Batuol mamman complete novel - Chapter 21
Batuol mamman complete novel Chapter 21: Batuol mamman complete novel Chapter 21. "Lallai wannan 'yar wulakanci ce" Radhiya tace a ranta. Ita bata san…
3,353 words
"Lallai wannan 'yar wulakanci ce" Radhiya tace a ranta. Ita bata san maganar wasa bane da zata yi tunanin da gaske aiki zata je yi mata. Hamma Awwab yafi karfin komai a wurinta tunda yake son Umminta da babanta da ita kanta. Kuma ba wani abu bane a wurinta ta taya matarsa aiki amma wallahi ba dai taje a house girl ba. Idan bata gwaba mata magana ko yaya bane tasan bazata ji dadi ba shiyasa ta ajiye katon murmushi a fuskarta tace "ko babu albashi zanyi miki aikin ma, kinsan mu 'yan kauye bamu san komai ba sai bautawa 'yan birni"
"No ki barshi fa bana bukata, idan ina so Yayana zai nemo min"
" Yes dai inzo inyi ko babu komai zan hutar da Hammana barnar kudi"
Hannuwansa ya zuba a aljihu yana kallon ikon Allah. Rigima ke neman tashi tsakaninsu daga su gaisa.
Daure fuska yayi yace "ku wuce ku shiga mu tafi"
Suna zuwa bakin motar Ibrahim zai bude gaba ya shiga saboda yana son Awwab ya koya masa tuki Ghazalatu ta riga shi budewa itama tana son zama kusa da masoyinta. Radhiya da ta fisu iyawa tayi sauri ta shige ta kofar bayan ta haura gaba. Awwab kansa sai ganinta yayi ta kusa fado masa garin sauri. Gyara zamanta tayi ta ballawa Ghazalatu da Ibrahim harara suna tsaye suna kallon abinda tayi.
"Ni dama ga wurina can kusa da Zeezee" Ibrahim yace yana shiga bayan inda Emzee ke yi masa dariya.
Ghazalatu ta kalli Awwab tana jira yayi magana "kace ta koma baya ina son muyi magana"
"Idan muna dawowa sai ki zauna a nan din kinji."
Tsabar bakinciki ji tayi kamar tasa ihu. Mami daga cikin tasu motar tace ta shiga su tafi rana tana kara yi. Hararar Radhiya tayi ita kuma tayi mata gwalo.
"Bansan mutum nayi ba sai naji a jikina"
"Alheran" taji yace muryarsa a dake sannan ya kalli Ghazalatu da take ta cika tana batsewa "ki shiga ki zauna mu tafi"
Daurewar da yayi yasa ta shige ba don ta hakura ba. Radhiya da take kusa dashi kuwa ji tayi kamar ta koma baya ita ma. Tukinsa kawai yake yi wanda baya masa dadi saboda bin bayan Abdallah da dole sai yayi tunda bai san hanya ba.
Motar duk sai tayi musu shiru mai bakin tsoro ya hanata magana Zayyana har ta soma gyangyadi a jikin Zahra. Su basu ma san me yake faruwa ba sai Ibrahim da yake tunanin saboda zaman gaba ne kawai.
Can dai taji shirun ya isheta ta dago a hankali ta saci kallonsa. Titi dai yake kallo har yanzu babu wannan sakin fuskar.
"Hamma" Radhiya ta kira sunansa a tausashe.
"Kar ki dameni please"
Shiru tayi ran sojoji ya baci. Ita kadai zaiyi fushi da ita bai ji masoyiyar tasa tana kiranta housegirl ba. Tura baki tayi ta juya duk jikinta tana kallon waje. Shima satar kallonta yayi yayi gajeren murmushi. Da gaske dai Alheran dinsa bata chanja ba sai ma abinda yayi gaba. Su mata abin rigima baya yi musu kadan ya kula. Su biyun kowa matsayinta daban to me ya kawo rigimar. Ko don Ghazalatu tace mata house girl? Shima kalmar bata yi masa dadi ba. Duka su biyun sai yayi aikin basu hakuri kenan. Haka kawai zasu tayar masa da hankali kamar wasu kishiyoyi. Ta mudubi ya hango Ghazalatu ita ma fuska babu wakwala kamar ma kuka take shirin yi. A take ya jinjinawa masu mata biyu. [5/22, 10:51 PM] Sis Ruky: "Gulmata suka rinya yi maka?" Tayi maganar a cikin shagwabar da batayi niyya ba. Hakan yasa Awwab sake yin murmushi. Daga shigowarsa gidan zuwa yanzu idan ma yana da damuwa to tabi ruwa tabi iska Radhiya ta dauke masa ita.
"Kinki zuwa na ganki ba sai na nemi labarinki ba"
"Ba ga su Mama ka gani ba maimakon kayi hira dasu shine zasu kawo maka zancena?" Ta sake marairaice masa.
"Kinsan me yasa na kasa zama na huta duk da tarin gajiyar da nayi?"
"A'a" tace tana girgiza kai.
"Because I missed you Alheran" yace suna hada idanu tayi saurin lumshe nata.
Tayi karatu bare ace bata jin turanci bata fahimce shi ba. I miss you ai sai masoya a iya saninta. Shiyasa taji wata irin kunya ta saukar mata.
Ko a jikinsa don iyakar gaskiyarsa kenan. Murna da sanin cewa ga inda take ya wadatar dashi ya hana shi sukunin duk wani hutu idan ba haduwa suka yi ba "sai da nazo na ga ashe ni kadai na damu dake, kina kallona kina basarwa"
Maganarsa ta bata dariya kamar yadda ya fadeta yana yamutsa fuska shi ba'a kyauta masa ba "wasa ne wannan amma ni fa ban iya tuna ka ba ne sai labarin da Ummi ta bani"
Hannu yasa ya karbi lemon da Fauziyya ta tsiyaya masa. Sai da ya kurba sau biyu ya sake kallonta "ko kadan?"
"Me?"
"Rashin tunawa dani din"
"Ka ga fa nayi kankanta lokacin"
Gefen girarsa ya shafa "kinga wannan tabon?"
Daga inda take tana ganin duhun layin "bille ne ya karkace? Ko ka hadu da wanzamin da bai san aikinsa ba. Me ya hada tsakiyar goshi da gefen gira? Ko irin na gefen nan mai uku-uku aka so yi maka?" Ta rinka jero masa tambayoyi.
"Na hadu da wanzamiya dai"
Fauziya za ta fara dariya don gidansu kowa yasan tabon aikin Radhiya ne ya kalleta sai ta sake tashi. Wai meye ne Hamma yake korarsu...kodai, kodai...dan murmushi ta saki amma kuwa da tayi farinciki idan haka ne. Abincin da Zahra ta gama hadawa ta karbo don so take ta sake ganin gulma.
"Ana wanzamai mata dama?"
"Alheran sunanta ma"
"Da gaske?"
"Yakushina fa kika yi" yace yana kallon yadda ta ware idano ta saman kofin hannunsa.
Tasowa tayi ta dawo kujerar gefensa yadda zata gani sosai tana ta karkata kai hagu da dama "Allah Hamma, ko dai don nace ban tunaka bane zaka dora min" ta rinka dage girarta duka biyu a tare tana cewa "eyye, eyye?"
"Cute" ya furta a sanyaye ya rasa me yake damunsa tun da ta fito daga dakin. Wasu abubuwa take yi da suke tado masa da memories din kuruciyarsu. Ta bude ido ta lumshe, ta turo baki ta sha kunu ko murmushi.
"Da kina yarinya kin fiye rigima da fada...uhmm harda kuka. Gashi naga alama babu wanda kika dena cikinsu."
"Tsokanata akayi ne, amma yanzu na dena fada"
Fauziyya da ta duka za ta zuba masa abincin a plate tace "A yaushe kika dena fadan?"
"Babu ruwanki da hirarmu bar abincin ma zata zuba min idan na tashi ci. Tafi kawai ki barmu kinsan ba wurinku nazo ba"
Dadi kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha yace ba wurinsu yazo ba. Kai na rawa tana jujjuya idanu tace mata " yehhh sai a tafi kinji me Hamma Awwab dina yace. Dama na fada muku idan ya zo zai dena kula kowa sai ni, nima kuma in dena kula ku ehe"
"Shikenan ka bata damar cigaba da raina mu ni da Zahra"
Kallon tuhuma yayi mata "wai haka?"
"Fada kawai take yi don ta hadamu, kowa ya shaideni a gidan nan wurin girmama manya ba daga nan ba" yanayin maganar kadai zai gane karya taje yi. Bata da innocent face, kana ganinta kasan akwai jini a jika.
"Allah Ya shiryeki Radhiya" Fauziyya tace tana tafiya za ta je kaiwa Zahra tsirku.
Abincin ya nuna mata ta soma zuba masa "ba kya son na kula kowa?"
Ta dago kai "eh wallahi, ko na yau kawai kada kayi musu magana su gani duk kafi sona. Ni kadai ce kanwarka banda su"
"Gobe zan koma Kt ba kya so nayi hira dasu Ibrahim?"
Dena zuba abincin tayi tana jin babu dadi a ranta "gobe kuma Hamma ko sabawa bamuyi ba zaka koma?"
Wannan karon shi ya fara janye idanunsa daga gareta. Ya rasa gane me yasa suna kallon juna sai yaji abu ya taba zuciyarsa. Ya dai alakanta hakan da dawo masa da tunanin baya da take yi ne.
"Akwai wani sabon da ya rage msna bayan wanda muka yi in less than an hour?"
Wuya ta shiga sosawa irin na marasa gaskiya tana sunkuyar da kai da murmushi. Dimple dinnan ya sake kallo ya miko hannu kamar zai saka yatsansa yadda ya saba yi mata a baya ya tallabo habarta da ragowar yatsunsa sai kuma yayi saurin janyewa. Alheran is not a child anymore ya yiwa kansa fada.
"Na yarda kayi hirar minti goma goma da kowa su Baba kuma awa daya, sauran kuma duka nawa ne."
"Bazaki gaji dani ba?" Bai san me ya kaishi yin tambayar ba. Yayi saurin datse bakinsa bayan ta fito.
Da ido daya ta karkace kai tana kallonsa "hmmm na gane wato ka gaji dani ko? Nasan komai idan ana yi min irin haka saurin fahimta nake yi. Kora da hali kake min irin na Ummi idan ta gani da hirata"
Hannu ya daga yana bata hakuri "ba haka nake nufi ba, yadda kike so haka za'ayi. A lokacin kowa ma sai a cire minti daya da rabi in kara miki"
Murmushi ta saki tayi masa gwalo "na maka wayau"
Girgiza kai kawai yayi yana jin nishadi da farinciki suna ratsa shi.
**********
Malamijo ke zaune a tsakar dakinsa akan filo yana sharba gumi. Zafi ya ishe shi daga shi sai dogon wando Hajjo da tayi karkon zama kamar Yadikko saboda bakinta dake kwatarta a wurinsa tana masa firfita.
"Ya kamata kaje asibiti fa, ka kwana ka tashi da abu daya ba'a zauna a gida ba"
Daure fuska yayi ga azaba ta ishe shi da kyar yake magana "zaki biya min kudin asibitin ne?"
"Lallai ma Malamijo, to don Allah zauna kada kaje ka gani idan zan damu. Ka bar kudin kar ka tabasu idan ciwo ya karasa ka a raba mana gado. Nasan a lalace idan ban saka dogon buri ba zan tashi da a kalla shanu uku manya."
Ido ya ware yana jin kamar ya shakota amma jikinsa babu kwari. Ta turo dankwali gaba tana lissafi da yatsunta "kaga mafi girma a ciki in sa a danne a yanka min. In soya, in gasa, inyi miya. Kai har tafasasshe sai naci. Sauran biyun kuma in sayar nayi sababbin dinkuna kafin Allah Ya kawo bazawari"
"Mmmugguwa, saaai kin riga..rigani mutuwa"
"A hakan, karmai-kamai da kai kamar kazar mayu?"
"Akwai mayyyyyyar da ta wuccceki ne?" Yace yana cije lebe.
Yadikko ta dago labule ta shigo fuskarta da damuwa "Malamijo anya zaku cigaba da zaman nan kuwa haka? Use da Asabe fa suma irin lalurarka ta same su. Asabe sai kuka take da kyar na bata hakuri na fito"
Hajjo na jin haka ta tashi da sauri "Yadikko kice ciwon na ango ne da amarensa. Wannan abu shi ake kira guzurin masoya. To ni nayi nan. Kayan lefen can da aka gama gani zan je in killace kada ayi sibare inzo banci nanin ba nanin ta cinyeni ace don ba ni na haifesu ba ina musu bakinciki na bari an kwashe musu kaya"
Fita tayi tana rangaji da dariyar mugunta. Malamijo da amarensa duka sun kasa fitsari. Duka duka Asabe watanta uku a gidan ya cike gurbi da Use. Auren sati uku an wayi gari sun kasa fitsari. Shi tun jiya ya fara gashi yace a matse yake amma ko digo ya kasa yi.
Bata gama gyara kayan ba Yadikko ta shigo babu walwala a fuskarta saboda yadda ta kula yana jin jiki.
"Hajjo me ya kamata ayi ne, rashin fitsarin nan fa ba karamin abu bane. Malamijo sai zufa yaje yi yana numfarfashi"
"Sai kiyi ta damun kanki Yadikko. Akan me? Nan yayi auren nan fa ya soma mana wulakancin da ya saba. Saboda alhaki kwikuyo ne da yace mu dena girki wai ya bamu hutu kannenmu suyi ai ga sakamako nan ya samo. Banda kwadayi irin na namiji yaran da basu fi yayi jikoki dasu ba wai sune kannenmu"
"To dai a bar tone-tone mu kira su Habu yazo ko da motar da yake haya ne a kaisu asibiti. Zan tura a fadawa Salame ke kuma ki kira Innawuro ta fadawa Mairama itama su zo babansu ba lafiya sannan ga karbar lefe ma da basu san anyi ba"
Ido Hajjo ta zaro "Ni shegiya inji dan daudu, da wane bakin zan fada musu mahaifinsu ya kamu da tagomashin soyayya? Kyaleni naji da aike gidan waccan mara mutumcin Salame. Amma Mairama ai akwai kunya taakaninmu, yarinyar mutumcinta yasa yanzu kunyarta ma nake ji"
"Meye kuma tagomashin soyayya ni Yadikko?"
"Sunan da ya dace da ciwon nasu kenan ai"
Yadikko ma dariya ce ta kama ta. Sai yamma aka samu biyu cikin mazan gidan suka dawo. Dama daga Mairama sai taron maza. Matan da suka taso kuma halin Malamijo ke korar musu manema. To yanzu anyi sa'a mutum hudu cikinsu abin yazo tare. An aikawa Salame dan aiken ko kallo bai isheta ba kamar ba kaninta ba. Mairama kuma Bature ne ya kira lambar Baffa Habubakari ya fada masa. A daren ya nemi layin Major ya sanar dashi cewa a fada mata.
**********
Hankalin Mairama ya tashi duk da bata san me ya sami Malamijo ba amma tunda aka fada mata tana ganin ba karamin abu bane. Major ya tsara musu tafiya washegari ganin duk ta tashi hankalinta. Dama motocin da yayi order biyu an riga an kawo su. Daya domin bukatarsa dayar kuma saboda Mami da kuma kai Zayyana makaranta da suke jiran a koma hutu ta fara SS1 sabon zangon karatu mai kamawa.
Jibi zai tafi Sakkwato kaninsa zaiyi masa rakiya su kuma yace washegari su tafi sai su tsaya a Kano su dauki yaran.
"Amma ina ganin motar zata yi muku kadan. Bus din da aka kai Awwab Kano kuma yace gobe zasu dawo. Dreban ya kamata ya huta haka shiyasa ba zan ce ya kwashe su ba"
"Awwab ya tuka ba sai ya bimu a baya ba" Mami tace su kuma dan gidan Hussainarta Abdallah ne zai tuka su.
"Bana son tukin Awwab a babbar hanya gudun nan nasa kamar yana iska".
Mairama ta fara musu godiya sannan tace "da kun barshi Daddy a hakan ma nagode sosai wallahi. Ba sai an sake wata wahalar daukarsu ba. Shima Awwab din yana bukatar hutu"
Mami ce mai kwantar mata da hankali tace "haba Ummin Awwab ki bar wannan godiyar mu dake duka daya ne. Babu matsala in sha Allah"
Babban abinda zai kai Major wanda zasu hadu da Baffa Gide a Sakkwaton shine binciken dangin Zayyan na Nijar. Idan da gaske rashin idonsa a duniya yasa suka zare hannunsu daga kan iyalinsa ko kuma su ma karya Maikudi ya shara musu duk zai jiyo. Shi kanshi sojan da yake tura kudin zai baro bakin aikinsa ya taho don ransa ya baci fiye da ba Major akan rainin hankalin da Maikudi yayi masa. Idonsa idon Maikudi kawai yake jira.
**********
Tun dare anyiwa Zainab waya game da zuwa Sumaila duba Malamijo. Ita bazata sami zuwa ba saboda Hadir gashi asibiti zasu koma. Tunda ba kwana zasuyi ba Mairama da su Radhiya ne kadai zasu kwana sai ta yiwa Ibrahim izinin fita duk da shine karfin taimaka mata akan babansa sai Emzee da yake taya shi sosai.
"Yaya zakiyi da Baba" ya fara cewa da tace yaje.
"Gara na fara sabawa, daga kai har Karami WEAC dinku ake jira a nema muku admission. In kana makaranta zanyi ta jiranka ne?"
Godiya yayi mata don yana son bin 'yan uwansa amma baya son kwana saboda kada aikin yayi mata yawa.
Dakin da aka sauki dreban gidansu Ghazalatu yaje ya tarar da Awwab ya karbi mukullin motar. Kudin mota da Zainab ta bayar a kai masa da zai koma Katsina yaje kai masa. Iyalan gidan su ma duka sati mai zuwa zasu taho Katsinan saboda bikin da yake na gida duka a garesu.
Shi kadai ya koma ciki Awwab ya zauna akan dan ginin da ya zagaye flowers din da aka shuka daga jikin bangon gidan. Waya yake son yi da Ghazalatu yau tun da ya taho tana fushi basu sake magana ba.
Da sauri ta dauka da ya kira sai kuma tayi shiru don ta nuna masa fushinta na kin kiranta da wuri.
"My G fushin ne ya tashi?" Nishadi yake ji sosai yadda suka rinka hira da Alheran kamar basu rabu ba. Kusan komai na rayuwarta da zata iya tunawa ta fada masa sai yake ga kamar a gabansa ta tashi.
"Idan nayi magana kace na fiye kishi ko korafi. Tun yaushe ka isa amma ko text ban samu ba talkless of waya."
Sai yaji babu dadi don ya sani bai kyauta mata ba. Hakuri ya bata don bashi da girman kai ko kadan. Yayi mata laifi dole ya kwantar da kai ya rarrasheta. Kusan wayar minti talatin suka yi sai da yaji ana masa warning na karewar credit.
"Zan kiraki gobe in sha Allah, zamu je duba baban Ummi a garinsu. Dawowarmu sai wurin jibi kenan dasu Mami"
"Mami ba tana gida ba?"
"Zasu taho da Ummina gobe sai mu wuce tare"
"Yayana kace mata zani please. Da saasafe sai na koma gidan mu taho tare"
Yaji dadi sosai saboda shima ya soma kewarta. Suna gama wayar yace ta kira Mami din credit dinsa ya kare. Ta kirata ta wayance da cewa wurinsu Zahra take son zuwa. Mami tace to ta zauna su zasu biyo su dauketa.
Falon ya koma ya same su kowa na cin abincin dare banda Radhiya da tasa plate a gaba tana kallonsu.
Akan doguwar kujera ya zauna ya kwantar da kansa baya. Alamun idanu yaji a kansa ya dago. Ai kuwa duka shi suke kallo har Radhiya
"What?" Yace yana kallon kansa.
Fauziyya ta nuna masa plate din gaban Radhiya. Taliya ce fara da sauce din ganyen alayyahu da ugu sai balangu mai dan karen dadi da Ibrahim da Emzee suka siyo. Dama yanzu sune 'yan zuwa aike.
"Me ya sami abincin Alheran?"
Kunya taji ta kasa fada masa bayan cika bakin da ta gama. Zayyana kuwa tace "kowa shaida ne Adda Radhiya zaki min gyaran akwatina tunda kin kasa"
"Dama akwai abinda zaki kasa?" Yayi tambayar yana kallonta.
Ta dai yi saranda inji bature kaudin nata bai kai nan ba ashe ta gama cika baki. Tana ganinsa taji ko da wasa bazata iya fada masa zaman me take yi ba.
"Emzee me ya kama bakin yayarka ne ta kasa magana?"
"Babu ruwana ni dai" ya cigaba da cin abincinsa yana murmushi.
"Ni bari na fada maka Hamma" Ibrahim yace yana kallo Radhiya ta daure fuska "Zayyana tace kafi sonta shine Radhiya tace don bata nan ne dama. To shine Zayyana tace mata ita fa ko me take so kana yi mata. Idan kana gida hatta abinci tare kuke ci. Shine Radhiya tace wai wannan na gaban nata kaine kace ta zuba muku tare kafin ka shigo. Betting su ka yi"
Zamowa yayi daga kan kujerar yana janyo plate din gabansa bayan ya tankwashe kafafunsa.
"Babu ruwana da wasanninku, Alheran matso mu ci yunwa nake ji"
Bude baki su kayi cike da mamaki harda ita Radhiyan.
Kifta mata ido Awwab yayi a kunyace ta matso ya dauki fork a kan tray din da aka kawo kwanukan abincin.
"Muyi kama-kama irin na yara?" Yayi magana yana kallon idanunta. Tsabar kunya tashi tayi zata gudu.
"Ba fa ki isa ba, wannan abincin na mutum biyu ne so just sit mu cinye"
"Kaci ka rage min Hamma Awwab" tace tana kallon su Zahra tana neman taimako.
"Tare zamu ci kada a barki da gyaran akwati"
"Babu komai zan iya"
Hade rai yayi "ina wasa dake ne?"
Ba shiri ta zauna tana bashi hakuri sai kuma ta waiga tana kallon kowa an zuba musu ido "don Allah ka bari su gama duka su tafi kunyarsu nake ji"
"Kin tabbata zaki zauna muci idan sun tafi?"
"Eh mana"
"Kamar gaske"
Bude baki tayi za ta sake magana kawai ya tura mata fork din da ya ciko da abinci tun dazu. Ibrahim ya dora hannu ya rufewa Emzee idanun da ya zaro sun ga abinda basu saba ba. Zahra ma sai ta rufe nata ta sakalo hannuwanta akan idanun Fauziyya da Zayyana suna faman dariya.