Kenza eBookz

Auren wata shida cmplete - Chapter 17

Auren wata shida cmplete - Chapter 17

Auren wata shida cmplete Chapter 17: Auren wata shida cmplete Chapter 17. Bayan sun kammala cin abincin dare, Abdallah da kansa yakira Hafiz ya sanar dashi…

3,295 words

Bayan sun kammala cin abincin dare, Abdallah da kansa yakira Hafiz ya sanar dashi komai"Wanda yyi farin ciki sosai da jin wannan al'a mari musammun dayaji cewa RIYAN k'anwar Abdallah ce," Cikin farin ciki yace gobe my man Ina hanya insha ALLAH dukda wannan watan my feedo take haihuwa,Amma zamuzo tare da ammi insha ALLAH goben..

D'akin Inna mairo umma ta nufa danta kwana,dukda bada niyar kwanan tazoba,jin Abdallah jinintane yasata kwana... Tabar riyan da Abdallah ad'akinsu Dan su sake ... Bayan fitar umma Abdallah ya dubi riyan had'e da yin k'asa k'asa da murya yace Mrs Abdallah zoki kamani na kwana pls...cikin ko inkula tace ai mlm ne ke kwantar da Kai ko inyakamaka addua ko"hmm Nike nakeso yau,inkuma bakyayi nasanar da umma bakyajin mgn ta...da sauri ta tashi , cike da tsoro ta nufesa. Ahankali ta mik'a Masa hannunta yakama ta dagosa dg kan kujerar"kasancewar gasu ga katifar"hakan yasa yyi saurin riketa Gam ajikinsa ,suka fad'a kan tatifar atare"ckin mugun tsoro riyan ke kokarin kwacewa ,amma sai yasaka hannunsa ya gyaramata kwanciya akan faffad'an kirjinsa" cikin murmushi yace matsoraciya anan Zaki kwana yau ,nima naji dumin jikin matata ,Koda yaushe saiki barni Ni daya na kwanta saikace wani gwabro ko" bacin inadake... eh d'in Nika cikani konamaka ihu ALLAH kuwa tafad'a tana son kwacewa dg jikinsa.. Murmushi yyi had'e da cewa so what?" Inkinmun ihun ne"garama ki kwanta Dan bazan cikakiba...sai zille zille take da koke koke,Wanda duk Wanda yagani zai gane shagwaba ce zalla take" hakan Kuma sai ya saka mutumin nata cikin wani yanayi....

Daskarewa Abba yyi agurin,me maganar ta kenufine?" Ta aikasa lahira inda na mik'a D'ansa" Zuciyarsa tace....

Share

BY MMN FAREESA [3/18, 4:12 PM] Mmn fareesa: 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🌺AUREN WATA SHIDDA🌺

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

Wannan shafin nakune Queen minart & pretty Ina mugun yinku, irin sosai d'in nan🥰🥰

Not edited❌

P 44 .... Zuciyar sa tace kanada wani d'anda ya wuce Abdallah ne!tuni gabansa yyi mummunan faduwa...Amma sai yaita ambaton sunayen ALLAH azuciyarsa"meke Shirin faruwane Dani ?" yatambayi kansa"ita takashe Abdallah Kuma ta keson ganin bayansa" Dakewa yyi ,yyi sallama had'e da boye damuwarsa da al'ajabin dake cikin ransa"itama amsawa tayi fuska asake"Zama yyi agefenta ,Yana cewa yau bazaiyi dinner ba ,da wuri zai kwanta.. Mik'a tayi had'e da cewa nima da wuri Zan kwanta muje ko"Ina Kenan ?"yatambaye ta sbd ba gu d'aya suke kwanaba ! bed room d'in ka Mana acan Zan kwana.. Kallon ta yyi had'e da hmmm Aida bacan kike kwana ba ,Amma inzaki iya muje Amma fa kisani banida lfy " Cike da mamaki had'e da zaton ko Suraj ya sanarda shi wani Abu "tace banganeba kamun bayani,kamar ya bakada lfy??" Tashi tsaye yyi Yana nufar bed room d'in sa Yana cewa , ma'ana bazan iya wani Abu dakeba Wanda yashafi auratayya....dam..dam...Damm kirjinta yabuga!am bbu komai ALLAH yabaka lfy "Amma meyasa bakasanar daniba?"eh to naga Baki bukatane shiyasa...bejira amsartaba yashige ciki... Har ciki ta bisa ta duba wayarsa sbd baya d'akin Yana toilet"ta duba text message bataga komaiba "haka Kuma vedio dakuma receive call nasa ... ajiyar zuciya tasaki had'e da ficewa... Cikin sauri Abba yafito dg toilet d'in sbd Yana hangenta ta kofar toilet d'in. Girgiza Kai yyi had'e da cewa akwai k'amshin gsky ga Wanda yaturomun sakon nan"sannan Wai da gske itace takashemun yaro?" Wani jiri yaji had'e da sarawa yaji kansa na Masa,jinsa yake tamkar bashiba " Number in da Suraj yabasa yarubuta sako kamar haka...

Inason ganin vedio d'in" Sannan inason sanin sirrinta...yyi saurin turawa .

Kwanciya yyi kan bed Yana juyi...wani mugun faduwa gaban sa yyi sakamakon tuno hjy Kaka mahaifiyar sa da yyi"rabonsa da ita 2 years kenan...wani iri yakejinsa jiyake kamar ma mafarki yake,ko Kuma wani Abu na damunsa...

********* Duk yadda riyan ta so barin jikinsa abun yaci tura,hakan yasa ta hakura ta lafe ajikinsa bacci yyi awan gaba dasu..

Washe gari ita ta rigasa tashi ,tawi wuf tabar jikinsa" Byan sun kimtsa umma da Abdallah na fira dukda Bata cika mgn sosaiba sbd kunya , yyinda riyan ke cikin d'aki sbd zamanta atsakar gd sai Abdallah ke jifanta da kallo Mai wuyar fassara.. Abdallah ya dubi umma fuska bbu walwala yace wlh umma gabana ke faduwa gashi nayi mafarkin Abba na,Ina gudun kada muguwar matar nan tayi Masa wani Abu"inaji ajikina Abba baya qlau....cikin damuwa umma tace insha ALLAH Yana klau kuma ALLAH ya fita ni inada wata shawara Abdallah... Sallamar Hafiz da ammi ya katse musu zance. Cikin farin ciki aka tarbesu had'e da murna,kafin ammi tagabatar da kanta gun umma, yyinda umma tamata godiya akan jajir cewarta ga lamarin Abdallah"suka Taya juna farin ciki...shikuwa Abdallah Jan Hafiz yyi gefe suna gulmal riyan..

Ammi ta ji Dadi sosai da kakar Abdallah keda Rai ,hakan yasa ta dubi umma tace inda wata shawara Mai zai Hana ,yau mu koma kano tare dake !gobe saimu nemi jirgi muje Mai duguri,muje mu warware wa hjy Kaka koami... ajiyar zuciya umma tayi had'e da cewa wlh kamar kinsan abinda ke Raina,inason sanar da Abdallah haka kuka shigo d'azun... Saidai matsalar guda bamusan gdn ba... murmushi ammi tayi had'e da cewa ga Abdallah nan zai bamu address na gdn.. Umma tace to" Nan ammi ta waiga gundasu Hafiz suke taga suna 'kus k'us tayi murmushi had'e da cewa inkungama gulmar sai kuzo ai...dariya sukayi bak'i daya had'e da tasowa.... Yyinda riyan byn sun gaisa tun d'azun tabar tsakar gdn...

Kaf ammi tamasu bayanin yadda sukayi da umma"cikin jin Dadi Abdallah yace eh ammi hakan yyi"kafin yabawa Hafiz ful address na gdn hjy Kaka...

Ana gama azahar ,su ammi da umma suka yiwa riyan da Abdallah bankwana dukda riyan taso binsu"umma ta Mata tas tace baza taba ,intabisu tabarwa wa mijinta"shikuwa Abdallah ganin tana kuka sai yaji bbu dad'i "yyi zaton k'ilama kukan k'insa take..

######## Haka Abba yakwana cikin damuwa da fargaba had'e da tarin tambayoyi wad'anda bashida Mai fassara Masa su...gefe guda Kuma yanajiran yaga suwa mom zata had'a shi dasu su aikasa lahira ,sbd shi garama yamutun ko yahuta da wannan halin dayake ciki...

Da misalin karfe 12:30 pm suka iso gdn hjy Kaka"umma ce agaba sbd tasan hjy Kaka afuska "kasancewar ammi batasantaba" Sallama sukayi acikin babban parlourn gdn"dattijuwar mace ce ,Yar kimanin shekara 70- 72 aduniya"zaune da farin glass a fuskar ta, kallo d'aya zaka Mata kasan tana cikin damuwa"kasancewar fuskar ta ta bbu walwala.. D'agowa tayi da nufin amsa sallamar masu shigowa,sukayi 4 eyes da umma... akidime ta tashi tsaye,tana nuna umma had'e da cewa Wana ke gani kamar BINTU? k'anwar HAJARA... murmushi umma tayi had'e da cewa eh hjy nice...kuka hjy ta fashe dashi had'e da cewa bintu Ina HAJARA da Abdallah jikana ,rabona dashi shekara 8 kenan ,ubansa kuwa ya manta cewa nice mahaifiyar sa shekarata 2 rabon da nagansa...ta fad'a had'e da sakin kukan bak'in ciki...da sauri umma ta k'arasa ta rungume hjy Kaka tana kukan tausayinta...

Bbu abinda kakeji sai shashshekar kukan hjy Kaka sbd bayan sun gaisa sun huta sunnmata bayanin komai da mutuwar wucin gadi da Abdallah yyi da aurensa da kurciyar da mom tayiwa HAJARA,"duka Saida suka sanar da hjy Kaka...cikin damuwa hjy Kaka ta hau yiwa su ammi da Hafiz godiya da kyakykyawar fata sbd gudunmuwar dasuka bada ga rayuwar jikanta..kafin ta dubi umma tace gsky bintu Zama a garin nan be kamaniba Dole nabiku muje kaduna Naga Yaya rayuwar d'ana take"tunda ta gama mallakarsa har yamanta Dani amatsayina na uwar dana haifesa"tsakanina da wannan Mata ALLAH ya isa har abada bazan yafe mataba"wannan wane irin rashin imanine wannan ? lallai ikon ALLAH baida karshe saikace almara,amma bbu komai haka ALLAH ya rubuta yakuma so ,tunda gashi Yana warware komai..ammi tace haka ne hjy ki kwantar da hankalinki to Amma ke miyasa Baki nemi HAJARA ba?" Wlh y'an nan ,tun bayan rasuwar mijina banida lfy ,hakan yasa k'anina dake aiki akasar Madina yamaidani can ,yana kuladani nakusa shekara 4 acan.. alokacin da nadawo ,nasmi HAJARA Bata nan ,natambayi Kabiru sai ya nunama besantaba ,da matsa Masa sai yace yarabu da ita,sai ayanxun nasan kurciya akamata"sannan na fahimci sarkin miskilancin nan(Abdallah) yadauka itace uwarsa ,Kuma beson laifinta,naso ankarar da shi,abin yaci tura,zuwan dayyi Wanda bansake ganinsaba har yanxun ,nace Masa yazo Zan sanar da shi wata mgn Mai mahimmanci,tundaga ranar bekoma zuwaba,saidai ubansa yace mun yatafi ingila karatu..bayan tafiyarsa da shekara 2 naje har gd ,nayiwa hassu tas na zageta and na fahimci ita taraba Kabiru da danginsa,nakuma bukaci yasaketa ,sai yanuna Sam bazai iyaba,yahau mun magiya ,nayi hkri.nikuma nace bbushi bbuni,na Hana kowa zuwa gdn,har tsawon shekara 2"bezoba babu Wanda yaje adanginsa,dama shine babban agurin a sai ,halliru kaninsa,da autata safara...

Shiru sukayi kowanne zuciyar sa cike da tausayin wànnan ahali nasu Abdallah , lallai mom irinsu aduniya annobace babba..

Bayan wasu mintina Hjy Kaka tace ,insha ALLAH zamuyi nassara akanta ,gobe insha ALLAH saina biku acan,har gdn sa ,muga zai ganeki ,Kuma zai nemi yafiyata sbd bayin kansa bane ,ta fad'a tana nuna umma..

Umma tace to shikenan ALLAH yasa hakan shiyafi alkhairi..

Suka amsa da Amin...

Washe gari da da guri suka kimtsa,kafin hjy Kaka takira su halliru da safara'u tasanar da su tafiyarta kaduna,juma suma zata bukaci ,suje nan gaba...

Gurin bayan sallar la'asar ta su hjy Kaka suka iso gdn Alh Kabir girma su 4 Hafiz,ammi,umma,hjy Kaka...

Kaitsaye babban parlourn gdn suka nufa, Hafiz yyi saurin cewa,kubari nashige gaba,ke Kuma matar sai kibiyoni abaya , yafad'a Yana nuna hjy Kaka Yana murmushi"dungure Masa Kai tayi tana cewa haba ai kamun tsufa ,nabarwa Matarka Kai, tafad'a tana dariya sbd har cikin ranta tana kaunar Hafiz jinsa take tamkar jikanta ne shima...

Sallama Hafiz yyi"mom na kwance cikin kushin ta aza k'afa d'aya kan d'aya,da alama duniyar ta Mata dad'i...

Amsawa tayi a yatsine, had'e da dubar Mai yin sallama,idonta yahango Hafiz...

Gabanta yyi mugun faduwa,rabaon ta dashi tun ran bakwai na marigayi Abdallah"had'e rai tayi had'e da cewa mlm lfy?"in maula ta kawoka,to ai Wanda kake zuwa gurinsa ya shek'a barzahu..azatonki kenan , matsiyaciya annamimiya Mai bak'ar aniya to jikana nabusa doron k'asa bai mutuba,tunda ransa ba a hannunki yakeba...hjy Kaka tafad'a had'e da fitowa dg bayan Hafiz, yyinda umma da ammi suka bayyana...

Wani mummunan faduwa gaban mom yyi,tuni gabanta yahau dukan 100 100 lolx...ammi tayi murmushi had'e da cewa naja'at Musa ce tsaye agabnki ,nasan a hospital Baki ganeniba,to yanzun nasanar da ke ,Kinga kin fita dg duhu ko...umma ta karbe zancen da cewa nikuwa nasan Baki sanniba nice BINTU k'anwar HAJARA da kikayiwa kurciya,Kuma nice mahaifiyar Riyan matar Abdallah...wani irin zabura mom tayi, tuni kunnan ta ke jiyo Mata gargadin klboka,inhar yaga jinin matarsa to zai tunata...saidai kafin tayi wani Abu , sallamar da Abba ya kwad'a tadaki dodon kunnanta..cikin tsantsar tashin hankali tace alh kada...kad... BINTU UUUUU!Abba yafad'a da k'arfi had'e da nunata da yatsaya,saikuma yadafe kansa had'e da runtse idonsa ,yanajin hajijiya, had'e da juwa ,asukwane Hafiz dake rungume da hannayensa na kallon tashin hankali acikin idanun mom,yyi saurin tarbe Abba... yafad'i sumamme... Mom kuwa da gudu ta nufi kofar fita,Amma Ina...umma tayi saurin fincikota ta wanketa da wani gigitaccan Marka lafiyayyu guda 3 ,saiada jinta na wucin gadi yadauke, kafin,ta hankada ta,ta fadi kanta yabigi k'asa...ammi ta kamawa umma suka aza keyar mom ,suka kaita wani d'aki suka rufe...

Kafin sukoma su Sami Hafiz na yarfawa Abba ruwa .

Wata nauyayyar ajiyar zuciya Abba yasaki ,Yana furta INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU'UN....

Faruq da Alhasan na shiga cikin gdn ,suka Sami hussy na kuka ummi na rarrashinta,Zama sukayi akan 2 seater, Alhasan yace kingani ko ummi ?abinda nake hangowa kenan gashi yafaru...

Ya isa haka Dan.... maganar ta mak'alewa ummi, sbd jin kanta yyi mugun sarawa...

Rufe ido tayi had'e kwantar da kanta jikin kujerar da ga nan Bata sake sanin inda kanta yakeba...

Da adduar tashi dg bacci ta falka abakinta, had'e da bud'e idanunta,taga su hussy , Alhasan da Faruq zagaye da ita suna Mata sannu... Kallon su take tamkar Mai nazari tasan tabbas yayantane,to Ina Abdallah yake ?" Cikin wani yanayi tace Kai Ina Abdallah yake???"" Da Kuma abbanku?....

Bayan tafiyarsu umma,akabar riyan nata hawaye..

Kekensa yaja ,ya iso gabda ita.

Ahankali yace....

Share

BY MMN FAREESA [3/19, 9:03 PM] Mmn fareesa: 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🌺AUREN WATA SHIDDA🌺

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

Story & written by mmn fareesa

Dedicate to all my fans🥰🥰

p 45

"""Ahankali yace Riyan !yakamata ace kindena kukan nan haka pls"inkuma nine bakya San gani insha ALLAH Inna sun dawo koban warkeba Zan sallameki "yafad'a had'e da kafeta da golden eyes nasa akan fuskarta.. Afirgice ta d'ago kanta suka had'a ido da shi,sai yyi murmushi Mai kashe zuciyar masoya..tsab yagane kobata sonsa to akwai tausayinsa azuciyarta da k'wayar idonta ,dama yyi hakan ne bisa plan d'in su dasuka shirya da Hafiz Dan yagane tana sonsa..mlm Dan ALLAH katafi kawani zo katsare da ido...ta fad'a had'e da murgud'a baki tana k'unk'uni" bedena kallonta bekuma Yi mgn ba,saima burgesa datayi ,sbd intana Masa hakan jinsa yake acikin nishadi... hannunsa Yayi saurin azawa kan nata ya rik'e Gam,kallonsa tayi tawani d'aure fuska ALLAH kacikamun hannu "kosokake kaci zalin d'ina ne?" Dariya yyi har fararan hakoransa suka bayyana...kafin yyi mgn jankwata k'ware(k'adangare) yafad'o k'asa jikake timmmmm!ahhhhh wayyo ALLAH Yaya Dan ALLAH kakoresa"riyan ta fad'a cikin tsoro had'e da buya bayan Abdallah ta rirrik'esa,kanta na a kafad'ar sa, hannunta nakan kirjinsa zuwa cikinsa, yyinda gogan naku yawani riketa Gam "Yana cewa yishiru bazai Miki komaiba"yafad'a had'e da Kiran Inna mairo dake cikin d'akinta...da sauri ta fito ...saikuma tayi baya ganinsu ahaka.shikuwa Abdallah ko ajikinsa saima cewa yyi Dan ALLAH Inna afitar da k'adangaren nan yatsoramun ita..sai asannan Inna ta lura dashi tasaka tsintsiya ta korasa...ajiyar zuciya riyan ta saki sai a sannan talura da yadda suke da Abdallah ,tayi wuf ta cikasa... amma sai yyi saurin riketa yace matsoraciya bbu inda Zaki tafi oya zauna inda kika tashi fira zamuyi yau"zance nazo... Batasan lokacin da tasaki y'ar dariya ba sbd yabata dariya"Wai zance yazo.shikuwa shagala yyi da kallonta,sai yaji kamar karta bar jikinsa...kinyi kyau my baby Riyan"turo baki tayi had'e da cewa Yaya niba baby bace"murmushi yyi had'e da cewa ke baby ce Mana amma aguna.. Riyan muje kirakani daki zanyi waya,yyi Mata k'arya...bbu musu ta bisa d'akin" Har gefen katifa ta kaisa ta taimaka Masa ya hau "wayar ta je ta kamasa sai ya karb'a yahade da hannunta,ya fisgota ta fad'o jikinsa" Lumshe ido yyi ya rungume ta akirjinsa Yana ajiyar zuciya,kafin yyi k'asa da murya yace aidai namiki wayo ,yanxun bacci zamuyi kafin ayi magrib.. Ba'ason baccin maraice nidai kacikani Dan ALLAH"Kai da bakada lfy,Amma saikayita.... had'e bakinsu yyi guri guda,hakan yasa takasa Ida zancenta....

**********

Kallon kowa yake da idanunsa"ahankali Yadubi hjy Kaka yace hjy Ina hajjona?"(sunan dayake Kiran ummi)wlh nayi wani mummunan mafarki Wai anrabani da ita Kuma Abdallah ya mutu... murmush me ciwo hjy Kaka tayi had'e da cewa ba mafarki kayiba da gske ne, labarin Mai tsayine Kabiru ,kaje kayi Sallah inkun dawo Zan maka bayanin komai ,nida wad'an nan bayin ALLAH n,ta fad'a had'e da nuna su ammi...tashi Abba yyi da taimakon Hafiz suka fice atare zuwa masjid.,,,,,

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJU UN!kalmar da dad'i ke fad'a kenan Yana , hawaye, tabbas hassu kin cuceni kin zalinceni ,kin rabani da matata har da juna 2 ajikinta,shin Ina zanga HAJARA ne?"inbacin dare yyi da yau bbu abinda zaisa naki zuwa Naga Abdallah.. yafad'a had'e da rungume Hafiz,yace nagode! nagode!! ALLAH yasa muku da alkhairi kaida mahaifiyar ka"tabbas Hafiz Kai Mai kaunar Abdallah ne,insha ALLAH kaida Abdallah bakuda banbanci agurina,Zan Kuma maye maka gurbin mahaifinka,tuni hassu ta so zugani akan nayimaka kaca kaca kafita arayuwar Abdallah"Ashe Kai garkuwane agaresa...shima Hafiz d'in kukan yake Yana cewa insha ALLAH Abba Dama can a uba na daukeka" Kallon umma Abba yyi yace wlh BINTU tun danaga RIYAN gabana yafad'i nayita tunanin Ina nasan mekama da ita, sannan naji Ina kaunar ta,Ashe y'ar kice jinin haraja ce"lallai ikon ALLAH kenan buwayi gagara misali, tabbas asanadin AUREN WATA SHIDDA da muka yiwa Abdallah da riyan gashi yyi sanadin warwarewar matsalar mu..wane irin AUREN WATA SHIDDA Kuma? Suka fad'a atare,Amma banda Hafiz Dan yasan komai... Nan Abba yyi musu bayanin komai,harda barazanar da mom tayiwa riyan sbd ta amince.... Salati sukayi bak'i daya,hjy Kaka tace lallai samun irin hassu 10 agari sai su tashi garin, lallai ta wuce tunanin Mai maitunani...nan Abba yasanar dasu tanada ciwon k'anjamau...kowa cewa yake madallah ai Bata gama ganiba...

Abba yatashi Yana cewa muje kukaini inda kuka rufe munafukar"tashi sukayi gaba d'aya suka fito..

Bud'e kofar sukayi,suka shige,atsorace ta d'ago kanta ,kallo d'aya tayiwa Alh Kabir girma ta dukar da kai k'asa sbd taga tsanarta muraran acikin idonsa...wani mugun shak'a Abba yyi Mata had'e da makata jikin bango,cikin muguwar tsawa yace makira maciyiya Amana !fasik'a,muguwa ,Ina kika kaimun matata?"natsaneki bana kaunarki ko kad'an Ashe da sihiri kika aureni,yo inada kamar HAJARA me Zan kalla ajikinki har na aureki, nagode ALLAH daban haihuwa dakeba" Auranki danayi nasan k'addara tace hakan...nasakeki saki 3 ALLAH ya isa tsakanina da ke bazan tab'a yafe mikiba har abada, yafad'a had'e da sakinta ya hankad'a ta kanta yabigi bongo...jikake k'uru rummmmm!cikin tsana Abba yadubeta had'e da cewa d'ana Abdallah Yana nan da ransa bisa taimakon wannan yanuna ammi da Hafiz, sannan bazaki bar gdn nan ba sai Abdallah ya warke , ma'ana ciwon yadawo jikinki ,kamr yadda bokanki yasanar da ke,duk cikin wad'anda kika zalinta kinfi cutar HAJARA da Abdallah,kin nuna Masa rashin girmama mutane ,kin koya Masa jin Kai da isa ,kin nuna Masa yyi miskilanci,Dan ma wasu abubuwan Ina hanashi,to kisani AUREN WATA SHIDDA da kika yimasa shine silar tonan asirinki,Kuma aure har abada tsakanin sa da matarsa sai mutuwa ce zata raba...

Tsaki hjy Kaka tayi had'e da cewa yabak'inki yabakin halinki,Naga alama ma Baki tubaba ,dama ance duk Wanda yatuba Dan wuya tubarsa be yiba,bakuma gama gani komai ba...

Shiru mom tayi sai zufa keta keto Mata,umma ta wurgo mata pure water guda had'e da cewa gashi Kisha sbd kada ki mutu bakiga dawowar yayataba da gudan jininta,inbacin hakan ko ruwan kwata bazan iya bakiba...

Bayan sun ci abinci kowa yaje yakwanta ,suna jimami had'e da farin cikin ganin matsalar su takusa zo wa k'arshe.

Washe gari,byn sun karya"Hafiz yace zaije gdnsa yaga Yaya feedo take,yakuma je office"Abba yace to shikenan Amma in zaidawo yadawo tare da feedo ,itama ammi nan zata dawo da Zama tunda akwai sassa ajikin gdn, kasancewar gdn unguwace guda..

Kafin Abba Yadubi hjy Kaka,yace hjy masu aiki zasuxo agyara ko wanne parts kema anan Zaki zauna banison nesa da ke... sannan nayiwa liman bayani d'azun da asuba danaje masjid"nace asauke alk'ur'ani Mai girma akuma tayamu da addua ALLAH ya bayyana ta,yabawa kuma Abdallah lfy"

Shine yace mun insha ALLAH indai tana raye to zata dawo hayyacinta,acikin 2 za'a yi guda Kota je gidana na kano kotaje k'auye gun iyayenta...

Ammi ta karbe zancen da cewa eh Alh ai munsanar da mutanan dake gdn intazo sukiramu awaya...

Abba yace Kai Masha ALLAH gsky doctor tsakanin mu dake sai godiya"ubangiji yabar zumunci"

Suka amsa da Amin"

Umma tace inkuma tayi k'auye Saida tasami Iro,duk ai bayan tafiyarta mahaifiyar mu tarasu ,kaga Bata saniba... salati Abba yyi cike da mamaki yace Wai Inna tarasu?umma tace eh wlh...

Ammi itace ta Kira Abdallah "alokacin suna tare da riyan,kan katifa,yahanata tashi yarik'eta Gam ajikinsa ,Kiran yashigo"yadauka da hannu d'aya yyi sallama..

Wa alaiku mussalam Abdallan Abba...muryar Abba ta daki dodon kunnan Abdallah...

Cike da mamaki dukda yyi zaton dama indai su ammi sunje gun hjy Kaka to Abba zaisan Yana raye..

Cikin muryar kuka yace abbana Kaine,?"kasami labarin komai ko?

Cikin tausayi Abba yace eh Abdallah kada kayi kuka kaji...be rufe bakiba Abdallah yafashe d kuka tamkar yaro karami, bakaramin tausayin sa Riyan ta jiba,batasan sadda ta rungume saba tasaki kuka itama,hakan yasa Abba yakashe wayar sbd shima zuciyar sa takare...

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull