Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 29

Batuol mamman complete novel - Chapter 29

Batuol mamman complete novel Chapter 29: Batuol mamman complete novel Chapter 29. Kwana biyar da komawarsu Awwab Katsina. Kullum zai kira Ummi ke dauka…

3,362 words

Kwana biyar da komawarsu Awwab Katsina. Kullum zai kira Ummi ke dauka Radhiya ta kirkiri wani abin da zai hanata karba. To ta karba tace me. Ta barshi da muguwar kewa ya gaza yin abin kirkin da yayi niyya wato zagayen gidajen 'yan uwa. A rana duk inda yayi biyu ko uku sai yace ya gaji. Sai dai fa duk dare suna tare da Ghazalatu wanda hira da ita ke debe masa kewar Alheran kadan. Yana takaicin yadda baya iya sake mata kamar da kuma hirar ma yana yi ne don kada ya wulakanta ta. Abin yazo ya fara damunsa ga tunanin Radhiya da rashin jin muryarta. Mafita ya nemawa kansa zuciyarsa kuma tayi na'am da shawarar.

Major yayi musu bayanin yadda ake ciki Ummi har kuka sai da tayi. Saboda abin duniya Maikudi ya kasheta ita da 'ya'yanta da bakinsa ya rabasu da danginsu.

Su Malamijo kuwa sauki ya samu daga shi har amarensa. Yau gidan an tashi da kukan Asabe tayi rantsuwar ko ana ha maza ha mata sai Malamijo ya saketa don bazata yarda ya kasheta da ciwo ba. Fafur taki karbar girki ita takarda take jira shi kuma yace bai gama cin sadakinsa da kudin da ya kashe na aurenta ba. Rigima taki ci taki cinyewa duk jama'ar gida yanzu sun san lalurar da ta kwantar musu da uba.

Nene tana gogawa Radhiya maganin makeron da ta karbo wanda a cikin sati kan har ya fara hadewa yayi baki ta hanata fita kallon rigimar da take son taje ta yi. Kunkuninta ta gama da zumbure zumbure ta hakura.

"Ni kuwa tun zuwanku Radhiya kinje gidan Gwaggonki Salame?"

"Gaskiya kada kice inje Nene bazan iya zuwa ba"

"Akan wane dalili"

"Ita da ko Malamijo bata zo ta duba ba sai nice zani?"

"Wannan kuma tsakaninsu ne. Ina ruwanki ko ke kika haifa masa ita?"

Ranta dai bai son zuwa ta soma jan hanci Nene ta dungure mata kai "me tayi miki kike gudunta rigimanatu"

Duk wani abu da zata iya tunawa da Salame ta taba yi musu ta rinka daukowa kawai saboda neman dalili. Karshe tace "kuma harda aurewa Ummi baban Danmama. Ai da na sani Ummina zai aura don ma dai bana so kawai kuma ana ta cewa an kusa biki fa sai Ummi ta makance ita kuma Gwaggon ya aureta."

Tashi tayi jin rikon Nenen yayi sauki ta suri hijabinta ta tafi kallon kwal uwar daka a tsakar gidan nasu. Nene ko bi ta kanta bata yi ba sai dogon nazarin da ta samu kanta da yi. Tabbas anyi haka amma tun lokacin bata jin wani yayi tunani a kai ma. Makantar Mairama farat daya tazo duk da an san tana ciwon ido. Bata mantawa ita Mairama ta bawa firinjinta ta sayar wani lokaci suka je asibiti akace babu komai a idon nata. Ko dai da hannun Salame tunda tafi kowa sanin abinda ya taba hadasu da marigayi Zayyan. Saurin kawar da tunanin tayi. Duk bakin halin Salame ace harda makanta kanwarta saboda namiji? Kasa nutsuwa tayi ta nemo yaro cikin yaran gidan ta bashi wayarta ya kira maigidanta. Tayi masa bayanin zarginta ne tace ya kamata a nemo kaikayi koma kan mashekiya.

"Haba Marka ina amfani wata ta warke wata ta makance? Yanzu dai tunda kin fara tunanin haka ki hadani da Mairama ko Radhiya din zan sanar dasu add'o'i da Ayatusshifa a karanta mata ana tofawa a ruwa tasha ta wanke idon. Zamu tsananta addu'a in Allah Ya yarda zamu sami makarin abin indai sihiri ne. Amma kada ki fada mata kada ki tada rigima idan zargi ne kawai. Ki bari mu gwada mu ga ikon Allah"

Godiya tayi masa ta ajiye wayar zuciyarta tana karfafa mata zarginta akan Salame.

***********

Washegari kuwa Nene bata yi kasa a gwiwa ba ta nemi Ayuba. Duk cikin yaran gidan shine ya tashi da ustazanci yana ma koyarwa a Islamiyya. Bayanin mijinta tayi masa shima ya hada da nasa ilimin da kansa ya siyo ruwan roba c'est bon babba yayi mata tofin nan yadda ya kamata. Ranar shi wuni tana sha tana shafe ido. Nene tace mata su gwada ko za'a dace ne ta karba da murnarta.

Bayan kwana biyu Ummi ta fara jin jikinta yana canjawa tafi jindadinsa sosai gashi ruwan tofin saura kadan. Radhiya ta nema saboda ta jiyo muryarta tana cewa Malamijo yau kwadayi take ji yana rantsuwar kada ta bishi gonar da zai tafi a lokacin.

"Kin raina min uba ko" ta tambayeta bayan ta amsa kiran.

Sanye take da riga da skirt na atampa ta gama shirinta da hijab ruwan madara wanda ya dace da kayan iya gwiwa za ta bishi gona tayi barna.

"Ummi balance dayet muke bukata"

"Allah Ya shirya min ke, zo ki dauki kudi ki siyo min ruwa irin wanda Ayuba yayi tofi a ciki. Ki siyo guda uku sai a ajiye"

Murmushi tayi "Ummi kin fara gani ko dan dishi dishi?"

"Ke dai ki sakani a addu'a ido ya bude na ganku ke da kaninki"

"Amin Ummi, wayyo dadi"

"To wuce ki tafi banda yawo" sai ana jaddada mata kamar karamar yarinya.

Tsokanar Ummin tayi tace "Ina zani ko azahar ba'ayi ba inje basu gama abinci ba balle na sa rai da balance dayet din"

Muryar Malamijo ta ji yana magana daga soro ta yi murmushin mugunta. Daga masa hankali zatayi tayi ta binshi yana fada ta dage gonar zata je tunda a kafa yake zuwa. Sai sun isa wurin shagon da zata je sannan zata rabu dashi.

Da dan gudunta ta taho kamshi da idanun da suka kafeta a gaban Malamijo suka kashe bakin da jikin nata baki daya.

Wani murmushi Awwab yayi mata ta mayar masa idanunsu sarke da na juna. Malamijo bai kula ba yana ganinta yace "Allah Ya taimakeni yau ga yayanku na Katsina yace sako ya kawo muku ke da Mairama. Idan kika sake kika biyoni zai koma da kayansa sai in ga karyar cin balanciye din"

Ficewa yayi ya barsu a tsaye. Wani irin kallo yake yi mata taji ta takura.

"Muje wurin Ummi din" tace bayan ta juya masa baya saboda wani nauyinsa da take ji.

"Wait"

A nutse ya tako ya dawo gabanta ya tsaya. Jeans navy blue da layin fari da ya dusashe daga tsakiya ta gaba da shirt mai maballai ruwan toka ya lankwashe dogon hannunta zuwa rabin hannun. Fuskarsa a gyare sai hancinsa ya kara fitowa. Kanta ta sunkuyar ta ma kasa kallonsa.

Da wannan muryar tasa mai kauri da tafiya da hankalinta yace "baki tambayeni me ya dawo dani ba, ko dama kinji a jikinki zan zo?"

