Baccin so complete by m shakur - Chapter 19
Baccin so complete by m shakur Chapter 19: Baccin so complete by m shakur Chapter 19. Jama'a yakuke ganin zata kaya ne😂 EPISODE 4️⃣4️⃣
4,499 words
Jama'a yakuke ganin zata kaya ne😂 EPISODE 4️⃣4️⃣
Gaban Baffa bugawa kawai yakeyi trying to understand what is happening, me yakeji, ko banda Ameenatu Amirah shima Daddy yanada diya da Maman Baby mai suna Aminatu dasuke kira da Amirah ne? Sai gaishe gaishe ake ana rabe raben abinci lafiyayyu, mabukata na rububi ana amsa, Daddy yazo inda Baffa yake a tsaye jiki asanyaye yawashe baki yana gyara Babban rigan giznan dake jikinsa yace "Bismilah Baffa" Baffa yabisa suka zaga waje inda Daddy yayi parking Range Rover dakeda rai tana numfashi Baffa yabi motan da kallo, Daddy yabude masa yace "shiga bismillah" shiga Baffa yayi yazauna Daddy ma yashigo yajawo kofan yarufe yawani kunna AC yace "yauwaa sanyi yadan dake ka, ahhhhm Malam Sani" yajira sunan Baffa yana zaro miliyan dayan daga aljihunsa saiya rabata biyu tsabagen maitan kudi yace "ga wannan miliyan dayan sadakin Amirah ce, ga dubu dari biyar ka kaiwa Uwarta a matsayina na ubanta dana aurar da ita narike wannan"Baffa dake wani irin kallonsa batare daya karbi kudin ba yace "Amirah ka aurar Yusufa!"? Daddy yace "to laifi nayi dan na aurar da ita uban waye ubanta inba niba? Nine yayan mahaifinta uwa daya uba daya, a hannuna ta girma mahaifinta ya rasu, dudda kan ba dadi amman Allah yayi ta sami miji da Saleem zata aurar Babban amman kaman yayi tunani yace yafasa auren, uban ya aurama dansa karamin likitan ta Dr Marwanu, to me aciki bakin ciki kake mata?" Zuciyan Baffa yayi zafi shine ke gayama Ammi kullum tayakuri idan tana kawomai karan Abba amman yau ransa ya munnana badan komi saidai tayaya zai kama yarinya ya aurar bai sanar da mahaifiyanta ba eh, Baffa yace "mesa zaka yanke wannan Babban hukuncin akan rayuwan Amirah batare daka sanar da mahaifiyarta ba Yusuf?" Cikeda gadara Daddy yace "sabida na isa ne uba keda yarinya ba mahaifiya ba, ni ba kiranka nayi muyi musayan yawun baki ba dan banda lokacin nan sauri nake nakoma gidana dake GRA da Range Rover dita, ga sadakin ta nan ka kaimata zan basu address na gidan ka suzo su amshi matarsu atoh! Wuce kafitarmin daga mota karka samin dauda nidai" Daddy ya shiga kakkabe kakkabe dan ko abu daya baiso yagani a motan, Baffa yadade yana kallonsa kafin yayi wata murmushi yasa hannu yadauki 500k da Daddy ya ijiyemai a jiki yajuya kudin ya kalla saiya kalli Daddy dake kallonsa yace "nayarda da abu daya daka fadi wanda babu amfanin musayar yawun baki nima bazanyi dakai ba amman dai kasani cewa akwai Allah Yusuf, sannan Allah yana kallon komi, ga kudinka niba dan sakonka bane, kaje ka kaiwa mahaifiyar yarinyar kudin da kanka"ya ijiyemai kudin yabude kofa yafita Daddy ya sauke glass kasa yana ihu yace "oho dai kuma idan an isa Kuki Kai yarinya gidan mijinta kuga wlh ko kötü kuka kaini nafiku gaskiya dan nine uban yarinya saidai ku mutu" Daddy yahau zage zage.
