Kenza eBookz

Arman maleek book 1 complete - Chapter 28

Arman maleek book 1 complete - Chapter 28

Arman maleek book 1 complete Chapter 28: Arman maleek book 1 complete Chapter 28. Bai fito daga part nasa ba sai dare, tana zaune a palon ta, ya shigo, da…

4,500 words

Bai fito daga part nasa ba sai dare, tana zaune a palon ta, ya shigo, da sauri ta ɗaga kai ta kallesa, lumshe masa idanunta tayi, tare da mishi tattausan murmushi, shima murmushin ya mata kafin ya zauna kusa da ita, "mai kike yanzu?", kallon Laptop din da yake kan jikinta yay, tare da cewa "Game!", daga kanta tayi, ba tare da tace komai ba, fesar da Numfashi tayi Alamar har lokacin zuciyarsa bata gama yin sanyi ba yace "ina son ki haɗa min kaya na zan je Abuja gobe, "kallonsa tayi da mamaki kafin tace "jikin fa ?", a hankali yace "na warke", cikin natsuwa tace "Shi kenan " , kama hannunta yay suka fito daga part dinta zuwa nasa, bb wanda suka haɗu da shi har suka shige, rufe ƙofar yay tare da cewa "mu je", tana gaba yana binta a baya har suka shiga ciki, Zama ya yi a gefen bed ita kuwa, Ƙara min Akwati ta fara ƙoƙarin daukowa daga Saman Wardrop nasa, amma ta kasa daukowa sai tintuɗo take.

Murmushi yay ganin ta dage sai ta dauko da kanta, kuma taƙi ta sa wani abu wanda zai dan ɗaga ta sama, bb tsammani ta ji an ɗagata sama, da sauri ta kallesa, murmushi sukawa juna, sai da ta dauko kafin ya sauko da ita ƙasa, komawa yay ya zauna, ita kuma ta Buɗe wardrop nasa, ta fara zuba masa irin suturun da tasan yana sawa, sai da ta cika Akwatin dam kafin tace ,"Abieh na gama", kallonta yay , kafin yace "kin sa komai dai ko ?", gyaɗa masa kanta tayi, "okay sannu da Aiki to, bari na yi wanka na fito", ya fada yana miƙewa, ita kuwa zama tayi a inda ya tashi, ta fara danna laptop dinsa, game ta shiga ta fara bugawa cikin ƙawarewa, game din ta riga da ta dauki hankalinta har bata san lokacin da ya fito daga ban ɗakin ba, sai maganarsa da ta ji, bata dago ba, kanta na ƙasa take basa bayanin duk tambayar da ya mata.

Har ya gama shiryawarsa cikin wasu fararen kaya yan silki masu santsi sosai , sun wani irin lafewa a jikinsa sosai, zama yay a gefenta tare da jaan yatsan ƙafarta, "Abieh dai na za su min game Over in kana taɓa ni", ta fada cikin sauri tana dariya, magana yake son yay da ita Amma gaba daya hankalinta baya garesa, hakan yasa ya dauke laptop din ya kashewa, ihu ta sanya masa wanda yasa ya toshe kunansa da sauri, faɗawa jikinsa tayi tare da cewa "Oooh Abieh, ai da ka bari na ci saura ƙiris ka kashe", ta fada tana kwantar da kanta a cinyarsa.

"Cutie pie!", jin yarda ya kira sunan yasa ta miƙa masa gaba daya Attention dinta tare da zuba masa idanu, "zan je Abuja , Amma ina tunanin daga chan zan wuce Umrah , kina son ki zauna anan ko zaki bini ?", ya fada yana kallonta, jim ta dan yi kafin tace "Abieh ni dai zan bika", ta ƙarasa da shagwaɓa, numfashi ya fesar kafin yace "toh je ki faɗawa Umma ta haɗa miki kayanki, sai ki dawo ina kiranki", ya fada cikin dan sanyi da kasalar tare da wani yana yi na musamman da suke ratsa gaɓɓan jikinsa, miƙewa tayi da sauri ta fita , bayanta ya fi da kallo tare da lumshe idanunsa, yana tunanin irin *KISAN MUMMUƘEN* (Littafin Sadeey Yar gatan Royal) da zai wa mutane da yawa, wani irin taushe lips yay da ƙarfi yana jin baƙin cikin dazun na dawo mishi, Addu'o'i ya shiga karantowa na neman tsari.

"Umma Abieh yace ki haɗa min kaya zamu je Abuja gobe", ta fada taba daga chan baƙin kofar ɗakin, dago kanta tayi ta kalleta kafin tace "to, shigo ki ƙarɓa sai muje na haɗa miki", ta fada tana tsiyaya wani abu cikin cup, shigowa tayi ta zauna, kusa da ita, tana kallon abun da take haɗawa, miƙa mata cup din da yake cike da wani Abu da batasan sunansa ba tayi, ƙarɓa tayi ta fara sha, da sauri ta cira bakinta tare da cewa "ba dadi ", harararta tayi kafin tace , "dama na ce miki da dadi ne ?, ni yi sauri ki shanye ki bani cup na" ta fada tana fito da wata gumba.

dakyar ta shanye Abun ta ajiye cup din, tana ajiyewa ta miƙa mata gumbar, "ni wlh in dai bb dadi bazan ci ba", ta fads tana gutsira tasa a bakinta, jin da dadi yasa ta ci gaba da ci.

miƙewa Ayyana tayi suka nufi Bedroom dinta, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama shirya mata kayanta duka, [6/3, 10:57 PM] (P.R.O) ƳAR LELEN ROYAL: PART 5. CHAPTER 4.

*P. 57*

Cikin ƙananin lokaci ta gama haɗa mata komai da zata buƙata, tana zaune a gefe tana buga game, har ta gama bata ce da ita komai ba, zama tayi a gefenta cikin hikima ta fara mata nasiha tare da daura mata da dubarun kama miji ya zamana yana a tafin hannunta, buɗe kunnanta tayi ta kwashe don bb abun da ta bari cikin Nasihu da kuma Shawarwarin da ta bata, sannan ta daura mata da kalolin Abin cicikan da Abubuwan shan da suke saukar da ni'ima tare da gyara jiki, nan suka raba dare tana fada mata Abubuwa masu Amfani da yakama ta ta ringa yi ta riƙa domin gyara Aurenta, da samar da natsuwa a cikin zamantakewarsu, hakan yasa bata koma kiran da yake mata ba, tayi barci anan, da sassafe Umma Jakadiya ta tafi kitchen, ita kuwa sai ma lokacin ta tuna sa cewar yace ta je ta faɗawa Umma aika tazo yana nemanta, da sauri ta sauko daga kan bed din da ta koma zata kwanta ta nufi hanyar waje, direct part dinshi ta nufa, Da sallama ta tura kanta cikin bedroom dinsa.

Babu kowa a bedroom din da alama ma bai dawo daga masjid ba Sallar Subhi, Alƙyaɓɓarsa da ta gani ajiye a kan bed ta yi saurin dauka, cikin ranta tace bari dai itama ta sanya taji ya ake ji in aka sanya Alƙyabbar nan da ya manne yake sawa ko yaushe.

Tun daga gurin sawa ta gama saduda da cewar ba ta Yara bace ta manya ce, wani wahalallan numfashi ta sauke bayan ta gama zuraAlƙyabbar a jikinsa, Abun daure Alƙyabbar ta ja ta daure, tare da zuro hannayenta ta inda aka tanada domin san ya hannaye, a ranta ta Ayyana lallai yana mugun ƙoƙari da yake sanya rigar.

Gaban Mirror ta ƙarasa tana duba kanta, ta mata mugun kyau, sai dai nauyin Rigar har ya shagara, juya bayanta tayi da niyyar cirewa, tsaye ta gansa a ƙofa ya nannaɗe hannayensa yana kallonta, da sauri tayi ƙasa da kanta. tana wasa da hannayenta, da sauri ta dago kanta jin ya riƙe hannayenta, "ta miki kyau", ya furta yana kissing forhead dinta , murmushi ta mishi tare da cewa "Thank you Abieh", jijjina kanshi yay kafin yace "je ki shirya jirgin Safe gare mu", ya fada yana wuceta izuwa banɗaki, itama ma zare Alƙyaɓɓar tayin ta fice da sauri.

8am suka fito cikin shirinsu, shi yana sanye daJallabiya da Alkyabba sai zuba kamshi yake, itama tana sanye da Doguwar rigar Abaya baƙa, fuskarta sanye da wani Sunglass wanda yay bala`in fito mata da yar chaƙas din face nata gwanin kyau, lokacin da suka fito gaba daya kayansu an shirya musu shi a boot din motar da zata kai su Airport , Sallama suka yi da Yan gidan suka shiga mota, kowa na dagawa kowa hannu.

Kai tsaye Airport suka nufa, suna zuwa kamar su ake jira jirginsu ya ɗaga zuwa Abuja, kafin ma su sauka a Airport din Abuja Mai girma President da kansa ya zo tarɓarsa har Airport din.

Bayan saukat jirgin da wasu yan minutes aka buɗe jirgin, passinger cikin jirgin ne suka fara saukowa daya bayan daya, har sai da suka kusan cire tsammanin ganinsu kafin ya fara fitowa, yana gaba tana bayansa, haka suka fara saukowa cikin wata iriyar natsuwarsu da ta zamana iri daya, hat kusan tafiya, inda yake aa kafarsa nan take sa tata.

Suna ƙarasowa gurin Mr President din ya rungume Shehi tare da mishi Welcome, gurin motocinsu suka nufa, ɓaƙar da ta kasance ta daban ba kalar sauran ba suka shiga, suna shiga aka rufe kai tsaye gidan gwamnati aka nufa da su, ana yin parking aka bubbuɗe musu ƙofofi a hankali suka zuzzuro ƙafafunsu suka fito.

Ko hutawa bai yi ba suka zarce Chan babban Hall din gidan Gwamnatinda ake taro, kamat ko yaushe in za'ayi taro, kowa ya hallara, wanda ganinshi da mai girma President ga karamin harraƙa zuciyoyin wasu da dama daga cikin Yan gurin yay ba.

A tunanin kowa yarda yake nuna ƙin Mulki muraran ko da an zo an kawo masa takadar fitowa takara da ake cikewa ga zai ko kalleta ba balle ya cike, Abun da ya basu mamaki, ana kawo masa ya karanta, da wani maƙirin murmushi akan fuskarsa yay sign aka basa abun dangwale ya dangwala, to fa sai idanu ya fara rarrabuwa wannan ya kalli wannan wanman ya kalli wannan, fuskar kowa babu dadi .

Alhaji Auta Baita ne ya kalli Alhaji Sammani shima ya kallesa, wani makirin murmushi suka saki a tare Alamar dai akwai wata ƙulalliya da suka ƙulla, wata kalar inkiya Alhaji Sammani yawa Abokan ƙulla mugun nufinsa, gaba dayansu suka saki murmushi tare da mishi jinjina alamar suna tare da shi duk rintsi, duk wannan ƙulalliyar da ake Maleeq na kallonsu ta ƙasan glass din da ya sanya, ya kuna tabbata wannan muemushin ba'a banza ba, kuma tasan ko mai za'a shirya a kansa za'ayi komai, Taron dai yau bb wata hayaniya don gaba daya Auta Baita ya linkesu da Kuɗaɗɗe, hakan yasa bb wanda yace komai , har mai Girma Gwamna ya gama jawabansa Maleeq ma yay nasa.

Mimmiƙa mishi hannu suka shiga yi na taya murna wanda shi kansa yasan ba wai na taya murnar bane, kawai dai yana basu hannun ne, Fitowarsu ke da wuya yan Jaridu suka baibayesu, da wasu irin tambayoyi, rasa ma yarda zai yi da tambayoyinsu da suka saukar masa da wani irin ciwon kai yay, daga cikin su ne wani yace "Yallaɓai wai da gaske ne kai aka tsayar a matsayin Ɗan Takarar Shugaban ƙasar Nijeriya, kuma har ka Cike takadar takara ?", ya tambayesa yama kallonsa.

Kamar daga Sama Maganarsa ta raki dodon kunnan Abueh , cikin dattaku da isa takama, haiba kwarjini da kamala ya gyara tsayuwarsa kafin yace "In sha Allah!", jinjina kai dan jaridar yay kafin yace "Yanzu ya zaka iya bayyanawa Al`umma game da baka takarar nan, duk da cewar a baya ka nuna ƙin Amincewarka sai kuma yanzu rana tsaka sai ga ka a matsayin Dan takara", wani murmushin gefe daya yay kafin yace "Uhmmm bb Abun da zan ce sai dai nace I`m very interrested Alhamdulillah " ya fada cikin dan kaushin murya.

Murmushi Dan jaridan yay kafin yace "To Maa sha Allah. mai kuma zaka iya cewa game da masu handama da babakere akan dukiyar Al`umma wanda ƙusoshi ne a gwamnati, an sansu sannan ana damawa tare dasu, za ka yi tafiyarka tare da su ko kuwa ?", wani kallo da yay wa mutumin yasa ya tsayar da maganarsa ba tare da ya ƙarasa, jijiiga kansa yay kafin yace !A gwamnati na bb Zalumci, bb Azzalumai, sannan bb Abun da zance da su sai dai na ce musu *MASU GUDU SU GUDU* , domin har in kasan ka ci kwandalar Al`umma gwara kasan inda dare yay maka, domin ba zan bar ko wanne Azzalumi ba, ko kwandala ka ci sai ka fitar da ita, Dodon Azzalumai", yana fadar haka ya wuce abun sa yana dafe kansa da yake masa wani irin ciwo sosai .

Tuni ko wane Gidan redio da Jarida suka naɗa, Ƙasa gaba daya ta dauka, bb abun da kake ji sai sunan *DODON AZZALUMAI* , tun ba'aje ko ina ba gaba daya Jama'a suka yi mubayu'a suka yi Amanar cewa shine zai zame musu *BANGO MAJIN GINA*, *FITILAR HASKA DUHU* *DAYA TAMKAR DA DUBU* sannan kuma *DODON AZZALUMAI DA MACUTA*, tuni su Autah Baita suka fara kaɗewa, sai dai su basa gudu ba kuma su jaa da baya, da su gudu gwara su mutu, ko wace rana ko wane minti da sakan neman hanyar kassara gwamnatinsa suke, neman hanyar da zasu rusasa suke kai neman hanyar da zasu kashesa baki daya suke.

Sati daya suka yi a Abuja suka tattara izuwa Ƙasa mai tsarki domin yin Umrah, sosai suka ji dadin zuwansu Umrar nan, suna kulawa da junansu yarda ya kamata, sun yi wani ƙiba sun yi kyau abunsu, wanda kallo daya zakawa Nahleerh kasan tana da shigar Yaron ciki, na yan satittika, Anty Matar Yaah Muhammad sai kula take da ita , shima kuna riritata yake ko kuɗa baya son ya sauka a kanta, Soyayya kuwa basa boyeta a gaban kowa, itama tana matuƙar jib dadin zamantakewarsu yana mata dukkan abun da take so.

daga nan kuma suka wuce Indiya gurin Mahaifinta, taga gata irin na Uba, taga kula da kauna, sai da ta ji kamar kar ta baro inda yake, da kuka suka rabu bayan yay mata Alƙawarin zuwa kwanan nan.

