƙafarta, miƙewa tayi ta zauna, kallon ta ya yi kafin yace "na tashe ki ko ?", tsareshi tayi da idanu ba tare da ta furta komai ba, hakan ya sa ya ci gaba da wanke mata ciwon, mutsu-mutsu ta hau yi da ƙafar , "sorry an kusa gamawa", ta fada yana fara sanya mata bandage a ƙafar, bayan ya gama yace "sauko a hankali ki zo ki yi Sallah", ya fada yana jingina kansa da jikin gado.

A hankali ta miƙe ta nufi Bathroom din, wawware idanunta ta shiga yi cikin toilet din don ita yanzu a cikin Sallah babu abun da bata manta ba, tunda ita dai rabon da tayi ta har mantuwarta ma ta manta, haka nan ta ƙwamutsa ta fito, idanunshi a kanta ta fito daga bathroom din kanta a ƙasa, cikin sanyayyiyar murya yace "zo!", babu musu ta zo gabansa ra zuƙunna.

Riƙe hannayenta ya yi ya zauna da ita gefensa, a hankali yace "ya naga lam'a a gaɓɓanki ?", ya fada yana lakato guiwar hannunta da bata wani wanku ba don wani gurin ma bai san da ana alwala ba.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull