Kenza eBookz

Baccin so complete by m shakur - Chapter 20

Baccin so complete by m shakur - Chapter 20

Baccin so complete by m shakur Chapter 20: Baccin so complete by m shakur Chapter 20. Wuraren 7:00AM Baffa ya fito tsar gida ya shirya tsaf cikin shiddan…

4,223 words

Wuraren 7:00AM Baffa ya fito tsar gida ya shirya tsaf cikin shiddan sa mai kyau kal kal, Ammi dake shirya Amirah datai wanka tana jamata zip na bayan riga ne Baffa ya kwalama kira, Ammi tace "maza to je wajen Miemie ta daura miki kallabi" wucewa tayi wajen Miemie da ita tagama sa kaya Ammi tafice waje tace "Baffa ina kwana" "amm ku tashi lpy zanje asibitin yanzu idan ba'a sallamesu ba nagansu, idan kuma an sallamesu zanyi tambaya naga kozan gano gidansu" gyadamasa kai Ammi tayi yawuce yaja Babur nasa yatafi.

Wuraren 8:30 Baffa yakai asibitin yayi parking har room number Ammi tabashi saiya wuce yashiga yawuce sama. Tun jiya da daddare da Dr yazo yaduba Marwan yace zai sallamesa sosai yaga he was much better this morning zasu tafi, Abba ma da sassafe yazo dan dakansa yakeso yatafi da su, Marwan na zaune ya chanza kaya zuwa wasu simple t-shirt na wando black inda aka masa operation ma baya masa ciwo ya warke tass, Mami tahada komi, knocking akayi a kofan dukansu suka kalli kofan sai Abba dayafi kusada kofan yataho yasa hannu ya bude wani dattijo yagani that is dressed properly yana kamshi mai dadi looking homely kai tsaye yamika masa hannu suka gaisa Baffa yace "amm kaine mahaifin Marwan? Nan ne dakin da Marwan yake"? Dasauri daga Mami har Marwan suka kallo kofa sai Abba yace "eh nan ne bismillah Bismillah" shigowa Baffa yayi kallo daya Marwan yamasa saiya sauke kansa kasa cikeda kunya yaga yanayinsa da Ammin Amirah Baffa yashigo Mami tace "ina kwana" dasauri yace "ina kwana yamai jikin" yakalli Marwan da kansa ke kasa anatse Marwan yace "ina kwana" kallonsa Baffa yayi anatse yace "ya karfin jikin Marwan? Allah ya sa kaffara ne " ahankali kowa yace "Ameen" Abba yanuna masa kujera yace "bismillah zauna zauna amm saidai ban gane fuskan ba"anatse Baffa yace "amm kuma ku zauna dan Allah yar magana yakawoni bamusan gidanku ba da nan mukazo amman anmin kwatancen nan saisa nazo nan din" zama Mami tayi Marwan ma yazauna kansa akasa Baffa yace "ammm sunana Muhammad nine Yayan Mahaifiyar Amirah uwa daya uba daya" Abba yace "Masha Allah ahh sannu da zuwa" dan shiruuu Baffa yayi sai yace "tsakanin mu babu boye boye, kanwata bata gidan Yusuf wanda yabaku auren Amirah, sannan Amirah ba diyarsa bace diyar kaninsa ce uwa daya uba daya wanda yarasu tun Amirah na karama sai aka hada mahaifiyarta da yayan baban Amirah Yusuf kenan aure Allah yabasu Maryam" Baffa yayi shiru shi kansa Marwan baitaba sanin mutumin ba shine mahaifin Amirah ba sai yau no wonder yanzu komi ke making sense, Baffa yace "dudda rabuwansu bai dade ba amman dai sun rabu, zancen danake maka bamuda sanin zancen auren nan sai jiya da safe daya kirani awaya kan yanaso nazo masallaci kaza danazo yace nadan jirasa bari agama dayrin auren nan yaganni nadaiji ana daura aure da Amirah, Baffa yayi shiru hakama duka yan dakin yace mahaifiyarta batasan komi akan zancen ba, Abba yasauke ijiyan zuciya, ahankali Baffa yace "dalilin dayakawo ni anan yau sabida nagana daku ne iyayen Marwan, sabida Yusuf ya sanar dane cewa ada yayan Marwan ne zai auri Amirah amman yafasa Dr ya aureta, daga mahaifiyarta hatta ni munada yar damuwa, na farko dai Amirah yarinya ce da bazan boye muku ba condition dinta ba yau ko jiyane yafara ba a'a tun tana yar kankanuwa abin yafara, so ba lallai tama iya wani zamantakewan aure ba, and condition nata is not a good thing da on top of everything zatai rayuwa da wanda ba lallai yana kaunantaba!" Hakanan Marwan yaji kirjinsa yafara bugawa yana Jin wani tsoro har baiso Baffa yasake wani magana dan gani yake kaman za'ace yasaketa kirjinsa bugawa yake kawai wlh wlh Sauda Mami ya lura, Baffa ahankali yace "munsan komi nufi ne Allah sannan bawai nazo danna kashe auren bane a'a abinda Allah yahada shine zai raba ba niba!" Wani boyayen ajiyan zuciya Marwan yasaki, Baffa yace "kawai inaso nasan cewa eh Marwan yasan wacece diyarmu sannan zai riketa amana, idan bazai iyaba amm…." Dasauri Abba yataresa yace "Hakan bazai taba faruwa ba!" Baffa yakallesa, ahankali Abba yace "ko bana duniya Marwan mutum ne dazan shedesa cewa bazai taba cutar da Amirah ba wallahi wallahi, zai riketa amana, and zai sama mata lafiya da izinin Allah" wani sanyi Baffa yaji azuciyansa ganin yanda iyayen mutanen arziki ne, anatse Mami tace "zaka iya binkici kan wanene Marwan tundaga kan asibitin nan zuwa gida dako ina, Marwan mutum ne mai amana, tausayi, dakuma zuciya mai kyau" murmushi Baffa yayi sai cikeda hikima irin na manya yace "Marwan!" Saida gaban Marwan yafadi yanda Baffa yakirasa, dago kansa yayi ahankali suka hada idanu da Baffa dake kallonsa anatse yace "zaka rike Amirah amana Marwan?" Lumshe idanu Marwan yayi saiya budesu ahankali, cikin murya mai dadi dakenan anytse ba garaje ciki yace "zan rike Ameenah amana Baffa namaka alkawari!"

Wlh wani sanyi Baffa yaji sai yaji ya yarda da yaron sai yayi murmushi yace "Masha Allah ina addu'a Allah ya albarkaci auren ku Ameen Ameen" Mami tadan kalli Marwan sai ta kalli Baffa tace "yaushe zamu iya zuwa daukan Amaryan mu" dan dariyan manya Baffa yayi yace "eh toh ga mai gidan nan Hajiya ai sai abinda yace" Marwan yasake sauke kansa dake kasa sosai cikeda kunya Baffa na kallonsa, Baffa yace "da so samune dai, Maryama zata tare gidan Mijin nata nan da sati biyu da yan kwanaki, to zanso ahada bikin ayisu idan Mijin nata ya yarda" Dasauri Mami tace "ai yama yarda muma kafin nan mun gama shiryawa gabaki daya" Abba yace "kwarai kam, Allah yakaimu lokacin" duk akace Ameen Ameen sai Baffa yatashi yace "to bari na koma" Abba jiyayi yanason Baffa sosai yace "muje na taka maka" tare suka fito suna zance na manya, harya rako Baffa wajen machine dinsa, Abba jiyayi yanason Baffa sosai saiya taba aljihunsa yaciro kudi duka dayake jikinsa wanda bundle na yan 100dollars ne yace ga wannan ayi tsaraba dasauri Baffa yace "ahhh bazamuyi hakaba Allah na amfana, nagode kwarai Allah yakara sauki damai jiki" ya buga machine nasa yayi gaba Abba yabisa da kallo sai yayi murmushi

Tunda yace Ammi bata tare da mutumin abu dayane yazo ransa Alhaji Bashiru babban abokinsa matarsa tarasu 10months kenan yanzu baiyi aure ba, yaga Ammi she's so gently and homely zaiso itada alhaji Bashiru suyi aure, yaransa uku duka maza duk sunyi aure, shi kadaine agida sai Chefs dinsa maza dake masa girki bari zaimai maganan yaga. EPISODE 4️⃣8️⃣

Komawa gida Baffa yayi wannan karan a falon Lami yasamesu gabaki daya, Amirah tayi lamo jikin Ammi tana danna wayan Ammi, yanda take bala'in son waya tanason game idan tagama game saita shiga danne danne babu inda bata sani awaya ba tafara danna wayan Ammi kona Miemie sai takusan karan da chajin ko ka amshi shine zaka tsira, doguwan rigane ajikinta na atampa red wani kalan sheki takeyi bana wasa ba, tana glowing ga kamshin datakeyi da turarata da akeyi, karbe wayan hannunta Ammi tayi tace "baki iya gaisuwa ba" ahankali ta tashi daga jikin Ammi takalli Baffa dake murmushi yana kallonsu murya yar karama tace "ina kwana" Baffa yace "Amirori yaya an tashi ince anyi kari dai"? Ammi tace "wannan tafi karaman Salma neman abinci da sassafiyan Allah" komawa jikin Ammi zatayi Ammi tace "jeki wajen Miemie tana daki" kin tashi tayi Ammi tace "maza nace" ahankali ta mike rikeda wayan Ammi tajuyo tana kallonta saita wuce tafita tashiga Dakinsu duk Ammi na kallonta kafin Ammi tajuyo takalli Baffa, dayayi murmushi na manya yace "Haleematu kinga dai bani kaunar halin Yusufa amman Allah yasani mijin daya aurama Amirah naga yaron kuma Allah ya dauramin kaunar sa da yarda dashi dan haka ni na yarda da auren nan dari bisa dari fatana Allah ya kyautata zamansu"

Wani kallon Baffa Ammi keyi, Baffa kuma ya gyadamata kai cikeda gamsuwa yace "I know duka abinda kike tunani, kina tunanin Amirah batai girma da wayan dazatai rayuwa inda babu ke ba, now the question is yan kwanakin datayi a asibiti ai baki wajen ko? And she was fine, infact kalli improve Ada Amirah bazata taba barinki taje wani daki ke kina wani daki daban ba" Lami tace "kwarai!" Baffa yace "ki kwantar da hankalinki kibita da addu'a karki rigima da mutumin chan Babansu ki barsa da halinsa, munyi concluding zasu tare rana daya da Miemie dan haka ki kama shirye shirye kinji" Baffa yadan sauke murya yasan yanda takeson yarinyar Amirah saidai in baka zauna da itaba wlh saika sota, ahankali yace "is time for Amirah to grow up a inda baki haka rayuwa yake, this is her next step na rayuwa, ki daure ki koyar da ita the little you can in this period, kibarma Allah komi, Allah na ganin komi Haleema, and Allah bazai baki kunya for all hakurin dakikayı ba, in sha Allah Dr Marwan will take care of Amirahn mu da kyau and zata warke tass tass kinji" gyadama Baffa kai tayi ahankali saita lumshe idanu saiga hawaye wlh wlh tana ma Amirah wani so da batason tarabu da ita ko kadan batason tarabu da baby girl dinta, Baffa yace "laaaaaa" Lami tai yar dariya tace "kukan tunanin rabuwa da yar diyarta take" Baffa yace "tun yanzu, yau naga Maman Amarya mai kuka" dan dariya sukayi, sai Ammi ta share fuskanta tass takalli Baffa da Lami tace "ragowan kudin dana rage zanja jari bari kawai muyi amfani dashi nama Amirah kayan daki ko" Baffa yace "nima zan kara miki daga miliyan daya ta wajena" dasauri Mami tace "ah'ah Baffa kabarshi" suka cigaba da hira.

Daga Bbaya Baffa yafice yaje kasuwa Ammi tawuce tashiga dakinsu Amirah na tare da Miemie tana kwance jikin Miemie suna kallo da wayan Ammi a YouTube dan Ammi nada data Miemie data dinta yakare amman anjima Umar zai samata, bama suji shigowan Ammi ba, Ammi tace "ahh yayi kyau sharan kenan ko Miemie" dasauri Miemie ta kalli Ammi Amirah ma haka saita taso daga jikin Miemie ahankali, Ammi tawuce bakin katifa ta zauna dasauri Amirah tazo wajenta Ammi zata mata magana kawai saita zauna ajikin Ammi tana kallon fuskanta sosai muryan nan chan ciki tace "Ammi" tsareta da idanu Ammi tayi tace "menene kika haumin jiki kaman mage"? Yanda Ammi taga tana kallon kwayan idanunta yasa tagane Amirah harta gane tai kuka kafin abin yashiga ranta ya zauna ya tada mata da hankali saitai sauri tace "gashi yafadamin ido, idanuna sunyi wani iri ne?" Gyadamata kai Amirah tayi itama Miemie na zuwa wajen dasaurin ta. EPISODE 4️⃣9️⃣

Cikeda hikima da dabara irin na Uwa Ammi tace "huramin idanun Amirah" Dasauri Amirah tadaura soft hannayenta akan fuskan Ammi saita hura mata iska a idanun, Ammi tai murmushi tace "iyye yammatana ta iya fa kinga gashin yafita Miemie, Miemie tai dariya, sai Ammi tasa hannunta takama na Miemie tazaunar da ita gefenta tace "zauna kiji" Zama Miemie tayi duk suka kalli Ammi, Ammi tai murmushi tace "mesa kika gayamin kinason Dr Marwan Amirah"? Wani kyalli idanun Amirah sukayi sabida Ammi tahanata maganan Dr Marwan tamata fada sosai ganin Ammi yau tamata tambayan akanshi wani sanyi taji saita kankame Ammi sosai Miemie tawani kwashe da dariya tace "Ammi wlh da gaske Amirah son Dr nan takeyi jibi yanda take farin ciki sabida kin tambayeta, ohh su Ya Amirah anga fine Dr"Ammi takalli Amirah yanda take murna tana wani blushing kyawawan hakoranta na nunawa tace "ina jinki fadamin" ahankali Ammi tai shiru tana kallon Ammi tana tuna duka abubuwan da Marwan yamata tace "Dr Marwan nama Amirah kirki kaman Ammi" Miemie tace "wooooohhh!" Ammi tai shiru harareta hakan yasa tai shiru Ammi ta kalli Miemie tace "mesa kikace haka"Safan kafanta tanunama Ammi ahankali yace "yasama Amirah takalmi da safa, yaba Amirah chocolate, da abinci mai dadi, yahana Amirah kuka, Dr shima Ammi na ne Ammi" Tunda Amirah ke maganganun Ammi ke kallonta batajin there'sa single soul in this world as innocent as Amirah ba, nobody can understand abinda Amirah tafadi inba a mother ba, in the moment when she was scared tai feeling alone ba Ammi ba Miemie gardawa sun dauketa mutum daya saved her with a kind hearted spirit yabata exact kulawa irin wanda Ammin ta ketaba sai for the first time sai Ammi taji zuciyanta ya natsu da auren it might be a good thing afterall, cike da hikama Ammi tace "na aura miki Dr Marwan" ahankali Amirah dake wasa da yan flowers na gaban rigan Ammi ta tsaya ta kalli Ammi dasauri, Miemie ma haka, wani tsare Ammi Amirah tai da idanu kaman tasan menene aure, Ammi tace "an daura auren ku jiya a masallaci karfe biyu sadakin ki na hannun Babanku, kema yanzu matar aure ce kaman Miemie rana daya za'a kaiku gidan mazajen ku" wani mamaki ne yakashe Miemie, wani kalan bugawa zuciyan Amirah keyi, ahankali tace "Mama Lami matan Baffa ne, Maman Baby Matan Daddy ne, Miemie Matan Ya Umar ne, Amirah Matan Dr Marwan ne?" Gyadamata kai Ammi tayi alamun eh, wani washe baki sai tawani kankame Ammi tahau kyalkyala dariya da karfi abinda basu tabaji Amirah tayi ba tawani kankame Ammi, Itama Miemie saitahau dariya tace "laaa Ammi wlh Ya Amirah batada kunya, wai dadi fa takeji an mata aure ko" Ammi kawai girgixa kai tayi irin na manya tana kallon yaran nata dake dariyan rashin hankali kawai tunani take yanda zata rabu dasu tai rayuwa ita kadai, dakewa tayi tace "ku tsaya ban gama magana daku ba zonan Amirah" Ammi tadagata daga jikinta wani murmushi takeyi sai Ammi taja kujera ta ijiye gabanta tace "zauna anan" zama tayi anatse, Ammi tace "kinason auren?" Dasauri ta gyadama Ammi kai, Ammi tace "kinsan me akeyi a aure"? Dasauri tace "zanci abinci nima na haifo katoton jariri" Miemie tawani kwashe da dariya Amirah ta kalleta sai itama ta kwashe da dariya dan she's extremely happy, Ammi ta kwadama Miemie duka tace "tashi ki fita wuce jeki daura sanwa mara kunya" tashi Miemie tayi takalli Amirah tace "Amaryan Dr Marwan" Amirah tasake washe baki.

Ammi na kallon ikon Allah saida Miemie tafita Ammi tace "ki natsu ko kinaso raina ya bacı?" Dasauri ta girgizama Ammi kai tana wani kalan cute smile dake melting zuciyan mutum, Ammi tace "anayin abubuwa da yawa agidan miji, dagayau zan fara koya miki girki, da yanda ake gyara gida kinji" gyadama Ammi kai tayi tace "Ammi anjima mijina zaizo?" Tsayawa Ammi tayi turus tana jin nauyin yanda Amirah tace "mijina" saita harareta tace "ban sani ba" Ammi tayi shiru tace "kin tuna wankan tsarki dana koyamiki kinayi duk idan kin gama period dinki?" Dasauri ta gyadama Ammi kai, magana Ammi zatayi saita kasa maganan yamata nauyi ita zata koyama Amirah bangaren nan? Saita kasa tace "kome yafaru tsakaninki da mijinki karki fadama kowa kinji, sirri ne" gyadama Ammi kai tayi, Ammi tace "muje kiga yanda Miemie ke daura abinci a wuta". ***

Tunda suka koma gida yasami all yayyinsa baimason surutun su dan harsun fara ango ango ya hade fuska yawuce dakinsa, bayi ya shiga yayi wanka da kyau yafito pajamas ya saka saiya fito yazo ya kwanta akan gado yayi shiru saiya lumshe idanu 3weeks is so long yafadi murya chan kasa saiya bude idanu dasauri maisa yafadi maganan? Deep down jiyake kaman yabude idanu yaga Amirah, da akace an daura musu aure dudda he's trying to fight d feeling saiyaji sonta yawani karu yakara doubling a zuciyansa. EPISODE 5️⃣0️⃣

2WEEKS! yau duka duka saura kwana 6 tarewa, bangaren Umar yagama gidansa tsaf dan ana maganan satin nan za'aje ayi jere Ammi babu abinda batama Miemie ba masu kyau na gata kuma, ta zage gyara yaranta take ba kama hannun yaro, ga mai gyara su yan Maiduguri, kyan da Amirah da Miemie sukayi yabaci, Amirah jikinta kaman glass, cikinta ciwo yake sabida kayan matan da ake bata kaman yasoma ma jikinta yawa da kanta Ammi tafara ragewa cus taga kaman Amirah tamafi Miemie sensitive jiki and abu namata aiki ajiki sosai.

Ammi babu abinda bata koya mata ba, gyaran gida, gyaran daki, girki, da yanda ake handling su gas, Ammi tayi iya kokarinta takoya mata intimacy takasa wani nauyi takeji, tagayama Lami tadan koya mata wani abu amman ina daga ita har Lami abu daya suke, sun kasa, gawani kamshi da Amirah keyi an gasa an huda jikinta da turaren shuwa Arab na Maiduguri, Amirah kullum saitayi maganan Dr Yaushe zaiso amman shiru babu wanda yasani, shirye shirye suke ba kama hannun yara, Umar yakawo ma Miemie dubu dari uku na dinkunan ta an kawo akwatinta yau wlh wlh yayi kokari, gobe da safe za'aje mata jere zai aiko da mota.

Bangaren su Mami suma shirye shirye suke bana wasa ba Abba ya ijiye kudi na ban mamaki hat chanza penti na gidan akeyi suma biki suke shiryawa meanwhile Mami tagama hada akwatin Amirah, Abba da kansa yakira su interior design ana sa komi agidan dayaba Marwan is like 2 houses tsakanin su, shida Mami suka yanke shawaran sAbida condition na Amirah plus Marwan na zuwa aiki gwara suma kusa dasu, kiri kiri Marwan yaki participating in anything, dudda azuciyansa yafi kowa duba calendar da date yawani irin koşa but kagansa he looks so uninterested saisa Abba ya tsaya tsayin daka kan lamarin gidan da interiors din.

Yau wuraren 9 manya manyan kawayen Mami guda biyu sukazo sai kannenta su Yaya Ammah aka tafi kai akwatina Abba yayi magana da Baffa so ansan da zuwansu an basu address. Ammi tasa Miemie ta tafi da Amirah gidan makotansu dasuke shiri da Lami sosai, Ammi tasa wata lace mai kyau tayafa mayafi mai kyau, wlh Ammi is a very very beautiful woman saitaci gayu ka kalleta saika kara kallonta, Sunyi girki, an soya kaji dan Baffa na kiwo, akai fankasau da waina, da alale na gwangwani dasu cincin da danbun nama makota duk sun shigo, wuraren 2 suka iso akai parking, su Ya Ammah suka shigo da farin cikinsu ana ayiririiii suna ina Maman Yarmu Lami na washe baki tanuna Ammi dake murmushi cikeda natsuwa wani irin rungume Ammi sukayi har Ammi saida tafarajin kunya, nan da nan aka shigo da akwatunan, anan tsakar gıda aka bubbude ana ayiriri, kafin afara kawo abinci, yanda sukaci abinci ko saida Ammi tai mamaki alalen tasss na kare waina da sinasir har take away sukayi suna tambayan waya dafa Lami tace "Maman diyarku ta dafa" sun dade sai wajajen four suka tafi suka basu tukuicin 200k suka karba suna godiya sosai duk saida sukai take away na abubuwan da aka musu suka tafi suja murna yau sai Ammi takarajin ta natsu ganin sunada kirki Amirah ta bazata wahala ba.

Marwan na sama yaji sun dawo anata hira ana bada labarin abinci babu wanda yayi maganan Amirah har wani gyara kunne yake da laptop jikinsa amman babu wanda yayi maganan Amirah, Farida ne tace "Yaya bakuga matan Ya Marwan dinba?" Wani ijiyan zuciya Marwan yasauke dasauri jin finally an tambayi Amirah, dariya Ya Fadila tayi tace "ai ba'a ganin Amarya sai rannan biki" wani irin Marwan yaji sai kawai yatashi yawuce yashiga dakinsa karaf a idanun Mami tai wani murmushi batace komiba.

Around 10 na dare Mami tai knocking gaban kofansa ahankali yace "come in" bude kofa tayi ta shiga tana kallonsa yana zaune gaban system yana aiki, Mami ta maida kofan tarufe tace "an baka 2months wajen aiki fa Marwan why are you still working"? Batare daya kalli Mami ba yace "just small abu nakeyi?" Mami tace "okay" tana wycewa closet nasa tace "wai bazaka hada kayanka ka kai gidan ku ba, kamaje ka duba gidan da abubuwan da akayi aciki?" Shiru yayi baice komiba Mami tafito saitazo wajen ta tsaya akansa tace "Allah idan baka tattara kayan nan ba nizam tattara nabada akai maka gidanka, you have just 5more days agidana kavar gidana kenan" kallon Mami yayi ahankali, Mami ta ballamai harara tace "nai magana da telenka jibi zai kawo dinkunan ka Abban ku duk yabasa" sauke kansa kasa yayi, Mami tai murmushi kawai tace "yaushe zakaje kaga matarka kabata kudin kitso da lalle da sauran shirye shiryen Amarya eh?" Kasa dago kansa yayi, murya chan kasa yace "Mami stopppp!" Baki Mami takama tace "ni kakejin kunya yau ahh lallai ango da kunya, gobe ka shirya kaje ka kaimata kudin shiryawa ko na cicci maka mutunci I will text you address na gidan"Mami tai maganan tana hanyan kofa tace "kuma go get hair cut kayı gyara gyaran ango" this time rufe fuskansa yayi duka Mami ta kwashe da dariya tabude kofa tafita daga dakinsa. He was smiling saikuma ya dakata yana mamakin ina Saleem yayi? He calls him everyday he's fine yana magana dashi yama gayamasa he's married yayi yayi yagaya masa ina yake yaki gayamasa.

Kasa zuwa gidan Marwan yayi kuma bakomi ke hanasa ba sai kunya dawani kalan jin nauyin Ammi baisan tayaya zai kalli Ammi ba, he feels like yamata laifi tundaga kan bada address da contact na gidansu da number Daddy, is as if he took advantage na privileged information din dayake dashi na patients so he feels he wronged Ammi sosai.

Yana fitowa daga masallaci daga Magrib yana sanye da jumper na milk yadi mai kyau yana kamshi ga glasses idanunsa yaga Abba tsaye gaban gudansu ga mota agaban gidan, zai gaida Abba Abba yamika masa car key yace "maza tafi kaga Matarka! Mami tacemin kaki zuwa, akwai kudi a motan jeka bata kudin lalle gobe bikinku inba hakaba zanyi fushi daki karbi makullin motan" ahankali yasa hannu ya amsa kansa akasa, yashiga motan ahankali yaciro wayansa zuwa address da Mami tabasa zuwa anguwansu Amirah gabansa sai faduwa yake, yaja yana tuki ahankali, sai Chan yakara gudu wlh he can't wait to see her kusan almost 4weeks bai ganta ba yanabin map harya shigo layin sai yayi parking a kofar gidan gabansa na bugawa kadan kadan yarasa mezaiyi, he's feeling nervous and anxious kaman zaiga wata sarauniyan duniya, baisan ma yaya zaiyi ba, wayansa yadauka ahankali yarasa wanda zai kira saiya kira Ya Fadila wacce yakebi kira daya ta daga tace "ya akayi Ango Ango" hade fuska yayi yace "okay bye" dasauri tace "yakuri Ang… au yakuri Doc" dan shiru yayi sai chan yace "I'm in front of their house yazanyi?" Dasauri tace "wani house? Ban gane maganan ba" dan jimm Marwan yayi sai murya chan kasa yace "my wife's….house" yarage murya sosai haba mezaiji sai shewa na muryan duka yayyinsa katse wayan yayi yanaji kaman ya nutse kasa, Mustapha yagani yafito daga gidan somehow duk suna yanayi they're all light skin horn yamasa tareda bude motan yafito dasauri Mustapa yazo wajen yana hada idanu da Marwan yamai wani kwarjini dasauri yace "ina yini" anatse Marwan yace "lafiya lau, please kashiga kace Marwan yazo wajen Ammi" zaro idanu Mustapa yayi yace "laaa kaine daman Ya Marwan Mijin Amirah! Dr" Mustapa yakara basa hannu yana kallonsa kamna zai cinyesa damn! Sai yawani murmushi Marwan ma haka Mustapa yajuya da gudu yayi cikin gida duk suna tsakar gida, Ya Rabbi anma Amirah lalle mai bala'in kyau, yanda Mustapa yashigo da gudu yana kwalama Ammi kira, Ammi, Ammi yasa kowa yajuyo harda Amirah dake cin abincin, Lami tace "kai lafiya?" Wani tsalle yayi yace "Ammi Mijin Amirah na waje Yaya Marwan wai yazo wajen ki!" Wani zabura Amirah tayi ta kwasa da gudu Ammi na kwala mata kira, ko kalli babu akan nan balle slipas, tace "ke! Amirah! Amirah!" Amman ina ta falle ta tsere da gudu tai zauren su!!!😂😂😂 EPISODE 5️⃣1️⃣

Gidan ba wani babban gida bane, daga nan kofar gidan da Marwan yake tsaye jikin mota yaji yanda Ammi ta kwalama Amirah kira, sai kuma yaji sahu da alamun gudu, gently yadaga kafansa yayi one step closer to kofar gidan, kirjinsa na bugawa yanajin wani kotsawa na ganinta kaman yayi shekara bai gantaba, just 3weeks zuwa 4weeks dinnan dabai gantaba but it feels like forever, daidai Amirah ta bullo daga zauren, wani kamshi da tunda yake arayuwansa baitabajin kalan kamshi dayamai dadi haka ba, kafin ita Amirah ma ta iso yay maza yataho dab gaban kofan cus yasan fitowa zatayi ahaka ba hula, ba takalmi, ya tsaya chak yazuba hannu a aljihun wandonsa yana kallonta, kirjin Amirah wani kara bugawa yake dum, dum, dum, ganinsa tsaye yazuba mata idanu cikin wani farin glasses din nasa, tanajin kamshin turarensa datai kewa kawai saitaji kaman ma bata gudu ayanda takeso tayi dan she feels like the little distance dayarage from inda take takai inda yake feels like forever, kara gudu tayi Marwan yawani lumshe idanu yabude su asanyaye yana sauke ijiyan zuciya bakinsa naso ya furta becareful karta fadi amman yakasa zuwa gabansa Amirah tayi saitaci birki tana kallonsa kirjinta na bugawa tana wani kalan numfashi irin na wayanda sukai game na racing dinnan, takai hannunta tasa abaki ahankali tana tsoro karya sake hanata rungumesa yanda yayi a hospital amman kawai sai jikinta yahau rawa, tana feeling wani mugun urge na hugging nasa, jikinta yayi wani karkarwa, kawai runtse idanunta tayi taciro hannunta daga baki batai wata wata ba kawai tai wani kalan hugging nasa tana daga feets nata sama sabida takai tsayin wuyansa dan Marwan nada tsayi bata wani kai ba amman saita kankamesa ta kwantar da kanta akirjinsa ahankali takai hannayenta duka biyun bayansa ta kulle ta kankamesa tana kara kankamesa kaman zata fasa jikinsa tashige ciki tana sauke ijiyan zuciya fast fast na gudu.

Readers Also Read