Kenza eBookz

Arman maleek book 1 complete - Chapter 29

Arman maleek book 1 complete - Chapter 29

Arman maleek book 1 complete Chapter 29: Arman maleek book 1 complete Chapter 29. Zaro idanunta tayi tare da cewa "Ooh dama har Budget din Aure gareka…

4,386 words

Zaro idanunta tayi tare da cewa "Ooh dama har Budget din Aure gareka bayan ka gama tsofewa", ta fada idanunta a kansa, "kina ga nin Celebrity din Guy kina zancen tsufa ni da tsufa ba yanzu ba Yarinya " jawoshi tayi idanunta na cikowa da hawaye tace "Wlh kai ma ka tsufa, ji furfura fa a kanka" ta fada tana shafa gemunsa, "ni kam bani da furfura ko daya, yarinya yar kyakyawa mai jini a jika ga kyau ga diri", ta fads tana wani lafiyayyan murmushi wanda ya haddasa lomawar beautiful point dinta.

"ina sauran kyan ?, kyan da duk na karar da shi , duba fa ki gani, dafin hannuna ya kama ko ina, Yarinya yanzu kin zama Chusss in ba ni ba bb mai iyawa, ji nan kin wani zama kamar Balloon", ya fada yana daura hannunsa a kirjinta, tuni ta ƙulu da haushi har bata san lokacin da ta fashe da kuka ba, dariya mai kyan gaske wadda ta bayyana fararan haƙoransa masu kyau da suke a jere.

"Come on Babe ke baki san wasa ba, daga wannan Yar maganar kike kuka ?", ya fada yana jawota jikinsa, harararsa tayi tare da cewa "ba ni na sake maka jiki kake mora ba har kake min gori", ta fada tana mayar da hannayenta a idanunta.

"Ahhhh Sorry , ni ya zan yi kika hanani kinsa yarda nake ji da karamin gari da Albarkar Man fetur din nan kuwa, ?, kika hanani sai an kasa gane kan Maleeq", ya fada yana sakar mata kiss, turo baki tayi tare da cewa "ni babu ruwana nan", ta fada cikin maganar da daka ji kasan ta zallar Yarinta ce"kina ƙoƙarin zama First Lady amma har yanzu baki bar Abubuwa irin na Childish ba" ya fada yana zare mata yatsar da tasa a bakinta.

"to! to!! Abieh dududu shekarata nawa, ni fa ji na nake kamar Jaririya", ta fada tana kallonsa, yar dariya ya yi kafib yace "Uhmmm ko ba Yarinya ba ?, " daga kanta tayi da sauri, jinjina kai yay tare da cewa "lallai kam wannan sai dai Uwar Ƴar, time is going fa", ya fada yana yunƙurawa, kallonshi tayi ta kalli tulin mutanan da suke gurin, wata zufa ta ji ta karyo mata, cikin dan shagwaɓa tace "Abieh nima zan bi layin ne wai ?", fuskarsa ba wasa yace "to wa kika fi ?", ya fada cikin irin babu abun da ya shafesa da ita in dai a harkar mulki ne, domin Alfarma da Nuna Sanayya ita ce take bawa Yan Nigeria din mu wahala, in yau kawa mutum daya Alfarma to gobe mutum goma ne zasu zo, jibi sai Ashirin sun zo, da haka yawan mutanan zai yi ta ƙaruwa, sai ka ga cikin ƙanƙanin lokaci guri ya gurɓata.

"Amma fa kasan ba zan iya jure tsayuwar ba da layi sosai", ta fada kwalla na cika idanunta, bai kalleta ba don yasan zai iya karaya , cikin bada Umarni yace "haka za kiyi hkr ki tsaya, ai ke kika tsayar da mu da yanzu mun gama kaɗawa" ya fada yana yunƙurawa zai fito.

Da sauri daya daga cikin Guard dinshi ya matsa gurinshi tare da cewa "Sir! da kun zauna A motar duk lokacin da layi ya rage sai ku fito", kallon da ya sha jinin jikinsa ya watsa masa tare da cewa "wato mu muna zaune a AC sauran Al`umma na waje cikin rana da zafi, sai sun gama ka fin na fita na kaɗa? gwara na je nima na ɗanɗana yarda suke ji domin nima ba finsu na yi ba", ya fada yana wucewa gurin da mutane suke.

da gudu Yan jarida suka fara zuwa gurinsa, domin kwasar Bayyanai, "Amma Yallaɓai ya muka ganka haka zaka tafi gurin Mutane gama gari ka tsaya maimakon ka tafi direct a maka Al`farma a ma", kallonsa yay da kyau, sai da ya tsura mada idanu na yan seconds kafin yace, "ni bana son Alfarma kuma bana nemanta in dai ba ta Annabi Muhammad bace, ban fi sauran Jama'a da suke tsaitsaye cikin rana suke ƙoƙarin kaɗa ƙuri'unsu ba, don haka yarda kowa ya bi layin ya kaɗa haka ni ma da iyalai na zamu bi layi har sai ya zo garemu mun kaɗa , babu wanda zai je neman Alfarma, domin nima babu wanda zan wa Alfarma domin ita ce take cutar Rayukanɓu, da Alfarma muke nakasa kawunan mu, da Alfarma muke lalata rayukanmu, da Alfarma muke durƙusar da dukkan wani tattalin Arzikin ƙasarmu, da Alfarma kuke lalatawa Yaranmu gobensu, da Alfarma Azzalumai suka samu damar da suke mulkarmu, da Alfarma Mugaye suke samun galaba a kan mun, na kuma yi Alwashin rusa dukkan wata Alfarma madamar bata Annabinmu bace", ya na gsma fadar haka ya wuce, dandanan gidajen redio jarida, TV suka shiga Yaɗa Labaransa, *BABU ALFARMA A MULKIN DODON AZZALUMAI* duk inda ka leƙa Headline din kenan, a social media , a gidajen tv , redio da sauransu.

Gaisawa suka shiga yi da mutane cikin mutuntawa babu alamar shi ya fisu ko wani abu babu kyama haka yake miƙawa wanda suka isa da wanda basu isa ba hannu suna gaisawa, wasu ma duk don ace sun gaisa da wanda zai zama shugaban ƙasa suke zuwa su gaisa, wasu burinsu suji ya yana yin fatarsa yake da gautsi kalar nasu ko kuna taushi gareshi, kowa da irin abun da yake sawa ya zo su gaisa.

Haka ya tsaya a layi, shine kusan ƙarshe, don a gabansa kusan mutum 150 ne, kujera aka kawo masa, wanda ya kawo masa kujerar ma ko kallonsa bai yi ba, haka ya tsaya a tsaye kan diga-digansa, ga rana ga zafi, abun da tunda yake rayuwarsa bai taɓa ba kenan, amma bb yarda zai yi, bai son fifita kansa akan Al`ummarsa, baya so tun yanzu suga gazawarsa da ganin kamat ba zai iya ba.

Ya zata yi ? , dole ta fito kamar yarda ya fita ya tafi gurin mutane itama haka tayi, lokacin da zata ƙarasa gurin mata, wasu mata kusan goma sun shiga tsakaninta da su Ayyana, dole ta tsaya a bayansu.

Bata ko iya tsayuwar 30 minutes ba jikinta gaba daya ya jiƙe da zufa, ƙafafunta suka fara wani irin ƙyarma, har basu iya daukarta, mararta ta wani ƙulle, har bata san lokacin da ta sukale ƙasa ba, da sauri matan da suke gurin suka mammatsa suna kallonta, Amatullah ce ta juyo domin ganin ko har yanzu bata fito a mota ba, don bata ganta a bayansu ba, ware idanunta tayi tare da cewa "Innalillahi Ayyana Nahleerh ta faɗi", ta fada da dan ƙarfi, da sauri suka juyo bayansu.

Kamar a kunnansa yaji an ambaci Nahleerh hakan yasa ya juyo, ganinta yashe ƙasa yasa zuciyarsa tayi wani kyakyawan bugawa, shi kansa yasa da mugun wahala in zata iya share wannan awannin a tsaye ba, shi kuma ba zai iya neman mata Alfarma ba kuma ba zsi iya bari ta nema ba.

Idanunsu ne ya tsarke da na juna, hawaye ya gani Sharrrr sun zubo daga cikin idanunta, wanda suka sa da sauri ya dauke idanunshi dags kallomta, don zai iya karaya sosai in yana gsnin hawayenta.

Da sauri Ayyana ta dagota, ta sanyata a jikinta, kafin su yi wani yunƙuri daya daga cikin Guard dinsa ya kawo mota gurin da suke domin ta shiga ta dan samu relief, kama hsnnunts Ayyana tayi tare da cewa "Sannu!" .

jinjina mata kai tayi tana zama cikin motar tare da sauke ajiyar zuciya, jera mata sannu sannu suka ringa yi ita kuwa sai faman zubar da hawaye take.

ganin sun sauka daga kan layin sun hargitsa gurin yasa ya matsa gurin rai ɓace, cikin faɗa yace "ya zaku zo ku ɓatawa mutane layo kuna kallo ?" ya fada yana nuna gurin mutanan.

"Kun zo kun tsaya gurin mota kuna jin AC alhalin sauran Al`umma gaba daya cikin rana suke tsaitsaye ko so kuke a fara zagin mu tun yanzu ?," ya fada cikin kakkausar murya.

"kana kallo fa Nahleerh ce ta faɗi ", Ayyana ta fada tana goge mara gumin fuskarta, "in ita ce ta faɗi sai ku hargitsawa mutane dubu layi saboda mutum daya ?", ya fads cikin wani faɗan, cike da mamaki duk suke kallonsa.

"Don Allah ku koma layi", ya faɗa yana haɗa hannayensa, babu wanda yay magana a cikinsu sai wucewa da suka yi jiki bb kwari, kallonta yay yace "ke fa ?", dakyar ta iya furta "bazan iya tsayuwa a layin nan ba", ta fada cikin rauni.

"Wani kika fi ?", ya bata Amsa a daƙile, girgiza kanta tayi tare da cewa "ban fi wani ba, Amma ban da lafiya", harararta yay tare da cewa "kowa kin san mai yake damunsa ne ?, don Allah ki fito ki koma layi Umarni ne ba shawara ba", ya fada na wucewa, babu yarda ta iya haka ta ƙara fitowa, ta dawo gurin, Girgiza kai Ayyana tayi tana jadadda irin halin Maleeq.

yana komawa cikin layi wayarsa tayi ring , ganin mai girma President ne yasa ya daga wayar cikin bada girma ya gaisheshi bayan sun gama gaisawa ne yace "mai nake gani haka ?, mai yake faruwa da Nahleerh haka , naga ta faɗi a cikin mutane?", numfashi ya fesar kafin yace, "bata jin dadi ne bata iya tsayuwa mai tsayi" daga chan yace "to mai zai hana ta koma mota in layinta yazo a mata ?", girgiza kansa yay kafin yace "A'a yarda kowa yake bin layi itama ta bi ba'a samun Yanci sai da wahala, in kasha wahala kafi riƙe abu da muhimmanci"."Maleeeq! Amma kana kallon irin Situation din da take ciki ba, in aka je aka samu wata matsalar kuna fa ?" ya fada daga chan.

Cikin dakiya da nuna shi din Adalin shugaba je yace, "don tana shirin zama First lady ba wai yana nufin zata ringa samun dukkan wani abu da take buƙata a lokacin da take so ba, wannan ma yana daya daga cikin darussan rayuwa, ta dandani wahala ko da kaɗan je daga cikin rayuwarta, ba zai yu Al`umma na cikin rana ita tana cikin AC ba don kawai tana Mata ta, Sannan babu Abun zai faru in sha Allah"cikin jinjina ƙarfin zuciyarsa yace "to Amma sa ma mata ko kujera ce ta zauna, Umarni ne " ya fada yana kashe wayar ba tare da ya jira jin mai zai ƙara cewa ba.

Kallonta ya yi, daga inda yake yana hango yarda ƙafafunta suke rawa, ga zufa ta wanke mata jiki, shi kansa yay bala'in tausaya mata, yasan tabbad ba ƙarin juriya tayi da ta iya tsayiwar nan ba, yasan kuma har in ta ƙara tsayuwa mai yawan ta ɗazun to komai zai iya faruwa, za'a iya samum ko wace kallar matsalar.

Daya daga cikin Guard dinshi ya turawa Sako akan ya kai mats kujera ta zauna, haksn kuwa ce ts faru, kujerar da aka kai masa aka dauka aka kai mata, tambayarsa tayi waya saya ya kawo mata,kai tsaye yace "Oga! ne Madam " wani fashi ne ta ji ya cikata, wato ma sai da ta gama galabaita zai sa a kawo mata gurin zama, to ita kuwa ba zata zauna ba, zata tsaya kamar yarda kowa ya tsaya kamar yarda yake fada bata fi kowa ba, zata tsaya domin nuna masan itama ba wai gazawarta bane, ko da kuwa Abun da yake cikinta zai iya samun matsala to bb ruwanta tunda tun Asali shi ya nuna rashin kularsa akan Abun da yake cikin .

"No. Thanks!", ta fada tana ƙarfaffa ƙafafunta, bb yarda bai yi da ita ba akan ta zauna ta ce furrrrr ita ba zata zauna ba, har mutane suka sa baki Amma tace bb komai zata iya tsayawa.

Dole suka ƙyaleta domin itama idan ta kafe akan abu to saukowarta ba karamin aiki bane, haka ta bi layi har gurarn 11 basu kaɗa Ƙuri'arsu ba, tun tana gajiya har ta ji ta daina ma ji sai mararta da take mata Azababban ciwo.

Sai Misalin ƙarfe daya na rana 1am kafin Allah ya bata sa'a ta isa gurin da ake dangwalan, cikin sa'a da nasara ta dangwala tana gama dangwalawar , ta juya ta je ta zuwa violet paper din cikin Box ta kasa takawa, ƙafarta ta riƙe, ta ko kasa dagata balle ajiyewa, ta wani kumbura sumtum , cikin galabaita tace "Don Allah ka sunya min bazan iya takawa ba" ta fada da kyar, cikin girmamawa daya daga cikin Escort dinta mata wanda zuwansu kenan ta sanya mata.

kafin mai sanyawar ta dawo, jini ya fara bin ƙafafunta, jin Abu na bin ƙafafunta yasa ta sunkuyar da kanta tana kallon ƙafafun nata, wata ƙarfaffiyar bugawa kirjinta ya yi, da sauri tayi baya zata faɗi.

Da sauro suka tareta, sosai hankalinsu ya tashi da suka ga jini, "bari na kira Sir!"daya daga cikinsu ta fada taza kiransa, da sauri ta riƙe hannunta, cikin cize lips tace "Uhmmmm bar sa ya kaɗa Quri'arsa", ta fada muryarta da tsananin Azaba.

Su dai sun ƙasa daukarta, kuna sun kasa ajiyeta , suna dai rirriƙe da hannauyenta, shi kuwa har sai da layi yazo kansa ya ƙafa ƙuri'arsa, juyowa ya yi yana kallon sashen mata, zuciyarshi ce tayi mummunan bugawa lokacin da ya fara cin ƙaro da jini a jikin ƙafafunta yana zubowa, da wani irin sauri ya nufesu, yana zuwa ya dauketa sai mota, shigar da ita yay tare da bawa Driver Umarnin kai su Asibiti, "Har ka gama kaɗa Quri'ar Mr President ?", ta fada masa cikin gatsali...... [6/7, 6:32 PM] (P.R.O) ƳAR LELEN ROYAL: PART 5. CJAPTER 6.

*P. 59*

"Har ka gama kaɗa Quri'ar ne Mr President ", ta fada da kyar tana zamewa a jikinsa , sakamakon tsananin Azabar da take ji, bai ce da ita komai ba , don yasan sam bai kyauta ba, cikin ƙanƙanin lokaci suka ƙarasa Asibiti, lokacin ita bama ta cikin hayyacinta.

Da sauri ya dauketa ya shiga da ita cikin Asibitin, da sauri suka ƙarɓeta saboda ganin da wanda ta zo, cikin gaggawa aka shiga bata taimakon da ya kamata, Allah y taimaka cikin bai ɓare duka ba, sai dai ya rage kwanakinsa sosai, don da ace ba'a kawota akan lokaci ba da tuni y ɓare.

Ko da aka gama faɗa masa, sanyayyan numfashi ta saki tare da goge zufar da ta zubo masa, tambayar Izinin Shiga Ɗakin yay, Amma aka hanasa ya shiga, domin akwai abun da ake son ƙarasa mata kafin a bari a shiga gurinta.

Reception ya koma, ya zauna a gefe, yana share zufar da take zubo masa har lokacin. Yan jarida da Yan gidajen radio kuwa sun samu abun haskawa, dandanan duniya ta dauki zancen dama ba Ƴarsa bace matarsa ce, Mugun mamaki ne ya kashesa, ganin Pics din ta da cikakken sunanta da yake yawo akan screen din gidajen TV , tunani ya fara ta inda bayanan nan ya fita, ta inda ma aka gano sunanta har ma da inda aka samu pics dinta.

Sanyayyan numfashi ya fesar, yana dan lumshe idanunshi, Mutane ya ji a ƙansa, hakan yasa a hankali ya fara ware idanunshi , fesss ya saukesu akan wani baƙin Ƙaton Ɗan sanda da Ankwa a hannunsa, idanunshi ya dan ƙara buɗawa , kafin yay magana yace "Mun zo ne domin mu kamaka", ya fada kai tsaye ba tare da shayi ko tsoro ba, da yatsa ya nuna kanshi , "sosai ma", Zayn da shigowarsa kenan yace "kamawa ?, akan wane dalili ?, ka kuwa san ko shi waye ?, kasan matsayinsa da har ka zo kamasa ?" ya fada da tarin ɗumbin mamaki a kan fuskarsa.

"Yes!, Of cause. shi Ɗan ƙasa ne kamar kowa kuma bai wuce hukunci ba, dalili kuwa bb ruwanka da sani, in kuma ka matsu da sani sai ka biyomu domin ka sani,"ya fada yana kama hannun Maleeq da ƙarfi ya sanya masa Ankwa, yana niyyar jan sa, "kai dakata , kasan risky din da kake ƙoƙarin jega rayuwarka kuwa ?, mutum kamar wannan zaka zo ka kama ba tare da bayya dalili ba, shin ma waye kai ina takadar Umarnin kamun?", Zayn ya fada a zuciye.

I'd card dinshi ya zaro ya nuna masa, kafin ya ƙara zaro wata paper daga cikin Aljihunsa yace "takardar Izinin kamu , zaka iya barina yanzu na tafi da shi ?", ya fads cikin shafawa idanunshi toka.

"Ba fa zan bari ka tafi da shi ba sai ka faɗa min laifin da yay", cikin fushi yace "dakata Malam ya kake son dole sai na faɗa maka abub da yay Ahalin baya cikin Aikina, sawa kawai aka yi na tafi da shi Amma ni ban san komai akan abun da yay ba, don haka kar ka dakatar da ni akan aikina ko kai ma na tafi da kai", ya fada cikin isgili.

Wani kyakyawan mari Zayn ya daukesa da shi tare da cewa , "Are you a mad ?, kasan waye ni kuwa ?, to ba kai ba har wanda yasa a kamasan za ku yi nadama, madamar baku gaggauta gyara harshenku sannan kuka faɗa mij Abun da ake tuhumarsa a kai ba", ya fada idanunshi na yin jajir alamar ransa ya ɓaci matuƙa gaya.

Yarda Zayn yake magana bb shakku bb Tsoro ballanta na fargabar ganinsu da Uniform din Yan sanda yasa Dan sandan ya dan fara shakkarsa,domin tabbas yasan in har bai taki wani abu ba ba zai tsaya a gabansa yana masa irin wa'innan maganganun bb tsoro balle shakka ba gashi har da mari ya sha.

Wani I'd Card Zayn ya fitar tare da miƙawa Dan sandan da yake riƙe da hannun Maleeq mai Ankwa, kallon fuskar na jikin I'D Card din yay ya kalli Zayn, da sauri ya sara masa tare da kamewa guri daya, ganin yarda yay ne yasa gaba daya sauran da suke bayansa suma suka ƙame cikin Al`amar bayar da girma.

Sara musu yay, tare da cewa "Yanzu zaka iya sakin sa, sannan ka min bayanin Abun da yasa aka zo kamasa ko kuwa ?", sara masa ya ƙara yi tare da furta "Sorry Sir! , zan faɗa maka komai Yallaɓai IG", da sauri su Ayyana , suka maimaita sunan da suka ji ya kirasa da shi cike da ɗumbin mamaki.

"Wasu ne suka shigar da ƙara akan ya kashe musu Ɗan uwa, sannan kuma ya dauki Ƴar Ɗan uwan nasu, tsayin shekaru ba tare da ya bari sun haɗu ba,ba kuma tare da ya bayyanar musu da tana hannunsa ba", kallon kallo aka yi tsakanin Zayn-Maleeq da kuma Arman-Maleeq.

Cikin zafin rai Zayn yace "su waye wa`innan ?", cikin bada Respect yace "Alhaji Auta Baita ne da Sauran Yan uwansa", "Alhaji Autah Baita!", Maleeq ya maimaita sunan cikin mamaki, yanzu har wannan abun ya zaga duniya kenan, har kuma Masu mugun nufi akanta sun farga da ita a doron duniya, har sun fara shirya wani rashin mutuncin bayan wanda suka yi a baya.

Cikin bada Umarni yace "to ka koma gareshi ka kawomin shi a bisa tuhumar Ɓatawa Ɗan takarar Shugaban Ƙasa suna, da kuma son tayar da tarzoma, domin Bincike ya tabbatar da cewar da sa hannunsa a dauki ba dadin da aka yi jiya da dare", ya fada cikin bada umarni, "Okay Sir!", ya fada yana sara masa, tare da barin gurin da sauri.

Sai da suka bar gurin kafin Ayyana ta samu zarafin yin magana, "Zayn Yaushe ka zama Dan sanda, har kake irike matsayin Inspector general , Amma ban sani ba ?", ta fada cikin kaɗuwa.

Shiru yay bai ce komai ba don bai ma san ta inda zai fara ba, Shafa kansa Maleeq yay, ba tare da yace komai ba shima, ganin duk basu son yin magana yasa itama tayi gum da bakinta, amma har lokacin ita dai bata dai na mamaki ba.

Har darw ba'a bari sun shiga sun ganta ba, don ita da kanta ta buƙaci hakan, dole suka tafi gida duka suka bar Ayyana domin kula da ita, cike da damuwa ya koma gida, ranar bai ko iya rumtse ido ba , sai Addu'o'in da yake ta yi mata na samun sauƙi, domin yasan zubar da jinin nan da ta yi zai iya haifar mata da matsala.

Washe gari da sassafe, ya shirya ya tafi Asibitin , lokacin da ya je tana kwance akan gado tana barci, sai Ayyana da take dan nesa da ita kan dadduma ta juya mata baya tana jan chasbaha, hakan ne yasa shi nufar inda take, gefen bed din da take kwance ya samu ya zauna, tare da riƙo hannunta daya wanda yake dauke da drip.

Cikin kulawa ya riƙe hannun tare da mata kiss, a hankali ta fara bude idanunta sakamakon wani kamshi marar dadi da ya bugi hancinta, wawware idanunta ta shiga yi domin ganin mai yake irin wannan warin marar dadi, duk ta gama hange-hangenta bata ga komai ba, idanunta ma yar kansa, tana toshe hanci tace "mai kazo da shi mai wari haka ?" dudduba gefe da gefensa shima ya yi bai ga komai ba.

Alƙyabbar jikinsa ta kama ta shinshina, da sauri ta saki ta koma baya kamar zata fadi sbd wani jiri da ya ɗebeta, dakyar ta iya furta "Abieh ka fita bana son jin kamshin turarenka", ta fada hawaye na zubo mata, ware idanunshi ya dan yi kafin yace "turaran nawa ?" , da sauri ta ɗaga masa kai, tare da cewa "yana sa ni jin jiri, tashin zuciya", riƙe bakinsa ya yi, "ka tashi mana!", ta fada tana buga kanta da jikin fillo, ganin yarda take kamar mai shirin tayar da jinnunta yasa yace "okay! okay na tafi", ya fads cikin damuwa da tausayawa, luf ta koma tayi a jikin fillon ganin ya tashi y bata guri.

Wasa-wasa bata son ganinsa kusa da ita, sai ta fake da bata son kamshin turarensa, tun yana damuwa har ya fara damuwa, tun baya jin haushi har ya fara jin haushi dan ya fahimci abun nata kamar rainin hankali ne, har turare ya chacchanja A sbd ita amma , amma da yazo zata sa mishi kuka ita bata son kamshin turarensa ya tashi ya bata guri.

Zaune take tsakiyar gado ta bude ledar Chocolate da yanzun ya zama Abin cinta tana ci , ya turo ƙofar Bedroom din, dan zuba mata ido ya yi yana kallonta, ta wani yi fresh tayi kyau sosai komai na jikinta ya ciccika, komai ya yi so maa sha Allah, tayi kamar ba ita ba, sai glowing take.yarda kasan an tsomata a cikin ruwan madara.

Idanu itama ta zuba masa, tana mamula Chocolate dinta,da yake cikin bakinta, gurin bed dinta ya zo zai zauna, da sauri ta kwaɓe fuskarta, tare da furta "zaka sa ni na yi Amai fa", ta fada kamar zata yi Aman dagaske.

bai kalleta ba ya zauna, "Don Allah ka fita", ta fada tana yarfe hannu, wani kallo da yama sai da ta koma cikin hankalinta, a zafaffe ya fara faɗa kamar zai ari baki, "ke bana son iskancin banza da wofi, in wani abu kike nema ki faɗa min mana, na gaji da wannan rainin hankalin da kike min, bb dama ke na raɓeki kin dinga min mita da koke-koke , turaruka nawa kika sa ni na chanja duk don sbd farin cikin ki, to yau dai ko turaren ban sa ba, da kike min wannan surutun, sannan haƙƙina nazo nema don nagaji", ya fada yana fesar da iskar mai zafi daga bakin sa alamar dai ransa ya ɓaci .

Muƙwai tayi da bakinta, don bata da bakin magana, "zaki ban ko kuwa sai na kwata ta karfi", idanuwanta ta zuba mishi, cikin zubar da kwalla tace "Abieh Fyaɗe zaka min ?", ta fada tana kallonsa, harara ya ɓalla mata ba tare da yace mata komai ba, kuka ta sanya tare da ƙifa kanta da jikin fillo ta ci gaba da raira masa kukan da baya kauna ko kaɗan.

Cikin zafi ya dago kanta, wawware idanunsa yay a kanta, tare da cewa "kuka! kuka!! kuka kike min akan haƙƙina ?, ni da haƙƙina kike min kuka ?, in dai a kansa ne ki je ki jiƙa abin ki ki shanye, Sai dai ki sani Aure zan ƙara don ni ba waliyi bane, ko dutsi", ya fada yana sakin ta ya fice ransa ɓace, yana mai shawa kansa Alwashin ba zai ci gaba da daukar irin wannan shaigantakar tata ba, dole ne zai gyara mata zamanta, don in har ya ci gaba da biye mata akan abubuwan da take so zai cutu.

Da wannan tunanin ya shiga Bedroom dinsa, sharin barci yay cikin Jallabiya, ƙure Karfin AC dinshi yay, ya kashe glove din bedroom din ya bar Dim light , fillo ya ajiye akan tiles ya kwanta, lumshe idanunshi yay , yana yan tunane-tunane.

Cikin diriricewa da tashin hankali ta daura hannunta akanta tare da sakin kuka iya karfinta, kukan take kamar ranta zai fita. jin kukanta yasa Umma Jakadiya nufowa Ɗakin domin ganin ko lafiya take kuka haka, gefen gado ta ganta ta daura hannayenta aka tana kuka sosai, cikin tsoro da fargaba ta zauna a gefenta, bakinta na rawa ta fara tambayarta lafiya, faɗawa jikinta tayi tana ci gaba da kukan, tambayarta ta shiga yi tana shafa bayanta, cikin kuka tace "Na shiga Ukku Umma!", ta fada tana ci gaba da kukanta, "Subhanallahi!. shiga ukku kuma ?" gyaɗa kanta tayi, cikin kuka tace "Umma wai Abieh ne yace zai ƙara Aure", ta fada tana riƙe hannayenta duka biyu.

"Aure kuma ?, waya faɗa miki ke ?", cikin kuka tace "Shi ne ya faɗa yanzun nan", ta fada tana nuna inda ya tsaya, "mai kika masa ?", girgiza kanta tayi kafin tace "ban masa komai ba ni", "bai yiyuwa dole wani abu kika masa", jim tayi kafin tace "zuwa fa yay shine nace ban iyawa ba ban da lafiya, shine ya ringa min shouting aka , har da cewa wai Aure zai yi", ta fada tana ci gaba da kukanta har numfashinta na yi kamar zai fita, murmushi Umma Jakadiya tayi don tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi dama, sai dai in dama tsoratar da ita zai yi akan wani abun da ta mishi.

"Chappp di ai ko dama na ji yanawa Ayyana maganar", ta fada tana kallonta ta gefen ido, "kin ji ba Umma. na shiga Ukku Abieh ya gama da ni, dududu wata na nawa da yin Aurenhar zai ce zai wani ƙara Aure At least ya bari ko 10 years na yi mana", ta fada hawayenta na zubowa sosai.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull