Kenza eBookz

Batuol mamman complete novel - Chapter 32

Batuol mamman complete novel - Chapter 32

Batuol mamman complete novel Chapter 32: Batuol mamman complete novel Chapter 32. Motsi kadan Radhiya sai ta kalli wayarta babu kiran Awwab. Yadda baiyi…

3,356 words

Motsi kadan Radhiya sai ta kalli wayarta babu kiran Awwab. Yadda baiyi bacci ba jiya yau ma hankalinsa gabadaya ya tashi ne saboda rigimar dake neman kunno kai a gidansu. Mami da Daddy sunje har gidan Alh Baba akan ya duba lamarin wanda zuwan nasu ya sake harzuka shi. Mummy da ta sami labari ko kallon arziki ta kasa yiwa yayarta. Ga Ghazalatu ta kwana kuka kuma tsabar wulakanci ko aurenta ba'ayi ba ace suna rokon a auro harda wata. Domin su tsayar da abin haka suka yanke shawarar bari a fara bikin da Ghazalatu. Idan yaso bayan ko da rabin shekara ne Daddy zai sake yiwa su Alh Baba maganar. Kwanaki biyu suka yi ana wannan tashin tashina.

A Kano kuma Mama ta bude wuta wurin gyara 'yar uwarta Ummi da 'yarta Radhiya. Salon ta kai Mairama da aka gama gyara kan akayi steaming sai ta sake komawa yarinya kyaunta ya kuma bayyana. Radhiya ganin Umminta a steamer harda kuka wai ita ya kamata a yiwa wannan gyaran amma saboda Innawuro bata sonta gashi yanzu tana ji tana gani babu damar shiga. Mai salon taji sai mita take tana fulatanci tana hausa ana ta kiran Innuwuro tace mata tazo ta shiga.

"Soya min fatar kai zaki yi ko"

Matar tayi dariya "gyara dai kanwata"

Bisa tsautsayi ta tuge dankwalin Radhiya wai zata yi mata gyara kyauta sai abin arziki ya bayyana kowa ya gani. Allah Yasa kan ya hade yayi baki sidik gashi ya soma tofowa. Amma duk da haka ranta ya baci ta tashi ta hade fuska tana kallon matan da ake yiwa gyara.

"Yasin mace tayi dariya in rangada mata balotelli ta tafi dashi gida"

Kana ganinta kasan ko bata aikata ba to dai zasu ji ba dadi. Mai salon ta koma bata hakuri sannan tace tazo tayi mata gyaran farcen hannu da kafa da steaming din fuska. Shikenan ta manta da fushin ta shiga jerin gyara tana ta firirita yau gata a salon. Kafin su bar wurin tasa mata da yawa dariya.

Washegari ana gobe zasu tafi mai kunshi tazo ta rangada musu baki da ja. Ummi dai safa ta saka a kafarta tana jin wani iri. Rabonta da ado haka tun Zayyan bai tafi Liberia ba. Yanzu kam wa zata yiwa. Nene kuwa sai zuga Mama take yi wai a gyare mata 'yarta ta samo miji dan ubansu.

Radhiya da Emzee suka taru suka rafka mata uwar harara sai da Mama ta hade kawunansu ta gwara.

"Nenenmu kuke harara"

"Mama wai miji fa take cewa, Ummi ke da aure sai a aljanna ke da babanmu" Emzee yace da dukkan seriousness.

"Maza iyayen kishi" Mama tace tana tuna lokutan da Ibrahim yake yi mata kunkuni akan me yasa ta tafi tabar babansa.

Ranar wuni suka yi ana ta gyare gyare saboda tafiyar su Mama da ta matso kusa sosai. Ibrahim zai koma gidan kakaninsa ya jira dawowarsu. Da safe ta kaisu tasha. Nene tayi ta yi musu addu'a ita da iyalinta tana fatan Allah Yasa a dace mijinta ya sami lafiya ya dawo da kafafunsa. Kamar kar su rabu ita da Ummi. Emzee ma dai dokin budewar idanun Ummi yasa zai bisu Sumaila. Ba don haka ba jira zaiyi sai sun tashi nan da kwana biyu sannan ya koma.

Sai da suka tashi Mama ta koma gida tare da Ibrahim mai nuna hanya. Suna isa Aisha 'yar wajen Alh Musa ta kirata. Sun gaisa da ita da kanwarta tace mata ga Mamansu su gaisa. Matar mai mutumci suka gaisa da tambayar juna iyali.

"Antin yara na bugo ne nayi miki godiya irin dawainiyar da kika sha da yaran nan. Na dawo gidansu biki ya matso babu abinda baki saya kin ajiye ba. Don Allah ina rokon mu cigaba da zumunci."

"In sha Allahu. Nagode"

"Ina fata kuma zaki zo bikin 'ya'yan naki"

"Ahhh banyi alkawari ba."

Nunawa tayi bata ji dadi ba har tana tambayarta ko don sun rabu da Alh Musa ne. Mama tayi dariya tace mata tafiya ce a gabanta zata kai mijinta asibiti. Maman su Aisha ta tausaya mata ta kuma jinjina mata wannan sadaukarwa da ta hanata zama gidan mutum kamar Alh Musa mai kudi da halin dattako. Bata yi kasa a gwiwa ba bayan ya dawo daga wurin aiki ta fada masa. Abin yafi taba shi duk da yasan ta koma gidan tsohon mijinta amma sai da yaji wani iri. Soyayyarta da tausayinta duka a hade. Nasa salon kaunar shine ya tura mata miliyan biyu da rabi a matsayin gudunmawa. Mama tayi kuka a ranar yadda Allah ke budawa bawanSa a lokacin da bai taba tsammani ba. Aurenta da Alh Musa ta yarda silar arzikinta ne da nemawa Hadir waraka.

A Sumaila kuma su Ummi sun isa gida ya fara cika da 'yan biki. Yawanci 'yan uwansu ne na bangaren Malamijo. Washegari kuma sai ga dangin iyayen amaren mata su ma sun fara zuwa. Innawuro da matan su Baffa Gide duka sun iso. Ranar ne za'ayi Kamu amare kowacce dangin uwa na kokarin rufa mata asiri. Shi dai Malamijo tunda ya bada abinda zai iya ya janye hannuwansa. Duk wannan abu da akeyi Salame bata samu zuwa ba saboda bata ma da kayan sawa ta shiga taro ga yunwa kamar taci babu ita da 'ya'yanta.

Ranar da yamma Nene ta rufa mayafi ta tafi gidan Salamen. A gaban murhu ta sameta tana ta uban kauri. Tsaki ta samu zata yi musu danmalele ita da yaranta suci. Girman kai ya hana ta kwantar da kanta gaban mahaifinta komai lalacewarsa ta nemi taimako. Taji labarin Mairama tana gidan amma bata gabanta tunda tasan ba ido gareta ba bata da abinda zata tsinanawa kanta ma. Kauyen da akace ta koma na dangin babarta ta tabbatar kila wahala kawai take sha daga ita har yaran. 'Yan lokutan da suke zuwa Sumaila lokacin tana shanawa a jikin Indararo bata ma zuwa gidan don kada a fara yi mata bani bani. Sai gashi a kasa da shekara guda duniya tayi mata juyin waina...sama ya koma kasa.

Idanu jazur ta dago tana fyace majina da gefen mataccen zaninta sannan ta kakalo murmushin dole.

"Nene kece a gidan namu yau?"

Rai a bace Nene Marka tace "nice Salame, cewa nayi bari nazo na gaishe da hamshakiya matar Alhaji tunda kinfi karfin kowa."

Kamar wata gaula tana fama da cikin da yake neman rinjayarta tace "to ni me nayi"

"Ban sani ba Salame. Mahaifinki ya kwanta ciwo yaci ya cinye har ya warke babu ke babu inuwarki balle asa rai da mijinki ma zai je. An kai lefen kanenki baki je ba yanzu don tsabar bakin hali ana biki a matsayinki na babbar 'ya a gidan kin gagara zuwa kuna gari daya. Anya Salame kin dauko hanya mai bullewa kuwa?"

Da kunya taje gidan nan bayan kowa ya santa a lokacin da take tsaka da jindadi dama kiris 'yan bakinciki suke jira ayi mata dariya. Jiya Ta Madina tazo har gidan itama ta kare mata tanadi wai kanwarta ta haihu bata je ba. Yaran da suka gama rainata suke murna da talaucinta.

"Kin dai ga yanayin da nake ciki dama shi kuke buri shiyasa babu wanda ya damu dani"

"Kaniyarki, idan zakiyi fitsararki kada kiyi min bazan miki da dadi ba. Idan ban ganki a wurin bikin nan gobe ba wallahi sai na saba miki. Mutuniyar banza wadda bata sawa zuciyarta komai ba sai kyashi da hassada. Malamijo ya cuceku wallahi"

Bayan fitarta Salame kuka ta saka. Tana ji tana gani ta zama bolar gida kuma miji yaki ya saketa ko tasan matsayinta. Tana cikin wannan halin ne kamar daga sama Halifa yazo. Matashin saurayi dan gatan Alh Salisu. Yaron babu abinda ya nema ya rasa a wurin mahaifinsa sai dai abu guda. Da matukar wahala babansa yake bashi kudi idan zai zo Sumaila. Da can yana bashi sai ya zamana Salame tana karanta masa bukatunta idan zai sake zuwa. A hankali Alh Salisu ya fahimci cewa kudaden da yake bawa dan nasa aikinta ne ko kunya babu. A yadda yayi matukar tsanar halinta tuni ya dakile hakan. Taje can ta karata idan Halifa ya soma sana'a yayi mata da nasa gumin.

Tsabar murna ji tayi kamar an ga watan sallah. Ta rasa inda zata saka kanta don dadi harda yada habaici wa Maman Danmama danta yazo. Shi dai kunyar irin wannan abubuwan nata yake yi to amma uwa uwace. Bai wani dade ba da zai tafi ya bata dubu biyar cikin abinda ya rage masa. Salame duniya tayi dadi ta rasa ina zata kai farinciki. Dreba ne ya kawo shi kuma yana jiransa ya tafi dashi. Dan cikinta a wannan hadaddiyar mota harda dreba. Kai inama dai ta kwantar da hankali a gidan Alh Salisu.

Washegari bayan sunci fara da mai harda hadin salak da kifi sukunbiya ta shirya 'ya'yanta kowa cikin kayan sallarsa na bara kafin Alh Indararo ya banzatar dasu. Itama wani leshi ta saka cikin irin alkhairin da ta samu albarkacin aikin malamin tsibbunta wanda ya fita yayi yanzu. Mayafin ma irin mai bakin leshi da ta dade da dena sakawa ta dauko don na yayin duk sun mutu babu na mora.

Tana tsakiyar yaranta dayake tafiyar kafa ce zata kaita gidan tana murmushin jindadi. Yau 'yan bakinciki sai dai su mutu. Tana nan kuma har yanzu tana damawa don tasan da wuya a sami mai dressing irin nata.

Ta kusa gidan bai fi taku kadan ya rage ba ta ji dirin motoci a bayanta sun taho a guje. Kana ganinsu kasan tafiya ce ta jerentawa wato convey. Motoci ne da suka amsa sunansu mota masu masifar kyau da daukar ido duka a maimakon nambar mota an rubuta G. AGALI wato Ghousman Agali kakan Zayyan Muhammad Tureta na wurin uwa.

Guda takwas ne sai kuma helux guda biyu da aka ciko su shakare da buhun hunan kayan abinci da lemuka na kwali da na roba. Mota cikon ta tara da ta fita daban da sauran duk da cewa itama tana da kyau sosai Awwab ne a ciki. Shine yayi musu rakiya zuwa garin Sumaila domin cika umarnin mahaifinsa da hada masoyiyarsa da dangin mahaifinta. Daga ita har Ummin an kasa samunsu a waya bare a sanar dasu zuwan bakin.

Sanye yake da wando chinos mai kyau coffee da shirt cream wadda ta dan kama shi. Idanunsa ya karesu da bakin glass wanda ya kara haska fuskarsa ya kuma boye bacin ran da yake kwana yake tashi dashi tun komawarsa Katsina. Umarnin Daddy yake son bi na kauracewa Radhiya har zuwa ayi bikin gidansu sati mai zuwa a gama sannan su sake tayar da maganarta. Yana ganin wayarta da text wanda bayan kwana biyu babu reply ta dena yi. A tunaninta ya koma ga Ghazalatu ne ya manta da ita shine take kishi tayi fushi ta share shi. Matsananciyar kewarta ce ta sanya shi cewa zaiyi musu rakiya batare da an nema ba. Daddy yasan dalilinsa kuma yana tausaya masa. Lokaci guda har ya soma rama ga maganganu sunki ci sunki cinyewa a dangi.

Salame dai sakin baki tayi tana mamakin wadannan kyawawan mutane mazansu da matansu da suke fitowa daga motocin alfarma irin wadannan wurin wa suka zo? Ko sunyi batan kai ne? Kila bakin Chairman ne ko gidan Hakimi.

***********

Su Alh Ghoumar tun kafin su iso cikin garin Katsina suka sanar da Major suna tafe. Da suka zo gabadayansu sun kwana a wani hotel ne da safe shi da Alh Sidi da mutum biyu cikin 'ya'yansu suka je gidan Rtd Major Mustapha. Yayi farinciki da zuwansu ya sake basu labarin duk yadda ta kasancewa Mairama da su Radhiya. Guda cikin wadanda aka je dasu wanda shine auta a 'ya'yan Alh Sidi mai suna Ridwan yace zai maka Maikudi a kotu domin ya ha'incesu ya fada musu karya game da iyalin dan uwansu.

Major baiyi yunkurin bada hakuri ba yace idan sun dawo daga ganinsu din sai su je Sakkwaton.

"Amma meyasa baku ce a kawo muku su ba kuka taho gabadayanku?" Ya tambayesu da murmyshi a fuskarsa.

"Domin mu nunawa duniya cewa Mairama, Alheran da Zayyan dangin mahafinsu suna kaunarsu. Waye zamu samu ya rakamu saboda drebobin namu biyu ne kawai 'yan kasar nan"

Awwab kamar jira yake dama yazo gaishesu ne da Mami tace sun iso shine yace zaije. Daddy bashi da niyar hana shi saboda tausayinsa yake ji yana mamakin irin wannan soyayya mai karfi da ta shigi dan nasa farat daya.

Fitarsu daga gidan ko awa daya ba'ayi ba Mummy Gambo da Hussainar Mami suka zo. Ba da mutumci suka zo ba su Fauziyya na gaishe su babu wadda ta amsa.

"Ina babar taku?" Hussaina ta tambaya a dakile.

"Hussaina kenan, gani...kai ku bamu wuri" tace dasu Zayyana, suka tashi kuwa suka yi daki da sauri.

Zama tayi domin su gaisa Mummy ta soma fadan da ya kawota.

"Saboda wata yarinya can bare da babu wata alaka tsakaninku Hassana kike neman bata mana zumunci? Awwab da bakinsa yace yana son auren Ghazalatu amma tashi daya zance ya sauya saboda kuna son ku burge wasu"

"To banda ma abinta akwai wani abu da ita yarinyar tafi Ghazalatu ne? Alh Baba da su Babanmu sunce basu yarda ba ba sai ku hakura ba. Amma ace da kanki kuka je har gabansa don ya amince a bar danki shafaffe da mai ya yi auren gata mata biyu lokaci guda"

Daurewa take yi suna ta caba mata maganganu a ganinsu ita ma bata son 'yan uwanta su rabeta ne.

"Banda naci irin na Ghazalatu nace mata ta hakura da yaron nan taki. Wallahi ba don tana son shi ba har yanzu bazaki sake ganina a gidan nan ba. Nayi zuwan karshe ne inji menene ya sanya baki son auren nan?"

"Gambo idan Hussaina bata fahimta ba ta biye miki kun hade min kai nayi zaton ke zaki fahimta tunda mun zauna tare kin kuma san komai game da iyalin Zayyan. Wallahi da munsan da batun Ghazalatu Daddy bazai taba zancen wannan hadi ba. Ku duba irin kunyar dake tattare da ya koma yace musu an fasa auren nan"

"Ke kuma gara a kuntatawa 'yar kanwarki da yaji kunyar cewa 'yan kauye an fasa auren 'yarsu. Na tabbata 'yar dubu hamsin aka mika musu magana ta mutu har abada" cewar Hussaina.

"Ki barta tunda Umma tace mu kyalesu mu zuba musu ido daga ita har yaya Mustapha din. Saboda rashin sanin darajar zumunci kun shirya batawa da kowa..."

"Ke har zaki fada min zumunci Gambo" Mami tace rai a bace su Fauziyya suna jiyota daga daki kamar yadda Daddy yake jiyota daga falonsa da bai taso ba bayan tafiyar su Awwab.

"Kinsan me na rasa saboda zumunci? Farincikin 'yata, irin wanda kike nemawa taki 'yar amma saboda zumunci, saboda bin umarnin iyaye, saboda kada nayi sanadin rushewar ginin da iyayenmu suka fara nasa kafa na take farincikin Zahra"

Daga cikin dakin nasu Fauziyya ta zubawa yayarta ido yayin da Zahran ta fashe da matsanancin kuka.

Mami kanta hawaye take yi yadda 'yan uwanta suka gagara fahimtarta da mijinta. Komai suna yi ne domin dabbaka zumuncin amma yanzu saboda fitinar Gambo Ummansu ma ta soma fushi da ita.

"Ni Hassana banfi kowa cikinku ko cikin dangi ma haka ma 'ya'yana amma nasan cewa munyi kokari sosai wurin basu tarbiya duk da sun tashi nesa da gida. Zahra tana da wanda take so amma rana tsaka Alh Baba ya kiramu yace yayi musu mazaje ita da Fauziyya. Nafi kowa sanin irin soyayyar dake tsakanin Zahra da Raji amma na tausasheta nace tayi hakuri ta farantawa kakaninta zaiyi daidai da mune muka farantawa iyayenmu. Babu wani sabo, shakuwa ko soyayya yaran nan suka amince amma duk baku gani ba. Kullum kwanan duniya ina tashi da zulumin rayuwar da Zahra zata yi a gidan mijin da bata so. Ni da ya kamata na tayata neman farinciki nice na dage kada ta fitar da maganar ko mahaifinta bai sani ba balle 'yan uwanta. Ku har zaku fada min sanin darajar zumunci?"

Shiru suka yi aka rasa me magana a cikinsu. Basu taba ganin fushin Mami irin wannan ba. Major yana tsaye basu sani ba yana jin abinda take fada.

"Na gaji da cin kashin da kuke yi min daga ke har Hussaina akan auren Awwab. Babu wadda ta haifa min dan kuma na fada bazan taba hana shi auren wadda yake so ba. Idan yace zai iya hada duka su biyun Allah Ya dafa masa."

"Gara ki fadi abinda kike son fada zaki nuna mana kece uwar Awwab"

"Kamar yadda ke uwar Ghazalatu kike wanke kafa kika taho gidana domin taki 'yar ba. Wai ma me kuke so nayi muku ne? Ince Awwab ya zama silar kunyata mahaifinsa? Har abada bazan ce ba. Ni na san waye Zayyan a rayuwar Daddy kuma in sha Allahu bazamu ji kunyar iyalinsa ba."

"Dangin dangiro sun fimu" Gambo tace rai a matukar bace.

"Hussaina, Gambo. Ya isa haka kuzo ku wuce gidajenku"

Major ne yayi maganar idanunsa sun kankance ya fito musu a rikakken sojansa. Basu iya sake tankawa ba suka fita suka bar Mami Hassana tana zubar da hawaye. [5/22, 11:03 PM] Sis Ruky: Sabon salon make murya yayi don ya ga alamun larabawa ne mutanen nan "Assalam alaikum ya 'yan uwa. Kaifal durus wa ayna kaifal amal"

Allah Yasa akwai hayaniya a wurin kuma ya make murya ba kowa yaji ba sai Ummi da Radhiya. Kunya kamar Ummi ta nutse Radhiya kuwa juyawa tayi zata bar wurin saboda kunya ga dariya na cin ta. Malamijo ko a kwalarsa ya rinka mika hannu ana gaisawa. Ya sha mamaki ashe Zayyan yana da wannan dangi masu arziki haka amma yaron nan Maikudi ko tsinanne wallahi. Yayi musu tsakani da arziki irin wannan.

Magariba har ta kawo kai suka tashi aka rako su waje. Mammee tana kallon Ummi da murmushi tace "ni kuwa ina wani yaro nan lokacin taron sunan Alheran wanda baya son kowa ya tabata. Har yanzu ina da hotonku tare"

Ummi ta kalli Awwab tana dariya lokacin ya gane dashi ake ya zubawa Radhiya ido aka rinka dariya da Mammee tana fadin irin rigimar da aka rinka yi dashi da masu son daukar baby.

"Ina fata dashi zamu yi bikin ko?" Alh Sidi yace yana riko hannun Radhiya da ta dukar da kai.

Malamijo sai dariya "au, au, ashe anata abu bani da labari. Kai abu kyau"

Awwab ya kurawa Radhiya idanu fuskarsa dauke da murmushi ko kunya, yadda kowa sai da ya fuskanci akwai wani abu a tsakaninsu. Iyaye sai murna don abin yayi musu dadi. Sun fadawa Ummi zasu shigar da kara akan Maikudi amma sai bayan sunje musu tukunna. Bayan tafiyarsu Radhiya da wasu suka je suna kwashe kwanuka a can gefe kuma Ummi ce ta zaunar dashi da plate din abinci.

"Na kula ba ka son cin abinci Awwab. Ko yanayin aikinka ne yasa ka zama haka? Ace mutum da ance abinci sai yace baya jin yunwa"

Janyo plate din yayi yana kallon inda Radhiya ta duka tana daukar food flask. Ummi ta kawar da kai tana murmushi har sai da ya gama cin abincin sannan ta nutsu ta fara magana.

''Awwab akwai abinda yake faruwa ne a Katsina?"

Da sauri ya dago don da fari wata 'yar kunyarta yake ji.

"Me kika ji?"

"Ka fada min dai idan akwai abinda ke faruwa wanda ya kamata na sani. Gobe in sha Allah zamu bika mu tafi tare don yadda naji kukan Fauziyya hankalina ya tashi"

Wayarsa ta ga yana lalube a aljihu hankalinsa duk a tashe ta mika masa saboda ya manta ya bata dazu da aka kira. Ita kuma bata son boye masa saboda iyaye ba abin wasa bane. Ta yiwu zai iya magance matsalar a matsayinsa na babba. Yana karba ya shiga kiran Fauziyya wayarta tana chaji bata ji ba.

"Ummi akwai bayanin da nake son yi miki"

A raunane yayi maganar shiyasa kafin ya fara hankalinta ya sake tashi. Bai boye mata komai ba dangane da Ghazalatu da Radhiya da yake son hadasu.

"Ita wannan din ce take tayar maka da hankali akan bazata zauna da Ghazalatu din ba ko yaya?"

Dukar da kansa yayi nauyin maganar yasa bai iya bude bakinsa yayi mata gaskiyar bayani ba.

"A'a Ummi ta amice"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull