Batuol mamman complete novel - Chapter 19
Batuol mamman complete novel Chapter 19: Batuol mamman complete novel Chapter 19. Kallon kin ma rainani ya jefa mata "sai ki tafi inda kika saba zuwa gidan…
3,366 words
Kallon kin ma rainani ya jefa mata "sai ki tafi inda kika saba zuwa gidan tsoho aje a ci abinda ya sauwaka"
Duk magiya da rokonta ta bayan kunnensa tabi sai da ranta ya baci sosai ta tsaya masa kerere a gaba. Tulun cikinsa kadai ya isa ya tureta dashi ta fadi.
"Ka sakeni in koma gidan ubana ai ba a titi aka daura mana aure ba. Wannan wace irin rayuwa ce ace matanka tsakaninka dasu bai wuce ka dirka mana ciki ba. Ci da sha da sutura sai dai mu yiwa kanmu. Ko kunya baka ji duk kudinka. Mune wankau, surfe da duk wani aikin kaskanci don mu ciyar da kanmu da 'ya 'yanmu"
Marin da ya zabga mata ne yana faman nade hannun malum malum ya gigita ta ta kasa cigaba da maida martani.
"Ki fita idona Salame, wannan jarababben auren naki kuma yanzu muka fara babu inda zaki je"
Fuuuu ya fice daga gidan sai dariyar Maman Danmama da ta cika mata kunne. Bata saurara ba sai da ta fito daga dakinta tazo gaban Salame tana mata dariyar mugunta.
"Mu dai sai dai muce Allah Ya kara karawa. Ki koma wurin bokanki kice masa kwabarki tayi ruwa. Irin wadannan ranakun tsakaninki da Alhaji su kan sani nishadi da wanke min zuciya. Anyi walkiya Salame mun ganki tsamo tsamo"
Dan sauran kuzarin nata na fada marin da ta sha ya tafi dashi, shiyasa ta kasa maidawa Maman Danmama. Ita kuwa batayi shiru ba.
"Ohhh ni 'yasu. Kamar ba'ayi zamanin da kike sa Alhaji ya zage ya zanemu a cikin gidan nan ba. Kika dawo kika saka shi sakin kowa banda ni wai na zauna nayi raino kema a gidanku uwargidan babanku aikinta kenan. Ai ance tsafi gaskiyar mai shi. Kinyi kin gama surkullen tazo ta kare miki"
Wani dukunkunannen hijabi Salame ta saka taki kula Mama ta fita tare da yaranta ta nufi gida.
A soro suka yi kicibus da Malamijo zai fita. Girma ya kara kama shi sai dai akwai kyan jiki tunda babu kiba kuma yanzu ya yarda da ci da sha wa kansa mai kyau a waje. 'Yar fara'ar da ya taho da ita sakamakon faranta masa da amarya tayi kafin ya fito ce ta bace yana ganinta.
"Allah Yayi dare gari ya waye an kwaso jiki an taho cin banza. To baki isa ba Salame. Tunda na aurar dake ko dan ihsanin nan na tsakanin da da mahaifi bai taba giftawa tsakaninmu ba sai ma dai ki karkace ki fada min magana idan kinso. Amma 'yan kwanakin nan kullum ana fada min sai kinzo, kuma ba kya tashi zuwa sai kin daidaici an gama abinci. Ki kwaso yara rabe-rabe azo aci bati. To na gaji, ki juya sawunki a likkafa ki koma inda kika fito"
Jikinta har bari yake saboda yunwar dake sasakarta fushi da maidawa mahaifinta martani ba nata bane yau dinnan idan ba so take daga ita har yaran yunwa ta kar su ba.
"Ku shige gani nan zuwa" tace tana kadasu ciki.
"Ya ina cewa ku koma kina turasu? Salame, Salame ki kiyayeni." Yace yana nunata da yatsa.
"Gaisawa kawai zanyi dasu mu tafi"
Tausayinta ya dan ji saboda ya tabbatar yadda ta fige dinnan tabbas kila mijin da har shi take iya yiwa rashin kunya a kansa ya juya mata baya ne.
"Jeki amma daga yau na sake ganinki zanje na sami Alh Indararon inji ko har ya cinye sadakinsa ne shiyasa zamu fara raba nauyin. Mairama ma da take ruga ta fiki abin arziki. Makanta, rashin miji da nisa basu hanata yi min alheri ba."
Kunci taji ya ziyarci zuciyarta saboda ya ambaci kamwarta da ta mayar kishiyarta ta karfin tsiya. Duk ita ce silar komai tunda dalilinta taje wurin boka aka rabata da Alh Indararo saboda kawai bata son ta ga tayi gaba ta barta ba wai don ita din sonsa take yi ba. Da asiri ta rinka cin galaba akansa da matansa komai na tafiya daidai ta kuma saki jiki tana ta haihuwa don ta tara magada sosai. Cikin jikinta na da wata biyu bokan nata yace ga garinku. Shikenan duniya tayi mata atishawar 'yan tsaki. Komai ya lalace wai ita da take mulkin gidan a tsakar gida Alh Indararo ya kalleta yace yaushe ya aurota. Da bakinsa yake cewa ina Mairama kanwarta. Rai a bace ta shige ta ce da yaranta su taso su tafi.
"Ki barsu yanzu zan zuba musu abinci Salame" Yadikko tace mata tana kallonta da tausayawa. Ko bata ce komai ba kana kallonta kasan akwai yunwa daga ita har yaran.
"Tafiya zamuyi, kai ku tashi mana"
"Umma ki bari muci abinci" babbar 'yarta tace idonta cike da kwalla.
"Ko ku tashi ko jikinku ya gaya muku ku duka. Aikin banza kai."
Duk yadda Yadikko taso kin zama tayi saboda kawai an yabi Mairama ta gwammace su sake kwana da yunwa.
**********
Karfe biyar da rabi Awwab ya sauka a Nnamdi Azikiwe International Airport da yake birnin tarayya. Ya saba tafiye tafiyensa babu wasu kaya sai 'yar jaka karama da yake saka kayan sakawa biyu ko uku ya danganta da kwana nawa zaiyi a garin. Wannan karon kuwa sai da ya hado da akwati mai kyau na turawa dan madaidaici. Jin kansa yake wasai babu tarin gajiyar nan saboda a fasinja ya taho ba pilot ba, tun daga tasowarsu sai minti goma kafin saukar jirgin ya farka. [5/22, 10:51 PM] Sis Ruky: Ruwa yaje ya watsawa fuskarsa yayi brush sannan ya dauko wani karamin hankici kamar tawul iya tafin hannunsa ya goge fuskar. Komawa yayi ya zauna yana jin kansa yayi wani fresh balle da ya tuna mutanen da zai gani. Kayataccen murmushi yayi shi kadai wata matashiya da suke zaune tare ta maida masa saboda ya dan fuskanceta ne yana laluben seat belt dinsa.
"Hi handsome" tace dashi da ingantaccen turancinta.
Sai da ya waiga bayansa ya tabbatar babu kowa sannan ya nuna kansa sai ta gyada kai.
"Hello" ya maida mata da kyar don baya son mace mara kamun kai. Da ace magana tayi masa kawai bazai damu ba. Amma idan kaji ana handsome ko beautiful ai kasan kwanan zancen.
"Kaima bahaushe ne ko?"
Baiyi mamakin da ta gane ba tunda suna zama ya soma waya bai dena ba sai da yaga jirgin ya fara tafiya.
"Kema haka ko?"
Murmushi tayi, a rayuwarta tana son namiji mai kaurin murya. Ba da karfi ya amsa mata ba amma amon muryar ya isa ya sanya mata da yawa muradin son kasancewa da mai ita musamman idan suka hado dashi. Wankan tarwada, dogo, hanci madaidaici da ya dace da kyakkyawar fuskarsa.
"Na kula baka ci komai ba tun tasowarmu."
Bai wani kare mata kallo ba yace "bana jin yunwa ne"
So take hirar ta tsawaita don tunda ta dora idanu a kansa zuciyarta bata kara samun sauki ba. Ta kula mutumin kamar yana da ji da kai sai dai kuma bazata bari shan kamshinsa ya hanata samun abinda take so ba. Dawowarta kenan daga Germany inda taje hutu wurin yayarta. Mahaifinta tsohon soja ne da ya tsunduma siyasa tun lokacin mulkin farar hula. Yanzu haka sanata ne da yake wakiltar mazabarsu a jihar Plateau.
"Suna na Arifah"
"Awwab"
Daga haka ya kafa waya a kunne don tuni sun sauka an bada damar kowa ya tashi. Cikin cabin crew din wata 'yar Nigeria da tasan Awwab tazo suna gaisawa da ya tashi zai dauki jakarsa.
"Captain yau fa ka yi mana wayo. Kasha bacci ka barmu da aiki"
Sai yanzu Arifah ta ga ya sake sakin fuska harda dariya "ki dauki hutu kema sai mu koma tare. Yanzu ina da wata guda na mantawa da kowa sai family dina"
'Yar hira suka taba sannan suka yi sallama. Awwab na fita Arifah ta bi bayan matar da suka gaisa mai suna Chisom ta roketa numbar wayarsa.
"Ki bishi ya baki da kansa, Captain Awwab baya son irin haka don an taba yi masa na gani"
Marairaicewa tayi tana fada mata yadda take son shi tare da rokon ta taimaka mata. Kudi ta dauko daga jakarta za ta mika mata Chisom ta bata rai "ba sai kin sayeni ba, Awwab is a nice man ga number dinsa ki gwada sa'arki"
Arifah kamar ta zuba ruwa a kasa tasha ta rubuce number din da ta karanto mata daga wayarta ta fita da sauri ko zata sake samunsa sai dai yayi mata nisa bata ma san ina yayi ba. Bata da damuwa tunda akwai numbar da zata same shi.
Yana fitowa waje hasken rana ya kwale a sama kamar ba shida ke neman yi ba. Jacket dinsa ya cire ya sakale a hannunsa ya jana jan akwatinsa.
Kamar ance ya kalli hagunsa suka hada ido da Ghazalatu. Taci kwalliya sosai don ta burge shi ta kuwa yi nasarar sanya shi murmushi. Daga ita sai dreba suka zo daukarsa kannenta suna makaranta.
"Yayana" tace da ya zagayo wurin motar tana murmushi.
"My G kinyi kyau fa"
"Ba wani nan, kai dai kawai ka dade baka ganni bane"
Gaisawa yayi da dreban ya shiga gaba ita kadai a baya suna ta hira. Ji take kamar ya dawo bayan motar su zauna tare. Ta rasa gane masa ne ana soyayya amma shi tamkar wanda ya taso a kauye. Baya irin yadda wayayyu suke yi. Ko gidansu taje hutu haka zata karaci zamanta hannu wannan bai san ya rike mata ba ko da su kadai suka fita. Yanzu wata hudu rabon da ya ganta amma simple hug ma su ji dumin juna ya gagara.
Waya ya rinka yi a rabin tafiyar saboda tazarar airport din da cikin gari. Mami ta fada masa su Alheran suna Kano amma Ummi tana tare dasu.
"In sha Allahu gobe asubanci zanyi zuwa Katsina. Sai na ga Ummi zanje wurinsu. Uhmm Mami tare zamu taho da Ghazalatu fa"
"Jiya Gambo ta fada min, sai kun iso. Jirgi zaku biyo?"
"Gamu nan dai sai abinda Mummy tace"
Sunyi sallama Ghazalatu ta rankwafa daidai kansa yana jin numfashinta a kunnuwansa da wuya.
"Daga kanki G" yace yana yin gaba da kansa saboda yadda yake ji.
Komawa tayi ta gyara zamanta "na daga shikenan, dama tambayarka zanyi ko kayi min tsaraba nima kamar kowa"
"Su waye kowa?"
"Yarinyar da ka tambayeni jiya me zaka saya mata"
"Allah Yasa ba kishi kike yi da yarinyar da ni dake duk bamu gani ba" yace yana dariya.
"Akwai dalilin da zanyi kishinta ne?"
"Ko kadan, please kada muyi abinda muka saba daga zuwana. A bar maganar haka ko."
Bata sake cewa komai ba har suka isa gida. Mummy Gambo tasa an hada masa kayan tarbar babban bako. Ranar da daddare da kansa ya sanar da ita abinda ke tsakaninsa da Ghazalatu. Gambo tayi murna sosai tana ta dokin maganar ta kai kunnen Hassana wato Mami. Abu ne da ya shafi dangi gabadaya ta bangarensu da bangaren mazajensu. Ga Awwab din da shiga rai dole taji dadin wannan hadi.
**********
Harun mahaifin Ghazalatu da ne ga Alh Baba. Babansu Mami kaninsa ne na uku yayin da baban Major ya kasance autansu. Harun ne ya biyawa Alhajinsu umara suka tafi tare. Mutumci, shakuwa da kyakkyawar alakar dake tsakaninsa da Major tasa ya kaishi Germany gashi yanzu shi ma ya tsaya da kafarsa.
Major bashi da wani abokin shawara a dangi kamar Harun shiyasa a daren ranar da ya sanar dasu Mami game da hadin Awwab da Alheran ya kira shi ya fada masa.
"Gaskiya kayi tunani mai kyau ko babu komai yanzu zaka fi ji a ranka cewa ka rike iyalin bawan Allahn nan. Allah Ya gafarta masa Ya nuna mana lokacin"
"Amin Harun"
"Zan fara yiwa Alh Baba maganar yadda muna dawowa za'a je neman aure. Bikin su Zahra duka duka baifi wata daya ba kuma gashi kace gara a hada"
"Gara a hada din muma sai mu sami sauki"
"Hakane, ga 'yarka can Ghazalatu ta tsaya ruwan ido da ta fitar itama ba sai muyi komai mu gama lokaci guda ba"
"Barni da ita, gobe suna hanya ita da Awwab zan binciketa ko akwai wani"
Hirarsu suka yi irin na 'yan uwantaka suna kulla shawarwari game da yadda bikin zai kasance.
Washegari Awwab ya sauka a garin nasu cike da tsantsar farinciki ya rinka sallama a kofar dakin Mami. Tana sane wai sai ta ja masa rai taki amsawa.
"Mami manaaaa"
Dariya tayi "shigo dai ba don halinka ba"
Da saurinsa ya bude kofar idanunsa suka sauka akan Umminsa Mairama maman Alheran. Murmushi take ta yi masa daga inda take zaune wai wannan muryar Awwab ce. Shi kuwa wani dumi yaji a idonsa da sauri ya karasa gabanta ya riko duka hannayenta biyu ya dago kai yana kallon fuskarta.
"Ummi"
Da hannunta daya take bin fuskarsa tana shafawa "Awwab kaine ka zama babban mutum haka"
Mami tana gefe tana murmushin jindadi Ghazalatu kuma ta coge a bakin kofa.
"Ummina kina lafiya? Kin rinka tunawa dani kuwa" yace yana matse hannuwanta cikin nasa. Yau gashi da Umminsa abinda ya dade da cire rai saboda yadda shekaru suke ta yawaita.
Hawaye ta soma yi "ban taba mantawa daku ba Awwab. Ina ma zan iya ganinka da kyau in gani ko wannan tsayin kamar bulala ka dan cike shi da tsoka"
A razane ya kalli Mami sai ya ga tana hawaye. Hannunsa yasa yana yawo dashi a gaban idanunta ya ga ko gezau. Awwab kasa mallakar kansa yayi ya kifa kansa a cinyarta yana kuka.
"Kaji mutum kamar ba namiji ba, meye na kukan? Ai komai ya wuce da yardar Allah"
Hawaye yake da gaske yaji bazai iya zama ba ya tashi ya nufi inda yasan nan ne dakinsa. Mami tace da Mairama ta dena damuwa zai hakura kamar kowa.
Ghazalatu ko shiga dakin bata yi ba ranta ya baci da kukan da wannan makauniyar ta saka mata shi. A take taji wani haushin Mairama ya kamata. Dama akan wannan da kallo daya zai sanar da mutum daga kauye take yake ta damuwa harda kuka.
"Ghazalatu shigo mana, kinga yayanki na kuka ko? Kada ki damu zanyi masa magana"
Ba yadda ta iya dole ta shiga tana nadamar tahowa don gidan har ya fice mata daga rai. Akwatinta ta tura gefe sai da Mami tace "ga Ummin Awwab ki gaisheta mana"
"Sannu"
"Yauwa sannu 'yata. Yaya gajiyar hanya?"
Mugun kallon da Mami ta watsa mata ya sa ta chanja salon gaisuwar tace "ina wuni" a dakile.
Ba jimawa Mairama ta shiga bandaki ai kuwa Mami rai a bace ta soma yiwa Ghazalatu fada.
"Kar ki yarda na sake ganin irin haka kina jina? Wannan matar da kike gani ba karamar daraja da kima gareta a wurinmu ba. Dangi kowa kokari yake ya tayamu karramata. Bazan lamuncewa dabi'ar banza ba kinzo kina wani cin magan"
Abinka da makaho kunne ya kara fikewa. Mairama tana jinsu tayi murmushi kawai. To dama yaushe zata yi tunanin kowa nasu zai sota. Ita ce fa wadda mahaifinta har yau bai taba bin sawunta ba sai dai ita har sau uku taje kuma tana aika masa da 'yan abinda ba'a rasawa.
"Kiyi hakuru gajiyar hanya ce" Ghazalatu tace da ta tuna Mami ce fa mahaifiyar Awwab.
"A dai gyara"
**********
Fauziyya da Zahra suna kallo a falo Zainab tana duba takardun asibitoci uku da likitann nan ya aiko mata. Ibrahim baya gidan yaje gaishe da kakaninsa Hadir kuwa bacci yake a daki.
Radhiya ce ta fito yau babu hijabi tana dan murmushi fuskarta tasha kwalliua harda janbaki. Fauziyya da Zahra suka shiga gyara dankwalayensu. Zayyana daga shiga deban abinci a kitchen ta kasa fitowa tunda taji muryar Radhiya tana cewa.
"Ha mutum ya fito yasha iskar Allah."
Tana zama su Zahra suka mike, Zainab ta kwashe da dariya. Radhiya ta zama horror tunda tace zata yi musu balotelli. Jiya a gabanta Ibrahim ya nuna musu hoton Mario Balotelli wani dan ball baki na kasar Italy wanda yake kwashe kansa hagu da dama ya bar tsoro guda a tsakiya tun daga gaba har keya.
A karkace ta kallesu "tashi kuma zaku yi daga zamana?"
"Ni bacci nake ji" cewar Fauziyya
"Fitsari zanyi ni kuma" Zahra tace tana matsawa gefe.
"To sai kun dawo, gumi ne ya dameni yau na saka lasi" kawai sai ta tuge dankwalinta rantal ya bayyana.
Wata irin dariya suka kwashe da ita har Zayyana dake kofar kitchen. Zainab na dago kai ta mayar dashi kan takardu kafin ta soma dariya itama. Radhiya ta bata rai "ayi dariya da kyau naje soja na dawo. Kuma na dena daura dankwali iska zan rinka sha"
"Ki rufa mana asiri don Allah ki rufe" Zahra tace idonta harda hawayen ganin wannan gashi na Radhiya tsilli tsilli.
"Allah bazan rufe ba iska nazo sha."
Kyalesu tayi suka sha dariyarsu tana cewa su kiyaye kada tayi sanadin da zaa kai amare da kwalkwal. Daga nan hira ta kaure don daga Zahran har Fauziyya basu da girman kai duk da ba sa'arsu bace. Suna cikin hira ta soma gyangyadi Zainab tace ta koma daki ta soma musu irin na masu magagi wai ba bacci take ba. Kafin la'asar ta bingire akan doguwar kujera abinta. Ana kiran sallah duka suka watse sai Zayyana.
Ta wayar Fauziyya Awwab ya kira yace yana kofar gida don dreban Harun ne ya kawo shi. Zayyana da ta amsa wayar taje ta bude masa gate tana murnar ganinsa.
Suna shigowa falo idanunsa suka gane masa Radhiya. Kanta yake iya gani sai rabin jikinta ta rufa dankwalinta daga kasa kuma fuskarta jikin kujera take kallo. Ya dai tabbatar kayan mata ne a jikin mai wannan kan a sanyaye ya karasa shigowa Zainab tana turo Hadir ya kallesu da tausayawa. Da guda daya tilo da suka haifa ashe dan daudu ne jiya da Mami da Ummi suna bashi labarin komai yana kwalla basu hada masa da wannan ba. [5/22, 10:51 PM] Sis Ruky: Zainab baki yaki rufuwa "Awwab, Masha Allah sannu da zuwa...zauna, zauna kasha hanya"
Shi dai murmushi yake yi amma hankalinsa gabadaya yana wurin wannan kan dake kwance akan kujera. Allah ne Ya taimaka Zainab ta kula da me yake kallo tayi saurin dora yatsanta a baki wai yayi shiru. Dankwalin da Radhiya ta rufe kafa dashi shi ta dauka a hankali ta mayar mata dashi kanta. Sai lokacin ya iya dauke ido daga kanta ya mayar garesu. Gaban Hadir yaje ya durkusa ya rike masa hannu yana jin kwalla ta taho masa.
"Nasan ka gama jin duk wani labari a wurinsu Mami kuma ka gama kukanka. Kayi hakuri ka saki zuciyarka muyi murnar sake haduwa" Zainab tace tana kallon yadda Awwab din ya koma ingarman matashi.
Motsi Radhiya ta soma yi dankwalin yana neman faduwa aka yi sa'a ya zauna. Ita dai Zainab a tsorace take kada ta tashi a hagu su rasa inda zasuyi da ita.
"Ina Ibrahim da Zayyan karami?" Yayi tambayar har ransa yana fatan Allah Yasa ba wannan na kwancen da ya kasa tantance waye ba za'a kira da daya daga cikinsu.
"Sun fita cikin gari amma nasan suna hanya"
Iska ya furzar yana fadada murmushinsa "da gaske? Huhhh Alhamdulillah"
Zainab sai tayi tunanin yana murna ne don tace suna hanya. Sake kallon Radhiya yayi shi dai hankalinsa gaskiya bai kwanta da ita ba. Kamar ta san tunanin da yake a kanta kuwa tayi mika ta tashi zaune. Dankwalin ya zamo daidai lokacin da ta sauke idanu akan fuskarshi. Shi ma ita din yake kallo daga sama har kasa don ya tabbatar da jinsinta sai dai fuskarta ta tsaya masa har ya kasa magana. Kai a lailaye ga fuskarta harda janbaki. A hankali idanunsa suka fara saukowa daga fuskar a kokarin kure mata kallo sai ya tsaya cak a wuyanta ya kasa karasawa yana jin wani yanayi da bai saba ba a jikinsa. A hankali ya furtawa kansa "mace ce".
Tsuke baki Radhiya tayi tana jin ba don Innawuro ce tayi mata askin nan ba wallahi da abinda zata fara yi idan ta koma rugar Barkindo shine ta sauke mata nata gashin. Waye wannan da ya cika mata ido ta kasa sakin baki a gabansa ya gane mata sirrinta. Motsa bakin ta sake yi ko ihu ne ta kwarma musu amma ta kasa. Kumatunta na dama da yake lotsawa idan tayi yunkurin magana shine ya sake daukar hankalin Awwab ya kuma kallonta da kyau.