Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 23

Batuol mamman complete novel - Chapter 23

Batuol mamman complete novel Chapter 23: Batuol mamman complete novel Chapter 23. Matsawa yayi gefen Malamijo da yake ta bawa Zayyana da Ibrahim labaran…

3,332 words

Matsawa yayi gefen Malamijo da yake ta bawa Zayyana da Ibrahim labaran kiriniyar Radhiya. Awwab yaso su tafi da gaske. Ya rasa gane kansa da zuciyarsa akan kanwar tasa. Zuciyarsa ta gaza nutsuwa balle ya fahimci me yake damunsa. Har yanzu dandanon sweet din da ta bashi yake ji a bakinsa na daban da lokacin da ya fara sha. Shi kadai yake murmushi yana satar kallonta tana wurin wanke-wanke tana magana da karamar Antinta cikin amaren da za'ayi bikinsu su hudu. Hajjo ta yiwa Mami da 'yan matan tayin ganin lefen kannen Mairama. A lokacin Mairama tace tunda bikin haka yake kurkusa gaskiya ta fasa komawa Rugar Barkindo. Zata jira ayi bikin a gama nan da kwanaki sha biyu sai su wuce Katsina kuma. Idan an gama biki kaf su tattara su tafi. Tasan Innawuro da matan Baffaninta ma zasu zo idan an aika musu. Dakin Hajjo suka tafi su duka kafin a gama gyara inda zasu kwana. Radhiya ta biyo bayansu zata shiga kenan Malamijo ya kwalawa Emzee da ya zage abinsa yana shara kira yana hura hanci shi mai arziki.

"Zayyanu yaka zo, bar wannan aikin zan sa a karasa. Ka raka wannan samarin gonata su gani"

Da baya da baya Radhiya ta dawo "ai wallahi tunda naji muma sai munje. Bari naje na kira su Adda Zahra"

"Ban gayyaceki ba fitinanniya, idan sai kinje ne na fasa kowa ya shiga daki ya kwanta dama kun kwaso gajiya"

"Ni din? Ashe yau rabon kosashiyar saniya za ta kasa ne"

"Buhun ubaki mai idanu a tsakar ka, Qur'anin Allah kika yi min barna a gona sai an biyani" yunkurin tashi yake don ya riga yasan hali. Muddin tace zata yi to da wahala idan basu dawo gida da nama ba. Shi yadda yake tsoronta ma yana tsammanin da kanta zata iya yiwa shanunsa rauni kawai don a yanka.

Awwab da Ibrahim sai dariya suke yadda ta dage sai taje Malamijo ma ya dage.

"Malamijo da dai ka kyaleta tunda kasan ko ka hana sai taje" Emzee yace da sigar laluma.

Malamijo ya tamke fuska yana kallon Awwab "yaro ga amana, idan kuka je ko kaza ce ta sami matsala sai kun biyani."

"An gama Malamijo" Awwab yace yana murmushi. Tsohon burge shi yake kamar yadda Zayyan Tureta yaji farkon haduwarsu.

"Ni nafi zargin ita wannan ce ya kamata ta fito a namijin shi kuma salihin nan ya fito a mace sai aka sami mushkila. Yasin duk mai auren 'Yar soja sai yayi shiri da gaske"

Murmushin Emzee ya fadada ya saci kallon Awwab da duk motsin Radhiya sai ya kalleta a ransa fata kawai yake ya ga ranar da za'a ce sunyi aure.

"Kirawo su idan basu gaji ba" Malamijo yace yana binta da harara. Fatansa Allah Yasa suje su dawo lafiya kada yaji labarin da zuciyarsa bazata iya dauka ba.

Da murnarta taje ta fada musu zasu je gonar Malamijo ganin dabbabinsa. Ghazalatu tana kashingide akan gadon Hajjo tace ita babu inda zata je. Gabadaya ranta ya gama baci da kwanan garin nan. Kana ganin gidan duk girmansa kasan gidan talakawa ne sai wani so ake a burge su. Tana ji lokacin da Yadikko ta tunawa Malamijo kajin da ya bayar ya hadiyi yawu don yayi zaton kajinsa sun sha kafin a sake shawarar kwana. Ba don yaso ba yace a dauka ayi miyar tuwon dare dasu.

Zayyana da Fauziyya tuni suka tashi aka gyara fuska suna murna zasu je. Zahra ma tace bazata iya zuwa ba kan ta ya soma ciwo. Ita dama bata da juriyar tafiyar mota daga amai sai ciwon kai.

Zasu fita Mairama ta dakatar da Radhiya "don Allah kada kije ki yiwa Malamijo barna kinji ko, kuma ana magariba ku dawo"

Dariyar shakiyanci tayi tana kissima me zata yi don babu yadda za'ayi taje ta fito sikau basu ci nama ba. Jama'ar gidan dashi kansa mara lafiyan da amarensa da ta gani kowa yana bukatar protein.

"Haka fa ya cewa Hamma wai ga amanata kada na taba komai. Ni yanzu Ummi da girmana me zanje in taba a gonar nan?"

Da yake Mami ta san waye Malamijo yanzu tun bayan labarin gidan da Mairama ta basu ga kuma sanin da ta yiwa 'yar tata sai ta rinka dariya ita ma. Ghazalatu na jin Radhiya tace Hamma ta diro daga kan gadon tana cewa ita ma zata bisu.

Radhiya ta tabe baki bata manta me tayi mata ba dazu "ba yanzu kika ce bazaki ba?"

"Iska nake son sha" tace fuska ba annuri. Indai Awwab zaije kuma Radhiya ma zata dole ne ta bisu. Bata son wannan likewar da take yi masa daga gani irin abin nan ne na 'yan kauye an ga dan birni ana so a cusa kai ko Allah zaisa yace yana so.

Emzee yace gonar a bayan gari take da 'yar tafiya shiyasa Awwab yace gara su je a mota tunda yamma tayi. Da sauri sauri Ghazalatu ta riga kowa fitowa. Awwab na bude mazaunin dreba lock din ko ina ya bude ta kama kofar gaban mota ta bude ta shige kamar wadda take tsere da wani. Burinta ta riga Radhiya shiga. Awwab na zaunawa ta kalle shi tana murmushi ya daure ya mayar mata. Ji yayi yafi son Alheran dinsa ta zauna ko da irin zaman dazu ne ta juya masa baya.

Duk abinda Ghazalatu tayi na saurin zama a gaban Radhiya ta gani. To dama ita dinma yanzu bata ra'ayin gaban. Bata son zama kusa da Awwab din saboda yadda yake sawa tajita kamar ba ita ba.

Kusa da Zayyana ta zauna a tsakiya tana ta zuba surutu. Awwab ya kasa hakuri ya gyara madubin motar yadda zai rinka ganinta da kyau. Yana saita madubin suna hada ido da Emzee. Hade girar sama da kasa yayi da Emzee ya dago masa hannu yana murmushin tsokana. Kansa ya janye gefe Awwab ya hango Radhiya tana nunawa Zayyana makarantar da tayi primary.

"Ranar hutun da muka gama primary 5 muka yi dambe da Danmama a wurin bishiyar can, ko me yake yi yanzu oho"

"Damben fada kika yi dashi?" Zayyana tace da mamaki.

"Ke baki ji wulakancin da yayi min bane. Malamijo suke zagi ni kuwa na nuna musu matsayinsu."

"Zan so sake ganin Danmama, yanzu sai dai muyi gaisuwar mutumci idan an hadu"

Wani azababben kishi ne ya turnuke Awwab "duk yawan 'yan uwanki basu ishe ki ba sai kin hada da abokin fadanki? Wai shin ke namiji ce ne ma kike fada da maza?"

Ita me tace da zai rinka yi mata fada daga labari. Kallonta yayi ta madubin ta murtuke fuska "kuma idan na zama soja ....."

"Stop dreaming babu inda zaki. Idan bazaki yi karatu irin na kowa ba sai ki hakura"

A duniya ita tana da burin da ya wuce zama soja ne? Duk mai son hanata bai nemi zaman lafiya ba. Ko da kuwa Hamma Awwab din da take ji dashi ne. A take ta bata rai "ai dai Daddy yace zai nema min"

"To zamu gani" yace yana shiga kwanar da Emzee ya nuna masa.

Fauziyya tace "Hamma ka barta tayi kawai mu sami soja mace. Ni har hangota nake yi. Kasan Radhiya bata daukar raini kowa zai shiga hankalinsa"

"Idan kin haifi taki 'yar sai ki turata amma wannan dai na gama magana"

"Kai Hamma kada fa mu ganku a rana wannan kanwar taka bata iya fada ba. Sai ku kwana kuna yi"

Bai ce komai ba yayi parking a gefen gonar. Tun daga inda suke suna iya hango shanu da tumaki. Malamijo fa akwai kudi arziki ne kawai babu don bashi da zuciyar fitar da kudinsa a mora. Kowa ya fita saura Ghazalatu da Awwab a motar. Gani yayi bata da niyar fita ya koma ya zauna yana tambayarta me taki fita.

"Yayana kaki zama muyi hira, nayi maka wani abu ne?" Ta marairaice masa.

Tausayinta yaji domin daga baro Abuja zuwa Katsina, Kano da Sumaila duka tayi dominsa ne.

"Kiyi hakuri, kinga ban samu na zauna bane"

"Amma ka sami lokacin hira da kanwarka ko?" Tace cikin yanayin da ke nuna tsantsar kishi.

"Me yasa Alheran ta tsaya miki a rai ne?"

"Shakuwar taku tayi yawa Yayana, bana son abin ya koma wanda bazai mana dadi ba a gaba"

"Idan zakiyi min adalci Ghazalatu kin sani cewa duk wanda yasanni da su Mami to dole ya taba jin zancen Daddyn Alheran, Umminta da ita kanta ko da sau daya ne. Family dinsu suna da matukar daraja a idanun iyayena" tunawa yayi da zancen rasuwar Zayyan da Daddy yayi masa a daren da zai taho Kano da nanata masa ko bayan ransa ya taya shi rikon amanar iyalinsa. A daren sai da ya zubar da hawaye. Yayi zaton idan ya ga Radhiya kawai shakuwarsu ta baya zai tuna kila ya ga ma ta sauya daga sanin da yayi mata. Sai ya zamana abin ba haka yake ba. Ganin kwana daya Alheran nema take ta shige kowane bangare na jikinsa.

"Tunanin me kake yi ne?"

"Fito muje ba dadewa zamuyi ba" yace yana fita.

Dole tabi bayansa a ran ta tana jin dole ne ma suna komawa ya sanar da nasa iyayen idan ma kudin aure ko saka rana za'ayi duka ayi da wuri kafin abin yazo yafi karfinta.

Yawo su Radhiya ke yi sosai ga masu kiwon dabbobin suna ta bin bayansu ana musu karin bayani. Wurin wata saniya suka je ana tatsar nono. Mutumin da yake tare dasu yace ta haihu ne wani sa ya tunkuye dan makarakin bai shura ba.

"Ina son yin tatsar nima" Zayyana tace da Radhiya wadda lokaci lokaci sai ta waiga baya ta gani ko su Awwab sun fito. Haushi ne ma ya kamata saboda yace bazata yi soja ba a gaban mutane ta yi gaba cikin takaici tana jin zuciyarta tana nauyi.

"Muje na koya miki" Emzee yace da Zayyana bayan ya gama karantar yayarsa.

Irin hular kaba da suke sawa su kare rana mai fadin kasa Radhiya ta gani wani cikinsu ya cire ta dauka ta kwama a kanta ta sami kasan bishiya ta zauna akan wani dutse tana kallon su Fauziyya harda Ibrahim kowa tatsar nono yake yi. Idan wannan ya gwada sai ya matsa wani yayi.

Awwab da Ghazalatu ta gani suna tahowa taji wani abu na taso mata daga kirji har wuya. Rufe idanu tayi ta ja hular ta dora akan fuskarta. Duk abinda take yi Awwab na kallonta har ya karaso inda take. So take ta bude fuskar saboda wani sihirtaccen hamami da yake tashi a ciki amma bata san ta ina Awwab ko Gayanatunsa zasu bullo mata ba. Babu wanda take son gani cikinsu. Wari ne ya isheta ba arziki ta cire hular tayi jifa da ita sai a cinyar Awwab da zamansa kenan.

"Wai Allah, wannan shi ake kira gumama inji takari. Wannan uban wari....."

Kasa karasawa tayi tana kallonsa da hular a cinyarsa tsabar mugunta ta rinka dariya. Shi da budurwarsa suka janyo mata saka hular ai.

"Kina da matsala, kin gama bata rai kin zo kina dariya" yace yana kara rungume hular

"Na ga ka kama hula ka rungume ne kamar ta ka"

Miko mata yayi ta goce da sauri kada ta sake tabawa "nagode, ungo abinki tunda taki ce"

"Warin maza take wallahi" ta kwashe da dariya da ta ga ya tashi da sauri hular ta fadi kasa.

Yamutsa fuska yayi yana kallon yadda take jindadi hankali kwance "wannan wace irin kalma ce haka ko dadin ji babu?"

Idanunta da ya yarda suna dauke masa hankali ta watsa masa "wace kalmar? au wai warin maza. Kada kace min baka ji ba. Dauko ka sansana"

Dukawa tayi zata dauko yasa kafa yayi ball da hular yana kada kai yana kai hannuwansa wurin hancinsa ya kawar da kansa da sauri "dirty girl wannan kika dora a fuskarki"

"Rashin sani, nasan yanzu fuskata wari take yi ko"

"Ban sani ba" yace yana yin gaba. Daya daga cikin mutanen ya tambaya ina zai sami ruwa yace sai dai a rijiyar da suke debowa dabbobin. Ina wani bambanci da hular da ruwan da ya tabbatar shima bashi da tsafta. Emzee ya kira ya fada masa ruwa yake so da sabulu.

Kallon rashin fahimta yayi masa "wanka zaka yi a nan?"

Awwab ji yayi kamar ya hada shi da Radhiya ya musu duka. Ghazalatu da sauran duka kallonsa suke yi.

"Abu na taba zan wanke hannuna shikenan!"

Kamar yadda ya zata su uku suka tafi siyo ruwan da Ibrahim da Zayyana. Awwab ya koma wurin da Radhiya take zaune Ghazalatu za ta bishi Fauziyya ta sako mata zancen bikin da shirye shiryen da zasu yi. Tayi haka ne don tafi son yayansu da Radhiya su fara soyayya taji dadi fesawa Mami. Bata san su ma burinsu ba kenan ga kuma rashin sanin tsakaninsa da Ghazalatu.

Kin yi mata magana yayi ita kuwa ta ga lagonsa ta biyo shi ta zauna a kusa dashi a kan katuwar jijiyar bishiyar da ta fito.

"Ko ba komai na rama"

"A'a kin dai yi kazanta kinji dadi. Me nayi miki ma da zaki rama?"

Tura baki tayi cikin shagwabar da ta koyi yi masa "Cewa kayi fa bazanyi soja ba"

Sai da ya fuskanceta sosai yace "haka kawai kamar courses sun kare a universities ki rasa abin zaba sai soja."

"To, to ni ba so nake na gaji su Daddy ba. Kuma Babana ma ai 'Yar soja yake ce min"

" 'Yar soja da Soja daya ne a garinku. Ki cire wannan tunanin a ranki da kaina zan zabar miki course. Kin ci SSCE din dai ko"

Kumbura baki tayi cikin fushi "naci"

"Bayan bikina gida na zaki koma sai kiyi karatun a Abuja. Gara ku fara shiri da Ghazalatu tun yanzu kada na fita watarana ku tayar min da gida"

"Ha'ann lallai ma Hamma ni bazan yi auren ba har sai kayi na dawo gidanka?" Ya ma za'ayi yace haka. To zaman me zata yi musu idan ba housegirl din da Ghazalatu ta kirata ba.

"Ashe aure kike so, gara da kika fada min"

Hannu tasa ta rufe fuska wai ita kunya "kai Hamma to ai kaine wai na koma gidanka nayi karatu...shi kuma abin sai yaushe?"

"You must be kidding"

"Me kenan ka ke nufi?"

Dariyar da baiyi niya ba ce ta biyo bayan tambayar ta ta. Yarinya 'yar shekara goma sha tara ke zancen aure. Karatu yake da burin tayi mai zurfi kafin maganar aure. Da kyar ya daidaita kansa bayan ya hango irin kallon da Ghazalatu take jefo masa.

"Okay, seriously kina da wanda yake sonki ne?"

Sama ta kalla kamar me tunani "akwai Kawu Zakari sai na koma gida zai gabatar da kansa sosai"

Ransa yaji ya soma baci to amma yanayin maganarta ke bashi dariya "zai gabatar da kansa wurin su Ummi?"

Innocently tace "a wurina dai, ai bai riga yace min I love you din ba"

"Ya Allah" Awwab yace dariya na sake kama shi sosai.

"Don na fada da turanci kake dariya?" Ita bata ga me tayi ba daidai ba. Wato shi yayi aure ita kuma ya hanata cikar burinta na zama soja sannan bazai barta tayi auren ba ita ma sai kace wata alhudahuda zai rinka kira mata karatu.

Sai da yayi dariya mai isarsa ya fadi abinda yaje mata a bazata "Allah Ka bani Alheran Radhiya" yana kallon kwayar idonta.

Wani irin abu ne ya fizgi zuciyarta zuwa gareshi a daidai lokacin taji farinciki ya saukar mata irin wanda bata taba ji ba. A nasa bangaren sai da maganar ta fito ya fahimci nauyinta. Maganar zuci ne ta fito fili. Sai dai kuma shi ya sani cewa zuciyarsa bata raya masa karya ba haka nan bakinsa bai fadi karya ba. Haduwar kwana daya jinta yake kamar basu taba rabuwa ba. Zuciyarsa ta ginu da son wannan yarinyar tun tana cikin mahaifiyarta. Tsayin shekaru bai sa ya manta da ita ba. Ya cigaba da rainonta a zuciyarsa har zuwa haduwarsu ta jiya a inda yadda ta koma ya sake kayatar da ruhinsa zuwa gareta. Da kwalkwalin kan, shirme, shiririta da fada duk yaji ya dauka yana son abarsa a haka.

Dena kallonsa tayi don duk abinta bata da rashin kunyar da zata iya jurewa kallon da yake yi mata.

"Ehemmmm ga ruwa ga sabulu a ina zan ajiye?"

Aikin Emzee ne da tun kafin su karaso ya hangosu suna magana. Allah Yasa Ibrahim da Zayyana sunyi wajen wata tinkiya da take haihuwa ya taho wurinsu shi kadai da ledar purewater da sabulu.

Kumatun Radhiya har wani ja yayi don tsabar kunya ta tashi da saurinta zata gudu.

"Da fuskar taki mai warin maza zaki shiga cikin mutane? Dawo ki wanke"

Emzee bai yi wata wata ba ya arce daga wurin. Ya kamata su Ummi su farga da wuri kafin a laluba a nemesu a rasa.

Sabulun ya bata ya farke ledar purewater din ya dauko daya "fara wanke wannan hannun"

Durkusawa yayi a gabanta tana cuda hannuwan yana zuba mata ruwa har ta gama wankewa.

"Saura fuska" yace mata. Sabulun ta sake sakawa ta dage hijab din ta soma cuda fuskarta ya duku gab da ita "wai nan kunya na baki ne kika kasa magana? Kowa yasan Alheran ta Awwab ce baki da wurin zama sai gidansa"

Kirjinta ne ya soma dukan uku uku ta kasa karasa wanke fuskar ya kuma cewa "cire hannunki in wanke miki"

"Me din?" Tace tare da bude idanun ta da sauri tana matsawa kada yaje ya taba ta. Ai kuwa kumfar sabulun ta shige duka idanun biyu ta soma ihu tana tsalle sai da su Fauziyya suka taho garesu da sauri.

"Kinji dadi kin tara min mutane"

"Ka dena min mita ka hure min idona...wayyo yaji"

Su Fauziyya sun kusa karasowa kuma baya son kowa a tare dasu yanzun da yake shirin daukan duka makaman yakinsa ya nemi daidaitawa da kanwarsa.

"To cire hannun mana"

"Naki wani ne zai shiga"

A daidai nan Fauziyya ta fara zuwa gabanta ya mika mata wani ruwan ta zuba mata ta wanke fuskar. Da kyar ta bari ta hure mata idanun sunyi jazur dasu kuwa.

Awwab da yake jin hankalinsa ya tashi yace mata ya idon. Harara ta maka masa kamar ba shine ya janyo mata ba yana wasu maganganu da suke juya mata tunani.

Ana ta yi mata sannu tace su zo su tafi gida an kusa kiran sallah.

"Mal Da'u yace mu tsaya tinkiyar can da ta haihu yanzu ta kasa" Emzee ya sanar da ita.

Idanun da suka gama yin ja da kumburi ta zaro "ta kasa me?"

"Ta haihu ya kasa cire mahaifar sai shure shure take yi. Yankata zaiyi kawai mu tafi da ita gida idan mahaifar bata fito ba"

"Gida? Da wa? So kake Malamijo yasa ayi muku farfesu na kuci da burodi da safe?"

Ibrahim da Fauziyya suna dariya ta fada musu Malamijo yace ko kazarsa ce wani abu ya sameta ita zai kama.

"Hamma kai ya bawa amana kace ka karba" Ibrahim ya tuna masa.

"Ku muje na ajiyeku kawai na nemi wurin kwana a waje da safe zan dawo daukarku. Naga alama kasawar ma zata yi"

Hankalinta dama a tashe yake ta kyabe fuska yadda Zayyana take yi "bakinka ya sari danyen...."

Da sauri ya dakatar da ita kafin ta karasa fadin kazantar "ahhhhh don Allah kada ki karasa. Bazai sara ba in sha Allah"

Ya kama kansa kuwa ta sami kofar ramawa tayi shu'umar dariyar da sai ta tashi tsokana take yinta "danyen mangwaro fa zan ce ka hanani. Ka ga bishiyarsa can da nake hawa na tsinko mu rinka dangwala da siga"

Shima harararta yayi na daukar hakkinsa da tayi sannan yace "kwadayi, meye abin dadi a danyen mangwaro da sugar?"

"Kai dai kawai ka tsorata kayi zaton danyen ka...."

Wannan karon shine fuskarsa kamar zaiyi kuka baya son jin kazantar da ta dage sai ta fada "habaaa mana Alheran!"

Sai da ta kalli su Fauziyya tace "yanzu danyen kashu din ma ban isa in fada ba? Shima akwai bishiyarsa daga bayan can"

Hatta Emzee sai da yayi dariya saboda yadda fuskar Awwab tayi.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull