Batuol mamman complete novel - Chapter 38
Batuol mamman complete novel Chapter 38: Batuol mamman complete novel Chapter 38. "Ina jinka, Tureta nawa kake nufi? Wa ya aikoka? Daga ina kake?" Ya rinka…
3,375 words
"Ina jinka, Tureta nawa kake nufi? Wa ya aikoka? Daga ina kake?" Ya rinka jero tambayoyin yana jijjiga shi.
"Liberia prison, the Lieutenant is waiting"
Hularsa ya tuge bai sani ba saboda yadda ya tashi tsaye da sauri "Lieutenant Zayyan fa kace"
"1993 Liberia Peace Keeping Troop"
Zuciyarsa bugawa ta rinka yi da sauri da sauri yana tsoron kada ya gaskata maganar mutumin ya tashi yaji ashe mafarki yake yi.
"Daga ina kake?"
"Liberia Prison"
"Innalillahibwa inna ilaihi raji'un" yace gumi na karyo masa "Zayyan yana da rai dama?"
"Yace akwai Hadir ko shima yana da rai?"
Hannuwansa Excellency ya riko ya tayar dashi tsaye "nasan Hadir, nasan Mustapha, nasan matarsa da 'ya'yansa kowa yana nan"
"Ahghhhh" Chibuzor yace da kyar saboda murdewar da cikinsa yayi ga dukan da ya soma sha.
Excellency da kansa ya tallabo shi a jikinsa ya ja shi zuwa motarsa jama'arsa suna kallonsa da mamaki. Wani ne yayi karfin halin cewa
"Your Excellency kawo shi mu saka shi a motarmu"
"Noooo muje kawai" ya amsa yana kankame Chibuzor a jikinsa. Da suka isa daidai kofar shiga cikin gidan ma da kyar ya bari aka shigar masa dashi ciki. Kansa ya kulle so yake yaji gamsasshen bayani. Matarsa da Arifah a ranar suka tafi Abuja daga shi sai ma'aikata. Abinci yasa aka kawo masa yana zaune yana jiran ya gama ci ya kara yi masa bayani. Shima a nasa bangaren baya jin zai iya yin komai sai ya sauke wannan nauyin.
"Sunana Chibuzor Kalu"
"Ci abinci tukunna sai muyi magana" ya fada batare da maganar ta kai zuci ba.
"Bazan iya ba..."
Cikakken labari ya samu daga wurin wannan yaro tun daga rabuwar Zayyan dasu Hadir zuwa yanzu. Sai ga His Excellency the Executive governor of Plateau state yana zubar da hawaye. Shekaru daidai-daidai har ashirin da biyu rabon Zayyan da iyalinsa. Kurkukun ce ta fado masa yaji wani kunci yana sauka a ransa. Garin yaya bai taba tunanin komawa su duba wurare ko za'a same shi ba? To amma a gaban idonsa aka yi masa harbi guda biyu ya fadi kamar matacce.
Wayarsa ya zaro wadda mutane kakilan suke da layin ga gumi duk ya jika tafin hannunsa saboda girgiza da yayi ya soma neman sunan Major Mustapha. Bai kai ga dannawa ba ya kwabi kansa. Bincike ya kamata ya fara yi ya tabbatar ba wai ya tayar musu da hankali bisa abinda bashi da tabbacinsa ba.
**********
Kwanansu Radhiya biyu da zuwa kuma gobe Tante da Yousuf suke sa ran tafiya Nijar. Jiya da Ummi tace suje gidan Daddy Haroun kafin lokacin fitar tasu dreban Major ya kawo rahoton wahalar mai da aka fara tun daren jiya shima bai sami labari da wuri ba. Yawancin masu ababen hawa kowa yana kan layin mai ko kuma ka daure ka saya wurin 'yan bumburutu idan kana da hali. Awwab na ji yace idan sun fita sai suyi full tank a wurin nasu. Raji ya nemi fassarar bayani a wurin Zahra da ta kawo masa dankadafinsa Femi ta fada masa da turanci. Sai cewa yayi wai yana son yayi experiencing bin layin mai irin wannan. Shi da kanwarsa a Germany aka haifesu kuma bai taba katarin samun wannan matsalar ba a duk zuwansa Nigeria.
"Raji ba fa wurin shakatawa bane, nima ban taba bi ba amma nasan labarinsa. Wahala ce kawai harda fada wani lokacin"
"To ba sai mu kafa tarihi ba" cewar Yousuf da yake jin hausa sosai kasancewar babansa ba yarensu daya da Nasara ba. Hausar Nijar suke yi mai kamanceceniya da Sakkwatanci.
"Gaskiya ba dani ba" Awwab ya fada zai gudu daga falon saboda ya ga zasu jajibo masa wahala baiji ba bai gani ba.
Magana har wurin Daddy saboda Raji ya matsa wai yau daya dai su dana. Ba don yaso ba aka ce ya tuna bakinsu ne ya karramasu da abinda suke so. Sai da suka yi la'asar suka bar gidan. Raji yasa Zahra ta hada masa 'yar jaka da irin pillon nan na matafiya a jirgi na kafada, abin rufa, touch light da 'yan kayan ciye ciye. Awwab da baya son zuwa sai gashi yana dariyar mugunta. Wai shi nan Raji hango abin yake kamar wani picnic ko camping. Yousuf ma da nasa shirin suka shige mota Awwab ya bi bayan dreban da daya motar.
Sa'arsu daya yau tun safe garin dama da hazo da sanyi sanyi ba kamar jiya da suka iso ba. Amma fa abu tun ana dariya sai gasu sunyi kicin kicin da fuska zukata sun matso kusa. Layin mai ma ana alfarma. Ga rigimar cin layi da dai sauran abubuwa marasa dadi da kan biyo bayan zama a layin mai. Layi har dare ko tafiya suka ce zasu yi yadda wurin ya cushe da wahala su sami hanya ta dadin rai. Haka suka zauna dare ya gabato sauraye suka ce salamu alaikum sanyin da zai koresu bai kankama ba gara suma suyi full tank. Dukkansu jikinsu ya fada musu kuwa. Ba su suka koma gida ba sai hudun dare. Zahra da Ummi ne kadai ido biyu. Take taken Raji na makalewa Zahra yana ta korafin wahalar da yasha yasa Awwab bin Yousuf bangaren Ummi yana girgiza kai. Zahra na ta zillewa amma yaki barinta. Awwab na jin yana cewa da a gida suke wanka yake so ta taimaka masa yayi ya dauki kayan bukatarsa ya fita. Baya son ganin abinda zai dame shi yazo yana jin kunya shi da kanwarsa su zama surukan juna. Gara ya basu wuri ko yaya ne ta kula da mijinta. Radhiya ce ta fado masa a rai lokacin da yake kwanciya a kan bargon da ya jefa a kan kafet din dakin Emzee ya buga tsaki shi kadai yana ayyana wai ta cuce shi da yanzu shima...kwafa yayi kawai ya kwanta.
"Kasan babu dadi ko? Ka dawo nan gadon zai ishemu" Yousuf yace da ya jiyo tsakin.
"Its okay mantuwa nayi mai mahimmanci, kaji ina tsaki ko" a rayuwarsa babu abinda yake masa wahala kamar kwanciya kusa da mutane. Sai yayi ta ganin kamar zai takura musu kuma shima baya son tasu takurar.
Karamar dariya yaji Yousuf yayi yana cewa "Raji yayi mana wayo. Mun sha wahala tare wato shi mai mata ya gudu"
"Kai me kake jira" Awwab ya tambayeshi cikin duhun dakin yana fata kada yace abu guda suke so. Yinin yau kadai Yousuf din ya kwanta masa akwai ilimi amma a wani kamfani yake aiki ba likita bane. Ko me yasa jiya yaji Mama tace likita?
"Da dai na fara shiri amma na kula kamar bazai yiwu ba." Yanayin maganarsa zaka san abin baiyi masa dadi ba sai dai a rayuwarsa bai yarda da cusa kai inda ba'a nemansa ba. Yana son Radhiya kuma kanwa ce gareshi har kullum amma jiya shi kadai yasan me ya gani suna yi da sunan cin abinci.
"Allah Ya musanya maka da mafi alkhairi"
"Amin, amma meyasa nake ji kamar kasan da wa nake?" Ya kuma yin dariya.
Wayancewa yayi shima yana dariyar
"Ban sani ba fa...kawai fatan alkhairi nake maka"
"Sai ka tayani nema tunda kasan irin wadda nake so"
Abin rufa Awwab yaja ya rufe kansa yana dariya lokacin da Yousuf yace kuma idan ya cigaba da jan rai zai ji ana biki a Nijar. Yasan so yake ya nuna masa ya gano wa yake so, shi kuma sai yaji kunya kada ya nuna abinda zai iya sosa ran Yousuf din. Da kyar suka yi sallar asuba jam'i su biyu don sai da aka idar Awwab ya iya farkawa saboda gajiyar da suka tara.
***********
Yau da Radhiya akayi aikin breakfast ita da Ummi suna yi tana kara yi mata bayanin project dinta. Abin ya kayatar da Ummi matuka tace me zai hana tayi magana da Daddy sai a nema mata alfarmar samun adireshin wasu daga cikin matan da suka zauna tare a Sakkwato wadanda mazansu suka rasu ta saka su a sashen shirin nata da ta kira da (Hidden Heroes).
"Ummi kece ta farko a cikinsu sai dai bazan iya saka ki a ciki ba saboda kuka zamuyi ta yi" tace da kwalla a idanunta.
Da murmushinta mai ciwo tace "Allah Ya jikan Daadaa dinku. Halinku kadan ne da bambanci. Shi baya shagwaba irin wadda kika koyo wurin Nasara sai dai ya shagwaba wasu"
Dan tsalle tayi tana son hirar babanta "Ummi yana shagwabani?"
"Kamar ba gobe" ta amsa mata tana tuno rayuwarsu ta da murmushi na kufce mata.
"Kema yana shagwabaki ko?" Ta tsare Ummin da idanu tana daga gira daya da wani dan banzan murmushi.
"Kaniyarki, fita ki bani wuri" ta biyota da cokalin miya. Dariya ta saka ta gudu daki.
"Na fa zata ta kintsu ashe nutsuwar ta karya ce" Ummi ta cewa kanta ita kadai tana girgiza kai. Mai hali baya fasa halinsa.
Yau ma atampa ta saka amma riga da skirt. Ita kadai take juyi a gaban madubin bayan ta gama kwalliya ta karkata nan ta karkata can tana turo baki.
"Fita mana kije kiyi a gabansa sai ya fada miki inda yake bukatar gyara idan akwai"
Ta madubin ta harari Fauziyya kamar idanu zasu fado ta zagaya karbar Jawad zata shirya shi Fauziyyan tayi wanka sai ga Zahra kamar an korota ta shigo da sauri kana ganinta farkawarta kenan.
"Jama'a na shiga dubu a gidan nan yau"
"Me ya faru Adda?"
Kasa fada tayi wai saboda Radhiya ba aure gareta ba.
"Babu komai dai"
"Ina fa babu komai dazu Mami ta aiko Zayyana da Femi wai tana ta zuba ido jiya da daddare kije ki karbe shi taji shiru ko kinzo kin kwanta ne kin bar mata shi. Bai dade da komawa bacci ba yana dakin Ummi"
"Duk dad dinshi ya ja min" tace kamar tayi kuka.
Fauziyya ta zauna a gefen gadon kusa da ita harda rage murya za'ayi gulma "kwana kika yi a can tare dashi?"
Duka ta daka mata a cinya kafin tace "dawowa yayi fa duk cizon sauro yayi wani iri...daga hada masa ruwan wanka bacci ya daukeni"
"Allah Sarki...kinsan bacci babu ta yadda baya zuwa. Ina fata dai kinyi ya isheki" Fauziyya tace tana dariyar ta dago me ya sami yayartata.
Radhiya taji sun sakata a duhu ta kasa fahimtar me suke nufi ga son jin zancen na cinta tace "don Allah kuyi min bayani dalla dalla"
"Ke da wannan bayanin sai a gidan Hamma" Fauziyya ta sake yin dariya. Bakinta ya kara budewa ta zama mai tsokana sosai.
"Me? Aure zaiyi? To ni ina ruwana ai dai ba zuwa gidan zan rinka yi ba" tace tana bata rai.
"Nasan ba fahimta zakiyi ba dama. Shirya Jawad ga kayansa nan zanyi wanka."
Hannu ta mika zata dauki yaron ya zille ya koma wurin mamansa ta kuwa harare shi kamar sa'anta ta fice daga dakin tana mita.
"Yara ku cigaba da yi min kyuya sai na baku mamaki. 'Yan mata zan rinka haifa in hanaku aurensu"
"Allah Ya tashemu zaki fara ko, ke da wa kuma?" Ummi tace ta fito da Femi ya farka yana neman mamansa.
"Jawad mana Ummi. Wai ni suke yiwa kyuya shi da Femi."
"Baki iya yi musu yadda zasu sake dake bane. Harararsu fa take yi Ummi"
Faduwar gaba taji tun da ya fara magana. Tabbas taji wannan kamshin mai shiga ko ina a jikinta yana tasiri amma duk a zatonta ya shigo ya fita ne. Ashe yana tsaye ne a bayanta da kofin kunu a hannu. Diba yayi zai koma daki ta fito tana mita.
Tayi matukar kyau kayan sun kara fito da ita. Rashin sanin yana wurin karamin mayafi ta yafa da ya dan zame baya yadda gaban gashinta da ta daure da ribbon ya kwanta ya bayyana.
"Kuma gara ta koya tun wuri don ni dai babu mai kawo min ajiyar 'ya'ya" Ummi ta fada tana kokarin barin wurin.
"Ummi kawo shi ki gani" ta zura hannu zata karbi Femi dan albarka sai ya yarda "kin gani ko..."
Zahra ce ta bude kofar dakin a lokacin yana ganinta ya soma kuka yana mika hannu da zillo. Radhiya taji kamar zai fadi ta mika mata shi. Tana karbarsa yayi shiru harda dora kansa a kafada ta shiga shafa masa baya.
"Nima dai inzo in haifi nawa su rinka like min ina muku yanga"
Ummi kada kai tayi ta fita tana murmushi da taji me take cewa. Sai yanzu Mama tayi mata wayar baby ya tashi don Ummi bata tashinsa yin wanka sai dai ta jira shi wai duk cikin 'ya'yan nasu shi tafi so dole ayi masa yadda yake so ba takura.
"Waye ya fada miki yara masu likewa iyaye dadi ne dasu?"
"Ba gashi kuna gayunku ba ke da Maman Jawad"
"Allah Ya baki muna gefe ai musha kallo. Wa yaga Radhiya da baby" Zahra tace tana komawa dakin domin bawa Femi abinci.
Satar kallon Awwab tayi da yake tsaye a bakin kofar dakin Emzee tun dazu ya tokare kafarsa da bango ya jingina. Hanyar fita tayi ya dakatar da ita.
"Kinyi breakfast ne?"
"Bana jin yunwa" tace a takaice.
"Realy? Kwaikwayona kika soma yi kenan" yace yana matsowa inda take tsaye. Yadda take ganin yayi matukar kyau haka shima yake ganinta.
"Kai ba gashi zaka sha kunu ba" ta dan tura baki tana lumshe idanu.
"Na Yousuf ne..nima bana jin yunwa" ya sami kansa da cewa.
Kawai don kada ya yarda shi take kwaikwayo har ya fassarata ta dauko kofi a cikin wata drawer mai kyan tsari dake gefen dinning table ta zuba kunu.
Gefenta ya tsaya ya rage murya tana jin wani abu na kwasarta "ki dena yi mana addu'ar yara masu kyuya don nima ina da son kulawa kada su rinka shiga lokacina"
Ta riga ta gama zuba kunun ta ajiye flask din da babu abinda zai hana ta sake shi yadda ta saki teaspoon din hannunta jiki na rawa saboda mamakin kalamansa.
"Careful and please kisa babban mayafi" yace yana kashe mata ido sannan ya ajiye mata kofin hannunsa ya dauki wanda ta zuba yayi gaba ya barta da bude baki.
Jiki a sake ta zauna zuciyarta da gangar jikinta suna neman karkata akalar tunaninta daga basarwa da jan aji zuwa sake fadawa cikin soyayyar Hammanta da bata taba fita a ranta ba. Ta dade da fahimtar manufar Yousuf a kanta amma sai tayi kamar bata sani ba saboda bata jin akwai wanda zata iya sakawa a gurbin da Awwab yake zaune cikin zuciyarta. Kwantar da kanta tayi akan table din tana bubbuga kafa "wai ni nake wahalar dashi ko shi yake wahalar dani...ahhhhhhh sai na rama nima"
Ta fuskanci da gangan ma ya fadi maganar don yasan me zata yi mata. Shikenan a tafi a haka zata sake dammara don so take taji ya fada da bakinsa yana sonta kafin ya koma aiki. Kai so take ya sota fiye da yadda a baya yayi ikirari. Yaji ta a ransa kamar yadda take jinsa a nata. Kwalla taji ta taru a idonta...soyayyar da take yiwa Awwab kamar tafi karfin kirjinta take ji lokuta da dama. Amma shine ya iya shareta duk tsahon lokacin nan kawai don tabi umarnin Ummi a abinda yake gyara ga zumuntar danginsu. Don dai yayi sa'a tana son shi ne amma ba hakura zata yi ba idan ba sai ta rama. Ta nanatawa kanta kafin ta dauki kunun da ya ajiye mata ta shanye duk da ya huce sai dumi kawai.
Karfe uku suka firfito Daddy yace su biya har Asokoro gidan Plateau state government house su gaishe da maman Arifah da take ta cigiyarsu. Taron matan gwamnoni ta taho Arifah tayi mata rakiya.
Dakin Ummi taje shiryawa ta samu ta sanar da Tante gidan wa zasu je fa.
"Kada kice min tsoronsu kike ji saboda abinda ya taba hadaku"
"Ni bana son zuwa ne kawai" tace a sanyaye da gaske tana jin karayar zuciya.
"Ina sojan 'yata ta shiga ta bar min wannan mai tsoron? Sunyi zaton suna da abinda zai kaiki kwadayi ne ina ga tun farko shiyasa suka kara rainaki."
"Duk fa akan Ghazalatun nan ne"
"Ai da baifi da ba amma Mairama tayi musu kawaici don a zauna lafiya. Ki saki jikinki in kunje idan ba haka ba za'ayi aurenku ne kina kin shiga dangin miji?"
Shagwabar ce ta motsa tace "Ni nace zan aure shi ne Tante?"
"Baki ce ba shiyasa tunda na kula Yousuf dina na sonki zan fadawa Papa"
Tashi tayi da sauri zata gudu Nasara ta rinka dariya tace ta saka kayanta ta gani. Tana taimaka mata ta shirya tana bata sirrikan sake janyo Awwab gareta "idan na gaji da gulmar taku zaki wayi gari watarana kawai a kaiki gidansa an daura aure kuna bacci"
"Kamar wata 'yar tsana"
"Yi sauri kafin Mairama ta shigo ta fara mana fada daga ni har ke"
Abaya ce ta gani a fada kalar lilac mai ado ruwan madara. Duwatsun jikinta kadan ne ba irin mai daukar ido daga nesa ba an jera su sunyi zagaye zagaye daga wuya har kasa a tsaye ta tsakiya. Gefen mayafin ma haka yake sai dai kafin tayi rolling sai da daura wani karamin dankwali saboda wancan yana da santsi kada ya zame ga maikon kanta. Kayan kwaliyar Laura Mercier take amfani dasu. Tayi light make up dinta tasa janbaki nude bayan tayi lining lebenta da lip liner purple. Sai ya tashi ya bada wata kala mai kyau. Wani killer smile ta saki tana kallon Tante tana gode mata a ranta. Matar nan ba karamin kulawa da gyara take bata ba. 'Ya take yi da ita da zuciya daya shiyasa itama ta bata matsayin da ya kamaceta na uwa.
Garin yayi lufluf sanyin bai fara hana sukuni ba. Takalminta heel ne shiyasa tana tafiya taku daidai irin na matan da suka san kansu ta fito da karamar sling bag wadda babu komai sai tarkacen su hoda da wayarta a hannu.
Tun daga kofar gidan Mami da suke jiranta saboda motocin a can aka ajiyesu Awwab yake kallonta ya kasa dauke ido. Wani mahaukacin kishi ne ya taso ya rufe shi da ya ga kamar duka hankula suna kanta ne. Itama shi take kallo tana murmushin da yake kara susuta tunaninsa. Gaskiya motar da zai ja yake so ta shiga ta zauna a kusa dashi. Da ka yayi mata alamar ta taho ai kuwa ta nufi motar. Sai da ta tsaya a gaba kamar zata bude ta juya wurinsu Fauziyya.
"Adda wannan zaki tuka?"
"Wannan Hamma ne zai ja"
"Ohhh" ta juya ta koma jikin daya motar ta shiga baya ita da Zahra da Femi. Gaba kuma Zayyana ce da Jawad sai Fauziyya da zata ja su.
"Rufe bakin mana loverboy" Raji yace da turanci suka tafa da Yousuf suna yiwa Awwab dariya. Wai shi zata yiwa haka ta sa masa rai ta basar. Ba don gudun fadan Ummi ba da babu inda zai je saboda bashi da kuzarin tukin ma. Wani kallo ya watsa musu suka sake kwashewa da dariya sannan suka shiga motar yana gaba Fauziyya na binsa a baya.
"Radhiya ba sauki yau kin motsa mana Hamma. Jikina yana bani kamar da wuya ki koma France babu aure fa kila ma da dan guzuri"
Zahra ce ta zunguro Fauziyya rainon Mama zata yi barin zance a gaban Zayyana. Jinsu kawai take tana murmushi da kewar 'yan uwanta Ibrahim abokin fada da Emzee mai lallabata. Da suna nan ko kallon wannan motar bazata yi ba. Radhiya tayi murmushi kawai zuciyarta fes. Masu sayar da irin lemukan nan da ake saka kankara a leda ta hango maltina yawunta ta tsinke. Da can bata iya sha har cewa suke giya ce. Zuwanta na karshe ta dandana shikenan ya zama abin shanta har da guzuri da zata koma.
"Adda don Allah saya min maltina"
"Wacce a ciki? Nima fakiriya ce irinki babu chanji a hannuna" Zahra ta amsa mata.
Dan turo kanta tayi gaba "Adda Fauzinmu taimaka"
"Ni da kika ki shirya min yaro harda harara"
"Yanzu kullata ta kika yi a ranki kamar ba babba ba? An dai yi abin kunya"
Yadda tayi maganar yasa su duka dariya. Zahra tace "Wani idan ya kalleki a haka dai zai ce irin high class babes dinnan ne. Sai an zauna dake a gane ashe 'yar soja ce mai balotelli"
Rokon maltina ta cigaba duk junction amma Fauziyya taki saya.
"Ki roki Hamma idan mun tsaya"
"Roko zaki koya min?" Ta zaro idanu.