Machine Baffa yahau bazaima iya tantance ga abinda yakeji ba aurar da Amirah? Yarinyar nan is a total sick girl, meta sani kan aure? He see sometimes Mamanta kemata wanka ma wlh, yana ganin yanda Amirah ke shirme, me Amirah tasani? Meta iya? Idan aka cutar da ita agidan auren fa mijinfa? Menene manufan su na auren yarinyar da ana gani andan cewa at this junction Amirah ba abar da za'a aura bace dan babu kan,… Sosai Baffa ke lissafi haryakai gida, azaure yayi parking da sallama yashiga gidan Amirah da Ammi yagani a tsakar gida Lami da Miemie na kitchen, Ammi na tsefema Amirah kalaban kanta Amirah kuma na rike da bowl da naman Kazan kayan matan Miemie ke ciki tanaci tayi wani irin kyau da fresh tayi bulbul takara haske dan ana musu gyaran jiki, sallaman sa yasa Ammi yadago kai lami ma tafito tace "harka dawo Malam" gyadamusu kai yayi Ammi ta tsaresa da idanu ganin yanayinsa daman yagaya musu ina zaije daki yashiga yace "zo Maman Amirah da Lami" dasauri Lami tabi Baffa ciki Ammi takalli Amirah dakecin kaza abinta tace "Miemie karki bari taje wajen rijiya" Miemie tace "toh Ammi" tafito tazo zata cigaba da mata tsifan Amirah ta make mai cikin tar kannauwan murya tace "naki zafi" Uwardaka Baffa yashiga Lami tabiyosa dasauri tace "meya faru Babansu? Mesa kai wani iri haka?" Daidai Ammi tai sallama Lami tace "shigo shigo Maman Amirah" labule Ammi tadaga tashigo tana kallon Baffa daya zauna bakin gado saitaja kujeran dake gaban dressing mirror ta zauna takalli Baffa tace "Baffa meya faru? Karka wani damu kanka indai mutumin nanne, meya faru?" Ammi ta kallesa sosai tana jira yayi magana, ijiyan zuciya Baffa yasauke ahankali yace "Haleematu ammm" yasake shiru sai gaban Ammi tashiga bugawa sosai, ahankali Baffa yace "mutumin nan ya aurar da Amirah!" Wani kalan zabura Ammi tayi tamike tsaye Lami ma haka ta dafe kirji tace "Innalillahi wa innailaihi raji'un, Amirah ya aurar" Baffa yadan sauke ijiyan zuciya yace "kodanakai masallacin naga mutane yace na zauna zamuyi magana bayan an daura auren nan kawai jinayi ana daurama Amirah aure, aka gama yakirani zuwa motansa yabani dubu dari biyar cikin miliyan daya na sadakinta wai nakawo miki, nabar masa kudin awajen yace zai bada address namu azo daukan Amarya" kirjin Ammi bugawa yake sosai ba wasaba, saita koma ta zauna ahankali takai hannu tadaura hannunta saman fuskanta brain dinta was blocked for a moment saita kalli Baffa da murya wanda bazaka iya tantance wani yanayi take cikiba tace "kasan wanda ya aura mata Yaya?" Ahankali Abba yace "that is where it gets complicated sabida Yusuf cewa yayi wai yayan yakamata ya aureta sai kuma aka aurama kanin Dr Marwan!" Dawani kalan sauri Ammi takalli Baffa, Baffa yace "kuma mahaifin ya sanar a masallaci cewan yayi hatsari yana asibiti iyakan abinda nasani kenan" Ammi tai shiru tai mutuwan zaune yaya yakamata ya auri Amirah sai aka bama kani wanda ke asibiti in all this thing the only person data sani is Marwan, da Yaushe har sukaje neman auren Amirah ita tana mahaifiyar Amirah batasan komiba, Dr Marwan bata taba ganin alamun yana son diyarta ba, wayan nan mutanen dasauri Ammi tace "yaya zaka iyamin kwatancen uban angon?" Baffa yace yanada jiki da katon ciki haka yanasa glasses a idanu gemunsa fari tabbas sune wayanda yagani rannan da sukaje inda Marwan yake does that mean wanda yaduka ya gaidata dinnan shine Saleem din sai yafasa aurenta maybe sabida mahaifin najin kunya sai aka bawa Dr ita, wani abu taji a wuyanta, saitaji zafi aranta badan komiba saidan cewa Dr Marwan datake ganinsa mai amana yasan da anason diyarta bai sanar da itaba, ahankali Baffa yace "dakata Haleematu yawanci akaga diya anaso uba ake nema ama magana ba uwa ba kada ki fushi dashi wannan itace gaskiya!" Ammi bamatasan maganan zucin datayi awaje tayisa ba, mikewa tayi azuciye dasauri Baffa yace "ina zaki?" Batare da Ammi tajuyoba tace "zanje naga mutumin nan nanne" fuu zata fice a falo Baffa yaci mata yarike mata hannu yace "Haleematou!" Dasauri Ammi tajuyo tace "Yaya me kakeso nayi look at her kalleta!" Tanuna Amirah dake compound kan tabarma Miemie namata tsifa saura guda daya hannuwanta biyu duka abaki tace "Yaya kai karan kanka zaka yarda a aurar da yarinya mai kalan wannan laluran me aure zai amfaneta dashi eh? Ka kalleta Yaya" Baffa yace "nasani Haleematu but fushi baya maganin komi ki tsaya ayi magana Asan yanda zamubi abim nan cikeda hikima dan aure fa ya dauru unless mijinta ne ya saketa kokuma kotu taraba aure amman dai Amirah kam ta auru MATAR wani ce yanzu" hawaye masu zafi Ammi suka fito daga idanunta, Baffa yace "I know what you're feeling amatsayina na babba abu daya zan gayamiki tashin hankali baida amfani karki manta abinda aka gayamiki game da Amirah bata kaynar ganinki cikin tashin hankali ko damuwa dan warke wan nan da muka samu tayi zata koma gidan jiyane, da Dane kin isa kibar Amirah kizo nan bata biyoki ba?"Ammi ta girgizamai kai Ammi tace "to kingani, shi mutumin chan so yake ki biyosa kuyuta bala'i kuma bazaki bisa ba, kome yayi yaje shida Allah, aure fa ta auru yabada iko yanada hurumin aurar da Amirah da Miemie dan haka kibar wannan I think ni atunanina tunda kunsan likitan nan amatsayinmu na manya mu nemesa da iyayensa mu sanar dasu laluran Amirah mu nemi yasaketa kawai" Ahankali Ammi tace "babu abinda bai sani kan Amirah ba" anatse Baffa yace "shine mutumin da Amirah tagayamin tanaso?" Shiru Ammi tayi saita gyadamai kai, zatai magana sai Lami dasauri tace "tsaya Maman Miemie, zuwa asibitin sa yaşa Amirah taji sauki haka kinyi tunanin cewa tunda tana sonshi aurensa yasa kuma ta warke gabaki daya fa"? Ammi dasauri tace "to shi yanasonta ne Lami? Shirme kawai Amirah takeyi? Yana likita akan wani dalili zai auri mai matsalan kai eh" anatse Baffa yace "banson ki nemi mutumin chan, ni zan nemi gidansu ko asibitin inda yake zaki gayamin naje nai magana dashi"Ammi tadade tana kallon Baffa batai magana ba, Baffa yace "I know you're hurting kiyakuri kinji" hawaye ne masu zafi suka zubo daga idanun Ammi batasan metama Daddy ya tsaneta da yaranta hakaba amman dai tabarsa da Allah. EPISODE 4️⃣5️⃣
Daga wajen daurin auren nan bayan ya gaggaisa da mutane driver ne yatuka Abba bai tsaya ko'ina ba sai asibiti, Mami na zaune kan gadon kusada Marwan data ke basa oath da kanta da yau shiya tambayi oat din, yarame Mami tayi kuka fin adadı bata taba sanin soyaya zata iyasa Marwan yafice hayyacin sa ba, wayanta ne yahau ringing hannu daya tasa zata dauka sai Marwan yasa hannunsa ahankali ya karbi bowl din yana magana kasa kasa yace "take your call Mami" Mami tadan kallesa taga yacigaba dashan Oats din ahankali, takai wayan kunne batamaso ta tambayesa an daura aure lafiya cus she's afraid she will hurt Marwan more sai kawai tai shiru, ahankali Abba yace "fito parking space akwai maganan dazamuyi" yanayinsa taji saitace "okay tom" saita kalli Marwan dayayi kaman baimasan da Abba take magana ba, tace "Abban ka na kirana, ina zuwa" Gyadamata kai kawai yayi baice komiba Mami tawuce tafita daga dakin tana gyara mayafinta tafito direct zuwa motan Abba daga ciki yabude mata baya tana zuwa saita shiga tana kallonsa baya farin ciki yana cikin damuwa tace "baka da lafiya ne meya sameka?" Takai hannunta zata taba jikinsa saiya kama hannunta tareda sauke ijiyan zuciya yace "Zainab yau namiki laifi" Abba yayi shiru Mami takasa magana gabanta sai faduwa yake Ahankali yace "I know Marwan kanni ki ne, kece matsayin mahaifiya garesa amman yau amatsayina na wanda ya dauki Marwan dan cikinsa na dauki wani babban hukunci kanaa batare dana tambayi shawaran ki ba" Abba yayi shiru saiyace "babu abinda zan iya boye miki aduniya" saiya bude wayansa yashiga chats na Saleem yace "watch this video"da zuciya daya Mami ta amsa tana danna video tai wani ihu ta yarda wayan kasa ta kulle idanunta tana salati Abba ma haka dukansu sunajin karan muryan Saleem da karan yanda yake sex dan Mami bata danna purse ba ta yarda wayan Abba ne yaduka yadauki wayan saiya tsaye da video yakalli Mami yace "nasan bai dace na nuna mikiba but inaso kiga abinda ya tunzurani nayi abinda nayi ne" yayi shiru yace "bayan Saleem yaturomin video nan yakirani video call yana kan aikata alfashan sa idona idanun Saleem ya sanar dani shi bazai auri Amirah ba karuwansa yakeso ina miko magana lokacin biyu tawuce jama'a birjik masallaci manyan mutane da fada aure bama ağa ango ba zai zama abin kunya gareni da iyalaina dana sana'ata, the only solution to the problem danagani is yaron daya daukeni tamkar mahaifi wanda bazai taba saba umarnina ba and bakowa bane wannan ba illa Marwan!" Abba yayi shiru yana kallon Mami kaman yanda take kallonsa, saiya kama hannunta asanyaye yace "I don't know idan zaki dauki abinda nayi kaman na cutar da kaninki ne na aura masa wacce bawai lafiya kaman kowa gareta ba, zaki iyamin kowani hukunci kikaga dama amman na aurama Marwan Amirah Sweetheart!" Mami tadade tana kallonsa she's extremely happy dan yau takara yarda cewan Allah baya bacci kuma inhar mutum matarka ce ko anika kake sai tazama matarka, ciwon da Marwan yake yakici yaki cinyewa sabida mugun so dayakema yarinyar nan, Abba knows nothing about Marwan na sonta amman look at how ya aurama Marwan, soyayyan da Marwan kema Amirah is a secret wanda ba huruminta bane ta fadaba tunda shi Marwan bai fadaba itama ganewa tayi dan haka bazata fadama Abba ba, lumshe idanu tayi tabude ahankali asanyaye tace "ka tabbatar da Saleem yafasa auren koko shaye shaye yasa ya furta haka banson abinda zai zama suzo suna ga maciji shida dan uwansa Marwan banso Alhaji" Mami tafadi ciki da damuwa Girgiza mata kai Abba yayi bacin ransa nakara bayyana yace "kinga Saleem!" Saiyayi shiru yace "banso na furta abinda ke zuciyana but I will tell you one thing wlh wlh koda ban aurama Marwan yarinyar nan ba bazan taba aurama Saleem itaba ko ina hauka yaje ya kashe yar mutane da kanjamao, koya dinga bata giya tanasha ko kayan hayaki, ai yaje chan ya auri daidai shi, nasan Saleem amanane amman baka iya tike amanan da baiso arike, nayi iyakan bakin kokarina, ni Saleem zai tozarta, ni zai aikama video alfashan dayakeyi sabida bai daukeni a matsayin komi ba i am nothing gani banza, ni Saleem zaima haka" Abba is really really hurt Mami ta matse hannunsa ahankali tace "ya isa, Allah ubangiji ya shiryar dashi, Allah ya ganar dashi gaskiya, Allah ya yafemak zunubansa" Abba baice komiba yace "muje naga d'ana" yabude mota yafito, Mami ma haka, suka wuce cikin hospital din Abba yana rike da certificate na aurensu wanda ayanzu manya manyan masallatai suke bayarwa, ahankali Mami tabude dakin da sallama Marwan na zaune yadan kishin gida, black tee ne ajikinsa mara any design sai white glasses a idanunsa, yayi wani haske, gashin kansa sun kara nannadewa sosai sabida yawan kwanciya dayake this days, lips dinsa sunyi pinkish sosai, yarame but he looks so damn cute and rich, irin rich yaran nan dake asibiti marasa lafiya, ya rufe da bargo daga kafansa zuwa wajen cikinsa ganin Abba yasa ya yunkuro, dasauri Abba yakamasa yace "yi zaman ka dan albarka ya jikin" gyadama Abba kai yayi batare dayayi magana ba yacire idanunsa daga kallon Abba dan kayan jikinsa yanuna daga wajen daurin aure yake zuciyansa yahau masa wani iri da har saida fuskansa ya nuna Abba yace "wani abu namaka ciwo ne nakira Dr"? Girgiza Kai yayi baiyi magana ba, gabaki daya yazama baya wani magani kwanan nan yakara zama miskili sosai har Mami saitayi da gaske zaiyi mata magana, Abba yadan sauke ijiyan zuciya saiya zauna bakın gadon Mami tazo ta tsaya gefensa dukansu suna kallon Marwan dayaki kallonsu yasa idanunsa akan TV dakin dake aiki dudda baisan me ake yiba bayama ganewa, ahankali Abba yace "Saleem baizo wajen daurin auren ba!" Sarai Marwan yaji me Abba yace amman sai baiyi any motsi ba, ahankali Abba yasauke ijiyan zuciya yace "ba'a daura auren da Saleem ba Marwan!" Juyowa Marwan yayi ahankali yakalli fuskan Abba da kyau trying to really get mai Abba yake nufi da ba'a daura auren da Saleem ba, ahankali bakinsa yayi motsi zaiyi magana saiya kasa, Abba yace "Saleem bazai taba chanza hali ba, shaye shaye, bin mata bazai taba chanzawa ba" gently Marwan yace "Abba Saleem ya chanza, yadena all those thin……." "Karya yamaka!" Abba ya katse Marwan. EPISODE 4️⃣6️⃣
Abba yace "karya yamaka Marwan, this is what he sent me" yaba Marwan wayan Marwan ya karba yana kallon watsapp din saiyamaki danna video dan from irin hoto dake nunawa ajikin video kafin ka danna ka kunna yaga Saleem dawata tsirara saiya ijiye wayan ahankali, Abba yace "Saleem yakirani awaya yana aikata abu mafi muni yana cemin yafasa auren Amirah na aurama wani karuwansa zai aura"sosai kirjin Marwan ke bugawa Allah yasani he believed in Saleem sabida yaga he was serious about yanda yakeson Amirah harda kwanciya asibiti he really did change what happened? Why? Ko Sheri aka masa, Marwan! Abba yakira sunansa Hakan yasa yakalli Abba yace "na'am Abba" ahankali Abba yamika masa certificate dake cikin babban envelop da aka rubuta Alhul Sunna Daawa community da larabci yashiga zaro certificate din gabaki daya idanunsa yasauka kan sunansa dakuma sunan Amirah kafin yagama gane kan abinda yake karantawa Abba yace "na auramaka Amirah! I choose you to become Mijin Amirah!"Faduwa certificate din yayi daga hannun Marwan yakalli Abba dasauri kirjinsa na wani kalan bugawa kaman saukan aradu dumm! Duumm! Dumm! Yakasa furta daidai da kalma daya, Abba ya lumshe idanu yabude, yace "I have so many soo many reasons dayasa na aura maka Amirah I will tell you few" Abba yayi shiru, yace "ata bangarena nasan duk duniya Marwan kai kadaine zaka cireni daga kunya dan uwana na jini almost made me karamin mutum amman nasan babu abinda bazakayi ba dan kare darajata da martabata a idanun jama'a so this is one of the reason that has to do with me outside that Marwan, bantaba ganin someone as caring as you're ba, I see the way kake tolerating Farida, Faiza da sauran yaran yayyinka inhar zaka iya kula dasu haka kayi hakuri dasu haka kakuma sosu haka Amirah take she will have your care, your attention koda baka sonta wannan shine dalilina na farko!"Abba yayi shiru dalilina na biyu shine I believe in you can help yarinyar ta warke gabaki daya, ban hadu da uta adakin nan dakai hatsari ba amman Maminka tacemin nan tazo sabida na gayamata mun ganta akasa, this simple means despite yanda yarinyar take batason jama'a dan data ganmu boyewa tayi bayan Mamanta harda rufe fuskanta da hijabin Mamanta abinda nake fadi anan shine despite condition nata zuciyanta acknowledge and identify you sama da mu anan duka har shi Saleem din rannan ko kallonsa batai ba, so what if dalilin auren nan naka yasa ta warke gabaki daya kasan kalan ladan daka samu"dalilina na uku shine I saw na girl all I see is a pure innocent girl da idan Allah ya bata lafiya mace ce dakowani namiji zaiyi burin damunta agidansa, you will teach her everything ilimin adını, boko zamantakewa, irinsu sune matan da ake building healthy and a fruitful marriage life with, and I see you in a better position to take care of her ba Saleem dakeda garagara ba, you are gentle so is the girl you're the best man for her just give it a time I know zakaso ta and for me na tunaninka na aura maka ita only means Allah ya kaddara daman matarka ce I know namaka ba daidai ba ban tambayi shawaranka ba but I feel inada wannna ikon akanka dan kai d'a nagari ne Marwan, dan haka Amirah, I mean Ameenatu matarka ce ayanzu, get well a sallameka zansa yayyinka suje gidansu dauko matarka kaji!"tunda Abba ke maganganun nan kirjinsa ke bugawa, he knows Saleem ayanda yakeson auren Amirah, kome yace Abba kome ya turoma Abba he did it in state of baya hayyacinsa he was high giya ta bugar dashi, ahankali yace "Abba!" Abba na kallonsa saiya hade fuska cikin kakkausan murya yace "banson ka furta koma wani kalamai kake kokarin furtawa dan zan saba maka Marwan!" Mami tai murmushi kawai bata cemusu komiba, sauke kansa kasa Marwan yayi yay shiru, asanyaye yace "Abba tayaya zanyi rayuwa da wacce yayana keso is it proper?" Dan dariyan takaici Abba yayi, saiya kalli Mami yace "kinsan mene everything is just coming back to me komi is getting clear yanzu nake kara fahimtan Saleem wato ko Allah ko cike yake daya hikima Allah kuma ba azzalumi bane baya bari acutar da mumini"yace "I don't think Saleem yataba kaunar yarinyar nan, dan iskan yaron nan if you look at it ubanme zaiyi da yarinya mara kai? Kawai shiyasan meya gani shirin morewa yayi, dan duk wanda yakeson wani so na gaskiya zaibar aikata abubuwan da Saleem yake yajira auren sa, so Please Marwan karna karaji kace Saleem na son yarinyar nan trust me Allah ne ya kubutar da ita daga hannunsa data kara haukacewa, Amirah matarka ce Allah ya sanya albarka a aurenku, bari naje manyan baki na na jirana a company" yadauki certificate din da kansa yasa a hannun Marwan saiya dago kan Marwan suka hada idanu ahankali Abba yace "I know babu abinda bazaka iyamin ba and you will never disappoint me, I choose this girl for you kariketa amana kabarni da Saleem, kayi wani abu Marwan I will not be happy with you this marriage" yanuna mai certificate din, yace "this Marraige is forever Marwan!" Saiya mannamai kiss a goshi yajuya kawai yafita Mami nawani kalan murmushi kaman taita ihu Marwan was speechless bazai iya tantance ga exact yanda yakeji ba, he feels wani sanyi sanyi azuciyansa yanajin duk wani damuwa na jikinsa na barinsa for the first time in this 7days dayake hospital saiyaji duka ciwukan dayakeji just varnish and dissapers, bangare daya na zuciyansa na tunanin Saleem kuma while bangare daya na zuciyansa na tunanin Amirah dayaji yana wani kalan jin yunwan kewanta he just wanna see her, dago idanunsa yayi suka hada idanu da Mami dake murmushi tana kallonsa dauke kai yayi dasauri saiyaji yanajin wani kalan kunya, da gangan Mami tace "uhn my son feels better barı na nemo Doctor Naji Yaushe za'a sallamemu" tawuce kofa tafita su Ammah takeso taje takira.
Marwan yayi shiru saiya kalli certificate din yakai yatsansa yana shafa rubutun sunansa zuwa rubutun sunan Ameenah he can't believe he's the husband is he dreaming? He can't just believe it at all, but bangare daya na zuciyansa sai tunanin Saleem yake wayansa yadauka saiya shiga jiransa har wayan ya katse ba'a daga ba, yacigaba da kiran he promised kansa bazai bar kiran wayansa ba saiya dauka amman shiru, akira na kusan biyar ne aka daga wayan tass tass tass kawai yakeji na sex ga ihun Precious datakeyi da gangan. "Yes Daddy! Yess Daddy! Yess yess yess…" cire wayan saga kunnensa Marwan yayi cikin kakkausan murya yace "Saleem!" Dasauri Precious tace "tell him the same thing you tell your brother Daddy so that they will leave us alone" "Saleem!" Marwan yakara kiransa hakan yasa Saleem yace "what!?" Mtsww yayi tsaki cikin muryan shaye shaye yace "I'm fucking some good damn ass pussy yoh, why d call? I said I don't wanna marry that pagal girl, fuck you Marwan and fuck yays!" Dasauri Precious tace "tell him ni zaka aura" dasauri Saleem yace "ama marry my baby right here! Suck suck suck my dick bab….." Marwan katse wayan yayi yay shiruuu saiya ijiye wayan kawai.
Sunci juna yafi sau ashirin sannan tasasa bacci tadauki wayanta tafita falo tashiga kiran Mommy tace "Mommy what next?" Mommy tace "good girl now when he wakes up kuje any mosque make sure you wear their kind of outfit kuje a daura muku aure, make a story that kin musulunta but his parents refuse to accept you okay" dasauri tace Mommy you are the best, dariya Maman tayi, bayi Precious tashiga tai wanka tanada sabuwan abaya ta saka tazo gado ta tada Saleem da kyar yatashi tacd "muje kayi wanka" wucewa yayi, koda yafito sanye da towel ya tsareta da idanu wani mahaukacin sha'awanta yakeji yayi kanta rikesa tayi tace "no idan mun dawo ga kayan dazaka saka" shaddan yadauka yasaka tace "muje" fita sukayi da kanta tai tuki har zuwa wani massallaci anan bakin titi tai parking tajuyo ta kallesa tace "we are getting married i want you kashiga that mosque kace na musulunta iyayenka refuse to accept me so kake muyi aure am I clear" wani iri yaji azuciyansa amman saiya gyadamata kai yafita yashiga haka akayi nan da na. Aka daura musu aure yabiya 50k cash dake jikinsa har wani tsalle takeyi.
WANNAN SHINE SALEEM YACI GINDI MAI TSADA!
MUJEDAI ZUWA!!!! EPISODE 4️⃣7️⃣
Har tsakar dare Ammi takasa runtsawa daga ita harsu Baffa da Lami babu wanda ya sanar da yaran abinda ake ciki, wayanta ta laluba saita kunna flash din cikin kudin data samu banda gadon data siyama Miemie tasa musu babba adakin da katifa mai kyau babban gado ne da ita da yaran duka suna kai, Miemie ce char karshen gado Amirah ko saita tabiyo Ammi ta kwakumeta sannan take iya bacci, tsare fuskanta Ammi tayi da kallo, she just can't help it ne dazaran kanada d'a dakeda damuwa you can't help it but to worry about yaron, tunaninta is tayaya wannan yar yarinyar da batasan komiba zatai aure, har yau har gobe tanama Amirah wanka ta shiryata da kanta, idan tana period ita ke shiryata, she knows tun suna yara tasa Amirah islamiyya but she's not even sure idan Amirah ta iya wani abu cus bata magana daga baya tazo tafara tsoron mutane hakanan tahakura tadena aikata islamiyyan, tasan cewa duk abinda aka koyama Miemie Islamiyya da gida idan tadawo tana koyama Amirah tare kuma sukeyi homework, but will she depend on that tace yarta tasan wani abu a islamiyya? Sabida condition nata Amirah bata taba azumi ba, tanasata tai salla but ita kanta Ammi batasan ko sallan ma mai kyau bace cus Amirah bata cikin yaran daza'a kira da sunada cikakken hankali, as long as suna tare duk sallan da Ammi zatayi tana sata tayo alwala tare sukeyi, Amirah ko indomie batasan ya ake dafawa ba, ko tea Amirah bata taba dafawa da kanta ba, itada Miemie does everything for her, bata wanki saidai tasa hannu taita wasa da ruwan kumfa tanajin dadi idan taga Ammi na wanki tayaya Amirah zatai rayuwa gidan miji or is she thinking too much? Is she exaggerating? Ammi ta tambayi kanta, abu na farko kenan da Ammi ke tunani, bata kalli Amirah as wacce keda wayau na tarairayan miji, kula da muhalli da abincin da miji zai ci ba, idan aka koma kan bangaren tarayyan miji fa? Ammi tun yaranta na kanana 3yrs haka take dena cire kaya gabansu dan babu kyau, she's not even sure cewa Amirah tamasan ya jikin mata yake balle na maza, ko Miemie batajin Amirah ta taba wani ganin jikinta haka ba balle kuma namiji tayaya zasuyi wannan rayuwan? Mijin ta zai iya hakura bai nemeta ba har zuwa sanda zata warke tasan menene rayuwa? Tayaya Amirah zatai handling bukatan miji idan kuma Mijin mabukaci ne yaya diyarta zatayi? Will aure help condition Amirah kuwa koko it will make it worse? Dr Marwan dudda yanada kirki amatsayinsa na likita shin zai kasance yanada kirki a matsayinsa na miji? Zai kula da diyarta? Yanason diyarta kuwa tunda wanaa ne yaso diyarta shi yace yafasa aka aurama Dr, dan da Dr na son diyarta dashi zai fara fadi tunda ai shine likitan Amirah? Ammi takama nan takama chan tadamu gani take banda ita babu wanda zai iya kula mata da diyarta aduniya batason Amirah tafada hannun miji kalan şu Daddy a azabartar mata da yarinya da daman bawai lafiyan ya isheta bane, yanzu yazatayi tajira su Baffa yaje yagansu tukunna ko mene?.