"Ba wurin Ummi kazo ba?"

"Basarwar ce?" yayi tambayar yana son sake hada ido da ita.

Hijabinta ta janyo gaban fuskarta zata rufe ya girgiza mata kai.

"Ahhh" yace yana mata alamar ta bude baki.

Kafada ta noke tare da murmushi.

"Please Alheran"

Sake nokewa tayi yace "dadin abin tare muke da My G tana mota"

"Ahhhhhh" tace da sauri har tana bashi dariya domin kuwa ya gama tabbatarwa ba shi kadai bane ya fada wannan kogin da baya fatan fita.

Irin sweet din rannan ce dai wadda ya taho da ita daga Germany ya fito da ita daga bakinsa ya kankance ido yana kallonta "See what you did. Kin cikani da surutu kinsa na kusa shanyewa"

A bakinta ya saka mata kunya tasa ta rufe ido da tafin hannunta.

"Kinsan wani abu" ya bijiro da maganar don kawar da hankalinsa daga kallon bakinta da take shan sweet din dimple dinta da yake matukar burgeshi yana ta sake shigewa ciki.

Kai ta girgiza masa ya dawo gefenta ya tsaya "ta kare miki Alheran auren dreba ya tabbata a gareki"

"Ni dai a'a"

"Are you sure? Ko da dreban mutumin da kike shan sweet din bakinsa ne?"

"Ya Allah" tace yadda yake yi idan yaga abin mamaki tana jin wani irin farinciki mara misaltuwa.

"Na sani ai bazaki so kada ta kare miki ba in dai shine"

Kokarin saita kanta tayi ga murmushinta yaki bacewa "inji wa"

"Ba sai munje nan ba kawai ki amince kamar yadda na amince"

Cike da shagwaba tace "Ni dai wallahi...."

"Me? Ba haka bane?"

"Alawar ce ta kare" tace tare da yi masa gwalo ta soma tafiya da sauri.

"Zaki aureni?"

Ita ce tambayar da taji ya jefa mata a daidai lokacin da kafarta daya ta fita daga soron. Tsayawa tayi a wurin ta kasa gaba ta kasa baya har ya karaso inda take ya rabe ta gefenta ya wuce har cikin tsakar gidan da sallama yana kiran Ummi. [5/22, 11:03 PM] Sis Ruky: Asibitin Nasarawa aka tura su Awwab domin samun kwararren likitan ido. Da za'a basu daki yace dakin mutum daya yake bukata kada a hadata da kowa. Sunyi sa'a kuwa an samu. Dakin a gyare yake amma duk da haka ya dage sai an sake karkade shi an wanke toilet. Da ya ga matar zata yi masa gardama wai sai da safe zata sake zuwa ya bata dubu biyu. Kafin Mama ta iso da su Emzee da 'yan tarkacen bukata na kwana irinsu bargo da zanin gado an gyara dakin.

Daure idanun Ummi aka yi da farin bandeji likitan yace bazai bude ba sai gobe a wurin gwajin ido. Budewar idanun lokaci daya da yawaitar haske ne ya janyo mata wannan ciwon kan saboda haka tana bukatar hutu. Da an sabunta mata glass din ido komai zai daidaita in sha Allahu.

Emzee fa rai bai so ba. Abinda aka fi gani wurin Radhiya yau sai gashi yana yi. Zama yayi kusa da ita a kan gadon yana rokonta wai ko dan yaya ta janye daurin idon ta kalle shi.

"Kayi hakuri mana Zayyanu gobe fa za'a bude mata."

"Nene shikenan sai ta kwana ni bata ganni ba." Yau abin nasa harda turo baki musamman da Radhiya take masa gwalo.

Ibrahim ya kalli yadda yake yi ya jinjina kai "yau kuma Zayyana ka koma? Ita ce bakinta kullum a tabe tsabar shagwaba"

"Kai kuma sarkin sa ido ko" inji Mama ta kalli Emzee tana bashi hakuri.

"Ka fita idona Surbajo" ya yi maganar yana nuna shi da dan yatsa.

"Sunan nan ya fita a bakinka fa"

"Kunga ku tashi mu tafi haka nan kafin ku cika mata kunne. Ummi bari mu gudu dare na kara yi"

Kwanukan da suka bata na abinci Radhiya ta hada zata kai mota Mama tace tayi musu sai da safe don tare zasu wuce Nene kadai ce zata kwana.

"Wayyo Mama nidai ki barni"

"Shagwababbun da yawa ashe, ai kuwa sai mun tafi don bazan bari ki zauna ki dameta ba"

Ibrahim da Emzee suka soma tsokanarta. A bangare daya kuma tasu rigimar su biyu bata kare ba. Mama dai kada su tayi duka suka fito wurin da ta ajiye motarta. Layin Awwab ta shiga nema don ya kusa awa daya baya dakin daga zuwa amsa waya.

Ghazalatu ce take kiransa dama shiyasa ya fita daga dakin. Mota ya koma suna waya. Ta sanar dashi cewa tana tunanin Daddy Haroun yau ya yiwa Alh Baba zancensu don ta ga ya tambayeta da safe. Hira yake da ita babu wannan irin dokin da yake ji akan Radhiya da ya hadu da ita kwanaki kadan da suka wuce. Har ga Allah sai yake jin babu dadi saboda baya son zama maci amana kuma baya son wulakanta kanwarsa. Biye mata yayi suna hirar kawai don ya faranta mata.

Wayar Mama da take ta shigo masa yace mata yana zuwa ya amsa kiran.

"Awwab ina kayi parking ne? Ka taho mu tafi gida don nasan bazaka gane hanya ba. Nima ba don Ibrahim ba bata zanyi"

"To Mama gani nan"

Zagayawa yayi inda suke Ibrahim da Emzee suna rige rigen shiga tasa motar saboda rigimarsu ta dazu tace Radhiya taje ta shiga su bisu a baya. Ibrahim da Emzee su shiga tata.

"Amma Mama ba mune maza ba sai mu bishi ki tafi da ita" cewar Ibrahim suna hada ido da Emzee suna dariyar shakiyanci.

"Ita tasan hanyar ne? Ko mu biyu kuke son mu bata?"

"Sai ku biyo mu a baya. Amma a haka kamar kinfi son ta bishi"

Ganin idon Mama kadai ya hana Radhiya kaiwa Emzee duka. Kunya ce ta kama ta sosai. Allah Ya taimaketa Mama ta kama kunnuwansu shi da Ibrahim ta gwara musu kai sannan tace su wuce itama tana murmushi.

Kwandon kayan abincin da ta dauko Awwab ya karba ya ajiye a baya sannan ya bude mata gaban. Ibrahim da Emzee kamar ba fada suke ba suka sake kwashewa da dariya harda tafawa.

"Shakiyai Allah Ya shirya min ku" Mama tace kawai tana tada mota.

Radhiya a kunyace ta shiga motar duk da cewa dazu tare suka zo a hakan daga Sumaila amma da Nene da Ummi. Yanzu kuwa su kadai duk bakin ma sai ya mutu. Bangaren window ta karkata gabadayanta tana kallon waje.

Yatsantsa ya kada mata ta juyo amma taki kallonsa "tunanin me kike yi?"

"Babu komai"

"To in baki abin da zaki je kiyi tunani a kai?"

Da ka ta amsa masa yace "baki da wani course da kike sha'awar karantawa?"

"Duk ban sansu ba, soja kawai na sani"

"Sojan ma ai yana karatu"

"Training din kuma ayi yaushe? Na zata fada kawai ake koya musu da harbin bindiga"

"Sai kace wasu 'yan ta'adda? Kinga kamar Daddy da yayi soja amma computer engineer ne."

Dena kallon wajen tayi ta gyara zamanta yana mata bayani yadda zata gane.

"Kin dami mutane da son zama soja bayan baki san komai akansu ba"

Baiyi tsammani ba kawai yaji tace "Hamma ka zaba min wanda kake so in karanta"

Kallonta da ya tsaya yi saura kiris motar Mama ta bace masa "kina son mass comm.?"

"Na 'yan jarida?"

"Yes"

Zata bashi amsa wayarsa ta hau ruri. Da yake a kusa da giya ya ajiyeta idonta ya kai inda hasken yake ta ga ansa My G. Wani irin abu taji ya soki zuciyarta ta dauke kai da sauri ta koma kallon waje. Awwab sai yaji gabadaya hankalinsa ya tashi. Wai haka ake yi da mata biyu dama? Shi tun kafin yayi auren kowacce yana kokarin ya ga ya kawar da abinda zai tuna mata da 'yar uwarta saboda alamun kishi da yake ganin suna dashi su duka. Wannan shine dauko ruwan dafa kai. Bai taba tunanin hada girlfriends biyu ba ma a lokaci daya balle mata. Shi irin mutanen nan ne da rigima ta taho ta hagu sai yabi dama babu karkace hanya. Duk abinda zai tada masa da hankali gudunsa yake. Shi kadai yake kwankwasar kansa da cewa sai ya jajirce ne fa komai zai tafi daidai. Yadda Alheran tasan ba ita kadai bace yana komawa Katsina gobe Ghazalatu ma zata sani. Kai iyayensa ma zasu sani don ya fara ji a ransa wannan shekarar da ya diba ko kadan bazai iya jira ba. Zamanta yanzu cikin motar ba karamin jinsa yake a ransa ba. Kiran ya katse wani ya sake shigowa ya dauka yace mata tuki yake zai kira idan ya tsaya.

Radhiya kuwa sai juya sunan take a ranta wai My G. Lokacin da ya gabatar mata da ita tun farko da haka ya ambaceta amma yanzu tafi jin abin a ranta. Har ya gama wayar bata kalle shi ba. Tunawa tayi da wayar da ya bata wadda bata samu nutsuwar dubawa ba ta dauko a hankali harda karewa da hijab don kada ya ga me take yi ta budo wurin sunaye. Suna daya tal ta gani a cikin contacts din. Hamma. To saura fatan akwai kudin kira. Satar kallonsa tayi idanunsa akan titi yana tunanin yadda zata kaya masa gobe a Katsina yaji waya ta sake kara. Ko kalla baiyi ba tunda yace zai kira yafi so ta kyale shi ya kira din.

Kamar ba wadda ranta yake a bace ba Radhiya tace cikin karamar murya "Hamma ana maka waya"

"Bari kawai zan kira idan na tsaya"

So take ta ga da wane suna yayi saving number dinta. Ko bai ma saka sunan ba. Gashi ya tura wayar a aljihu.

Da ta katse sai ta sake kira "Hamma ka dauka mana"

"Yadda kika bata rai dazu idan na dauka kila kuka zaki yi min" yace daidai lokacin da Emzee yake bude gate Mama tana shigar da motarta Ibrahim kuma ya shige ciki ya fadawa kawunsa kanin Baba da ya zauna dashi sun dawo.

Sake kiransa tayi na ukun ta turo baki "ni dai ka duba mana"

Bai taba kawowa ita ke kiran ba ya dauko wayar da saurinta kuwa ta leka. Shi yana mamakin kiran me take yi masa ita kuma tsabagen bakinciki tana mamakin wannan wane irin suna ne ya lakaba mata.

"Meye wannan Hamma? Nawa sunan kenan, meye sha...sha me ma?" Ta daga kai tana kara kallon rubutun wayar kuma ta katse bata gama hada harufan ta karanta ba.

Idanunta taf da kwalla ta dagosu ta zuba masa "sake nuna min nawa sunan" tace kamar me bashi umarni. Ya kuwa danno sunan nata ya bata wayar.

Kallon sunan ta sake yi ta ma kasa karantawa. Wata uwar harara ta doka masa ta kama kofar zata fita ya danna lock kafin ta bude.

Dukan kofar ta shiga yi "ka bude min in fita, kuma na fasa soja zanyi, kuma likita zan aura"

"Allah baki isa ba Awwab ne mijinki"

"Ni na fasa ka bude min" sunan kawai take tunani ranta yana kara baci. Anya ma ba shashasha yake nufi ba. Kwafa tayi tana jinjina kai.

"Calm down Schatzi, me ya faru?"

Sai ga digon hawaye ya ziraro "nice shazi din? Ni ko? Ni ko?"

Dariya ta bashi yadda ta kwabe fuska da gaske wai ranta ne ya baci. Gyara motar yayi a cikin gidan suna kallo kowa ya shige ciki ya sake tambayarta ta fada masa laifinsa.

"To ba kaine..."

"Me nayi ni Hamman Alheran sarkin laifi"

Sai kuma taji nauyi amma dai dole ta fada ayita ta kare. Bazata yarda kawai don ita tana da hakuri ba a cewarta kuma yayi mata haka tun yanzu ba.

"Ita da ta kiraka ba my G ka saka mata ba...."

Ido ya lumshe yana dariyar kuruciyarta "shine kika kira ki ga me na saka miki?"

"Eh, kuma kiran yayi min amfani gashi ni nawa sunan ko ma'ana babu. Mu sake gani ma don na kasa karantawa"

"Schatzi" yace da wata irin siga da ta sauke mata tarkacen rigimar da ta debo ba shiri. Idanunta yake nema su hada da nasa taki dagawa "Schatzi yana nufin sweetie in german." Cusa kanta kawai tayi a tsakanin cinyoyinta saboda tsabar kunyar da ta dirar mata. Tana ji yana tambayarta "Idan kuma ba kya so sai na koma kiranki my A. Bari na chanja miki" ya fara danna wayar.

"Don Allah ka bari"

"Kina so?"

Ta wani rufe fuska tana dariya ya kada kai ya bude motar suka fito tare. A daidai bakin kofa zasu shiga ciki yace "rigimammiyar Awwab". Da dan gudu ta shige ciki ta barshi a nan yana jin kamar an bashi dukkan farincikin duniya.

**********

Washegari Awwab bai bar Kano ba sai da ya tabbatar an gama komai na gwajin da za'a yiwa Ummi. Ko kwandala basu biya ba shi yayi komai. Ummi da Nene sai addu'a kawai suke masa yayin da Radhiya take jin sonsa yana kara shigarta. Duk wanda zai mutunta maka iyaye hakika masoyi ne na kwarai.

Ya fito daga dakin zasu raka shi bakin mota Emzee ya kawo mata wayar Ummi "Kawu Zakari ne yake son magana dake"

Murmushi ta saki ta mika hannu zata karbi wayar "Allah Sarki Kawu Zakari kwana biyu"

Yadda Awwab ya juyo da sauri Emzee sai da yaja baya ya fasa bata wayar.

"Ba ka gaisa dashi ba?"

"Eh mun gaisa"

"To kace tana gaishe shi, ke kuma muje ki rakani"

Sumsum ta wuce Emzee ya yi murmushi. Hamma yana burge shi kuma ya tabbatar da gaske yake son 'yar uwarsa shiyasa yake kara ganin girmansa. Mutum biyu ne damuwarsa a duniya, daga Ummi sai Adda Radhiya. Farincikinsa shine ya gansu cikin farinciki da kwanciyar hankali. A dole yayi masa karyar bata kusa. Yace to babu matsala gobe suna tafe duba Ummi dasu Innawuro.

Saboda tsokana Emzee sai ya daga murya yadda zasu ji "Adda yace zaku hadu gobe zasu so duba Ummi"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull