Kenza eBookz

Baccin so complete by m shakur - Chapter 21

Baccin so complete by m shakur - Chapter 21

Baccin so complete by m shakur Chapter 21: Baccin so complete by m shakur Chapter 21. Wani kalan bugawa kirjin Marwan keyi kaman zai fito, no one has ever…

4,207 words

Wani kalan bugawa kirjin Marwan keyi kaman zai fito, no one has ever hugged him like this irin real intentional hug dake nuna mutum yayi kewanka, ga kamshin datakeyi gabaki dayanta da wanda gashinta keyi shima yana fizgansa, gashi shifa yana tsaye ne gaban kofan zauren yana daga waje ita tana daga ciki ga jama'a and anyone daga gida ayanda ake kiranta dinnan zai iya biyota aka gansu ahaka fa, da kyar ya tattaro duka karfinsa dawani kalan murya da yaune rana na farko da ita kanta Amirah kejin muryan yace "cikani!" Juya kanta Amirah tayi a kirjinsa alamun no, ta daga takai hannunta tadaura saman kan inda nipples dinsa cikin that baby voice yar karama tace "ciwonka ya warke?" Ya Rabbil Alameen wani abu Marwan yaji tundaga kafansa zuwa kansa baisan sanda ya gyara muryansa zuwa very strict ba yace "fitan mini daga jiki!" Ahankali Amirah tafito daga jikinsa dan idan yamata tsawa ko ya maida muryansa so strick tsoronsa da shakkan sa take saitakai hannayenta biyu tasa abaki tasauke kanta kasa tadan turo baki, tundaga kan kafafunta dasuka sha kunshi ja da baki zuwa hannunta dake baki dasuka sha lalle yabi da kallo, yakalli kitson da akamata yaji wani abu a wuyansa, da haka zata fito har waje agama ganeta, strictly yace "ina hulanki?" Hannunta tadaga takai saman kanta tai wani kwaba kwaba da baki kaman zatai kuka, ashagwaba tace "zafi yakemin, Amirah tayi kuka da ana mata kitso" lumshe idanu da sauri Marwan yayi saiya dauke kai cus Amirah na neman halakasa, murya ciki ciki yace "go back inside" kallonsa tayi shirin fashewmai da kuka take strictly yace "kikamin kuka ranki zai baci anan" turomai baki tayi tajuya ahankali tawuce yabi bayanta da kallo dake juyawa zuwa kitson da aka mata dasuka zubo sosai, sai alokacin Mustapa yafito anatse yace "ance ka shigo" gyadama Mustapa kai Marwan yayi saiya fara tafiya ya shigao gidan, ko'ina looks extremely neat, har falo Mustapa yakaisa falon na kamshin turaren wuta Marwan yazauna.

Amirah dake dakinsu Ammi na mata fada tana yafa mata mayafi cikin yar karaman muryan nan tace "Ammi ni zan tafi wajen Ya Marwan" cikeda fada Ammi tace "zan makeki fa Amirah wannan wani kalan abune" Miemie dake tsaye tace "ke baki iya jan ajiba"? Strictly Ammi tace "zauna anan da Miemie bari naje muka gama magana sai kije" juyawa Amirah tayi da gudu saita wani fada jikin Miemie ta kifa kanta akirjin Miemie tawani fashe da kuka mai bala'in ciwo, gani take Ammi nahana ta ganin Dr Marwan dinta, turus Ammi tayi ta tsaya tana kallon ikon Allah ganin kalan rigiman da Amirah keyi akan Marwan, Ammi kawai tajuya aranta tana zakici kankyanki nan gaba saikin dinga neman inda zaki gudu kije, anutse tai sallama tareda daga labule ta shiga dakin da Marwan ke ciki ganin Ammi ce tashigo dagudu Marwan yawani zame daga kujeran yazauna akasa, kansa akasa, murya chan kasa ya amsa sallaman Ammi, wucewa Ammi tayi tasami waje kan kujera ta zauna, cikeda Kamala tace "tashi ka zauna Marwan" girgizama Ammi kai yayi alamun a'a kansa akasa still murya chan kasa yace "ina yini Ammi" wani irin kunyan Ammi yakeji da bazai iya hada idanu da itaba, he feels he wronged Ammi with abinda yayi, anatse Ammi tace "lafiya kalau ya wajen su Umman ka"? Kansa akasa still yace "suna lafiya sunce agaidaku" Ammi tace "madallah muna amsawa" daganan bata kara magana ba dakin kowa yayi shiru, sunkai wajen good two minutes ahaka sai Ammi ta mike tace "bari naje" tai wajen kofa daidai tamika hannu tadaga labulen zata fice asanyaye Marwan yace "I am sorry Ammi" yadanyi shiru kansa akasa sai chan yace "dan Allah kiyakuri" juyo da kanta Ammi tayi ta kallesa yanda kansa ke kasa, calmly tace "bakomi, komi yariga yawuce, Allah ya albarkaci auren ku" Ammi na maganan tawuce tafita tashiga dakinsu taga daga Lami har Miemie lallashin Amirah dake kuka ba wasa suke, har wani ijiyan zuciyan kuka take saukewa, Ammi tamata wani mugun kallo tace "tashi to kitaf….." bata karasa maganan ba Amirah harta mike dagudu tayi kofa duk suka bita da kallo mayafin ma bata saka ba tadaga labule kawai tafice daga dakin abinta. EPISODE 5️⃣2️⃣

Lami ta kwashe da dariya tana kallon Ammi datai turus kawai tabi Amirah da kallon mamaki, Miemie na murmushi kasa kasa, Lami tace "yaran zamani ba kunya ko kadan, daga gobe ne ai mun kaita gidansa muhata da wannan darun datake mana"Ammi batace komiba kawai tasami waje ta zauna tadauki charbi abinta tanaja.

Marwan na zaune a inda Ammi tabarsa Miemie tashigo dasauri ba kallabi still fuskanta kaman ta wanke da ruwa sabida kuka, Marwan yadago kansa ahankali ya tsareta da mayun idanunsa kirjinsa nawani kalan bugawa, tana tsaye gefen kofa batare data karaso wajen ba, she wants to hug him but tasan yahanata saisa batazo ba tawani turo baki ta lankwashe wuya ashagwabe kaman baby tana kuka still, Marwan ya tsareta da idanu ko kyaftawa bayayi, daga inda yake zaune yanajin kamshin datakeyi dake fizgansa sosai, bakinsa yabude ahankali yace "come" kaman jira Amirah take dawani irin sauri tazo gabansa kirjinta na bugawa taduka zata zauna agabansa idanun Marwan suka sauka kan gaban boobs nata sabida riganta ya zazzago bawai yagansu full bane but yaga saman dasuke nan acike tammmm farare tasss, ya lumshe idanunsa dasauri, he's feeling kaman ya tsaga kirjinsa yasata aciki yahuta kawai, zama Amirah tayi agabansa dab dashi tana kara turo baki hawaye na zubowa bude idanunsa Marwan yayi ya tsareta da idanu kaman yanda take kallonsa asanyaye itama da idanunta dake kyalli na tears, cikin yar karaman murya yace "yaushe kika dawo rigimammiya"? Makemai kafada tayi another new hawaye na zubowa, duk yanda Marwan yaso yadaure yakasa hannunsa yakai ahankali yadaura saman fuskanta, wani sanyi Amirah taji da tafiyan abubuwa a cikinta da batasan sanda tawani sauke ijiyan zuciya ba da saida iskan yasauka akan fuskansa, yatsan hannunsa yakai ya sharce hawaye kaman yana magana da baby yace "why are you crying Little Meenah?" Wani yammmm Amirah taji sabida yanda yakirata da batasan sanda takai hannunta takama hannunsa dake kan fuskanta ba tarike tana sauke ajiyan zuciya da sauri da sauri, wani irin abu takeji game da Marwan that's unexplainable but she knows kaman ta cinyesa, kota hadiyesa, kota koma jikinsa gabaki daya takeji, wani yarrrr Marwan yaji jin yanda Amirah takama hannu sa tarike hannunta bala'in taushi gashi duk yayi zufa lallen da aka mata ya rabbi hannunta kaman ba hannun mutum ba tsabagen kyau, kawo fuskansa dab da nata yayi yana kallon kwayan idanunta dake kyalli sosai yace "rigiman me kikeyi" ahankali like a little baby ke magana tace "Ammiiiiiiiii" murmushi kadan Marwan yayi Amirah tawani tsaresa da idanu ya rabbi murmushi yamai kyau sosai tana kallon glasses na idanunsa, shikuma yasauke idanunsa kan kitson da aka mata baisan sunan style dinba but baitaba ganin kitso mai kyau in his life like this one ba, tunda yake arayuwansa baitaba ganin kitso dayamai kyau like this ba sauke hanunsa yayi daga fuskanta ya ijiye kan fatan wuyanta, wani irin ijiyan zuciya Amirah tayi dan she felt cold har a bargon kashin dake jikinta, tsayawa yayi yanaso yacire hannun nasa daga wuyanta but yakasa, her neck is so soft, is so warm and very smooth, gently yashiga shafa wuyanta da hannunsa tsigan jikin Amirah yawani tashi dahar saida yagani yakai hannunsa yakamo gashinta dasuka azube so silky gashin bakin kirin tana wani kamshi, ahankali yakalli kwayan idanunta kaman yanda take kallonsa yace "kitson nan yayi kyau"wani irin dadi Amirah taji kawai bazato tashige jikinsa tai hugging nasa tana manna fuskanta a kirjinsa, tanason kamshin dayake sosai bana wasaba, bugawa kirjinsa keyi nonstop kallon kofan dakin yayi da labulene kawai he will feel wani iri idan wani yazo yagansu ahaka, murya chan kasa Marwan yace "bana hanaki ba" dago kanta tayi daga kirjinsa jikinta duk yamata wani iri, hannunsa yakai yadanja hancinta yace "ke mage ce?" Washemai Baki yayi saiya dagata daga jikinsa, mikewa yayi dasauri Amirah tamike itama tana shirin kuka, saiya ciro kudade daga aljihunsa dayawa ya ijiye akan kujera yace "jeki cema Ammi zan tafi" hannunta tasa abaki saita wuce tafara tafiya ahankali tafita, ijiyan zuciya Marwan yasauke saiya fito daga dakin EPISODE 5️⃣3️⃣

Daga bakin kofan dakinsu Amirah ta tsaya tace "Ammi" tajuyo tana kallon Marwan daya fito daga dakin idanunta yaciko da hawaye dan bataso yatafi, Miemie tafara fitowa akunyace tace "Ya Marwan ina yini"? Anatse Marwan yace "how are you Maryam"? He talks to her like an elder brother, ahankali tace "lafiya lau" Lami tafito tareda Ammi, Marwan yasauke kansa kasa dasauri yace "saida safe Ammi" Ammi tace "agida mutan gida" gyadama Ammi kai yayi yay hanyar zaure zai fice, kawai Amirah tawani rushe da kuka tana tsaye daga wajen kofan dakinsu datake tana kallonsa, chak Marwan ya tsaya batare daya juyoba, Ammi tadan kallesa sai kawai tawuce takoma ciki, Lami da Miemie suka bita suma cikin dakin, dan juyowa Marwan yayi suka hada idanu da Amirah dake kuka sosai, da idanu yamata alamun tazo, dasauri ta taho wajensa ta tsaya dab dashi tana kuka harda shesheka, ahankali murya chan kasa Marwan yace "why are you crying?" da yar muryan nan nata dake fita da kyar cikin kuka yar karaman gaske sounding like a baby tace "zan bikaaaa" hannunsa yakai yadaura kan fuskanta ya sharce hawayen ganin hawayenta kaman river basu da wahalan zubowa kuma nan da nan sun wanke mata fuska tass, murya kasa kasa ta yanda babu wanda zaijisu yace "we will be together tomorrow okay, stop crying, daga gobe i will never leave your side, I have to go yanzu kinji" yayi maganan ataushashe da sigan lallashi, gyadamai kai tayi tana sauke ijiyan zuciya ahankali na kuka tana kallonsa, Marwan yayi shiru yana kallonta zuciyansa nabugawa sabida yanda yakejin sonta, kaman gobe tayi yanzu yatafi da ita kawai, ahankali ya kawo bakinsa wajen goshinta sai gently ya manna soft lips nasa kan goshinta ya sakin mata wata yar karaman light kiss wani yirrrrrrr Amirah taji da saida shi kansa yagani, dan komawa baya yayi anatse yace "go to your room now" gyadamai kai tayi saita juya ahankali tana tafiya tana juyowa tana kallonsa shima yana tsaye bai wuceba har saida takai dakinsu tashiga sannan yajuya yafice yashiga mota yaja yabar anguwan.

Komawa dakin Amirah tayi tana kuka ahankali Ammi ko kallonta batayiba ahankali tazo inda Ammi take tazauna, still Ammi bata kalleta bata kalleta ba, gently ta kwanto jikin Ammi, Ammi ta kalleta dasauri Amirah ta runtse idanunta bataso Ammi tamata fada takara kankame Ammi tai lamooo, ahaka bacci yayi awon gaba da ita Ammi sai kallon yaran take dan itama Miemie tayi bacci, she feels kaman kar gobe tayi tarabu dasu.

Ahankali Ammi ta kwantar da ita agadon tamike tafito alwala tadauro kawai tadawo daki ta shimfida dadduma tafara salla wanda yaranta kawai takema addu'a Allah ya albarkaci aurensu, yabasu zaman lpy da mazajensu, Allah yaba Amirah lafiya completely har saida aka kira sallan asuba sannan ta tashi ta tada Miemie da Amira dan ayi salla Lami ma ta tashi makota har an fara shigowa daura abincin biki.

Gabaki dayan rannan shima Marwan bai runtsa ba yakosa gobe tayi akawomai matarsa, yayinsa kowa na gidan anyi lalle da sauransu, har lokacin no one knows whereabouts na Saleem. Daga masallacin sallan asuba Marwan yafice abinsa dan baiso ma agansa atasahi gaba. **

Wuraren 11 aka gama yima amare makeup wanda da kyar Amirah ta yarda dan she was feeling uncomfortable, makeup is something da bata taba yiba, Ya Rabbi ita karan kanta Ammi saida takara kallon Amirah cus yaune rana na farko datake ganin Amirah tazaman mata yar budurwa a ido dan she always sees Amirahnta as a baby, Amirah tayi kyau cikin black and gold lace data saka ana gama makeup din tazo wajen Ammi adaki ta zauna taboye abayan Ammi, batason yanda mutane keta kallonta da yanda taga mutane dayawa agidan acike ana hayaniya dudda babu kida ko DJ but she doesn't like it. Kallonta Ammi tayi tace "tashi muje" ahankali ta tashi Ammi tariketa, saita kaita dakin Baffa wanda babu kowa ciki tazuba mata abinci karba tayi tafara ci ahankali, Ammi na kallonta taci sosai sannan ta kalli Ammi tace "Ammi anjima zamu tafi gidan Ya Marwan?" Gydamata kai Ammi tayi, murmushi tayi tacigaba da cin abincin sosai taci tana gamawa sai bacci, gyaramata kwanciya Ammi tayi tafito daga dakin tana kallon Miemie dake tareda kawayenta Miemie tayi kyau sosai, tadade tana bacci sai bayan asir ta farka Miemie tagani kusada ita tana kuka tana goge hawaye tashi Amirah tayi zaune ta tsareta da idanu saita matso ahankali tazo kusada ita murya chan kasa like a baby tace "menene?" Cikin kuka Miemie tace "Amirah banson narabu da Ammi dake, banso" saita rungume Amirah tana kukan wani iri Amirah tashigaji sai hawaye yashiga cikowa a idanunta, ahankali tadago Miemie saitakai hannunta kan fuskanta ta girgiza mata kai alamun tadena kuka, Miemie tadade tana kallon Amirah saita gyadamata kai, daidai Ammi tabude dakin tashigo takalli Miemie da idanunta sukai jajir anatse tace "kuzo ku shirya anzo tafiya daku" daidai nan Lami na shigowa dakin tace "ina suke muje muje ga motoci sunyi layi a waje ana magrib zaku wuce, muje muje" tai wajen Miemie tadagata suka fice, Ammi takalli Amirah tace "zomuje" tasowa Amirah tayi saitazo dab da Ammi tana kallon fuskan Ammi sosai cikin yar karaman muryan nan tace "Ammi ai tare zamuje gidan Yaya Marwan ko"? Tsareta da idanu Ammi tayi saita gyadamata kai kawai, murmushi Amirah tayi ta rungume Ammi suka fito tare tana mammannewa jikin Ammi tana boye fuskanta wanka Ammi takaita tayi dawani ruwan turare sannan tafito da ita sukaje daki Ammi da kanta tashiga shiryata cikin wani lafaya black and red tasata tai salla Ammi bata mata wani kwalliya ba tasa mata kwalli saita zauna gaban Amirah tana kallonta hawaye Ammi taji zasu zubo daga idanunta dasauri tadauke kai dakin aka bude dasauri Amirah ta tashi taboye bayan Ammi tai lamo kaman yar yarinya, Lami dasauran manyan matan wajen suka shigo da Miemie dake kuka sosai an lullubeta sukace "ammm Ammi ga Miemie za'a tafi da ita" tsareta da idanu Ammi tayi saita lumshe idanu bata taba sanin this is how a mother feels when she's saying goodbye to her children ba sai yau, she's feeling kaman ta taya Miemie suyita kuka tare sabida yanda takeji amman saita dake anatse tace "Maryama I know daidai gwargwado nabaki tarbiya mai kyau, ke yarinya ce mai hankali da bazaki taba bani kunya ba, baki taba kuntata min ko batamin raiba, I pray Allah yabaki farin ciki irin wanda baki taba tunanin zaki samu ba gidan mijinki Allah ya albarkaci aurenku, go start your new life kinji My Babygirl Miemie" rungume Ammi Maryam tayi tama kasa magana sai kuka da kyar tace "Ammi banso narabu dake" dariya akahau yi adakin itama Ammi tai murmushi tace "ai duk diya mace saita rabu da iyayenta mumanan duk hakane maza dena kukan nan" Ammi ta dagota, bakin mayafinta Ammi takama ta share mata fuskan tasss saita manna mata kiss a goshi tace "go to your home Maryam" wasu sababbin hawaye ne suka shiga zubo mata. EPISODE 5️⃣4️⃣

Lami tace "muje toh" ahankali Miemie ta tashi saita zagayo bayan Ammi tai takalli Amirah dataga idanunta sun ciko da hawaye duk tayi wani irin kaman tasoma gane abin is getting real, ahankali Miemie tace "kin haddace number na dana Ya Umar ko?" Gyadamata kai Amirah tayi ahankali, Miemie tace "toki kirani idan kika sami waya kinji bazan iya rayuwa babu ke ba Ya Amirah, you're my best Sister kuma in sha Allah zaki warke Ya Marwan zai kula dake kinji" gyadamata kai Amirah tayi tana kallon yanda Miemie ke kuka saita rungume Miemie ahankali tace "kuka bari" tadagota tana share mata fuska murmushi Miemie tayi tace "tom nadena, Bye Ya Amirah na" Lami tazo takama Miemie suka fita da ita daga dakin Amirah tabisu da kallo sai kawai tafado jikin Ammi tana kuka sukaje waje.

Ammi tariga tagayama Lami itace zatabi Amirah cus Amirah bata yarda da kowa hakan yasa sai Harira kanwar Lami itane jagoran kai Miemie gidanta, saida Lami ta tabbatar an shiga mota sannan aka tafi yarage saura motocin su Tawagan Marwan, friends nasa guda biyu that are Drs yasanar sai Abba yabada motoci da drivers guda uku, dawowa dakin Lami tayi da kawayen Ammi dakuma makota har lokacin Amirah kuka take, da idanu Lami tama Ammi alamun it's time, dagota Ammi tayi tace "dena kukan yanzu tashi kibi Mama Lami kutafi gidan Mijinki Marwan anjima kadan ni sainazo idan na sallami baki na" makema Ammi kafada tayi cikeda rigima alamun a'a, Ammi tadan hada fuska tace "kinason nayi fushi dake"? Ahankali ta girgizama Ammi kai, Ammi tace "yauwa yarinyar kirki tashi to kuje, muje nasaki a mota da kaina" kasa ma tashi tayi daga jikin Ammi da kanta Ammi tadagata daga jikinta saita gyaramata mayafin saita bata wani flat shoe black na Gucci ya Allah kafafunta sunyi kyau a takalmin tasaka Ammi tai jimmm tana kallonta itama Amirah haka sai kawai Ammi ta rungumeta Amirah ta kankame Ammi kaman jira take tafashe da kuka, Lami ta girgizama Ammi kai alamun kartai kuka da kyar Ammi ta daure saita dago tace "ke yarinya ne kike kuka haka, wuce muje" Ammi takama hannunta da kanta Ammi tafitar da ita har waje jama'a na binsu abaya wata roll Royce Dr Hassan yabude yace "motan Amarya ne wannan" Ammi da kanta tasa Amirah aciki Lami tashiga ta dayan side din, su biyu kawai zasu zauna a motan sabida yanzu tana ganin jama'a saita rikice, Ammi ta dake tai murmushi tana kallon Amirah data rirriketa that looks so scared tace "Ammi mutafi" Ammi tace "eh bari kutafi zan taho uhn yarinyana tayi kyau, Lami bari nai sauri ganinan zuwa" Lami tace "yauwa kiyi sauri Maman Amirah"Ammi tace "to cikani sabida nai sauri na biyoku" ahankali tasaki Ammi tana kallon fuskan Ammi sosai, Ammi tamata murmushi tace "good girl bari naje toh da sauri" Ammi tai maza tamaida kofan tarufe tawuce zaure Amirah tabuta da kallo aka kunna mita akaja Ammi na labe azaure tana kallon ana tafiya da Amirah ta gidan miji kawai sai Ammi tafashe da kuka duk yanda zatai bayani bazata iya ba, but she's feeling too many things at a time, her only two daughters leaving her in the same day to start a new life, cikin those 2 imagine the sick one, that's helpless, weak, have zero idea how the world is itama ta tafi gidan miji, Amirah should be by her side, she should be protecting her not ta aurar da ita me Amirah tasani what if Marwan is not a good man ya cutar mata da yarinya eh? Babu abinda Ammi bataji kaman tafita tace adawo mata da yarta tafasa aurar da ita she's feeling so lonely Wayyoo Allah na, idanun Ammi har saida suka kumbura sabida kuka sannan ta lallaba ta tashi tashiga ciki.

"He's calling again" Dr Hassan dake tuka motan yafadi yana daukan wayan, "Hey Dr ka kirani yafi sau miliyan yau, yes mun daukota she's here we are on our way" dan juyowa yayi saiya ba Lami wayan yace "mijinta wants to talk to her" Lami murmushi tayi ta karbi wayan saitace "Amirah ga Mijin naki" tabata wayan karban wayan Amirah tayi garin karba tasa a speaker, murya chan kasa Marwan yace "Ameenah….!" Kaman yabude abinda ke rike mata kuka kawai saita fashe da kuka sosai harda wani rerawa Marwan yayi shiruuuu yana sauraronta chan saiyace "so kike ki kasheni!" Dan zaro idanu Lami tayi dasauri ta juyarda kai Dr Hassan yayi murmushi, Amirah da baruwanta da wayan na speaker ta girgizamai kai alamun noo, asanyaye cikin lallashi da tsantsan kauna yace "stop crying kinji" gyadamai kai tayi asanyaye yace "wat do you want me to buy for you"? Ahankali ashagwabe tace "wayaaaa" ahankali yace "mezakiyi da waya?" "Miemie" murya chan kasa yace "okay zan sayama matana waya wanda yafi na kowa kyau dazata dinga kiran Miemie, da Ammi, da Ya Mustapa da Baffa aciki ko"? Shiru tayi tana sauraronsa hankalinta nawani kalan kwanciya mamaki yakashe Lami daman Marwan din na magana haka, ahankali Amirah tace "uhn" dan shiru Marwan yayi duk yanda yaso yadaure yakasa murya chan kasa yace "I'm so happy you've become my wife Ameenatu, and I'm ready to give you not just this world but my entire life, I Love you!" Wani bugawa kirjin Amirah yahauyi Dr Hassan ganin kar abokinsa yawuce gona da iri ga iyaye a mota yasa yace "yoh Docs you're on speaker" wani kunya Marwan yaji dasauri ya katse wayan.

Amirah ta ijiye wayan jikin Lami tai shiru kanta sai maimaita mata I love you I love you yake, daga wajensu zuwa bangaren su Marwan it's soo far is like daga area yaku bayi zuwa area masu kudi almost an hour drive sukakai family house nasu Mami inda akai decorating sosai za'ayi kamu parking akayi a dankareren compound din ganin mutane a compund din sai Amirah tarike Lami dasauri tana shirin fashewa da kuka ta tsorace tace "Ammiiii" cikeda hikima Lami tace "Ammi na wajen nan muje ki ganta" daidai lokacin Mami datasha shigan alfarma dasauran yayin Marwan sunzo wajen ana guda harda su Faiza da Farida da sun kosa suga wacece matan Ya Doc, dudda kan Amirah a lullube but tana ganin kowa ganin fuskokin dabata saniba sai kallonta suke suna murmushi suna guda saita wani koma baya dasauri tashige jikin Lami taja gyalen lami tarufe fuskanta duka tana sakin kuka ahankali kaman zata koma cikinta dan jimmm Mami tayi saita kalli su Ya Ammah tace "ku wuce ku tafi" babu wanda yayi musu duk suka wuce, ahankali Mami tamika mata hannu calmly tace "Amirahhhhh!" Dan dago kanta daga jikin Lami tayi Lami tace "je mamanki na kiranki"hannunwanta Amirah tasa taja mayafin baya ta kalli Mami dake kallonta tanama Mami kallon tsoro idanunta na fitar da hawaye, sosai Mami ke kallon Amirah Ya Subhanallah Allah yayi halitta mai kyau awajen nan yarinya kaman ita tai kanta, and shes so adorable yanda take kukan ashagwabe, anatse Mami tace "taho muje bazan bari su kalleki ba kinaso kiga Marwan"? Tsare Mami tayi da idanu kaman bazatai magana ba saita gyadama Mami kai ashagwabe, Mami tace "yauwa toh zomuje" tadade tana kallon Mami batasan mesa ba kawai saitaji zuciyanta yadan kwanta da Mami saita taho ahankali tasaka hannunta acikin na Mami, ita kanta Mami saida ta jinjina kalan taushin da Allah yama tafin hannun yarinyar tanajin kamshin datakeyi saukowa tayi ta tsaya gaban Mami, Mami tai murmushi sosai tasa hannu taja mayafin ta rufe mata fuska kawai she feels very happy yanda Amirah ta yarda da ita itama Lami taji dadin hakan Mami tace "sannunku da zuwa Bismillah ku" Mami da Amirah na gaba tawagan kawo Amarya na baya, sai kallon Amirah da ba'a ganin fuskanta ake but lallenta takalmin kafanta kayan jikinta kadai abin kallo ne yanayin fatanta kadai zaisa kasan tanada kyau, before sunso adanyi rawa but yanayin Amirah da Mami tagani kawai saita wuce da ita falo ta zaunar da ita kan kujera itama ta zauna kan kujeran tawagan kawo Amarya aka zazzauna su Ya Ammah dasu Farida suka shishigo sun kosa suga Amaryan ya Marwan, gaishe gaishe aka fara aka shiga kawo abinci da abubuwan ciye ciye dangin Amarya sukace Abiya kudin bude fuskan Amarya aiko su Mami da su Ya Ammah akai barin kudi sai Lami ya tashi tazo gaban kujeran ahankali ta yaye gyalen daga fuskan Amirah da rinanun idanunta, Amirah takalli kowa yanda ake kallonta dan har su wayanda suka kawota kallonta suke sai da sauri kawai tai hugging Mami taboye fuskanta abayan Mami, Farida tace "wowwwww Faiza this is Matar Ya Marwan she's dead pretty" Ya Fadila tadan sosa kai tana kallon Ya Maryam tace "no be lie my brother sabi choose wife, he no disappoint" duk cikin whispering suke maganan Maryam tace "but she's nuts" Fadila tace "that's his specialty give her a month I doubt idan yarinyar nan bazata ji sauki ba" takashe mata idanu sukahau dariya, wlh Mami doesn't know why but saitaji tana wani irin son Amirah kaman yanda takeson Faiza da Fadila somehow morethan yanda ma takeson Faiza da Fadilan cus this is a sick girl da batasan anything ba and kaninta hopelessly loves, she hopes and pray Allah yabata lafiya albarkacin auren nan da aka mata, Mami tadan juyo takalleta tace "nakaiki dakina inda babu wanda zai ganki?" Gyadamata kai Amirah tayi ahankali, murya chan kasa tace "Mami ruwaaaa" da kanta Mami ta tashi zata wuce tadauki ruwa dasauri Amirah ta tashi sai Mami ta tsaya tace "bani ruwa Faiza" dasauri Faiza tadauki bottle water tazo wajen Amirah taboye bayan Mami Faiza ta leka bayan Mami suka hada idanu da Amirah tace "Hi" tsareta da idanu Amirah tayi batare datayi magana ba, Mami tace "stop scaring her Faiza she will all get use to you guys give her some time" Mami tabude ruwan sai tabata takarba kadan tasha taba Mami tasha sai Mami tacema Lami bari kuje gidan nata ita tana nan zuwa Mijin nata yazo saisu tafi tare, Lami tai murmushi tace tom wucewa gidan Amirah sukayi Mami ta tafi da Amirah sama zuwa dakinta.

Readers Also Read