Barrister ibrahim khalil complete - Chapter 7
Barrister ibrahim khalil complete Chapter 7: Barrister ibrahim khalil complete Chapter 7. "Banson sharri shegiya ke babu abinda kika iya sai saka idanu,…
4,456 words
"Banson sharri shegiya ke babu abinda kika iya sai saka idanu, yanzu me kikazo yi ne don nasan ba banza takawo ki ba?".
Waro ido Zainab tayi tace
"To me kike nufi? Ko nace miki wani abu nazo amsa wajen ki? Kinga ni tare da Safna muke zamuje gidan aunty Zaituna, shine nace bari in shigo ko zamuje tare sai gashi Mama ma bata nan".
Halwa tace "wato da Safna ma kuke taƙi shigowa? Lallai kam zataci uban ta wlh dani take zancen".
Zainab tace "ni fa bana faɗa miki bane kije kuyi halin naku".
"Ai kibar ni da ita zamu haɗu ne wlh, kuma kisanar da ita hakan".
"Baki da ƙafa ne? Kifito kije kisame ta mana". Zainab tafaɗi hakan tana nufan ƙofa zata fice
Gyara zaman ta Halwa tayi taɗau littafinta tana faɗin
"Banda lokacin ku yanzu, sai mun haɗe a school".
Zainab tace "Allah yakai mu to" sannan tafice da gudun ta
Kifa littafin Halwa tayi saman katifan tabi kai takwanta tana sakin numfashi, shiru tayi tana tunani aran ta, abun da yafaru da ita kwanaki 8 da suka wuce ne yadawo mata cikin ranta, take hawaye masu zafi suka soma sulmiyo mata a fuska
"Har yaushe ne zata dena tuna wannan abinda yafaru da ita? Yaushe ne zata manta da wannan baƙin ranan acikin sauran ranakun da tayi a doron ƙasa? Har yaushe ne zuciyarta zata dena shiga cikin wannan ƙunci da baƙin cikin?"
"Ya Allah gani gare ka, ya Allah kabi min haƙƙina akan wannan azzalumin, haƙiƙa yazalunce ni yasaka min tabon da bazan taɓa iya cire wa ba, Allah ya isa tsakanina dashi bazan taɓa yafe masa ba har duniya tanaɗe".
Tafaɗi hakan afili tana saka bayan hannunta tashare hawayen fuskarta.
***** ***** ********
*AFTER THREE DAYS*
Fitowa yayi daga ɗakin sa hannun sa riƙe da waya, yasami waje saman kujera yazauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, wayan sa yasoma latsawa yana yi yana ɗan ɗago kan sa yana kallon t.v, Lubna ce tafito daga kichen riƙe da coololi a hannun ta, dainning tanufa tajera kana tasake komawa taɗauko wasu su ma tajera su, bayan ta gama tanufi inda yake zaune ahankali tace mishi
"Na gama girkin, ko akwai wani abu?".
Girgiza mata kai kawai yayi idanun sa a kan wayan sa, juyawa tayi tanufi ɗakin ta, shi kam sai da yafi 10mins kafin yamiƙe yanufi dainning ɗin yazauna, aje wayan nasa yayi yasoma buɗe coololin abincin yana taɓe baki, gaba ɗaya babu abinda yayi masa aciki don baya tunanin zai iya sanya wani abu me nauyi acikin sa, rufewa yayi yatashi yanufi kichen, babu daɗewa yadawo hannun sa riƙe da glass cup ya haɗa Black tea, direct dainning table ɗin yakoma yaɗau wayan sa yadawo cikin parlour'n yazauna yasoma sipping tea ɗin yana kallon t.v, ahaka har yagama kafin ya'ajiye cup ɗin saman Centre table yaɗau remote yasoma sanja Channels, har yasaka wani tasha me suna *ƳAN CI T.V* yana shirin sauyawa aka nuno fuskar ta, hakan yasa yatsayar da tashan yana ƙure ta da idanu, duk da ba sosai yakalli yarinyan ba but zai iya shaida itace wacce sukayi karo a kwanakin baya, tana sanye ne cikin wata baƙar abaya me ɗan karen kyau da tsada, ta yane kan ta da Black veil, kasancewar ita fara ce sosai tayi kyau cikin kayan, tana gabatar da shirin ta kamar haka:
"Assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa acikin sabon shirin mu na *RAYUWAR DUNIYA,* wacce ni Kausar Ali Aliyu zan riƙa kawo muku aduk ranan Litinin da Alhamis, shiri ne dake kawo muku abubuwan dake faruwa acikin duniyar mu, tare da bankaɗo muku duk wani abinda ke ɓoye don kusani..."
Ahankali yalumshe idanuwan sa yana jingina kan sa saman kujeran, yana jin muryan ta na ratsa cikin kunnen sa, sai kuma yabuɗe idanun sa yasake saukewa akan fuskarta, sosai yarinyan yaji ta burge shi, rana ta farko kenan da yaji mace tabashi sha'awa har be san sanda yadunga murmusawa ba, yanda take gabatar da shirin ta da komi nata a natse ne
Wayan sa da yasoma ringing ne yasaka shi ɗan ɗago kai yana kallon wayan, ganin sunan DPO na yawo a screan ɗin wayan, hakan yasaka shi miƙa hannu yaɗau wayan tare da rage volume ɗin t.v'n yana karawa a kunne, basu fi 5min suna wayan ba yacire Phone ɗin a kunnin sa yamiƙe yanufi ɗakin sa, Direct sif ɗin sa yawuce yasauya kaya zuwa milk colour ɗin riga me dogon hannu, rigan kamar Jaket ne da coller a wuyan, but sai dai bata da nauyi ƴar shugula ce, wandon sa pencil ne kalan blue Black, sai yasaka Combat shi ma kalan wandon da igiyar shi milk, sosai yayi kyau cikin shigan yafeshe jikin sa da Expensive Parfumer's ɗin sa me shegen ƙamshi, yaɗau wayoyin sa da car keey's yafice, yana fita Compound ɗin gidan yashiga cikin motan sa ash colouer yabar gidan.
...... ....... .........
Yana zaune a office ɗin DPO yana mishi bayani kamar haka:
"Ah BARRISTER a binciken da mukayi na daga ɓatan Matar da kakawo mana, ahm lokacin da kabamu report mun je wajen gidan ka don gudanar da binkice anan muka haɗu da wani mutum yana leƙa gidan ka, dama numban da kabamu mun riga da mun duba sai dai akashe yake kuma an datse hanyar sadarwan shi, to wannan dai mutumin mun kamashi don bamu yarda dashi ba, don haka koda muka kawo shi nan muka saka shi yayi bayani sai yayi mana taurin kai, sai da muka bashi wahala tukun yafaɗa mana abinda yasani, yace "shine wanda yake gadin Matar da ƴaƴan ta, sannan yazo gidan ka ne saboda aiko shi da akayi wajen ƴarinyan Matar da take gidan ka, munyi-munyi yayi mana bayani akan mutanen da suka saka shi aikin but yace "shi be san su ba, shi dai kawai an saka shi yatsare su ne", kaji abinda yafaru, but duk da haka dai muna tsare dashi ko zamu sami wani inpermation akan su".
Gyara zaman sa da kyau Khalil yayi yana kallon DPO ɗin yace
"Yanzu ina suke?"
"Suna nan mun aje su a wani ɗaki, zaka iya tafiya dasu yanzu haka but ko wani lokaci zamu iya neman su".
"Ok babu matsala ai".
Miƙa mishi hannu yayi sukayi musabaha kafin suka miƙe atare suka fice.
Bayan kamar minti goma Khalil yafito cikin station ɗin, bayan sa wata dattijuwar mata ce da matasan yara maza su biyu, buɗe musu mota yayi suka shiga sannan yakulle shima yashiga yaja yatafi, Direct gidan sa ya'isa, bayan yayi parcking yasake buɗe musu suka fito yace "su biyo bayan shi" babu musu suka bi shi a baya har cikin parlour'n, zama yayi bayan da yace
"Umma kuzauna mana".
"Toh". Cewar matar sannan suka zauna
Wayan sa yasaka yakira Lubna sai gata tafito, ai tana cin karo dasu tasheƙo da gudu tana kiran "Ummana", rungume Umman tayi tasaki kuka, su ma ƙannin ta suka rungume ta duk suka fashe da kuka, Khalil kallon su kawai yake yi yana murmushi cike da tausayin su, sai da suka gama rungume-rungumen junan da koke-koken kafin Lubna taɗago kanta fuska a jiƙe takalle shi tace
"Nagode Sir, ban san da bakin da zan maka godiya ba, na gode sos.."
"Shiiiiihh ya isa haka, kibasu abinci suci su huta sai ki kira ni bayan sun gama ok?"
Gyaɗa masa kai tayi tana share hawayen ta, shi kuma tashi yayi yashige ɗaki yarufo ƙofan, ahankali ya'isa gaban gadon sa yazauna tare da jinginar da kan sa a jikin gadon, rufe idanuwan sa yayi yana jan iska da ƙarfi yana fesar wa, tunanin abinda yakamata yayi kawai yake yi, tsawon lokaci kafin yaji wayan sa tana ringing, Koda yaduba yaga Lubna ce sai yamiƙe kawai yafice
Kallon Umman yayi bayan da yazauna yace
"Umma kuna da wasu ƴan uwa ne a wani wajen, ko dama anan kuke zaune?"
Umma tace "a'a muna dasu a ƙauye, dama mu ma can muke zaune sanadiyan aiki ne muka dawo nan muka kama haya".
Gyaɗa kan sa yayi kana yace
"To Yakamata ki ɗauki ƴaƴan ki gaba ɗaya kubar nan, ko ki koma ƙauyen ko kuma ku sauya wani waje me nisa, sabida mutanen da sukayi garkuwa daku ko wani lokaci zasu iya dawowa gare ku".
Sannan yamayar da idanun sa kan Lubna wacce itama kallon shi take yi yace
"Kije kihaɗa kayan ki".
Daga haka yamiƙe yakoma ɗakin sa, ita kam Lubna kasa riƙe kukan da yazo mata tayi tasake shi ahankali, Umman nata tace
"Ai hakan yadace muyi Lubna, wlh ko be ce mubar nan ba baza mu sake kwana ba, ai Allah mun gode maka da yataimake mu da bamusan me mutanen nan zasu yi mana ba, kitashi kije kihaɗa kayan ki mutafi".
Babu musu tamiƙe tashiga ɗaki, lokacin da tafito riƙe da trolly ɗin kayan ta shima Khalil yafito yana kallon ta, sauke kanta ƙasa tayi hawaye na zubo mata, bazai iya juran ganin hawayen ta ba don haka yaɗauke kan sa yanufi wajen Umma yace
"Ga wannan Umma, da fatan zai ishe ku ko da sana'a ne sai ku kama".
Jiki na rawa Umma tasaka hannu ta'amshi maƙudan kuɗin da yamiƙo mata
"Har da ɗawaniya ɗan nan? To mun gode Allah yasaka da alheri, Ubangiji yabiya maka duk kan buƙatun ka, mun gode ƙwarai da gaske".
Murmushi kawai Khalil yayi yana motsa laɓɓan sa, yana nan tsaye har suka fice kana yasami waje saman kujeran yazauna, lumshe idanuwan sa yayi yana tuna ranan da Mom ɗin shi takawo mishi Lubna a matsayin ƴar aiki, wacce zata riƙa taimakon shi da gyaran gida
Asali ita Umman Lubnan itace ƴar aikin Mom, daga baya ne tayi wani ciwo da yakwantar da ita tsawon lokaci har ta'ajiye aiki Mom kuma tasamo wata, lokacin bayan Umma ta sami sauƙi sai tazo wajen Mom tane mi alfarma ta samar ma Lubna aiki, shine ita kuma Mom tace "Khalil yaɗauke ta yatafi da ita, tunda dole yana buƙatar wacce zata riƙa dafa mishi abinci da sauran abubuwa na gyaran gida" babu musu Khalil yatafi da ita, wannan shine dalilin da yasaka LUBNA take aiki a gidan sa, kuma a gidan nasa take kwana but wani lokacin kuma tana komawa gidan su, musamman kamar ranan Weekends haka.
Ajiyan zuciya yasauke yana buɗe idanun sa, gyarawa yayi yakwanta a kan kujeran yasake lumshe idanun sa. [9/16/2020, 8:26 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 21*
Kiran sallan magriba ne yasanya shi buɗe idanun sa da suka yi ja sakamakon barcin da yaɗauke shi, ahankali yamiƙe yanufi ɗakin sa, alwala yaɗauro yafito yanufi masjid, as usual sai da akayi sallan isha'i yadawo gida, Direct ɗakin sa yawuce yacire rigan sa yabar singlate ɗin dake jikin sa, drower yabuɗe yaɗauko keeys sannan yarufe, yaɗau briefcase ɗin sa yafito parlour, akan 2sitter yazauna yana ajiye briafcase ɗin saman Centre table, wayan sa yaɗauka sai da yalatsa kafin yakara a kunne, yana jin an ɗauka yace
"Kazo ina neman ka".
Daga haka yacire wayan ya'ajiye, buɗe jakan yayi yaciro Computern sa yasoma aiki
Da sallama wani matashin saurayi yashigo ciki, amsa masa sallaman yayi batare da yaɗago daga abinda yake yi ba
"Gani Sir". Cewar saurayin bayan da yaduƙa gaban sa
Ɗago kai yayi yana kallon sa yace
"Sale daga yau aikin ka zasu ƙaru agidan nan, zaka riƙa zuwa kana gyara min cikin gidan nan, don haka zan ƙara maka albashi in babu matsala".
Washe baki Sale yayi yace
"Ai babu komi Sir duk zan iya, har da ma abun da bakace ba".
"Ok.. ga keeys ɗin gidan sai kariƙe a hannun ka ko".
Hannu biyu yasa ya'amsa
Yace "katashi kaje".
Miƙewa Sale yayi yana godiya kafin yatafi, shi kuma yaci gaba da aikin sa, wajen ƙarfe 09:00pm. Yadakata kasancewar yunwan da yaji yana ƙwaƙulan cikin sa, miƙewa yayi yanufi kichen, tsayawa yayi yana nazarin abinda zai ci domin sosai yaji cikin sa na kukan yunwa, don haka kawai yayanke shawaran dafa indome, cikin abinda be gaza minti 12 ba yagama, indome ne haɗe da ƙwai yasoya yaɗauka yafito, zama yayi yasoma ci ahankali yana tunani har yagama, yatashi yamayar da plate ɗin da spoon cikin kichen sannan yadawo yaci gaba da aikin sa, sai wajen ƙarfe 12:04pm. Sannan yanufi ɗakin sa, sai da yaɗauro alwala yagabatar da sallan nafila tukunna yasauya kayan sa zuwa kayan barci yakwanta.
Washe gari ƙarfe 06:45am. Tuni yagama shirin sa na zuwa office, suit yasanya sky blue da ƴar cikin milik colour, sosai yayi kyau babu abinda yake yi sai tashin ƙamshi, yaɗau briafcase ɗin sa yafice, a farar motan sa yashiga yabar gidan.
Ƙarfe 02:30pm. Yadawo gida, yana shiga cikin ɗakin sa ya'ajiye briafcase ɗin sa sannan yazauna yasoma zare Combat ɗin ƙafan sa da socks, bayan ya gama yacire suit ɗin tare da necktie ɗin wuyan sa duk yazube saman gado, miƙewa yayi yashiga Toilet, be daɗe ba yafito yanufi parlour, kichen yawuce yahaɗa tea me kauri yazauna nan yasoma sha, bayan ya gama yafito yakoma ɗaki yacire kayan sa yashiga wanka
Lokacin da yafito yashirya cikin wani ɗanyen Boyel maroon colour, ba ƙaramin kyau suka yi masa ba kamar wani sabon ango, yafeshe jikin sa da farpume's yakwashi wayoyin sa da keeys ɗin mota yafice, mota yashiga yabar gidan, Direct super makert yawuce yayi shopping masu yawan gaske, yahau motan sa yanufi gidan ɗan uwan sa
Lokacin da ya'isa yana yin hon aka buɗe masa motan yakutsa ciki yayi parcking, yanayin gidan da komi irin nasa ne, sai dai ɗan abinda ba'a rasa ba, yana fitowa me gadi yanufo sa da gudu yana kai gaisuwa tare da taimaka masa yashigar da kayan, a parlour ya ajiye masa, shi kuma yaciro kuɗi yabashi yana ta godiya sannan yafita, zama yayi saman sofa yana sauke idanun sa akan plasma dake aiki shi kaɗai babu kowa, yafi minti 5 da shigowan sa be ji wani zai fito ba, hakan yasaka yaɗau wayan sa yasoma latsawa yana neman layin Sameer, sai ga Abida tafito, ƙanwa ce ga matar Sameer ɗin, tana hango shi tanufo wajen shi cike da fara'a tana faɗin
"Laa Ya Khalil yaushe kashigo?"
Ɗago kan sa yayi yakalle ta kana yace
"Yanzu".
"Sannu da zuwa to".
"Yauwa, ina masu gidan?" Yatambaye ta yana mayar da idanun sa kan wayan sa
Murmushi tayi tana zama akan hannun kujeran da yake kai, kana tace
"Suna ciki, ko in Kira su?"
Gajeren tsaki yaja batare da yace mata komi ba, yana ganin rainin hankali ne, har sai yace ma takira su zata kira mishi su? wayan sa yakara a kunne yana faɗin
"Bro gani a gidan ka fa".
Abinda yafaɗa kenan yakatse kiran, ita kam Abida kallon sa kawai take yi tana murmushi, sosai take ƙaunar Khalil sai dai ko kaɗan shi baya sakar mata fuska, ko tayi yunƙurin shiga jikin sa to baya bata dama
Sameer ne da Hakima suka fito daga ɗakin su, sun ci ado cikin wani farar kamfala iri ɗaya har aikin
"Uhmm ai wlh nayi fushi ba kaɗan ba, wai ace tun yaushe kadawo ƙasan nan har akayi suna bakazo ba sai yanzu?"
Cewar Hakima tana zama a ɗaya daga cikin kujerun parlour'n, yayinda shima Sameer yasami gefen ta yazauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kyakykyawar murmushin sa yayi kana yace
"Afwan Matar Bro, I know nayi laifi, amma sai da nace ma Bro yafaɗa miki uzurina, ko ba haka muka yi ba Bro?".
"O'o niii? Kar kahaɗa ni da matata, a yaushe mukayi haka da kai?" Cewar Sameer ɗin yana ɗaga hannaye sama tare da fito da idanuwan sa
"You see ka gani ko? Ai nasan Mijina bazai maka ƙarya ba, kai dai kawai bakayi ninyan zuwa ba sai sanda kaga dama". Hakima tafaɗi hakan tana murmusawa
"To yanzu dai first kifara ɗauko min My son nagan shi sai aci gaba daga baya".
"Hmm ai yayi fushi shima bazai gan ka ba".
"Haba Matar Bro Ni ne fa ko kin manta ni? Bro kasaka baki mana". Khalil yafaɗi hakan yana langwaɓar da kan sa kamar ƙaramin yaro
"To sweetheart ki yafe masa tunda naga kamar yayi nadama, but nest in yasake ki hukunta shi".
Gaba ɗaya sukayi dariya, yayinda shi Khalil ɗin murmushi kawai yayi yana shafa kan sa
Hakima tace "Abida ɗauko mishi Aamir".
"Tom Aunty".
Miƙewa tayi tawuce ciki, ita ma Hakima tashi tsaye tayi tana faɗin
"Bari nakawo maka abin motsa baki Mijin".
Khalil yace "No kibar sa kawai na hutar she ki".
Sameer yace "waɗannan ledojin fa? Menene aciki kakawo mana?".
"Shopping ɗin My Son ne".
Hakima tace "to mun gode".
Lokacin Abida tafito riƙe da Aamir a hannu takawo mishi, hannu yasaka ya amsa wanda har hannun su yana gogan juna, shi be ma lura ba yaron kawai ya'amsa, yayinda ita kuma Abida taji wani iri ajikin ta hakan yasaka tasaki murmushi tana jin farin ciki, yau rana ta farko jikin mafi soyuwa a cikin zuciyarta ya haɗu da nata
Bayan yagama ganin yaron ma sai tamiƙo hannu don yaba ta, but sai yamiƙe yaje yamiƙa ma Hakima yana faɗin
"To ni tafiya zan yi, sai kuma na sake kewayo wa".
"Da wuri haka?" Cewar Hakima bayan ta amsa yaron
Amsa mata kawai yayi ataƙaice, daga nan suka yi sallama suka fito tare da Sameer, sun kai wajen mintuna 30 atsaye wajen motan Khalil suna tattaunawa kana yashiga motan sa yatafi.
Yana tafiya a cikin motan sa ya kawo anguwan su, zai sauka kan titi yaji Motan tayi faci sakamakon taka ƙusa da tayi, tsaki yaja yana ɗan murza hannun sa a sitiyarin motan, yajingina kan sa jikin kujeran yana kallon saman motan, tsawon mintuna yana nan ahaka kafin yaji hon a bayan sa, hakan yasaka yaɗago kan sa yana kallon motan dake bayan sa ta mirror, siririn tsaki yaja yana mayar da kan sa yalumshe ido, motan ce tazo dai-dai setting shi kana tazuge glass ɗin motan tana kallon shi
"Kana neman taimako ne?" Tafaɗi hakan cike da sanyin murya
Ɗago kan sa yayi yakalle ta, ita ce dai budurwan da sukayi karo kwanaki kuma yaganta cikin t.v, sai yagyaɗa mata kai a hankali still yana kallon ta, murmushi tayi masa don ita tariga da tagane sa hakan yasaka tatsaya
"Ok why not kazo narage maka hanya in babu damuwa fa".
Murmushi yayi mata kana yafito daga motan yarufe, sai da yaciro wayan sa yayi ɗan gajeren text yatura kafin yanufi motan nata yashiga, taja suka tafi.
_Ku ƙara yawan Comments plzzzzzzz_ 🥰🥰🥰 [9/17/2020, 11:04 AM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.```
_Wannan shafin naku ne duk wani masoya littafin Brr. Ibarhim Khalil, ku ji daɗin ku_🥰🥰💃💃💃💃
.
*CHAPTER 22*
"Anan zaki sauke ni". Yafaɗi hakan yana nuna mata setting gidan sa
"Laa kace kusa da juna muke ma". Tace hakan lokacin da tatsayar da motan
Kallon ta yayi yace
"Really?"
Murmushi tayi itama tana kallon shi tagyaɗa masa kai
"But ban taɓa ganin ki ba ai? Kuma ina yawan ganin wani matashin saurayi yana fitowa gidan".
"Eh ai ni bana ƙasan ne, ina can Maleysia ina karatu, sai kwanan nan nadawo".
Gyaɗa kan sa yayi kana yace
"Ok thanks for your help me".
"Babu damuwa, yiwa kai ne ai".
Sai kuma tamiƙo mishi hannu still da murmushi a face ɗin ta tace
"Zamu iya zama friends?"
Kallon hannun nata yayi sai kuma yakalle ta, sannan yagyaɗa mata kai batare da yamiƙa mata hannun ba, janye hannun nata tayi tana yarfe shi tace
"Oh sorry" nayi tunanin ko maleysia muke". Tafaɗi maganar tana waro idanu
Hakan yasaka shi murmushi batare da yace komi ba, yabuɗe motan zai fita
"Aff baka sanar dani sunan ka ba?" But ni sunana Kausar Ali Aliyu, and You?"
Tafaɗi maganar tana ƙure shi da idanu
"BRR. IBRAHIM KHALIL". Yayi maganar ataƙaice shima yana kallon ta
"Wowwww! Nice Name, zan ji daɗin abota da kai kenan coz ni ƴar Jarida ce".
Cike da ƙosawa da surutun ta yasaka ƙafarsa awaje zai fice still tasake faɗin
"Am baka ji ba?"
Yajuyo yana kallon ta fuska a haɗe tare da nuna gajiyawar sa, ita kuma sai tayi murmushi tace
"Sorry na takura ka, dama zance ne kagaishe min da Madam kafin nashigo".
"Wa yace miki ina da mata?"
Yafaɗi maganar yana ficewa gaba ɗaya yataka yatafi batare da yajira amsar ta ba, ita kam babu abinda take yi sai murmushi, sosai Guy ɗin yaburge ta, ko kaɗan bashi da rawan kai irin samarin zamanin nan, sai da taga shigewan sa sannan ta tada motan tanufi bakin Gate ɗin gidan su tadanna hon da ƙarfi.
Shi kuma daga shigan sa gidan yamiƙa ma Gate Man keeys ɗin motan sa in Drever yazo yabashi, sannan yashige cikin gida, bayan yayi wanka ya kintsa cikin ƙananan kaya yasake fitowa yanufi masallaci, sallan asar yayi yadawo yazauna nan parlour yana danne-dannen waya, tsawon 1 hour yana wajen kafin yamiƙe yanufi kichen, Coffee yahaɗa yafito yazauna yakunna t.v yasanja channel zuwa MBC Action, abinda yake so kuwa ake yi wato wrestling, haka yakafa idanun sa akan kallon yana yi yana spping Coffee ɗin, sai da aka gama yamiƙe yanufi kichen ya ajiye cup ɗin yashiga ɗaki, ahankali yabuɗe ɗakin da yake aikin sa yazauna kan kujera, yajanyo Lapton ɗin sa yasoma aiki.
......... ........ ........ .....
Asalin Alhaji Abdurra'uf Abdullahi da Hajiya Hajara fulani ne kuma mazauna garin Katsina, Alhaji Abdurra'uf wato Dad shi irin baƙaƙen Fulanin nan ne na daji masu yawo wannan garin zuwa wancan garin, yayinda Hajiya Hajara wato Mom ita kuma irin fararen nan ne waɗanda kallo ɗaya kayi musu zaka gane su ɗin Fulani ne, Babban Family ne dasu, lokacin da su Dad suka zo Garin Katsina dashi da iyayen shi Mahaifin Mom ne yabasu mazauni a nan gidan su, zuwan sa gidan ne kuma yasoma karatu har matakin degree, da sannu da sannu suka saba da ƴan gidan har suka zama tamkar Family ɗaya, kuma alokacin ne Soyayya me ƙarfin gaske yashiga tsakanin Dad da Mom har suka yi aure, Allah ya albarkace su da yara biyu duk ka Maza Sameer da Ibrahim Khalil, kuma daga kan su basu sake haihuwa ba.
Rayuwan Sameer da Ibrahim Khalil sun yi shi ne cikin gata da ƙaunar iyayen su har zuwa matakin da suka girma, kuma sun yi karatun su ne a ƙasan Gamerny har zuwa sanda suka gama suka dawo, shi Sameer ya karanci Doctoring ne fannin ƙashi, shi kuma Ibrahim Khalil ya karanci BARRISTER
A tare Sameer da Khalil suka ƙera gidan su, sai dai ba anguwa ɗaya bane, Lokacin da Sameer ɗin yayi aure shima Khalil yace "bazai zauna a gidan su ba" shine yakoma sabon gidan shi, shekaru kusan biyu kenan da faruwan hakan.
Wannan shine taƙaitaccen tarihin su.
***** ****** ******
*TWO WEEKS AGO*
Da dare wajen ƙarfe 09:00pm. Khalil ne zaune a cikin Garden ɗin gidan sa, gaba ɗaya wajen haske ne yamamaye wajen tamkar rana don baza kace dare ne ba, yana sanye cikin wasu kaya riga da wando three qweater tamkar na sanyi, red colour ne irin dack ɗin nan, sun bala'in yin masa kyau sosai, kan sa babu hula sai gashin sa da iska ke ta kaɗawa, gaban sa kuma ɗan ƙaramin table ne ya ɗaura Lapton ɗin sa akai, gefe ɗaya kuma glass cup ne da Fruits a cikin plate, aiki yake yi time to time kuma yana ɗan kurɓan Black tea ɗin, wayan sa dake ajiye ne tasoma ringing yaɗan tsayar da aikin yakalli wayan, ganin sunan Dad ya fito raɗo-raɗo a screan ɗin yasanya shi saurin ɗauka yana peacking call ɗin tare da karawa a kunne
"Hello Dad.. au assalamu alaikum".
Murmushin Dad ɗin ne yabayyana cikin wayan kafin yace
"Kai dai baza ka dena halin nan naka ba ko?"
"Sorry Dad na manta ne, but ai na gyara ko?" Yayi maganar a shagwaɓe
Still Dad murmusawa yayi yace
"Auta kenan, Mom ɗin ka tariga ta gama ɓata ka, kana yin abu sai kace ƙaramin yaro".
Murmushi Khalil yayi yana shafa kan sa yace
"Dad ai ku kaɗai nake ma wa, coz a wajen ku ni har yanzu yaro ne".
Dad yace "to gobe da safe kafin kawuce office kabiyo gida ina neman ka".
"Dad lafiya kuwa?"
"Lafiya lau My Son, sai dai in ka zo zaka ji, kar kuma kace min ka manta kashanya ni jiran ka".
"Tom Dad, insha Allahu zan zo". Khalil ɗin yafaɗa cike da girmama wa
Daga nan sallama suka yi Khalil ya'ajiye wayan sa yaci gaba da aikin sa. [9/17/2020, 7:20 PM] نفيسة أم طاهرة: 🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️🎗️ *BARRISTER IBRAHIM KHALIL* ♠️
*Written:✍️ By Nafisat Isma'il* _(Feenah Jikar Lawal Goma)_
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖ *FEENAH WRITER'S ASSO📖* ```®Ɗaya tamkar da Dubu💪✓```
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattpad: UmmuƊahirah*👈
*\F.W.A📚/*
```ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH``` _ALLAH nagode maka da kabani damar rubuta wannan littafin Brr. Ibrahim Khalil, Allah kabani ikon rubuta abin da zai amfani al'umman mu, kuskuren da zanyi aciki kuma Allah kayafe min AMIIN 🤲 ya Allah._
*SADAUKARWA* _na sadaukar ga ƴan uwana musulmai baki ɗaya._
*MARUBUCIYAR* ```NAFEESAT LABARIN DEEBIZAH JARUMAI RAYUWATA NUSNIM BUTULCI SO MAI ZAFI.```
.
*CHAPTER 23*
*TOMORROW MORNING*
Khalil ne zaune a parlour'n mahaifin nashi yana sauraron abinda yake faɗa mishi
"Ibrahim har yanzu dai bakasan zurun ba ko? Tun yaushe nayi maka maganar aure but har yanzu shiru babu wani motsi da kake yi".
Ɗago kan sa yayi yana kallon Mahaifin nashi, be yi tunanin wannan maganar ce tasaka yakira shi ba, kuma ko kaɗan be shirya ma hakan ba
"Ina jin ka tunda ka bari sai na tambaye ka, yanzu kasanar dani wacce yarinya ce kake so don mugaggauta nema maka auren ta?"
Shiru Khalil yayi yana sad da kai ƙasa
"Kayi shiru kuma?" Dad yatambaye sa yana kallon sa
"Uhm Dad ni har yanzu ban sami wacce nake ƙauna ba".
"Ohho nagane me kake nufi Ibrahim".
Cewar Dad yana kaɗa kan sa, sannan yaci gaba da cewa