Daga chan kuma suka koma Ƙasa Nigeria inda shirye-shiryen zaɓe ya taho sosai, don bai fi sauran sati ba, tun kuma da suka dawo bashi da zama kullum yawan Campaign yake gari gari, don ma baya shan wata wahala sosai sakamakon Yarda Jama'a suke kaunarsa, sai dai abun da ya taɓasa shine Alhaji Sammani da aka basa a matsayin Mataimakin shugaban ƙasa .

A yau ya gama yawon Campaign dinsa, in da daga Ƙasar Katsina ya juya, zuwa Gombe, A mota suka tafi shi yasa yay matuƙar gajiya sosai, basu sauka ba sai dare .

Suna Zaune a palo suna fira, suka ji dirar Motoci, kallon-kallo aka shiga yi don bb wanda ya faɗawa dawowarsa sai dai zuwansa, taɓe baki Nahleerh tayi tare da ci gaba da cin Dan Sululun da Umma Jakadiya tayi mata, ya sha man ja da yaji ga yankakkiyar danyar Albasa, Da Sallama ya shigo cikin palon, yana shigowa idanuwansu suka fara haska masa ita, ɓoyayyiyar ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske ya sauke, duk sun lura da shi ban da ita da ta basar kamar Allsh bai yi ruwan mutum a gurin ba.

Sannu da hanya suka shiga mishi, sai da ya gama Amsawa kafin ya wuce ciki, ganin bata tashi ra bisa bane Umma Jakadiya tace "tashi kije ki haɗa masa ruwan wanka mana" taɓe bakinta tayi kafin tace "Ai bai faɗa min zai dawo na" sakin baki Umma tayi tana kallonta , ganin ta ƙara sharewa.

"ke kam dai zn yi yar jakar Uba, dole ne sai ya faɗa miki zai dawo, tun da dai ya dawo ai a gode Allah", taɓe baki tayi tare da cewa "Aikam fa, to sai ki je ki haɗa masa ai" ta fada cikin sigat wasa, daƙuwa ya kwada mata tare da cewa "zaki tashi ko sai na cin miki futsararra", miƙewa tayi , maimaƙon tayi part dinsa sai tayi nata, ta sa key ta kulle tare da hayewa gado , tana cewa "kawai na je ya manne min Alhalin ko sanin sa zuwansa ban yi ba, aiko ba zan je ba don ni nan ta jikina ma nake" ta fada tana lumshe idanunta.

Abun ka da mai Yaron ciki, tuni barci ya dauketa ba tare da ta shirya ba, barcinta take haiƙan, yay ta kiran phone nata tana silent bata ji ba.

gajiya yay ya nufo part dinta ta cikin part dinshi, da yake an yi ƙofa wadda zata isa sadasa da part nata daga cikin palonsa, nannaɗe hannayensa yay yana kallonta ko don ya kwana biyu bai ganta ba sai ya ga ta ƙara mai girma a ido , komai na jikinta ya chanja ta zama kamar ba ita ba, idanu ya tsurawa fatar cikinta da take a lafe har lokacin ba zaka taɓa cewa akwai wata halitta ko ta Yan hanji balle mutum a ciki ba [6/6, 12:04 AM] (P.R.O) ƳAR LELEN ROYAL: PART 5. CHAPTER 5.

*P. 58*

Cike da natsuwa yake takawa zuwa gurin gadon, idanunshi a kanta ba tare da ya ko ƙyafta ba, har ya hau gadon ya shige jikinta bata sani ba, sai da ta ji ana kiciniyar cire mata rigar jikinta kafin ta farka da sauri, Tura bakinta tayi tare da cewa "Abieh!", bai Amsa mata ba, bai kuma fasa abun da yake niyyar yi ba, "Ayya Abieh please bana da lpy fa", ta fada idanunta na tara kwalla, don har yau ita bata wani saba da baƙuncinsa ba, kullum a sabo yake zuwar mata.

tsareta yay da idanu, sai a sanan ya gano ruftawar da idanunta suka yi, idanunshi da suke dauke da zallar muraduwa da buƙatuwar miji zuwa ga matarsa ya lumshe, yana dan lasar lips dinsa don yay mugun miss nata, sati ba wasa ba, musamman shi da kamar an ƙara masa fitina a kanta, baya iya dauke kai .

Rungumeta yay tare da furta"mai yake damun cutie pie na", ya fada yana kiss goshinta, shiru tayi don ita bata ma san mai zata ce ba, ciwo dai irin na masu ciki da zaka rasa mai yake maka ciwo, amma kai dai kasan baka da lafiya, "Allah Abieh ina takura da Cikin nan", ta fads hawaye na zubo mata, cikin tausayawa ya ce "Oooh sannu zaki dai na da yay kwari zaki ga kin dai na jin komai", ya fada yana daura hannunsaakan cikin.

Ƙamshin turarensa da yake mata dadi ta kankamesa tana shaƙa , sai dai kamshin ji take yay mata kaɗan, hakan yasa take ƙara cusa fuskarta a kirjinsa, tana shaƙar kamshin jikinsa, zazzafan numfashi take fasa masa, wanda yasa gaba daya yanayinsa ƙara daguluwa, bata san lokacin da ya ballw mata bottoms din rigarta ba, sai dai ta ji jikinta felat bb komai sai Pant din da bata iya kwanciya in bb shi, bra kam ai sai ta fi sati bata sa ba in har ba zata unguwa ba.

Cikin natsuwa yarda ba zata wahala ko ta ji ciwo ba, ya fara bi da ita, sai dai duk da haka sai da ta ji zafi kamar ana baɗa mata barkono a HQ dinta, yarfe hannu ta shiga yi hawaye na zuba a idanunta, cikin shagwaɓa take dan dukan bayanta tana cewa "Uhmm, Ahhh Abieh ,Wayyo uhmm-uhmmm Abieh da zafi, wayyo marata", ta fada da kyar tana jin mararta na murɗawa, wata iriyar zufa ce ta gama wanke mata gaba daya jikinta, jin yarda take sakin nishi , yasa da sauri ya zare jikinsa, yana dagota a firgice yake mata magana ganin yarda jikinta yake wani cira, zufa na karyo mata daga dukkan sassan jikinta, "ke lafiya ?", ya fads yana jijjigata.

"Abieh marata", ta fada tana manna masa hannayensa akan marar tata , da ta wani ƙulle a guri daya ya cure, numfashi ya fesar cike da tsoro, ɗagota yay ta jingina da jikinsa, share mata zufar ya shiga yi, yana fesa mata da sanyayyiyar iskar bakinsa, a hankali ta ji abun yana warwarewa, har ya gama warewa gaba daya.

nannauyan numfashi ta jaa kafin ta zame a jikinsa ta kwantar da kanta akan filo tana jaan ajiyar zuciya, jin jikinta take yay wani irin liƙis bata iya aikata komai take ji, sai wata iriyar yunwa da tasa jikinta ya fara wani karkarwa.

"Abieh yunwa", ta fada hawaye na zubo mata, da sauri yace "tashi ki tsarkake jikinki, kafin na sama miki abun da zaki ci", ya fada yana miƙewa tsaye, dakyar ta iya miƙewa, tafiya ta fara yi tangal-tangal ta fara yi kamar zata fadi hakan yasa yay saurin tareta, kanta ta kwantar a kirjinsa, tana jin kamar zata faɗi , "Jiri!", ta fada tana rumtse idanunta, tafiya ya shiga yi da ita zuwa Bathroom , ruwa mai dan ɗumi ya sanya mata , sai da ta shiga ciki ta gasa kanta sosai kafin ta fito, Cikakken wanka tayi, tare da dauro towel ta fito a hankali , tana tafiya kamar kwai ya fashe mata a ciki sbd ji take in ta taka kamar wani abu zai faɗo daga jikinta.

Yaye blanket din da yake kan bed din tayi ta zauna gefe, tare da jin gina da jikin bed din, bata jima da zama ba ya shigo Ta ƙofar part dinshi, hannunsa riƙe da tea cup sai plate , zama ya yi a gefenta, tare da kallon cikin tausayawa yace "tashi ki ci", ya fada yana tallafo bayanta.

Matsowa tayi jikinsa tare da jingina da jikinshi, cikin natsuwa ya shiga bata tea tana sha, yana gutsirar kwan da ya soya mata yana bata, har sai da ta cinye duka, a hankali tayi sanyayyiyar gyatsa tare da furta "Alhmdllh", lumshe idanunshi yay ya buɗe tare da furta "Maa sha Allahu", ya fada yana miƙewa, bathroom din ta ya shiga ya tsarkake jikinsa, kafin ya fito har barci ya sureta, hakan yasa bai koma kan gadon ba ya wuce gurin da take yin Sallah ya shiga kai kukansa ga Allah, tare da roƙon kariyar maƙiya a garesa, da iyalansa gaba daya.

bai tashi daga gurin ba sai da aka fara kiran Sallar Farko, bathroom dinta ya ƙara shiga, yayo wanka wata Jallabiya mai laushi da tsantsi, yasa tare da sanya Alƙyabbarsa, turarenta da yanzu sam bata son kamshinsa ya fesa don dama nasa ne ta mishi fin karfi, A hankali ya matsa kusa da bed din, babbar yatsar ƙafarta ya kama, cikin natsuwa ya fara jaan yatsar nata, har sai da ta bude idanunta, "na lura gaba daya yanzu kin koma kasa, ki yashi lokacin Sallah ya yi", ya fada yana ficewa abunsa, sai da ya fita kafin ta iya miƙewa ta fada banɗaki, wanka tayi da Al`wala , lokacin da zata fito an fara kiran Sallah sauri-sauri ta zura tattausay Jallabiyarta fara, ta sanya Hijab ta hau kan daddumarta, Bata tashi daga gurin ba sai guraren 7 , gyara zamanta tayi tare da lumshe idanunta, tuni barci y dauketa .

Haka rayuwarsu ta ci gaba da tafiya, shi yana chan yana ji da mutane ita kuwa bata da aiki sai barci, barci dai da ta kwanta sai barci, ita kanta abun damunta yake, ganin yanzu bata taɓuka komai, wani abun ma tana son yi Amma barcin sai ya hanata, shi kam yanzu ya saba ma da yin hkr, don yanzu bata kaunar ma ya raɓeta in kuwa ya kusance mararta ta ɗunkule sai ta ta shan wahala kafin ta samu ta warware, shi yasa baya ma takura mata, sai dai ya rage zafi ta wani fanonin.

Dayan Bangaren kuwa, Zaɓe nata tahowa, inda abu yazo gab sosai, su Alhaji Sammani kuwa basu fasa mugun ƙullinsu akan Maleeq ba, don ma Ubangiji ya basa kariya, duk abun da za su jefesa da shi sai Allah y karesa, ya kuma basa hanyar ɓullewa, sai dai duk da rashin nasarar da suke samu basu daddara ba, kullum a gurin tsara mugun nufi suke yini.

Basu far ga ba , sai gani suka yi har gobe zabe gashi bb wani Abu da ya samesa, zaɓe kuma bb fashi, mabiyansa sai ƙara gaba suke basa baya, sai fa anan je hankullansu yay mugun tashi, dandanan suka ƙira Yan dabansu, tare da bada Umarnin su shiga cikin gari su tayarwa da mutane hankulla ta yarda ba za'ayi Zaɓe cikin lumana ba.

Dan-danan kuwa suka shiga Aikin da Ubannin gidansu suka sanyasu, suka shiga far wa mutane, suka sassararsu, dukansu da ji musu ciwo, dandan ƙasa duka ta dauka, Cikin tashin Hankali Mai girma Saif- Wazeer ya kira Shugaban Sojoji da na Yan sada, cikin bada Umarni ya fada musu duk rintsi duk wuya, kar gari ya waye ana wannan tashin hankali, suyi duk yarda za suyi su samar da zaman lafiya kafin gobe, cikin Amsar Umarni suka sara masa tare da ficewa.

Cikin lokaci Ƙanƙani komai y fara saituwa, dom gurare da yawa an daina fadan , an kuma kakkama wanda suke faɗan, haka washe gari aka tashi da yawan rashe-rashe da tashin hankulla ba ciwace - ciwace, amma duk da haka, hakan bai hana dubban mutane fitowa ba, duk da suna da fargabar kar a far musu a gurin zaɓen Amma ƙwarin guiwar da Maleeq ya basu a Speech din da yay a wayewar safiyar ranar.

Da Misalin karfe takwas na safiyar ranar, duk Ahalin Abdul-Azeez Sarki suka gama shirinsu na zuwa gurin kaɗa ƙuri'a, dukkansu Lifaya suka sanya, har Uwar Gayyar Nahleerh da ba wani dadi take ji ba, amma ya zamar mata dole zuwan, tana sanye da Lifayarta Coffee wadda ta hau jikinta sosai, ta Amah's Blue , Ayyana ta sanya Baƙa.

Dressing din mazan kuwa sai ya kasance fari gaba dayansu fararen Yadi suka sanya Boyle, da baƙar hula, Sai Maleeq ne kawai ya daura Babbar Alƙyabbarsa irin ta Malaman nan Baƙa , da ratsin Coffee a jiki, a tare suka fito ita ta fito daga part dinta, ta na ta ƙoƙarin sanya Agogo Gucci'n ta, shi kuwa ya fito yana dan daddana wayarsa, sautin takun takalminta da kamshi turarenta, yasa shi dago dara-daran fararen idanunshi ya zuba mata, kallo daya yay mata ya ji zuciyarsa ta girgiza, kafeta yay da manyan idanunsa yana ƙara godiyawa Uban gijin talikai wanda ya halitta masa wannan kyakyawar halitar kuma ya Azurtasa da samunta a matsayin matarsa, lumshe idanunshi yay cikin shauƙin kaunarta da take kara tsuma zuciyarsa, ya ware mata hannayensa, cikin ƙasaita da isa ta shige jikinsa tare da kwantar da kanta akan kirjinsa, sanyayyan kamshin turarensa na Huge Boss ta shaƙa tare da lumshe idanunshi, "Uhmmmmmmmmm I really Miss you Sweet Cucumber ", ta fada tana zagaye dukkan hannayenta a waist dinsa ta manne da jikinsa sosai.

kiss ya mata a kanta tare da matseta a jikinsa ya furta "Miss you more Cutie pie", ya fada yana lumshe idanunshi, sun jima a haka kafin ya kama hannunta suka fito waje, gaba daya Securities din da aka basa suna tsaye a bakin ƙofar shiga sashen da bindigu a hannayensu ga kuma Dogarai a gefe da gefe, da sauri aka buɗe musu mota, Ita ta fara shiga kafin shi y shiga .

Yana shiga ta koma jikinsa ta lafe, tare da lumshe idanunta , kafin su ƙarasa gurin da zasu kaɗa ƙuri'unsu tuni tayi barci, har da munshari , sai da aka ƙaraso filin gurin kafin a tsayar da motocin chan dan nesa da mutane aka yo parking din motar, Securities ne suka buɗe musu mota, suna budewa dogarai suka baibaye gurin motar suka baza manyan rigunansu.

A hankali yasa tafukan hannayensa akan kumatunta , cikin natsuwa ya daura lips dinsa akan nata, cikin natsuwa ya fara tsotsar lips din, A hankali cikin natsuwa ta fara buɗe idanunta, "Abieh!", ta fada tana tura baki, idanu ya tsurawa lips din, taɓe baki ya dan yi kafin yace "ni ki saukar min a jiki, sai barci kike min salon ki lalatamin jiki tun kafin na tsufa, Salon na rasa matar da zata Auran", ya fada yana zameta daga jikinsa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull