Auren wata shida cmplete - Chapter 14
Auren wata shida cmplete Chapter 14: Auren wata shida cmplete Chapter 14. "Malam bai fitaba Saida yakama Abdallah aka mayar da shi kan kekensa tukum ya…
3,186 words
"Malam bai fitaba Saida yakama Abdallah aka mayar da shi kan kekensa tukum ya fice.. Bayn fitar mlm riyan ta basa yaasha"kafin tafara kokarin shafa masa,my riyan!banza tayi had'e da cigaba da aikinta"riyan Wai miyasa kukeson yimun hakane ?kidinga kallona Mana innayi mgn...hmmm ah ah basaina kallekaba sbd ni banason yawan kallon Wanda bayason akallesa, sannan naji dad'i sosai dakafara mgn da alama bazamu jimaba zakaida warkewa burina yacika...da sauri yace meye burinki? Rabuwa da Kai"tafad'a Kai tsaye... azuciyarsa yace why!tabbas yarinyar nan batasona ,inhar tanaaona ai bazatayi maganar rabuwaba"cikin wani yanayi yace nikuwa banida niyar rabuwa dake "asalima na yanke auren contract d'in "hmmmmaikuwa dole karabu da jarababbiya naje na auri jarababbe D'an uwana"tafad'a ranta na zafi sbd duk abinda yake Mata dagaya Mata bak'ak'en maganganu wannan maganar tamata ciwo.. Riyan anason Dan Adam yakasance Mai yafiya Mana kada ki tuna baya...Dan ALLAH Yaya Abdallah mubar maganar...shiru yyi Yana kallon Dan karamin bakinta... Bayan ta idar da shafa Masa tamasa alwalla yyi Sallah.. Bayan ya idar "yadubeta had'e da cewa zokiji wata mgn"turo baki tayi had'e da cewa Ni baby inda zanzo kafada koma miye ne! shikenan tunda baza kizoba kiramun Hafiz awaya...bbu musu tayi calling d'in Hafiz...da sallama yad'aga Yana cewa riyan yayadai?ai nakusa sauka!my man...da sauri Hafiz yace Dan ALLAH da gske ne?muryar AK fa nakeji"nine my man kada ikon ALLAH ko"cikin farin ciki da murna Hafiz yace Masha ALLAH gsky zanjewa da ammi da babban albishir Kai Alhmdllh naji dad'i"to ke riyan ai saikiyi sadaka marigayi AK yafara mgn ko"yayi maganar cike da tsokana...hmmm inaso kayiwa wannan wawan salinsun nan mgn idanunsa sudaina kallon my iyali wlh sbd Ina d'aga Masa sbd mlm ne... Dama kanada iyaline?cewar Hafiz Yana danne dariyarsa sbd ya lura kishine Kecin Abdallah "azuciyarsa yace nida sabon shiga...bansaniba! murmushi Hafiz yyi had'e da cewa Inna sauka mayi mgn"kafin yakashe wayar...
Riyan ta tab'e baki had'e da juyawa sbd ganin yadda Abdallah ya tsareta da golden eyes nasa....
Hakan ce takasance"Hafiz na isa gd yajewa da ammi da babban albishir d'in Abdallah yafara mgn"cikin farin ciki ammi ta Kira suka gaisa dashi da riyan dakuma mlm...
******* Da dare bayan sun gama Shirin kwanciya"Abdallah na kan katifa kwance"yyinda riyan ke kan tabarma ta aza blanket ta kwanta akai"ahankali cikin wata iriyar murya Abdallah yace riyan taso mu kwanta kinji"cikin dauriya sbd jin muryar sa har wani kasala tasakarmata ,ta mak'e kafad'a had'e da cewa baza a zoba "to naji shikenan tunda baza kizoba,yanxun kibani wani long story kinji?Dan ALLAH mlm ka kwanta kacikawa mutane kunne da surutu ai sai kaina yyi ciwo...
Murmushi yyi"azuciyarsa yace lallai yarinyar nan wato rama abinda namata abaya take kenan" Yyinda riyan ta lumshe ido tsikar jikinta natashi "fatanta ALLAH yasa hasa shenta yazama gsky ma'ana Abdallah SONTA yake.
Sbd tun ranar da suka had'a ido da shi taji zuciyar ta na kaunarsa.
Amma in har hakane dole ta garasa ta nunamasa ta bambanta da sauran Mata ,takuma Kama ajinta... ruwa Zan Sha...muryar Abdallah ta katse Mata tunani.... [3/16, 9:12 PM] +234 810 194 3850: 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🌺 AUREN WATA SHIDDA🌺
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
Ina mik'a godiya ta ga d'inbin makaranta novels d'ina,da masu kirana suji lfy ba'a yi update ba.nagode sosa uzurirrikane suka boyeni.👏🥰🥰
Not edited❌
p 36
Batare da tace komaiba ta tashi ,tajawo katan na swan ta fito da 1 ta matsa gabansa had'e da kafa Masa abaki " Bayan yagama Sha!"yawani lumshe ido"ahankali yace thanks.tabe Baki tayi had'e da komawa tayi kwanciyarta batabi ta kansaba dukda tanajin yana magana k'asa k'asa....
Washe gari sai riyanta Sami kanta da jin kunyar tayiwa Abdallah wanka gashi yau sai wani binta da kallo yake Yana murmushi, yyinda yakebata mamaki"tana tambayar kanta Ina ya aje girman kan da Shan k'amshin?" Turasa take Yana Jan keken zuwa bayin gdn"hmmm wata yarinya yacika tsoro wlh...taji yafad'a Yana girgiza Kai"ware ido tayi azatonta bada ita yakeba,saitaga Yana murmushi,da sauri ta dubesa sai yad'age Mata gira guda.. Kauda Kai tayi had'e da addua suka shige bayin.. Keme me Abdallah ya ki rufe ido kamar yadda yake kullum inzata Masa wanka"kauda Kai tayi had'e da cewa mlm karufe idonka Mana!hmmm oh riyan meye n wani kunya bacin kingama kalleni,Aina ganoki innarufe ido ki kalleni son ranki ko?"cikin wani tsoro tace mekake nufi?"to nama fasa maka wankan tunda kace haka ai Ni bana tunanin Kai cikakken namijine dazan tsaya dubarsa...wani killer smile yasaki had'e da cewa babu damuwa ALLAH ya bani lfy Zaki maimaitamun da hujja! yafad'a had'e da rufe idonsa sbd yalura inbe rufenba zata iya fasa yimasa wankan..
Da misalin karfe 5:35pm riyan na zaune atsakar gd bayan tagama yiwa Inna mairo tankad'an garin tuwo tana game da wayar Abdallah" Can wayar tafara ringing" da sauri riyan ta duba taga ummace! Murmushi tasaki had'e da dagawa ta nufi dakinsu"nan suka soma gaisawa...cikin wani yanayi na damuwa umma tace riyan kina Ina?Ina fatan badai duniya kikashigaba ko? Sbd jiya muka dawo dg k'auye yaunaje gdn mama zuwaira mugaisa sai take mun gaisuwa nace Mata waya rasu?"tace mijinki!nayi mamaki had'e da sanar Mata bansaniba,tafaru ta Kare riyan ta fada azuciyarta... Salati riyan ta yi hade da cewa ki kwantar da hankalinki umma bbu inda natafi asalima Ina tare da mijina..da sauri umma tace miyake faruwane kinsani aduhu ?"yanxunfa dg gdnsu mijinki Nike ,nayiwa mahaifiyar sa gaisuwa na tambayeta kina Ina tace ai yayar mahaifiyar ta tazo ta tafi da ita,Amma na lura batason nice mamankiba"hankalina yatashi Riyanatu bandaice Mata komaiba nabar gdn da niyar nakiraki awaya naji kina Ina ne...ajiyar zuciya riyan ta yi sbd jin umma Bata lalata musu aikiba. Kallon gefenda Abdallah ke bacci tayi taga baccinsa yake. Ahankali tace wlh umma bbu lfy Amma zanmiki bayani ki kwantar da hankalinki Amma kada kigayawa mama zuwaira da kowama Wai mijina na araye sbd ko abbansa yadauka ya mutu !zankiraki anjima namiki bayani...batajira me umma zatace ba ta kashe wayar... Meyasa bazakiyi Mata bayanin yanxunba? Muryar Abdallah ta daki dodon kunnanta"cikin zaro ido had'e da Shan jinin jikinta ta d'ago kanta suka had'a ido da sauri ta janye nata idon sbd wani yarrrrrrrrrrrr!dataji ajikinta"kinyi shiru!kisanar da ita gsky kodan hankalinta ya kwanta... Ahankali tace to... sannan ta Kira umma "kaf tamata bayanin komai.salati kawai umma keyi tana jinjina wannan lamari tamkar almara"ta tsorata da D'an Adam, sannan ta yarda tabbas akwai k'addarar data saka suka baro garinsu"gashi sunfara ganinta sai fatan ALLAH yasa su ida ganin karshenta lfy...tayiwa riyan nasiha sosai dukda riyan Bata fad'a Mata auren contract sukayi da Abdallah ba, Kuma shima yaji dad'in kin fad'ar datayi.
********
Mom ce tsaye fuska bbu walwala"yyinda hjy ikilima ke zaune jigum tamkar masu zaman makoki" cikin bacin rai mom tace nayi mamakin meyasa hakan tafaru?Amma ba ri ubansa yadawo dukda shi yasan banina haifesaba Amma ai bazaimun musu ko hanani iko da abunsaba" Hjy ikilima ta karbe zancen da cewa Ni wlh abinda yatsoratani shine rufe account d'in da Kuma b'oye number d'in daakayi amfani da ita"kodai wani yasan me muke nufi... Cikin faduwar gaba mom tace Kai haba!bana tunanin hakan gsky"Amma Bari Alh yadawo naji koshi yarufe account d'in Abdallan" Haushin guda bbu kud'i da yawa guna ,gashi Suraj ya matsamun akan 3 million yakeso"kinsan innace alh yabani zai tuhumeni akan mezanyi dasu ,Kuma bansan amsar dazan bashiba" Haba Mana karkibada Mata saikace ba TSIYA TSABA ba!kusamu karyan dakika Masa Mana ki karba may bee dg baya musan yadda zamu yi abude account d'in Abdallan,sbd Kinga inbaki bashiba akwai matsala, sannan in kikayiwa alh maganar account d'in Abdallan shima zaimiki wani zato ko fassara,Koda kina ganin ki Masa asiri azuciyarsa zai Yi wani zato daban Koda ke bazaimiki mgn ba.... Ajiyar zuciya mom tayi had'e da cewa wannan gsky ne aminiya"ta fad'a suna dariyar mugunta....
###### Bayan wata 2 ,kwanci tashi asarar Mai Rai" yanxun dai su riyan da Abdallah watansu 2 kenan akauyen karaye"bbu laifi jikin Abdallah saidai muce Masha ALLAH !sbd yanzun kusan abinda yarage ajikinsa kad'an ne Dan yanzun hannunsa da kafarsa suna aiki da motsi har kansa ma zai iya turawa Yana akan keken..yanxun tashi yyi tafiyane kawai matsalar sa,shima Kuma mlm yad'age Gurin basa taimako, yyinda shida riyan sakaci da adduar neman tsari da azkar...
Har iya yanxun riyan Bata sakarwa Abdallah fuskar yyi Mata wata mgn dashafi soyayya inma yyi sai tabasar"inkuma Hafiz ya zo dubiya yaroki yatayasa camphane "sai yayi k'ememe yace bbu ruwansa...hakan yasa Abdallah ya Dena rokarsa"sannan itama yadena nuna soyayyar sa yabar wa yasamu k'afa tukum dukda wani lokacin say tari yakan kwatanta intazo basa Abu yahad'a da hannunta yarik'e"saita daure fuska ta kwace hannunta"ranar da yarik'e hannun ta yafisgota tafad'a ajikinsa yaga bacin ranta "batace komaiba sai kuka kawai "hakan yanuna Masa cewa tabbas riyan Bata SONSA takuma tsanesa Wanda abad'ini ba haka bane.. Gefe guda Kuma mlm yahana salisu ahiga gdn sbd lura da yyi inhar Abdallah ya ganshi musammun in riyan nagun to besake mgn ko faraa,in salisun Kuma yamasa mgn da k'yar yake amsawa...hakan yasa mlm yace insuntafi yadingashigowa sbd yafahimci Abdallah nakishin iyalinsane, sannan Kuma bega laifinsaba...
Yau yakama juma'a"bayn sundawo dg masjid, Abdallah yacewa Inna mairo adama Masa fura,bacin ga riyan wacce ta nunama ko ajikinta Dan talura yau wani shan k'amshi yakeji ga wani kyau namusammun da yyi sbd anmasa aski da gyaran fuska...har cikin ranta taji bbu dad'i Amma saita share..
Yyinda gogan keta aikin satar kallonta"sbd tunda yake da riyan sai yau yamata kallon tsab "wata zazzafar kaunar ta na fisgarsa"jiyake kamar yajanyota jikinsa Amma ba damar hakan"ita kuwa Sarai tasan Yana kollonta sbd ta na lura ta gefen ido.
Inna mairo ta mik'o wa riyan cuein fura had'e da gidauniya da nono kindirmo aciki tace gashi kidama Masa.
Dagowa tayi taga ita yake kallo"harara tasakarmasa,sai yyi murmushi had'e da d'age Mata gira guda"
Lumshe ido tayi ,kafin ta cigaba da dama furar har ta idar akan idon Abdallah.
Shikanshi Yana mamakin wannan kauna dayakewa riyan "
Ko sadda take Masa aiki ,in yasata kuka bayajin dad'i ga tausayinta yanaji,dukda yasan atime d'in baso bane"sannan yanajin dad'in yadda take kiransa da Yaya Abdallah...
Tura kansa yyi har cikin d'akin sbd ganin ta tashi ta shiga d'akin.
Ahankali yace madam abani "tunda baza'a cemun gashiba...
Tashi tayi had'e da turo baki tace aibaka tambayaba"
Hmmm Anya ke ba auta bace my riyan?" Mik'o Masa tayi had'e da cewa me ruwanka da hakan"
Murmushi yyi yace nidaiko riyan ya?
Eh din meza iyayimun?"insha ALLAH daka warke anan gdn zaka sallameni ,bazan bikaba ,balle kamun mugunta.
Ko ka manta da azabtar Dani dakayi adaren da aka kaini gdnka?
Shiru yyi jikinsa yyi sanyi sbd bemason tuna wannan abubuwan....
Waiwaye...
Share
Zakuji shin maman Abdallah Ina tadosa bayn fitarta dg gdn alhj Kabir girma?" Tana raye kobata raye?
Muhade a next page...
BY MMN FAREESA [3/16, 9:12 PM] +234 810 194 3850: 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🌺AUREN WATA SHIDDA🌺
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
Not edited❌
P 37
Waiwaye Tunda tabar gd Gurin karfe 5:30 am na asuba taketa Jan trolley dinta guda2 da hand bag nata "tana tafiya kawai batasan Ina zata dosaba?" gaba d'aya taji garin yamata zafi tamkar ana sukan jikinta da allura"ga kunci da bacin rai tana ji ,Wanda batasan Kona meye bane"ge fe guda Kuma Tama manta ita wacece" Tafiya kawai take Yi "tun gari da duhu har Rana ta fito. Tana bakin wani titi taga motoci na wucewa"can taji wani mutum nacewa ADAMAWA ko YOLA...cak tatsaya had'e da juyowa tanufi Gurin motar... Karfe 6:25 suka d'auki hanyar YOLA....tunda tashiga motar Bata um bare um um tayi gum da bakinta tana Yan kalle kalle...can wata yarinya budurwa dabata wuce shekara ashirin zuwa da d'aya"sai kallonta take , yyinda itama yarinyar tana cikin damuwa. Sunyi tafiya Mai nisa akatsaya Dan aci abinci ayi Sallah" Bayn sun gama sallar gefen wani guri da ake siyar da abinci"sai sai ummin Abdallah ta tashi taje ta siyo plate d'aya har zata Fara ci"sai takula da yarinyar ce kadai ke Bata siyi abincinba!dakuma alama tanason abincin "da hannu ta yafitota"bbu musu ta taso tazo gurinta. Ahankali tace ke miyasa bazaki ci abincinba?"shiru tayi hawaye na zuba afuskar ta"cikin damuwa tace banida kud'i!asalima ko kud'in motar bandashi Kuma bansan inda zaniba.... tafad'a had'e da rushewa da kuka. Rarrashinta ummi tayi had'e da siyamata abincin "kafin sokoma mota suka dauki hanya..
Karfe Gurin karfe 4:18 suka iso garin YOLA"duk anata sauka kowa da kowa dake cikin motar"nan ummi ta biyama kanta da wannan budurwa , yyinda taji zuciyar ta wasai tarage Zin kunci tabacin Rai sannan ayanxun inxaka kasheta bazata iya ce maka ko ita wacece ba.. yarinyar dkeda suna yusra ta dubi ummi tace to hjy nagode sosai ALLAH yabiya ki da wannan taimako da kikamun "murmushi tayi had'e da cewa Amin.. Kafin yusra tace kema anan garin kike ko Gurin wasu kikazo?? Hmmm acikin tambayoyinki bbu kodaya"da sauri yusra ta dubeta da mamaki ganin mace har mace ,kallo d'aya zaka Mata kasan tana cikin hutu da jindadin rayuwa Kuma agdn wadata...kafin yusra tace wani Abu ummi ta rugata da cewa bansan miyake damunaba nasan dai inada aure da d'a ayanxun haka Kuma i nada ciki" Amma bazan iya nuna mijin ko d'anba balle Kuma dangina "Nadai tsintsi kaina ahaka"salati yusra tayi cikin tausawa kansu sbd itama tanada tata matsalar" Ajiyar zuciya ummi tayi had'e da cewa mutambayi Ina ne gdn Mai anguwa ko"yusra tace mezamuyi acan ne?" Inaso musami masauki ko zuwa gobe ne sai nasamu hayar gd ko Kuma karami nasiya Dan nazauna ...Dan ALLAH kitemakeni na zauna gurinki kafin nadan wani lokaci nadaidaita da iyayena"nakoma gunsu agarin kano... Meye laifin da kika aikata musune?" Ajiyar zuciya yusra tayi had'e da cewa suna yusra Ahmed iyayena Yan asalin kanone Amma munda dangi asokota"byn na kammala NCE d'ina "saurayina ya yaudareni yakaini d'akin abokinsa yamun FYAD'E sanadin hakan nasamu ciki "iyayena suka koreni akan nazubar ,nikuma bazan iyaba "sbd tamkar nayi kisan Kaine"Kinga laifi 2 kenan dukda ba'ason Raina hakan yafaruba"to dalilin haka yasa babana yakoreni"yakuma gargade Ni inhar yaji labarin naje gdn y'an uwansa zai tsinemun... Hakan yasa naso ingudu awannan yanayin mota ta kadeni sai cikin yazube ,wanda yakadeni yakaini asibiti nayi kwana3 sannan nakoma gd nasanar dasu"tun kan in ida shiga gdn babana yyimun dukan tsiya yakoreni, mahaifiyata na kuka nabasa hakuri be saurareniba"tace natafi gdn danginta"sai yace innaje bakin aurenta!hakan yasa na kwana amakotanmu yau da asuba na hau motar Yola amma bansan Ina zanijeba.. Saida ummi ta Mata kuka sbd tausayi "sannan tace ki kwantar da hankalinki ,insha ALLAH zamu zauna tare kidai rik'e Amana Dan ALLAH. Kukan farin ciki yusra tayi had'e da Mata godiya,kafin su tambayi gdn Mai anguwa aka nuna musu...
Byn sun gaisa had'e da samun tarba ta mutunci gun matan Mai anguwa.
Ummi ta Masa bayani,kamar haka"
Sunana HAJARA! wannan Kuma yusra kanwatace,mu Yan gudun hijirane,ankashemun miji da iyayena dg Ni sai muka tsira da cikin dake jikina.. ajiyar zuciya mlm dauda ( Mai anguwa)yyi Yana dubarsu had'e da nazartarsu.
Can yace to yanxun miye dalilin xuwanku anan gurina!
Ummi tace munaso Dan ALLAH kabamu masauki zuwa gobe insha ALLAH sai asama Mana gd karami musiya mukoma.
Masha ALLAH bbu damuwa !cewar mlm dauda"
****** Haka kuwa akayi washe gari mlm dauda yaje dasu ummi kasuwa ta siyar da sarkan gwal d'in ta anaira million d'aya da dubu dari bakwai... Aka Samar musu gd karami na million d'aya da dubu dari"daki biyune sai kitchen da toilet sai soro guda. Bbu laifi gdn Mai kyaune Kuma sabo yasha tayis da fanti ga famfo akwai..
Acikin kwana2 suka koma bacin sunyi Yan siyayyar abun amfani aciki harda katuwar freezer da yusra tabada shawarar ummi ta siya taruka Sanaa sbd Gurin akwai jamaa ga Kuma islamiya dake gaban gdn.
Hakan yasa ta siya bbu bata lokaci suka farayin zobo da kunun Aya ,cikin ikon ALLAH abin yasami karbuwa da albarka..kullum sai sunyi sob'o na tiya 2 kunun Aya na tiya3 ga pure water anashigowa asiya"Kuma duk cikin gd suke siyarwa harya Kare. Da wannan Sanaa sukeci suke sha...
Cikin ikon ALLAH cikin jikin ummi nata girma byn wata6 ta haihu agd Kuma twins..mace da namiji"murna Gurin yusra baa mgn...
Acikin haka Yara suka tashi da kiriniya had'e da b'anna..
Kyawawa dasu macen wankan tarwada ce namijin bak'i ne.
Saidai matsalar dasuka Fara fuskarta itace!da farko anxata mijin ummi yarasu,byn ta yaye twins sai jawarawa sukayimata caaaaaa!abinka da farar mace bafulatana Kuma kyakykyawa...ita kuwa tasan Sarai tanada aure hakan yasa Bata kulasu..ko sakan musu fuska.
Hakan sai yasa ake zundensu Wai ai yaranta shegune basuda uba basuda asali"
Duk intaji hakan ranta na zafi da k'una"ita kanta yusra batajin dad'in hakan.
Sau tari insun fito waje saikaji yaran anguwa na tsokanarsu da cewa Ina babansu basuda uba.
Dasunzo gd sai suyita tambayar ta,ummi Ina abbanmu?"
Wani lokacin har hawaye take sbd rashin amsar dazata basu.saidai tace abbanku ya mutu.
Da wannan yanayin suka Fara tasawa har suka Kai she kara5 tasaka su skul harda islamiya.
Suntaso darashin ji had'e da k'iri niyar tsiya ga fad'a"akwaisu da Jan fad'a ,sai suyi Taran dangi ga Wanda suka ja.
Suna mugun son junansu da tsokanan juna musammun ALHASAN"yyinda yake Kiran HUSAINA da anty hussy!kasancewar itace babba"
Duk ranar da aka goranta musu Alan basuda uba sai sunyi kuka dukda atime d'in yarana sosai.
Hakan yasa ummi hanasu yawan fita sai intare da yusrane ko Kuma zuwa skul..
Ana cikin hakan"sunje kasuwa siyayya itada yusra...kwatsam yusra taga k'anin baban ta"yakuwa tsaidata had'e da tambayar ta Ina ta tafine anata nemanta tsawon she kara5 da wasu watanni?"
Ummi tamasa bayanin suna tare "byn yabinciko gsky yyimata godiya sosai washe gari yazo yatafi da yusra gd gun iyayenta... wannan shine dalilin rabuwarsu da yusra ,suka dawo rayuwa su kad'ai...
Bayan shekara 20....
Kuyi manage da wannan" Happy week end🥰
Share
BY MMN FAREESA [3/16, 9:13 PM] +234 810 194 3850: 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
🌺AUREN WATA SHIDDA🌺
🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾
Story & written by mmn fareesa
Not edited❌
p 38
Bayan shekara 20 ""Abubuwa da yawa sunfaru "aciki harda girman twins da tashinsu dg gdn dasuke da ALHASAN Yacanza musu sbd ayanzun shi cikakken d'an jaridane(Yana aiki agdn TV) kasancewar sa Mai k'wazo yasa acikin wad'anda gwamnati tabawa schooler ship hardashi"yatafi malesia yyi 5years acan"bayan yadawo yasami aiki yacanza musu gd.. Yyinda hussy tazama nursing"harda yanzun cikin su bbu maimarmarin aure arayuwarsa sbd basusan kosu suwayeba!hakan yasa basa soyayya dukda hussy tanada tarin masoya Bata kulasu wasukuma insunji basuda asali saisu shareta" ALHASAN miskili ne shima akwai izza Amma baikai Abdallah ba"betaba son wata ya maceba,Amma yanada wata friend salimat dasukayi karatu a malesia tare "da farko suna mutunci Amma dg baya data nuna sonsa take sai ya nuna be ganeba yyi baya da ita,gefe guda Kuma y'an matan Yola na masifar sonsa kasancewarsa Dan jarida Mai farin jini.... Basa Jim dad'i suk sadda suka tuna basu son asalinsuba"sannan Kuma insunso tambayar ummi saitakama kuka hakan yasa suka Dena Mata mgnar" Hussy ta tashi kyakykyawa wankan tarwada gajera yyinda Alhasan yatashi saurayi Mai jini ajika dogo Baki kyakykyawa Mai aji,miskili... Inna kagansu zaka d'auka ba twins bane sbd hussy karamin jiki gareta saikace Alhasan ne yayanta. Har yanzun shakuwarsu Na nan saima karuwa datayi...ayanxun shekararsu 26.,,,,,